Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Ashirin Da Hudu

5
(1)

<< Previous

Wayar ta sa a caji kamar yadda ta faɗa mishi, sai dai ta kasa dagowa daga tsugunnan da ta yi. Wayar take kallo tana gane asalin ma’anar ‘Yawo kan gajimare’. Duk da ba za ta ce ga ranar da wuyanta ya gajiya da ɗaukar nauyin kanta ba, yau kam jinshi take kamar baya jikin ta, gashi yana mata tamkar iska ta cika shi tana fita ta hancinta da kunnuwanta har ma da idanuwanta. Kafin kan nata ya yi wata irin sarawa cike da fahimtar ma’anar ‘Aure na yi ana gobe zan dawo Waheedah, ban san ya zan faɗa miki ba.’

Da kuma abinda hakan yake nufi a rayuwarta, numfashinta take ji yana barazanar ƙin wuce ƙirjinta ya kai inda zai ba zuciyarta damar ci gaba da dokawa yadda ya kamata. Wani irin numfashi take ja a wahalce, a karo na farko a rayuwarta da tashin hankalin da take ji ya fi ƙarfin hawayenta.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Ta samu furtawa tana zama sosai kafin ta ja ƙafafuwanta ta ɗora kanta a sama ko za ta ji sauƙin zafin da zuciyarta take mata, lokacin da ta fara laulayi jinta take a wata duniya ta daban, duniyar da wanda ya taɓa shiga halin da ta tsinci kanta ne kawai zai fahimta, bata san akwai duniyar da za ta shiga ta fi waccan wahalar sha’ani ba sai yanzun. Ciwo take ji daya wuce fatarta da jininta zuwa cikin ƙasusuwan jikinta. Idan ta ce ga asalin abinda ya fi mata ciwo ƙarya take.

Auren da ya yi da bata da darajar da za ta sani kafin a ɗaura shi, kallon idanuwanta bayan an ɗaura ɗin da yi mata murmushi kamar babu wani abu mai muhimmanci da yake tunanin ya kamata ya sanar da ita, ko kuma zaɓar ya faɗa mata abinda ya canza rayuwarta da ta tashi ta saƙon waya.

“Banda daraja har haka a idanuwanka Sadauki? Ban nuna maka farin cikin ka na da muhimmanci a wajena bane da zai isa in baka goyon baya akan kowanne irin al’amari ba?”

Waheedah take maganar kamar zararriya, don bata san a fili take yinta ba, ta dai san daga wani ɓangare na zuciyarta mai ciwon gaske maganganun suke fitowa. Bata san iya lokacin da ta ɗauka a zaune tana kallon bango ba tare da ta san asalin abinda take tunani ba, ban da wani irin ciwo da bata tunanin akwai abinda yake da maganin shi bata jin komai. Kamar a wata duniya da ta jima da bari take jin wayarta na ruri, da ƙyar ta iya raba idanuwanta daga bangon da take kallo tana sauke su akan wayar.

‘Sadauki’

Ta gani rubuce a jiki.

“Me kake so da ni Sadauki?”

Ta tambaya tana kallon wayar har ta yanke, wani sabon kiran ya sake shigowa. Hannu ta miƙa ta zare wayar daga chargy tana dannawa ta amsa kiran tare da karawa a kunnenta da wani irin sanyin murya ta ce,

“Hello…”

Tana miƙe kafafuwanta da suka yi mata sanyi, ga abinda ke cikinta da ta ji ya dunƙule waje ɗaya kamar yana tayata ɗaukar ciwon da take ji, hakan na sa ta fahimtar wani irin ciwon mara da bata san tun yaushe ya fara mata ba.

“Kin fara bacci ne?”

Kai ta girgiza mishi a hankali, a karo na farko da ta ji muryarshi na ƙara mata ciwo, ta ji da magana dashi gara mata kallon bangon da take yi, shi baya ƙara mata ciwo, amma muryar Abdulƙadir ɗin kamar gishiri a sababbin ciwukan da ya ji mata take jin ta.

“Na sa caji ne.”

Ɗan jim ya yi ta ɗayan ɓangaren kafin ya ce,

“Ina ta kira tun ɗazun babu network.”

Sama-sama take jinta, komai na mata wani iri.

“Har kun taho?”

Ta tsinci kanta da tambaya.

“Tun ɗazun, amma cunkoso har yanzun muna cikin Lagos.”

Kai ta jinjina mishi.

“Allah ya tsare maka hanya, ya kawo ka lafiya.”

Amsawa ya yi da,

“Amin…”

Yana ɗorawa da,

“Ki kula da kanku.”

Ita ta jinjina kan tana kasa cewa komai ta sauke wayar daga kunnenta, cajin ta mayar, da ƙyar ta iya miƙewa, wani irin jiri daya ɗibeta yasa ta koma tana kiran sunan Allah duk wanda ya zo bakinta. Numfashi take fitarwa a wahalce, ciwo take ji da ba zai misaltu ba, ta fi awa ɗaya a zaune kafin ta iya miƙewa, Fajr ma bata iya ta matsar da shi gefe ba, ita ta ja jiki kan katifar ta kwanta gefen shi. Ko sallar isha’i bata yi ba, amma ciwon da take ji ba zata iya zuwa banɗaki har ta iya yin alwala ba. Daga kwancen ma jiri take ji. Bata san dare ya yi ba sai lokacin da ta samu ta saukowa daga gadon ta ɗauki wayarta ta ga ƙarfe ɗaya. Ajiyewa ta yi, har lokacin jiri take ji.

Ga ciwon marar da takeji ya tsanantar mata, ga wasu ciwukan daban da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, amma mararta da zuciyarta su tafi ji. Bango ta dinga bi har ta kai banɗaki, da ƙyar ta iya ɗaura alwala ta fito. Daga zaune ta yi sallah don ba za ta iya tsayuwar ba, Azkar ta gabatar na bayan sallah, tana kwanciya a nan kan kafet ɗin don ko addu’a bata iya yi ba. Sunayen Allah duk wanda ya zo bakinta faɗin shi take yi ko za ta samu sauƙin azabar da take ji. Akan kunnenta akai kiran sallah na farko, har aka sake yin wani aka shiga masallaci tukunna ta iya raɓa jikinta da kafet ɗin. Alwala ta sake zuwa ta yi don bata jin ta cikin yanayin da za ta tabbatar tana da alwalar.

