Skip to content
Part 15 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Tunda suka shiga gidan Yassar ta gaisa da matar shi Hauwa da ‘yar kanin Abba ce ya aura, ta samu kujera a falon ta zauna. Bata san me Yassar ɗin ya ce mata ba, ta ga dai ta zo tace mata ta tashi ta je ta huta, ɗaya daga cikin bedrooms ɗin ɗakin ta rakata. Fajr ƙin binta ya yi saboda yana kallon cartoon, da yake Yassar ɗin ma yakan je ya ɗauko shi ya yi hutun ƙarshen mako a gidanshi wasu lokuttan, yaron ya saba da su. Tana shiga ta kwantar da Ikram, banɗaki ta shiga ta ɗaura alwala don ko sallar azahar bata yi ba. Ta fito ta gabatar da sallah, zaune ta yi akan kafet ɗin tana ɗora kanta a jikin gadon, kanta a cunkushe take jin shi, ta rasa abinda yake mata daɗi a gaba ɗaya duniyar.

Tunani ne ya ɗauke ta yana watsata shekaru shida da wasu yan watanni da suka wuce, kafin rayuwa ta kawota inda take.

*****

Tun bayan bikin Nuriyya, sai ya zamana babu abinda Waheedah ta saka a gaba banda karatunta, takan yi kwana biyu bata leƙa gidan Nuriyyar ba, duk da ba wani nisan kirki ne a tsakanin su ba, ita tana cikin Naira da Kwabo, su kuma su Waheedah ɗin a ƙofar Ruwa, ko da ƙafa za ta gangara. Amma suna yawan waya, kusan kullum za su yi chatting, wani lokacin kuma in ta riga Nuriyya tashi daga makaranta takan biya ta FCE ɗinsu sai su gaisa. A yanayinta take fuskantar yadda har lokacin taƙi kwantar da hankalinta da auren Anas ɗin.

Sai dai faɗan da Waheedah take mata yasa ta daina gaya mata komai, in ta tambaya ma sai dai Nuriyyan ta yi murmushi ta ce mata lafiya ƙalau, duk da ta san ƙarya take yi, bata takurata, kullum Nuriyyar na cikin addu’o’inta akan ta samu kwanciyar hankalin da kowace mata take samu a ɗakin aurenta, tare da mata addu’ar nutsar da hankalinta da auren Anas din. A ɓangaren samarin da suke kawo ma Waheedah tayin soyayya ma babu abinda ya canza, don bata fasa gaya musu cewar an mata miji ba, kamar yadda bata fasa ba wa Abdulƙadir labarin yadda ranarta ta kasance a kullum ba. Duk da yanzun saƙnonin nata na zuwa, suna kuma nuna alamar an karanta. Amma tun kafin bikin Nuriyya rabon da ta samu amsar shi.

Bata san ya aka yi ba, amma a shirunshi take karantar akwai abinda yake damun shi, tana kuma jin hakan har ƙasan zuciyarta, kuma koma menene yake damun shi ɗin, tare suke cikin damuwar, don ita ma nata hankalin ba a kwance yake ba. Daina ƙirga kwanakin zuwan shi ta yi, za su fi mata sauri idan bata ƙirga ba, sosai ma ta yi mamakin kanta da bata taɓa tambayarshi yaushe zai zo ba. Tana alaƙanta rashin yin hakan da yadda jikinta yake bata ba lafiyar shi ba. Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar mata har bayan shekara ɗaya, shekarar da ta yi dai-dai da lokacin fitar Abdulƙadir daga NDA.

Lokacin da har a fuskar Mami takan karanci damuwar da ta kasa furta mata akan rashin wani da za a nuna a ce yau ya zo zance wajenta. Musamman da aka sa bikin Zahra, don wannan karon yara uku Hajja za ta aurar, Zahra, Mubarak da kuma Yazid da sai yanzun da alama surutun kowa ya ishe shi ya fito da matar aure, duk da sukan jima ba su saka shi a idanuwansu ba, da alama ya bar Kano ɗin kenan kuma sai dai ziyara. Duk da gidan nasu Allah ya yi musu fahimta kan cewa shi aure lokaci yake da shi.

