Skip to content
Part 5 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Da yawan lokuta idan aka tashe su daga makaranta sukan fi mintina sha biyar suna jira kafin a zo a ɗauke su. Yazid ya fi kawo su ya zo kuma ya ɗauke su, amma kowa in za a tambaye shi zai ce ya fi son Mubarak ya zo, don duk gidan babu ɗan raha irin shi, kuɗin duk da yake aljihun shi kuma ranar akan su zai ƙarar, duk abinda za su nuna suna so sai an tsaya an siya. Yanzu ba sa komawa lokaci ɗaya da Abdulƙadir, saboda yana tsayawa extra lesson ɗin da zai taimaka mishi wajen zana jarabawar aji shida.

Yau ɗin kuwa sa’a suka ci Mubarak ne ya zo ɗaukar su, kowa ka duba fuskar shi kar take.

“Ina Commander ɗin naku?”

Ya buƙata yana sa Amatullah jan wani numfashi a tsorace.

“Hamma…”

Suka kira kusan gaba ɗaya, dariya Mubarak ya yi.

“Ban san ya akai bai ji sunan nan ba har yanzun.”

Jinjina kai Zahra ta yi, tana hasaso kalar dramar da za a yi duk ranar da ya ji suna kiran shi da Commander ɗin nan. Mubarak har ya juya motar ya hango mai yalo a tsallaken titi.

“Wa zai siyo mana yalo?”

Ya buƙata yana kallon Waheedah da ke zaune a gaba, don kafin ma ta ja ƙafarta cikin sanyin tafiyarta da mutane da yawa za su iya kuskurewa da yanga sun gama shiga motar, gaba kaɗai ya rage. Jakarta ta ajiye tana cewa,

“Kawo a siyo… Wane iri? Farin?”

Daga baya Nazir yace,

“Ni dai bana cin fari.”

Mubarak juya ya harare shi.

“Ka ji min yaron nan fa, na ce zan siyo da kai ne?”

Ya zaro ɗari biyu ya miƙa wa Waheedah.

“Kowanne na ɗari.”

Motar ta buɗe ta sauko, bayan ta ɗan tsaya daga bayan motar, abubuwan da take tsoro a rayuwarta ba su da yawa, tsallaka titi na ɗaya daga cikinsu, ba ta so ta yi magana ne su isheta da tsokanar su da ba ta ƙarewa shi ya sa ta karɓa, amma zuciyarta dukan uku-uku kawai take yi. Da ƙyar ta iya tsallakawa ɗaya hannun, tana tsaye a tsakiya, ganin motocin da mashina take suna wucewa da gudun da take tunanin ko suna da niyyar tashi sama ne. Banda zare idanuwa babu abinda take yi , juyawa ta yi don ta tsallaka ta koma, amma abin ya gagara, da ta sani ta ce wani ya je, yanzun take jin gara tsokanar su da wannan tashin hankalin da take ciki.

Yana daga ɗayan ɓangaren shi da Imran da Nawaf da suka jashi suna fitowa da shi, kasancewar ba sa fara extra lesson ɗin sai biyu da rabi cif, ana bada rabin awar don sallah da cin abinci.

“Lokaci yana tafiya, wane iskanci ne wannan wai? Ku siyi kome zaku siya mu koma don Allah.”

Cewar Abdulƙadir yana duba agogon dake manne a hannun shi. Imran ne ya kalle shi, don Nawaf bai yi niyyar asarar bakin shi ba.

“Karka ɗaga mana hankali Malam, ka koma abinka mana.”

Wani kallo Abdulƙadir ya watsa wa Imran ɗin.

“Ai kuwa ƙarya kake, ku biyun, yadda kuka janyoni na fito haka za mu koma tare.”

