Skip to content
Part 22 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Har ya shiga gida ran shi a ɓace yake jin shi. Yana jin Waheedah tun da ta amsa mishi sallama ta yi mishi sannu da zuwa tana bin shi da ido. Ya san ta fahimci ran shi a ɓace yake. Kitchen ta shiga ta samu babban plate ta zuba musu abinci a ciki, manja ta zuba musu ta saka cokulla guda biyu a cikin abincin, maggi ta ɗauka da robar ya ji ta fita falon. Abdulƙadir na zaune in da ta bar shi akan kujera, so take ta tambaye shi wa ya ɓata mishi rai, amma bata jin daɗin jikinta, bata jin za ta iya da faɗan shi da daren, shi yasa ta yi shiru. A ƙasa ta ajiye abinci da robar yajin ta ɗora magin a sama.

Kitchen ta koma ta ɗauko wani plate ɗin da kofuna guda biyu, ta buɗe fridge ta ɗauko pure water guda biyu, sai robar da cittarta take ciki, in dai an kawo ruwan roba gidan Abdulƙadir ne ya zo ya fita ya siyo shi, ɓarnar kuɗin nan ba da ita ake yinta ba, akwai gidan ruwa a unguwarsu, Maigadi take ba ya siyo mata leda goma ta zuba a fridge ɗin, sai ta kwana biyu bata nemi ruwa ba. Don ma Fajr na mata ɓarnar shi, idan ya gan shi a roba kuma bakinta baya hutawa da surutu, babu ƙishin da yake ji, zai ɗauko ne kawai don ya sa ta magana.

A ƙasa ta samu Abdulƙadir ya sakko, ita ma ta ajiye ruwan ta samu waje ta zauna. Magin ta barbaɗa ta buɗe robar yaji ta zuba, duka ta cakuɗa, ta san Abdulƙadir zai tsaya kallonta sai ta cakuɗa in da za ta ci su ci wajen tare, ko ta cakuɗa mishi na gaban shi, in sun je gidan su har mamakin yadda yake komai da kan shi take, amma da sun dawo ya ga su kaɗai ne zai shagwaɓe mata. Ba don bata son hakan ba, wani lokaci abin kanyi mata yawa, gashi, ga Fajr. Abincin suke ci, baka jin komai na tashi a ɗakin sai ƙarar cokula. Sun gama kenan ta zuba mishi ruwa ta miƙa mishi kofin suka ji sallamar Yassar.

Ita ta amsa mishi sallamar tana kallon yanayin shi ko za ta fahimci dalilin zuwan shi da dare haka. Murmushi ya yi mata yana amsa gaisuwar ta tare da ɗorawa da,

“Duk suna lafiya. Ya jikin ki?”

Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa a kunyace, tana amsawa can ƙasan maƙoshi, idanuwa Yassar ya sauke kan Abdulƙadir, hakan da Waheedah ta kula da shi yasa ta miƙewa ta ɗibi kwanonin ta wuce kitchen, a can tasha ruwa tukunna ta fito tana ma Yassar sallama ta wuce ɗaki. Kowa ya ɓata wa Abdulƙadir ɗin rai ta san ba zai wuce a gida bane, tunda ta ga Yassar ya zo. Shi yasa ta basu waje, in Abdulƙadir yana so ta ji da kanshi zai faɗa mata, ita kam kaya za ta sake ta kwanta abinta.

Yassar miƙewa ya yi, bai san yadda aka yi ya iya ɗora murmushi a fuskar shi ba, bayan abinda yake so ya yi da ya shigo shi ne wanke fuskar Abdulƙadir ɗin da mari. Abinci zai ci Abba ya kira shi rai a ɓace yake faɗa mishi abinda Abdulƙadir ɗin yake shirin yi da ko a mugun mafarki Yassar bai taɓa hango faruwar lamarin ba.

“Magana nake son yi da kai.”

Kallon shi Abdulƙadir ya yi yana ƙanƙance idanuwan shi, ran shi ya ƙara ɓaci, Abba kiran Yassar ya yi ya faɗa mishi kenan, kuma bai ga dalilin yin hakan ba, tunda zai faɗa ma Yassar ɗin da kan shi, magana ce da ba ɓoyuwa za ta yi ba, don bai ga abindae zai sa shi ya fasa ba, ya riga da ya furta.

