Skip to content
Part 21 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

A watanni uku babu dabarar da take tunanin tana da ita da za ta yi aiki akan Abdulƙadir. Ga wata irin soyayyar shi da take ji kamar ana hura mata wuta. In da ance ita Nuriyya za ta ajiye yadda take ji da kanta ta ɗauki duniya ta faɗa wa ɗa namiji tana son shi za ta ƙaryata. Amma sai ga ta, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba, har ta ɓace ƙirgan lokutan da ta furta wa Abdulƙadir din kalmar so. A rana tana iya tura mai saƙonnin text fiye da goma, tana tambayar lafiyar shi, ko ya ci abinci, da sauran duk wani abu da take tunanin in ta tambaye shi zai amsata.

Sai dai tun kafin ma ta ce mishi tana son shi ɗin, tana iya tura mishi saƙonni hamsin a whatsapp ya buɗe ya karanta ya yi banza ya ƙyale ta. saƙonnin ma da alama suna zuwa, amsa ce kawai bata samu, tana iya kiran shi sau goma a jere bai ɗaga ba. Yanzun kuma ta tsagaita mishi da kiran wayar, tunda ya ɗaga ya balbaleta da faɗin,

‘Ko matata sau biyu take kirana. Karki sake min kiran yara Nuriyya. Ba ki san bana so a dameni ba ko? Me yasa za ki dameni? Ranki zai mugun ɓaci kika sake min kiran yara. Idan ina son magana da ke, kiran farko zan ɗaga, idan bana kusa na zo na gani zan kiraki…’

Ko amsarta bai jira ba ya kashe wayar. Kwana ta yi tana kuka daren ranar. Komai sai da ta ji baya mata daɗi. Ta yi dana sanin sanayyar da ke tsakaninta da Waheedah, sanayyar da ta sa take kishinta, take son mallakar duk wani abu da take da shi, sanayyar da ta jefata cikin son mallakar Abdulƙadir har yake mata wannan wulaƙancin. A tsawon watannin kwata-kwata bata taka ƙafarta gidan Waheedah ɗin ba, sai dai su gaisa a waya, ko ta whatsapp wasu lokutan, haka ta ce mata tana gidan kawunta da ke Bebeji, ta je ta ɗan huta.

A watannin ko fita bata yi, tana gida kullum, samarin ma sun fita daga ranta, tana ɗan ɗaga kiransu ne wasu lokutan saboda ta samu katin waya. Waheedah kuma kan turo mata na dubu ɗaya da ɗari biyar duk wata, ta siyi data. Duk da tana jin lokaci zai zo da ba za ta buƙaci wannan taimakon daga wajen Waheedah ɗin ba. Ta dai samu Abdulƙadir ɗin, satin da ya gabata, har gayawa kanta ta yi ta haƙura da shi, ta gaji da wulaƙancin da take kwasa, amma da safe sai ta tsinci kanta da tura mishi saƙo ta gaishe da shi.

Yau ma kamar ko da yaushe, yana online wajen ƙarfe goma da rabi, don ya saka hoton Fajr a status ɗin shi, har ta buɗe ma ta yi mishi magana.

‘Fajr fa ya fi ku kyau.’

Ko buɗewa bai yi ba. Wani raɗaɗi ƙirjinta yake don ta san da Waheedah yake chatting, zuwa yanzun wani irin kishi take da ita na ban mamaki. Bata san me Abdulƙadir ya gani a jikin Waheedah ba, akan ce kana ƙiba in ka haihu, amma tana nan yadda take, kamar sillen kara, in za su jera ita da Waheedah, babu abinda Waheedah take da shi da za ta nuna mata. Tana da kyau ta sani, daga na fuska har na jiki, bata san abinda Waheedah ɗin take da shi har haka ba. Ko me ta yi wa Abdulƙadir ɗin har ya aureta.

“Yanzun haka mayyar ita tace tana son shi.”

Ta faɗia fili, zuciyarta kuma na saƙa mata, in dai wannan hanyar Waheedah ta bi, to ita ma gata akai, amma babu alamar nasara. Saƙe-saƙe take a zuciyarta. Kafin ta ji wayarta da ta saka a silent tana zuuuu alamar kira ya shigo. Ƙaramin tsaki ta ja, don bata san kowanne maye bane cikin dare, tana dubawa jikinta ta ji har kyarma yake, ga zuciyarta na wani irin dokawa, ganin sunan Abdulƙadir ɗin da ta yi editing zuwa,

‘Masoyi 💕’

Na fitowa ƙiiri-ƙiiri, tun da ta ce tana son shi ta sake sunan, haka kuma takan kira shi da shi a duk saƙonnin ta, bai taɓa kiranta ba, ita ɗin ma inta kira shi ba ɗagawa yake ba. Jikinta rawa yake sosai lokacin da ta kara wayar a kunnenta.

