Skip to content
Part 19 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Kamar yadda ya faɗa, a hanya ya tsaya ya yi sallar magriba, sannan ya ƙarasa gidan Yassar. Ya gwada kiran wayar Waheedah bai samu ba, hakan ya sa shi shiga gidan kanshi tsaye tare da yin sallama. Hauwa ta amsa mishi suna gaisawa, Abdulƙadir ɗin ya ɗora da,

“Waheedah fa?”

Ɗan jim ta yi na minti ɗaya, bata san me yake faruwa ba, ba kuma ta son shiga ko ma menene, idan akwai abinda zama da Yassar ya koya mata bai wuce ƙin shiga abinda babu ruwanta a ciki ba. Don haka ta nuna mishi hanyar ɗakin da Waheedah ɗin ta ke ciki, ta ci gaba da hidimar da ta ke yi ta fito musu da abincin dare. Sauri Abdulƙadir yake yi yana gode wa Allah da bai ga Yassar ba, don zai iya cewa ba zai ga Waheedah ɗin ba. Ɗakin ya tura ko sallama bai yi ba yana mayarwa ya rufe.

Tsaye ya ganta ta goya Ikram tana jijjigata, kallon mamaki ta ke mishi, don ta ɗauka ma Fajr ne ya shigo mata ɗaki babu sallama haka, juyowa tayie ta yi mishi faɗa ta ga Abdulƙadir a tsaye. Lumshe idanuwanta ta yi ta buɗe su akan shi tana jiran soyayyar shi da takan ji ta taso mata duk lokacin da zai bayyana a gabanta, amma shiru, babu abinda takee ji banda son ƙara yin nisa da shi.

“Waheedah…”

Ya kira muryar shi na fitowa a karye da ganin nisan da ta yi mishi cikin idanuwanta duk da tana tsaye a gaban shi.

“Ba zan iya bacci ban san me kike so dani ba…”

Murmushi ta yi, kallon ta yake, da gaske murmushi ta yi, shi kam ko kaɗan bai ga abin nishaɗi a yanayin da suke ciki ba.

“Da wane yare kake so in faɗa maka? Na maka da Hausa, in maka da turanci ko da larabci? Su kaɗai na san kana fahimta… Sakina nake so kayie Sadauki, ka faɗa min idan akwai abu mai wahala cikin gane hakan.”

Tabbas ranar ta zo mishi da abubuwa na ban mamaki, Waheedah yake kallo yana son ganin ko da gaske matar shi ce a gabanshi, da gaske Waheedahr shi ce da ko murya bata taɓa ɗaga mishi ba, balle ta tsaya idanuwanta cikin nashi tana gaya mishi magana irin hakan. Ji yake kamar an watsa mishi ruwan sanyi an kunna mishi AC. Jikin shi ba La’asar kawai ya yi ba, Isha’i ya yi makararriya.

“Waheedah?”

Ya iya furtawa yana kallonta, ganin ta ƙi sauke idanuwanta, kuma bata da alamar amsa shi ya sa shi faɗin,

“Nine fa, Waheedah ni ne?”

Kai ta jinjina.

“Na ganka ai… Ka ga na nuna alamar ba kai bane?”

Wannan karon dariyar takaici mai sauti ta kubce mishi.

“Yaushe kika koyi rashin kunya?”

Maganar da ya yi zaton cikin kanshi yayii ta fito fili, sautin muryar shi na dukan kunnen shi da wani yanayi. Kafaɗu ta ɗan ɗaga mishi.

“Zama da maɗaukin kanwa…” Waheedah ta faɗi tana zama gefen gadon.

“Me kike nufi?”

Cewar Abdulƙadir cikin ɓacin rai, kallon shi ta yi wannan karon tana ganin yadda yake gab da birkice mata.

“Karka tasar min da yarinya, Sadauki ba zan iya hayaniya ba, don Allah in ba takarda za ka bani ba ka fita…sa’adda ka shirya bani ka san inda nake.”

Kai kawai ya iya jinjinawa, yana juyawa ya buɗe ƙofar ya fice daga ɗakin, a falo ya samu Yassar da alama lokacin ya shigo.

“Abdulƙadir…”

Ya kira cike da mamaki, ko inda yake Abdulƙadir bai kalla ba, hanyar da za ta fitar da shi daga ɗakin kawai yake nema, saboda yana jin yadda wani agogo yake harbawa cikin kanshi yana mishi kashedin saura ƙiris ya cika, ba ya so lokacin da koma meye ya ɗibar mishi ya cika a cikin mutane, kar a samu matsala. Rabon da ranshi ya ɓaci irin haka har ya manta, don har wani duhu-duhu yake gani. Ganin hakan yasa Yassar ƙara kiran shi.

