Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Sha Uku

4.5
(2)

<< Previous

“Mutumin da kike so na tare da uniform ɗin nan, ban san waye ni ba tare dasu ba, ban taɓa son kaina babu su ba, bana tunanin za ki iya.”

Kai ta girgiza mishi, hawaye ne cike da idanuwanta amma sun ƙi zuba, in haka masu ciwon zuciya suke ji za su kasance cikin addu’arta a ko da yaushe, saboda ciwo ne mai matuƙar raɗaɗi.

“Ba soyayyar nake tsoro ba Sadauki, ba miƙa maka dukkan zuciyata bane yake min wahala, rashin tabbacin ka a rayuwa ta ne, ba zan damu da raba soyayyarka da uniform ɗinka ba, shi ɗin da ya fi ni muhimmanci ne matsalar.”

Ta ƙarasa maganar tana jin ɗacin son kan da ta ke son yi a harshen ta, zaɓi take ba shi, ita da take baƙuwa a rayuwar shi ko uniform ɗinshi da ya girma da soyayyar shi? Tana jin idanuwan shi na yawo a fuskarta cike da son ta ɗago nata su sauka cikin su, amma ta ƙi yarda hakan ya faru.

“Waheeda…”

Ya kira sunanta, yana jan haruffan cikin sigar da shi kaɗai yake iya hakan.

“Karki ce min in zaɓa… Ba za ki so amsar ba.”

Runtse idanuwanta ta yi tana buɗe su da wani irin ciwo. Me yasa ya ƙi ganin abubuwan da ta sadaukar saboda soyayyar shi.

“Duk abinda kike tunanin kin sadaukar saboda soyayyata bai kai uniform ɗina muhimmanci ba…karki so kanki da yawa haka.”

*****

“Adda! Addaa!!”

Idanuwanta da ta ke ji sun mata nauyi ta buɗe, tana jin Amatullah ta kwashe da dariyar da ta sa ta jan ƙaramin tsaki, don mafarki take yi, kamar yadda a kwanakin nan mafarkan Abdulƙadir ɗin suke addabarta. A cikin ɗaya daga mafarkan ta kira shi da Sadauki, tun bayan tashin ta tsinci kanta da kiran shi Sadaukin don sunan ya dace da shi ta kowane fanni. Bata san murmushi ya ƙwace mata ba sai da ta ji Amatullah ta sake kwashewa da dariya.

“Addaaaaa!”

Harararta Waheedah ta yi da yasa Amatullah ɗin sake yin dariya.

“Jiba inda kike bacci fa, cikin kaya.”

Miƙa Waheedah ta yi tare da yin hamma tana miƙa hannu ta ɗauki wayarta ƙirar Nokia Symbian E5 da ke ajiye a gefe ta danna don ta duba lokaci, ƙarfe biyu har da kwata. Gaba ɗaya jikinta a gajiye ta ke jinshi.

“Anata nemanki fa…”

Kai Waheedah ta ɗaga wa Amatullah ɗin, tana kallo ta fice daga ɗakin. Zaune ta yi a wajen tana tunanin ta inda zata fara miƙewa, gajiyar da take ji har cikin tsoka da ƙasusuwan jikinta. Idanuwa ta lumshe, fuskar Abdulƙadir na mata yawo, wata irin kewar shi ta ke ji ta ban mamaki, za ta alaƙanta hakan da jimawa da ta yi ba ta ganshi ba, tun hutun da ya zo na sallah, shi ma ranar idi ne, tun da suka dawo daga masallacin idi ba ta sake sakashi a idanuwanta ba har ya tafi. Satin da zata fara zuwa makaranta, Babban Yaya ya basu wayoyi, taga cikin mazan gidan ma kusan duk ya ba ‘yan matasan. Matanne yace sai sun gama aji shida.

Sosai ta ji daɗin kyautar wayar har ranta. Yassar ya saka mata manhajar kafofin sada zumunta, ciki harda Whatsapp, har kati Yassar ɗin ya saka mata. Lambar Abdulƙadir ce ta farko da tazo sakawa taga Yassar duk ya saka mata lambobin su. Sunan kawai ta sake zuwa Sadauki. Shi kuma ta fara dubawa a whatsapp, sai lambar ta nuna ba ya yi. Sosai zuciyarta ta ji ta yi mata nauyi, lambar Yazid ta nema taga Yassar ya saka mata, shi kuwa yana Whatsapp. Sallama ta yi mishi tana faɗa mishi itace. Shi ma ta yi kewar shi ba kaɗan ba. Za ta iya cewa shi ma tun bayan Sallah da canjin wajen aiki ya ɗauke shi zuwa Abuja.