“Masoyi…”

Ta tsinci kanta da faɗi, muryarta a karye, tana jin shige da ficen numfashin shi ta cikin wayar, ya fi mintina biyu bai ce komai ba, ba don numfashin shi da take ji da shuu kamar alamun yana cikin mota ba, za ta iya rantsewa ya kashe wayar. Kafin ya ce,

“Sai da safe…”

Ya kashe wayar ba tare da ta samu damar amsa shi ba, murmushi ta yi ta sauke wayar ta rungume a ƙirjinta, wani irin nishaɗi take ji yana ratsata ta ko’ina. Ko ba komai yau ya kirata da kanshi, hakan kawai nasara ce. Da tunanin shi fal a ranta bacci ya kwasheta.

*****

Bata gane cikin Fajr kamar sadakar shi aka bata ba sai yanzun da take ɗauke da cikinta na biyu, da tun a satika kaɗan da shigarshi ya soma wasan kura da rayuwarta. Daga zazzaɓi zuwa amai tun kafin Asubahi. Duk wani labari da ta ji masu ciki na bayarwa lokacin da take da cikin Fajr ne ya haɗu waje ɗaya yake wujijjigata. Bata son jin ƙamshin duk wani abinci mai miya. Nabila ta kira ta kwashe mata duk wani kayan miya da yake cikin gidan ta tafi da shi. Abinci sai dai ta sa mai da yaji, man ma na ja, idan ta sha baƙin ruwa sai ta yi kamar za ta amayar da kayan cikinta. Citta ta gyara ta dandaƙa da kanumfari ta saka a fridge, duk in za ta sha ruwa sai ta ɗan tsiyaya a ciki don ya canza launi.

Bata taɓa ganin tashin hankali irin na watanni ukun nan ba, ga cikin har ya fito mata, kamar mai ‘yan biyu. Hankalin Abdulƙadir ya ƙi kwanciya, duk yadda take tabbatar mishi da lafiyarta ƙalau, laulayi ne kawai, kuma an ce zai mata sauƙi in cikin ya ɗan ƙara girma. Amma duk wani ɗan lokaci da zai samu cikin kiranta yake. Har dariya takan mishi idan yana mata wasu tambayoyin.

“Kanki na ciwo? Kina jin zazzaɓi, bani lamba daga 1 zuwa 10 ya kike ji?”

Wani lokacin har da fushin shi in ta ce mishi ita lafiyar ta ƙalau, ya sha kiran Hajja in ya ji muryarta can ƙasa yasa ta zo, kunya yakan bata kamar ta nutse a ƙasa. Akwai ranar da suna cikin waya amai ya taso mata, ta ajiye wayar, ashe yanata magana, sai da ta gama aman ta dawo hayyacinta ta kira shi.

“Wahee ban samu Hajja ba, na kira Abba amma, yace za a turo wani.”

Babu kalar salatin da bata yi ba, balbaleta da faɗan shi ya yi, me yasa ba zai kira Abba ba, ai ba abin kunya bane ba, su da za su je da baby gidan har ma su bashi. Meye don yasan babyn na hanya. Shiru ta yi har ya gama ya kashe kiran, ta yi murmushi kawai. Rigimar shi babu kalar da bata sani ba, akwai kalar da ta kasa sabawa da ita ne har yanzun kawai. Nabila ta zo ta yi mata su shara da mopping, anan ta kwana, da safe ma sai da ta soya mata dankali da ƙwai ta sa a kula, ta dafa ruwan zafi, har taliyar Hausa da Waheedah ɗin ta ce tana so a bayar ai mata sai da Nabila ta dafa mata, tukunna ta wuce gida.

