Skip to content
Part 11 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Mami ce da ta fito daga ɗaki ta kalli Waheedah da ta ke kwance, tana murmushi ta ce,

“Ki tashi an kusan kiran sallah.”

Hannun kujerar Waheedah ta kama tana miƙewa da ƙyar, kanta take jin kamar baya liƙe da jikinta saboda rashin nauyin da ya yi mata. Tunda aka fara azumi babu wanda ya bata wahala kamar na ƙarshen nan, ita bata damu da duk wani aikin gida ba. Amma tana azumi ace ta fita sosai take wahala. Gashi a ɗakinsu kowa zai sha ruwa ranar tunda girkin Mami ne. Amatullah da za ta tayasu wani abin wuni ta yi gidan kitso, bata jima da shigowa gidan ba.

“Mami hanjina kamar an kwashe.”

Waheedah ta faɗi tana taɓa cikinta da yake a shafe. Dariya Mami ta yi.

“Idan wani ya ji sai ya ɗauka za ki ci wani abin kirki…”

Kai Waheedah ta jinjina tana faɗin,

“Haba ai yau yunwar da nake ji zan baku mamaki.”

Murmushi kawai Mami ta yi tana shiga kitchen ta ɗauko robar dabinon da ta ɗauraye ta fito da ita tana ɗorawa kan hannun kujera. Kitchen ɗin ta sake komawa tana ɗauko babban kwanon tangaran ɗin da yankakkun kayan marmari ne a cikinsu ta ajiye tsakiyar ɗakin. Ta miƙa hannu ta ɗauko robar dabinon daga kan hannun kujera, samarin gidan suka soma shigowa da sallama, dai-dai lokacin da aka kira sallah. Wasu dabinon kawai suka ɗauka suna ficewa daga ɗakin don tafiya masallaci, Mami ma ɗaki ta shige don gabatar da sallar Magrib. Da ƙyar Waheedah ta kai hannunta tana ɗaukar kankana tare da yin Bismillah tukunna ta saka a bakinta.

Zata rantse da Allah inuwar shi ta banbanta da ta kowa, shekara ɗaya da kwanaki.
“Assalamu alaikum…”

Muryarshi ta daki kunnuwanta, tana sa tari ƙwace mata saboda ruwan kankana da ya bi mata ta hanyar da bata shirya ba, zuciyarta da take wani irin dokawa bata taimaki yanayin da take ciki ba. Ya ce mata zai zo da sallah, tun satin take baza ido ta inda zai ɓullo amma shiru, kallo ɗaya Abdulƙadir ya yi mata yana ganin yadda take tari sosai, takawa ya yi zuwa kitchen ya ɗibo ruwa a kofi ya dawo ya miƙa mata. Karɓa Waheedah ta yi tana shan ruwan tare da sake yin tari, tukunna ta yi gyaran murya. Maƙoshinta kamar zai ciro take jin shi.

A hankali ta ɗago tana kallon Abdulƙadir ɗin da yake tsaye yana kallonta, ta ɗauka akwai shekarun da mutum yake kaiwa ya daina ƙara tsayi ko girma, amma banda Abdulƙadir ɗin. Za ta rantse ya fi lokacin da ya zo tsayi da girma. Kalar askin da yazo da shi ne wancan karan, jikinshi sanye da farar riga mai dogon hannu sai wando daya rufe gwiwar shi da kaɗan, baƙi ne yana da igiyoyi daga jikin ƙafafuwan. Wani irin kyau ya yi mata har zuciyarta na matsewa waje ɗaya. Hannu ta ga ya miƙo mata, dube-dube take tana neman abinda za ta ba shi.

“Kofin… Ki ban kofin Waheedah…”

Abdulƙadir ya faɗi a gajiye, babu abinda ya canza a tattare da ita, sai girma da ta ƙara mishi. Kofin ta miƙa mishi ya karɓa yana wucewa ya mayar kitchen, yana fitowa hanyar ƙofa ya nufa, sai lokacin Waheedah ta samu bakinta ya motsa saboda wani irin yanayi da take ji da ba zai misaltu ba.

“Baka ɗauki komai ba.”

