Skip to content
Part 25 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Present

A rayuwar shi bai taɓa sanin menene asalin ma’anar kalmar wulaƙanci ba sai da ya je NDA, kamar yadda ba zai ce ga tun lokacin da yake son saka uniform ɗin Sojoji ba. Sai dai shi mutum ne da idan ya sa abu a ranshi, wahala ko makamancin hakan baya hanashi cimma burin shi. Zai iya rantsewa a ‘yan shekararsu babu wanda ya sha wahalar da ya sha a NDA, daga horo zuwa jibga, akwai lokuta da dama a shekarar shi ta farko da bai yi tunanin zai gama NDA da ran shi ba. Saboda bai iya tauna magana kafin ya faɗeta ba, kuma bai iya yin shiru idan yana tunanin akan gaskiyar shi yake. Abin da ya ja mishi tsana da ƙauna daga wajen manyan shi.

Zai iya cewa kwana biyar ɗin da ya yi ba komai bane akan irin wahalhalun da ya sha a baya. Abin da ya bambanta da sauran lokutan shine, ba shi ya yi laifin da kan shi ba, kuma yanzun da yake hanyar shi ta zuwa gida zai shiga gidan ba tare da ya ga Waheedah ba, kuma ya yi kwanakin biyar da tunaninta cunkushe a kan shi, ranakun da suka yi mishi wani irin tsayi na ban mamaki. Sabon da ya yi da rashin wanka na tsayin lokaci idan aiki ya kai su wajajen da babu nutsuwar yin hakan bai hanashi jin wari da ƙarnin jinin da yake yi ba.

Ko sallama bai yi ba lokacin da ya shiga gida, ɓangaren Nuriyya ya wuce, don haka ko kaɗan bata tsammaci shigowar shi ba. Ta ɗauka auren Anas shi ne babban tashin hankalin da ya faru da rayuwarta, sai kwanaki biyar da suka wuce da ta dawo gida tana rasa inda za ta saka rayuwar ta ta ji sanyi. Da zazzaɓi ta wuni, ta kuma tashi da shi ganin har an kwana ɗaya Abdulƙadir ɗin bai dawo ba, ta yi tunanin zuwa gidansu ta sanar da su halin da ake ciki, amma ta rasa samun ƙarfin gwiwar yin hakan. Wanda duk suke ɗan son ta a gidan su Abdulƙadir ɗin sanadin Waheedah ne dama, tun bayan auren ta da Abdulƙadir babu wanda ya sake ko kallon in da take ballantana magana ta haɗa su.

Ta gwada zuwa gidansu Abdulƙadir ɗin sau ɗaya, tunda Hajja ta amsa mata gaisuwa bata sake ce mata komai ba, ta muzanta fiye da tunani ranar, don har kuka ta yi bayan ta fito, bata kuma sake marmarin komawa ba. Babban tashin hankalin da ta shiga shi ne tunanin abin da zai biyo baya da fitowar Abdulƙadir ɗin, ta kira lambar Waheedah bata san adadi ba, amma a kashe, don ta san in ta faɗa mata za ta gayawa ‘yan gidansu Abdulƙadir ɗin a yi wani abu a kai. Hankalinta in ya yi dubu a tashe yake da ta ga kwanaki na tafiya babu alamar Abdulƙadir ɗin.

Yaune ta yanke hukuncin ko me su Hajja za su yi mata za ta je ta same su, don in su basu kashe ta ba, zullumi zai kashe ta, ko abinci ta ɗan samu ta dafa, plate ɗaya haka za ta wuni tana jagalar shi. Ta yi zuru-zuru ta fita hayyacin ta, ko hankalinta a kwance yake sai ta yi kwana biyu bata share ɗakinta ba, shi ma idan Abdulƙadir na gari ne sai ta yi shara ta gyara gado. Da ya tafi kuma tana haɗa sati ɗakinta bai ga tsintsiya ba, yanzun kuwa a kwanaki biyar ɗin nan ko wanke-wanke bata yi ba, falon a hautsine yake da gwangwanin lemuka da robobin ruwa, don tun da ta zo gidan shi rabon ta da shan pure water, in ya bata kuɗi ruwan roba take zuwa ta siyo.

