Skip to content
Part 17 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Tun da aka fara kamun hankalinta na kan wayarta da Amatullah ta baro mata a gida. Mutuwa ta yi, hakan ya sa ta bata don ta sa mata a caji. Ba tunanin gidan da yake shaƙare da mutane ko za a sace mata waya ta ke yi ba. Amatullah ta tabbatar mata da ta rufe ɗakin da mukulli ta kuma taho da shi. A’a, duk inda ƙarfe bakwai ta yi ta san Abdulƙadir zai kirata, a watanni shidan nan da suka wuce mata kamar ƙiftawar idanuwa, ƙarfe bakwai ya zama lokacin wayarsu. Duk da tun jiya take baza idanuwa ta ga ta inda zai ɓullo, amma shiru, kuma ko da ya kirata jiya sai ta tsinci kanta da jin nauyin tambayarshi yaushe zai zo ɗin.

Gashi kamun babu maza, mata ne kawai, bata yi tunanin zai kai su har lokacin ba, satin bikin ma jinshi ta ke yi kamar a mafarki. Ita ce za a yi bikinta wai. Tunda satin bikin ya kama ta ke baza ido ta ga ta inda Nuriyya za ta ɓullo, amma sai text ta yi mata cewar an kwantar da ita asibiti saboda haka ba za ta samu damar zuwa ba. Ta kikkirata ya fi a ƙirga tana mata ya jiki, sosai ta so zuwa har asibitin don ta dubata amma bata samu dama ba. Ta ɗauka ta ji jiki lokacin bikin Nuriyya ɗin, sai yanzun ne ta san yadda ake jin jiki da nata bikin ya zo, abinci ma duk yinin ranar bata samu ta saka shi a cikinta ba. Har wani haske ta ke gani yana gilmawa ta cikin idanuwanta duk idan ta miƙe saboda yunwar da ta ke ji.

Jiya da suka yi waya da Abdulƙadir ya yi mata faɗan shi kamar zai ari baki da ta ce mishi bata ci komai ba, kanta na mata ciwo. Yanzun ma tana jin alamar ciwon kai na barazanar yi mata sallama, cikinta da ta ji ya yi ƙarar yunwa ta dafe tana gyara zamanta kan kujerar da ta ke zaune.

“Ni fa na gaji wallahi, ba ki ji yunwar da nake ji ba.”

Cewar Zahra da take zaune kusa da ita, ta yi matuƙar kyau cikin alkyabbar da ta ɗora kan kayan jikinta da iri ɗaya ce da ta Waheedah ɗin.

“Nifa duk yau babu abinda ya je cikina banda ruwan shayi da safe.”

Juyowa Zahra ta yi tana kallon Waheedah da tambayar,

“Kina aikin me?”

Langaɓar da kai ta yi, Zahra ɗin na ganin ta yi mata wani irin kyau da kwalliyar da aka yi mata marar hayaniya. Jambakin ya zauna kan laɓɓanta kamar da su aka halicce shi.

“Babu wanda ya ba ni abinci fa… Anty Hafsah ce ta tambaya ko na ci, to ta ce bari ta kawo min kuma ta shiga wata hidimar ina jin ta manta…”

Taɓe baki Zahra ta yi.

“Zubawa na yi na shige ɗaki na zauna na ci abuna…ulcer ba za ta kamani ranar bikina ba.”

Dariya Waheedah ta yi sosai tana sa Zahra ɗin yin dariya ita ma. Haka suka ci gaba da hira da take tsayawa iya kunnuwansu.

***

Tsaye yake a bakin wajen, jikin shi sanye da shadda ruwan toka mai cizawa sai hula da ta yi matuƙar dacewa da shaddar jikin nashi. Ya ƙanƙance ma Anty Ramatu ƙanwar Hajja idanuwan shi da suke cike da rikici.

“Ban san sau nawa zan gaya maka babu maza ba Abdulƙadir, duk da yawancin mutanen da suke wajen ‘yan uwane…me ma ka zo yi wajen kamu?”

Ta sake mishi tambayar, don ita ma wata maƙwafciyarsu da ta zo mata e za ta tafi, ta rakota bakin ƙofar wajen ta samu Abdulƙadir ɗin ya cakumo rigar ɗaya daga cikin masu gadin wajen yana shirin haɗa shi da bango saboda ya ce mishi maza ba sa shiga.

“Me zan yi a wajen kamu. Waheedah za ki kira min ko ki matsa in shiga in kirata da kaina.”

Kai Anty Ramatu ta girgiza mishi.