“Abdulƙadir…”

Gani ya yi ya fice daga ɗakin, babu shiri Yassar ya bi bayanshi, ko takalma bai tsaya ya saka ba. Kafaɗar shi ya dafa yana juyo da shi.

“Magana nake maka.”

Ya faɗi yana yawata idanuwan shi kan fuskar Abdulƙadir ɗin, ba kuma ya son abinda yake gani shimfiɗe akai.

“A haka za ka shiga mota ka yi tuƙi? Saboda ba ka da hankali.”

Numfashi Abdulƙadir ya sauke yana jan hancin shi da yake ji kamar yaji-yaji a ciki, muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Me yasa igiyar aure ta shiga tsakanina da Waheedah? Hamma me yasa?”

Runtse idanuwa Yassar ya yi, cikin alamar rarrashi ya ce,

“Abdulƙadir…”

Kai Abdulƙadir ɗin ya girgiza mishi yana jin kama zai kama da wuta da yadda jikin shi ya ɗauki ɗumi saboda ɓacin rai.

“Na mareta da safe, ban san ya akai ba Hamma, wallahi ban sani ba, amma cikin idona ta kalla ta yi min rashin kunya… Yanzun ta ƙara… Ban san me ya faru ba, ban san me na yi mata haka ba….amma a karo na farko ina jin igiyar auren da ta haɗa mu bata yi min adalci ba. Da ta ba ni damar da zan dake ta yadda raina yake so da ta dawo hayyacinta ta faɗa min me na yi mata sai in san yadda zan yi in gyara…”

Dafe kai Yassar ya yi, bai san abin da ya kamata ya yi ba, a yini ɗaya yana ganin Abdulƙadir ɗin na shirin susucewa, bai san me zai faru in aka ɗauki kwanaki a haka ba, tsintar kanshi ya yi da musu addu’ar samun maslaha su duka biyun, don sun saka shi a tsakiya ta yadda ba zai iya zaɓen ɓangare ba. Motar shi Abdulƙadir ya buɗe tukunna ya sake juyowa.

“Ka faɗa mata, wallahi bata isa ba…wallahi bata isa ta birkita min lissafi ina zaune lafiya ba…idan rigima ta ke so Hamma ka faɗa mata Abdulƙadir ne…ta ga wajen kwanana shi yasa ta raina ni haka…”

Da idanuwa yake bin Abdulƙadir ɗin da kallo, murmushin da bai san ta inda ya taho ba yana shirin ƙwace mishi. Abdulƙadir na kiran Waheedah bata isa ta birkita mishi tunani ba, amma hauka yake tuburan, tsaye ya yi sai da ya ga yadda Abdulƙadir ɗin ya birka mota kamar zai taka shi tukunna ya matsa da sauri. Numfashi Yassar ya sauke, yana hango Abdulƙadir ɗin ya ziro kai ta window ɗin motar ya kalli maigadi da bai buɗe mishi ƙofa da wuri ba, da sauri Yassar ya taka ya ƙarasa kafin ya jibgi yaron mutane a banza.

“Don ƙanwar uwarka ba ka ji ƙarar mota bane halan?”

Abdulƙadir ɗin ya tambaya yana kallon yaron da yake a tsorace, da hannu Yassar ya yi mishi alamar ya matsa, da kanshi ya buɗe wa Abdulƙadir ɗin mota yana faɗin,

“Allah ya tsare samarin Hajja…”

Tsaki Abdulƙadir ya ja.

“Idan na zagekae a fili yanzun za ka ce na maka rashin kunya.”

Wata irin dariya ta kubce wa Yassar ɗin, har Abdulƙadir ɗin ya figi mota Yassar na tsaye ya riƙe gate ɗin yana kwasar dariya, da ƙyar ya samu ya shiga cikin gida, har lokacin da murmushi a fuskar shi, a rayuwar shi bai taɓa hango abinda zai saka Abdulƙadir susucewa a yini dayae haka ba, har Waheedah ɗin da kanta kuwa.

*****

Tana kitchen ɗin har aka kira sallar Magriba, bata miƙe ba sai da ta ƙarasa yanka dankalin tukunna, wanke shi ta yi ta tace a kwando, tana ganin kamar yankan yayi girma, amma ta riga ta gaji, ko bata gaji ba ma ba za ta sake tsayawa yankawa ba, ranta a ɓace ta ke jin shi. Gas ta kunna ta ɗora kasko ta zuba mai a ciki, tunanin ta barbaɗa wa dankalin gishiri bai zo mata ba, man ma ko ɗumi bai yi ba, balle ya yi zafi, ta ɗibi rabin dankalin ta zuba a ciki tukunna ta fice daga kitchen ɗin. Ɗakinta ta wuce tana shigewa banɗaki ta ɗauro alwala ta fito, sallah ta gabatar a nutse, bata tsaya addu’a ba ta tashi ta nufi kitchen ɗin don ganin halin da dankalin ta yake ciki.