Ya ƙarasa maganar yana gyara tsayuwarshi, kamar ance ya ɗaga idanuwan shi, ya kuwa sauke su kan Waheedah, duk da tana juyawa zuwa ɗayan ɓangaren haɗi da ba shi baya bai hanashi ganeta ba, akwai farare a makarantar sosai, har da yaran ƙwarori da suke makarantar, yana tunanin da kalar farin su ne kawai zai iya kwatanta na Waheedah, yanzun ma yadda ya shigar mishi idone ya gane ita ce , sai kuma yanayin sirantakar. Sake ƙanƙance ƙananun idanuwan shi ya yi ganin ta sake juyowa ta fuskanto inda yake tsaye, da alama a rikice take. Apple ɗin dake hannun shi ya juya yana tunanin abinda ya tsallako da ita titi. Bai amsa Imran da ke tambayar shi ko ya sake shawarar tafiya babu su ne ba, don abarba suka siya ana fere musu. Titin ya tsallaka yana takawa harya ƙarasa inda take. Saboda a daburce Waheedah take ko kula ba ta yi da shi ba.

“Uban me ya tsallako dake?”

Muryar shi ta daki kunnuwanta ta ƙara tsoratata, baya ta yi saboda yadda zuciyarta ta yi wani irin tsalle, da zafin nama Abdulƙadir ya riƙo hannunta ɗaya ya mata wata irin damƙa kamar zai karyata, bakin shi da take ganin yana motsi ya tabbatar mata da ba magana kawai yakeyi ba, faɗan shi yake mata da ba ya ƙarewa, amma ba ta jin shi, ta tsorata har cikin ranta, da bai riƙe ta ba da labarin ya banbanta, tana ji ya ja ta suka tsallaka ɓangaren titin da ya baro. Hannunta ya saki ya kai nashi hannun ya ɗan goge wani abu a goshin shi da yake jin ya taru.

Ba don yadda zuciyarshi take bugawa ba da ya ɗauke ta da mari.

“Me za ki yi a tsallaken titi?”

Ya buƙata yana kafeta da idanuwan shi da suka saukar mata da wata irin nutsuwa.

“Ya… Yalo zan siya.”

Numfashi Abdulƙadir ya ja yana saukewa, wani irin yanayi yake ji da ba ya son alaƙanta shi da tsoron da ya ji, runtse idanuwan shi ya yi yana sake buɗe su, sam ba ya son tuna yadda ta kusan faɗawa titi.

“Hamma Mubarak yace in siyo…”

Waheedah ta faɗa a tsorace, ba tsoron titin da ta kusa faɗawa ba, tsoron yanayin da take ganin Abdulƙadir ɗin a ciki, yadda ya ɗago da idanuwan shi ya sa ta kai hannuwanta duka biyun ta rufe kuncinta da su, wani irin dogon kallo ya yi mata ya kai hannun shi wajen fuskarta, matsawa ta ɗan yi a tsorace ta rufe idanuwanta gam, cikin yanayi biyu zuciyarta take bugawa, yadda take cike da tsoron shi, da kuma yadda ta kan yi duk idan yana kusa da ita haka. Ɗari biyun da ke cikin hannunta ya kai ‘yan yatsun shi ya fizge haɗi da nufar inda mai yalon yake, bai san me take tunanin zai yi ba, dukanta ne ƙarshen abinda ya zo mishi.

Mai yalon ya miƙa wa kuɗin ya tsaya.

“Na nawa?”

Mai yalon ya tambaya.

“Na duka.”

Kai ya jinjina wa Abdulƙadir ya ɗauko leda tare da sake faɗin,

“Wane iri?”

Wani irin kallo Abdulƙadir ya watsa mishi, yalo duk ba yalo bane da zai tsare shi da tambayar banza.

“Malan ka saka min yalo, karka isheni da tambaya dan Allah.”

Ya ƙarasa maganar da jan ƙaramin tsaki, daya miƙo mishi ma a hasale ya karɓa, ranshi a ɓace yake jin shi. Waheedah na tsaye inda ya barta, ta sauke hannuwan ta daga kuncinta saboda batai ji marin da ta yi tsammani ba. Ba tare da yace komai ba ya sa ɗayan hannun shi ya damƙi nata da shi ya ja ta ba tare da yace komai ba, hannun nashi ta bi da kallo, wani irin yanayi na lulluɓeta, kafin ta kalli fuskar shi da take a nutse, yadda wani abu ke motsi a kuncin shi da ke nuna alamar ciza haƙoran shi yake ta cikin bakin shi ta san ranshi a ɓace yake. ‘Yan gidan duka sukan ce kullum ma ran Abdulƙadir a ɓace yake.