Ita kanta rabonta da wanka tun jiya, duniyar take ji ta haɗe mata waje ɗaya. Yanzun da Abdulƙadir ɗin yake a gabanta, wata irin ajiyar zuciya take saukewa da bata san daga inda take fitowa ba, ta ɗauka hawayenta sun gama ƙarewa, sai yanzun da ta ji idanuwanta sun ciko taf da hawaye. Bata taɓa tunanin baƙin mutum zai iya ƙara baƙi ba sai yau, duk kumburin fuskar shi bai hana idanuwan shi yin zuru-zuru suna ƙara shigewa ciki ba. Gashi ya yi wani irin duƙun-duƙun. Kallon ta kawai Abdulƙadir ya yi yana wucewa cikin ɗakin baccin su, kai tsaye banɗaki ya wuce yana cire kayan da ya san sun riga da sun tashi aiki.

Banɗakin yake gani ya yi mishi kaca-kaca, ga kayan wanki saman injin wanki har da jiƙaƙƙu, wanka ya yi, ya saɓa jikin shi da sabulu ya fi sau biyar amma duk da haka jin shi yake kamar akwai sauran dauɗa a jikin shi. Towel ya ɗauka yana goge jikin shi ya ɗaura shi a ƙugun shi ya fito, idan ya ce ga asalin abin da yake ji ƙarya yake, don baya jin komai, zafin dukan da yake jikin shi, ko ɓacin rai, shiru komai yake mishi. A karo na farko da ko ganin Nuriyya ɗin bai saka shi jin komai ba. Ban da Waheedah babu abinda yake cikin kan shi. Takawa ya yi yana fita daga ɗakin, a tsaye bakin ƙofa ya ga Nuriyya tana kallon shi.

“Masoyi…”

Ta faɗi muryarta na rawa, fuskar ta da bayyanannen tsoro. Idanuwan shi Abdulƙadir ya ƙanƙance a kanta yana ƙara saka tsoro cika zuciyarta.

“Don Allah… Don Allah ka yi haƙuri… Ka ji… Ba zan sake ba…. Don Allah karka sake ni, kai min komai karka sake ni, don Allah…”

Numfashi mai nauyi Abdulƙadir ya sauke, da gaske yake baya jin komai, ciki har da magana da ita, wucewa ya yi da nufin ƙarasawa ɓangaren Waheedah ya ɗauki kayan da zai saka. Bin bayan shi Nuriyya ta yi tana kamo hannun shi, gaba ɗaya shirun shi ya ƙara rikita ta.

“Masoyi…”

Tsaye Abdulƙadir ya yi ba tare da ya juyo ba, hannun shi yake ƙoƙarin zamewa daga cikin nata, ta sake kamashi tana matsawa ta zagaya ta fuskance shi, wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, tana saka shi tuna yadda ko kaɗan bata san shi ba, da ta ƙyale shi, ta nemi waje ta zauna, da bata tsaya a gaban shi tana mishi kukan da bai ga dalilin shi ba. Numfashin ya sake saukewa.

“Kaji… Don Allah ka yi haƙuri… Don Allah… Wallahi ba zan sake ba.”

Nuriyya take faɗi kuka mai ƙarfi na ƙwace mata, hannun shi Abdulƙadir ya zare daga cikin nata, yana raɓa ta ya wuce, jin takun tafiyarta yasa shi juyawa.

“Ban ce kin min wani abu ba, ban miki magana ba saboda bana son yin magana da kowa, ki ƙyale ni Nuriyya, ki ƙyale ni kafin mu samu matsala…”

Abdulƙadir ya ƙarashe maganar yana juyawa ya wuce, da idanuwa Nuriyya ta bi shi, za ta ce yana da wata irin kula da ko a tunaninta ba ta yi zaton za ta samu a gidan aure ba, abinda duk ta nuna tana so yana ƙoƙarin yi mata, idan kuɗi ta tambayeshi yana bata, wani lokacin yana ce mata ba shi da kuɗin da zai bata ta kashe, akwai hidimar da zai yi. Sai dai akwai ɓangaren shi da take jin bata sani ba, sannan mutum ne shi mai wahalar sha’ani duk da ba sosai zaman su yake tsayi ba, in ya dawo kwana biyu ne , ita ɗaya, Waheedah ɗaya, amma za ta yi ƙarya idan ta ce bata takura da kwana ɗayan.