Sai kwanaki da aka ce mata ya shigo, ita kuma ta je gidan ƙanwar mahaifinta, kuma ba sosai take kwana ba, ranar dai rabon ba za ta haɗu da shi bane yasa ta kwana ɗin, ta ji takaicin abin. Ta kuma yi mamakin da Yazid bai je can ɗin ya sameta sun gaisa ba, Yazid ɗin da ta sani zai nemeta, ba zai zo Kano bayan watanni masu yawa ya koma ba su gaisa ba. Sai dai Zahra ta ce mata da Asuba ya wuce, a cewar shi ayyuka sun mishi yawa. Abdulƙadir ɗin kuwa text ta yi mishi tana faɗa mishi ita ce, tukunna ta sake tura mishi wani tana tambayar lafiyar shi. Kasa haƙura ta yi duk da bai amsa mata sauran saƙonin ba, ta tura mishi wani tana cewa ba ta ganshi a Whatsapp ba, ya buɗe.

Bata samu amsa ba sai bayan kwana wajen biyar tsakani, a kwanaki duk lokacin da ta samu tana duba wayar ta ga ko ya amsata batai gani bane. Sosai zuciyarta ta matse lokacin da take dubawa. Ba wata doguwar amsa bace. ‘Na buɗe’ kawai ya tura mata a taƙaice. Amma zuciyarta ta mata wani irin sanyi. Tun lokacin suke magana ta WhatsApp ɗin, ko ta ce take mishi magana, don tana iya tura mishi saƙonni sama da ashirin bai amsata ba, lokuta da dama za ta ga ya buɗe ya karanta. Amsawar ce takan mishi wahala. Bai dameta ba a lokacin, har zuwa yanzun kuma ba ya damunta. Saboda ba shi yake son magana da ita ba, ita ce ta ke son magana da shi.

Indai ya gani ya karanta, har ƙasan ranta ya wadace ta, duk rana za ta ba shi labarai kala-kala, abinda akai a makarantar su, me ta yi a ranar, me ya faru da ‘yan gida. Wani lokacin zai karanta ya turo mata Emoji ɗin murmushi, ranar da ta wuni ba ta yi mishi magana ba zai sake turo mata da Emoji, idan ya ga ta jima ba ta amsa shi ba zai kira sunanta. Zata rantse akwai yanayin yadda yake rubuta sunan da takan gane idan a gajiye yake ranar, idan ranshi a ɓace yake, ko idan yana jin faɗan shi. Takan yi murmushi a dukkan yanayoyin tukunna ta ba shi labari kamar ko da yaushe.

Ba ta taɓa gwada kiran shi ba ko sau ɗaya. Takan tura mishi voice notes a whatsapp, a ƙasan zuciyarta tana fatan shi ma zai fahimci tana kewar muryar shi ya tura mata. Hakan bai taɓa faruwa ba. Sai dai lokacin da ta yi wani zazzaɓi mai zafi, ta kwana biyu ba ta ko samu ƙarfin duba waya ba. Kuma ranar da ta duba ɗin ba ta da katin da za ta siya data ta duba whatsapp ɗin. Har washegari, tana kwance a ɗaki ya kirata, tana ɗagawa ta kara a kunne, kafin ta ce wani abu muryar shi ta daki kunnenta.

“Me ya sameki?”

Lumshe idanuwanta ta yi, muryar shi na nutsar da wani abu cikin ƙirjinta da ba ta san a tashe yake ba. Kafin ta amsa ya ɗora da,

“Me yasa ba za ki faɗa min kina wani abu ba?”

Murmushi ta yi.

“Hamma…”

Bai bari ta ƙarasa ɗin ba ya ce,

“Karki sake min haka, bana so Waheedah.”

Numfashi ta sauke a kunnen shi.

“Ba ni da lafiya ne Hamma.”

Ya kai daƙiƙa talatin kafin ya sake magana cikin wata irin murya da ta dinga shigarta har kwanya. Duk da hirar ba ta yi tsayi ba ta yi mata daɗi. Satin sai da ya jera kullum sai ya kirata yana jin ya jikinta. Da za ta iya mishi ƙarya za ta ce ba ta warke ba don ya ci gaba da kira. Amma ba za ta iya ba, daga lokacin kuma idan har ya kirata to ta dawo makaranta a gajiye tana ba shi labari ta ce kanta na ciwo, yana kira yace mata ta sha magani ta kashe waya ta kwanta. Amma ba zai amsa maganar tata a whatsapp ba. Mutane da yawa za su yi mamakin bauɗaɗɗen halin shi, ita kam babu wani abu a tattare da shi da bai mata ba, ko yake ba ta mamaki.