Da Fajr ta wuce, ita ma ta samu sauƙi. Tana da tabbacin dai Abdulƙadir zai je ya ɗauko shi in ya iso. Ta ga ma har goma da rabi, wayar shi take kira ta ji yana ina, in ya bi motar dare da sassafe yake isowa. Ta ji sallamar shi, sanyi take ji saboda zazzaɓin da take ta fama da shi tunda dare, da ruwa mai zafi ta yi wanka, amma duk da haka sanyi take ji. Wando ne a jikinta dogo, baƙi, ta saka T-shirt, ta ɗauki rigar sanyin Abdulƙadir ɗin ruwan toka mai haɗe da hula ta saka. Kalaba ne manya a kanta da Nabila ta taimaka ta yi mata, ko ɗankwali bata saka ba, hular rigar sanyin ta ja ta saka a kanta.

Kafin ya buɗe kofar ta sakko daga kan gadon, a tsakiyar ɗakin suka hadu tana rungume shi, ya zagaya hannuwan shi a bayanta ya lumshe idanuwan shi, ƙamshin turarukanta sun canza mishi.

“Sannu da zuwa…”

Ta faɗi tana sake maƙalewa a jikin shi, wata irin kewar shi take ji tana danneta duk da yana tsaye a gabanta, tana jin ɗumin shi a jikin ta.

“Turarenki ya canza min.”

Abdulƙadir ya ce maimakon ya amsa mata sannun da ta yi mishi. Murmushi ta yi, batasan kalar sabon da ya yi da komai nata ba, da kuma kalar kula da yake yi, ko a whatsapp suke chatting in ya ga tana amsa shi kayi ɗai-ɗai sai ya fara tambaya me ya yi mata bata mishi hira. Baya so ya ga canji a tare da ita kowanne iri ne. Murmushi ta yi.

“Akwai ƙamshin da bana so a wancen, shi yasa…”

Ɗagota ya yi daga jikin shi ya sa ɗayan hannun shi ya taɓa kuncinta da shi zuwa wuyanta.

“Zazzaɓi kike ko? Ina hijabinki mu je asibiti.”

Kai take girgiza mishi tun kafin ya ƙarasa maganar.

“Na sha paracetamol ai, zai tafi, yana mun haka wani lokacin.”

Ƙanƙance mata idanuwa Abdulƙadir ya yi.

“Waheedah…”

Ya kira cike da alamar tambaya da rashin yarda da ita, yana ƙara taɓa jikinta, dariya ta yi ta kama hannun shi ta sauke daga wuyan ta.

“Da gaske.”

Numfashi ya ja yana fitarwa

“Nikam cikin Fajr ba haka ya yi bafa, baki sha wahala da yawa ba…”

Sanin halin shi yasa ta canza maganar da faɗin,

“Abinci ko za ka fara watsa ruwa?”

Ɗan jim ya yi, don yanajin yunwa sosai. Amma yafi so ya ci a nutse, jakar da ya dawo da ita ma a falo kan kujera ya ajiye. Tare suka shiga banɗakin, ya korota karta taɓa ruwa tun da ya ganta da rigar sanyi, ta mishi wani irin fayau, kamar cikin yasa ta ƙara haske sosai. Wanka ya yi ya fito, kaya ma shi ya ɗauko da kan shi, don tana gefen gado ta zauna. Tare suka fita zuwa kitchen ɗin, ya ɗauko mata kula da plate. Shayin shi ya haɗa a kitchen ya fito da shi, ita ta zuba taliyarta da manja, tunda babu abinda ta iya saka ma cikinta.

Zama suka yi, Abdulƙadir ya ɗan fara shan shayin da yake tunanin kamar ya mishi yawa ma, gashi sukarin bai ji ba, Waheedah ita da ta zuba in ya sha sai ya ji ya yi dai-dai.

“Shayin salaf…”

Ya faɗi yana ƙara kurɓa

“Baka zuba sukari ba?”

Ƙanƙance mata idanuwa ya yi.

“Na zuba.”

Taliyarta take cakuɗawa.

“Ka je ka ƙara…”

Kafada ya maƙale mata, don a gajiye yake jin shi, kuma zaman ya mishi daɗi. Tashi ta yi yana binta da ido, ta ɗauko kwalin sikarin ta ajiye a gaban shi, kallonta ya sake yi.

“Guda nawa zan saka?”

Ɗayan hannunta da babu manja ta saka ta ɗibi guda uku ta jefa mishi a kofin ta cakuɗa, don gara mata Fajr da taɓarar Abdulƙadir lokuta da dama, sai da ya ɗauka ya kurɓa, ta ce mishi,

“Ya yi?”

Kai ya jinjina mata yana soma cin dankalin.