Bata cika tsawaita tunaninta akan abin bane kawai, amma Abdulƙadir ɗin da Waheedah kan yi magana da shi ko da yaushe daban yake da ita wanda take gani. Abdulƙadir ɗin Waheedah namiji ne da ko a littafin Hausa bata jin akwai irin shi, don mazan littafin Hausa miskilai ne, Abdulƙadir ɗin Waheedah ba haka yake ba, Abdulƙadir ɗin Waheedah kan mata abu ba tare da ta tambaye shi ba, yana girmamata fiye da yadda take nunawa, don Nuriyya da idanuwanta ta ga hakan. Abdulƙadir ɗin Waheedah ba shi da wani hali marar kyau, ita shi ne mutumin da take so, mutumin da ta yi tunanin ta aura.

Sai bayan auren da ta fara cin karo da kashedi a darenta na farko ta ji zuciyarta ta tsinke, sai kuma lokuta da dama da zai yi tunanin ta yi mishi abu ta yi ƙoƙarin bayani ya rufeta da wani irin faɗa mai cin rai, ƙananun abubuwa masu tarin takaici da ba za ka gani daga nesa ba, ko kuma take tunanin Abdulƙadir ɗin Waheedah ba zai taɓa yi ba, sannan yana surutai cikin baccin shi, yana firgita sosai, ranar farko da hakan ta faru tsoron shi ta dinga ji, musamman da ta yi ƙoƙarin taɓa shi bayan ya farka ya hankaɗeta yana mata wani irin kashedi da har yau bata sake ƙoƙarin zuwa kusa da shi in yana surutan shi a bacci ba.

Abdulƙadir na da matsalolin da take da tabbacin bata gama gani ba. Sai dai bata san ita kaɗai yake nunawa ba, ko har da Waheedah. Falonta ta koma ta zauna tana jin wasu hawaye masu ɗumi na zarya kan kuncinta. Ita dai yanzun koma me zai yi in dai ba zai saketa ba da sauƙi.

*****

Abdulƙadir yana sake kaya, ɗakin Nuriyya ya koma ya shiga banɗaki yana ɗaukar wandon da ya cire ya zaro wayarshi da wallet, wayar da take a kashe ya kunna yana fitowa. saƙonni ne guda biyar suka shigo tana gama loading, buɗewa ya yi, biyu daga MTN ne, ɗaya bankin shi ne , ya san albashi ne, biyu kuma Yassar ne, ya shiga na farkon,

‘Lafiyar ka kuwa? Wayarka a kashe. Duk da ba ina so ka zo ka dame ta bane, lafiyarka ko?’

Fita ya yi yana shiga ɗayan.

‘Ka kashe wayarka ne, ka yi shiru don in ɗaga hankalina in goyi bayanka ko Abdulƙadir? Ya yi maka kyau.’

Murmushi ya ɗan yi duk da nishaɗi na ɗaya daga cikin ƙarshen abin da yake ji. Wallet ɗin shi ya saka a aljihun shi. Ya samu waje gefen gadon yana zama, don da ya ga albashin shi baya so su kwana bai yi hidindumun da zai yi da su ba. Waheedah ya fara tura wa kuɗin nata hidimar na wata kamar yadda ya saba, sannan ya tura wa Nuriyya ma, sai ya tura wasu cikin account ɗin shi na ajiyar kuɗin tsaron lalura. Ya tura wa Abba da Hajja. Kati ya tura wa sauran ‘yan gidan kamar yadda ya saba duk watan duniya, ko yayane yakan tura musu. Wata natsuwa ya ji ta daban da ya sauke wannan nauyin.

Wancan watan da ya fita ya ƙaro musu kayan abinci, don shi yake siyan su shinkafa da su taliya, sai mai. Ƙananan abubuwa ne yake basu kuɗin a hannunsu. Haka suke tsarin da Waheedah, Nuriyya ma da ta shigo bai canza ba. Duk da ita tana tambayar shi kuɗi, Waheedah kuma ba zai tuna ranar ƙarshe da ta tambayeshi kuɗi ba, in ya ɗauka ya bata tana karɓa, in bai bata ba bata taɓa tambayarshi. Na Nuriyyar baya damun shi sam, yakan yi mamakin abin da take yi da kuɗi ne kawai wasu lokutan.