Duk yadda kaso ka kawar da yaro, idan lokacin shi bai yi ba dole za ka haƙura, shi yasa sam Abba baya jira, wanda duk Allah ya fitowa da miji aurar da shi yake yi, ko Nusaiba akwai wanda ya fito cikin ‘yan uwa da nufin aurenta, ta ƙi da cewar ita karatu take so ta yi, tunda ko sakandire bata kammala ba, babu yadda ba su yi akan a tsayar da magana ba, Abba ne ya ƙi, cewar shi su dai jira in za su iya, yarinyar ta ƙara mallakar hankalin da za ta yarda da auren ɗansu, kar ya yanke hukuncin da zai zama kowa bai ji daɗin shi a gaba ba. Ita kanta Waheedah zuwa lokacin tana so ace ta fara kula wasu, ta sha faɗa wa kanta daga yau duk wanda ya zo mata da tayin soyayya za ta amsa shi, amma sai ta tsinci kanta da kasa yin hakan.

Ko wani ta tsaya da shi takan ji kamar tana cin amanar Abdulƙadir ne, tana jin rashin hankalin da ke cikin hakan, tunda bai furta mata kalmar so ba, asalima bai san tana haukanta ba, amma haka take ji. Zuwa yanzun azumi ta fara da tsayuwar dare akan neman zaɓin Allah, sai take jin da duk rana kamar ana ƙara rura mata wutar son Abdulƙadir ɗin ne a zuciyarta. Yau ma a gajiye ta dawo daga makaranta, don bata dawo ba sai yamma liƙis, har a ƙasusuwan jikinta take jin gajiya.

Da sallama ta shiga ɗakin tana zare takalmanta a ƙofa.

“Mami…”

Ta kira tana cilla jakar hannunta kan kujera, da hijabin ta nufi hanyar kitchen in da ta samu Mami tana tace zoɓo. Kanta ta ɗora a bayan Mami ɗin tana faɗin,

“Mami ƙashina kamar zai fito waje…”

Dariya Mami ta yi tana ture Waheedah ɗin.

“Ɗaga ni ni kam… Ƙashin ne kamar zai fito waje?”

Kai Waheedah ta ɗaga mata, cikinta take jin ya tattaru waje ɗaya saboda yunwa.

“Na gaji sosai, gashi yunwa nake ji.”

Robar sukari Mami ta ɗauko tana zubawa cikin bokitin zoɓon.

“Ki je ki ci abinci…”

Daƙuna fuska Waheedah ta yi.

“Mami baki dafa mana komai ba?”

Murmushi kawai Mami ta yi, kamar Waheedah za ta yi kuka ta baro kitchen ɗin tana zira takalmanta ta fice daga gidan. Ta manta girkin Mama ne ranar da ta ci wani abu a makaranta, yunwar da take ji kuma ba za ta barta ta tsaya ko da indomie ta dafa ba. Za ta je ta ga ko abinda Mama ɗin ta dafa zai ciyu. Ɓangarenta ta wuce tana shiga da sallama, bata samu kowa a ɗakin ba, don haka ta wuce kitchen ɗin, kulolin da ake zuba abinci ta buɗe, tana cin karo da malmalolin tuwon shinkafa da suke kulle a fararen ledoji. Plate ta ɗauka, ta saka malmala ɗaya a ciki, lumshe idanuwanta ta yi tana addu’a a cikin zuciyarta miyar ta kasance ta taushe ce, ko ya aka watsal-tsala za ta iya daurewa ta ci ko don yunwar da take ji.

Zuciyarta ta ji ta yi wani irin tsalle da yasa ta buɗe idanuwanta tana dafa ɗayan hannunta jikin kantar kitchen ɗin, batasan me ta gane nashi ba, takun tafiyar shi, kusancin shi, ba za ta ce ga asalin abinda ta ji ba, amma ba sai ta juya ba, ta san shi ɗin ne ya shigo kitchen ɗin, Abdulƙadir ne, sosai take jin shi gab da ita, jikinta ya yi mutuwar da ta kasa juyawa ne kawai, tana kallon shi ya miƙa hannu ya ɗauki plate ta saman kanta, ta gefe ya zira hannu yana dauko tuwon guda ɗaya, ya saka a plate ɗin ya ƙaro wani guda ɗayan. Tunda la’asar ya dawo gidan, yana ɗaki a kwance ne saboda baya son surutu, baya son magana da kowa.