Ta shiga wata duniya mai wahalar misaltawa. Sallah ta dawo ta yi, tana sake komawa ta kwanta kan kafet ɗin. Sai yanzun take jin dama ta kira Yassar jiya ya ɗauki Fajr, don ko wanka ba za ta iya mishi ba, ballantana abin da za ta bashi ya ci. Wajen shida na safe ko motsin kirki bata iya yi, ga wani irin zazzaɓi mai zafin gaske da ya lulluɓeta. A haka Abdulƙadir ya shigo ya sameta, don shi ya ɗauka bacci take yi da ya yi ta sallama ya ji shiru.

“Waheedah…”

Ya kira yana jin gaban shi ya yi wata irin faɗuwa, da sauri ya ƙarasa yana tsugunnawa ya ɗagota, jikinta da ya ji kamar garwashin wuta yasa shi faɗin,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Yana ɗorawa da,

“Baki da lafiya? Tun yaushe Wahee? Me yasa baki faɗa min ba?”

Da ƙyar ta iya buɗe idanuwanta ta kalle shi, da gaske ƙara mata ciwo yake yi, daga muryarshi har taɓatan da yake yi. Tana ji ya zame ta daga jikin shi ya je ya tashi Fajr da ya shagwaɓe fuskarshi cike da bacci zai yi kuka, ganin Abdulƙadir ɗin yasa yaron wartsakewa dukkan shi.

“Paapi.”

Ya faɗi yana riƙo Abdulƙadir ɗin da ya kama shi ya sauko da shi daga kan gadon.

“Fajr tashi, Omman ka za mu kai asibiti.”

Abdulƙadir ya ƙarasa maganar yana yin banɗaki da Fajr, fuska ya wanke mishi ya ga abin ba zai yi ba. Da kanshi ya yi wa yaron wanka ya goge mishi jiki da towel, kaya ya zo ya ɗauko mishi yana jin daɗin yadda komai yake a shirye, bai sha wata wahala ba. Yana gama saka wa Fajr kaya da yake ta mishi surutun da hankalin shi baya kai, ya ga Waheedah ta ja jiki da ƙyar ta miƙe. Muryarta na rawa ta ce mishi,

“Ni kam ka barni da zuwa asibitin nan.”

Ko in da take Abdulƙadir bai kalla ba, Fajr ya zaunar kusa da ita, ya koma ya ɗauko wayarshi da ke cikin jaka. Yassar ya kira, sai da ta kusa yankewa tukunna ya ɗaga ba tare da ya ce komai ba, jin hakan yasa Abdulƙadir faɗin,

“Hamma banzo da mota ba, Waheedah bata da lafiya kuma…”

Da sauri Yassar ɗin yace,

“Subhanallahi, ina zuwa yanzun.”

Ya kashe kiran daga can ɓangaren shi, yana saka Abdulƙadir ɗin ɓata rai, baya so a kashe mishi waya a kunne, ko kadane abin na ɓata mishi rai, ya kuma rasa dalili. Wayar ya ajiye kan gado ya ƙarasa ya kama hannuwan Waheedah duka biyun, bata yi mishi musu ba. Ƙasa ya yi da muryarshi sosai saboda Fajr da ke zaune a wajen,

“In taya ki ki yi wanka?”

Kai ta girgiza mishi,

“Zan iya yi… Ka rakani banɗakin kawai.”

Taimaka mata ya yi har cikin banɗakin, duk da hankalin shi bai kwanta da ya barta ita kaɗai dine ba, fitowa ya yi ya tsaya a bakin ƙofar banɗakin, duk bayan wasu daƙiƙa sai ya kira sunanta duk da yasan babu kyau ta yi magana a banɗakin. Ba don Fajr ba shikamy shiga zai yi, karta faɗi a ciki ya shiga uku. Sai da ya ga ta fito tukunna hankalin shi ya ɗan kwanta, kama hannunta ya yi yana janta zuwa gefen gado ta zauna. Da kan shi ya ɗauko mata doguwar riga da inners ya ajiye mata akan gado gefen ta.

“Sannu, Bari in haɗa wa Fajr Tea.”

Kai Waheedah ta ɗaga mishi, ya kama hannun Fajr ɗin suka wucewa kitchen. Flask ya fara jijjigawa ya ji akwai ruwan zafi a ciki, ya samu kofi ya zuba madara da milo ya haɗa mishi rabi, ya saka sukari yana juyawa. Hannun yaron ya sake kamawa har falo ya zaunar da shi kan kafet yana ajiye mishi kofin shayin, Fajr na kama kofin ya ga yana tiriri ya kalli Abdulƙadir ɗin.

“Ba mai zafi Omma take bani ba.”

Kofin Abdulƙadir ya ɗauka ya kurɓi shayin, babu wani zafin da ba zai iya sha ba.

“Wanne irin shayi ne ba mai zafi ba Fajr?”

Shagwaɓe fuska Fajr ya yi.

“Na Omma…”

Kai Abdulƙadir ya jinjina yana ajiye kofin.

“Bata da lafiya, sai ka sha nawa yau.”

Turo baki Fajr ya yi.

“Baka bani biscuit ba.”

Runtse idanuwa Abdulƙadir ɗin ya yi, wajen matar shi yake son zuwa ya dubata, yaron yana da rikici, duk ƙarancin shekarun shi baya hana Abdulƙadir ɗin zane shi. Kitchen ya koma ya dudduba, bai ga in da Waheedah ta ajiye biscuit ba, idan akwai kenan. Ya dawo yana faɗin,

“Ni banga biscuit ba.”

Narai-narai Fajr ya yi da idanuwa.

“Ka san Allah idan kai min rigima zane ka zan yi Fajr. Ka zauna ka sha Tea ɗin ka kana jina…”

Ya ƙarasa yana juyawa ya koma wajen Waheedah, har ta saka kaya, da alama ta ɗan ji ƙwarin jikinta da ta yi wanka. Kusa da ita ya zauna yana taɓa wuyanta, da zazzaɓi har lokacin.

“Shi ne jiya baki faɗa min baki da lafiya ba?”

Idanuwanta ta ware mishi.

“Zazzaɓi ne kawai, zai tafi.”