“Ina jin ka ai.”

Ya amsa, miƙewa Yassar ya yi, idan Abdulƙadir ba shi da hankali, shi yana da shi, da alama Waheedah bata sani ba, ba zai so ta fara ji daga bakin shi ba.

“A waje zamuyi magana ba anan ba.”

Cewar Yassar yana ficewa daga ɗakin, tashi Abdulƙadir ya yi ya bi bayan shi har wajen motar shi, suka tsaya. Sun kai mintina biyu Yassar na son haɗiye abin da yake ji yana taso mishi ko zai samu nutsuwar yi ma Abdulƙadir ɗin magana ba tare daya ɗura mishi ashar ba.

“Abba ya kira ni…”

Shiru Abdulƙadir ɗin ya yi, yana jira Yassar ya faɗa mishi wani abu da bai sani ba, wannan tsohon zance ne tunda gashi tsaye a gefen shi yana huci kamar sabon biredi.

“Ka ce min wasa kake Abdulƙadir, don wallahi na kasa wrapping ɗin kaina akan maganar nan.

Kallon shi Abdulƙadir ya yi.

“Yaushe Abba ya zama abokin wasana? Meye wahala a fahimtar maganganun da na yi? Auren da zan ƙara ne yake maka wahalar fahimta?”

Numfashi Yassar yake ja yana fitarwa a hankali, da alama idan bai kai zuciyarshi nesa ba, mota zai koma ya jata ya take Abdulƙadir ɗin duk su huta.

“Bansan me kake so in ce maka ba Hamma… Ban san me yasa ka zo kana kallona kamar akwai haramci a cikin abinda nake so in yi ba.”

Abdulƙadir yake faɗi ranshi in ya yi dubu kowanne a ɓace yake, tun a hanya yake jin maganganun da ya faɗa ea Abba suna dawo mishi, abin na mishi kamar mafarki, yana kasa yarda da abinda yake shirin faruwa ɗin. Amma zuwan Yassar ya ƙara tabbatar mishi da cewa auren zai yi babu fashi. Don bai ga dalilin da zai sa Yassar ya dinga mishi kallon da yake mishi ba. Kai Yassar yake girgizawa, muryarshi a gajiye ya ce,

“Bani da matsala da auren ka, wadda zaka aura ɗin ce damuwata, me yasa sai ita? Ƙawarta ce Abdulƙadir…”

Ƙanƙance mishi idanuwa Abdulƙadir ya yi.

“Sai me ya faru don ƙawarta ce? Haramun ne in auri ƙawar ta?”

Dafe kai Yassar ya yi da yake jin wani irin ciwon kai ya dirar mishi. Ga zuciyar shi da ke zafi, in har yana jin haka da abinda Abdulƙadir yake shirin yi, bai san ya Waheedah zata ji ba.

“Ka daina yin kamar mai Asthma Hamma, ba zai sa in fasa auren nan ba. Ban san me yasa Abba zai faɗa maka ba, tunda ai zan gaya maka da kaina dama.”

Da hannuwa biyu wannan karon Yassar ya tallafe fuskar shi. Da an ce mishi akwai ranar da za ta zo da zai ji baya son ganin Abdulƙadir zai ƙaryata, amma abinda yake ji yanzun, maganganun Abdulƙadir ɗin sun sa ko kaɗan baya son ganin ko inuwar sa. Da shi ake jinjina maganar matan da suke cakawa mazajen su wuƙa duk idan hakan ya faru, Abdulƙadir yasa shi fahimtar kaɗan daga cikin dalilin da maza suke ba matansu har shaiɗan ya yi galaba akan su, su hau dokin zuciya su aikata abinda zai sa su da na sani daga doron duniyar har lahira.

Idan akwai mazaje ɗari irin Abdulƙadir, yana da tabbas lahirar mata da yawa za ta raunana, za su zama barazana da kwanciyar ƙabarin mata da dama. Fuskar shi Yassar ya buɗe yana jan wani irin numfashi ya fitar da shi rai a ɓace.