Ko passing out da akan yi shagali a gida, a yi su Calenders su menene ya faɗa wa Yassar ya gaya wa su Hajja baya so, su yi mishi addu’a kawai, kar wanda ya tara mishi mutane, in sun yi ko da ya zo zai juya. Sanin halin shi yasa ba su yi komai ɗin ba, duk da haka Hajja ta sa ya ɗaukar mata hoton shi guda ɗaya, ta yi babban agogo ta kafe a falonta. Tun da can baya son mutane, saboda suna bashi haushi, yanzun abin ne ya ƙaru, ko kaɗan baya son jin shi cikin mutane. Yana jiran list ɗin sunaye ya fito zuwa inda za a kai shi ya haɗa jakarshi ya yi gaba. Tun da ya zo yunwa ke cin shi, bai faɗa wa kowa yana hanya ba, a cikin abokan shi wani zai zo Kaduna ya biyo shi.

Don haka bai samu kowa a gidan ba, yaran gidan wasu na boko, wasu na Islamiyya, Hajja kuma ta fita, har kitchen ya shiga bai samu wani abinda zai ci ba, Nazir kaɗai ya gani yace mishi girkin Mama ne, hakan yasa yunwar tashi ɓacewa na wani lokaci, kafin yanzun ta sake taso mishi tana fito da shi babu shiri. Hijabin jikinta ya sanar da shi ita ɗin ce, baya jin akwai mai saka dogayen hijabai har suna share hanya a gidan nasu banda ita. Ba zai ce ga asalin abinda ta yi mishi take bashi haushi ba, duk da haushin kowa da komai yake ji. Amma nata ya yi yawa, yana jin inda ta faɗa mishi Nuriyya ta fara kula wasu da ya yi wani abu akai kafin lokaci ya ƙure mishi.

Duk da tun daga ranar da aka ɗaura mata aure, bai sake bari tunaninta ya dame shi ba, ya riga ya faru, babu abinda zai iya akai, amma ya taɓa dhi ta fannin da shi kanshi bai taɓa tunani ba. Ganinta yanzun ɗin yana saka wani abu matsewa a ƙirjin shi. Wajen tukunya ya ɗan matsa yana buɗewa, wata irin miyar kuka ta yi mishi sallama, tunda yake bai taɓa ganin miyar kuka mai muninta ba, yana ganin ruwan daban, kukar daban, man da yake a sama kamar daga baya akai tunanin zuba shi yana gefe shi ma.

“Mama!”

Ya kira yana saka Waheedah sake lumshe idanuwanta da yadda muryarshi ta sauka cikin kunnuwanta tana saka tsikar jikinta tashi. Sai lokacin ta samu ƙarfin juyowa tana sauke idanuwanta akan shi, rigar sojoji ce a jikinshi mai dogon hannu, sai gajeran wando, ya ƙara mata wani irin girma na ban mamaki, sai ta ganta ‘yar ƙararrama a gaban shi. Wani yawu ta haɗiye ko zuciyarta za ta rage gudun da take a ƙirjinta.

“Mamaa!”

Ya sake kira a karo na biyu, dai-dai lokacin da Mama ta ƙaraso kitchen ɗin a rikice, don ko bata ji muryarshi ba tasan babu wanda zai mata wannan kiran sai shi, bata dai tsammace shi a lokacin bane saboda ta san baya garin.

“Wace irin miya ce wannan?”

Ya buƙata yana tsareta da idanuwa, kallon shi Mama ta yi girman shi na bata mamaki, kaf gidan bata jin akwai mai tsayin shi.

“Abdulƙadir… Saukar yaushe?”

Ta tambaya maimakon amsar tambayar da ya yi mata.

“Wace irin miya ce wannan?”

Ya sake maimaitawa yana yin kamar bai ji maganar da ta yi mishi ba, tare da ɗorawa da,

“Ya mutum zai saka wannan miyar a bakin shi? Me yasa za a yi mana tuwon shinkafa da wannan miyar? Me yasa kike mana girki kamar Abba baya bada kuɗin da za a yi mana me daɗi?”

Numfashi Waheedah ta sauke ganin yanayin da ke fuskar Mama yasa ta faɗin,

“Hamma…”

Sai lokacin ya juya yana sauke mata ƙananun idanuwan shi da suke cike da rikici, kai ta ɗan girgiza mishi alamar ya bari, ko me yake shirin sake faɗa kar ya faɗa, ya yi shiru kawai. Wani irin tsaki ya ja yana ajiye plate ɗin ya fice daga kitchen ɗin, ita ma Waheedah nata plate ɗin ta ajiye tana rufa mishi baya, Mama ta bi su da kallo kawai, don Abdulƙadir ya daɗe da daina bata mamaki.