Ta san ba dariya yakan yi ba, in kuwa ya yi takan ga baƙuntar yanayin akan fuskar shi, amma ita tana gane idan ranshi a ɓace yake ko ba a ɓace yake ba, ba ta san ya akai take ganewa ba, tunda ta taɓa gwada yi musu bayani sau ɗaya suka saka ta a gaba da dariya ba ta sake kwatantawa ba. Fuskar shi take kallo tana binshi duk inda ya ja ta, ba ta san sun tsallaka duka titin biyu ba sai da ya saka ledar yalon a hannunta ya saki hannun tukunna.

“Idan na sake ganin ko da wasa kin nufo kusa da titi sai na zane jikin ki Waheedah, Allah sai na zane ki, kina jina ko?”

Kai ta ɗaga mishi a hankali, bai jira amsarta ba, duk cikinsu ita kaɗai ce ba ya damuwa da sai ta mishi magana da bakinta, in ta ware mishi idanuwanta haka tana kallon shi da farar fuskarta ya san ko kasheta zai yi ba iya magana za ta yi ba. Don haka ya juya ya zagaya inda Mubarak ya fito daga motar ya tare mai yoghurt yana zaɓa yana sakawa a mota.

“Hamma idan ka san za ka siyi wani abu tsallaken titi ka daina aiken yara, in ba zaka tsallaka da kanka ba ka haƙura.”

Ɗago kai Mubarak ya yi yana kallon Abdulƙadir ɗin da in za su gwada tsayi a kafaɗar shi a kanshi zai tsaya. Duk da ba wani nisa bane a tsakanin su ta ɓangaren shekaru, amma ya girmi Abdulƙadir ɗin, yadda ya yi tsaye yana ba shi umarni ya sa shi yin dariya da faɗin,

“To Abba…”

Cikin ido Abdulƙadir ya kalle shi.

“Da gaske nake, karka sake aiken su tsallaka titi, ba na so…”

Kai Mubarak ya ɗaga mishi, don ba zai iya da masifar Abdulƙadir ɗin ba, juyawa yake da shirin tafiya, Mubarak yace,

“Ka zo ka ɗauki yoghurt.”

“Bana sha…”

Kallon shi Mubarak ya yi.

“Daga abin arziƙi?”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Ni ma bance wani abu ba, bana sha kawai nace.”

Hannu Mubarak ya ɗaga mishi.

“Naji, sai anjima, jeka abinka.”

Tafiyar kuwa yayie ya nufi hanyar da za ta mayar da shi cikin makarantar. Waheedah kuwa da ƙyar ta iya jan ƙafafuwanta ta shiga cikin motar. Kan sit ɗin da Mubarak ya tashi ta ɗora mishi ledar yalon, hannunta take murzawa inda take jin na Abdulƙadir har lokacin, zuciyarta na mata wani irin yanayi da ta kasa fahimta. Har Mubarak ya shigo ya ba wa kowa yoghurt ɗin shi, nata kam karɓa ta yi ta zage aljihun jaka ta jefa a ciki, haka yalon ma, don ji take sun takura yanayin ta, kanta ta jingina da jikin motar tana lumshe ido, kafin ta daina jin hayaniyar da suke a cikin motar don ta ɓace a cikin duniyar tunani.

Jikinta gaba ɗaya a sanyaye take jin shi, banda yanayin fuskar Abdulƙadir ɗin lokacin da ya riƙo ta babu abinda take hasasowa, so take ta ji ta a kwance a ɗaki, ta janyo bargo ta rufe jikinta gaba ɗaya har kanta, ba za ta ƙi bacci ya ɗauke ta cike da tunanin shi ba, don a ɗaki ne kawai take da tabbacin babu wanda zai uzzura mata balle ya katse mata tunanin ta.

“Waheedah…”

Ta ji an kira ana taɓo ta, juyawa ta yi fuskarta babu walwala.