Miƙewa ya yi ya saka wayar a aljihu, mukullin motar shi ya gani ajiye akan drawer ɗin kusa da gadon ta, ya ɗauka ya fito, ko inda take bai kalla ba ya taka yana ficewa daga gidan. Motar ya shiga ya tayar, kan shi tsaye gidan Yassar ya nufa, yana kallon yadda maigadin Yassar ɗin ya ƙara sauri wajen buɗe gate ɗin ganin motar tashi. Saurayi ne matashi, daga yanayin shi Abdulƙadir ɗin ya fuskanci yaron tsoron shi yake ji. Har cikin harabar gidan ya shiga da motar yanayin parking, tukunna ya taka yana ƙarasawa cikin gidan. Sallama yake ta yi bai ji alamar akwai mutane ba.

Ranar aiki ce ya sani, Yassar ɗin zai yiwu yana wajen aiki, matar shi ma tana aiki a asibiti, ɓangaren accounting tunda abinda ta karanta kenan. Sai dai ya san Waheedah na nan, don haka ya taka zuwa ɓangaren da ya sameta zuwan ƙarshe da ya yi.

Ƙwanƙwasa ɗakin ya yi tukunna ya tura tare da yin sallama, ƙamshi na dukan hancin shi, duk da ba na turarukanta bane ba, ƙamshin ya yi mishi daɗi sosai. Wani irin tsalle zuciyar shi ta yi na ban mamaki ganin Waheedah a zaune, doguwar rigace ta atamfa a jikinta wani irin ɗinki da ba zai ce ga yadda yake ba, ta saka Ikram cikin jakar goyo ta goyata ta gaba tana tallabe da yarinyar da take bacci.

Kwalliya ce a fuskarta da ba ko da yaushe take yi ba, ta ɗaura ɗankwalinta ya zauna ɗas a saman kanta kamar a jiki aka yi. Tana zaune gefen gado ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, da plate ɗin soyayyen dankali a gefenta da cokali mai yatsu a ciki, ta ɗora system ɗin da yake zaton ta Yassar ce akan wani ɗan tebur tana kallo. Ƙafafuwanta yake kallo da suka sha zanen flower ta yi wani irin ja mai duhu, kafin ya yawata da idanuwan shi yana tsayarwa kan hannunta ɗaya da ke tallafe da Ikram da shi ma ya sha ƙunshin.

Kai ta ɗago tana kallon Abdulƙadir ɗin, zuciyarta na wata irin dokawa da wani sabon tashin hankalin da ta kwana biyar bata ji shi ba, duk wani abu da su Yassar suka san zai ɗauke mata hankali ya rage mata tunani shi suke yi mata. Har system ɗin Hauwa da ke cike da fina-finai daga American zuwa na Indiya har da na Korea da ta fi so ta kawo mata, ta manta lokacin ƙarshe da ta huta haka. Ji take yi kamar ta yi wata takwas rabonta da samun bacci mai nutsuwa, wata takwas rabon da ta zauna ta huta wa rayuwarta, rabon da ta yi wani abu don kanta kawai.

Ta ji daɗi da Abdulƙadir ɗin bai dame ta ba, shi yasa ta kashe wayarta ta ajiye. Ba shi kaɗai ba, har ‘yan gidan su bata son kowa ya yi mata maganar, kuma kowa ya ƙyale ta. Yanzun ganin Abdulƙadir ɗin na mata barazana da ɗan kwanciyar hankalin da ta samu, don jiya da aka zo yi wa Hauwa ƙunshi ita ma yi mata aka yi, jinta take yi daban, kamar ta baro waccan Waheedahr a gidan Abdulƙadir, yanzun kuma wata ce daban da bata san akwaita ba ma.

“Wahee…”

Abdulƙadir ya kira da wani irin sanyin murya mai tattare da mamakin ganin hankalinta a kwance yake. Don ganinta yasa komai dawo mishi, dukan da ya sha a barikin Sojoji da yake nan garin Kano, yunwar da yake tattare da ita ta kwanaki na rashin samun wadataccen abinci, rashin bacci, da duk wani rauni da baya iya nunawa a gaban kowa. Ita ma Waheedah kallon shi take yi, tana kallon kumburin da ke ƙasan idanuwan shi da tasan rashin bacci ne, da kuma wasu kumburin na alamun duka. A karo na farko a rayuwarta da ta ji halin da yake ciki bai dame ta ba, ballantana har ta tambaye shi ya akai ya shiga ciki.

Ɗauke idanuwanta ta yi daga kan shi tana mayar da hankalinta kan kallon da take yi, ta kai hannu ta ɗauki plate ɗin dankalinta ta ci gaba da ci.