Numfashi ta sauke ta samu ta miƙe da ƙyar, don in ta zauna tunane-tunane ba tashi za ta yi ba. Kayan da ta zo ɗauka ta saka cikin wata ‘yar jakar biki da aka ba Mami wajen Walima, ta ɗauka. Ficewa ta yi daga ɗakin, ta ci karo da Mami a falo.

“Ba dai tun shigowar da kika yi ba?”

Kai Waheedah ta langaɓar.

“Wallahi Mami jikina ciwo yake… A gajiye nake jina.”

‘Yar dariya Mami ta yi.

“Ai dole, tunda ku ne ƙirjin biki.”

Dariyar ita ma Waheedah ta yi, tana faɗin,

“ƙirjin biki kam na shan wahala Mami.”

Ta ƙarasa maganar tana ficewa daga ɗakin. Gidan su Nuriyya ta shiga da yake cike da mutane, tana samun Mama ta ba ta kayan da ta ɗauko. Tukunna ta sake komawa gidan nasu, wannan karon ɓangaren Anty. Tana shiga ɗakin da sallama. Idanuwanta na sauka kan Nuriyya da ake wa ƙunshi.

“Wai har yanzun ba a gama ba?”

Waheedah ta faɗi tana ƙarasawa ta samu waje ta zauna. Nuriyyar ba ta amsata ba, ko ɗagowa ba ta yi ba ma. Ba ta tsammaci amsa ba, ita kanta zuciyarta ta mata wani irin nauyi, don zata ce ita kaɗai tasan halin da aminiyarta take ciki. Don a watannin nan biyu yadda take tashi ta gabatar da sallolin dare kan matsalar Nuriyya, ko ita da Nuriyyar ba ta tashi ta yi addu’a kan matsalar irin haka.

Watannin su shidda da fara zuwa makaranta dukkan su, sun yi jarabawar zango na farko a cikin biyun da yake a shekara ɗaya. Don Nuriyya ma ta riga Waheedah gama jarabawarta ta farko. Duk da lokacin wata irin wayewa taban mamaki ta shigi Nuriyyar. Wasu irin samari take tarawa da Waheedah ba ta san daga inda ta kwasosu ba. Ko wayar hannunta Nokia C2, ɗaya daga cikin samarin da ta yi ne ya kawo mata. A gida ta yi karyar cewar Anas ne. Waheedah kawai ta san asalin gaskiya, har faɗa suka yi akan wayar. Don Waheedah ta ga rashin kyautawar abinda Nuriyyar take yi.

Kowa yasanta da Anas, duk da tana tare da shi ne har lokacin saboda yadda yake wahala da ita. Ta yi wasu samarin da suka fi shi kuɗi, kyau, da komai, amma a cikinsu babu wanda yake ɗawainiyar da Anas ɗin yake mata, shi yasa ta kasa rabuwa da shi. Duk da ya dameta da maganar aure, hakan yasa ta yi kuskuren cewa ya gaida mahaifinta. Ta san Baba ya san da Anas, don Mama kan nuna mishi in ya siya mata kaya, ko ya kawo musu wani abin. Yakan yi hakan, idan lokacin doya ne ko dankalin Hausa, da yawa yake siyowa ya kawo musu, haka kayan marmari.

Baba ya fara mata faɗa kan tara samari, duk da tsoron shi da take kamar ranta, don Baba ba ya wasa. Tsayayyen mutum ne, bai hanata cigaba da tara samarin ba, sai dai takan ce su zo da yamma idan Baba baya nan. Tashin hankalin duniyarta ya farane ranar da Baba ya zo ya sameta da wani ɗan makarantar su, da sai ya yi magana ne zaka san Bahaushe ne, idan ka ji sunan shi kasan musulmine saboda yanayin shigar shi da kuma askin da yake kanshi. Ranar dukanta ne kawai Baba bai yi ba saboda faɗa. A ranar ne kuma yace ta yi wa Anas magana idan da gaske yake ya turo.