“Hamma…”

Waheedah ta kira tana mayar da numfashi saboda gudu-gudun da ta yi wajen binshi, juyowa ya yi gaba ɗaya yana sata runtse idanuwanta tukunna ta buɗe su.

“Menene?”

Ya buƙata yana tsareta da idanuwan shi da suke birkita mata lissafi, akwai kwarjini na musamman da shi kaɗai ne yake mata.

“Me za ka ci?”

Ta buƙata, kai Abdulƙadir ya girgiza mata, ya sake juyawa. Yanajin idanuwanta na bin shi har ya sha kwana. Numfashi ta sauke tana kai hannu a ƙirjinta inda zuciyarta take doka mata, ta kai mintina biyu a wajen tukunna ta wuce tana komawa ɓangarensu, sam ta manta da wata yunwa da take ji, tana shiga ta wuce ɗaki, tana samun Amatullah ta fito daga banɗaki da alamar alwalar magriba ta yi don ana gab da kira, hijab ta cire ita ma ta shiga banɗakin ta gabatar da alwala.

****

Sa’adda ya dawo daga sallar isha’i ya samu abinci a ɗakin shi an ajiye. Tunanin farko da yazo mishi shi ne Waheedah ce, zama ya yi yana ɗaukar plate ɗin ya buɗe, dankali ne da ƙwai, sai ƙaramin flask ɗin da yasan shayi ne a ciki, buɗewa ya yi yana zubawa, ƙamshin shayin yasa shi sanin ba Waheedah bace ba, Hajja ce, ita kaɗai take saka Na’a’na’a a shayinta. Haka kawai a ƙasan zuciyarshi sai ya ji ya so ace ya fito daga hannun Waheedah ne, da ya girgiza mata kai ba yana nufin ba zai ci komai bane ba, yana nufin bai san me zai ci ba, amma bata kawo mishi komai ba.

A kofi ya zuba shayin ya soma haɗawa da soyayyen dankalin da ƙwai yana ci, lokacin ya ji an turo ɗakin da sallamar da kafin ya amsa Yassar ya ɗora da,

“Ba za ka iya ce min za ka zo ba?”

Kafaɗu ya ɗan ɗaga wa Yassar ɗin bayan ya amsa sallamar da ya yi, gefen shi Yassar ya zauna yana ɗaukar cokalin da ke cikin plate ɗin ya cako dankalin ya sa a bakin shi yana soma taunawa tukunna ya ajiye cokalin.

“Kafaɗu za ka ɗaga min?”

A kasalance Abdulƙadir ya ce,

“Me kake so in yi to? Na riga na zo, komawa zan yi in kiraka in ce maka zan taho?”

Kai Yassar ya jinjina, sosai rashin kunyar Abdulƙadir ta ƙaru tun shekarar da ta wuce, wani abu ya same shi da baisanyi menene ba, ba komai yake faɗa mishi ba, amma ba ya rufe shi har haka, ko kiranshi ya yi a waya da cewar zai je Kaduna ya dubashi sai ya ce mishi babu lokacin da zai ganshi, tun yana zuciya ya ƙi zuwa har ya kula Abdulƙadir ɗin na ɓoye mishi ne, sai ya dinga share shi baya kiranshi sai ya shiga Kaduna tukunna. To har yanzun kuma ɓoye mishi yake, wannan ba ƙanin shi bane ba.

Wayarshi da take a hannun shi Yassar ya danna don ya ga ko ƙarfe nawa, hakan ya sa Abdulƙadir cewa,

“Na san yarinyar nan…”

Yana daƙuna fuska, danna wayar Yassar ya yi haskenta ya ɗauke, da sauri Abdulƙadir ɗin ya kai hannu yana fisge wayar Yassar ɗin ya sake dannawa.

“Ka ban wayata Abdulƙadir…”

Sosai yake kallon hoton fuskar wayar Yassar ɗin.

“Hauwa ce ko?”

Ya tambaya yana miƙa wa Yassar ɗin wayar daya karɓa yana faɗin,

“Ban sani ba.”

Kai Abdulƙadir ya jinjina yana ajiye plate ɗin dankalin ya ɗauki kofin shayin shi da ya riƙe da hannuwa biyu yana kurɓa.

“Tun yaushe?”
Shiru Yassar ya yi ya ƙyale shi.

“Hamma magana fa nake maka… Tun yaushe? Za ka fara dating ba ka faɗa min ba ashe?”

Kallon shi Yassar ɗin ya yi.