“Waheedah…”

Abdulƙadir ɗin ya kira wannan karon cike da rashin yarda cewa ita ɗin ce ta nuna mishi halin ko in kula, ita ɗin ce ya shigo waje ta kalle shi ta ci gaba da wata hidimar kamar baya nan. Takawa ya yi yana ƙarasawa inda take ya zauna gefenta yana son ta sake ganin shi ɗin ne.

“Baki ganni bane?”

Ya tambaya yana kallon fuskarta da babu kowanne irin yanayi akai, dankalin da ta tauna ta haɗiye ta tsayar da fim ɗinta don bata son komai ya wuce ta.

“Na ganka… Menene? Takardata ka kawo min?”

Wata irin dariya mai sauti Abdulƙadir ya ji ta suɓuce mishi, tabbas Waheedah na da aljanu, yana mamakin yadda akai basu taɓa tashi ba sai yanzun, fim ɗinta ta danna ma play tana mayar da hankalinta a kai. Hannuwan shi Abdulƙadir ya saka fuskar shi a ciki yana fitar da wani irin numfashi, ba shi da ƙarfin yin ko hayaniyar kirki, duk wani ƙashi da yake jikin shi ciwo yake, yasan yadda ake dukan ma’aikata in na horo ne, sun san inda suke duka da zai shigeka ba tare da ya ji maka ciwon da zai hanaka zuwa aiki washegari ba. Lokuta da dama ko fuskarka ba za ta gwada alamun dukan da ka ci ba.

Suna dukan inda uniform zai kare shatikan ko ciwukan. Sauke hannayen shi yayi yana runtse idanuwan shi da yadda Haƙarƙarin shi ya amsa, yasan ba karaya ko ɗaya a jiki, amma wajen ya tara jini saboda dukan da ya sha , ba shi bane na farko, Waheedah kan sa towel da ruwa mai zafi ta gasa mishi ta bashi panadol ko da baya son sha.

“Kwanana biyar a barikin sojoji…”

Abdulƙadir ya tsinci kanshi da faɗi da wani irin sanyin murya, Waheedah bata ma ji shi ba, don gaba ɗaya hankalinta ya tattaru kan kallon da take yi, hannu Abdulƙadir ya kai ya rufe system ɗin, hakan yasa ta kalle shi.

“Bana so, ban ma ga dalilin da za ka shigo min ɗaki ka nemi ɗaga min hankali ba.”

Murmushi Abdulƙadir ya yi.

“Ina da duk wani dalili da zan shigo ɗakin nan, hankalina ba a kwance yake ba, banga dalilin da zai sa naki ya kwanta ba Wahee, ke kika zaɓa mana wannan rayuwar…sannan ba ɗakinki bane wannan… Ɗakinki yana gidana.”

Da kalar rigimar da ke cikin idanuwan shi take kallon shi tana jin dai-dai take da duk wani abu da ya shirya tarar ta da shi, gaba ɗaya ya gama fita daga ranta, ko ganin shi bata son yi, auren shi take ji kamar wata igiya da ta shaƙe mata wuya tana hana mata yin numfashi a walwale, shi yasa take so ya datse ta ya warware mata ko za ta samu ta shaƙi iska mai nutsuwa.

“Bani da ɗaki a gidanka, bani da komai a gidan ka sai kayan da nake gab da zuwa in kwashe don takardata za ka bani tunda babu inda aka taɓa aure dole.”

Mikewa Abdulƙadir ya yi, ya ɗauka ba shi da ƙarfin yin hayaniya, amma tunda can Waheedah ta fi kowa damar ɓata mishi rai, bata amfani da wannan damar ne sai yanzun.

“Igiyar aurenki a hannuna take, yanzun kuma na fara riƙon ta, kaya kuma Allah ya baki iko, kina jina? Allah ya baki iko da ke da duk wanda yake da tsautsayin shigo min gida da nufin taya ki kwashe su… Aljanu ne kike da su da bansani ba sai yanzun, to wallahi ko su ubansu ya yi ƙarya….ke da kanki ma kin yi ƙarya ki sa ni yin abinda ban yi niyya ba.”

Kallon shi Waheedah take yi ita ma tana tsintar kanta da miƙewa tsaye.

“Ana dole ne? Na gaji… Na gaji da auren ka.”