Tsaye duniyar ta yi mata waje ɗaya, saboda ko kaɗan Anas baya cikin tsarin mazan da take son aure, a rikice ta wuni ranar tana jiran Magriba ta yi, Anas ya zo ta ba shi haƙuri ta gaya mishi ba za ta aure shiba, kafin ya jaza mata masifa. Magriba na yi kuwa sai gashi ya zo, sai dai ba ta samu damar faɗa mishi ba, Baba ya fito ya same su yana gaya mata ta koma cikin gida. Da kanshi ya yi wa Anas ɗin magana. Abu kamar wasa washegari sai ga dangin Baban Anas ɗin a gidansu aka tsayar da magana aka kuma saka biki wata uku kacal. Don shi dama a shirye yake.

Baba kuma yana ɗan tanadi, tunda yasan auren Nuriyyan zai iya zuwa kowanne lokaci, duk abinda ya samo yakan ba Mama ta ajiye, ita kuma adashi ta shiga irin na talakawa don a taru a rufa wa kai asiri. Har da Abba aka karɓi kayan sa ranar Nuriyyan aka kuma tsaida magana. Babu kalar tashin hankalin da bai faru a watannin ba, da kukan ta shaɓe-shaɓe, da duk yadda take tsoron Baba ta same shi tana tsugunnawa kan gwiwoyinta akan cewar ita ba ta son Anas. Baba ya ce ta makara, don shi ba zai zama ƙaramin mutum ba, idan ba ta son shi me yasa tasa ya je ya gaishe shi. Me yasa ta dinga karɓar mishi kaya?

Tabbatar mata Baba yayi idan an fasa auren sai dai idan shi ne ya kwanta dama, ko Anas ya zo gidan da kanshi ya ce ya fasa aurenta. Tun daga ranar tashin hankalinta ya fara, a watannin babu kalar wulaƙancin da bata yi wa Anas, duk da har faɗa mata ya yi za ta cigaba da karatunta, shi zai yi ƙoƙari ya biya mata komai, duk dan hankalinta ya kwanta. Amma kamar duk wani abu da zai yi don kyautata mata yana ƙara tunzurata ne. Haka za su zauna ita da Waheedah su sha kuka. Ita kanta Waheedah ɗin sai da ta yi zuru-zuru a ‘yan lokutan.

Tayi-tayi da Nuriyya ta kwantar da hankalinta, ta ci gaba da addu’a, bata san abinda Allah ya ɓoye a auren ba, amman taƙi. Kullum Anas cikin kiran Waheedah yake ya kawo mata ƙarar Nuriyyan, amma ko maganar takan kasa yi wa Nuriyya saboda halin da take ciki. Abin har ya fara ba wa Waheedah tsoro don wayar ƙarshe kan ƙarar Nuriyya da Anas ya kawo mata, maganganun shi sun tsaya mata.

‘Nima akwai zuciya a ƙirjina Waheedah, nima na iya fushi. Wulaƙancin da Nuriyya ta yii min jiya yasa na ji kamar in samu Baba a fasa auren nan. Sai dai kinsan me? Wallahi bata isa ba, bata isa ta mayar da ni ɗan iska ba, har gardama na yi da Mamana akanta da ta ce min ita auren bai kwanta mata ba. Ta haƙura sabo da na nuna mata bazan iya barin Nuriyya ba. Zaman wulaƙancin take so mu yi aiko? Ki faɗa mata a shirye nake da ita, wanda duk ya gaji sai ya sauko a yi zaman lafiya. Amma ko za ta mutu sai an ɗaura auren nan.’

Sosai maganganun shi suke ma Waheedah yawo, bata gani ba, amma takan karanta wulaƙancin ɗa namiji a litattafan Hausa, takan kuma gani a fina-finai. Shi yasa take guje wa wulaƙanta mutane ko yaya suke kuwa. Musulunci ma ya yi hani da hakan, duk mazan da kan bita a makaranta takan faɗa musu an mata miji, don bata son fara abinda ba za ta iya ƙarasawa ba. Tana jin yadda bata da wani wajen saka kowa a zuciyarta, Abdulƙadir ya cike ko’ina.