“Ni baki bani taliyar ba Waheedah…”

Ta bakinta ta haɗiiye tukunna ta amsa shi,

“Sadauki taliyar hausa ce… Kwanaki dana dafa cewa ka yi min wacce irin taliya ce wannan?”

Shayin shi ya sake kurɓa.

“Amma ban ce bana ci ba ai, kuma wannan ba irin waccan bace, da manja fa, ina ta kallon ki tun ɗazun, baki bani ba. Kuma raina ya biya…”

Murmushi ta yi, ta tsame hannunta daga taliyar tana miƙa mishi kwanon, ita kenan Nabila ta dafa mata, don bata ɗauka zai ci ba, miƙewa ta yi ta wanko hannunta a kitchen ta dawo. Ta same shi ya cinye taliyar yana faɗin,

“Ki ƙara dafa mana anjima…. Irin wannan.”

Kai ta jinjina mishi kawai, shi ya kwashe kwanonin ya dawo.

“Bacci nake ji.”

Ya ƙarasa maganar yana miƙa mata hannun shi, ta kama tana miƙewa. Ta riga ta san ko bata jin bacci sai ta kwanta, rigimar Abdulƙadir bata ƙarewa, ko da Fajr na jariri haka ta dinga fama da su biyun. Sai dai ta saka Fajr daga gefenta, Abdulƙadir na bayanta. Ɗakinta suka wuce, duk da yana da nashi ɓangaren da bata ga amfanin shi ba, sai ta kwana huɗu ma bata taka sashin ba, takan shiga ta share in ya yi ƙura, haka ya siyi gidan ɓangare biyu, ɗayan ɓangaren bai kai nan inda take girma ba, amma da falo da bedroom da banɗaki, har da kitchen. Nata kuma bedroom biyune, kitchen harda store, kuma akwai banɗakin baƙi daban ta cikin falon nata.

Har kujeru da komai Abdulƙadir ya zuba a ɗayan ɓangaren, kitchen ɗin ne kawai babu komai, wasu lokutan in yana nan, takan ja shi su shiga, su zauna, kafin aljanu su samu wajen laɓewa. Ko minti sha biyar ba su yi da kwanciya ba, bacci ya ɗauke shi, ita ma gyara kwanciyarta ta yi ta rufe nata idanuwan tana jiran bacci ya yi gaba da ita.

*****

Bacci suka wuni yi, da suka yi Azahar ma komawa suka yi har la’asar, gara ma Abdulƙadir ace ramuwar bacci yake. Ita kam cikin ne yake sa ta wani irin bacci kamar kaza. Taliyar ta dafa musu suka ci. Suka zauna suna kallon wani indiyan fim, gaba ɗaya Abdulƙadir ya langaɓe mata, duk da zazzaɓin da take ji ya sauka, jikinta babu ƙarfin kirki. Amma ya tattara ƙafafuwan shi ya dora kan kujerar don ya kwanta a jikinta.

“Ka karya ni Sadauki… Sai ka huta ka ga.”

Waheedah ta faɗi jin yadda ya sake naniƙe mata. Sake gyarawa ya yi bai kulata ba, tunanin da ba shi da dalili ne baya son yi. Nuriyya kuma ta addabi rayuwar shi, tunda ya shigo gidan ya kashe wayarshi ya ajiye. Yasan yana kunnawa zai ci karo da saƙonninta. Bai san me take so da shi ba, bayan bata jira shi ba, aure ta yi abinta ta ƙyale shi, tunda bata san tana son shi ba sai yanzun. Shi yasa bata samun amsar shi, ɓacin ran da ya yi tunanin ya binne a NDA ne ta taso mishi da shi gaba ɗaya. Ba kuma ya so ana taso mishi da abinda ya riga ya wuce shi yasa.

Kusancin nan da Waheedah yasa ya ji sanyi-sanyi. Tunda ya shigo ya ɗora idanuwanshi akanta cikin rigar shi da ta yi mata yawa ya ji komai ya kwance mishi. Nuriyya na manne cikin kan shi, amma Waheedah ta saka shi jin nutsuwar da ita kaɗai take saka shi samu. Saboda haka ba zai kulata ba, ta saba cewa zai karya ta dama, ko hannunta ya riƙo sai ta fara cewa zai karya ta. Ko shi farkon auren su lallaɓata yake kamar yana tsoron da gasken zai karya ta. Amma zai iya rantsewa dama can Waheedah don dan shi aka yi ta.