Cikin hargowa ya ce,

“Ni ban gaji ba, gajiyarki bata da wani muhimmanci.”

Dariya Waheedah ta yi tana jin duk wani kwanciyar hankali da ta samu a kwanakin nan na ɓace mata

“Abubuwa da yawa da suka shafe ni basu da muhimmanci a wajenka dama, saboda haka ban yi mamaki ba.”

Cike da rashin fahimta Abdulƙadir yake kallon ta.

“Bangane abubuwa da suka shafeki basu da muhimmanci a wajena ba.”

Gyara wa Ikram zama ta sake yi a jikinta tana ƙara tallabeta.

“Ƙwaƙwalwa ce a kanka duk da ba ko yaushe kake amfani da ita ba, sai ka yi tunani ai.”

Kallon ta Abdulƙadir yake yi, ya ɗauka ya gama shan mamakinta tun da ta iya buɗe baki ta nemi ya sake ta, amma da duk wani gani da zai mata bayan haka da yadda take ƙara shayar dashi mamaki.

“Zagina za ki yi Waheedah?”

Kai ta girgiza mishi, zagi ba ɗabi’arta bane tun da can, ko Fajr ma za ta ƙirga lokutan da ta zage shi balle shi Abdulƙadir ɗin.

“Idan ba zagi ba, me maganganun ki suke nufi? Rashin kunya kike neman yi min da bansan lokacin da kika koyeta ba.”

Ya ƙarasa maganar da wani irin ɓacin rai marar misaltuwa.

“Ni fa ban zage ka ba, rashin kunya kuma in dai koya na yi bai kamata ka yi mamaki ba tunda na yi rayuwar aure da kai.”

Da hannu yake nunata.

“Gashi nan… Yanzun me kika yi.. Wani zagin ne wannan ai… Wallahi Waheedah ki kiyayeni, kina gwada haƙurina… Kuma tashi za ki yi mu koma gida.”

Abdulƙadir ya yi maganar yana son ture alamun da yake ji kamar na tsoro na son taso mishi, ga hankalin shi da yake a tashe ƙasan ɓacin ran da yake fama da shi, musamman da Waheedah ta yi mishi wani irin kallo tana komawa ta zauna tare da faɗin,

“Sai ka ɗauke ni ka ɗora saman kai ka mayar da ni ai.”

Kai Abdulƙadir yake jinjina mata, inda take ya ƙarasa, rashin hankali take nuna mishi ƙarara, zai nuna mata duk abin da take ji dai-dai yake da ita. Belt ɗin da yake kafaɗunta na jakar goyon yake ƙoƙarin ɓallewa, ta ture hannun shi.

“Me kake yi?”

Ta tambaya muryata cike da tsoro, hannuwanta Abdulƙadir ya kama duka biyun yana saka ƙarfi ya riƙe su, belt ɗin ya kwance duk ihun da Waheedah take mishi, da hannu ɗaya ya zame Ikram ya sauke ta daga jikin Waheedah ɗin.

“Sadauki ka sake ni, don Allah ka ƙyale ni, ka ga Ikram na kuka.”

Waheedah ta ƙarasa tana jin idanuwanta sun ciko da hawaye duk yadda ta faɗa wa kanta ta gama yi mishi kuka.

“Ashe muryarki na sauka haka, har na manta saboda yadda kike ɗaga min ita a kwanakin nan.”

Cewar Abdulƙadir ɗin yana kama hannuwanta da yake riƙe da su ya ɗagota ya miƙar tsaye, zuwa lokacin ta daina kiciniyar ƙwacewa, ɗagata ya yi ya saɓa ta a kafaɗar shi kamar ya ɗibi kayan wanki, yasa hannuwan shi yana mata riƙon da ta san ko da wasa ba za ta iya ƙwacewa ba, ikon Allah take saurare kawai tana tabbar da Abdulƙadir na da taɓin hankali, bata sani bane tuntuni sai yanzun.

“Wallahi ka sauke ni, wannan kidnapping ne, shekara goma sha biyar za ka yi a gidan yari.”

Dariya Abdulƙadir ya yi, wannan karon tana fitowa daga ɓangaren zuciyarshi da ya kwana biyu bai ji ya buga mishi ba.

“Ka sauke ni, bana son haka, ka sauke ni…ko ka kaini ba zama zan yi ba Sadauki…na faɗa maka na gama auren ka.”