“Dallah ana ta miki magana, mu kwance kai yau, kin ga Alhamis babu islamiya, gobe in Allah ya kai mu sai mu je kitso gaba ɗayan mu.”

Da sanyin murya amsa Zahra da cewa,

“Ku je kitson ku, Nuriyya za ta yi min.”

Harararta Zahra ta yi.

“To mai Nuriyya da ta iya kitso, sai ki ta zuwa ai.”

Tana kallon Amatullah ta taɓe baki, juyawa ta yi ta gyara zamanta ta ƙyale su, ba ta san me Nuriyya ta tsare musu da ba sa sonta har haka ba, ko wani abin ake in ta ce da Nuriyya za ta yi takan ga ƙiyayya shimfiɗe a fuskarsu, musamman Amatullah da takan ce ta ma fi son Nuriyya akan ta, ba ta raba duk wani lokacin da ta samu tare da ita sai da Nuriyya, za ta iya cewa duka ‘yan uwan nata kan yi mata wannan mitar, kamar suna kishi da Nuriyya ɗin, dariya takan yi musu kawai, yau kam ko dariyar ba su samu ba, don tunanin Abdulƙadir ya addabeta fiye da kowane lokaci, da shi manne a ƙasan zuciyarta kuma suka ƙarasa gida.

*****

Bai shigo gidan ba sai gab da Magriba, ɓangaren su ya wuce ya tura ƙofar ɗakin da sallama ya shiga, ƙafafuwan shi da jikinshi cikin shigar kayan ball. Ɓangaren da gaba ɗaya mazan gidan suke daban yake, da ka shiga falo za ka samu da kujeru a ciki, sai ƙofofin ɗakuna a zagaye, ɗakin bacci huɗu ne a cikin wajen manya-manya, sai ƙaramin nashi da yake tunanin anyi shi na baƙi. Da shi da Mubarak suke kwana, kafin ya tattara ya bar mishi ɗakin, bai damu da kwana shi kaɗai ba, asalima hakan na mishi daɗi da ɗakin ya kasance nashi ne shi kaɗai, amma bai san dalilin da ya sa kowa yake gudun haɗa ɗaki da shi ba, abin na ɓata mishi rai wani lokacin, ko kujera mai zaman mutum biyu ya zauna da wahala ka ga wani ya zauna kusa da shi.

Kusan su huɗu ya gani a falon suna kallo, bai bi ta kansu ba, kitchen ya fara wucewa ya buɗe fridge ɗin da yake kitchen ɗin ya ɗauki ruwa, ba wani amfani suke da kitchen ɗin ba, banda kwanonin da in suka shiga cikin gidan sukan zo su jibge, sai ya gaji da ganin su yake sa wani ya kwashe ya mayar cikin gidan. Ɗakinshi ya wuce ya cire kayan jikin shi ya shiga banɗaki, ruwa ya watsa cikin hanzari don ya san ana gab da kiran sallah ya ɗauro alwala ya fito, ƙananun kaya ya saka, don Hajja har ta gane shi, in ya saka manyan kaya to sallar juma’a za shi, kayan duk da za a ɗinka musu manya da sallah, yana dawowa idi yake zare su daga jikin shi.

Fitowa ya yi ya ji ana kiran sallah, har ya kai ƙofa ya juyo ya ga su Yasir a zaune.

“Kuna ji ana kiran sallah, kuna ƙara gyara zama.”

Yassar ne ya ɗago daga cikin kujera yana kallon Abdulƙadir ɗin.

“Ka wuce abinka kai dai…”

“Badai kyau wallahi.”

Cewar Abdulƙadir din, don ya gane Yassar ne a yanayin shi, kusan duk gidan zai iya kwantanta zafin ranshi da na Yassar ne, ba ya tunanin ko Mama tana iya banbance su in ba da hakan ba, kamannin su ya ɓaci, gashi ya rasa jarabar da ta sa komai iri ɗaya suke yi, har askin kansu, in suna tare ka kira ɗaya su dukan su suke juyowa. Da zafin ransu ne kawai ake ganewa.

“Karka bari in taso Abdulƙadir.”

Yassar ya faɗa, amma ko motsi Abdulƙadir bai yi ba.