Dawowa ya yi ya ɗauki kankana guda ɗaya yasa a bakinshi tukunna ya fice daga ɗakin. Cikin sanyin jiki Waheedah ta miƙe daga falon, har wani zazzaɓi-zazzaɓi take ji yana shirin kamata, yanayi ne da kusanci da Abdulƙadir ne kaɗai yake haifar mata da shi. Gama aji shida, cin nasara a duk matakin da ɗaliban da suke son samun gurbin karatu a jami’ar Bayero suke buƙata bai sa Abdulƙadir ya bar zuciyarta ko na minti ɗaya ba. Bata ji daɗi ba da Nuriyya bata samu gurbin karatu a Bayero ba itama, sai nan Poly Abba ya yi mata cuku-cuku ta samu Business administration, kuma ƙarfin karatun tun daga kan kuɗin makaranta da komai shi ya faɗa wa mahaifin Nuriyyan zai biya, hakan ba ƙaramin zumunci ya ƙara tsakanin gidajen nasu ba. Su dukansu sai bayan sallar za su fara registration.

Zuwa yanzun tasan cewar son Abdulƙadir ɗin take, wani irin so take mishi da rashin algus ɗin da yake ciki har mamaki yake bata. Son Abdulƙadir take irin soyayyar da ta ginu domin Allah, soyayyar da babu wani tsammani a cikinta, soyayyar da take jin ko ta samu kwatankwacinta ko akasin hakan duk ba matsala bane ba, zuciyarta abu ɗaya take gane mata, shi ne son Abdulƙadir. Nuriyya kaɗai ta furta ma da ta kalleta sau ɗaya tana ci gaba da abinda take a lokacin, bata sake mata maganar ba, ita ma kuma Nuriyyar bata tayar mata da zancen ba. Hakan yasa Waheedah ɗauka ko Nuriyya tana tunanin wasa take mata.

Da ƙyar ta iya wucewa ɗakinsu, inda ta samu Amatullah na sallah. Banɗaki ta wuce ita ma ta gabatar da alwala, da ƙyar ta yi gefe da tunanin Abdulƙadir ta gabatar da sallar Magriba. Ko da ta fita falo duk suna nan, an cika falon ko’ina tarkace ne ana hidimar shan ruwa. Kan kujera Waheedah ta zauna, Yazid ya tashi daga inda yake ya koma kusa da ita, hannun shi riƙe da kofin shayi.

“Na ɗauka ai ba za ki fito ba.”

Ya faɗi yana kallon Waheedah, da tunda Mami ta aike su cefane da yamma take faɗa mishi yadda azumin yake wuju-wuju da ita. Murmushinta ta yi mishi da yake jin yana nutsar da wani abu da bai san a tashe yake ba cikin ƙirjinshi. Duk idan ta yi mishi murmushi haka yakan ji kamar ya buɗe bakin shi ya furta mata yadda ya gama tsara gaba ɗaya rayuwarshi da ita, amma ya rasa abinda yake danne shi, gani yake kamar har yanzun da sauran yarinta a tattare da Waheedah ɗin, hakan kuma na da alaƙa da tazarar shekarun da yake tsakanin su.

Waheedah tasan ya kamata ta ci wani abu, amma idanuwanta kafe suke kan ƙofa tana jiran shigowar Abdulƙadir.

‘Don Allah Hamma ba ka shigo ina sallah ka sake ficewa ba. Don Allah karkai mun haka, ba mu gaisa ba, ban gaisheka ba.’

Take faɗi cikin zuciyarta. Yazid fuskarta yake kallo yana tunanin abinda yasa ta nutsuwa haka.

“Waheedah…”

Ya kira a hankali yana sata raba idanuwanta daga kan ƙofar tana sauke su akan shi.

“Ki ci wani abu… Tun ɗazun kike kiran yunwa.”

Ba tare da ta ce komai ba ta miƙe tana nufar kitchen. Akwai wake da shinkafar da Mami ta yi musu jiya, jallof ce ta sha busashen kifi da nama, sosai ta yi mata daɗi shi ya sa da ta rage ta kwashe ta saka a fridge. Ɗaukowa ta yi tana saka robar a microwave ta kunna don ta ɗumama. Tsaye ta yi a kitchen ɗin har sai da ta fara jin ƙamshin abincin alamar ya yi, ta fito da robar kenan ta ji muryar Abdulƙadir.

“Menene kike dafawa? Ina ci…”

Juyowa ta yi da murmushi a fuskarta, tana jin kusancin shi fiye da tazarar dake tsakanin su, tana jin shi har ƙasan zuciyarta.

“Hamma…”

Ƙananun idanuwan shi ya ƙanƙance mata.

“Yaushe ka zo? Ashe za ka zo.”

Numfashi Abdulƙadir ya sauke yana amsa ta da,

“Ban yi niyyar zuwa gida ba yanzun. Ba yanzun na so zuwa ba.”