“Ina son shi Nuriyya, ina son Hamma, wani irin so da bana tunanin inda zai kai ni, saboda ban san ko zuciyar shi zata doka min yadda tawa take doka mishi ba, amma ina son shi, ban damu ko zai so ni ba shi ma…”

Dariya Nuriyyar ta yi mata lokacin tana tambayarta ko a fim ɗin Hausa ta ji kalaman, to a watannin nan ma sam bata ma Nuriyya zancen Abdulƙadir ɗin. Don hankalinsu ba a kwance yake ba. Tunda satin bikin ya kama, Nuriyyar ma ta yi wani irin sanyi na ban mamaki, ko magana bata yi sosai. Kamu kaɗai za su yi washegarin ranar juma’a, ran asabar a ɗaura aure tare da yinin biki, ƙawayensu na Islamiyya duk sun zo, har da Ƙawayen Nuriyya na FCE ɗinsu duk sun zo suma yin lallen da Anty ce ta ɗauki nauyin shi. Abba kam Allah kaɗai ya san me ya yi musu, don da ta shiga gidan Mama na mata godiya sosai.

Mami ta siyi kayan kitchen masu yawan gaske, tunda aka saka ranar take siya tana ajiyewa a hankali a hankali. Duk da a yanayin da auren ya zo na Nuriyya bai hana Waheedah jin daɗin yadda danginta suka hidima wa aNuriyyar ba. Kusan duka hidimar bikin Waheedah ce tsaye akai. Daga kan ɗinkunan da Nuriyya za ta saka, ita ce mai zirga-zirga wajen tela, haka sauran hidindimun da za a yi. Tunda satin ya kama kuma rabon da su yi magana da Abdulƙadir. Har wayar shi ta kira a karo na farko, ta ji ta a kashe. Duk saƙonnin da ta tura mishi a whatsapp ba su je ba. Tana faɗa mishi hidimar bikin da suke yi.

Yanzun ma Whatsapp ɗin ta sake buɗewa ta na bashi labarin zirga-zirgar da ta yi, da ƙunshin da za a yi musu, da yadda take tunanin zaman ƙunshin. Sai da ta ajiye wayar tukunna take tunanin sai da satin bikin ya kama tukunna take faɗa mishi. Yazid ne ta faɗa wa da suka gaisa kamar yadda sukan yi lokaci zuwa lokaci. Sai ta ga kamar Abdulƙadir ɗin. A ƙasan zuciyarta take addu’ar Allah yasa lafiyar shi, shirun nashi ya fara mata yawa, inda tana ganin saƙonninta sun tafi ya karanta, tasan yana lafiya, amsata ne kawai bai yi ba.

Ƙunshin aka yi mata itama, suna ɗan hira da ƙawayen Nuriyya, don ita ta lafe a gefe ɗaya tana kallon ƙunshin da ke hannunta, tana jin kamar bata cikin gangar jikinta, kamar ruhinta ya fita daga jikin ya koma gefe yana kallon abinda yake faruwa da ita, abin yana mata kamar mugun mafarkin da za ta iya farkawa daga shi kowanne lokaci. Bata hango ma kanta auren Anas ba ko na minti ɗaya, in da ta san hakan zai faru da ta jima da sallamar shi ta haƙura da kwaɗayin hidimar da yake mata. Ta san Baba fiye da kowa, idan ba mutuwa ta yi ba ba za a fasa auren ba. Amma tana jin da gaske mutuwar za ta yi idan aka ɗaura auren.

Ba za ta iya zama da Anas ba, bata hango rayuwar aure da shi ba, ko bikinta ba haka ta hasasoshi ba. Saboda ta hango auren hamshaƙin mai kuɗi, biki irin na alfarma, gida tanƙameme da iyayenta ba za su yi tunanin kayan ɗaki ba. Duk da ta ji Baba na faɗa wa Mama cewar Abban su Waheedah ya siyi kayan ɗaki, katifa kawai za su siya. Tana kuma da tabbacin masu kyau ne, za a saka mata kayanta a gidan da bai cancanta ba. Gyara zama Nuriyya ta sake yi, sosai take jin abin kamar a mafarki. Waheedah da take ta hira da ƙawayenta suna dariya take kallo, tana jin wani nauyi a ƙirjinta.

Yadda ƙawayenta na FCE da basu taɓa ganin Waheedah ba suke zancenta ya yi mata zafi, yadda take shiga zuciyar duk wanda ya ganta lokaci ɗaya na tsaya wa Nuriyya a maƙoshi. Yanzun yadda take dariya na ƙara haɗa mata zafi, babu abinda take tunani sai kanta, da za a ɗaureta a auren Anas cikin kwanaki biyu, Waheedah za ta ci gaba da hidimarta babu nauyin auren kowane talaka akanta. Za ta iya samun mai kuɗi ta aura, ƙarshen abinda take so ya faru kenan. Za ta ƙarasa mutuwa idan Waheedah ta samu Abdulƙadir, shi yasa take addu’ar kar ya taɓa kallon Waheedah ɗin da wannan niyyar.