Kai Abdulƙadir ya girgiza.

“Bana so… Karki kara min wannan, idan baki da lafiya ki faɗa min ni dai.”

Kai Waheedah ta jinjina mishi, ba za ta iya doguwar magana ba, ƙirjinta ya yi nauyi, mararta na ciwo har lokacin. Kiran Yassar ya gani, hakan yasa bai ɗaga ba ya miƙe yana ficewa daga ɗakin da falon gaba ɗaya. Fajr na ajiye kofin shayin ya bishi da gudu ko takalmi babu a ƙafarshi, yana ƙara gudun shi ganin Yassar ne, cike da farin ciki yake faɗin,

“Uncle…”

Ɗaga shi sama Yassar ɗin ya yi yana dariya.

“Fajr…”

Ya kira yana riƙe shi a jikin shi sosai.

“Zan bika ni.”

Kai Yassar ya jinjina.

“Tare za mu tafi ai kam.”

Tukunna ya kalli Abdulƙadir da yake mishi murmushi, haɗe fuska Yassar yayin kamar ba shi ya gama dariya ba.

“Ya mai jiki?”

Ya tambaya, kai Abdulƙadir ya jinjina.

“Yanzun kai ma Fajr dariya kana magana muryarka lafiya ƙalau…”

Mukullin dake hannun shi Yassar ya miƙa wa Abdulƙadir ɗin yana juyawa tare da Fajr ɗin tunda yana da kaya a gidan. Ƙyale shi Abdulƙadir ya yi ya koma cikin gida suna fitowa tare da Waheedah, da kanshi ya buɗe mata mota ta shiga ta zauna, ya rufe tukunna ya zagaya ta ɗayan ɓangaren, ya tayar da motar, yana ja suka fita daga gidan zuwa wani asibitin kuɗi na masu ciki da ba shi da nisa sosai da gidan.

*****

Har Azahar suna asibitin, don ruwa suka saka mata leda biyu. Har Hajja ya kira bata ɗaga wayar ba. Sosai ran shi ya ji bai mishi daɗi ba, dama ya faɗa mata ne, sai a turo wani cikin ‘yan gidan da zai taya su aiki, Waheedah ɗin ta huta. Amma zai yi komai da zai iya, kuma ya ga Waheedah ɗin da sauƙi, duk da an ce ta samu wadataccen hutu, kafin a sallamesu su tafi gida. Magunguna kala biyu ne kawai aka basu, duk zuwan da yake asibitin tare da ita, wannan ne karo na huɗu magani sai dai ya ga guda ɗaya ko biyu, sam basa tula magunguna.

“Nikam kamar in dinga zuwa asibitin nan in bani da lafiya, sam basa ba da magunguna masu yawa.”

Ya faɗi yana kwance takalman ƙafar shi, sai da Waheedah ta cire hijabinta tukunna ta kalli Abdulƙadir ɗin.

“Asibitin masu cikin Sadauki?”

Daƙuna mata fuska ya yi.

“Me yasa sai masu ciki ne kawai za su je? Basa bada magani da yawa.”

Kai Waheedah ta girgiza.

“Don na masu cikine shi yasa basa bayarwa da yawa, ba kowanne magani ake sha ba in ana da ciki.”

Kai ya jinjina mata yana fahimta, ita kuwa hannunta take murzawa inda akai mata ƙarin ruwa tana jin yana mata ciwo. Har lokacin ba za ta ce ga asalin yadda take ji ba, kallon Abdulƙadir ɗin kawai take yi duk in da ya yi, kamar tana jira ya ce mata maganar da suka yi daren jiya wasa ne, sai dai ta san akwai maganganun da ba don ba a wasa da su ba, Abdulƙadir ɗin ne dai ba zai taɓa mata wasa da su ba. Idanuwanta ta lumshe ta ji ya ce,

“Me za ki ci?”

Buɗe su ta yi a kanshi a hankali.

“Taliyar Hausa nake so, zan dafa idan na tashi. Kai me za ka ci?”

Don shi ya kamata ta tambaya ma, da ya kwaso tafiya, ko hutawa bai yi ba.

“Nima ina ci, a ina kika ajiye in dafa mana?”

Tun kafin ya ƙarasa take girgiza mishi kai, ita za ta shaida dahuwar taliyar shi, narkewa ne kawai bata yi ba, amma har shi kan shi bai iya yaci ba, daga ta tafi kitso, ta yi miyarta take ce mishi taliya za ta dafa, da ta dawo tun da babu wahala shi ne ya dafa, ta naɗi uban ruwan da ta tabbatar bai tafasa ba ya zuba taliyar.

‘Kin ga da na ɗauko ɗaya sai in ji kamar ta dahu, amma na ga bata yi fari ba kamar yadda kike dafawa.’

Abdulƙadir ɗin ya faɗi lokacin da ta shiga kitchen ɗin ta samu taliyar kan wuta. Idan ya dafa taliyar Hausa tabbas Kunu za ta koma.

“Na gode . Allah ya bada ladan niyya Sadauki. Zan dafa. Ka je ka watsa ruwa ka kwanta. Baka huta ba.”

Kai ya girgiza mata.

“Zanyi wanka, ni kam bana jin bacci. Ke da baki da lafiya, ya za a yi ki iya dafa taliya…na ga yadda kike yi. Zan dafa ni kam… Bari in fito wanka.”

Ya ƙarasa maganar yana shigewa ɗaki, bai jima ba ya fito, ya saka riga mai yankakken hannu da gajeran wando. Rigima ce cike da idanuwan shi, ɓarnar taliyar da take bala’in ji da ita zai mata.

“Akwai sauran doya, a dafa doya kawai.”

Murmushi Abdulƙadir ya yi.

“Baki yarda da ni ba ko? To wallahi sai na dafa…”

Ya faɗi yana shiga kitchen ɗin ya ɗauko tukunya. Miƙewa Waheedah ta yi tana bin bayan shi.

“Sadauki don Allah ni dai kabar shi, zan iya. Ka ga zazzaɓin ma ya sauka tun ɗazun.”

Da gasken take tun kafin a cire ruwan farko da ta samu bacci zazzaɓin ya ɗauka, ciwon marar ma ya yi mata sauƙi. Ƙirjinta ne dai take jin kamar zai buɗe da wani irin ciwo.