Cike da rashin fahimta Waheedah take kallon shi, idanuwan shi da ya sauke cikin nata na saka wani abu tsirga mata har tsakiyar kanta.

“Hamma…”

Ta furta muryarta can ƙasan maƙoshi, kai Abdulƙadir ya ɗan ɗaga mata, da gaske yake har zuciyarshi, bai yi niyyar zuwa gida ba sam, saboda tunda ya tafi Nuriyya na manne a wani waje tare dashi, duk ƙoƙarin da ya yi na ganin ya cirota daga duk inda take maƙale da shi ya kasa. Baƙon abu ne a gurin shi, tun tasowar shi abinda duk yasa ranshi sai ya yi shi yake yi, ko da su Hajja za su karya shi ne kuwa. Shi yasa kasa cire Nuriyyan yake ɓata mishi rai. Suna shawowa kwanar gida shi da Yassar da ya je ya ɗauko shi komai na sake danne shi. Sai ma da ya fito daga mota yana sauke idanuwan shi ƙofar gidansu, da zuciyarshi a maƙoshi saboda dokawar da take ya shiga gida.

Har yanzu kuma ranshi a ɓace yake jin shi, saboda ba ya son fara tunanin abinda mannewar da Nuriyya ta yi mishi yake nufi, sam ba ya so, babu abinda hakan zai haifar mishi banda raini. Yana ganin yadda waje kaɗan Nuriyya take jira ta samu ta raina shi, ba sai an faɗa mishi ba, a yanayinta da fuskarta ya karanci akwai wannan halayyar a tare da ita. Shi kam a duniya raini ne babban abinda baya so, ko wanda suke da tazarar shekaru a tsakaninsu baya so su raina shi, shi yasa yake bala’in riƙe girman shi. Watan shi biyu da komawa Kaduna ya ji yadda kwata-kwata ba ya son komawa Kano.

Koda zai koma ɗin ba nan kusa ba, a ƙalla ya ƙara ɗaukar wasu shekara biyun tukunna, wataƙila hoton Nuriyya ya disashe mishi daga cikin kai. Amma duk idan ya kwanta ya rufe idanuwanshi baya ganin komai sai fuskar Waheedah da alƙawarin da ya yi mata na cewar zai zo hutun sallah.

‘Da gaske za ka zo? Don Allah ka zo Hamma, ka ji… Ka zo don Allah.’

Shi ne abinda yake mishi yawo duk lokacin da ya yi tunanin ƙin zuwa hutun sallar, ranshi a ɓace yake, bai san wa zai ɗora wa ba, shi yasa ya zaɓi ya raba ɓacin ran da ita, tunda ita ce dalilin saka shi ɗauko ƙafafuwan shi daga Kaduna zuwa Kano.

“Ke kika sa na zo…alƙawarin da na yi miki yasa ni zuwa. Jibi zan koma.”

Ya yi maganar, kallon da yake mata na saka ta jin wani raɗaɗi a ƙirjinta da ba za ta ce ga daga inda ya fito ba. Kallonta yake yana ɗora mata laifin zuwan da ya yi, duk da hakan bai hana zuciyarta jin daɗin zuwan nashi ba, ko ba komai ta ganshi. Amma ita bata ce ya yi mata alƙawarin zai zo ba, bata san me yasa yake kallonta ba.

“Ki bani abinci ni kam.”

Abdulƙadir ya ce yana ɗauke idanuwanshi daga kanta, baya son ganin yadda take kallon shi kamar tana son sanin dalilin da yasa yake ɗora laifin zuwan shi akanta. Bayan ita ce dalilin da yasa shi zuwan tun daga farko, da bata kalle shi da idanuwanta ɗin nan ba, da bata kalle shi da farar fuskarta ta sa shi alƙawarin da yake dana sani ba, babu abinda zai kawo shi Kano. Sai dai ɓacin ran da yake ciki ba shi da alaƙa da abinci. Bai taɓa fushi da abincin ba, cikin shi daban, abinda yake faruwa da shi daban. Plate Waheedah ta ɗauko ta ɗauraye, gaba ɗaya wake da shinkafar ta juye mishi, tana kallon shi ya ɗauko cokali kafin ta gama zubawa.