“Hamma Yasir kaima biye mishi za ka yi? Don kun fito a ‘yan biyu ba zai sa a rufeku a kabari ɗaya ba fa, wallahi jibgar banza za ka sha…”

Miƙewa Yassar ɗin ya yi ya fara takawa zuwa inda Abdulƙadir ɗin yake dariya a tsaye, sai dai kafin ya ƙarasa har ya buɗe ƙofar ya fice da gudu.

“Ɗan banzan yaro marar kunya, da ka tsaya ai.”

Yassar ya faɗa, ya sa Yasir yin dariya.

“Banda kai a gidan nan, banga wanda Abdulƙadir yake wasa da shi haka ba.”

Mubarak ne ya jinjina kai yana miƙewa.

“Halin su ne ya zo ɗaya shi ya sa, yaron can ko tsokanar shi na gwada yi zai ce min ba ya so, zansa yara su ji su raina shi.”

Dariya kawai Yassar yayi ya wuce ya bar su anan, banda Yasir da suka fito rana ɗaya, ba ya jin akwai wanda yake ji har ƙasan ranshi a gidan kamar Abdulƙadir, duk da kusancin su ba ya hana ya yi mishi rashin kunya sosai, amma kuma shi kaɗai yake ɗaga wa Abdulƙadir hannu ya sauke ba tare da Abdulƙadir ɗin ya gwada ramawa ba, sai dai ya sake faɗar maganganu ya wuce, ko rikici ake yi da shi, Yassar ɗin ake kira don shi kaɗai yake iya raba rikicin Abdulƙadir. Alwala duk suka yi suka fita masallaci tare.

*****

Abdulƙadir bai shigo gidan ba sai bayan sallar isha’i, bai samu kowa a falon ba sai Yassar da yake cin abinci, ƙamshin wake da shinkafar da ya hango ya ji busashen kifi yake ya sa shi sanin girkin Mami ne, don duk ranar bai ci abinci a gidan ba, da safe ya riga su fita makaranta don shi yake da duty, acan ya siyi abinda ya saka wa cikin shi, da ya dawo kuma sunje gidansu Imran, acan suka ci abincin rana. Cikin shi ya ji ya murɗa da yunwa, ya ƙarasa ya zauna kusa da Yassar ɗin, hannu yakai zai ɗauki cokalin Yassar ya doke hannun shi.

“Tashi ka zubo naka.”

Daƙuna mishi fuska Abdulƙadir ya yi.

“Hamma mana…”

Abincin Yassar ya ƙara ɗiba ya cika bakin shi yana faɗin,

“Zanci ubanka wallahi.”

Sake daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Sai ka dinga zagina, ko a gaban yara sai ka zageni, salon ka sa yara su raina ni. Ni kam bana so kana min irin haka.”

Hannu Yassar ya sa ya kai mishi duka saboda bakin shi da yake cike da abinci, miƙewa Abdulƙadir ya yi, duk gidan babu wanda yake mishi irin wannan cin mutunci sai Yassar, ya rasa kuma menene tattare da Yassar ɗin da yakan sa shi ɗaga mishi ƙafa tunda ba tsoron shi yake ba, ba ya tunanin idan faɗa ya haɗa su Yassar zai iya ɗibar wani abu a jikin shi, amma sai ya barshi yana ci mishi mutunci haka, ko Abba bai taɓa dukan shi ba, balle kuma Hajja, Yassar ne mutum na farko a duniyar shi daya fara ɗauke shi da mari bai iya ramawa ba, lokacin da faɗa ya kaure tsakanin shi da Babban Yaya, kan ya mare shi ya rama.

Amma da Yassar ɗin ya kafe shi da idanuwa tsintar kanshi ya yi da barin wajen, yana mishi kwarjini na ban mamaki. Yanzun ma kallon da yake mishi ya sa shi fita daga ɗakin. Kanshi tsaye ɓangaren Mami ya wuce ya shiga har tsakiyar falon tukunna ya yi sallama, Mami ɗin da ta fito daga kitchen ta amsa shi.

“Ina wuni.”