“Gara ki ɗauko min taliya ki je ki zauna. Kuma ba wasa nake ba.”

Taliyar ta ɗauko mishi, ta ajiye ta ja kujerar roba da take ajiye a kitchen ɗin in za ta yanka wani abu tana jin ƙyiwar tsayuwa ta zauna.

“Ruwan sai ya tafasa.”

Ta ce wa Abdulƙadir ɗin ganin duk mintina biyu sai ya buɗe tukunya. Da taimakon ta ya dafa musu taliyar, tana da soyayyen manja da zafi bai sa ya kwanta mata ba. A asibitin suka yi sallah dama. Don haka Waheedah ta je ta ƙara watsa ruwa itama ta sake rigar jikinta da take jin tana mata warin asibiti har lokacin tukunna ta fito sukaciy abinci. Yinin ranar babu in da ya fita sai masallaci, duk da tana iya ƙoƙarinta na ganin jikinsu bai haɗu da juna ba, ko hannunta bata so ya riƙe sai ta ji ya ƙara mata ciwon da take ji a ƙirjinta. Abin har tsoro ya fara bata. Bai mata zancen auren ba, ita kuma ta wa kanta alƙawarin in bai tayar mata da maganar ba, ba za ta ce mishi komai ba.

In ya tayar mata ɗin ma maganar da ta faɗa mishi jiya ita za ta maimaita mishi, bata da wasu kalaman ban da wannan. Sai da daddare ya samu ya tura wa Nuriyya text.

‘Ya kika wuni? Zan zo sai gobe in shaa Allah. Waheedah bata jin daɗi. Zan kira ki goben, ki kula da kanki.’

Bai jira amsarta ba yasa caji ya kwanta gefen Waheedah da duk idanuwanta da ta rufe bai hana shi ƙaƙume mata ba. Ta gode wa Allah da bai jima ba bacci ya ɗauke shi, amma ko ya ta motsa sai ta ji ya sake riƙe ta kamar zai shige jikinta. Ta jima sosai saboda yadda kusancin da ya yi da ita yake ƙara wa ƙirjinta ciwo, kafin ɓarawon bacci ya sace ta.

*****

Washegari da ƙarfinta ta tashi, babu abinda take jin yana mata ciwo ban da zuciyarta. Doya ta dafa, Anty ta aiko mata da wani yaji mai daɗi, lallaba shi take yi kar ya ƙare, tata doyar ta ɗiba don da mai da yaji take jin ci. Abdulƙadir ta soya mishi tashi. Tana gamawa ya fito shi kuma suka ci karo a bakin ƙofar kitchen ɗin.

“Ni ban isa ba ko Waheedah? Bazan ce kar ki yi abu ki ji ni ba.”

Kai ta girgiza mishi.

“Ya yi kyau, yanzun kuma ƙarya na yi. Me nace miki da na dawo masallaci? Ko shara kar ki yi… Amma ban isa ba shi yasa kika fito.”

Numfashi Waheedah ta sauke, ta san zai yi faɗa dama, amma ta kasa komawa bacci, aikin da ta fito tana yi yana rage mata tunani tunda babu wuta balle ko kallo ta yi, ko da wutar ma bata jin yin wani kallo ita.

“Ka yi haƙuri, ba wani aiki na yi ba, doya kawai na dafa na soya.”

Yadda ta yi maganar yasa shi jin wani iri, ƙarasawa ya yi yana kama hannunta.

“Don kin ga bana iya miki faɗa shi yasa kika daina jin magana ta.”

Murmushin ƙarfin hali ta yi tana ware mishi idanuwa.

“Don Allah kar ki ƙara yin komai, ki huta, in kin ji sauƙi sai ki yi.”

Kai ta ɗaga mishi. Ya sumbaci gefen fuskarta, ya ɗago hannunta yana shafa inda ya yi ja da alamar hudar zaman allurar ƙarin ruwan da aka yi mata.

“Sannu…”

Ya furta cike da kulawar da ta rage wa kusancin da ya yi da ita kara mata ciwon da take ji.

“Za ka karya yanzun?”

Kai ya ɗaga mata, ta ɗora da

“Ina da zoɓo a fridge, ko za ka sha Tea?”

Da sauri ya girgiza mata kai

“Yaushe kika yi zoɓo?”

Hannunta ta zame daga cikin nashi ta bude fridge ɗin ta ɗauko roba ɗaya.

“Tun shekaranjiya, da yawa na yi, Fajr duk ya min ɓarnar shi.”

Tare suka fita da kayyakin, Abdulƙadir a kular ma ya ci tashi doyar. Ita ma ta yi mamakin wadda ta ci don lokacin da suka zauna ko yunwar bata ji. Abdulƙadir ɗin ya kwashe kayan tana zaune. Tana jin shi yana ta kwaramniya da kwanoni. Sai da ya fito taga hannuwan shi duk ruwa.

“Me ka yi?”

Ta tambaya

“Wanke-wanke… Har gogewa na yi.”

Murmushi ta yi mishi da yake ganin kamar bai kai idanuwanta ba.

“Sannu da aiki…”

Amsawa ya yi da,

“Yawwa.”

Yana ɗan nazarin yanayinta kafin ya wuce ɗakin. Wayar shi ya ɗauka ya kira Yassar, yau dinma sai da yayi tunanin ba zai ɗauka ba tukunna ya ɗaga.

“Ina jin ka.”

Numfashi Abdulƙadir ya sauke.

“Gaba babu kyau Hamma…Kuma yanzun mun girma mu ba yara bane, bai kamata muna irin wannan…”

Bai ƙarasa ba saboda Yassar ɗin ya kashe mishi waya a kunne, lumshe idanuwa Abdulƙadir ya yi yana buɗe su tare da furzar da wani numfashi ran shi a ɓace, wayar Yassar ɗin ya sake kira, wannan karon yana ɗagawa ya ce,

“Wai meye?”

Numfashin Abdulƙadir ya sake fitarwa, zai ɗauki girman yau, girman da Yassar ɗin ya kasa ɗauka.

“Motar ka dama, in ba za ka buƙata ba, zan yi abu da ita.”

Ɗan shiru Yassar ya yi.

“Me yasa baka zo da taka ba? Wanne abu za ka yi?”