Miƙa mishi plate ɗin ta yi ya karɓa, yana shirin juyawa ta yi saurin faɗin,

“Hamma…”

Sai dai sauran kalaman sun maƙale mata, bata ma san me take shirin ce mishi ba, gashi ya kafeta da ƙananun idanuwan shi da suke rikita mata lissafi, kanta ta sauke ƙasa tana kallon ƙafafuwanta. Ya kai mintina biyu a tsaye, ganin bata da shirin magana yasa shi juyawa. Mami da ya gani a falon zaune ya kalla da faɗin,

“Sannu da shan ruwa.”

Da fara’a ta amsa shi tana ɗorawa da,

“Abdulƙadir. Saukar yaushe?”

Duk yadda ya so ya yi murmushi ya kasa, ranshi a ɓace yake har lokacin, a gajiye ya ce,

“Ɗazun…”

Kai Mami ta jinjina sanin halin Abdulƙadir, wucewa ya yi abinshi, har ya kusa ƙofa ya ji Yazid na tambayar,

“Yaushe kuka ƙaraso?”

Juyowa ya yi yana ƙanƙance ido ya ce,

“Me ka sa a kunnen ka?”

Kai Yazid ɗin ya girgiza mishi.

“Ban sa komai ba.”

Ya amsa cike da rashin fahimtar tambayar Abdulƙadir ɗin.

“Me yasa kake tambayata abinda na amsa yanzun to? Salon in yi magana ka ce na maka rashin kunya?”

Murmushi Mami ta yi tana mishi addu’ar shiriya a ranta kafin ta miƙe tabar wajen. Ba za a yi koma menene a gabanta ba. Hannuwa Yazid ya ɗaga cikin nuna alamun saduda.

“Allah ya ba ka haƙuri…”

Juyawa Abdulƙadir ɗin ya yi da shirin ficewa daga ɗakin, ya ga Nabila tsaye a bakin kofa, ta ga alamar ranshi a ɓace yake, shi yasa ta yi tsaye don kar ya sauke tambotsan akanta.

“Ubanki kike a bakin kofa?”

Ya tambaya yana watsa mata harara, juyawa ta yi da niyyar komawa inda ta fito, wani dogon tsaki Abdulƙadir ɗin ya ja ya fice daga ɗakin yana nufar ɓangarensu. Nuriyya na manne da shi ya rasa yadda zai yi ya cirota, haushin kowa yake ji, komai ya ci karo da shi ƙara ɓata mishi rai yake. Ƙofar ɗakinsu ya gani a ɗan buɗe, dubawa ya yi ya ga takalmi ne ya tokareta. Tsugunnawa ya yi, plate ɗinshi a hannu ɗaya, yasa ɗayan hannun ya ɗauko takalmin yana juyawa ya yi cilli da shi, ƙiris ya make Yasir da yake tahowa.

“An zo an ajiye wani banzan takalmi salon sauro ya cika mana ɗaki.”

Yake faɗi shi kaɗai yana sauke numfashi. Ƙarasowa Yasir ya yi yana kallon ikon Allah.

“Kai kuma kai da wa? Kake ta huci kamar kububuwa.”

Ba tare da Abdulƙadir ya juyo ba ya ce

“Ban sani ba…”

Ya wuce yana shigewa cikin ɗakin. Yasir bai san me yasa yanayin Abdulƙadir ɗin ya bashi dariya ba, dariya yake sosai a bakin ƙofar da ya kasa ƙarasa shiga ma. Har cikin ranshi Abdulƙadir yake jin dariyar Yasir ɗin, kofar ɗakinshi ya tura yana shiga tare da rufeta da ƙarfin gaske. Idan har ya koma ya yi wa Yasir magana faɗa za su yi, yadda yake jin ranshi a ɓace, kan wanda zai huce yake nema. Abincin ya cinye tas ya sha ruwa, ganin idan ya zauna tunanin da baya buƙata zai danne shi, fitowa ya yi ya tafi masallaci abinshi.

*****

Ƙirjinta take ji kamar an ɗora dutse, tana yin isha’i ta wuce ɗaki ta kwanta abinta, ɗaya daga cikin hoton Abdulƙadir ɗin da yake cikin ƙaramin pillow ɗinta ta saka hannu ta zaro tana dubawa, shigowar Amatullah ɗakin yasatay saurin mayar da hoton inda ta ɗauko shi. Waje Amatullah ta samu gefen gadon ta zauna tana ajiye robar dake hannunta a ƙasa tana faɗin,

“Hajiya Adda ai sai kin sauko ƙasa ko?”

Cikin rashin fahimta Waheedah ta ce,

“In sauko ƙasa in miki me?”

Ware idanuwa Amatullah ta yi.