Danƙare ta same shi, kasancewar man da ya sha ya yi luntsum, haka ta ci gaba da cakuɗa shi, duk ya kakkarye ya dame cikin man, ya ƙara jagula mata lissafi gaba ɗaya. Bata jin a cikin abubuwan da mata suke yi na zaman aure akwai wanda ya kai girki ɓata lokaci da wahala. Bata taɓa tunanin suyar dankalin za ta yi mata wannan rashin mutuncin ba, barin shi ta yi ya ɗan ƙara yi, tukunna ta kwashe, bata jira man ya tsane ba ta juye a wani kwano da ta ɗauko. Sauran dankalin ta zuba, tana komawa falo ta zauna. Da fitilar wayarta ta ke ta amfani, kasancewar har lokacin ba su dawo da wuta ba. Ga Abdulƙadir ya jima, balle ya zo ya kunna musu generator, ko kallo ta yi ta rage zafi.

Shi ma sauran dankalin haka ta yi ta juya shi duk ya dagargaje mata, ta kwashe tana kallon yadda a ido ma bai yi kyawun gani ba. Gashi sai ta yi wata sauce kuma. Ba don tana tsoron faɗan Abdulƙadir ɗin ba, ƙwai za ta soya su haɗa da shi. Sauran kayan miyar da ta ɗauko kitchen ɗin Waheedah ta fito da shi ta juye a tukunya ta ɗora kan gas. Tukunna ta ɗauko albasa ta fara yankawa, ga yajin albasar da ya cika mata ido, ga kayan miyar da ya fara kamawa, banda tsakinta ba ka jin komai na tashi a kitchen ɗin, sai kuma ƙauri. Albasar ta zuba ciki, tukunna ta zuba mai wajen ludayi takwas, don kusan na kaskon da ta yi suya ne ta kusa juyewa, cakuɗawa ta yi, ta ga kamar ta mata yawa, ta fara saka ludayi tana rage man.

Ganin miyar na ƙara ƙonewa yasa ta kashe gas ɗin.

“Wane irin bala’i ne wannan?”

Ta Yi maganar kamar za ta saka kuka, tunawar da ta yi bata saka maggi ba, guda takwas ta ɗibo ta ɓare, dandanƙa shi ta yi ta zuba a ciki tana cakuɗawa, sai ta ga kamar miyar ta ƙara baƙi. Taɓe baki ta yi, don kanta har ya fara ɗaukar alamar ciwo. Sa’adda ta fito daga kitchen ɗin ana Isha’i, tana da alwalar ta, hakan yasa ta wuce ɗaki, tana idarwa ta fara kiran lambar Abdulƙadir, sau huɗu tana kira bai ɗaga ba. Na biyar ɗin ne ta ji ringing ɗin wayar a cikin gidan ta ɓangaren ta. Hakan yasa ta fito tana ɗora murmushi a fuskar ta.

“Sannu da zuwa…”

Kai kawai Abdulƙadir ya iya ɗaga mata yana zama kan kujera, wayar shi ya ajiye a gefe.

“In zubo mana abinci?”

Da kai ya sake amsata, ta wuce kitchen ɗin, plate ta samu ta juye dankalin a ciki, ta samu ƙaramin wajen zuba miya ta zuba, ta haɗo ta fito, a kan kafet ta ajiye. Tana kallon Abdulƙadir da gaba ɗaya hankalin shi ba a kanta yake ba. Ƙafarshi ta taɓa, ya sauke wani numfashi mai nauyi. Waheedah ba za ta sa shi kin cin abinci ba, bata isa ta ɗaga mishi hankali yana zaune lafiya ba.

“Meye wannan Nuriyya?”

Ya buƙata yana kallon dankalin da ya koma kamar dambu a cikin plate. Zuciyarta ta ji ta doka a cikin ƙirjinta, nan take idanuwanta suka ciko da hawaye. Ranshi Abdulƙadir ya ji ya ƙara ɓaci, in da Waheedah ce ya shigo tana kallon shi za ta gane halin da yake ciki, kuma ko me zai ce mata ba za ta nuna ranta ya ɓaci ba don ta san nashi a ɓace yake, balle ta yi shirin mishi kuka.

“Bana son kukan banza da ba shi da dalili, tambayarki na yi, ki ba ni amsa, meye wannan?”