“Babban kuskuren rayuwar Waheedah shi ne amince ta auren ka.”

Wannan karon Abdulƙadir ne ya ja wani irin numfashi, kai yake girgizawa.

“Baka faɗa min maganar nan ba Hamma, ka janye kalamanka…”

Mukullin shi Yassar yake lalubawa cikin aljihu, ya kuwa yi nasarar ciro shi yasa a jikin murfin mota ya buɗe. Abdulƙadir ya mayar da murfin yana rufewa, ya kuma riƙe hannun ƙofar gam. Muryarshi can ƙasan maƙoshi yake cewa,

“Hamma ka janye kalaman ka, don Allah ka janye ko za su rage mun zafin da suke yi…”

Tsaki Yassar ya ja.

“Ka matsa min daga jikin mota kafin in kwaɗa maka mari Abdulƙadir… Wallahi yadda nake ji komai zai iya faruwa…”

Kallon shi Abdulƙadir ɗin yake yi, a tsawon rayuwar shi yau ce rana ta farko da Yassar ya faɗa mishi maganganun da yake jin ciwon su har cikin ƙasusuwan shi, akan maganar abin da addini ya halarta mishi ta kowacce fuska. Ya sha ganin ya ta mutu, ƙanwarta ta auri mijin, bai san me yasa nashi zai banbanta ba.

“Me yasa zaka faɗa min haka? Hamma me yasa? Saboda na ce zan auri Nuriyya? Don zan yi abinda Allah bai haramta min ba…ya tana mutuwa, mijin ko bai nuna yana son ƙanwar ba a bashi, me yasa nawa zai yi maka zafi haka?”

Ture shi Yassar yayi yana faɗin,

“Mahaukaci ne kai wai? Don ubanka allurar sojojin kai ka miƙa musu suka caka maka ita? Addini bai haramta maka auren Nuriyya ba, amma al’ada ta haramta maka shi, kunya ta haramta maka, ko mutuwa Waheedah ta yi ka nuna kana son auren ta, akwai mutane da yawa da zasu ga rashin kyautawar haka… Ka matsa min Abdulƙadir, ka matsa min in wuce…mahaukacin banza marar tunani.”

Yassar ya ƙarashe yana ƙara sa hannu ya ture Abdulƙadir ɗin, ya buɗe motar shi ya tayar. Abdulƙadir na bin shi da kallo har ya fice daga gidan. Bai ce mishi komai ba, saboda ya ga alama Yassar ɗin marin shi zai yi idan ya sake magana, a karo na farko kuma da ya san in ya mare shi ramawa zai yi, don shi ma ran nashi ya gama ɓaci. Ya fi mintina goma a tsaye a wajen, kafin ya iya wucewa ya shiga gida. Kai tsaye ɗaki ya shiga yana wucewa banɗaki ya sakarwa kanshi ruwan sanyi ko zai samu sauƙin abinda yake ji.

Daga shi sai towel ya fito, ya samu gajeran wando ya saka, Waheedah har ta yi bacci ya hau kan gadon yana matsawa gab da ita. A hankali yake girgizata.

“Wahee…. Waheedah…”

Buɗe idanuwanta ta yi cike da bacci tana jin fitilar ɗakin da ke kunne ta shigar mata idanuwa yana sa ta mayar da su ta rufe babu shiri.

“Ki tashi Waheedah…. Kin ji… Ki min hira.”

Abdulƙadir ya ƙarashe yana ƙara girgiza ta, buɗe idanuwan ta ta yi tana kallon fuskar shi.

“Bana jin daɗi Sadauki… Don Allah ka barni in yi bacci.”

Kai ya girgiza mata, ita bata jin daɗi ne, shi zuciyar shi zafi take mishi kamar ƙirjin shi zai buɗe, hannunta ya kamo ya ɗora kan ƙirjin shi inda yake ji yana mishi ciwo na gaske.

“Wahee raina a ɓace yake, zuciyata zafi take min wallahi, Hamma ya ɓata min rai.”