“Matar kowa daga ƙashin haƙarƙari ake cirota, na sha taɓa nawa haƙarƙarin Waheedah, ƙasusuwan nada kauri, ki kalle ki don Allah…”

Ya taɓa ce mata, lokacin da ya kamo damtsen hannunta ya ji shi kamar babu tsoka a jiki, ta yi dariya kamar me ranar, amma fuskar Abdulƙadir ɗin ko alamar murmushi babu, don daga zuciyarshi ya yi maganar. Har sa mata ido ya yi kan abinci, amma tana ci lafiya ƙalau, kawai jikin ‘yan matan kenan. Yanzun daya gane ba zai karya ta ba, shikenan kuma. In ma ta faɗa sai dai ya yi dariya kawai. Ture shi Waheedah ta yi tana miƙewa ta nufi kitchen ganin biyar har ta yi. Wake ta ɗiibo ta dawo tana zama kan kafet tare da faɗin,

“Taso ka taya ni tsince wake…”

Kafaɗa ya maƙale yana sake kwanciya cikin kujera.

“Ni ki bar ni… Na gaji. Jikina ciwo yake min.”

Murmushi ta yi, neman tsokana ne yasa ta cewa ya taya ta ɗin dama.

“Ko za ka je ka ci abinci a wajen Hajja?”

Cike da rashin fahimta yake kallonta yana jiran ƙarin bayani kan dalilin da zai sa ya je gida cin abinci bayan ga gidan shi, ganin ta yi shiru yasa shi faɗin,

“Saboda ban tsince wake ba shi yasa ba za ki bani abinci ba?”

Dariya Waheedah take yi tana girgiza mishi kai.

“Abincina yanzun da mai da yaji ne, ko kana so ka ci da miya, ko ƙamshin nama bana so… Shi yasa na ce ko za ka je can.”

Kai ya girgiza mata.

“Ko me kika bani kin san zan ci ai, zan ci da mai ɗin nima.”

Shiru ta yi bata ce komai ba, ta san halin shi da abinci ne, shi yasa ta ce ko ya je wajen Hajja ɗin ya ji, har ranta hakan ba komai bane ba, in dai zai ci abinda yake so ya wadatar da ita. Amma Abdulƙadir ne, ko yana so ɗin ba zai je ba, gani zai yi tunda shi ne sanadin ƙin cin miyar tata, sai su ci ko me ya samu a tare. Kallon suka ci gaba da yi, ta ƙarasa tsintar waken ta je ta wanke ta ɗora. Da zai fita da magriba binshi ta yi ta kulle ƙofar daga ciki, duk da akwai Maigadi a bakin ƙofa. Don ya ce mata zai je gida ya gaishe da su Abba. Ta san kuma zai iya kai ƙarfe tara bai dawo ba, don har wajen Yassar sai ya biya.

*****

Gidan Yassar ɗin kuwa ya fara biyawa. Kowa a gidan na mishi mitar baya zuwa a gaisa. Banda Yassar babu wanda yake ganin shi, baya kulasu, ko Hajja ta mishi faɗa fushi yake mata. In gaisuwa ce suna yi a waya, kuma sukan haɗu a gida, idan an yi wani abu na rashin lafiya in ya zo ta faɗa mishi yakanjee ya duba su. Bai ga dalilin da zai sa a takura mishi da cewar sai ya je gidajen su ba, kuma da ƙaramar sallah duk ana haɗuwa har wanda suke nesa ma suna zuwa.

A masallacin unguwar su Yassar ya yi Isha’i tukunna ya hau babur zuwa Ƙofar Ruwa. A hanya ya kunna wayar shi yana jin saƙonni na ta shigowa ya kuma san Nuriyya ce. Jinta yake a wuyan shi, a rayuwar shi baya son abinda duk zai saka shi tunani, kuma ba zai ma kanshi ƙarya akan abin da yake ji a kanta ba. Kofar gidansu babur ɗin ya ajiye shi, ya sallame shi, ya saka canjin a wallet zai mayar aljihu ya hango Nuriyya tsaye ita da wani a bakin motar shi. Ko babu fitilar ƙofar gidan su Abdulƙadir ɗin da ta haska mishi ita, yana da tabbacin zai gane ita ɗin ce.