“Kamar yanda wani abu ya sameka ba ka faɗa min ba kake nufi?”

Numfashi Abdulƙadir ya sauke don ba shi da abinda zai faɗa, wani abu ya same shi da gaske, amma kuma ya riga ya wuce, faɗar ba shi da amfani tunda ba wani abu ne zai canza ba idan ya yi hakan.

“Me yasa ba za a haɗa da na su Hamma Yazid ba?”

Abdulƙadir ya buƙata yana son sake akalar zancen. Yassar ya gane hakan, ba zai takura shi sai yasan me ya same shi ba.

“Bamu daɗe ba, ba mu fi wata biyu ba, kar wani abu ya canza a gaba…”

Kallon shi Abdulƙadir ya yi.

“In har ka sa ta a fuskar wayarka kana jinta a ranka Hamma, bana tunanin akwai abinda zai canza…”

Murmushi Yassar ya yi, wata biyu da faɗa wa Hauwa yana sonta, amma ya ɗan jima yana yin haka daga nesa-nesa dama, duk sanda za su zo gidan, kuma suna ɗan chatting kaɗan a WhatsApp. Baya so abinda ya faru da Yazid akan Waheedah ya faru da shi, shi yasa bai yi nauyin baki ba, kuma da dukkan alamu ita ma ta jima tana jinshi ɗin, duk da haka baya son yin gaggawa, duk da zai fi so su yi shagalin bikin nasu tare da Yasir, amma sam Yasir ya ce mishi shi bai shirya yin aure a ɗan lokacin ba, da alama zai riga shi.

“Ka yi magana kawai a yi bikin nan duk mu huta.”

Abdulƙadir ya faɗi cikin sigar tsokana. ‘Yar dariya Yassar ya yi.

“Lallai yaron nan, to kai ma ka yi auren mana.”

Girarshi duka biyun Abdulƙadir ya ɗaga wa Yassar.

“Da wa?”

Ya tambaya yana kurɓar shayin da ya ƙware shi da jin amsar Yassar ɗin.

“Waheedah…”

Tari yake sosai don shayin ya bi mishi ta hanyar da bai kamata ba, sosai yake ƙara kurɓar shayin ko zai samu sauƙi, muryarshi a dishe ta fito daga ƙasan maƙoshin shi.

“Wane irin wasa ne wannan?”

Ya buƙata yana sa Yassar ɗin hararar shi.

“Karka raina min hankali Abdulƙadir, shekara nawa kana yawo da hotonta a wallet? Don ban yi magana ba baya nufin ban kula ba, ita ma kuma ina kallonta, bata kula kowa, ban taɓa ganin ta fita zance da wani ba…”

Kallon Yassar yake da dukkan alamu Hausa yake mishi, amma da wani yare daban yake jin maganganun Yassar ɗin na dira kunnuwanshi saboda yadda ya kasa fahimtarsu, yanayin fuskar Abdulƙadir ɗin Yassar yake kallo, mamaki na bayyana akan tashi fuskar.

“Tsaya… Me kake son ce min?”

Ya tambaya yana kasa gasgata abinda yake gani a fuskar Abdulƙadir ɗin, kai Yassar yake girgizawa.

“Abdulƙadir…”

Ya kira yana cigaba da girgiza kai, Abdulƙadir ɗin bai yi magana ba har lokacin, kallon Yassar ɗin kawai yake kamar ƙaho ya fito mishi a tsakiyar kai.

“Abdulƙadir…”

Yassar ya sake kira a karo na babu adadi, yana jinjina abinda yake gani a fuskar ƙanin nashi, har ranshi, duk tsawon shekarun nan ya ɗauka soyayya suke da Waheedah ɗin, yana kuma da tabbacin ba shi kaɗai bane yake zaton hakan. Wani zafi ya ji ƙirjinshi na yi, ya hana Yazid furta mata yana sonta saboda a tunanin shi Abdulƙadir ɗin na son ta, yana kuma da tabbacin idan shi baya sonta ita tana son shi, don yadda take tambayarshi akan Abdulƙadir ɗin kawai ya tabbatar mishi da haka daga nata ɓangaren.

“Me yasa?”

Yassar ya tambaya, sai lokacin Abdulƙadir ya ce,

“Me yasa me?”

Kai Yassar ya jinjina.