Yadda ya ƙarashe maganar yasa ta miƙewa, sosai take kallon shi, idanuwan shi har sun canza launi saboda ɓacin rai, tashi zaune ta yi tana jingina bayanta da gadon, zazzaɓi ne ruf a jikinta, tashin da Abdulƙadir ɗin ya yi mata yasa har amai take ji. Ganin ta tashi yasa shi barin pillown shi yana komawa kan cinyoyinta ya kwanta, ya kama hannunta ya ɗora kan fuskar shi yana neman sauƙi ko ya yake.

“Kayi haƙuri don Allah… Ko me zai faɗa maka na san baya nufin kalaman, ɓacin rai ne kawai… Da ya huce shikenan, ka yi haƙuri.”

Ta faɗi a tausashe, ƙara naniƙe mata ya yi, ba za ta iya hana shi ba, duk da zazzaɓin da take ji, yanayin shi ya gama raunana tata zuciyar, in dai za ta sama mishi sauƙi ko ya yake za ta ƙoƙarta. Biye mishi ta yi, bata samu ya yi bacci ba sai wajen ƙarfe biyun dare. A daddafe ta shiga banɗaki tana dubawa ko da ruwan zafi don basu bar wutar ta zauna ba. Da ƙyar ta iya watsa ruwa, ga wata yunwa da take wujijjigata, kitchen ta wuce ta duba sauran abincin da yake tukunya, ba za ta iya cin shi da sanyi ba, don haka ta ɗora ta yi warming.

Ta ɗauko plate kenan ta fara zubawa ta ji takun Abdulƙadir ɗin, kafin ta juya ya rungumeta ta baya, muryarshi cike da bacci ya ce,

“Shi ne kika barni ko?”

Numfashi ta sauke.

“Yunwa nake ji…ka koma ka kwanta, da na ci abinci zan dawo…”

Tana jin shi yana girgiza mata kai, ko da ya farka bai ji ta a kusa da shi ba ran shi ne ya ji yana shirin ƙara ɓaci. Ya duba banɗaki bai ganta ba, shi yasa ya fito nemanta.

“Sadauki don Allah… Karka karya ni.”

Magana ya yi mata da ta tsaya iya kunnenta, ta ture shi tana dariya. Abincin ta zuba, falo ta koma ya bita ya zauna a gefenta. Wani lokaci har bata so a ɓata mishi rai, in kuwa ya faru gara ta tambayeshi ya sauke mata faɗan shi da ya shiga yanayin nan da ko banɗaki ta shiga ta bar shi sai ya bita. A kanta abin yake ƙarewa, yanzun ɗin kuma ya ƙi fahimtar ba ita kaɗai bace ita ma, ko ƙarfin kirki bata da shi. Ya barta ta ci abincin a nutse ya ƙi, sai murza ido yake yana hamma, gashi rabin jikin shi a kanta yake. Samu ta yi ta gama suka wuce suka kwanta.

*****

Tunda ya dawo sallar Asuba ya ga saƙon Hajja.

‘Ka zo ina neman ka.’

Wayar ya kashe gaba ɗaya. Zai je in ya tashi, sai ya gama baccin safen shi amma. Waheedah kuwa dankalin Hausa ta ji tana marmari, tana da shi don haka ta fere bayan ta idar da sallah, ta yayyanka ta zuba a ƙaramar roba ta saka ruwa. Abdulƙadir na dawowa Masallaci ya ga tana karatun Qur’ani ya samu waje ya zauna a gefen gado, tana idarwa ta ajiye ta cire hijabin ta wuce kitchen ya bi bayanta.

“Yanzun Waheedah sai kin soya dankalin za mu kwanta? Bacci fa nake ji.”

Abdulƙadir da yake tsaye ya ce wa Waheedah da take share wajen da ta ɓata. In dai bacci ne ta fishi buƙata, tun da bai bari ta samu na kirki ba, yama fi ta samun baccin, bata ce mishi komai ba.

“Ke kaɗai nake wa magana ki jini kuma ki yi shiru.”

Abin kwashe shara ta saka cikin dustbin, ta wanke hannunta tukunna ta kalle shi da faɗin.

“Yi haƙuri… Mu je.”