“Lallai Adda Wahee… Ƙunshin fa?”

Numfashi Waheedah ta sauke, sam ta manta da wani maganar ƙunshi, kitso dama Nuriyya ta yi mata, guda goma tace ma. Nuriyya bata saurareta ba ta yi mata ƙanana duk da kan ba wani gashin kirki yake da shi ba. Ba za ta iya bin layin wani baƙin ƙunshi ba, amma Amatullah ta iya jan lalle kala-kala, duka ‘yan gidan ita ta yi musu.

“Ni na manta da wani ƙunshi. Da kin barni Amatu, jikina ciwo yake min.”

Tunda ta fara magana Amatullah ke girgiza mata kai.

“Wallahi baki isa ba Adda, tunda ba takaba kike ba. Lallena da na kwaɓa fa? Waye zai yi amfani da shi. Ba ma zai yiwu bane ba, har Mami ta yi jan lalle….ni wallahi da ina da farinki da an ga lalle.”

‘Yar dariya Waheedah ta yi, Amatullah ɗin ba baƙa bace, amma kuma ba za ka kirata fara ba, tana da hasken fata irin na yawancin yaran gidan Bugaje ɗin.

“Ki fa sauko…”

A kasalance Waheedah ɗin ta sauko daga kan gadon. Ta san halin Amatullah idan ba a yi ƙunshin ba fushi za ta ɗauka da ita. Tsegumi kam sai kanta ya fara juyawa, gara ta yi ta huta. Hira suke taɓawa ita da Amatullah ɗin har ta gama saka mata lallen a duka ƙafafuwa da hannuwanta, ita ta taimaka mata ta hau kan gado ta kwanta, gaba ɗaya duniyar take ji ta tattaru a hannuwanta da ƙafafuwanta da suke a ɗaure da ledoji. Ita kam bata ga komai a cikin ƙunshi banda wahala ba. Bata jin za ta iya bacci da wannan ledojin a jikinta, da wannan tunanin bacci ya ɗauketa cike da mafarkin Abdulƙadir.

****

Washegari, kasancewar safiyar sallah, yanayin garin kanshi ya yi sanyin da safiyar sallah ce kaɗai kan haifar. Tunda suka tashi suke hidimar su, Waheedah bata ga ƙunshinta ba sosai sai da gari ya fara wayewa tunda babu wutar lantarki. Kyau ya yi mata sosai, gashi ya kama har wani ruwan ƙasa-ƙasa mai cizawa yake. Da gudu ta taho tana rungume Amatullah da take tsaye ta baya.

“Kin san ina son ki ba?”

Ta faɗi, Amatullah ɗin na tureta.

“Soyayya da soka min ƙasusuwa?”

Dariya Waheedah ta yi ta sake komawa ta riƙe Amatullah ɗin da ke kiciniyar ƙwacewa gam.

“Adda Wahee mana.”

Amatullah ta fadi tana samu ta ture Waheedah ɗin, da murmushi a fuskarta, Mami ce ta fito ta gansu.

“Mami kalli ƙunshina.”

Cewar Waheedah tana ɗaga wa Mami hannuwanta, jinjina kai Mami ta yi.

“Ma shaa Allah. Ya yi kyau sosai kuwa, yanzun kika zama ‘yan mata.”

Shagwaɓe fuska Waheedah ta yi.

“Me kike nufi Mami?”

Amatullah ta karɓe zancen da amsa ta.

“Kin fi kowa sanin me take nufi.”

Numfashi Mami ta sauke.

“Ni kam ku matsamun ina da aikin yi.”

Matsawar suka yi ta wuce, suna rufa mata baya zuwa kitchen ɗin. Wanke-wanke suka yi ita da Amatullah ɗin. Sun gama kenan, Amatullah ta fice daga kitchen ɗin, Nuriyya ta yi sallamar da Mami ta amsa mata tana ɗorawa da,

“Nuriyya idonki kenan?”

Dariya Nuriyya ta yi, don kwana biyu bata shigo gidan ba, ita ma sunata hidimar sallah.

“Wallahi Mami ina ta kitso ne fa. Ina kwana.”

Murmushi Mami ta yi.

“Lafiya kalau, ya kowa da kowa?”

Da murmushi a fuskar Nuriyya take amsa Mami da ta fice daga kitchen ɗin bayan sun gama gaisawa. Hijabinta Nuriyya ta cire tana ɗorawa kan window ɗin kitchen ɗin, yanayin da yasa Waheedah kallonta.

“Na ga kin cire hijab.”