Wani irin tuƙuƙin kishi da ya sa idanuwan shi har lumshewa suke yi ne abin ya ba shi mamakin da bai tsammata ba. Bai san ƙafafuwan shi na takawa ba sai da ya ganshi tsaye a gabanta. Ita kanta ta girgiza don bata tsammaci ganin shi ba, tun da safe take kiran wayarshi a kashe, ga saƙonnin duk da ta tura basu nuna alamar sun shiga ba, ya kirata jiya da dare ya ɗorata kan tsanin buri, da safen nan ya girgizata ta faɗo. Har kuka ta yi, tunanin shi ne ya yi mata yawa shi yasa ma ta fito zancen ko bakomai za ta rage dare, in ta koma ta sake kiran shi in bata samu ba ta haƙura ta gwada kwanciya ko bacci zai sace ta, shi ne tunaninta lokacin da ta fito.

“Masoyi…”

Ta faɗi murmushi na ƙwace mata, kallo ɗaya Abdulƙadir ya yi wa yaron da yake tsaye ya zagaya ya shiga motar shi ya ja ta yana barin wajen.

“Me kike tsaye da wancan yaron Nuriyya?”

Ya buƙata ranshi a matuƙar ɓace, saboda bai ga dalilin da zai sa ta addabi rayuwar shi idan ta san za ta dinga kula wannan yaron ba, bai san me yasa za ta ce tana son shi ta fito tana kula ƙananun yara ba. Kafin ta bashi amsa ya ɗora da,

“Me kike so da ni? Me yasa za ki dame ni kuma ki fito kina kula wannan yaron? Da wannan yaron za ki haɗa min soyayya Nuriyya? Raini kike son ja min?”

Kai take girgiza mishi, gaba ɗaya yanayin shi ya tsoratata, muryarta a karye ta ce,

“Ka aureni, ka aureni….in ba ka son ganina da ƙananan yara ka aure ni.”

Murmushi Abdulƙadir ya yi mai sauti da ko kaɗan ba shi da alaƙa da nishaɗi, tana maganar aure kamar abu ne mai sauƙi, shi yasa ta zaɓi ta yi auren ta barshi tun daga farko. Magana zai yi ya ga ta matsa da sauri tana ɓoyewa a inuwar shi. Hakan yasa shi juyawa ya kalli inda idanuwanta suka bari, bai san waye ya shiga gidan su ba, amma ba zai wuce wani cikin ƙannen shi ba. Hankalin shi ya mayar kanta.

“Me kike ɓoye wa?”

Idanuwanta cike taf da hawayen da bata san ta inda suka taso ba ta tsinci kanta da faɗin,

“Naziru ne ya wuce…”

Lokacin da ta ce tana son shi, bata hango girman hakan ba, asalima idanuwanta a rufe suke da tunanin samun shi, ta manta alaƙar da take tsakaninta da Waheedah da za ta iya saka auren shi ya zame mata abu mai matuƙar wahala.

“Me yasa za ki ɓoye?”

Abdulƙadir ya sake tambaya, Nazirun ba baƙon ta bane, bai ga dalilin da zai sa ta ɓoye ba.

“Zai ganmu a tsaye.”

Ta amsa a sanyaye, tana saka hannu ta share ƙwallar da ta taru a gefen idanuwanta, wata irin soyayyar Abdulƙadir ɗin na dafa ruhinta.

“Me yasa kika ce kina sona idan ƙananun abubuwa irin wannan za su dame ki?”

Idanuwanta ta sauke cikin nashi tana rasa abinda za ta ce mishi, numfashi Abdulƙadir ya sauke, gaba ɗaya kanshi ya yi nauyi, baya so abu ya dame shi, ya ga alama kuma Nuriyya za ta dame shi.

“Kina sona da gaske?”

Kai ta ɗaga mishi, in ta ce kalamai za ta yi amfani da su ba za su isheta ba, kalar son da take mishi har mamaki yake bata. Kai ya jinjina mata.

“Zai zo ƙarshe in na sake ganinki tsaye da wani, bana so, raina zai ɓaci idan na ganki da wani.”

Kan ta sake ɗaga mishi.

“Bana so ana min magana da kai, ki buɗe bakinki in san kin fahimci abinda nake faɗi.”

Wani abu da ya yi mata tsaye a wuya ta haɗiye tana kallon fuskar Abdulƙadir ɗin.

“Ba zaka sake ganina da kowa ba.”

Wannan karon shi ya jinjina mata kai, ya juya yana barinta a tsaye a wajen, sai da ta ga ya shiga gida tukunna ita ma ta wuce, zuciyarta na wata irin dokawa ta ban mamaki. Abdulƙadir kuwa wani irin yanayi yake ji da bai taɓa tunanin zai ji ba, cikin gida ya shiga yana wucewa ɓangaren su. A ɗaki ya samu Hajja da ko gaishe ta bai yi ba, sallamar da ya yi ma bai jira ta amsa shi ba ya ce,

“Hajja ina Abba?”