“Muma yanzun za mu taho… Addu’a kawai za a yi… Ka wuce gida gamu nan.”

Kallon da Abdulƙadir yake mata ya fara tabbatar mata da cewar babu inda zashiy kafin ya buɗe baki yana tabbatar mata ta hanyar faɗin,

“Ki kira min Waheedah…”

Yana jin haƙurin shi na gab da ƙarewa, ba ya son faɗin wata magana da za ta ce ya mata rashin kunya. Tun ƙarfe wajen biyar ya iso garin Kano, kiran wayarta ya yi ya ji ta a kashe. Duk da yana hanya ma bai hanashi buɗe WhatsApp ɗinshi ko zai ga saƙonta ba, amma shiru, yinin ranar ko ɗan text bai samu ba. Ƙiris ya kira Yassar ya roƙe shi ya ce ya duba mishi ko tana lafiya, ko ciwon kan ne ya hana ta buɗe wayar. Da damuwarta ya sauka garin Kano. Ake faɗa mishi suna wajen kamu. Ya jira har lokacin da ya saba kiranta don yana da tabbacin ko da bai kirata ba ita za ta kirashi, amma wayarta a kashe.

Ba ya son ya zauna yana wani tunani, don ba abokin yinshi bane, ya sa ɗaya daga cikin sababbin kayanshi da Yassar ya nuna mishi, ya so su fita amma ya ƙi , bai bi ta kanshi ba suka wuce koma ina ne za su ɗin, don shi bai tambaya ba, ba ya son hayaniyar. Waheedah yake jin gani ya ji dalilin da ya sa ta rufe waya bayan ta san zai kira ta. Amma Anty Ramatu na son ɓata mishi rai. Ba da ita yake jin yin faɗa ba, da Waheedah ne. Yana kallonta ta jinjina mishi kai.

“To ka yi haƙuri don Allah ka jira, a yi addu’ar ina jin ma an fara sai mu fito gaba ɗaya…”

Ganin har lokacin idanuwan shi na kafe a kanta yasa ta ƙara faɗin,

“Ka ji… Yanzun za mu fito.”

Kai ya jinjina ma Anty Ramatun a hankali yana juyawa ya koma jikin wata mota ya tsaya saitin ƙofar wajen. Don shi a motar Yassar ya zo tunda ba shi da tashi har lokacin. Kuma bai yi parking ɗinta a kurkusa ba, kasancewar akwai motoci da yawa a wajen. Bai fi mintina goma a wajen ba ya fara ganin mutane na firfitowa, hakan yasa shi raba bayanshi da jikin motar da yake jingine yana tsayawa tare da duba Waheedah da idanuwanshi a cikin taron mutanen. Anty Ramatu ya hango riƙe da hannunta, duk da ba ya ganin fuskarta da take sadde a ƙasa, ga hular alkyabbar jikinta ta ƙara ɓoye mishi fuskarta.

Yana ganin yanayin tafiyarta, har suka ƙaraso inda yake ɗin.

“Gata nan mintina biyar, ku yi maganar da za ku yi tafiya za mu yi.”

Daƙuna wa Anty Ramatu fuska ya yi.

“Zan taho da ita gida. Na zo da mota.”

Kai ta girgiza wa Abdulƙadir ɗin, ba da ita za a yi wannan rashin hankalin ba.

“Ku yi maganar ku, ko ka bari mu je gida sai ka yi maganar a nutse. Amma yadda muka zo tare haka za mu koma tare da ita.”

Ta ƙarasa maganar tana sauke numfashi. Cikin ɓacin rai yake kallon Anty Ramatu.

“Me yasa ba za mu tafi gida tare da ita ba?”

Kallon shi take ita ma.

“Haka kawai…”

Kai Abdulƙadir ya jinjina, ko da zai ji maganar da aka faɗa mishi yana son a yi ta da hujjar da za ta gamsar da shi, kaf gidansu Yassar ne kawai yakan saka shi yin abu wasu lokuttan ba tare da ya bashi ƙwaƙƙwaran dalili ba kuma ya yi. Amma ko Abba yana faɗa mishi dalili, da Anty Ramatu ta bashi wani dalili mai ƙarfi zai iya juyawa ya tafi in ya so sai su haɗu a gida. Amma haka kawai ba za ta fara gaya mishi abinda zai yi ba. Hannun shi ya miƙa da nufin kamo na Waheedah ya ja ta subar wajen, Anty Ramatu ta tare da faɗin,

“Ai ba a ɗaura ba tukunna, Malam Abdulƙadir.”