Kai Nuriyya ta jinjina.

“Ba zan cire in sha iska ba?”

‘Yar dariya Waheedah ta yi, idan wani ya ga Nuriyya ta cire hijabin zai yi zaton aiki za ta taya ta, ita da yake ta san hali bata saka a rai ba, don Allah ya zuba wa Nuriyya ƙyuya, ko aikin gida aka sakata sai ta zuba ha’inci a ciki, wani lokaci Mamansu na kallonta za ta tsallaketa tayie aikinta, a cewarta ko wanke-wanken Nuriyya ba fita suke ba, haka za ka ga maiƙo cikin kofuna.

“Ke jiya Anas ya zo da daddare, sai ma bayan isha’i tukunna.”

Nuriyya ta faɗi wani tattausan murmushi na bayyana a fuskarta da yake nuna alamun Anas ɗin ba ƙaramar hidimta mata ya yi ba. Sun haɗu ne lokacin da suka kai mishi ɗinkin uniform ɗin Nuriyya na Green Olive, Yazid ne ya haɗa su da shi a cewar shi yakan mishi ɗinki wasu lokutan, basu da nisa da shi sosai tunda suna Ƙofar Ruwa ne, shi kuma yana Kurna babban layi ta wajen ‘yan doya. Kusan tun lokacin ya manne wa Nuriyya, da yake ana barinta fita zance, sukam gidansu sai ka gama sakandire tukunna. Anas ya gama Diploma ɗinshi a yadda Nuriyya take faɗa wa Waheedah, sai dai bai ci gaba ba, shi ne babba a gidansu, kuma Allah ya yi wa mahaifinshi rasuwa, hakan ya sa ya yi tsaye kan sana’arshi ta ɗinki da take kawo mishi rufin asiri dai-dai gwargwado.

Don a cikin sana’ar yake wa kanshi da mahafiyarshi har ma da ‘yan uwanshi duk wata hidima, duk a yadda Nuriyya take sanar da ita, yana da gidanshi na gado mai ɗaki falle-falle guda biyu, sai banɗaki da kitchen, don in yanzun Nuriyya ta bashi dama a shirye yake da ya turo a tsayar da magana. Abinda bai sani ba shi ne ko kaɗan Nuriyya bata jinshi a ranta, duk da Anas ba shi da wata makusa a matsayinshi na matashi, yana da kyau na misali da cikar zarrah, ga nutsuwa da kamala shimfiɗe a fuskar shi. Ko kaɗan Anas ba tsarin aurenta bane ba, ba shi bane mijin da take buri.

Tana kulashi ne saboda hidimar da yake mata, hannun shi a buɗe yake, ko yaushe cikin mata hidima yake, sau biyu yakan zo a sati, duk zuwan da zai yi da kalar kayan ciye-ciyen da zai kawo mata. Da sallar nan kaya ya yi mata kala uku, mayafi har da jaka da takalmi, shi ya yi mata ɗinkunan, ya kuma kawo dubu biyu ya bata ta yi kitso da ƙunshi. Sosai Waheedah take son Nuriyya da Anas ɗin saboda yadda yake da nutsuwa da kuma son Nuriyyan da take gani a tattare da yanayin shi.

“Turarenki yana gida…”

Nuriyya ta sake faɗi tana ‘yar dariya. Tana ƙara jin daɗin yadda haɗuwa da Anas take bata damar yi wa Waheedah kyauta irin haka.

“Don Allah fa… Turare ya kawo miki?”

Waheedah ta tambaya cike da jin daɗi itama, kai Nuriyya ta ɗaga mata.

“Har guda uku ma.”

Ɗan buɗe baki Waheedah ta yi.

“Aikam baki isa ba sai na zaɓa… Mai ƙamshin cikin nake so.”

‘Yar dariya Nuriyya ta yi.

“Banza in mun je gidan duk wanda kike so sai ki ta ɗauka. Ina da wasu ai.”

Ƙarasa share kitchen ɗin Waheedah ta yi suna hirar Anas ɗin da Nuriyya.

“A fara Poly Anas ya turo mu sha biki.”

Haɗe fuska Nuriyya ta yi waje ɗaya.

“A’a kin manta, uwar biki za ku sha.”

Dariya Waheedah take yi.

“Ki daina min wannan wasan, na ce miki ina son shi ne?”

Kai Waheedah take girgiza mata.

“A’a amman kina karɓe mishi kaya ai, wallahi Nuriyya kar Allah ya kama ki.”