Ƙanƙance mata idanuwanshi ya yi da suke cike da rikicin da bata da ƙarfin biye mishi. Kwanciyar suka yi, sa’adda ta tashi ƙarfe goma, ruwa ta watsa ta saka doguwar riga ta material da farar hula tukunna ta wuce kitchen tana ɗora mai don ta fara soya dankalin. Idan Abdulƙadir ya tashi zai fara mata maganar abinci ne ta sani, kuma tashin zai yi, don da ya laluba ya ji bata kusa da shi tashi zai yi.

Tana sauke kaskon farko Abdulƙadir ɗin na fitowa daga shi sai towel.

“Baki ɗauko min kayan da zan saka ba.”

Ya faɗi, in ta ce ya je ya ɗauko da kan shi dogon surutu za su yi, kuma ƙarshe ita za ta ɗauko mishi, sauran dankalin ta juye ta wuce ɗaki ta ɗauko mishi farar riga marar nauyi da wani three quarter mai igigoyi daga ƙasan, sai singlet da boxers, turare ta fesa mishi a jiki tana ajiye mishi kan gadon. Murmushi ya yi mata yana sa hannu ya taɓa fuskarta,

“Ya kuka tashi? Ya jikin ki?”

Murmushi Waheedah ta yi.

“Baka tambayi jikina ba sai da ka gama sani aiki ko?”

‘Yar dariya ya yi, ta gaishe shi da Asuba, ya taɓa ta ya ji babu zazzaɓin, bai dai tambaya bane sai yanzun. Ganin ya yi shiru yasa ta faɗin.

“Mun tashi lafiya. Ka sa kaya, kar dankalina ya ƙone…”

Kafin ya amsa ta juya da sauri ta fice daga ɗakin. Albasa ta yanka don tana so, ta zuba a cikin wancan da ta kwashe, na biyun bai ƙarasa ba har Abdulƙadir ya fito, falo ya wuce ya zauna yana jiranta, tana gamawa ta haɗa mishi shayi ta zubo dankalin ta fito. Ci suka yi suna hira, suna gamawa ya ce mata zai je gida. Raka shi ta yi har ƙofa tukunna ta dawo ta haɗa wanke-wanke ta yi, ta goge kitchen ɗin tukunna ta koma ɗakin su ta gyara gadon, bata jin za ta iya share shi tun da ba dauɗa ya yi ba, kuma bata ma jin daɗin jikinta. Komawa ta yi ta kwanta tana tunanin abinda za su ci da rana.

*****

Gida ya shiga, bai samu Hajja a falo ba, ya wuce ɗakinta yana ƙwanƙwasawa, ya tura bayan ta amsa tare da yin sallama. A zaune ya sameta kan gado ta miƙe ƙafafuwanta ta saka glass ɗin ƙaratu da littafin ‘Tarihin Annabi Kamalalle’ a hannunta tana karantawa.

“Hajja…”

Ya faɗi cikin sigar gaisuwa, littafin ta ajiye tana cire gilashinta shi ma ta ajiye shi a gefe. A nutse take kallon Abdulƙadir.

“Menene matsalarka? Abdulƙadir yau kam ka gaya min menene matsalar ka.”

Da mamaki a fuskar shi yake kallon Hajja yana girgiza mata kai.

“Bani da matsalar komai Hajja”

Numfashi ta sauke.

“Kawai wulaƙanci ne kenan ko? So kake ka ja mana abin magana shi yasa kake so ka auri Nuriyya… Ita ma Nuriyyar don ubanta idan tana da kunya ai ko mutuwa Waheedah ta yi idan ka zo mata da wannan maganar za ta dubi amintakar da ke tsakanin su ta ƙi amincewa. Amma na ga alama yadda ka sa ƙafa ka shure duk wata kunya da ake halittar ɗan Adam da ita haka ita ma ta yi fatali da tata.”

Gefen Hajja Abdulƙadir ya zauna yana faɗin,

“Hajja akan maganar ne ke ma kike so ki ɓata ranki? Me yasa ba zan aureta ba bayan addini ya halarta min, me yasa kuke son haramta min abinda Allah bai….”

Ƙara ya ji cikin kunnen shi na haggu da ya katse mishi maganar da yake shirin yi, kafin daga baya ya fuskanci abinda ya faru. Hannun shi yasa yana taɓa kuncin shi cike da tsantsar mamaki.