Buɗe baki ya yi zai gaya mata maganar da take yawo cikin kanshi Anty Talatu ta ƙaraso wajen tana riganshi da faɗin,

“Hajiya Ramatu ke aketa nema. Ashe kina nan… Abdulƙadir…”

Anty Talatu ta ƙarasa maganar tana maida hankalinta kan Abdulƙadir da har lokacin Anty Ramatu yake kallo.

“Ai kamun namu babu maza.”

Kallonta Anty Ramatu ta yi.

“Na faɗa mishi fa, wai yanzun tare yake so su koma gida da Waheedah…. Na ce ya je za mu taho gidan…”

Murmushi Anty Talatu ta yi, don ita ta san halin shi sarai, Anty Ramatun ma da alamu ba sosai suke haɗuwa da Abdulƙadir ɗin ba.

“Ki faɗa mata da Waheedah zan koma gida… Bana so in yi magana ta ce na mata rashin kunya.”

Abdulƙadir ya faɗi yana kallon Anty Talatu. Kai kawai ta jinjina mishi tana faɗin,

“Allah ya tsare…muma gidan muka yo.”

Ta ƙarasa maganar tana janyo hannun Anty Ramatu da ta ke kallon Abdulƙadir da ya ƙanƙance mata idanuwanshi cike da rashin kunya.

“Hannunta fa zai riƙe Hajiya Talatu. Kina ganin babu wata matsala su tafi gida su kaɗai… Yaran yanzun ba su da kunya wallahi.”

Wannan karon dariya Anty Talatu ta yi.

“Abdulƙadir ne Hajiya Ramatu… Babu abinda zai faru… Idan ba su tafi taren bane matsala…”

Kai kawai Anty Ramatu ta jinjina, amma duk da haka bata so tafiyar Abdulƙadir da Waheedah ɗin ba, musamman da ta juya ta ga ya riƙe hannun Waheedah ɗin tana bin bayanshi. Wannan taɓe-taɓen rashin kunyar ko kaɗan ba sonshi ta ke yi ba. Idan ya yi haƙuri gobe dai-dai lokacin ta riga da ta zama mallakin shi duk riƙon da zai mata ladan hakan zai samu ba yanzun da babu komai cikin hakan sai tarin zunubi.

*****

Bai tsaya da ita ko ina ba sai gaban motar, har lokacin bai ga fuskarta ba, kanta a ƙasa yake, banda dokawa babu abinda zuciyarta ta ke mata. Abdulƙadir ya gama saka ta a kunya, bata san ya za ta fara haɗa idanuwa da su Anty Ramatu ba yanzun, sosai ta ji daɗin zuwan Anty Talatu wajen don a ƙasan zuciyarta ta ke jin yadda Abdulƙadir yake gab da tsula wa Anty Ramatun rashin kunya. Tana nan tsaye kanta a ƙasa har ya buɗe mata murfin motar, alkyabbar jikinta ta tattara tukunna ta shiga, zama ta yi ta rufe murfin motar tana wasa da yatsun hannunta da ta ajiye kan ƙafafuwanta.

Bai mata magana ba shi ma, motar ya ja suka kama hanyar gida. Zai iya rantsewa da duk wani abu na jikinshi hattta gashin da ke bayan wuyanshi yana sane da zamanta a gefen shi. Fuskarta yake son gani ko yaya ne, amma hular alkyabbarta ta kare mishi. Ko ƙunshinta bai gani ba sosai, ta turo mishi hotunan da ta ce ana mata, amma da aka gama bai gani ba, ya yi jira ko za ta tura mishi amma shiru, sai bai tambayeta ba tunda zai zo ya gani da kanshi. A nutse yake tuƙin har suka ƙarasa gida sannan ya samu waje cikin harabar gidan yayi parking.

Fitilar da ke cikin motar ya kunna haske na gauraye su. Gyara zaman shi ya yi yana kai hannu ya ja hular alkyabbarta yana sauketa daga saman kan nata. Hakan ya sa Waheedah da ta yi zurfi cikin tunanin da ba za ta ce gashi ba ta juyo tana sauke mishi manyan idanuwanta da kwalliyar da akai musu ta saka su ƙara girma. Wani irin numfashi Abdulƙadir ya tsinci kanshi da ja yana furzawarwa tare da yawata idanuwan shi akan fuskarta da ta yi mishi kamar ba tata ba. A hankali yake jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa musamman da ta motsa laɓɓaanta da yake komai don ganin bai saka yatsan shi akai ya ji ko janbakinta na da maiƙon da yake gani marar walƙiya ko kuma idanuwan shi ne suke haska mishi hakan.