Tsaki Nuriyya ta ja tana ɗaukar hijabinta daga kan ƙofa tana sa Waheedah tambayarta,

“Ina za ki je?”

Ko kulata Nuriyya bata yi ba, ta saka hijabinta, don ta gama ɓata mata rai, wato fatan ta auri Anas take mata, don kar ta huta. Ko a hanya aka ganta an san bata yi kalar auren tela ba, Diplomar da yake da ita ya faɗa mata ba shi da niyyar ci gaba, tunda yana da tsayayyar sana’a, ita kam sai wanda yake zuwa office, babu abinda za ta yi da tela.

“Hamma yazo…”

Waheedah ta faɗi cikin sanyin muryar da yasa zuciyar Nuriyya wani irin dokawa, da sauri ta juyo.

“Haba dai…”

Kai Waheedah ta girgiza mata.

“A’a ki tafi, ba tafiya za ki yi ba?”

Ɗan murmushi Nuriyya ta ɗora kan fuskarta.

“Dallah ai kece kike son ɓata min rai. Ban labari yaushe Hamma ɗin ya zo?”

Wannan karon wani tsadadden murmushi ne ya bayyana kan fuskar Waheedah.

“Allah Nuriyya ina son shi fa…”

Wani zafi Nuriyya ta ji ƙirjinta ya ɗauka, ta faɗa mata kwanaki, bata kulata bane, saboda ta yi kamar sai lokacin ta san tana son Abdulƙadir, bata san me yasa take maimaita mata ba yanzun.

‘In sha Allah ba za ki taɓa samun shi ba.’

Nuriyya ta faɗi a cikin ranta, a fili kuma taɓe baki ta yi ta ce,

“Kina da hankali kuwa?”

Narai-narai Waheedah ta yi da idanuwa, ita kanta ta san bata da hankali, ta kuma san ta rungumowa kanta dala ba gammo.

“Ban san ya zan yi ba Nuriyya. Na san banda hankali, shi yasa ma ban taɓa tunanin samun shi ba, kawai dai na san ina son shi.”

Ta ƙarasa maganar muryarta cike da rauni.

“Ya fi miki alkhairi…”

Nuriyya ta faɗi a taƙaice tana ɗorawa da,

“Bari in je gida… Zan dawo anjima.”

Don bata san Abdulƙadir ya dawoba da ba za ta shigo gidan haka ba, sauri za ta yi ta je gida ta yi wanka ta tsara kwalliya tukunna ta dawo, bata san me yasa ba, haka kawai ta ji bata so ya ganta ba tare da ta yi kwalliya ba. Kai kawai Waheedah ta iya ɗaga mata don bata jin za ta iya wata magana, tunanin Abdulƙadir ya cika zuciyarta fal.

*****

Yassar na kula da yanayin Abdulƙadir ɗin tun jiya da ya je ɗauko shi, da yake sun yi waya a bakin gate ya same shi tsaye da jakar shi, ba tare da ya ce wa Yassar ɗin komai ba ya zagaya ya shiga mota. Hannu ya saka ya kunna radio ɗin motar cikin nuna ma Yassar ɗin alamar baya son yin magana. Haka daren jiya duk wanda ya zo don su gaisa da masifa Abdulƙadir ɗin yake amsa su, kamar sannu da zuwan nasu na ƙara mishi ɓacin ran da Yassar ya kula ya zo da shi. To yau ma da alama da yanayin ya tashi, shi yasa tun Asuba bai koma ɗakin nashi ba, duk da zai yi ƙarya idan ya ce abin bai dame shi ba.

Maɓallan kayansu da tela bai saka musu ba Yassar ɗin yake sassaka musu a jikin riguna, daga shi sai Aminu a falon, don duk yawanci sun faffara shiga wanka.

Abdulƙadir ne ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando.

“Ina kwana Hamma…”

Aminu ya gaishe da shi sanin halin shi, shiru Abdulƙadir ɗin ya yi, hakan yasa Aminu sake gaishe da shi don a zaton shi ko bai ji bane, daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Karka dame ni Aminu, me yasa za ka fara gaishe ni tunda sassafe.”

Numfashi Aminu ya sauke yana jinjina kanshi kawai, da idanuwa Yassar ya yi mishi alama da ya bar falon, bai musu ba ya miƙe ya nufi ɗakinsu, sai da ya shiga ya turo ƙofar tukunna Yassar da bai ɗago daga maɓallin da yake sakawa ba ya ce,

“Me yake damunka?”