Ya furta a hankali, duk cikin matan Abba ya fi ganin girmanta, ita kaɗai ce ba ta taɓa shiga harkar shi ba, asalima banda gaisuwa babu abinda yake haɗa su, yanzun ma wucewa ta yi hidimar gabanta, shi kuma ya taka ya ƙarasa har kitchen ɗin, inda ya ga Waheedah a tsaye, juyowa ta yi tana kallon shi, kafin a ɗan daburce ta ce,

“Hamma…”

Ludayin da yake hannunta ya karɓa, jajayen kayane a jikinta da ya ƙara fito da farin ta ya saka shi daƙuna fuska.

‘In shaa Allah babu abinda zai haɗa ni hanya da farar mace.’

Ya faɗa a ƙasan ranshi, plate ya ɗauko ba tare da ya kulata ba, yana kallo ta matsa ta haɗe bayanta da kantar kitchen ɗin, abincin da yake tunanin zai iya cinyewa ya zuba.

“Ina miya?”

Ya tambaya yana ƙin kallonta don farinta na shigar mishi ido, da hannu ta nuna mishi ta sake matsawa don zuciyarta bugawa take sosai, da tunanin shi manne ta yini, har fita ta yi harabar gidan ko za ta ganshi ba tare da ta san dalilin hakan ba, ta gaji da leƙe-leƙenta ta dawo cikin gida, ko sallar isha’i sai yanzun ne ta yi alwalarta, a falo ta zauna tana jiran ko za ta ga ya shigo ɗibar abinci, sai yanzun da yake tana da rabon ta gan shi ɗin. Cokali ya sa hannu ya ɗauka haɗe da wani plate ɗin da ya ɗora kan abincin ya rufe ya fice ba tare da ya sake kallon inda take ba. Ɓangaren su ya koma, abincin ya fara ajiyewa tukunna ya je ya ɗauko ruwa ya dawo ya zauna. Daga shi sai Yasir da Yassar, Ahmad da suke kira da Babangida, sai Mubarak a falon.

Film ɗin da lokacin ake rubuta sunaye alamun farawa ya tsayar da idanuwan shi akai.

‘Paheli.’

Ya karanta sunan film ɗin da tun daga kiɗan dama ya gane indiya ne. Abinci yake ci ya kuma nutsar da hankalin shi kan film ɗin, don sosai yake jin daɗin shi, kafin ya ji an harbar mishi baya da ƙafa, ya kuma san Yassar ne.

“Sojan gobe ne yake kallon soyayya haka?”

Yassar ya yi maganar yana dariya.

“Babu abinda zai hana insa a rufemun kai ko kwana biyune, saboda babu wanda ya rainani a gidan nan kamar ka.”

Dariya Yassar ya sake yi.

“Lallai ma yaron nan. Ka zama sojan tukunna.”

Juyawa Abdulƙadir ya yi yana ƙanƙance mishi idanuwa.

“Na kusan applying NDA ai, in shaa Allah. Kuma wa ya ƙi soyayya?”

Wannan karon Babangida ne yace:

“Tambaye su dai, kamar su ma ba kallon suke ba.”

Murmushin gefen fuska Abdulƙadir ya yi.

“Allah Hamma ba zan auri matar da bana so ba, ina da buri mai yawa kan matata.”

Dariya suka yi gaba ɗaya.

“Hmm, ta dai shiga uku da masifarka, ai kai mai zama da kai tana da aiki wallahi.”

Mubarak ya faɗa.

“Shi ya sa nace zan auri wadda nake so…”

Murmushi Yasir ya yi mai sauti.

“Yaron da ko tafasa bai yi ba yana maganar soyayya da mata. Allah ya shirya.”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“A’a Hamma…a’a wallahi, na ji kamar kana so ka ce min yaro.”

Ware idanuwa Yasir ɗin ya yi, bai gama mamakin Abdulƙadir ba ya ji ya ɗora da:

“Kai ma yanzun kake level 2, ba wai ka girmeni bane can da yawa.”

Yassar ne ya ƙara kai mishi duka da ƙafa, wannan karon ya kauce don ya gan shi.

“Me nayi? Ƙarya na faɗa? Ni dai Hamma Yasir karka fara gwada kirana yaro wallahi, ko mu kaɗai ne balle a gaban yara.”