“Tana sonka Abdulƙadir…”

Yassar ya yi maganar can ƙasan maƙoshin shi, tausayin yarinyar na cika zuciyarshi, plate ɗin dankalin shi Abdulƙadir ya ɗauka yana ɗiba ya cika bakin shi da shi taf yana cigaba da taunawa, maganar Yassar ɗin na mishi yawo a duk ilahirin jikin shi.

‘Tana sonka Abdulƙadir.’

Ko a mafarki mai nisa bai taɓa hango soyayya da Waheedah ba, ko kaɗan, soyayya fa, da Waheedah, tana da muhimmancin da shi kanshi bai san iyakarshi ba a rayuwarshi, amma soyayya da ita, shi ne ƙarshen abinda yake hangowa. Sai dai soyayya da kowa ma a yanzun ba abu bane da yake tunanin zai faru, ba ya jin yana da wannan lokacin.

“Abdulƙadir …”

Yassar ya kira ganin yadda yake cin abincin.

“Karka ƙware…”

Bai kulashi ba, dankalin kawai yake zubawa a bakin shi yana taunawa. Hakan yasa Yassar miƙewa ya fice daga ɗakin da tunani kala-kala a ranshi. Tari Abdulƙadir ya soma yi yana fita, babu shiri ya ɗauki shayi yana kora dankalin bakin shi da shi, haɗiyewa ya yi yana sauke numfashi. Ƙafafuwan shi ya ja yana ɗora su kan gadon tare da kwanciya ya ja bargo ya rufe jikin shi. Pillow ɗin da ya ɗora kan shi ya ji ya soma isar shi, don ba haka yake kwanciya da pillow ba, ɗagawa ya yi yana ɗora pillow ɗin akan hannun shi tukunna ya ɗora kan shi a sama, ya ɗan ji dai-daito a kwanciyar.

Yassar ya sa shi abinda ba ya son yi, idan akwai abu na biyu da ba ya so bayan raini, tunani ne, ko kaɗan ba ya son ya zauna yana tunani, ta ya Yassar zai ce Waheedah na son shi, ita Waheedah ɗin bata da bakin da za ta faɗa mishi ko me yake faruwa, kanshi ya bala’in ɗaurewa cikin yanayin da bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba, komai yake ji ya cakuɗe mishi haka kawai. Tun ran ɗaurin auren Nuriyya rabon da ya yi tunanin wani aure, yanzun kuwa gaba ɗaya tunanin ne a ranshi.

Ta ina zai fara? Wace yarinya zai fara tunkara? Yaushe ma zai ganta? Duk da ya san indai yana da rai da lafiya aure abu ne da ya zame mishi dole, ko don gudun faɗawa halaka, tare da Waheedah yana da tabbacin ba za ta taɓa raina shi ba. Asalima raini na ɗaya daga cikin abinda yasan ba zai taɓa shiga tsakanin su ba. Kuma a yadda yake ji ba zai iya kallon idanuwan kowacce yarinya da sunan soyayya ba a yanzun, ba shi da ma da wannan lokacin, da an yi posting ɗin shi zuwa inda zai fara aiki kuma zai ƙara samun ƙarancin lokacin duk wannan abubuwan.

Tashi ya yi zaune, karo na farko a tsawon lokaci da ya ji zuciyarshi na dokawa da abinda yake shirinyi. Wayarshi ya ɗauko ya kunna data ɗin, WhatsApp ɗinshi ya buɗe, sunan Waheedah ne farko da saƙonninta da suke ta shigowa, sosai bugun zuciyarshi yake ƙaruwa , buɗe saƙonnin ya yi:

‘Me ka ci?’

‘Karka kwanta da yunwa Hamma.’

‘In dafa maka indomie? Ko za ka sha Tea?’

‘Shine ba ka faɗa min za ka zo ba ko?’

Dubawa ya yi ya ga tana online, rubutu ma take yi, jikinshi yake ji har kyarma yake mishi, a hankali ya soma rubutu yana tura mata:

‘Waheedah…’

Rubutun da take ya ga ta tsayar, hakan ya sa shi cigaba:

‘Waheedah…’

Runtse idanuwan shi ya yi yana sake buɗe su kan screen ɗin wayar.

‘Hamma’

Ta amsa, ya karanta sunan nashi da muryarta, ba ya son yin abinda zai yi dana sani, sanin ba za ta taɓa raina shi bane abinda ya ba shi ƙwarin gwiwar rubuta;

‘Kina so na?’

Karanta tambayar tashi ya yi, ganin bata fara ko typing ba, ba lallai ma ta gane kan tambayar tashi ba.