“Hamma…”

Ta kira cikin sanyin muryarta da ya ji ya saukar mishi da wata kasala ta ban mamaki.

“Me yasa kika kashe wayarki? Kinsan zan kira me yasa kika kashe?”

Maganar tashi ta fito a matsayin tsegumi maimakon faɗan da ya yi niyya, ta gama kashe mishi duk wani faɗa da yake ji, kanshi ya jingina jikin kujerar motar yana ƙanƙance mata idanuwanshi.

“Banda caji ne shi ya sa, wayar mutuwa tayi…”

Waheedah ta faɗi tana kallon yadda shaddar jikin shi ta yi matuƙar karɓar kalar fatarshi.

“Kayan nan sun maka kyau.”

Ta tsinci kanta da furtawa tana saka shi daƙuna mata fuska.

“Na wa kayan kyau dai…”

Dariya ta yi da ta saka shi runtse idanuwanshi yana buɗe su akanta, wani irin kyau ta yi mishi da bai taɓa sanin tana da shi ba. Kamar kullum ya dinga ganin fuskarta ɗauke da kwalliya haka. Har shigar mishi ido da haskenta yake yi yau ya nema ya yi ya rasa, farin nata ya ji ya yi mishi dai-dai.

“Kinyi sallah?”

Ya buƙata yana kallonta har lokacin, kai ta girgiza mishi tana tuna mishi da yadda ita kaɗai ce a faɗin rayuwarshi da take amsa mishi magana ba tare da ta buɗe bakinta ba, kuma ya karɓi amsar. Ita tunda aka fara hidimar bikin a dai-danta take. Ko za ta samu tsarki sai zuwa washegari.

“Za ki je ki yi ne sai ki dawo? Lokaci na tafiya.”

Abdulƙadir ya sake faɗi, don sallah na ɗaya daga cikin abubuwan da baya wasa dasu a rayuwar shi, ba kuma ya bari duk wani makusancin shi ya yi wasa da ita. Sai dai ga mamakin shi kai ta sake girgiza mishi, tana saka shi faɗin,

“Me yasa?”

Cike da wata irin kunya da rabon da ta ji ta a tsakaninsu ta manta ranar ta sauke idanuwanta daga cikin nashi tana faɗin,

“Hamma mana…”

Ɗan ware idanuwanshi ya yi cike da fahimta, da murmushi a fuskarshi ya ce,

“Oh…okay… Na gane. Duk yau me kika ci?”

Ganin ta sake sadda kanta ƙasa ya sa shi faɗin,

“Yau ma ba ki ci komai ba Waheedah? Jiya ban ce ki ci wani abu ba? Me yasa ba ki ci ba? Saboda kin rainani ko? Ban isa in saka ki abu ki yi ba…”

Ɗagowa ta yi ta kalli fuskarshi da take ɗauke da yadda ranshin yake a ɓace.

“Hamma…”

Ta kira cikin sanyin murya tana so ya fahimci ba don ta raina shi yasa bata ci abinci ba, ba kuma don bata ji yunwa bane ba, ana ta hidima ita ba su bata abincin bane shi yasa, amma ta san halin shi, idan ta ce ba a bata abinci bane shi yasa bata ci ba faɗan ƙaruwa zai yi.

“Ki jira ni ina zuwa…”
Ya yi maganar yana buɗe murfin motar ya fice. Gyara zamanta ta yi sosai, ta san ana can ana nemanta wataƙila, ba za ta iya rikicin Abdulƙadir ba da ta ce mishi za ta shiga cikin gidan don kar a nemeta. Tana wannan tunanin Abdulƙadir ɗin ya dawo ya buɗe motar yana shigowa, robar take away da abinci a ciki ya ɗora akan cinyarta yana gyara zamanshi cikin motar ya rufo murfin, robar ruwan a jikinshi ya ajiyeta yana ɗaukar robar da ke jikin Waheedah ya buɗe ya saka mata cokalin da bata kula yana hannun shi ba a ciki, ƙamshin fried rice ɗin da ta sha kayan haɗi da nama ya daki hancinta yana ƙara mata yunwar da take ji.

Ba tare da tunanin komai ba ta sa cokalin ta ɗibo abincin ta kai bakinta ta tauna, Lumshe idanuwa ta yi don ya mata daɗi na fitar hankali, bata san ko hakan na da alaƙa da yunwar da ta ke ji ba, haɗiyewa ta yi tana ƙara ɗibowa, yadda ta ke cin abincin da sauri yasa Abdulƙadir faɗin,

“Slow down, karki ƙware Waheedah…”

Kai ta girgiza mishi, tana haɗiye abincin da yake bakinta.