Hanyar da za ta fitar da shi daga ɗakin ya nufa yana buɗe ƙofar ya ci karo da Yassar da ya miƙo hannu da alama yana shirin ƙwanƙwasa ƙofar ne ko ya buɗe. Don tunda ya shigo gidan yake jin kamar maganganu shi ya sa ya nufo ɓangaren Waheedah ɗin, muryarta na tabbatar mishi da Abdulƙadir na ciki. Yanayin maganganunta ne ya hanashi bankaɗa ƙofar kar ya ga abinda bai kamata ba, tunda yasan Abdulƙadir ba hankali gare shi ba ballantana kunya. Sai dai baki a buɗe yake kallon Abdulƙadir ɗin.

“Ka matsa min Hamma…”

Ya faɗi yana gyara wa Waheedah zama a kafaɗar shi.

“Me kake yi Abdulƙadir? Me kake yi?”

Yassar yake tambaya yana kallon Abdulƙadir ɗin kamar a fim, don bai taɓa ganin abinda yake yi a zahiri ba, cikin kuka Waheedah take faɗin,

“Hamma ka ce ya sauke ni, don Allah ka yi mishi magana, ni ba zan koma gidan shi ba…”

Muryar Yassar har lokacin da mamaki ya ce,

“Ka sauketa Abdulƙadir…. Ka sauketa tun kafin ranka ya ɓaci.”

Ƙanƙance idanuwa Abdulƙadir ya yi.

“Ita ta ce in ɗauke ta a kai in tafi da ita…”

Waheedah na jin hawayen da ke ɗigar mata, ga kanta da ya fara tara jini saboda yanayin yadda Abdulƙadir ɗin ya riƙe ta.

“Ni ban ce mai ba Hamma… Don Allah ka ce ya sauke ni.”

Ƙoƙari Yassar yake yi kar murmushi ya ƙwace mishi, idan Abdulƙadir ya ga alamar wasa ko ya take tattare da Yassar ɗin ba zai sauke Waheedah ba.

“Ka sauke ta na ce maka Abdulƙadir…”

Baisan ya aka yi maganar Yassar ɗin ta yi tasiri akan shi ba. Sauketa ya yi tana dafa ƙofar wajen jin zata faɗi, tana tsayuwa sosai ta sa hannu tana goge fuskarta, ɗankwalinta bata san ma lokacin da ya faɗi ba, ga wata irin matsananciyar kunyar Yassar ɗin da ta kamata. Wani irin kallo ta watsa wa Abdulƙadir ɗin.

“Aurenka ko na zobe ne sai ka rabu da ni… Kuma wallahi sai na faɗa wa Abba.”

Ta ƙarashe maganar wasu hawayen takaici masu zafi na zubo mata. Abdulƙadir kuwa Yassar ya kalla.

“Ka gani ko? Hamma kana jin irin rashin kunyar da take min.”

Hannu Yassar ya ɗaga mishi.

“Ka wuce ka tafi.”

Kafaɗa Abdulƙadir ya maƙale.

“Ni ban gama magana da ita ba.”

Kai Yassar ya girgizawa yana sauke numfashi, so yake ya bar wajen kafin dariya ta ƙwace mishi.

“Ka tabbata za ka yi mata magana kamar mai hankali?”

Kai Abdulƙadir ɗin ya ɗaga mishi, sai da Yassar ɗin ya ɗan tsaya tukunna ya juya. Ƙofar Abdulƙadir ya tura yana mayar da hankalin shi kan Waheedah da ta ɗauki Ikram tana ƙoƙarin lallashin ta.

“Babu ribar da za ki ci a faɗa da ni Waheedah… Ki taho mu koma gida, na baki haƙuri.. Ki yi haƙuri don Allah. Ki zo mu koma… Kin ga ni bana son yin faɗa da ke.”

Ya karasa maganar yana sauke muryarshi, amma a idanuwanta yake ganin yadda maganganun shi ko kaɗan ba su yi tasiri ba, ci gaba ya yi da faɗin,

“Kin ji Wahee… Kina ta ɗaga min hankali akan magana ƙarama, Wallahi kwanana biyar a barikin Sojojin garin nan, ki kalli fuskata, na manta rabona da wadataccen bacci balle abincin kirki…”

Yayi maganar yana kama rigar jikin shi ya daga mata, jini ne ya yi baƙiƙirin a gefen cikin shi da duka haƙarƙarin shi, tana kallo ya juya mata har bayan shi da nan ma jinin ne a kwance, kowanne irin duka akai mishi ba ƙarami ba ne ba, zuciyarta take ji a bushe babu wani abu da take son yi banda shaƙar numfashi ba tare da igiyar auren shi ta ɗaure mata wuya ba. Sakin rigar shi Abdulƙadir ya yi.