A ranshi Abdulƙadir ya yi niyya tun jiya, daya koma akwai abokan aikin shi da za su taho Kano su biyu satin sama, zai basu motar su taho mishi da ita, yabarta a gida tunda sai ya zo yake gane ya fi buƙatarta anan ɗin fiye da can Lagos. Tun da in ba wani dalili ba sun fi fita da motar aiki.

“Da gaske kana son sanin abin da zan yi da ita?”

Murya a daƙile Yassar ya ce,

“In ka gama ka dawo min da motata gaskiya.”

Ya kashe wayar. A karo na biyu a rana ɗaya da ya kashe wa Abdulƙadir ɗin waya a kunne, in da wani ne a gidan ba Yassar ba, ko me zai yi da motar ya haƙura, amma shi kan shi Yassar ɗin ya san ba zai yi zuciya ba. Shi kaɗai Abdulƙadir yake tambaya abu, ya zage shi, kuma ya bashi abin ya karɓa. Shaƙuwar da ke tsakanin su ta daban ce, Yasir ne suka kwanta a ciki ɗaya a lokaci ɗaya, amma zai iya rantsewa babu shaƙuwa mai ƙarfi irin wannan a tsakanin su. Don zai iya kwana biyu ma ba su gaisa da Yasir ɗin ba, musamman yanzun da shi yana Katsina, tunda aiki ya mayar da shi can ya samu ‘yar Katsina ya aura.

Falo Abdulƙadir ya dawo yana samun Waheedah a zaune in da ya barta. Zama ya yi ya zame jikin shi ya kwanta yana ɗora kan shi a cinyarta. Jin yana gyara kwanciya yasa ta faɗin,

“Karka danne min hancin yaro Sadauki.”

Dariya Abdulƙadir ya yi.

“Yarinya dai.”

Shiru ta yi ta ƙyale shi, cikin Fajr ma haka suka yi ta wannan gardamar, sai ta haifi namiji. Kuma shi ya ce baya son sani a asibiti, wannan ɗin ma ya ce mata ko an tambayesu za su ce basa son sani, sai ta haihu tukunna.

“Ina so in fita, amma bana so in barki ke kaɗai.”

Hannunta ta ɗora kan fuskar shi, tana jin maganar shi can nesa, da wani yanayi a fuskar ta ta ce,

“Ka fita abinka, na ji sauƙi ai. Ka taho min da kwakwa in ka gani.”

Kai Abdulƙadir ya jinjina mata.

“Bacci zan yi yanzun. Sai Azahar tukunna, kwakwa kawai?”

Ya ƙarasa maganar yana juya kwanciyar shi, ta ɗaga mishi kai. Bai ce komai ba ya lumshe idanuwan shi. Kanta Waheedah ta jingina jikin kujerar da ke bayanta. Tunani take, amma ba za ta ce ga ko na menene ba, kawai tasan ta lula tsakiyar wata duniya da bata ganin farkonta balle ta yi tunanin ƙarshenta.

*****

Jikin shi ya mishi nauyi saboda baccin da ya yi, don sai da Waheedah ta tashe shi da aka kira sallah. Hamma kawai yake a mota, har ya ƙarasa ƙofar gidan su Nuriyya ya yi parking, gida yake son shiga, amma baya so su ɓata mishi rai, kan shi a cunkushe yake jin shi, baya son haɗa abubuwa da yawa waje ɗaya, tunanin zai iya damun shi. A cikin motar ya yi zaman shi yana kiran wayar Nuriyya ya faɗa mata yana ƙofar gidan. A cikin motar ta same shi, tana zama da wani irin bugun zuciya na ban mamaki.

Turarenta da ya cika motar na mishi daban.

“Ina wuni”

Ta gaishe da shi cike da kunyar da bata san tana da ita ba.

“Lafiya ƙalau. Ya kike?”

Kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta da suka sha ƙunshin jan lallen da rashin aikin yi yasa ta ɗaura shi shekaranjiya. Ta mishi maganar tarewa ne saboda zaman gidan ya isheta, kwata-kwata Mama bata hira da ita, gaisuwa ce kawai take haɗa su, ko dariya take in ta hangota za ta daina, Baba ma in ta gaishe shi da ƙyar yake amsawa. Gashi babu damar ta fita daga gidan ballantana ta sha iska. Yanzun ma maganar take sason yi mishi, amma kunya ta hanata.

“Alhamdulillah.”

Ta amsa, Abdulƙadir ɗin na tsintar kanshi da kamo hannunta yana wasa da yatsunta da suka sha ƙunshin da ya yi mishi kyau sosai. Sai yake ganin hannun ya mishi daban, ko a mafarki bai hango riƙe hannun wata macen da za ta kira kanta da matar shi ban da Waheedah ba. Komai baƙo yake jin ya dawo mishi, duk da hannun Nuriyya ɗin a cikin nashi yasa wani abu tsirga mishi cikin kai yana yamutsa mishi tunani.

“Kin shirya ne?”

Da sauri ta ɗago kanta tana sauke idanuwanta cikin nashi tana kasa yarda da cewar shi ɗin mijinta ne.

“Eh na shirya, amma ban faɗa wa su Mama ba tukunna.”

Kai Abdulƙadir ya jinjina mata.

“Ki faɗa musu to, sai ki kira ni in ji yaushe… Gobe in shaa Allah zan wuce.”

Shagwaɓe fuska Nuriyya ta yi.

“Gobe? Da wuri haka Masoyi? Jiya ban ganka ba.”

Kallonta yake, sunan da take kiran nashi da shi na mishi banbaraƙwai a lokaci ɗaya kuma yana saka mishi wani irin nishaɗi. Murmushi ya yi da yasa gwiwoyin Nuriyya yin sanyi. Ta sha ganin murmushin a fuskar shi, amma yaune karo na farko da ya yi shi domin ita, wani shauƙin ƙaunar shi ta ji yana fisgarta.

“In ɗauko wasu kayan ka tafi min da su?”