Hawayen ta ke ƙoƙarin dannewa, amma sosai suke mata barazana. Muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,

“Wallahi ban san ya akayi ya yi haka ba nima…”

Kai Abdulƙadir ya jinjina, ya san ana samun akasi wajen girki, a ranakun da ranshi ba a ɓace yake ba, zai mata uzuri da cewar ɗan Adam baya wuce kuskure, amma yau haushin shi yake son hucewa akan kowa ya samu, ita kaɗai ce kuma a gaban shi.

“Hannu zan saka?”

Ya sake buƙata yana ƙanƙance mata ido, kai ta girgiza mishi da sauri, tana miƙewa ta wuce kitchen ɗin, sai da ta matse ƙwallar da ta taru cikin idanuwanta, tukunna ta ɗauko cokula guda biyu ta dawo, miƙa mishi ta yi ya karɓa, yana sakawa cikin miyar da ya rasa gane wace iri ce, ga man da yake kwance a miyar zai iya ganin fuskar shi in ya leƙa cikinta.

“Me yasa baki saka mana nama ba? Wacce irin miya ce wannan?”

Abdulƙadir ya ƙarasa tambayar yana jujjuya cokalin shi cikin miyar, kafin Nuriyya ta amsa ya sake faɗin,

“Ni sauce na ce ki yi mana, ita Waheedah ta ke yi idan ta soya mana dankali.”

Yau ne karo na farko da Nuriyya ta ji takaicin rashin iya girki a rayuwarta, don shi ne karo na biyu a rana ɗaya da Abdulƙadir ya haday girkin ta dana Waheedah, kishin da ta ke ji kuwa ƙirjinta har zafi yake mata. Shi kuwa sunan Waheedah da ya faɗi yasa ranshi ƙara ɓaci, babu shiri ya ɗibo miyar ya zuba akan dankalin daga gefe yana cakuɗa shi kamar shinkafa ya ɗibo da cokalin ya kai baki, yana jin ƙaurin da ya cika mishi hanci daga cikin bakin nashi. Haɗiyewa ya yi ba tare da ya tauna ba, da ƙyar ya iya cokali huɗu, yunwar da yake tunanin yanajii ya nemeta ya rasa. Miƙewa ya yi kawai, Nuriyya na binshi da ido har ya fice daga falon.

Tsoron kar ya yi mata faɗa yasa bata tambaye shi in da zai je ba. Ita kanta a dole ta ke cin dankalin, sai da ta ji cikinta ya cika tukunna ta kwashe kwanukan ta mayar kitchen, ta dawo ta zauna, jin har lokacin Abdulƙadir bai tashi generator ba yasa ta yi tunanin ko ta kira wayar shi, sai taganta ajiye akan kujera. Salama ta saka wa ranta ta ci gaba da danne-danne wayar da rashin abin kallo ya sa ta. Don ita ba ma’abociyar chatting bace ba, dama karatu ne, nan ta fi ƙwarewa, to duk litattafan da take bi, ba a ɗora sabon cigaba ba.

Abdulƙadir kuwa waje ya fita ya samu waje kan matattakalar shiga gidan ya zauna. Yana kallon farin watan da ya haske harabar gidan, yana kuma ɗaukar tunanin shi ya watsa satin su na biyu da tarewa a gidan shi da Waheedah.

*****

Tunda suka je gida ta samo fina-finai wajen Nabila, da ta gama aiki bata komai sai kallo, da ya tambayeta wane irin film ne ta ce mishi Korean, jiya da ya farka ya ganta tana kallo, da kan shi ya kashe system ɗin, sai da ya zare mata ido da gaske tukunna ta haƙura ta kwanta, da ta shagwaɓe fuska za ta yi mishi kuka. Yau ma aikin kallon ta ke yi da gab yake da haramta shi sai ya bar gidan, tunda ta rage samun lokacin shi. Hidimar shi ya gama yi ya fita sallar isha’i. Fajr na ɗakin shi yana bacci, don shi da anyi Magriba cikin shi ya dauka sai bacci, inba yana jin rigima ba.

A matattakalar shiga gidan ya sameta zaune, jikinta sanye da rigar sanyin shi da ba hannun bane kawai ya yi mata yawa, har da rigar gaba ɗaya, sai dai Waheedah ce, haka take mishi, sai dai ya ga rigunan shi a jikinta, in ya yi magana za ta ce ƙamshin turarukan shi take so, kuma gasu a ajiye. Yakan ce ta fesa ta ajiye mishi rigar shi, dariya ta ke yi kawai.