“Hajja… Marina kika yi Hajja… Mari Hajja.”

Kai ta jinjina mishi tana faɗin,

“Ina gab da ƙara maka wani in baka ɓace min da gani ba wallahi. Tun da kai baka san abinda ke maka ciwo ba, abin da duk ka ga dama shi kake son yi…. Aure ko? Auren cin amana, a yi lafiya Abdulƙadir, wallahi ba baki na yi maka ba, alhakin Waheedah ba zai barku ba.”

Hajja ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin tarbe hawayen da take jin sun cika idanuwanta don takaici, roƙar mishi yafiyar Allah take da yadda ya ɓata mata rai kar wani abin ya same shi. Miƙewar ya yi kuwa, baya niyyar bata haƙuri ko ya ce mata ya fasa auren. Muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“In kin huce ki min addu’a Hajja…”

Ya wuce yana fita daga ɗakin, ya ja mata ƙofar a hankali, yana jin yadda ita kaɗai ce za ta mishi abinda ta yi mishi ɗin. Duk da ran shi ya kai ƙololuwa a ɓaci. Daga jiya zuwa yau, abinda Abba ya yi mishi, Yassar, yanzun kuma ita. Kamar tunzura shi suke yi da son yin auren, don yana jin ba shi bane mutum na farko da addini ya halarta wa abu al’ada ta haramta mishi. Zai dai zama cikin mutane ƙalilan da ba za su taɓa barin al’ada ta yi nasara akan su ba.

Yana fita daga gidan, mashin ya tare ya hau zuwa zoo road, rabon shi da gidan ƙanin Abba, Alhaji Ali da suke kira da Kawu Ali, har ya manta. Amma shi kaɗai ne mutumin da yake da yaƙinin zai tsaya mishi kan maganar, don a gidan su Abba kaf shi ne yake ɗan boko na gaske, kuma mutumin da ko a yaran shi za ka fuskanci wayewar da suke tafiyar da rayuwar su a kai. Duk da a baya Abdulƙadir ɗin kan yi tir da kalar tarbiyar tasu, yau dai Kawu Ali zai mishi ranar da bai zata ba.

Da yake ranar Lahadi ce, babu aiki, ya kuwa yi nasarar samun Kawu Ali a gida. Faɗa mishi abinda yake faruwa ya yi, sosai Kawu Ali ya jinjina maganar

“Shima Alhaji yana da matsala wallahi, yanzun da ku zo kuna abinda bai kamata ba ai gara a yi auren. Ka yi hankali da ka zo ka same ni da maganar, ka je abinka, zan kira shi mu yi magana in shaa Allah.”

Ɗan jim Abdulƙadir ya yi kafin ya ce.

“Gobe in shaa Allah zan wuce ne Kawu, nafi so a gama maganar kafin in tafi.”

Kai Kawu Ali ya jinjina yana faɗin,

“Bari in kira shi yanzun in ji idan bai fita ba, sai mu je gidan.”

Gyara zama Abdulƙadir ɗin ya yi, yana sauraren Kawu Ali ya kira Abba, baya jin me Abban yake cewa. Amma da alama baya gida, Kawu Ali na sauke wayar ya kalli Abdulƙadir.
“Sai da dare, ya fita. Amma karka damu in shaa Allah komai zai yi dai-dai.”

Godiya Abdulƙadir ya yi wa Kawu Ali tukunna ya wuce, gida ya nufa, a kitchen ya samu Waheedah tana ta aikin da bai san na menene ba, falo ya koma ya kwanta kan doguwar kujera. Babu abinda yake so sai ya ga an ɗaura auren ya gama da wannan matsalar, ganin tunani zai mishi yawa in ya kwanta yasa shi tashi ya bi Waheedah kitchen ɗin.

“Me kike dafa mana?”

Kallon shi ta yi ta ce,

“Dambun shinkafa.”

Murmushin da ya yi mata yasa ta ji gaba ɗaya wahalar dambun ta ɓace mata.

“Ina son shi sosai”

“Na sani… Har da zoɓo na dafa mana, shi zan haɗa yanzun.”