Nuriyya ta buƙata da sauri tana ɗora ɗayan hannun nata saman nashi, tana jin daɗin yadda take da damar yin hakan yanzun. Kai Abdulƙadir ya ɗaga mata, ya faɗa mata in da za ta zauna akwai komai, kitchen ne kawai ba kaya. Ta siyi kayan kitchen sosai, kusan abinda ta yi da kuɗin da ya bata kenan, dama akwai sauran kuɗin kayan ɗakinta wancan da ta siyar bayan ta fito daga gidan Anas. Da su da sadakinta ta haɗa ta siyi fridge. Yana gidan Asma’u ƙawarta, don duk kayyakin ma ita ta dinga tura wa kuɗin tun da sana’arta kenan, siyar da kayan kitchen ɗin. Ta kuma kawo mata komai da ta siya, fridge ɗin ne da babu inda za ta ajiye.

Hannun Abdulƙadir ta saki ta fita daga motar cike da zumuɗin kayanta za su isa gidan Abdulƙadir ɗin, ita ma kuma za ta bi bayansu babu jimawa. Ganin ta fara fitowa da kaya yasa Abdulƙadir fitowa daga motar ya buɗe mata boot, yana taimaka mata ta zuba wanda za su shiga, wasu kuma a bayan motar. Tukunna suka yi sallama, yana wucewa gida. Da niyyar in ta kirashi ta ranar za ta tare ba, sai ya tura mata kuɗin abinci, dama wancan watan bayan tafiyar shi sai da ya tura mata kuɗin abinci tunda tana ƙarƙashin kulawar shi, yasan hakan haƙƙinta ne.

A hanya ya yi la’asar tukunna ya wuce gida. A mota ya bar kayan. Ya fara shiga gidan da sallama, a falo ya samu Waheedah, ta mishi wani irin kyau cikin jan lace ɗin da ya karɓi fatarta, ga jambakin da yake so manne da laɓɓanta tana saka komai kwance mishi.

“Wahee.”

Ya tsinci kan shi da faɗi maimakon amsa sannu da zuwan da ta yi mishi. Ƙarasawa ya yi ya zauna gefenta kan kujerar yana fuskantarta.

“Ya jikin ki?”

Idanuwa ta ware mishi

“Na ji sauƙi.”

Numfashi Abdulƙadir ya shaƙa yanajin komai ya mishi dai-dai.

“Sannu.”

Murmushi ta yi mishi da yasa ya kai hannu yana taɓa laɓɓanta, yadda baya dangwalo janbakin ta yana ba shi mamaki, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Idan babu matsala zata zauna a gidan nan, ɓangarena tunda bana amfani da shi.”

Abdulƙadir ya yi maganar yana sa tana jin kamar tana da zaɓin da bata ga dalilin da zai sa ya bata shi ba, bata ko hango auren shi ba, gashi da shi yanzun, kamar yadda yake da iko da kan shi, haka yake da iko da gidan shi.

“Banda matsalar komai.”

Ta faɗi tana jinta sama-sama, kamar gangar jikinta ce a zaune tare da shi. Ruhinta na tsaye a gefe yana kallon abubuwan da suke faruwa kamar bai shafe shi ba. Gyara zama Abdulƙadir ya yi yana kwantar da kanshi a kafaɗarta, ita ɗin alkhairi ce a rayuwar shi fiye da yadda za ta taɓa sani. Ta sa yana jin sauƙin abin da ko a labarin da yake ji mai matuƙar wahala ne.

“Na gode. Na gode da yadda kika sa komai ya zo min da sauƙi.”

Bata ce komai ba, don bata san me ya kamata ta ce ba, ya kai mintina goma a zaune ya yi luf a jikinta, kafin ya tashi.

“Sai ina?”

Ta tambaya.

“Akwai kayanta a mota, zan shigo da su “

Miƙewa Waheedah ta yi.

“Baka faɗa min yau za ta zo ba, ba ƙara share wajen ba.”

Ɗan daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Ban sani ba ni ma, kayan ne dai kawai. Ba za ki yi shara baki da lafiya ba.”

Kai ta girgiza mishi.

“Amman a haka za a saka mata kaya babu shara?”

Idanuwa Abdulƙadir ya ƙanƙance mata, a halin da take ciki ba za ta iya ƙarawa da faɗan shi ba. Shi yasa ta yi shiru, wajen ta bishi har bakin mota, duk da ya hanata ɗaukar komai. Tsaye ta yi tana kallon shi yana kwasar kayan yana kaiwa, jinta take kamar a mafarkin da za ta iya farkawa ko da yaushe. Har ya gama kwashe kayan tas. Tukunna ya kama hannunta suka koma cikin gida. Harya zauna ya tuna da kwakwar daya siyo mata tana mota, ya sake fita ya dawo da ita a leda. Guda biyar duk sun ɓare mishi. Miƙa mata ya yi.

“Na ɗauka ka manta.”

Kai ya girgiza mata, ya zauna, ita tana miƙewa ta nufi kitchen. Guda ɗaya ta wanke, ta saka sauran a fridge, wuƙa ta sa ta huda ta tsiyaye ruwan tana shanyewa ta yanka kwakwar da ta san ciki ne kawai ya saka mata sha’awarta, don sai dai in za ta yi kunun aya ta ɗan ɓalla, amma ba damunta ta yi ba, a kofi ta zuba ta ɗauka tana komawa falo, wuta ta gani.

“Yaushe suka kawo?”

Ta tambayi Abdulƙadir.

“Yanzun fa, kina tashi.”

Zama ta yi, komai a kunne yake, remote ɗin na hannun Abdulƙadir yana yawon shiga tashoshi da shi.

“Wahee baki bani kwakwar ba…yau kina cin abu baki bani ba.”

Murmushi ta yi mai sauti, duk da bata jin wani nishaɗi.

“Yi haƙuri … Wallahi na manta ne.”

Langaɓar da kai ya yi, bata saba mishi ba, kome take ci tana ba shi, bai saba tambayar ta ba. Miƙa mishi kofin ta yi, yasa hannu ya ɗauka. Kallo suke suna hira jefi-jefi har aka kira Magriba. Ita ta yi ɗaki, shi kuma ya fita masallaci. Ya dawo ne ya samu text ɗin Nuriyya.

‘Masoyi duk sa’ adda ka tashi ka zo mu tafi, na faɗa musu, na gama haɗa sauran kayan kuma.’

Wayar ya mayar aljihun shi. Yana cewa Waheedah,

“Yau za ta zo.”

Idanuwanta ta ware akan fuskarshi, kafin ta ɗaga mishi kai a hankali, cike da wani yanayi a idanuwanta da yasa shi ƙarasawa inda take ya zauna, ya kama hannunta yana riƙewa.