“Ƙamshin ai ya haɗu da naka…”

Shine amsar ta a lokuta da yawa. Murmushi kawai yakan yi, a duniyar shi gaba ɗaya ita kaɗai ta ke mishi abinda ta ke so, ita kaɗai yake cewa ta yi abu ta maƙale mishi kafaɗa alamar ba za ta yi ba, kuma ya haƙura, wani lokacin ma kai kawai za ta girgiza, idanuwanta na cikowa da hawaye, sai ya ji gaba ɗaya gwiwoyin shi sun yi sanyi.

“Me kike yi a waje?”

Ya buƙata yana ƙarasowa ya zauna kusa da ita. Hancinta da sanyi ya cika ta ja, tukunna ta amsa shi,

“Wata nake kallo.”

Murmushi ya ƙwace mishi mai sauti.

“Wata?”

Ya maimaita cike da alamar tambaya, yana kallon ta, kai ta ɗaga mishi. Gaba daya film ɗin da ta gama kallo ya tafi da imaninta, duk wani abu da akai a film ɗin ta ji tana son yi itama, balle kuma kalar soyayyar da aka zuba. Sai dai akwai haukan da ita kanta ta san ba za ta fara tunkarar Abdulƙadir da shi ba. Shi yasa ta fito ta kalli watan abinta.

“Me yasa za ki fito kallon wata?”

Ya ƙara tambaya har lokacin yana kallon ta, shagwaɓe fuska ta yi.

“Ba a magana fa Sadauki, shiru ake yi a kalli kyan watan… Da ‘yan…Subhanallah…”

Waheedah ta ƙarashe tana miƙewa babu shiri ta fara zazzage skirt ɗin da ke jikinta tana ɗorawa da,

“Cinnaka… Hamma cinnaka wallahi…”

Skirt ɗin ta ke zazzagewa tana murza cinyarta da take da tabbacin cizon da ya manna mata ya wuce biyu. Abdulƙadir ta ke kallo da yake dariya har da riƙe ciki.

“Ba abin dariya bane, da gaske cinnaka ne…”

Kai kawai Abdulƙadir ya iya ɗaga mata saboda dariyar da yake yi, da ƙyar ya iya cewa,

“Sannu… Mu ƙarasa kallon watan…”

Kafin ya rufe baki ta fara girgiza mishi kai, tana murza cinyarta da azaba ta ishe ta.

“Akwai dalilin da yasa ba ma yin wasu abubuwan a Najeriya…”

Wata dariyar Abdulƙadir ya ji ta sake kubce mishi.

“Mu koma ɗaki…”

Waheedah ta faɗi tana wucewa, ya bi bayanta, ƙasa ta zauna kan kafet tana cigaba da murza cinyarta, Abdulƙadir ɗin ya zauna kusa da ita, tare da riƙo hannunta, da murmushi a fuskar shi har lokacin, yanzun ya tabbatar da abinda ta gani a fim ne ta so gwadawa, saboda bata da hankali.

“Ki daina murzawa…”

Hannunta ta ƙwace, ya sake riƙo shi, ya sa ƙarfi wannan karon, skirt ɗin ya kama da ɗayan hannun shi ya ɗaga sama, yana duba inda cinnakan ya cijeta, wajen har ya yi burdi, abinka da farar fata, har ya yi ja. Duk da tausayin ta,da yaji bai hana shi cewa,

“Baki da hankali Waheedah…”

Shiru ta ɗan yi, tana tunanin abinda ta yi, kafin dariya ta kubce mata, ta sa Abdulƙadir ɗin jin wata sabuwar dariyar shi ma, dariya suke kamar babu wani abu da zai iya taɓa farin cikin su.

*****

Yanzun ma dariyar yake yi da sautin ta ya dawo da shi hayyacin shi, yana saka wani abu matsewa a ƙirjin shi, dariyar na dishe mishi, kan shi ya dafe da hannuwa biyu.

“Waheedah….Waheedah karki min haka don Allah… Ki rufa min asiri…”

Yake faɗi shi kaɗai. Bai san iya lokacin da ya ɗauka zaune a wajen ba, kafin sauron da yake ta girbar shi yasa shi miƙewa ya koma cikin gidan, ɗakin Nuriyya ya wuce, ya sameta a kwance, da alamar ta yi bacci, don ta kunna fitilar wayarta ta ɗora akan drawer ɗin gefen gadon. Kayan jikin shi ya rage ya wuce banɗakin ya watsa ruwa. Fitowa ya yi ya saka gajeran wando ya zagaya ta gefen gadon ya hau ya kwanta. Bai fi mintina goma ba ya ja ƙaramin tsaki ya sauko, wayar Nuriyya ya ɗauka ya haska har zuwa falon ya ɗauki tashi wayar.