Ba zai taɓa yiwuwa a liƙa mata auren Anas, Waheedah kuma ta samu Abdulƙadir ba. Sai dai ko bata same shi ba, ta san za ta samu wani wanda ya fi Anas ɗin kuɗi, za ta samu abinda ita bata samu ba kamar ko da yaushe. Hakan kaɗai idan ta yi tunani tana jin kamar za ta yi hauka. Ko kaɗan rayuwa bata yi mata adalci ba, Waheedah ta zama kamar ƙaddara ta shigo da su rayuwar junan su don ta nuna ma Nuriyya abinda duk take son zama amma ya yi mata nisa. Idanuwanta ta lumshe, alƙawari ta yi wa kanta ta gama zubda hawaye akan abinda yake faruwa, tunda Anas ya ce ya ji ya gani, za ta ga ko zai iya jure zaman aure da ita. Don ta gama shirya mishi wulaƙancin da zai saka shi da na sanin aurenta.

*****

NDA Kaduna

Wanka ya fito, daga shi sai gajeran wando, da towel rataye a wuyan shi. Ahmad da shi kaɗai ne abokin shi a zaman shi makarantar horar da sojojin tunda ya zo ta shekaru huɗu da wani abu, har yana shirin fita kuma, don watannin da suka rage musu ba su da yawa. Suna shekararsu ta ƙarshe kenan. Babu ruwan shi da kowa, in ba ka shiga lamarin shi ba , sai abinda ba zai iya kaucewa bane kawai zai haɗa ku. Ko wajen motsa jiki, ko training, ko a aji, wani abu dai da ya zama mishi dole, saboda akwai masu saurin ɗaukar zafi irin shi. Sai dai ba kowa yake jurewa hukuncin manyansu idan faɗa ya kaure ba.

Tun suna mamakin taurin zuciya irin na Abdulƙadir har sun bari, shi yasa zuwa yanzun babu mai shiga sabgarshi sai ta kama, a ‘yan Terma five kenan, balle kuma wanda suke ƙasan shi, har ba sa so wani abu ya haɗa su da Abdulƙadir ɗin. Zai dake ka kamar ya samu ganga, musamman idan ya tashi yana jin ɓacin rai, in ya samu wani ya huce a kan shi yakan ji ya dawo dai-dai.

“A. Bugaje.”

Ahmad ya ce kamar yadda kowa yake kiranshi a NDA ɗin.

“Baka gyara wayar nan ba ashe?”

Screen ɗinshi ya fashe, a kwana biyu yana ɗan samu ya amsa kira idan ya shigo, sai ta ƙara faɗuwa, ya je ya gyara ɗin ne bai je ba. Yassar ma a wayar Ahmad ɗin yake kira su gaisa.

“Zan gyara.”

Ya faɗi a taƙaice yana ƙarasawa kan gadon ya kwanta. System ɗinshi ya janyo da take ajiye kan tebur ɗin da ke ɗakin, buɗewa ya yi, hannuwan Waheedah da ƙunshinta na cika screen ɗin. Har yau bai ga ƙunshin da ya yi mishi kyau kamarshi ba.

“Hannuwan nan na min kyau wallahi, ina ma in gano yarinyar da take da shi.”

Ahmad ya faɗi yana miƙa kanshi do n yan hango sosai. Abdulƙadir ya kai hannu ya latse system ɗin yana kasheta gaba ɗaya.

“Au don baƙin ciki kar in gani?”

Ya yi maganar yana dariya. Har duba system ɗin ya yi bai ga hoton ba, ya rasa kalar ɓoyon da Abdulƙadir ya yi ma hoton, idan zai mutu yana tambaya ko ya san mai hannun ne, ko yana da alaƙa da ita kamar yadda ya yi zato da farko ba zai kulashi ba ballantana ya samu amsa. Kamar yadda yanzun ma bai kulashi ba. A gidansu Abdulƙadir banda Yassar bai san kowa ba, sai Hajja don sukan gaisa idan ta kira.