“Wahee ki min magana don Allah… Ki daina kallona haka… Ki min magana zai fi.”

Murmushin ƙarfin hali ta yi

“Abinne yake mun baƙunta, shi ne kawai.”

Numfashi ya sauke yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, duk da bata saba mishi ƙarya ba, haka kawai zuciyarshi ta kasa nutsuwa waje ɗaya. Bai ce mata komai ba ya sumbaci hannunta yana miƙewa.

“Saina dawo.”

Kai Waheedah ta ɗan ɗaga mishi.

“Allah ya tsare hanya.”

Tana sake kwanciya cikin kujerar. Abdulƙadir kuma ya fice daga gidan. Yana mota ne yake tunanin haka ya so bikin shi da Waheedah, ya je ya ɗauko matar shi su tafi, babu wannan al’adar na cewa sai an rakota, ya ɗauka duk sai an yi su walima da kamu kamar auren shi da Waheedah. Anty Talatu ce take faɗa mishi, ko da za a yi wani abin sai dai ko ita Nuriyya in za ta yi walima, kuma bata ce mishi za ta yi ɗin ba. Hakan ya fi mishi, ba don zai hanata in ta so yi ba, amma yana ganin ɗaurin aure ne kawai ya zama dole, kuma yake da muhimmanci, shi baya son duk wani abubuwa da bai zame mishi dole ba.

Sai dai abin da ya dinga mishi yawo bayan ya je ya ɗauko Nuriyyan a hanyarsu ta zuwa gida shi ne yadda Babanta bai buƙaci ya ganshi ba, ko ita Mama ɗin ma, a tunanin ko za a yi musu wata nasiha kamar yadda aka saka shi a gaba lokacin auren Waheedah. Sai ya ga ta buɗe mota ta shiga ba tare da ta ce mishi iyayenta na son ganin shi ba. Wata zuciyarsa sai take ɗarsa mishi ko haka aure na biyu yake, tun da ana ganin babu wata ƙuruciya a tattare da su biyun, kuma duk an riga da an faɗa musu abin da ya kamata a aurensu na farko.

*****

A hanya ya tsaya da suka yi siyayyar abin da yake tunanin za su buƙata, saboda Nuriyya ɗin, don yasan Waheedah ba komai ta ke ci ba yanzun. Ya dai siya mata apple ko za ta ci , tunda ya san tana so sosai. Tukunna suka ƙarasa gidan. Sai da Nuriyya ta ganta a cikin harabar gidan tukunna ta ji wata irin faɗuwar gaba da bata taɓa tunani ba. Da bata damu ba da ta faɗa wa su Baba cewar Abdulƙadir ɗin ya ce zai zo su tafi. Su duka Allah ya kiyaye suka yi mata ba tare da sun ƙara wasu kalaman a kai ba. Ita tana cikin nishaɗin da fushin da suke da ita ne ƙarshen abinda yake ranta.

Amma yanzun tunanin fuskantar Waheedah ya dawo mata da komai sabo, wani irin tsoro take ji har ƙafafuwanta na mata rawa. Da Abdulƙadir ya zagayo ya buɗe mata motar sai da ya miƙa mata hannun shi tukunna ta kama ta fito daga motar, ya mayar ya rufe, yana sakin hannunta ya buɗe bayan motar ya ɗauko ɗayan akwatinta ya soma jan shi zuwa cikin gidan. Da wani irin sanyin jiki na mamaki take bin bayan shi, tana kallo ya tura ƙofar ya shiga da cikin gidan da sallama.

Amsa shi Waheedah ta yi tana miƙewa, ta sake kaya zuwa wata atamfa da ta fi ɗazun yin kyau, ga wani irin kwarjini da ya ga ta mishi, gidan gaba ɗaya sai ƙamshin turarukanta yake yi da ya yi mishi daɗi.

“Sannu da zuwa…”

Ta faɗi, tana ware idanuwanta ganin Nuriyya, harara ta watsa mata.

“Sannu Nuriyya.”

Ta faɗi, don rabon da ta sa ta a idanuwanta har ta manta, duk da suna chatting kuma su yi waya. Amma bata ce mata ta dawo ba, tunda ko shekaranjiya ta kira ta sun gaisa. Ita kuwa Nuriyya wani irin ras ƙirjinta ya doka jin kalaman Waheedah ɗin, da kuma hararar da ta yi mata. Maganar tata na sa Abdulƙadir ya ji nashi ƙirjin ya doka, cikin wani irin tashin hankali ya taka yana kama hannun Waheedah ya soma janta, juyawa ta yi ta ce wa Nuriyya.

“Ina zuwa…”

Kafin ta mayar da hankalinta kan Abdulƙadir ɗin cike da mamaki. Har bedroom ɗinsu, sannan ya saki hannunta tana kallon zufar da goshin shi yake yi.

“Waheedah…”

Ya kira yana jin sauran kalaman sun maƙale mishi, kallon shi take yi da irin zufar da yake yi, kafin wani abu ya sara mata a tsakiyar kai. Lokacin da ta yi wa Nuriyya magana ta ga ta matsa tana ɓoyewa bayan Abdulƙadir ɗin har jikinta na taɓa nashi, bata san me yasa sai yanzun ƙwaƙwalwarta ta zaɓi ta yi processing wannan yanayin ba. Numfashi take ja a hankali tana fitar da shi, a nutse take yin hakan tana son iskar ta isa inda ya kamata. Kafin ta iya kallon Abdulƙadir, muryarta na dukan dodon kunnensa da faɗin,

“Nuriyya…”

Ta yi shiru tana sake jan wani numfashin ta tabbatar da ƙirjinta ba zai buɗe zuciyarta ta fito ba, tukunna ta ci gaba,

“Nuriyya ka aura?”

Kasa magana ya yi, zufa yake ji tana tsatsafo mishi a duk wata kafa da zai iya ji, abin har mamaki yake bashi, tun da zazzaɓi ne ruf ya ji ya rufe shi duk da zufar da yake yi.

“Ma shaa Allah.”

Waheedah ta faɗi tana sake kallon shi da faɗin,

“Ka barta ita kaɗai.”