“Hamma yunwa nake ji sosai, ban ci komai ba fa duk yau… Ba zan ƙware ba.”

Ta ƙarasa maganar tana kai wani cokalin a bakinta. Sosai ta ci abincin ɗan kaɗan ta rage da ta ji ta ƙoshi har cikin maƙoshinta. Ruwan Abdulƙadir ya kwance ya miƙa mata, ta karɓa kuwa tana kaiwa bakinta. Yabi ƙunshin da yake hannunta da kallo. Ruwan da ta sauke ya karɓa yana sha shi ma, maƙoshin shi ya bushe ba tare da dalili ba tunda ba ƙishi yake ji ba. Numfashi Waheedah ta sauke wata nutsuwa na saukar mata, cokalin ta gyara ma zama cikin robar ta rufe, tana jin yadda Abdulƙadir yake binta da idanuwa, kafin yasa hannu ya ɗauki robar abincin ya ɗora a gaban motar ya ajiye. Gyara zaman shi Abdulƙadir ya yi yana jingina da kujerar motar sosai ya lumshe idanuwan shi.

“Hamma…”

Waheedah ta kira ganin kamar shirin bacci Abdulƙadir ɗin yake yi a cikin motar.

“Karki da me ni da surutu Waheedah, hutawa zan yi.”

Ya faɗi ba tare dayae buɗe idanuwan shi ba, gaba ɗaya ba ya jin ƙarfi a jikinshi, sai da ya yi sallar isha’i kafin ya ƙarasa wajen kamun, amma ba ya jin shiga cikin gida ya kwanta a ɗaki. Anan cikin motar inda take yake son hutawa, kokawa yake da abinda ke son ɗora ko da kanshi ne a jikinta ya yi bacci, ba sai ya yi tsayi ba, awa ɗaya ma ya ishe shi. Ba sosai yake samun bacci ba tunda ya tafi, yanzun ganinta yasa duk wata gajiya da yake riƙe da ita saukar mishi. Ita kaɗai ce a rayuwarshi yake iya nunama kasawarshi ko gajiyarwar shi.

“Za a nemeni Hamma…”

Waheedah ta yi maganar kamar za ta yi kuka, tana saka shi buɗe idanuwanshi ya duba agogon da tun wanda ta siya mishi ne.

“Ƙarfe takwas da rabi, tara da rabi sai ki tafi.”

Duk da ya yi maganar babu wajen musu bai hanata faɗin,

“Hamma tara da rabi.”

Idanuwan shi ya sauke cikin nata.

“Musu za mu yi da ke?”

Ya buƙata yana sa ta girgiza mishi kai.

“Good…”

Ya faɗi ya gyara zaman shi cikin kujerar yana lumshe idanuwan shi.

“Ki zauna sosai.”

Ya yi maganar ba tare da ya buɗe idanuwan shi ba. Ita kam bata ga ta zama sosai ba, awa ɗaya Abdulƙadir yake son ta yi a zaune cikin motar, ba don bata son zama da shi ba, har ranta awa ɗaya ma ya yi mata kaɗan tare da shi, amma za a nemeta ta sani, da ba a hidima ba zata damu ba.

“Ina jin sautin tunaninki har nan Waheedah…babu inda za ki je kuma.”

Shagwaɓe mishi fuska ta yi duk da idanuwanshi a lumshe suke.

“To in je in ɗauko wayata?”

Ta buƙata, ko wayar ta latsa kafin awa ɗaya ta cika, za ta fi mata sauri, hannu yasa a aljihunshi yana zaro wayarshi ya miƙa mata, hannu ta sa ta karɓa ganin idanuwan shi a lumshe suke.

“Waheedah.”

Ya faɗi yana sauke numfashi. Cike da rashin fahimtar kiran sunanta da ya yi ta ke kallon shi, kamar ya ji hakan ya sa shi faɗin,

“Password ɗin Waheedah.”

Zuciyarta ta ji ta kumbura ta cika fam, sunanta ne mukullin sirrin wayarshi, dannawa ta yi kuwa ta ga wayar ta buɗe, murmushi ta yi tana gyara zamanta, ta kasa daina murmushi, abinda bata sani ba shi ne kowanne abu nashi da yake buƙatar mukullan sirri sunanta ne, hotunan shi ta shiga tana dubawa, duk wanda ta gani saita shiga WhatsApp ɗinta ta turawa kanta shi. Bata san awa ɗaya ta cika ba, bata ma san ya buɗe idanuwan shi ba, sai da ta ji ya fisge wayar daga hannunta yana faɗin,

“Me kike min da waya…”

Yana dubawa, hotunanshi ya gani ta tura wa kanta ta WhatsApp, yana da tabbacin gaba ɗaya hotunanshi ne da suke cikin wayar. Kai kawai ya girgiza, da ta ce yabar mata wayar ma ta je ta tura ba sai ta ƙarar mishi da data ba. Mukullin motar ya zare yana zagayawa ya buɗe mata, fitowa ta yi. Hamma ya yi saboda bacci yake ji sosai.