Murmushin Abdulƙadir ya sake yi mata, a cikin gidan su ya baro marin da Hajja ta yi mishi, don ba zai saka abin a ranshi ba. Abu ɗaya da kowa bai sani ba shinee yana da Waheedah, babu wani abu da zai ɓata mishi rai fiye da rana ɗaya. Za ta yi wani abin da zai sa shi ranshi ya yi ƙal, kamar yanzun ɗin ma, gashi duk da hasken da yake ganin ta ƙara, ta mishi kyau cikin riga da skirt ɗinta, ɗankwalin ta ɗaura shi simple, da jan jambaki a laɓɓaanta da tunda ta kula yana so take sakawa, don ita kwalliya ba damunta ta yi ba.

Ganin yana matsowa cikin ƙoƙarin haɗe space ɗin da ke tsakanin su yasa ta nuna shi da ludayin hannun ta tana matsawa baya.

“Sadauki aiki nake wallahi, don Allah ka je ka yi zamanka, zoɓo zan haɗa ka ga…. Ka ji.”

Dariya Abdulƙadir ya yi yana ja ya tsaya, har sai da ta ƙarasa wajen kantar kitchen ɗin, tukunna ya taka yana taɓa fuskarta zuwa wuyanta.

“Ni zan ji ko da zazzabiy a jikinki ne kawai…”

Murmushi ta yi, ta san halin shi sarai. Shi ya miƙo mata robar sukari ta haɗa zoɓon da zallar shi ne ya sha kayan ƙamshi, sai flavor ɗin abarba da ta ɗan ɗiga na ruwa. Da ɗumin shi haka Abdulƙadir ya ce mata shi yana sha. Dole ta zuba mishi tukunna ya fitar mata daga kitchen ɗin yana komawa falo, ta ci gaba da aikinta.

*****

Kafin isha’i Kawu Ali ya kirashi da su haɗu a gida. Don haka yana fitowa daga masallaci ya hau mashin ya wuce. Ɗakin Abba ya nufa, zuciyar shi a dake yake jinta. Don ya gama yanke hukuncin duk abinda za su faɗa ba zai canza ra’ayin shi ba. Da sallama ya shiga ɗakin Abban yana samun shi zaune da Kawu Ali. Wani irin kallo Abba ya bi shi da shi da yake jin yana neman sanyaya mishi jiki.

Yana zama kuwa kamar jiran shi Abba yake.

“Ni ban isa ba ko Abdulƙadir? Ban isa da kai ba kake son nuna min, kuma na gani. Allah ya yi maka albarka ya kuma shiryeka…. Aure a yi lafiya amma wallahi babu hannuna a maganar.”

Numfashi Kawu Ali ya sauke, ya buɗe baki zai yi magana Abba ya katse shi da faɗin,

“Ku biyun tashi za ku yi ku bani waje, kai boko ta hanaka ganin aibun abinda zai yi, shi kuma taurin kai ko? Allah ya ba da zaman lafiya, sai kuje ku yi duk abinda kuke so, bana son jin kowacce irin magana indai kan auren nan ne…”

Ganin sun zauna yasa Abba miƙewa ya shige bedroom ɗin shi yana barinsu. Abdulƙadir kan shi a ƙasa yake, tunda yake da Abba bai taɓa ganin ranshi ya ɓaci haka ba. Shi kan shi Kawun jikin shi a sanyaye yake jin shi.

“Abbanka yace yarinyar nan maƙota take, kuma bazawara ce, abin ba zai yi wahala ba…da Babanta yana nan ma sai mu fara magana.”

Miƙewa Abdulƙadir ya yi yana jin shi kamar yana yawo a gajimare, komai yake jin ya yi mishi wani irin shiru.

“Sai mu duba mu gani.”

Ya faɗi, muryar shi na dawowa kunnuwan shi da wani irin yanayi. Tare da Kawu suka fita har ƙofar gidan su Nuriyya, sallama suka yi da Babanta, ya kuwa fito, ya gane Abdulƙadir ɗin, amma ya yi mamakin ganin su a ƙofar gidan. Gaishe da shi Abdulƙadir ya yi yana jin Kawu Ali na mishi bayanin komai. Sosai Baba ya nutsu yana sauraren su. Duk yadda yake son saka wa Nuriyya ido, zai yi ƙarya idan yace matsalar yarinyar bata damun shi tana kuma ɓata mishi rai.