Ya buɗe bakin shi ya fi sau biyar yana mayarwa ya rufe kafin ya iya furta,

“Waheedah…”

Dariya ta yi da ta sa shi sake kallon ta.

“Sadauki… Ka je…”

Ba don yana son ya tafin ba, sai don yana so ya fita daga ɗakin ko zai ji iska na ratsa shi. Fita ya yi yana samun Nuriyya a tsaye bakin ƙofa kamar mai jiran kyat ta buɗe ta yi ta kanta. Da gasken a tsorace take, don tana da tabbacin Abdulƙadir ɗin ya janye Waheedah ne don karta far mata.

“Mu je..”

Ya faɗi lokacin da ya ƙarasa yana kama akwatinta ya ɗauki sauran ledojin da bai san ya sake su ba, suka wuce har ɓangaren da za ta iya kira nata yanzun. A falo ya ajiye akwatin ya nufi bedroom ɗin ta bi bayan shi, ledar ya ajiye yana shiga banɗaki ya ɗauro alwala, ita ma ya ce ta je ta yi. Sallah ya ja su suka yi ta godiya ga Allah, kafin Abdulƙadir ɗin ya miƙe ya ɗauko ledojin yana cire na Waheedah ya fice daga ɗakin ya nufi ɓangaren ta, ƙwanƙwasawa ya yi yana turawa.

A tsaye ya sameta tana ɗauko kayan bacci.

“Sadauki…”

Ta faɗi, ya ƙarasa.

“Apple na siyo miki.”

Hannu ta miƙa ta karɓi ledar.

“Aikam ka kyauta, don bana jin cin komai.”

Space ɗin da ke tsakanin su Abdulƙadir ya haɗe yana zagaya hannuwan shi ya rungumeta a jikin shi. Zuwa yanzun ya kasa gane ko da gaske lafiyarta ƙalau, ya san Waheedahr shi daban take da duk wasu mata da ya taɓa cin karo da su. A kaf duniyar shi kuma Hajja ce kawai macen da Waheedah bata yi wa nisa ba, duk da haka yana jin kamar ya kamata ta nuna mishi ranta ya ɓaci, ko ya ga kishi a idanuwanta, amma ya kasa ganin komai, yana kuma jin kamar tana ɓoye mishi asalin abinda take ji ne.

Sosai ya riƙeta a jikin shi

“Allah ya bani ikon yi muku adalci.”

Ya furta a hankali yana lumshe idanuwan shi, ba don zuciyar shi bata dokawa Nuriyya ba, sai don yanajin in da Waheedah take babu wanda ya taɓa hangowa balle har ya zauna. Ita ɗin daban ce a rayuwar shi. Hannuwanta Waheedah ta zagaya ta bayanshi tana sake shigewa jikin shi, ta lumshe idanuwanta da yadda take jin zuciyarta kamar da ɓulallun tsokoki aka jerata, yanzun kuma rugujewa take ta ko’ina, ƙurar ce take saka jikinta ɗaukar wani irin ɗumi. A hankali ta zame jikinta daga nashi tana sauke idanuwanta cikin nashi, ranƙwafowa ya yi ya sumbace ta.

“Sai da safe.”

Ya faɗi yana juyawa, bata iya ce mishi komai ba, har ya fice daga ɗakin yana komawa ya samu Nuriyya da tunda ya fita take jin kamar ta bi bayan shi ya dawo saboda wani irin azababben kishi da ya turnuƙeta, gani ta yi ya daɗe, zuciyarta har tafasa takeyiy, kwana ɗaya take da shi, ya ce mata gobe zai wuce, Waheedah ba za ta bar mata shi ya dawo ba, zuwa yanzun kishi ya maye gurbin duk wani tsoro da ta shigo da shi gidan. Murmushi ta yi tana ganin ya shigo, jikinta ya mutu ganin bai mayar mata da murmushin ba.

Ƙarasawa ya yi ya zauna gefenta yana kallonta, fuskar shi babu alamar wasa ya ce,

“Bana son tashin hankali, bana son rigima ba don ban iya ba, ban san yadda zan daina ba idan na fara. Na san halin matata tun kafin in aureta, na san abin da Waheedah za ta yi da wanda ba za ta yi ba tun kafin in san zan aureta, ban san halinki ko ɗaya ba na aureki, idan har na ji rigima a gidana daga wajenki hakan zai fara.

Ko baki girmama Waheedah ba idan baki shiga huruminta ba na san ba za ta taɓa biye wa ko me za ki yi ba. Zaman lafiyarta na da muhimmanci a wajena, idan har zamana da ke zai yi nisa za ki zauna da ita lafiya…”

Kai Nuriyya ta jinjina mishi a hankali, ita ma ta san halin Waheedah ɗin, ba sai ya jaddada mata ba, wanda duk yake tare da Waheedah ya san halinta, kuma ita bata shigo gidan don ta nemi rigima da ita ba, duk da tana jin idan Waheedah ta yi mata ba za ta ƙi ramawa ba. Za dai ta yi ƙarya in ta ce idanuwanta basa mata yaji da shirin taruwar hawayen baƙin cikin maganganun shi. Wani irin kishi take ji marar misaltuwa, zuciyarta na ɗan tsahirta mata da hannunta da Abdulƙadir ɗin ya kama.

*****

Waheedah kuwa Abdulƙadir na fita daga ɗakin ledar apple ɗin ta buɗe ta ɗauki guda ɗaya ta shiga banɗaki ta wanko ta dawo kan gado ta zauna. Cinye shi ta yi ba tare data gane ɗanɗanon shi ko dalilin da yasa take ci ba, kafin ta ja ƙafafuwanta zuwa kan gadon ta kwanta akan bayanta, jin ƙirjinta na shirin buɗewa yasa ta juya tana kwanciya kan gefen hannunta na dama. Wani abu take ji yana zubar mata, da sauri ta sa hannu ta taɓa fuskarta, amma babu ɗigon hawaye ko ɗaya, kuka take amma daga ciki.

Ranar ne ya zame musu MAFARIN komai da ya kawo su inda suke yanzun, ranar ne kuma Waheedah tajie ta shiga wata duniya da ta yi nisa da zubar hawaye, duniyar da ta bata mukullin waccan da ta bari tana buɗewa tana zuba duk wani ɓacin rai da zai sameta ta rufe har zuwa yanzun.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×