Cike da mamaki take kallon Abdulƙadir ɗin.

“Lafiya? Me ya faru?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza mata.

“Lafiya ƙalau Hajja, ina son magana da shi ne, yana ina?”

Ita ba girkinta bane ba, Mami ke da girki, don haka ta ce wa Abdulƙadir ɗin,

“Yana ɓangaren shi…”

Kai ya jinjina mata ya fice zuwa ɓangaren Abba, da sallama ya shiga, ya samu Mami tana haɗa kwanonin abincin da da alama Abba ya gama ci.

“Abdulƙadir…An iso kenan.”

Abba ya faɗi da fara’a a fuskar shi. Murmushi Abdulƙadir ɗin ya yi shi ma yana gaishe da Mami da ta amsa shi cike da fara’a, kunya irin tata bata iya tambayarshi ya Waheedah ba, ta fice daga ɗakin ta barsu. Kan hannun kujera Abdulƙadir ya zauna.

“Abba…”

Ya kira yana ɗorawa da,

“Ina wuni.”

Gyara zama Abba ya sake yi kan kafet ɗin.

“Lafiya ƙalau, ya aikin? Ka samu kowa lafiya dai ko?”

Kai Abdulƙadir ya jinjina yana tsintar kanshi da daburcewa a karo na farko a rayuwar shi.

“Abba.. Dama zan yi magana da kai ne… Za muyi magana…”

Ya rasa kalaman da ya kamata ya yi amfani da su. Cike da kulawa Abba ya ce,

“Allah yasa lafiya”

Numfashi Abdulƙadir ya fitar da bai san yana riƙe da shi ba, sakkowa ya yi daga kan kujerar yana zama a ƙasa a gaban Abba ɗin, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Aure zan yi Abba…”

Maganar Abba yaji kamar daga sama, yadda ya ji ta ya fi yadda maganar auren Abdulƙadir ɗin daga farko ta dirar mishi.

“Aure Abdulƙadir?”

Abba ya tambaya cike da shakku, duk da matan shi huɗu, hakan bai hanashi jinjina maganar Abdulƙadir ɗin ba, don yasan ‘yan zamanin su da zamanin su Abdulƙadir ɗin akwai banbanci, adalci na wa yaran yanzun wahala, kuma da yawa sukan yi auren ne ba don ra’ayin hakan ba, sukan yi ne saboda dalilai da kala-kala, da yawa don suna samun matsala da matan su na gida ne. Maimakon su tsaya su fuskanci matsalar su shawo kanta, sai a dinga basu shawarar su ƙara aure, kamar hakan zai zama sanadin ɓatan matsalar da suke fama da ita.

Wasu kan yi don su huce haushin wani abin da matarsu ta gida ta yi ko take musu, wanda duk dalilai ne da basu kamata a duba su wajen ƙarin aure ba, shi yasa gasu nan, yara ƙanana suna fama da mata biyu da basu san yadda za su yi da su ba, tun da ta farkon ma tana neman fin ƙarfinsu. Baya so Abdulƙadir ya kasance cikin mazan da za su duba wannan dalilin wajen ƙara aure. Duk a cikin yaran shi babu wanda yake da mata biyu, a matan dai akwai wanda suke da abokan zama. Jin Abdulƙadir ɗin ya yi shiru yasa shi ɗora tambayar tashi da,

“Me yasa kake son ƙara aure? Kuna samun wata matsala da Waheedah ne?”

Kai Abdulƙadir ɗin ya girgiza mishi da sauri, ba zai ce a zamansu da Waheedah basu taɓa samun matsala ba, amma in zai faɗi gaskiya ya fi ɓata mata rai fiye da yadda take ɓata mishi rai, don ko abu ya yi mata bata taɓa ɗaga mishi murya ba, in ta yi mishi maganar ya balbaleta da faɗan shi sai dai ta bashi haƙuri ta wuce ɗaki, da duk idan ya bita kuka yake samun tana yi

Waheedah mace ce da yasan maza da yawa za su so samun irinta, bata taɓa bashi wani dalili na da na sanin aurenta ba, asali ma hukuncin aurenta na ɗaya daga cikin abubuwa mafi girma na alkhairi da ya samu rayuwar shi.