Alhaji Ahmad mutum ne da yake gani da matuƙar mutunci, kuma yana taimaka mishi sosai da sosai. Ba zaiso Nuriyya ta zama sanadin da wannan zumuncin da suka shafe shekaru suna ginawa ya zube ba. A nutse yace wa kawu Ali,

“Ku bani mintina biyar in dawo.”

Cikin gida ya shiga ya sa aka kira mishi Nuriyyar, muryarshi babu alamun wasa yace,

“Abdulƙadir ne yaron Alhaji Ahmad da Kawun shi suka zo kan maganar auren ki.”

Ɗagowa ta yi ta kalli Baba tana jin ta kamar a mafarki, text ɗin ƙarshe da Abdulƙadir ya yi mata shi ne,

‘Karki kira ni, ki jira ni zan yi wa Abba magana.’

Bata kirashi ɗin ba kuwa, da zullumi ta kwana fal ranta, ko abinci sai ɗazun da Magriba ta tura shi ba don tana gane kanshi ba, haka kawai zuciyarta rawa take mata. Gani take ko sama da ƙasa za su haɗe ba za a bari Abdulƙadir ya aureta ba, yanzun kuma da Baba yazo mata da maganar sai take ganin kamar mafarki take.

“Kin ga abinda kika yi mana aurenki na farko, ba don bana miki addu’a ba, amma wallahi ban taɓa tunanin za ki samu namijin da yake da masu yi mishi faɗa bayan yayi bincike ya ji abinda ya fito da ke daga gidan mijinki su bar shi ya aure ki. Idan za a yi magana ta gaskiya ni ba zan bari ɗana ya aureki ba. Zuwa na yi in tambayeki don idan kika kaso wannan auren ki nemi inda za ki wuce daga gidan mijin, wallahi Nuriyya ba zan yi kaffara ba, kika kaso auren nan ba zaki zauna min a gida ba.”

Kai ta ɗaga mishi, haka kawai idanuwanta na cika da hawaye. Juyawa Baba ya yi ya koma ƙofar gidan ya samu su Abdulƙadir yana faɗin,

“Idan yanzun kun shirya ma ana iya ɗaura aure tunda ba budurwa bace.”

Ware idanuwa Abdulƙadir ya yi, yana da inda zai ajiye Nuriyya, yana da kuɗin Sadaki da zai bayar, amma akwai su lefe da sauran ƙananan abubuwa, duk da an taya shi bikin Waheedah ba zai manta kalar kuɗaɗen daya tara ba.

“Baba akwai su lefe”

Dariya Kawu yayi yana cewa,

“Kayya Abdulƙadir… Ai ta taɓa wani auren, za a iya ɗaurawa yanzun, duk da gaggawa na daga shaiɗan, amma auren za a iya ɗaurawa sai ku yi maganar lokacin tarewa da sauran abubuwa.”

Kai Abdulƙadir ya ɗaga yana faɗin,

“Babu kuɗi a jikina, sai dai in je banki in dawo yanzun.”

Jinshi yake kamar a mafarki, kai Kawu Ali ya girgiza mishi yana faɗin akwai kuɗi a wajen shi. Mota suka koma Kawu Ali ya ƙirgo dubu hamsin suka sake fita, masallaci suka je aka yiwa Liman magana, da wasu manyan mutane da suke zaune a majalissa nan gefen masallacin. Cikin ƙasa da mintina talatin aka ɗaura auren aka gama komai. Kawu Ali da kanshi ya sauke Abdulƙadir har gida don ya ce mishi ba da mota yazo ba.

Ya shiga cikin gidan, ya ɗora hannun shi kan handle ɗin ƙofa, amma ya kasa murzawa, komai da ya faru yake ji yana danne shi, kamar wani mafarki ne yake yi sai yanzun ya farka ya samu mafarkin da gaske ne. Aure ya yi, Nuriyya ya aura, ba wannan bane damuwar shi, bai faɗa wa Waheedah ba, bai kuma san ta in da zai fara faɗa mata ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 21Abdulkadir 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×