‘Ba so na ‘yan uwa ba Waheedah… So na aure. Kina so na?’

Tana online har lokacin, amma bata ko fara rubutu ba, kuma ya ga ta karanta, zuciyarshi yake ji har cikin maƙoshin shi sabo da dokawar da take mishi.

‘Ki amsani, zan ƙirga ɗaya zuwa goma. Karki amsa sai kina da tabbaci, idan ba ki da shi karki amsa, nida ke za mu yi kamar ban tambaya ba, maganar ba zata sake haɗa mu ba har abada.’

Ya faɗi yana jin yadda maganganun nashi suka zauna mishi, ita da shi suna da daƙiƙan da za su ɗauke shi ya ƙirga ɗaya zuwa goma, amma zai yi ƙarya idan ya ce ba ya tsoron shirunta.

‘Ɗaya…’

‘Biyu…’

‘Uku…”

Rubutu ya ga ta soma, hakan ya sa shi barin ƙirgar da yake, can kuma ya ga ta daina.

‘Huɗu…’

‘Biyar…’

‘Shida…’

Rubutun ta sake cigaba da shi, tana sake dakatawa bayan wani lokaci.

“Ki kasheni kawai Waheedah.”

Abdulƙadir ya furta a fili, yana jin alamar zufa a goshin shi da bayan wuyan shi.

‘Bakwai…’

Zuwa lokacin hannuwan shi kansu zufa suke fitarwa, shi bai ma taɓa tunanin soyayya da ita ba, yanzun hakan bai san rashin hankalin da ya kaishi yin abinda ya yi ba, bai sani ba, gashi ya zo yana jin bugun zuciyar da bai taɓa tunanin zai iya ji ba ma akan jiran amsarta, Yassar bai tabbatar ba, hasashe yake yi, bai tabbatar da Waheedah na son shi ba, ƙila ma tana da wanda take so, ya yi tunanin yana jin wani tuƙuƙi na tokare mishi maƙoshi.

‘Takwas…’

Ya tura, yana jin yadda zai bar garin Kano da sassafe, yana jin yadda ya yi wa kanshi ƙarya da tunanin amsarta ko rashin amsarta ba zai canza komai ba, da gaske baya tunanin zai iya haɗa idanuwa da ita idan bata amsashi ba. Duk da baya jin yana da na sanin tambayarta ɗin, Yassar ya sa shi son sanin ko tana son shi ko bata son shi.

‘Tara…’

Ya tura yana gyara zaman shi tare da fitar da wani irin numfashi mai nauyin gaske, idanuwan shi ya runtse a hankali ya buɗe su kan screen ɗin wayar.

‘Ina son ka, ina son ka da aure Hamma Abdulƙadir.’

Sake karantawa ya yi yana sauke numfashin da bai san yana riƙe da shi ba. Wayar ya ajiye gefe yana dafe kanshi da hannuwanshi duka biyun, wani irin numfashi yake saukewa mai nauyin gaske, kafin ya miƙe yana zira takalman Yassar da ke bakin ƙofar ya fice daga ɗakin ya nufi hanyar wajen ɓangaren nasu. Takawa yake zuwa ɓangaren Abba yana jin shi kamar wanda yake tafiya a gajimare, jinshi yake kamar yana yawo a wata duniya da ba tashi ba, kamar yana gefe yana kallon wani mafarki da shi a ciki.

*****

Ɗakin Abba ya shiga da sallama, ya same shi a tsakiyar falon a zaune, Mama na kan kujera.

“Abdulƙadir…”

Abba ya faɗi da fara’a yana jin daɗin ganin ɗan nashi.

“Abba…”

Abdulƙadir ya ce yana ƙarasawa ya zauna gefen shi.

“Abba zan yi magana da kai.”

Murmushi Abba ya yi.

“Soja manyan Kjasa, ina saurarenka ai.”

Ɗaga kai Abdulƙadir ya yi yana kallon Mama da ke zaune, yana saka Abba ƙara faɗaɗa murmushin shi, miƙewa Mama ta yi, bata son sake shiga hancin Abdulƙadir ɗin kafin ya tona mata asiri wajen Abba.

“Bari in ba ku waje ku yi sirrin ku.”
Cewar Mama tana ɗora murmushi kan fuskarta, lokacin da ta fice daga ɗakin. Kallon Abba yake yi a nutse ya ce,

“Aure zan yi Abba… Kafin in koma nake so a ɗaura.”