“Sai da safe…”

Ya ce mata yana murza idanuwanshi cikin yanayin da ya yi mata kyau. Ganin ta tsaya tana kallon shi yasa shi faɗin,

“Ko in raka ki?”

Da sauri ta girgiza mishi kai. Zata lallaɓa ta shiga ɓangaren Anty, inta ɗan jima anan sai ta koma gida, ba sai ya rakata kowa ya san tare suke ba. Juyawa ma ta yi ko sai da safe bata yi mishi ba, kafin rikicin shi ya yanke mishi hukuncin rakata.

*****

Washegari hidimar ta fi haɗe musu, tun ƙarfe bakwai aka gama musu kwalliya ita da Zahra, wata doguwar riga ce ruwan ƙwai, wuyan rigar dogo ne irin wanda ake kira high-neck a Turance, sosai ta karɓe su duka biyun, daga ɗaurin ɗankwalayensu zuwa yanayin lulluɓinsu za ka gane amare ne ko ba ka kalli ƙunshin da ke hannuwansu ba. A harabar gidan aka fito da su don a yi hotuna. Abdulƙadir ya fi duka mazan da ke wajen tsayi, shi ma yana sanye da shadda fara ƙal da babbar rigarta kamar sauran angwayen. Abin gwanin ban sha’awa, sosai akai musu hotuna, angwayen da amarensu su kaɗai, su duka gaba ɗaya, sai kuma da sauran mutane da abokan arziƙi.

Kasancewar ɗaurin auren na karfe takwas ne, Zahra kanta ba a Kano za ta zauna ba, Katsina ne, ga Yazid da matarshi shi ma. Don haka aka saka bikin da safe don ana dawowa za a tafi da amaren. Suna gama ɗaukar hotunan, babban masallacin da ke nan ƙofar ruwa inda za a ɗaura auren suka ɗunguma suka nufa su dukkansu da abokan su. Ran Abdulƙadir a ɓace yake, tun da safe da ya samu Hajja da tambayar,

“Wai da gaske za a kai Waheedah ne ita ma?”

Cikin rashin fahimta Hajja ta ce,

“Ban gane za a kai Waheedah ba.”

Daƙuna mata fuska ya yi.

“Ina nufin rakiya… Yadda za a raka Zahra har katsina, ita ma za a rakata har Minna?”

Kai Hajja ta jinjina sai lokacin ta fahimci abinda yake faɗa.

“Eh, Hajiya Talatu, Hajiya Aisha, Dadda, Da waye na ji suna maganar, su bakwai dai ne za su rakata, saboda sauran za su raka Zahra.”

Girgiza wa Hajja kai yake yi tunda ta fara magana, shi ba ya son wannan al’adar, a tsarin shi ko da ba wani gari bane ya zo da mota ya dauki matarshi su tafi, su Anty Talatun da take magana su suka je suka yi jeren kaya har Minna ɗin tun satin bikin. Hakan ma ya isa, Allah ya amfana ba sai sun raka mishi mata ba, ba ya son wannan al’adar ko kaɗan.

“Ki ce musu su zauna abinsu Hajja, ni da ita kawai za mu tafi da na dawo ɗaurin auren…”

Kallon shi Hajja take kamar ba shi da hankali.

“Ban gane me kake son cewa ba.”

Numfasawa ya yi.

“Wani rakiyar amarya nake magana… Ni bana so… Su zauna.”

Wata dariyar takaici mai sauti da bata da alaƙa da nishaɗi Hajja ta yi, ta sa Abdulƙadir faɗin,

“Ko ni in gaya musu su yi zamansu?”

Cike da takaicin da ta kwana biyu bata ji irin shi ba take kallon Abdulƙadir ɗin.

“Wallahi idan ba ka ɓace min daga nan ba saina kwasheka da mari…”

Kallonta Abdulƙadir ɗin yake yi shi ma.

“Mari fa Hajja…me na yi ni? Me na yi?”