Abdulkadir ɗin ko shi ya kira, sai Zahra da ita ma suna waya, ita ce ma da ya tambayi Abdulƙadir ɗin ko ƙanwarshi ce ya samu amsar,

“Ban damu da ka kusa zama cikakken soja ba, zan karyaka Ahmad, da gaske zan karyaka…”

Yayi dariya sosai, kuma hakan ya tabbatar mishi da cewa ƙanwar Abdulƙadir ɗin ce. Akwai yarinyar da yake yawo da hotonta a wallet ɗinshi. Wasu lokutan kuma yakan cire hoton ya saka a aljihun shi, duk idan aka ɓata mishi rai Ahmad na kula yakan saka hannun shi a aljihun shi, kamar hoton na da wani sihiri da zai hutar da fushin shi. Duk yadda yake so ya tambayeshi alaƙar shi da yarinyar hoton sai ya kasa, sabo da a bayyane yake. Tana da muhimmanci na gaske a rayuwar shi. Bai dai taɓa nuna alamar yana da budurwa ko yana son wata ba. Idan har hirarsu ta tsawaita to ta dangancin aikin da suke gab da fuskanta ne na kare ƙasarsu.

Sai dai watanni kusan bakwai da suka wuce, yakan ga Abdulƙadir ɗin manne da wayarshi duk dare, ba daddanawa yake ba, da alama dai yana karanta wani abin ne, yakan kuma ga yana murmushi shi kaɗai in ya zauna da wayar a hannun shi. Gashi ya buɗe whatsapp ɗin da babu yadda bai yi da shi ya buɗe ba, ya ƙi. In kuma ya ɗauki wayar Abdulƙadir ɗin don ya yi kira ko wani abu, banda ‘yan gidansu da zai ga Hamma wanne, ko Adda wance, sai su Zahra, baya ganin kiranshi da kowa sai lambar da ya sakama ‘Wahee’. Yakan kuma ga saƙonninta na shigowa wasu lokutan. Bai da tabbas, amma yana alaƙanta hotonta ne Abdulƙadir yake yawo da shi.

Juya mishi baya Abdulƙadir ya yi, yana jan pillow ya ɗora hannuwan shi akai, don baya sakawa a kanshi, ko ya kwanta ya sa pillow da ya fara bacci yake zarowa ya ɗora hannunshi akai. Gashi har yanzun kwanciyar jarirai yake, jikin shi a dunƙule haka yake bacci. Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na mishi yawo kamar ko da yaushe, tun yana ƙoƙarin danne shi har ya haƙura ya barshi . Ya daina kokawa da zuciyarshi akanta, zuwa yanzun ya fahimci zuciyar shi na doka mata. Zai yi wani abu akai, sai ya fita daga NDA ya ɗan samu nutsuwa, yanzun koma menene yake ji dole ya jira shi ya nutsu tukunna.

Lokaci irin wannan hirar Waheedah yakan karanta, har ta yi mishi sai da safe, yakan koma baya ya yi ta sake karantawa har sai ya fara jin bacci. Amma kwana biyu hakan ba ya samuwa saboda bai gyaro wayarba. Yana kewar hirarrakinta, don takan hana mishi tunanin Nuriyya irin haka, takan ɗebe mishi kewar gida da guje ma ganin Nuriyya ya hanashi zuwa. Sosai surutun ta yake mishi daɗi.

‘Hamma ka san me ya faru yau.’

Yakan karanta saƙonninta da sanyin muryarta, har yanayin idanuwanta yakan gani, kamar tana cikin ɗakin tare da shi. Idan an ɓata mishi rai yakan lumshe idanuwan shi ya ji muryarta cikin kanshi.

‘Banda saurin fushi Hamma, don Allah banda saurin fushi ka ji.’

Takan faɗa mishi haka a saƙonninta, tana saka murmushi Kjwace mishi. In ba ita ba, babu wanda ya isa yana ba shi umarni haka, ko abinci takan mishi magana ya ci, kar ya zauna da yunwa, wata rana sunanta kawai zai rubuta, za ta ce mishi ya ajiye wayar ya kwanta. Yadda take karantarshi har mamaki yake ba shi, tashi ya yi ya ɗauko wallet ɗinshi ya ajiyeta gefen kanshi yana gyara kwanciyarshi. Hotonta ya yi amfani da shi ya danne na Nuriyya da zai sakashi tunanin abubuwan da za su addabeshi. Baccin ya fara jin yana fisgarshi.

‘Hamma ka yi addu’a.’

Ya ji muryar Waheedah na faɗi cikin kanshi, ba tare da ya buɗe idanuwanshi ba yayie addu’a, ko tofawa bai yi ba, bacci ya ɗauke shi.