Abdulƙadir ya ƙarasa faɗa yana kumbura fuska.

“Me zai faru in na ce maka yaron?”

Yasir ya tambaya.

“Nidai ai kashedi nayi.”

Ganin abin zai zama faɗa ya sa Yassar cewa,

“Ya isa haka… Abdulƙadir tashi daga falon nan.”

Kallon Yassar yake kamar ya mishi magana da wani yare daban da na Hausa.

“Yes ka tashi na ce, ka ji ni kuma.”

Wata dariya mai sauti Abdulƙadir ya yi.

“Ba zan tashi ba fa, don kallo nake, sai dai shi ya tashi.”

Ya ƙarasa maganar yana nuna Yasir da ɗan yatsa, murmushi kawai Yasir ya yi.

“Ka ƙyale shi kawai Yassar.”

“In bai ƙyale ni ba ya zai yi da ni dama?”

Dafe kai Yassar ya yi yana sauke numfashi, su Babangida da Mubarak dama basu sake saka musu baki ba, asalima kallon su suka ci gaba da yi, don babu wanda ya shirya rashin kunyar Abdulƙadir ɗin, ganin kowa ya yi shiru ya sa Abdulƙadir mayar da hankalin shi kan film ɗin, duk da zuciyar shi da yake ji ta kawo wuya. A hankali yake jin soyayyar da ake gudanarwa a film ɗin na nutsar mishi da wani abu a ƙasan zuciyarshi, kamar yadda ya faɗa ne, yana da buri mai yawa akan matar shi, kuma auren soyayya zai yi, ba zai auri yarinyar da ba ya ji har ƙasan ranshi ba, don da kaɗan soyayyar da yake ma kakin sojoji za ta ɗara tata.

*****

Kamar yadda Waheedah ta ce Nuriyya za ta yi mata kitso, hakan ya faru ranar juma’a, tana dawowa daga makaranta, kaya kawai ta sake ta faɗa wa Mami za ta shiga gidan su Nuriyya, Amatullah ma anan ta bar ta za ta yi wanke-wanke ta shirya itama su fita kitson da su Zahra. A ɗakin su Nuriyyan suka zauna don yin kitson.

“Karki min manya fa.”

Waheedah ta faɗa, ta sa Nuriyya kwashewa da wata irin dariya.

“Dame za a yi ƙananun kitson to?”

Duka Waheedah ta kai mata.

“Bana son iskanci, ai kinga dai gashina ya fara dawowa Allah.”

Dariya Nuriyya ta sake kwashewa da ita, tana kallom gaban kan Waheedah ɗin da duk ya gwagwiye, da ma bawai tana da gashin kirkin bane, ta je wata ‘yar ajinsu ta faɗa mata ta yi retouching da Petals yana saka baƙin gashi, don farin Waheedah ya sa gashinta ja ne, Petals ɗin bai saka mata baƙin gashi ba saima gaban da ya ƙara kwashewa kamar an aske.

“To za ki sake gwada Petals ɗin ne?”

Nuriyya ta tambaya har lokacin tana dariya, ita kanta Waheedah murmushi take yi.

“Allah zai kama mun ke, ɗan gashin nan da kike min wulaƙanci sai kin tashi da safe ya ƙwaƙushe.”

Duka Nuriyya ta kai mata, duk da ba za a sakata a layin masu dogon gashi ba, Allah ya ba ta yalwarshi babu laifi, tana kuma bala’in ji da gashin har ranta.

“Aniyarki ta biki.”

Wannan karon Waheedah ce ta yi dariya, hira suke sosai ana kitson, a haka har aka gama.

“Ki tambaya Mami mu je rijiyar lemo gobe in Allah ya kai mu.”

Nuriyya ta faɗa, gidan Antynta take son zuwa, kuma Naira Hamsin gareta, ba ta jin za ta isheta, in suka tafi da Waheedah ɗin ta san za ta biya kuɗin motar. In ta tambayeta ma ba za ta hana ta ba, tambayar ce ba za ta iya ba, wani abu na mata zafi a ƙasan zuciyarta da tunanin hakan. Kai Waheedah ta girgiza mata.