Zagayawa Abdulƙadir ya yi ya zauna inda Aminu ya tashi, baya son yin magana, baya so ai mishi magana, komai baya mishi daɗi.

“Da kai nake, me yake damunka?”

Yassar ya sake tambaya wannan karon yana sauke idanuwanshi kan fuskar Abdulƙadir da babu alamar walwala a tare da ita.

“Karka dame ni Hamma, don Allah. Gida ne ban yi niyyar zuwa ba.”

Rigar da ke hannunshi Yassar ya ajiye yana mayar da hankalin shi kan Abdulƙadir ɗin.

“Uban wa yace ka ɗaga waya ka kira ni in zo in ɗaukeka to? Idan ka san ba ka yi niyyar zuwa ba sai kai zamanka…me yasa za ka zo kana wa mutane baƙin rai, ubanka akai maka?”

Yassar yake faɗi don shi ma ranshi ya fara ɓaci, hakan Abdulƙadir ya kula da shi yasa shi fara shirin miƙewa don ya bar wajen.

“Wallahi idan ka tashi ranka sai ya ɓaci, ka zauna ban gama maganar da nake ba…”

Komawa Abdulƙadir ya yi ya zauna, ƙarshen abinda zai so a yanayin da yake ciki shi ne ɓacin ran Yassar ɗin, yana da zuciya ya sani, abinda yake ɓata mishi rai a kusa yake, amma yana sauka da wuri, wasu lokutan idan ya yi duka ko ya yi faɗa shikenan. Amma na Yassar daban ne, yakan jima ranshi bai ɓaci ba, amma idan ya ɓaci duka gidan sai hankalin kowa ya tashi.

“Me ke damunka? Ba zan sake maimaitawa ba.”

Numfashi Abdulƙadir ya sauke yana rasa amsar da zai ba Yassar ɗin, ba shi da wata ƙwaƙƙwarar amsa, me zai ce mishi? Ranshi a ɓace yake saboda zuciyarshi na son ja mishi abinda su dukansu ba zai musu daɗi ba? Ko kuma faɗa mishi zai yi yadda yake ta ƙoƙarin ciro Nuriyya daga duk inda take a cikin jikinshi kafin ta zame mishi matsala amma ya kasa? Wanne daga ciki zai faɗa mishi da ba zai mishi kallon marar hankali ba, ko zai faɗa mishi yadda Waheedah ta saka shi zuwa gida bai yi niyya ba, yadda alƙawarin da ya yi mata ya mishi tsaye a wuya sai da ya janyoshi garin Kano. Amsar da ta fi mishi sauƙi ya ba wa Yassar ɗin.

“Bansani ba, komai ba ya min daɗi.”

Numfashi Yassar ya sauke, yanayin da Abdulƙadir ɗin ya yi maganar na saka ɓacin ran da yake ji soma dishewa.

“Ka yi ta Istigfari, yana yaye damuwa.”

Kai Abdulƙadir ya jinjina mishi yana miƙewa tsaye.

“Bari in yi wanka… Kayana fa? An ɗinka min?”

Ɗan kallon shi Yassar ya yi.

“Da bikin su Hamma ai masifa kai min, na maka ɗinkin da bai maka ba….”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Da wane kayan zan je sallar idi?”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗu Yassar ya yi.

“Baka zo da kaya ba?”

Idanuwa ya ƙanƙance wa Yassar.

“Gajerun wanduna ne fa…”

Maɓallan shi Yassar ya ci gaba da sakawa, ganin Abdulƙadir ɗin na tsaye har lokacin yasa shi faɗin,

“Ka min tsaye a kai.”

Da mamaki Abdulƙadir ya ce.

“Hamma da gaske ba ka ɗinka mun ba?”

Wani kallo Yassar ya watsa mishi da ya tabbatar mishi da gaske ya yi maganar. Kuma da gangan ya ƙi ɗinka wa Abdulƙadir ɗin kaya, saboda rashin kunyar da ya yi mishi wancan karon, har cewa ya yi shi ba zai saka wasu manyan kaya ba. Ya faɗa wa kanshi ba zai sake ɗaga wa Abdulƙadir ɗin hannu ba, tunda ba yaro bane yanzun, amma hakan ba ya nufin ba zai nuna mishi kuskuren shi ba. Yana jin Abdulƙadir ɗin ya wuce, don ko ɗagowa bai yi ba, ya saka ɗaya daga cikin nashi kayan, idan za su yi mishi kenan, don ya ga ya ƙara buɗewa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 10Abdulkadir 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×