Anan ya tsaya yana kiran lambar Waheedah, ta kuwa shiga, da alama ta kunna wayar, ɗagawa ta yi, ya numfasa zai magana ta kashe wayar a kunnen shi, tana sa shi dawo da fuskar wayar ya kalla don ya tabbatar da kashe mishi waya ta yi a kunne. Wata irin dariya da bata da alaƙa da nishaɗi ya yi, yana sake dannawa ya kirata, a kashe ya ji wayar. Wata dariyar ya sake yi.

“Zaman lafiya ne ba kya so Waheedah, tashin hankali kike nema da ni shi yasa kika kashe min waya a kunne.”

Ya faɗi yana wucewa ɗaki ya koma ya kwanta, juyi kawai yake yana duba agogon wayar da ya ga kamar ba ya tafiya dai-dai, don ya ƙi yin sauri. Gari yake so ya waye, Asuba a gidan Yassar za ta yi mishi, zai ji dalilin da zai sa ta kashe mishi waya a kunne, bayan ta fi kowa sanin baya so.

*****

Bai samu bacci ba sai bayan sallar Asuba, don yadda ya ga rana haka ya ga dare, da safen ma ciwon kai ne ya saka shi kwanciya. Tun da Waheedah na gidan Yassar babu inda za ta je, in yayi baccin ya tashi sai ya je ya sauke mata. Ba zai ce ga abinda yake faruwa ba, don bacci yake da ya kwana biyu bai samu irin shi ba, ya ji kamar ana taɓa shi, wata irin damƙa ya kai wa hannun Nuriyya da ya sa ta sakin ihu, idanuwan shi da suke cike da bacci ya sauke akan ta, tukunna ya saki hannunta da yake riƙe da shi.

“Masoyi da ka karya ni…”

Ta faɗi a shagwaɓe, kan shi yake ji kamar ana buga ganga a ciki saboda ciwon da yake yi.

“Ki kira sunana in za ki tashe ni daga bacci, karki taɓa ni…”

Kai ta je ɗaga mishi tana murza hannunta.

“Zan fita ne dama…”

Cike da rashin fahimta yake kallonta, hakan yasa ta ɗorawa da,

“Na ce maka zan je wankin kai, tun shekaranjiya…”

Kai ya jinjina mata, don ya manta sun yi maganar, idanuwan shi ya fara lumshewa da alamun shirin komawa bacci ta ce,

“Masoyi….”

Ba tare da ya buɗe idanuwan nashi ba ya amsa ta da faɗin,

“Nuriyya ki duba wallet ɗina ki ɗauki kuɗi, don Allah ki bar ni ni kam.”

Turo laɓɓaanta ta yi tun da ba ganinta yake ba, ya bata kuɗi tun ranar da ta yi maganar, hakan dai ba zai hanata sake ɗauka ba, tunda ya manta.

“Dama in ɗauki motar ka tun da bacci kake, ko za ka fita?”

Ko kaɗan baya son dogon surutu, tsoro ya hana Waheedah koyon tuƙi tun lokacin da ya siyi mota, ba yadda bai yi da ya koya mata ba, ya gaji ya ƙyale ta, Nuriyya kuwa da kanta ta nuna mishi tana son koya, ko sati biyu basu haɗa ba ta fara hawa babban titi, karambanin ta yana burgeshi lokuta da dama. Zai fita da motar shi, in dai Nuriyya ce yasan za ta ɓata lokaci kafin ta dawo, amma bayason yin surutun shi ya sa ya ce mata,

“Allah ya tsare, ki ƙara my n mai… Karki daɗe kuma.”

Murmushi tayi, sai da ta sumbaci fuskar shi tukunna ta zagaya gefen shi tana ɗaukar wallet ɗin shi da ke ajiye kan gado, kuɗin ciki ta ƙirga ta ga dubu bakwai ne, duka ta kwashe tunda ya ce ta ƙara zuba mishi mai. Mayafinta ta ɗauka ta saka, tukunna ta ɗauki mukullin motar ta fice. Ranta ƙal ta ke jin shi, za ta fito a matar hamshaƙin da take jinta, tun daga shigar jikinta, da leshi ne da ya sha ɗinkin doguwar riga zuwa takalman ƙafarta da mayafinta, ta san ta wuce rainin kowa. Gata matar Soja, wanda ta ga dama za ta taka babu abinda zai faru.

Haka ta shiga gidan man da ta fara samu a hanya, sosai ta ƙosa saboda layin da yake gidan man a ranar kamar anayin wata hidimar, duk da watan azumi ya gabato, amma sauran wajen kwanaki takwas, ballantana ace siyayyar azumi ce ta saka garin cunkushewa, danne-dannen waya ta ke yi a cikin motar tana haɗe rai ita kaɗai, ta sauke gilasan motar dama yadda za a fi hangota, tana kuma jin daɗin yadda duk wanda ya kalleta sai ya ƙara kallon ta. Man dubu uku ta zuba, ta ja motar kenan da nufin fita daga gidan man wayarta ta fara ruri, ƙawarta ce da suka yi FCE tare. Bata kashe motar ba ta tsaya amsa wayar, barkewa sukayi da labari, tana faɗa mata auren wata bazawarar ƙawar su da za a yi da kuma kalar shagulgulan da suka tanada.