“Da wahala Mami ta barni wallahi.”

Don duk yadda Mami ta yarda da ƙawancen su da Nuriyya, ta san ba ta son yawon da babu dalili, duk da in ana biki ko suna a ɓangaren su Nuriyyan takan barta ta je wasu lokutan, amma yanzun ta san babu wani dalili, faɗa ma za ta yi mata. Hannu ta saka cikin aljihun wandon Pakistan ɗin da take sanye da shi ta zaro Naira ɗari, kuɗin makarantar da aka ba ta ne ranar, babu abinda ta siya da shi.

“Ki dai siya ma su Nana ko gwaiba ce.”

Karɓa Nuriyya ta yi cikin ranta tana faɗin,

‘Ashe su Nana.’

A fili kuma ba ta ce komai ba, don bakinta yakan yi nauyi da ta yi wa Waheedah godiya a irin yanayin nan, ita ma Waheedah ba ta taɓa damuwa ba, don a ganinta sun zama ‘yan uwa ita da Nuriyya, babu wannan a tsakanin su, miƙewa Waheedah ta yi tana kakkaɓe jikinta tare da durƙusawa ta ɗauki hijabinta.

“Ki gaishe da Antyn don Allah. Bari in je na san su Amatullah ba su dawo ba, in kamawa Mami girki.”

Kai Nuriyya ta jinjina, tana jin son cin ko meye za su girka ɗin, don ta tabbatar zai ji nama. Mami ba ta ƙwauron nama a abincinta.

“Inkin dawo ki biyo, dambun shinkafa Mami za ta yi mana, in kuma baki biyo ba na ba Aminu ya kawo miki.”

Dacin da takan ji wasu lokuttan Nuriyya ta ji ya mata sallama a cikin maƙoshinta, za ta yi komai don su yi musayar matsayi da Waheedah, da duk rana take sa tana ƙara jin yanayin.

“Wai aita magana ki yi shiru ki ƙyale mutane.”

Numfashi Nuriyya ta sauke.

“Ba kunne yake ji ba? Ai ina jinki ko?”

Kai kawai Waheedah ta jinjina tana saka Hijabinta.

“Allah dai ya shirya halinki.”

Ta juya ta fice daga gidan, wanka Nuriyya ta shiga, da yake ba nawa gareta ba, nan da nan ta shirya, ta ci uwar kwalliya, wata doguwar riga da Abban su Waheedah ɗin ya siyo musu lokacin da ya je Umrah ta saka ta naɗe kanta da mayafin rigar da ya bala’in karɓarta. Sallama ta yi da Mama ta fita daga gidan, a ƙofar gidan su Waheedah ta ci karo da Abdulƙadir don nan ne hanyar da za ta bi ta nufi titi, haka kawai zuciyarta ta yi wata irin bugawa, ba tun yanzun yake mata kyau ba, yakan yi mata kama da mazan da takan karanta a litattafan Hausa.

“Ina wuni Hamma?”

Ta furta a hankali, a karo na farko da Abdulƙadir zai ce ya tsaya ya ƙare mata kallo, bai san tana da kyau har haka ba, ga yanayin jambakinta ya zauna a fuskarta, raini ne ba ya so ko a wajen ‘yan gidansu, shi ya sa duk wasu tarkacen ƙawayen su Zahra ba ya damuwa da su, in sun gaishe shi ya amsa, in basu gaishe shi ba shikenan, sam bayason raini da rashin kunyar ƙananun yara.

“Lafiya…”

Ya amsa tukunna ta wuce, cikin gida ya koma, yana ƙudurtawa a ranshi kuɗin kayan kwalliya daban zai ware wa matar shi, don ko wajen aiki ya koma yana son tuno fuskarta da kwalliyarta da ya san za su rage mishi kewar ta da zai yi. Burin shi akan matar shi mai girma ne, shi kanshi ya sani, duk da burin shi na saka uniform ya girme shi nesa ba kusa ba, amman ya matsa mishi ya samu wajen zama daram a zuciyarshi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 4Abdulkadir 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×