Da mamaki bayyane a fuskar Abba yake kallon Abdulƙadir ɗin, kafin ya numfasa da faɗin,

“Aure Abdulƙadir?”

Kai Abdulƙadir ya ɗaga mishi, yana jin maganganun na fitowa daga zuciyarshi.

“Eh Abba…”

Wannan karon Abba ne ya jinjina kai, maganar na dirar mishi da wani yanayi, yana kuma son karɓarta da buɗaɗɗiyar zuciya, idan har Abdulƙadir ɗin zai buɗe baki da maganar aure to yana ƙoƙarin ganin ya guje wa faɗawa halaka ne, kuma yanzun yana da sana’ar da Abban yake da tabbacin za ta riƙe mishi mata, sai dai shi baya son yin abu cikin gaggawa, musamman magana ta aure.

“Yaushe za ka koma?”

Jim Abdulƙadir ya yi kafin ya amsa,

“Sati biyu in na daɗe.”

Numfashi Abba ya sake saukewa.

“Maganar aure a sati biyu Abdulƙadir, abu ne da ba zance ba zai yiwu ba, amma gaggawa ba abu bane mai kyau. Aure kuma yana buƙatar shiri. Na san kana da aikin da zai riƙe maka mata, amma wajen zama fa? Lefe da sauran hidindimun biki.”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi, shi bai yi wannan tunanin ba kwata-kwata. Ya ma manta ana wani abu wai shi lefe a maganar aure, ya kuma manta ana neman wajen zama. Magana Abba yaci gaba da yi.

“Ana iya maganar auren, idan kana ganin za ka iya shiryawa nan da watanni shidda sai a haɗa da na su Yazid duk ayi…”

Kai Abdulƙadir ya jinjina, hakan ya mishi, zai tara kuɗin da za su ishe shi yin lefe, wajen zama za su iya farawa da barikin sojoji tunda ya san za a bashi muhalli, amma ko kaɗan ba daɗewa zai yi ba, kafin ya tara kuɗin da zai mallaki nashi ne za su zauna. Baya son yaranshi su tashi cikin bariki, ba don wani dalili ba, ra’ayin shi ne kawai hakan. Dariya mai ɗan sauti ya ji ta kubce mishi, ya ɗan girgiza kai. Da gaske ya samu matsala, shi ne da maganar aure har da tunanin rayuwar yaranshi da yadda yake son ta kasance.

“Hakan ya yi Abba… Zan tara kuɗin sai in ba ma Hajja ta siyo abinda ya kamata…”

Murmushi Abba ya yi, Abdulƙadir din ya kalle shi yana faɗin,

“Waheedah ce Abba… Waheedah zan aura.”

Kallon shi Abba yake da mamaki shimfiɗe akan fuskar shi.

“Waheedah? Waheedah ta nan gidan?”

Ya ƙarasa tambayar da alamar rashin yarda a muryarshi da fuskarshi gaba ɗaya. Akance sai halayya ta zo ɗaya ake zama wuri ɗaya ma har a ƙulla alaƙa, Abba na ganin ƙaryar zancen a abinda Abdulƙadir yake faɗa mishi, don ta kowacce fuska Abdulƙadir bai dace da Waheedah ba, halayyarsu da komai nasu ya banbanta, bai kuma hango ta yadda akai suka fara soyayyar ba.

“AbdulKadir ka tabbata? Ita Waheedah ɗin ita ta ce tana sonka?”

Kai Abdulƙadir ya ɗaga wa Abba, inda bata ce tana son shi ba, ba zai taɓa zuwa ya furta ma Abba zancen aurenta ba.

“Allah mai iko… Oh Allah.”

Abba yake faɗi har lokacin da Abdulƙadir ɗin ya miƙe jinjina maganar yake, don kai kawai ya iya ɗaga wa Abdulƙadir ba tare da ya ji ko me yace ba, har ya fice daga ɗakin. Sosai yake jinjina al’amarin auren Waheedah da Abdulƙadir, shi kam zai kira Waheedah ya tabbatar daga wajenta kafin ya yanke kowanne hukunci, don jikin shi na mishi wani iri akan auren, sanyin Waheedah ya yi yawa, zafin Abdulƙadir ko su da suka haife shi addu’a suke binshi da ita, yana ƙaunar su biyun duka, yana jin Waheedah har ƙasan zuciyarshi, zai yi komai don ganin ba a cutar da marainiya da sa hannun shi ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 14Abdulkadir 16 >>

2 thoughts on “Abdulkadir 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×