Jerin littattafan ƙagaggun labaran Hausa na farko-farko

Mutane 1971 sun karanta wannan.

A makalun da suka gabata mun rigaya mun kawo muku tarihin samuwar ƙagaggun labarai na Hausa da yadda rubutu ya samu ci gaba tun daga Ajami zuwa rubutun book. Har ila yau mun kawo muku irin gudunmawa da marubuta da kamfanoni da gungiyoyi suka bayar wajen bunkasa littattafan Hausa. A wannan makala zamu jero muku sunayen littattafai da mawallafansu wanda aka buga daga shekarun 1960s har izuwa 1980s kamar yadda ya zo a Yahaya (1988).

Ga jerin sunayen kamar haka:

S/No Sunan littafi Sunan mawallafi Shekarar
1. Ruwan Bagaja A. A. Imam 1933
2. Ganɗoki M. B. Kagara 1933
3. Idon Matambayi M. M. Gwarzo 1933
4. Shaihu Umar A. A. T/Ɓalewa 1933
5. Jiki Magayi Shekarar T. Wuasas da R.M East 1933
6. Iliya Ɗanmaiƙarfi Ahmadu Ingawa 1933
7. Magana Jari ce 1-3 A. A. Imam 1937
8. Yawon Duniya Hajji Baba A. Tunau 1966
9. Da’u Fataken Dare Tanko Zango 1959
10. Ban Dariya A. B. Ahmed 1958
11. Gandun Dabbobi Bala A. Funtua 1975
12. Dare Dubu Da Ɗaya M. Kano da Edgaer 1933
13. Littafin Mamaki M. M. Kumashi 1954
14. Iblis Ɗan Lis M. M. Mairiga 1959
15. Nagari Na Kowa J. Abdullahi 1959
16. Tauraruwar Hamada S. A. Daura 1959
17. Tauraruwa Mai Wutsiya U. Dembo 1969
18. Dare Ɗaya A. Ka’oji 1973
19. Duniya Tumbin Giwa I. Y. Muhammad 1973
20. Gimbiya Sakinatu I. Y. Muhammad 1974
21. Muƙamar Abu Zaidi (1-5) A. I. Argungu 1959
22. Duniya Ina Zaki Da Mu? A .N. S. Wali 1971
23. Gonar Dabbobi Inuwa Garba 1971
24. Gari Ya Waye M. B. Umar 1977
25. Masu Hikima Sun Ce A. B  Ahmad 1958
26. Shararrun Hiƙayoyi Huɗu ———— 1958
27. Sauna Jac J. Hare 1975
28. Littafin Mafarki S. Gamagira 1963
29. Wannan Zamani Da Wuya Yake U. Ringim 1971
30. Kitsen Rogo A. Ɗangambo 1979
31. Gogan Naka Garba Funtua 1979
32. Abokin Hira 1- 2 A. H. Aliyu 1978
33. Ba Ruwan Maza Da Wankan Biƙi A. A.  Aminu 1968
34. Sihirtaccen Gari A. Katsina 1978
35. Baki Abin Magana I. Y. Muhammad 1976
36. Ladi Da Ƙare Da Guguwa U. I.  Galadanci 1984
37. Aljanar Bishiya U. I.  Galadanci 1984
38. Aljanar Kabewa U. I.  Galadanci 1984
39. Umma Da Giwa U. I.  Galadanci 1984
40. Gaskiya Dokin Ƙarfi    S. U. Abdullahi 1985
41. Jagorar Fahimtar Malam Aminu Kano S. U. Abdullahi 1982
42. Robin Hood 1958
43. Robinson Kuruso D. Defoe 1958
44. Baran Mancuzan R. E. Raspe 1958
45. Maƙesu Mai Kirki D. Jolly 1976
46. Kunnenka Nawa? I.  Zakariya 1981
47. Jumhuriyar Gurguzu Ta Bulgaria A. Anwar 1982
48. Mulkin Soviet Da Muƙamin Manoma V. I.  Lenin 1979
49. Tsuntsu Mai Farin Kwiɓi J. A. Tafida 1980
50. Kwaɗo Matafiyi V. Garshin 1980
51. Sauna Da Ɓarayin Banki Ɗan Fulani 1982
52. Sauna Ɗan Sanda Ɗan Fulani 1982
53. Sauna Ya Kuɓutar Da Su Ɗan Fulani 1982
54. Sauna Da Masu Sayar Da Ƙwaya Ɗan Fulani 1982
55. Duniya Budurwar Wawa Ɗan Fulani 1982
56. Magana Ba Kaya Ba I. Y. Muhammad 1977
57. Ƙwal Uwar Ɓari (1-2) I. Y. Muhammad 1977
58. Tafiyar Goga Tsibirin Lillifa Inuwa Dikko 1983
59. Tsaka Mai Wuya Ƙamaruddeen imam 1983
60. Tsalle Ɗaya Idris Imam 1983
61. Kowa Ya Kwana Lafiya Shi Ya So Ɗan Fulani 1985
62. Gishiri (1-3) Ɗahiru Bebeji 1986
63. Niyya Ba Ta Ga Rago C. Sanderson 1914
64. Kuɗinmu Sun Ƙare 1946
65. So Aljannar Duniya Zainab Abdulwaheed 1980
66. Ahmadi  Na Malam Amah Magaji Ɗanbatta 1980
67. Mallakin Zuciyata, Sulaiman Ibrahim Katsin 1980
68. Zaɓi Naka M. M. Katsina 1982
69. Tsumagiyar Kan Hanya M. M. Bello 1982
70. Ƙarshen Alewa Ƙasa B. Gagare 1982
71. Turmin Danya Sulaiman Ibrahim Katsin 1982
72. Tura Ta Kai Bango Sulaiman Ibrahim Katsin 1983
73. Tafiya Mabuɗin Ilmi A. A. Imam 1944
74. Sidi ya Shiga Makaranta U. Ladan 1981

Akwai ƙagaggun littattafi da dama da aka rubuta bayan wadannan kamar yadda muka yi bayani a wannan makala ko kuma wannan, musamman lokacin bunkasar kasuwar adabi ta Kano.

In Allah Ya yarda zamu ci gaba da bincike mu dora akan wadannan a duk lokacin da muka samu dama.

Manazarta

Yahaya, I.Y. (1988) Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa: Ibadan: University Press Plc

Wanda ya rubuta: Lawi Yusuf Maigidan Sama, daga Jalingo, Najeriya

3 thoughts on “Jerin littattafan ƙagaggun labaran Hausa na farko-farko”

  1. Slm, Da fatar alheri. Da Allah ina cigiyar sunayen wasu littattafan adabin kasuwar Kano masu labarin tatsuniya a ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *