Skip to content
Part 18 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Minna

Gajiya ta ke ji har a ƙasusuwanta, wannan ne karo na farko a rayuwarta da ta taɓa zuwa wani waje da ya wuce ƙauyen Bugaje. Ji ta yi kamar za su je ƙarshen duniya, kamar tafiyar kwanaki ce a maimakon ta yini ɗaya. Sosai ta gode wa Anty Aisha da ta haɗa mata ruwa mai zafi ta ce ta je ta yi wanka. Sosai ta ɗan ji daɗin jikinta, wasu kayan ta samu an ɗauko mata, doguwar riga ce ta atamfa sabuwa fil, ɗauka ta yi ta saka tukunna ta ɗauki hijabin da ta gani don gabatar da sallar Magriba ta bi da ta Isha’i tunda ta samu tsarki.

Hakan kuwa ta yi, lokacin da ta idar an kawo musu abinci kala-kala a take-away da alama siyowa aka yi. Guda ɗaya aka ajiye mata a gabanta, ta cire hijabin ta ɗora kan gadon da yake ɗakin kenan tana shirin buɗe robar abincin da ke gabanta da bata jin yunwar cin shi ko kaɗan saboda kewar gida da ta ke yi ga kuma gajiya, aka ƙwanƙwasa ɗakin.

“Waye? Shigo…”

Anty Talatu ta amsa, Abdulƙadir ya shigo da sallama, a bakin ƙofar ya yi tsaye yana faɗin,

“Anty sannunku da hidima… Waheedah ɗan zo.”

Wata irin kunya ta ji ta rufeta ganin gaba ɗaya su Anty ne a wajen, har da danginta na wajen uba guda biyu.

“Ki tashi ki je mana.”

Anty Aisha ta faɗi, ƙafafuwanta da matuƙar nauyi ta ja su tana miƙewa, mayafinta da aka fito da shi shima sabo ta ɗauka, sai lokacin Abdulƙadir ya mayar da kanshi yana fita daga ɗakin, ƙafafuwanta babu ƙarfi ta wuce tana fita daga ɗakin, ji ta ke yi kamar idanuwansu na kanta duk da tana ji suka ci gaba da hirarsu kafin ta ja musu ƙofar. Kamar hakan Abdulƙadir yake jira ya kama hannunta yana fara janta.

“Ina za mu je?”

Ta tambaya, juyowa ya yi yana kafeta da idanuwanshi da suka saka ta yin shiru. Sai da ta ga suna shirin nufar hanyar da za ta fita da su daga gidan tukunna ta ce,

“Takalmana Hamma…”

Hannunta ya saki yana kallon ƙafafuwanta, hanyar bedroom ɗin da suka baro ya nufa, tsinin takalmanta yasa shi gane su ne, ya kwaso mata yana dawowa ya ajiye mata su, sakawa ta yi ya sake kama hannunta suka fita. Sai lokacin ta ke ƙarewa barikin sojojin kallo, sai dai saurin da Abdulƙadir yake yi ya sa ta maida hankalinta kanshi tana bin shi kamar wadda aka jona ma batiri. Tafiya suka yi har bakin kofar wajen tana mamakin ganin motar Yassar, don bata san da su da abokan Abdulƙadir ɗin aka zo rako shi ba, hotel suka kama, sun ɗauka rashin son hayaniya yasa Abdulƙadir kama nashi ɗakin daban, kuma nesa da nasu, tun da gidan nashi ɗaki biyu ne kuma su Anty a nan za su kwana suma.

Sai da ya ce wa Hajja a gaya musu kar su zo, kowa ya yi zaman shi ta balbale shi da faɗa kamar ya mata laifi. Ga gidan nan su yi ta kwana, shi kam da matarshi a hotel za su kwana. Bata ce mishi komai ba har suka shiga motar ya ja su, a gajiye ta ke jinta.

“Hamma na gaji wallahi, jikina ciwo yake…”

Ta faɗi ganin har lokacin ba su kai inda za su kai ba.

“Mun kusa…”

Ya faɗi yana shan kwanar da za ta kai shi hotel ɗin, shiga ciki ya yi ya samu waje ya yi parking ɗin motar. Tukunna ya buɗe mata ta fito, a gajiyar da take ji bin Abdulƙadir da yake riƙe da hannunta ta yi duk inda ya yi da ita, har suka ƙarasa bakin wani ɗaki ya buɗe yana jan hannunta suka shiga ya mayar da ƙofar ya rufe. Hannun nata ya sake kamawa ya ja ta kan gadon ya zaunar da ita, takalmanta ta cire tana ƙare wa ɗakin kallo, tana mamakin yadda bata jin tsoro ko ɗar a zuciyarta, sanin Abdulƙadir ɗin ba zai taɓa yin abinda zai cutar da ita ba.

Abinci ta ga ya ɗauko yana faɗin,

“Sakko mu ci…”

Kai ta girgiza mishi a hankali.

“Jikina na min ciwo…”

Gira ya ɗaga mata.

“Shi ne ba za ki ci abinci ba? Sauko kafin ranki ya ɓaci.”

Turo laɓɓanta da har lokacin da sauran janbakin kwalliyar da ta wanke a jiki ta yi tana saukowa, hannu ya sa yana zare mayafin da ta ƙi cirewa ya ajiye shi a gefe ba tare da ya ce mata komai ba. Itama bata yi magana ba ta ɗauki cokalin tana sakawa cikin abincin, tare suka ci , turawa kawai ta yi, ta gode wa Allah da bai mata magana ba. Miƙewa ta ga ya yi ya shiga banɗakin da ke cikin ɗakin, ƙarar ruwa ya tabbatar mata da wanka yake yi, ya jima kafin ya fito. Tanajin wayarshi na ƙara, bata ko motsa daga inda take ba ballantana ta yi ƙoƙarin ɗaga wayar.

Har ya fito ɗaure da towel a ƙugun shi da yasa ta ɗauke idanuwanta daga kanshi, wayar ya ƙaraso ya ɗauka. Anty Talatu ce, hidimar bikin ya sa shi samun lambarta. Ɗagawa ya yi yana faɗin,

“Hello…”

Daga ɗayan ɓangaren ya ji ta ce,

“Ina kuka je Abdulƙadir? Ka san dai kowa ya kwaso gajiya ko? Kwanciya za mu yi ka dawo da ita haka.”

Ƙanƙance idanuwan shi ya yi.

“Ku yi kwanciyarku kawai, za mu kwana a hotel.”

Ya faɗi.

“Hotel?”

Anty Talatu ta maimaita da matuƙar mamaki a muryar ta.

“Hotel fa Abdulƙadir…”

Daƙuna fuska ya yi yana faɗin,

“Sai da safe.”

Ya kashe wayar tashi gaba ɗaya. In ba za su kwanta ba su nemi motar Kano su juya a daren. Ba ya son wani dogon surutu shi yasa ya kashe wayar gaba ɗaya. Towel ɗin ya kwance yana barin gajeran wandon da ke jikinshi ya koma banɗaki ya ajiye. Kan gadon ya ƙarasa yana shirin kwanciya kenan ya ji ana ƙwanƙwasa mishi ɗaki, tashi ya yi ya je ya buɗe ƙofar yana tsayawa a bakinta ganin Yassar na sauke waya daga kunnen shi.

“Ɗaukota ka yi ka kawo nan? Saurin me kake Abdulƙadir?”

Daƙuna wa Yassar fuska ya yi.

“Ina da ikon ɗauko matata in kaita duk in da ya min.”

Ya ba Yassar ɗin da ya dafe kai amsa.

“Abdulƙadir… Oh Allah na, ka tashi ka mayar da ita… Me yasa za ka ɗaukota? Ka san surutun da za ka ja wa Hajja kuwa? Me yasa baka da kunya ne?” Hamma Abdulƙadir ya yi don bacci ne a idanun shi.

“Wallahi ba zan mayar da ita ba, ai na ce wa Hajja kar su zo, kar su zo saboda za a takura ni, za a shiga rayuwata, bata faɗa musu ba. Ni ka bar ni…” Baki a buɗe Yassar yake kallon shi kafin ya ce,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Kallon shi Abdulƙadir yake yi.

“Ka daina yi kamar an yi mutuwa fa… Ba zai sa in mayar da ita ba. Da ka wuce ka kwanta zai fi maka alkhairi…”

Ya ƙarasa maganar yana rufe ƙofar a fuskar Yassar da yake tsaye. Cikin ɗakin ya shigo in da ya samu Waheedah a zaune tana jin duk wata kunyar duniya ta tattarar mata waje ɗaya, bata jin za ta iya komawa gidan nan ta haɗa idanuwa da su Anty. Amma bata san ya za ta yi da Abdulƙadir bane ba. Yanzun ma hannunta ya kama yana miƙarwa ya ɗora kan gadon. Hawa ya yi shi ma yana kai hannu ya kashe musu ƙwan ɗakin, kwanciya yayi yana jan Waheedah ya kwantar da ita kan ƙirjin shi yanajin wata irin nutsuwa na saukar mishi.

Yadda yake jin bugun zuciyarta a ƙirjinshi ya sa murmushi ƙwace mishi.

“Ba ki da hankali Waheedah… Ki yi bacci ni ma bacci zan yi…”

Ya yi maganar yana ƙara gyara mata kwanciya a jikin shi, da gaske yake mata baccin za su yi. Baya jin yin bacci shi kaɗai ne shi yasa yaje ya ɗauko ta, addu’a ya yi tana jinshi ya tofa musu, amma ta kasa ko da runtse idanuwanta ne balle bacci ya ɗauke ta, sai da ta ji numfashin shi ya canza alamar bacci yake da gaske tukunna ta sauke wata irin ajiyar zuciya da bata san tana riƙe da ita ba. Hannunta ɗaya ta ɗora kan ƙirjinshi tana gyara kwanciyar ta, tana gode wa Allah da ya nuna mata zama matar shi.

Kanta ta gyara kan ƙirjinshi, bugun zuciyar shi na nutsar da wani abu a cikin nata ƙirjin har baccin gajiya ya yi gaba da ita.

“Waheedah…”

Abdulƙadir ya sake kira a karo na huɗu, fuskar shi ɗauke da murmushi, bai san kalar gajiyar da ta yi ba, sallar Asuba ma da ya tashe ta kallon shi ta dinga yi kamar ya ƙwace mata wani abu, da ya ja su sallar suka idar, yana kallonta ta ja jiki ta koma kan gado, ko hijab bata cire ba. Yanzun ma hannun shi da yake kan kafaɗarta ta ke turewa tana shagwaɓe mishi fuska.

“Me zan yi?”

Ta tambaya muryarta cike da bacci, har lokacin idanuwanta a rufe suke, murmushi ya yi har haƙoranshi suka fito. Gyara zaman shi ya yi gefenta ya saka hannuwan shi duka biyun ya ɗagota tare da girgiza ta.

“Ki tashi Waheedah…Hamma zai kashe ni in ya dawo ba mu shirya ba, idan muka je gida sai ki yi baccin…”

A hankali ta ke buɗe idanuwan ta, tana jin kanta kamar an ɗora buhun siminti, duk wata gaɓa da ta ke jikinta ciwo take mata, bata taɓa gajiya irin wadda ta yi daga satin bikin zuwa wayewar garin ranar ba. Kallon fuskar Abdulƙadir da yake mata dariya ta yi, tana tunanin in da take kafin komai ya dawo mata.

“Hamma…

Ta kira tana jin kunyar duniya ta tattaru ta rufe ta. Dariya ya yi.

“Ki tashi ki watsa ruwa mu tafi…”

Kai ta ɗaga mishi tana bin hannuwan shi da suke riƙe da ita da kallo, hakan ya sa Abdulƙadir sakinta, ta ɗayan ɓangaren ta ja jikinta ta sauka, kanta a ƙasa ta wuce shi zuwa banɗakin tana rufo ƙofar, wani numfashi da bata san tana riƙe da shi ba ta sauke. Ruwa ta watsa tana mayar da gaba ɗaya kayan da ta shiga da su, tukunna ta fito. Abdulƙadir na zaune in da ta barshi yana danna wayar shi, sai lokacin ta tuno da tata wayar tana gida cikin jaka. Hakan kuma na tuna mata da su Anty Talatu da suka bari da yadda za ta fara haɗa ido da su yanzun.

“Hamma…”

Ta kira cikin tashin hankali, ɗago da idanuwan shi ya yi yana ƙanance su a kanta.

“Ina za mu je?”

Ta buƙata, da mamaki yake kallon ta.

“Gida…”

Ya amsa a taƙaice, kai ta girgiza mishi, tana sa shi ɗaga mata gira cikin alamar tambaya.

“Su Anty na nan, ban san me zan ce musu ba…”

Buɗe baki ya yi da niyyar amsata, ƙwanƙwasa kofar da aka yi ya hana shi.

“Wallahi ba don Waheedah ba da tuni mun tafi…yanzun ma ba zan sake magana ba…”

Yassar ya fadie daga wajen ɗakin, da alamun ranshi a ɓace yake, miƙewa ya yi yana ɗaukar hijab ɗin Waheedah ya ƙarasa inda take tsaye, juya hijab ɗin ya yi zuwa dai-dai tukunna ya juyo da wajen kan yana saka mata, damtsen hannunta daya ya rike yana jinshi kamar kara a cikin hannun shi, gyara mata zaman hijab ɗin ya yi sosai, ya juya ya koma ya ɗauko ɗankwalin kayan nata, hannunta ya sake kamowa ya saka a ciki, kallon shi kawai ta ke yi.

Sadauki su Anty na nan…Don Allah… Ban san me zance musu ba.”

Waheedah ta ke faɗi muryarta a karye, ko inda ta ke Abdulƙadir bai kalla ba, wayarshi da wallet ya ɗauka ya saka a aljihu, ya zo ta gabanta ya wuce, sai da ya zira takalman shi tukunna ya ɗauko mata nata yana ajiyewa a gabanta.

“Hamma…”

Idanuwanshi ya ƙanƙance mata.

“Ki zaɓi abinda za ki ce min guda ɗaya…”

Da sauri ta amsa shi.

“Sadauki…”

Kai ya jinjina mata yana ɗorawa da,

“Ki sa takalmanki, idan Hamma ya yi min faɗa raina zai ɓaci, naki zai ɓaci kema saboda na shirya tun ɗazun ke kike ɓata min lokaci.”

Takalman ta saka, idanuwanta na cika da hawayen da bata san dalilinsu ba. Gaba Abdulƙadir ya yi tana bin bayanshi suka fita daga ɗakin, tsaye ta yi ya kulle ƙofar, kanta a ƙasa yake, ko da ya kama hannunta binshi kawai ta ke yi, inda duk ya cire ƙafarshi nan ta ke saka tata, da ya tsaya ba da mukulli ma a reception, tsayawa ta yi ba tare da ta amsa gaisuwar da matar ta yi mata ba, asali ma ko ɗagowa bata yi ba balle ta ga kalarta, tana tunanin da idanuwan da za ta kalli su Anty Talatu ne.

Har bakin motar Yassar suka ƙarasa, yana tsaye daga waje, addu’a Waheedah ta ke yi kar Yassar ya yi mata magana, shi ma ganin kanta a ƙasa ya sa shi ƙin ce mata komai, Allah ya haɗa ta da wani irin miji da suka yi hannun riga shi da kunya. Shi kanshi Yassar ɗin taya ta jin kunyar abinda Abdulƙadir ya yi yake yi. Wata irin harara Yassar ya watsa ma Abdulƙadir yana faɗin,

“Wallahi da ka ƙara minti biyar da sai dai ku nemi abin hawa…”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi yana amsawa da,

“Na tashi lafiya Hamma, thank you, fatan kai ma ka tashi lafiya?”

Wata hararar Yassar ya watsa mishi don yasan gatse ya yi mishi, zagayawa ya yi ya buɗe motar ya shiga. Sai da Abdulƙadir ya buɗe wa Waheedah bayan motar ta shiga, ya mayar da murfin ya rufe sannan ya shiga gaban, Yassar ya ja motar yana fita daga hotel ɗin zuwa hanyar da yake tunanin za ta mayar da shi barikin su Abdulƙadir ɗin, yana addu’a ya gane hanyar ba sai ya yi magana da Abdulƙadir ba.

*****

Bayan Abdulƙadir ta ke bi har cikin gidan, kanta a ƙasa cike da wata irin kunya da bata taɓa tsintar kanta ciki ba. Jikinta ta ji ya soma ɓari jin Abdulƙadir ya yi Sallama, kuma Anty Talatu ta amsa mishi muryata ɗauke da wani irin yanayi.

“Anty. Sannunku da gida… Ya gajiya?”

Kallon shi Anty Talatu ta ke yi, murmushin takaici mai sauti na ƙwace mata, ba tun yanzun ta san Abdulƙadir ba shi da kunya ba, tun ranar da ta zo gidan aka ce ya mayar da ita, ta yi mishi faɗa kan ya zagi wani saurayi da ya kusan bigewa ya gaya mata maganganu, ta ce ya tsaya ya sauketa, ya kuma yi parking gefe yana jira ta fita. Amma jiya ne ta tabbatar da gaske ba shi da kunya. Yanzun ma yadda yake haɗa idanuwa da ita ya ƙara tabbatar mata da hakan.

“Waheedah ina son magana da ke kafin mu wuce.”

Anty Talatu ta faɗi, tana saka Waheedah ɗago da manyan idanuwanta tana kallonta cike da tsoro, tukunna ta kalli Abdulƙadir da yake gefenta, ɗan ɗaga mata kafaɗu ya yi, yana kallon Anty Talatu da ta juya. m”Anty gaishe ki fa na yi, baki amsani ba kika wuce.”

Abdulƙadir ya ce cike da takaici, don ba kullum yake bata gaisuwar shi ba, yau ma don yana cikin nishaɗi ne shi ya sa ya gaisheta, amma ta wuce bata amsa ba kamar ya mata wani abu. Ko juyowa bata yi ba, hakan yasa shi ƙanƙance idanuwan shi, yana jin yadda ranshi yake gab da ɓaci. Cikin sanyin jiki Waheedah ta wuce ta bayan Abdulƙadir zuwa ɗakin da Anty ta shiga. A tsaye ta sameta, daga bakin ƙofa ta tsaya tana jin idanuwanta sun fara tara hawaye, bata son faɗa, ko kaɗan bata son ta yi wa kowa laifi a rayuwarta. Hankalinta gaba ɗaya a tashe yake.

“Waheedah idan kika biye wa soyayyar namiji za ki sha wahala wallahi, ban ce karki bi mijinki ba, amman ba a kowanne yanayi ba, yanzun ke mutuncinki ne ace darenki na farko a gidan miji kin ɗauki ƙafa kin bishi hotel?”

Kai Waheedah ta girgiza, hawayen da suke cike da idanuwanta suna zubowa, ci gaba da magana Anty za ta yi aka turo ƙofar. Idanuwan shi Abdulƙadir ya sauke kan Anty, ranshi ya gama ɓaci.

“Ki faɗa min Hadisi ɗaya ko ayar da ta ce kar matata ta bi ni hotel…”

Ya ƙarasa maganar yana ci gaba da kallonta, shi yasa ba ya son mutane, saboda irin wannan ra’ayoyin nasu ya sha banban da nashi, idan kuma ana maganar ranshi zai iya ɓaci, bai san matsalar Hausawa da hotel ba, yawancin su suna tunanin babu wanda yake ziyartar wajen sai mazinata, ba sa tuna cewa akwai matafiya da halin kwana ya kama a hanya suka tsaya, akwai wanda aiki ko kasuwancin ‘yan kwanaki ya kai shi, ba shi da zaɓin da ya wuce kama hotel ɗin don ya zame mishi masauki.

Ranshi na ƙara ɓaci da amfi ma duk macen da za a gani a hotel kallon marar tarbiyya, musamman idan aka gansu tare da namijin da zai iya zamowa Yayanta ne tafiyar ta kamasu, ɗakunan da za su kwana mabanbanta ne, ko kuma mijinta ne, kowa za ka gani a hotel yana da dalilin shi na zuwa wajen, ba kuma duka dalilan bane suke zama na banza.

“Kar ka yi min rashin kunya Abdulƙadir…”

Anty Talatu ta yi maganar ranta a ɓace.

“Saboda na nemi ki ba ni hujja kan dalilin da yasa rashin mutunci ne kwanan da muka yi a hotel?”

Miƙewa Anty Talatu ta yi daga zaman da ta yi a bakin gadon tana faɗin,

“Allah ya shirya ya ba da zaman lafiya

Abdulƙadir ɗin ya amsata da,

“Amin…”

Yana matsa mata ta raɓa shi don ta wuce, kafin ta fita ya ɗora da,

“Mun gode Allah ya saka da alkhairi ya mayar da ku gida lafiya.”

Bata amsa shi ba ta fice daga ɗakin, ya mayar da ƙofar ya kulle a bayanta, yana mayar da hankalin shi kan Waheedah da ta ke faman hawaye. Kuka ba ya damun shi sam, ya sha zane Zahra ya zauna ya jirata ta gama kukan da za ta yi su yi magana, kuka marar dalili ne ba ya so, amma wannan da Waheedah ta ke yi har ƙasan zuciyarshi yake jinshi.

“Bana so Waheedah, bana son kuka marar dalili.”

Kallon shi ta yi, wasu hawayen na ƙara zubo mata, tsoro take ji kar Anty Talatu ta faɗa wa Mami ta mata wani abu, Mami za ta mata faɗa ta sani.

“Karta faɗa wa Mami.”

Dariya Abdulƙadir ya yi yana girgiza mata kai.

“Ba ki da hankali ke kam…”

Ya ƙarasa maganar yana kama hannun ƙofar.

“Bari in yi sallama da su Hamma…”

Kai ta ɗaga mishi ta sa hannu ta goge fuskarta, yana fita ta ƙarasa gefen gadon ta zauna. Har lokacin hankalinta ya ƙi kwanciya, ko kaɗan bata son tashin hankali.

Present Day

Ƙwanƙwasa ƙofar da ta ji an yi ya katse mata tunanin da ta ke yi, sallama Hauwa ta yi da Waheedah ta amsa mata cikin sanyin murya, turo ƙofar ta yi tana faɗin,

“Na ɗauka kin yi bacci, Yassar na son magana da ke dama.”

Kai Waheedah ta girgiza mata, ta dafa gado ta miƙe, juyawa Hauwa ta yi, ta bi bayanta, a bakin ƙofar ta samu Yassar ɗin a tsaye.

“Waheedah yanzun Anty ta kira ni, tace za emayar da ke asibiti ashe…”

Numfashi Waheedah ta sauke.

“Don Allah Hamma ku barni da asibitin nan, hutawa suke so in yi kuma zan huta…”

Kallonta Yassar yake, a yanayin da yake ganinta baya so ya takura mata, amma kuma lafiyarta na da muhimmanci.

“Da gaske zan huta… Allah kuwa, idan na ji bana jin daɗi sosai sai mu koma.”

Ta yi maganar cikin son tabbatar mishi, a hankali ya jinjina mata kai.

“Don Allah ko ya Kike ji ki yi magana mu koma, na san ba shiri kuke da Abdulƙadir a yanzun ba, amma zai kashe ni idan wani abu ya sameki ƙarƙashin kulawata.”

Murmushin ƙarfin hali ta yi tana rasa abin da za ta ce mishi.

“Allah ya sauƙaƙa.”

Yassar ya yi maganar cikin sanyin murya, sai da ta amsa shi da,

“Amin…”

Tukunna ta juya ta shiga ɗakin tana turo ƙofar da ta buɗe da sauri tana  fadin,

“Hamma wayata… Tana can, sai kayan su Ikram…”

Kai Yassar ya jinjina mata, ta sake mayar da ƙofar ta rufe. Shi kam hanyar da za ta fitar da shi daga gidan ya nufa yana ce ma Hauwa,

“Bari in dawo ba daɗewa zan yi ba…”

Cike da damuwa ta ke kallon shi.

“Ba ka ci abinci ba har yanzun…”

Murmushi ya yi mata.

“Zan ci da na dawo… Ki ci ke dai…”

Kai ta girgiza mishi.

“Ni dai zan jira ka… Karka daɗe ka ji?”

Numfashi ya sauke yana jinjina mata kai ya wuce, har wajen motar shi ya ƙarasa ya shiga yana nufar gidan Abdulƙadir.

*****

A harabar gidan ya yi parking ɗin motar shi, ba tare da ya fito daga ciki ba ya kira wayar Abdulƙadir ɗin ya faɗa mishi yana cikin gidan. Ko mintina biyar ba a yi ba sai ga Abdulƙadir ɗin ya fito. Da murmushi a fuskar shi yake takawa zuwa wajen motar don a zaton shi Waheedah Yassar ya dawo mishi da ita, ya sani dama, a jikin shi yake ji Waheedah ba za ta iya kwana wani waje yana gari ba, bata taɓa ba, ba kuma za ta fara ba yau. Yana ƙarasawa wajen motar ya kama murfin bayan yana kikiniyar buɗewa, kasancewar gilasan baƙaƙe ne ba ka ganin waye a ciki daga waje.

Ƙasa da gilashin gefen shi Yassar ya yi, ya ziro kai yana faɗin,

“Ka maida hankali ka karya min murfin mota Abdulƙadir…”

Sakin ƙofar ya yi yana matsowa saitin Yassar ɗin.

“Tana ina?”

Cike da rashin fahimta Yassar ya ce,

“Ita wa?”

Daƙuna mishi fuska Abdulƙadir ya yi, yanayin da yasa Yassar ɗin jan ƙaramin tsaki.

“Malam ka wuce ka ɗauko min kayanta da na yara, sai wayarta ta ce tana nan in haɗo mata da su.”

Lokaci ɗaya murnar da Abdulƙadir ɗin yake yi ta ɓace, wani tuƙuƙin ɓacin rai na maye gurbinta, ga yunwar da ke cinshi na ƙara taimakawa wajen rura mishi ɓacin ran.

“Ka ce mata ta zo ta ɗiba da kanta.”

Buɗe motar Yassar ya yi ya fito, shi ma nashi ran yake ji a ɓace.

“Kalleni…”

Ya faɗi yana ɗorawa da,

“Ka kalleni don ubanka. Na yi maka kama da abokin wasan ka? Ko na maka kama da ɗan aike… Karka ƙara ɓata min rai fiye da yadda yake a ɓace…”

Juyawa Abdulƙadir yayi yana nufar hanyar gidan, Yassar ba zai ƙara ɓata mishi rai ba, Waheedah ta gama haɗa mishi zafi. Bin bayan shi Yassar ɗin ya yi yana tsayawa cikin falon, dai-dai fitowar Nuriyya da wando ne a jikinta ko cinyoyinta bai rufe ba tana faɗin,

“Masoyi…”

Da sauri ta yi baya babu shiri ganin Yassar ɗin, Abdulƙadir ko in da take ma bai kalla ba ya wuce hanyar da za ta kaishi ɗakin baccin Waheedah ɗin. Bata ma yi tunanin sa ko abaya ta dawo ta gaishe da Yassar ɗin ba, ta san ya tsaneta kamar sauran ‘yan uwan AbdulKadir din, gara ƙannen shi suna gaishe da ita ciki-ciki. Amma ko wacce irin gaisuwa ta yi wa Yassar ɗin yakan amsata ne da

‘Sannunki.’

Ya mayar da girar ƙasa da ta sama ya haɗe. Yanzun ɗin ma ganinta ya ƙara ɓata mishi rai, ko lokacin da ta ke Kjawance da Waheedah bata yiymishi ba sam, yanzun tsanar da ya yemata ta ƙara linkuwa, yakan so ko yayane ya dinga mata fara’a saboda Abdulƙadir ɗin, amma ya kasa. Ya kai mintina goma a tsaye a wajen kafin Abdulƙadir ɗin ya fito da wata ‘yar jaka da kaya a ciki, kan kujera ya ajiye ya ɗora mishi wayar Waheedah da charger a kai ya juya ba tare da ya ce komai ba. Shi ma ɗauka ya yi ya fice daga gidan.

Ɓangaren Nuriyya in da ya bar tashi wayar ya nufa yana ɗaukar ta ya rikee tukunna ya samu waje ya zauna kan kujera, ƙirga mintunan da yake tunanin za su kai Yassar ɗin gida yake yi, gara yakai ma Waheedah wayar, sai ya kirata ko zai samu ta faɗa mishi dalilin da yasa take son tarwatsa mishi zaman lafiya haka. Nuriyya ce ta fito daga bedroom ɗinta, don ta ji motsin shi, ta san Yassar ya tafi. Kan kujerar ta ƙarasa ta zauna tana jingina jikinta da shi, hannun shi ya zagaya ya riƙo ta, sauƙi yake nema ko ya yake, so yake ta ɗauke mishi hankali daga tunanin da yake don bayaso.

Gefen fuskarta ya sumbata, ta sake narke mishi.

“Jikina namun ciwo…”

Muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Me kika yi?”

Sake kwanciya ta yi a jikinshi, hanyar da za ta guje wa yin girki ta ke nema.

“Me za mu ci da dare? Ko mu sha Tea?”

Tun kafin ta ƙarasa kalmar Tea ɗin yake girgiza mata kai, ana zaune lafiya ba zai sha shayi ya kwanta ba, yunwar da yake ji ma ta fi ƙarfin shayi.

“Wani abu dai banda shayi.”

Shagwaɓe fuska ta yi tana sauke muryarta cike da kissa.

“Kamar me? Ka zaɓi wani abu mai sauƙi.”

Daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi, yanayin na mishi baƙunta, shi fa sam bai saba faɗan abin da zai ci ba, dafawa Waheedah ta ke yi ta kawo mishi.

“Ki dafa komai ma, ni ban saba zaɓan abinci ba, ko me kika ba ni zan ci, amma banda shayi.”

Numfashi ta ja tana saukewa.

“Ko mu fita mu ci a waje?”

Kallonta yayi yana ƙanƙance mata idanuwan shi.

“Saboda me?”

Ya buƙata yana jiran jin dalilin da zaisai su fita waje su ci abinci. Haka kawai tunani ya watsa shi washegarin auren su da Waheedah.

****

“Me za ki ci in siyo mana?”