Yake tambaya yana son sanin dalilin da Hajja za ta ce za ta mare shi don ya faɗi ra’ayin shi, ya ga kirki ne shi su Anty Talatun za su yi wa , kuma ya ce ba ya so ba sai a yi abinda ya ce ba tunda matar tashi ce.

“Saina marekan za ka bar min ɗaki ko?”

Daƙuna fuska ya yi.

“Ai ban san me na yi bane ba… In faɗa musu zan ɗauki matata ko za ki faɗa musu.”

Numfashi Hajja ta sauke, idan ta biye wa Abdulƙadir ba mari ba kawai, rufe shi da duka za ta yi. Bata san ranar da zai yi hankali ba, har ranta ta ji daɗin haɗin auren shi da Waheedah, ko ba komai tana fatan hankali da nutsuwar yariyar su tausasa halayyar Abdulƙadir ɗin, har daɗi ta ke ji ganin tunda aka fara hidimar bikin babu wanda ya yi kuka da shi, babu wanda ya ce ya yi mishi rashin kunya. Amma yanzu yana son ja wa kanshi zagi da bakin mutane.

“Al’adace hakan, ba kuma za a canzata daga kanka ba, daga nan har Minna za ka ce abarka ku tafi ku kaɗai saboda kai ba ka da hankali…”

Hajja take maganar cikin faɗa.

“Hajja…”

Abdulƙadir ya kira tana katse shi da,

“Wallahi idan baka ɓace min da gani ba sai ranka yayi mugun ɓaci… Kuma in ji ka sami wani da maganar nan don Allah… Yau ka nuna min ban isa da kai ba Abdulƙadir kai musu maganar nan…”

Hajja ta ƙarasa tana miƙewa ta ci gaba da haɗa kayanta da ta ke yi lokacin da ya shiga ɗakin. Tunda ya fita ranshi a ɓace yake har ya ƙarasa shiryawa suka fito suna hotunan nan sama-sama yake jinshi, addu’a yake kar wanda ya taɓo shi ballantana ya sauke mishi ɓacin ran da yake ji. Ko da ake musu hotuna da Waheedah, yana jinta ta yi magana dai-dai kunnen shi.

“Wa ya taɓa min kai Sadauki?”

Taso ta sa murmushi ya ƙwace mishi, tun ranar da ta fara furta mishi sadaukin nan ya ji sunan ya mishi daɗi sosai. Sai dai hakan bai sa ɓacin ran ya tafi ba, ko amsa ma bata samu ba har suka bar wajen. Da ɓacin ran ya ƙarasa masallacin, haka har aka gama ɗaurin auren aka fito daga masallacin, a ƙasan ranshi yake jin wata irin nutsuwa ta ban mamakin da igiyar da ta ƙulle tsakanin shi da Waheedah. Nan ma sai da aka tsaya ɓata lokaci wajen ɗaukar wasu hotunan, don ma Abba ya ce musu a tafi gida, akwai tafiya a gabansu.

*****

Babbar rigarshi ya cire don jinshi yake a takure yana sake kayan, duk da wata shaddar ya sake sakawa, amma ba ya jin nauyinta kamar wadda ya cire, ninke su yake yi ya ji Yassar ya shigo ɗakin da sallamar da ya amsa yana ci gaba da linke kayan da yake yi.

“Ka yi sauri, an fara shirye-shiryen tafiya…”

Kai kawai Abdulƙadir ɗin ya ɗaga wa Yassar yana saka shi faɗin,

“Abdulƙadir…”

Bai amsa ba tunda kunnuwa ne suke jin magana.

“Abdulƙadir…”

Ya sake kira, ƙananun idanuwanshi ya sauke kan fuskar Yassar.

“Kunnuwane suke ji Hamma… Kasan ina jinka ai.”

Numfasawa Yassar ya yi.

“Za ka ɗauki ‘yar mutane zuwa wani gari, Abdulƙadir ba a aura maka ita don an gaji da ita ba, ba kuma a aura maka ita don an gaji da kula da ita ba. Roƙonka nake karka ƙuntata mata, karka cutar da ita…”

Idanuwan shi Abdulƙadir ya ƙanƙance.

“Don ba a jarabawar samun limanci da na ce ka yanki form Hamma…”

Kai Yassar yake girgiza da murmushi a fuskar shi.

“Don ubanka ba maganar wasa nake da kai ba, nasiha nake maka.”

Ware mishi idanuwa Abdulƙadir ya yi.

“Abinda yasa na ce limanci zai maka kyau kenan.”

Dafe kai Yassar ya yi, bai san ranar da Abdulƙadir zai fara ɗaukar abubuwa da muhimmanci ba, ganin babu alamar zai saurare shi yasa shi miƙewa yana faɗin,

“Abba na kira…”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Don Allah Hamma ka ce ba wata nasihar za a yi min ba… Wai ita Waheedah ba za a mata bane ba? Nima ai aurena aka bata, me yasa ni kaɗai za a dinga yi wa…. Ita ma ka je ka ce ta riƙeni amana, kar ta cutar dani…”

Ƙofar Yassar ya buɗe kamar bai ji abinda Abdulƙadir ɗin ya ce ba.

“Hamma magana nake kana tafiya…”

Ficewa ya yi yana jan ƙofar, fuska ya ƙara daƙunawa yana ɗibar kayan ya tura cikin ƙaramar jakar da ya shirya duk kayanshi da zai iya ɗauka a ciki, yawanci ƙananun kaya ne, manyan fiye da rabi a nan gida ya bar su. Jakar ya bari kan gado ya fita daga ɗakin zuwa ɓangaren Abba yana shiga da sallama, babu kowa sai Waheedah da take zaune a gaban Abba, ta sake rigar ɗazun, bai gama ganinta ba sosai cikin rigar ta sake, yanzun baya ma iya ganin fuskarta don lafayane a jikinta an ja shi an rufe fuskarta gaba ɗaya, yanayin yadda kafaɗunta suke rawa yasa shi gane kuka take yi.

Gefenta ya zauna yana faɗin “Abba ga ni…Hamma ya ce kana kirana.”

Kai Abba ya jinjina yana kallon yaran nashi, yanajin ƙaunar su fal cikin ranshi, yana kuma mamaki har lokacin yadda ƙaddarar rayuwa ta kawo su inda suke yanzun. Cikin ranshi yake wa Allah godiya yana ƙarawa da musu fatan zaman lafiya da rayuwar aure mai inganci.

“Idan da wani ya ce mun za ku zo nan a rayuwar ku ko na yarda zan jinjina lamarin…”

Abba ya fara magana yana ɗorawa da,

“Ko da kuke jin ana kiran haƙuri a zaman aure, ba don yana jigon auren bane gaba ɗaya, sai don yana taka muhimmiyar rawa a zamantakewa ta yau da kullum. Abu ɗaya zan faɗa muku, kar ku ba ni kunya, ku dukanku kar ku ba ni kunya. Matsalar aurenku ku yi ƙoƙarin ganin kun shawo kanta da kanku, sirri na ɗaya daga cikin abubuwan da suke da muhimmanci a aure… Ku riƙe sirrin junanku kamar fitar da shi zai iya zame muku matsala.

Don na ce hakan kuma ba ina nufin ya baku damar da zaku cutar da junanku don za ku riƙe a matsayin sirri ba. A duk lokacin da hakan ya faru, kuke ganin ba za ku iya ba ku ɗaga waya ku kira ni, shi ne kawai mutuntakar da za ku yi min, ku sanar da ni kafin yanke hukunci mai girma…”

Su dukansu sunyi shiru suna sauraren Abba, Waheedah dama tun da aka rakata wajen Mami take kuka, har aka kawota wajen Abba, yanzun ma kukan ta ke yi sosai. Abdulƙadir kanshi Abba ya sa jikinshi yin sanyi, tabbas aure abu ne mai girman gaske, ba zai tuna ranar ƙarshe da Abba ya zaunar da shi yana mishi nasiha har yana jin ƙaunar shi a tare da kalaman shi ba sai yau.

“Allah ya yi muku albarka a zamantakewar ku, Allah ya tabbatar muku da dukkan alkhairi…”

Abba ya ƙarasa da wani yanayi mai nauyi a muryarshi, har a ƙasan ranshi ya fara jin kewar yaran nashi.

“Mun gode Abba…”

Abdulƙadir ya faɗi yana miƙewa, amma Waheedah ta kasa miƙewa, magana zai mata Anty ta shigo, bata ce mishi komai ba ta zo ta kama Waheedah tana janta suka fice daga ɗakin. Kukan da take ya yi mishi tsaye a maƙoshi. Bin bayansu ya yi yana wucewa ɓangaren su don ya ɗauki jakarshi, ya san zai kwana biyu bai shigo Kano ba, makarantar Waheedah ma transfer akai mata zuwa Minna ɗin, ba don Abba ya san mutane ba da hakan ya yi musu matuƙar wahala. Kuma yadda yake ji ba zai iya barinta a Kano ba, inda duk ya sa ƙafa nan za ta mayar da tata. Sai dai ta haƙura da makarantar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 16Abdulkadir 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×