Honking ta ji an isheta da shi, ta ja ƙaramin tsaki tare da zuro kai ta window ɗin motar, har lokacin bata sauke wayar daga kunnenta ba, a wulaƙance ta ce,

“Idan sauri kake yi, ka juya ka fita ta inda ka shigo mana.”

Shi ma mutumin da ke cikin motar shi ƙirar golf leƙo da kai ya yi.

“Ban gane in juya in fita ba, Hajiya ba ki ga layin da yake bayana bane? Ke ai yakamata ki yi gaba sai ki amsa wayar… Wannan ai rashin tunani ne…”

Buɗe baki Nuriyya ta yi tana kallon shi cike da mamakin kalaman shi da take ɗauka a matsayin tsantsar rainin hankali, tunda can ma ba haƙuri gareta ba, don ko matar babanta sai da ta ce ta ɗauka aure zai sa ta rage faɗa, amma Hausawa kan ce mai hali baya barin halin shi.

“Asma zan kira ki, ina zuwa…”

Ta ƙarasa tana sauke wayar daga kunnenta ta buɗe murfin motar ta fito, zuwa lokacin hankalin mutane da yawa ya fara dawowa kan su, musamman zagin da Nuriyya ta fara sirfawa mutumin, ganin kalar motar da ya fito daga ciki da kuma yadin jikin shi, sam bata kula da su biyu bane, ɗayan babban mutum ne, zai kai shekaru arba’in da biyar ko da ɗoriya ma. Jikin shi sanye da shigar ƙananun kaya, rigar mai dogon hannu. Fuskar shi manne da farin gilashi.

“Hajiya daga cewa ki wuce ki ba mutane wuri su fita za ki fara zagin shi? Kanki ɗaya kuwa?”

A hasale Nuriyya ta mayar da hankalinta kan shi.

“Ko zaka rama mishi ne?”

Jinjina kai mutumin ya yi, ya rufe murfin motar ya zagaya a fusace, hakan yasa ɗayan abokin tafiyar tashi riƙe shi, da sauran mutane ma, har da ma’aikatan gidan man da suke ta ba Nuriyya haƙuri ana so ta wuce ta tafi, amma ina, jinta take matar Soja ce ita, Sojan ma Abdulƙadir, tana da tabbacin babu wanda ya isa ya taɓa a. Mutumin da ake riƙewa kuwa faɗi yake,

“Alhaji Mannir ka sake ni in ci uban yarinyar nan…”

Kafin wani ya kula, hannun Nuriyya ya tashi sama ta kuwa yi nasarar zira shi tana ɗauke mutumin nan da marin da yasa wajen yin shiru na mintuna, kafin a taru a shiga tsakani. Huci kawai take tana girgije-girgije. Wasu mata da su ma suka zo shan mai suka fito daga motar su suna kama Nuriyya ɗin suka janyeta gefe, kuka ta fashe da shi tana faɗin,

“Don sun ganni mace shi ne za su ci min mutunci, wallahi sai na kira mijina… Don ba zan yarda ba.”

Daga gefe mutumin da har lokacin bai daina ƙoƙarin ƙwacewa ba ya ce,

“Ki kira shi fa, don yau ina son ganin uban da ya tsaya miki a faɗin garin Kano da ƙetaren ta…”

Sosai mutane suke ƙoƙarin bashi haƙuri, don ɗayan abokin tafiyar da ya kira da Alhaji Mannir ne ya samu ya fitar musu da motar su sukayi parking daga can gefe suka tsaya. Duk da mutane da suke basu haƙurin cewa su tafi, kafin rigimar ta yi nisa, tunda da alama Nuriyya ɗin matar wani babban ce shi yasa ta ja rigimar. Ita kuwa Nuriyya Abdulƙadir ta kira tana saka mishi kuka cewar wasu sun ci mutuncinta a gidan mai. Sai da ta faɗa mishi sunan gidan man ta kuma ji ya ce mata ta jirashi, tukunna ta kashe wayar ta koma gefe tana matse hawaye.

Mutanen gmwurin kowa da abinda yake faɗa, wanda ba a fara rigimar a gabansu ba suna tambayar me ya faru, da yawa da aka fara a gabansu kuma suna tir da hali irin na Nuriyya ɗin, wasu ma tafiya suka yi, da yawa kuma sun ma sha man, amma suna tsaye don ganin ƙarshen rikicin.