“Ban shigo da nufin yin faɗa da ke ba, har kuɗin hidimar gida na tura miki ɗazun…”

Kalamai yake nema da zai lallasheta da su, amma ya rasa, saboda basu taɓa faɗa ya wuce yini ɗaya ba, ko ya ce bata taɓa faɗa da shi ya wuce yini ɗaya ba, tunda ba biye mishi take yi ba, ita ta saba lallashin shi, shi ya sa komai ya kwance mishi. Takawa ya yi ya ƙarasa ya kamo ɗayan hannunta da yake jikin Ikram yana saka ta riƙe yarinyar sosai.

“Kin ga Azumiya kusa, saura kwanaki kaɗan, ana yafewa juna kafin azumi, ba ma kyau faɗa kafin azumi.”

Cikin idanuwan shi Waheedah ta kalla.

“Ka sauƙaƙe min kafin azumin…don Allah Sadauki…Ka ji…ka sake ni in huta nima. Na gaji da auren ka.”

Ta ƙarasa maganar tana zame hannunta daga cikin nashi ta share ƙwallar da ta zubo mata. Wani irin numfashi Abdulƙadir ya sauke yana juyawa ya fice daga ɗakin, bai tsaya ko ina ba sai cikin motar shi, tayar da ita ya yi ya fita daga gidan Yassar, a gefen hanya ya yi parking yana haɗe kan shi da abin tuƙin motar. Kan shi ciwo yake da ba shi da alaƙa da yunwa ko rashin bacci. Wani irin tsoro yake ji da bai taɓa sanin akwai shi ba. Kalaman Waheedah ke mishi yawo da wani yanayi na ban mamaki.

Bata yi mishi maganar da hayaniya ba, asalima idanuwanta cike suke taf da hawaye, da neman alfarma, bata taɓa roƙon wani abu a wajen shi ba, yau ne yake ganin alamar tana roƙon shi, kuma roƙon farko da ya shiga tsakanin su shi ne na ya raba ta da auren shi, so take ya buɗe bakin shi ya furta mata kalaman da za su warware igiyar da bai yarda an ƙullata tsakanin su ba sai da nufin mutuwa ce kawai zata raba. Bai taɓa tunanin cewa zata roƙe shi wani abu da zai kasa yi mata ba, ko don girman matsayinta a wajen shi, amma sai ta tambayeshi abin da yake jin duk duniya babu wanda ya isa ya saka shi yin shi.

Wani irin tsoro yake ji da ya danne duk wani abu da yake damun shi. Lumshe idanuwan shi ya yi yana hango yin rayuwa babu Waheedah, da sauri ya buɗe su yana ɗagowa daga jikin motar, don jin shi ya yi duniyar ta yi mishi wani irin girma, ga kaɗaici na ban mamaki da ya lulluɓe shi. Da aurenta ya san akwai abinda babu a rayuwar shi sai bayan ta shigo ta, daga ranar da igiyar aure ta haɗa su zama a ƙarƙashin inuwa ɗaya bai ƙara hasko wani lokaci a rayuwar shi da babu ita a ciki ba. Ko tunanin mutuwa yake bai taɓa hango zata riga shi ba, abu ne da tunanin shi ma baya hasaso mishi.

Fim idan yana kallo in dai za ai mutuwa, ya fi son ya ga mijin ne ya mutu ya bar matar, don baisan yadda zai yi da sauran rayuwar shi idan babu ita a ciki ba.

“Bazan iya sakinki ba Waheedah… Ko meye nai miki me zafi haka haƙuri za ki yi ki dawo. In ke za ki iya barina ni bazan iya barinki ba wallahi… Bazan iya ba.”

Ya ƙarasa maganar yana dafa fuskarshi da duka hannuwan shi biyu. Ya fi mintina talatin a cikin motar kafin ya tayar da ita ya nufi gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 24Abdulkadir 26 >>

1 thought on “Abdulkadir 25”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×