“Kawai ina son ƙara auren ne, babu wani dalili bayan haka Abba…”

Abdulƙadir ya ƙarasa maganar da yake ji tana fitowa daga zuciyar shi. Kai Abba ya jinjina, haka kawai yake jin maganar ta kasa zauna mishi. Har ga Allah duk lokacin da zai ga Waheedah a gidan sai ya ji gaban shi ya faɗi, don yana tunanin ko Abdulƙadir ɗin ya yi mata wani abu, amma har gashi aurensu na dosar shekaru biyar ko a fuskar yarinyar bai taɓa ganin damuwa ba. Ya fi kowa murna, don bai yi tunanin akwai macen da za ta iya haƙuri da bauɗaɗɗen halin Abdulƙadir na tsawon lokacin ba. Shi yasa ya ji auren bai zauna mishi ba, yana jin yaron har ƙasan zuciyarshi, baya son yana zaune lafiya ya jajibo abin da zai zame mishi matsala. Numfashi mai nauyi Abba ya sauke.

“Ka yi tunani akan maganar nan dai Abdulƙadir, aure ba abu bane da za ka tashi ka ji kana son yi, yana buƙatar natsuwa a cikin shi.”

Kai Abdulƙadir yake girgizawa, baya son abu ya dame shi, gudun tunanin ne yasa shi yanke hukuncin yin auren. Bai ga dalilin da Abba zai ce mishi ya ƙara yin wani nazari ba.

“Na gama duk tunanin da zan yi… Auren kawai nake son yi, shi yasa na zo na faɗa maka.”

Shiru Abba ya yi kafin ya ce,

“Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, ‘yar gidan wacece? Wacce unguwa take? In yaso sai ka yi mata magana su saka mana rana, ni da Alhaji Hamisu da Alhaji Hadi sai mu je a yi magana.”

Goshin shi Abdulƙadir ya taɓa yana share zufar da ya ji alamar tana tarar mishi. Bai taɓa tunanin muryarshi za ta yi saukar da ta yi yanzun da yake furta,

“Nuriyya ce Abba!”

Kallon shi Abba ya yi yana jiran ya tabbatar mishi da rashin hankalin da Hajja kance yana tattare da shi. Wani abu da ya ji ya tokare mishi wuya Abdulƙadir yake haɗiyewa, ko kaɗan baya son kallon da Abba yake mishi.

“Abba ita Nuriyyar…Don Allah karka ce wani abu…ita nake so in aura.”

Abba bai taɓa tunanin akwai ranar da zai so wanke fuskar Abdulƙadir da mari haka ba, da auren shi har da yaro.

“Ban taɓa yarda da baka da hankali ba sai yau Abdulƙadir, wallahi yau ka tabbatar min da cewar baka da hanlali. Nuriyya kake magana, ƙawar Waheedah, Nuriyya aminiyar matarka, ita ka zo kana faɗa min kana so ka aura.”

Kallon Abba Abdulƙadir ɗin yake yana roƙon shi da ya fahimce shi, ya san lokuta da dama mutane na barin abin da addini ya halarta musu saboda al’ada na ganin hakan bai kamata ba, kuma tun da ya fara tako ƙafarshi da niyyar furta maganar auren Nuriyya yasan zai fuskanci wannan matsalar, amma shi mutum ne da surutu irin wannan ba sa damun shi sam, baya jin akwai wani abu da addini zai halatta mishi kunya ta hanashi yi.

“Ba fa haramun bane Abba.”

Abdulƙadir ɗin ya faɗi yana jin yadda ranshi ya soma ɓaci, Hajja ce ya tsammaci za ta mishi wannan maganar ba Abba ba, tun da shi namiji me zai fahimta.
“Idan baka fitar min daga ɗaki ba, wallahi sai na wanke ka da mari, marar kunyar banza da wofi…”
Miƙewa Abdulƙadir ya yi yana faɗin,

“Babu abin da na yi da ba dai-dai ba Abba, ni kam zan aureta…”

Dafe kai Abba yayi, yana jin zagin da bai taɓa tunani ba na mishi yawo a cikin kai, da yana da tsohon hawan jini ɓacin ran da yake ciki yanzun zai taso mishi da shi. Yana jin Abdulƙadir ɗin na sake cewa,

“Zan mata magana sai ta faɗi ranar da za ku je ɗin.”

Kafin ya ja mishi ƙofar yana ficewa daga ɗakin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 20Abdulkadir 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×