*****

Gajeran wando ya saka, ya ɗauki farar riga ya ɗora, wayar shi ya saka a aljihu ya ɗauki wallet ɗin shi, dubawa ya yi ya ga babu kuɗi a ciki, bazai iya tsayawa ATM ba, ran shi in ya yi dubu a ɓace kowanne yake, tun jiya yake neman inda zai huce haushin da yake ji, bai samu ba. Sai yanzun da Nuriyya ta katse mishi baccin da yake yi, ga yunwar da yake ji har hanjin shi ƙullewa yake. Fitowa ya yi ya wuce ɗakin Waheedah. Cikin jakunkunan ta ya ɗauko ya duba, ɗari biyar ya ɗauka a ciki ya saka a aljihu yana ficewa.

Mai babur ya tara zuwa gidan man, jikin shi har ɓari yake yi da ya ƙarasa ya samu wanda zai jibga, ko canji bai tsaya karɓa ba, ya shiga cikin gidan man, inda ta ke yake nema, kafin ya hango motar shi, da kuma Nuriyyar da ta ke jingine a jiki. Har yayi hanyar ya hango kamar Major M. Alƙali a tsaye jikin wata golf, sake dubawa ya yi kuwa, shi ɗin ne, don sun yi aiki tare a Lagos. Mutum ne shi da matsayin shi da kakin shi bai taɓa sa ya wulaƙanta kowa ba, duk da yana da zafi in an taɓa shi, kuma yana cikin sojojin da Abdulƙadir ya sani da suka tsani wanda yake amfani da kakin shi ya ci zarafin mutane.

Fasa ƙarasawa ya yi inda Nuriyya take, sai da ya ƙarasa can wajen shi yana kai gaisuwa, amsawa ya yi bai ma iya tambayar Abdulƙadir ɗin abinda yake a gidan man ba. Ganin kamar ran shi a ɓace yake yasa Abdulƙadir ɗin yi mishi sallama yana takawa ya ƙarasa wajen Nuriyya da ta fara fifita fuskarta da mayafin jikinta tun daga lokacin da ta hango Abdulƙadir ɗin ya ƙarasa ya sarawa mutumin da ta wanke da mari. Hawayen ne wani na bin wani yake saukar mata.

“Ki daina kuka… Su waye? Waye ya taɓa ki?”

Abdulƙadir yake tambaya, sai dai ta kasa amsa shi, kuka take kamar za ta shiɗe mishi, baki ya buɗe zai sake magana, kamar daga sama ya ji muryar Major M. Alƙali yana faɗin,

“Matarka ce ta wanke ni da mari kenan? Shi ne ta kira ka ka zo ka yi amfani da kakinka ka ci min mutunci…”

Cikin tashin hankali Abdulƙadir ya juya yana kallon Major, kafin ya juyo ya kalli Nuriyya da ta ja mishi bala’in da bai san ta inda zai fara fita daga cikin shi ba.

“Nuriyya…”

Ya kira muryar shi ɗauke da wani yanayi. Kuka take tana girgiza mishi kai, don ita kanta bata san kalar tashin hankalin da zai biyo baya ba kenan, da ta san Soja ne, Sojan ma da alama ya yi wa mijinta fintinkau da bata fara tsayawa ba, tun sanda ake cewa ta tafi, da lokacin ta shiga motarta ta wuce.

“Mu je ko…”

Major ya faɗi yana kallon Abdulƙadir. Shi kuma ya kalli Nuriyya kafin ya bi bayan Major ɗin, da sauri Nuriyya ta ke shirin bin bayansu, wani irin kallo Abdulƙadir ya watsa mata da ya sa ta jin gaba ɗaya kayan cikinta na yamutsawa, idanuwanta cike taf da sababbin hawaye ta ke kallon su, har suka ƙarasa wajen golf ɗin su Major da ta raina har ta yi musu ɗibar albarka, boot ɗin motar ta ga ya buɗe, Abdulƙadir ya shiga ya kwanta, ya kuma mayar da murfin ya rufe, suna shirin shiga su tafi. Ai bata san lokacin da ta kwasa da gudu ta yi wajen su tana faɗin,

“Ina za ku kai shi? Ina za ka tafi min da miji? Ka rufa min asiri, don Allah ka yi haƙuri… Ka rama marinka ka ƙyale min miji.”

Wani irin kallo Major ya watsa mata.

“Marin zai fita a jikin mijinki, karki damu.”

Ya buɗe motar ya shiga, suka wuce suna barin Nuriyya nan tsaye ta ɗora hannunta saman kai tana faɗin,

“Na shiga uku na…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 18Abdulkadir 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×