Ya buƙata bayan tafiyar su Anty, yana kallon yadda ta ke daƙuna mishi fuska tana tambayar shi,

“Muna da abinci a kitchen, me yasa za ka siyo?”

Kafaɗu ya ɗan ɗaga mata.

“Sai an dafa…”

Ya amsa a taƙaice.

“Na sani, amma akwai.”

Kai ya girgiza.

“Amarya bata girki.”

Murmushi ta yi mishi tana miƙewa ta nufi kitchen ɗin, bin ta ya yi. Tare sukai buɗe-buɗen abubuwa a kitchen ɗin har ta gama ɗauko wanda ta ke buƙata, da wani gari da ya gani kamar ya ji, sai dai yafi ya ji ja ya ga ta jiƙa a ruwa, sai tumatir na leda, Macaroni ta yi musu jalof da sauran kajin da aka kawo musu da su Anty ba su cinye ba suka saka mata a fridge. Sosai yaci abincin don ya mishi daɗi.

*****

“Masoyi…”

Nuriyya ta faɗi tana riƙo hannun shi, ganin ya yi shiru kamar yana tunani.

“Ki soya mana ko dankali sai ki mana sauce.”

Ya faɗi da wani nisantaccen yanayi a muryarshi, ranta ta ji ya ɓaci saboda zaman fere dankalin da za ta yi.

“Banda dankali fa, sai dai in siyowa za ka yi.”

Kai ya girgiza mata, ba ya jin fita sam.

“Ki duba kitchen ɗin Wahee… Tana da shi.”

Miƙewa ta yi tana nufar ɓangaren Waheedah ɗin da tunanin yaushe za ta dawo gidan. Don ita ba za ta iya wannan bautar ba sam-sam, rabonta da wani girki har ta manta. Gashi ta kula da Abdulƙadir ɗin na da mugun cin abinci, kuma tana da tabbacin Waheedah ta lalata shi haka. Kwando ta samu ta kwashi dankalin da take tunanin zai ishe su ta koma nata ɓangaren. Ta wuce Abdulƙadir zaune inda ta same shi, wayar Waheedah ya kira a kashe, hakan yasa shi ajiye tashi yana jin ranshi a jagule.

“Masoyi ba za ka zo ka taya ni ba? Da yawa fa dankalin…”

Nuriyya ta faɗi daga bakin ƙofar kitchen ɗin kamar za ta fashe da kuka, gashi bata iya saka peeler ba, dole sai dai da wuƙa.

“Ban iya ferewa ba ni kam.”

Ya yi maganar da iya gaskiyar shi, yakan dami Waheedah da zai taya ta aiki in tana yi, amma banda Maggi bata ba shi komai, sau ɗaya ta ba shi yankan albasa, yajin da ya cika mishi ido yasa har ya yanke hannu, bata ƙara ba, da yayi magana za ta ce ya rufa mata asiri, kafin azo a kamata ta ba Soja aiki ya yanke hannu. Sai dai yakan miƙo mata su cokali ko kwano. Jin Nuriyya bata ƙara mishi magana ba yasa shi zamewa ya kwanta kan kujerar, ya ɗora hannun shi saman goshin shi yana lumshe idanuwan shi.

Baifi minti biyar ba ya buɗe idanuwan shi, sai dai me, yadda tunanin Waheedah ya addabeshi da ya rufe idanuwan hakan ma dayai buɗe su. Tashi zaune ya yi, tunani baƙon abu ne a tare da shi, babu abinda ya isa ya saka shi tunani haka, Waheedah ta sani, ba zai iya kwana bai san matsayar matsalarsu ba. Wayar shi ya ɗauka ya wuce ya ɗauko mukullin mota tukunna ya dawo yana faɗin,

“Nuriyya bari in dubo Waheedah, zan yi sallah a hanya…”

Kai ta ɗaga mishi da ya saka shi daƙuna mata fuska, babu shiri ta ce,

“Tam a dawo lafiya, ka yi mata sannu.”

Nashi kan ya jinjina mata, ita bata isa ta yi mishi ba, tana kuma lura da Waheedah na amsa shi da kai baya ce mata komai, amma ranar farko da ta kwatanta magana ya yi mata, da ta gwada yi mishi shiru ma sai da ya sauke mata masifarshi har kuka ta yi ranar. Akwai abubuwa da yawa da ta ke lura Waheedah kawai take yinsu yana ɗauka, hakan kuma na mata ƙuna har ƙasan ranta. Tana jin takun tafiyar shi har ya ɓace mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 17Abdulkadir 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×