*****

Washegari da yake ya faɗa Asabar, Ahmad ya dame shi, suka shiga kasuwar wayoyi ya gyara screen ɗin wayarshi tukunna suka dawo. Suna dawowa charge ya saka wayar don ya ga ya yi ƙasa sosai. Ya yi sallar azahar ya zo ya zauna ya fara cin abinci, wayar ya ciro daga chargy ya buɗe data ɗinshi yana ci gaba da cin abincin, text ɗinshi ya shiga ganin wajen saƙonni ashirin, ya kuma san Waheedah ce. Dubawa ya yi duka na jin ko yana lafiyane. Zuciyar shi na ɗaukar wani irin ɗumi da sa ƙonninta ne kaɗai kan haifar. Tana bashi kulawar da yake so, kulawar da babu wanda yake ba shi ita sai Hajja, ita ma ba kowanne lokaci ba.

Whatsapp ɗin ya shiga, saƙonninta ne da yawa, zai ce ita kaɗai take turo mishi saƙonni haka, su Nawaf gaisuwa ce, sai kuma zagi idan ya karanta bai amsa ba. Yassar ma hakan ne, ya fi jin daɗin nata fiye da na kowa, ita kaɗai ce bata taɓa magana akan halayyarshi ba, asalima tana saka shi jin babu wani abu marar kyau a abinda yake yi ɗin. Bata damu da ko ya amsata ko bai amsata ba, idan ta zo takan sake mishi magana ta kuma bashi labari, Waheedah daban take da kowa na rayuwar shi.

Daga farko ya fara karanta saƙon, da gaisuwa ce, hirar makaranta. Sai kuma ta fara bashi labarin suna hidimar biki. Karanta saƙonnin yake yana cin abinci, kafin ya ji shinkafar ta bi mishi ta hanyar da bai kamata ba, tari ya kuwa sarƙe shi, ruwa ya ɗauka babu shiri yana kwankwaɗa, amma tarin bai daina ba, ga ƙirjinshi da yake ji kamar an fara haɗa wuta a ciki, idanuwan shi har sun kawo ruwan wahalar shaƙewar da ya yi, hakan ya sa shi ƙanƙance su yana sake duba saƙon Waheedah.

‘Ni kam na gaji sosai Hamma, dama haka hidimar bikin ƙawa yake? Allah na fi Nuriyya gajiya.’

Ƙasa ya yi babu shiri yana isa saƙonta na ƙarshe.

‘Hamma har an ɗaura auren Nuriyya fa.’

Karanta saƙon yake yana son fahimtar asalin ma’anar shi, kafin ya ji numfashin shi na barazanar ɗaukewa. Kanshi yake girgizawa yana sake danna wayar ko zai ga wani sabon saƙon Waheedah ɗin da zai ƙaryata na ƙarshe.

“No… No… Wasa ne wannan.”

Ya furta yana jin zuciyarshi kamar tana rabewa biyu, kullum Waheedah na mishi hira, me yasa bata taɓa ce mishi Nuriyya za ta yi aure ba, sai yanzun ne za ta faɗa mishi an ɗaura mata aure.

“Haka na ce ki jirani, in nutsu waje ɗaya Nuriyya. Na ce ki jira ni.”

Yake faɗi kamar wanda ya samu taɓin ƙwaƙwalwa, ji yake gaba ɗaya duniyar ta haɗe mishi waje ɗaya. Wayar ya cilla kan gado yana ture abincin, miƙewa ya yi ya fice daga ɗakin kwanan nasu. Wajen motsa jiki ya nufa, yana addu’ar kar wani ya tare mishi hanya, don ko gani ba ya yi sosai, wani abu yake son duka, idan ba punching bag ba, to fuskar duk wanda tsautsayi ta gifto da shi. Allah ya taimake shi har ya ƙarasa wajen motsa jikin bai ci karo da kowa ba, bai kuma kula ko ana kaucewa bane idan an hango shi.

“A. Bugaje!”

Ahmad da ke wajen ya kira ganin yanayin Abdulƙadir ɗin.

“Ka matsa min Ahmad…”

Abdulƙadir ya faɗi yana ƙarasawa ya ɗauki abin nade hannu ya fara nannaɗawa a hannun shi. Ahmad na ƙarasawa wajen shi.

“Me ya faru? Lafiya? Kai min magana don Allah…”

Ɗayan hannun Abdulƙadir yake naɗewa.

‘Hamma har an ɗaura auren Nuriyya fa.’

Shi ne maganar da ke mishi yawo a ko’ina na jikin shi tana ƙara saka ƙirjinshi wani irin raɗaɗi, ya san ɓacin rai, ya san fushi, ya san abubuwa da dama. Amma yanayin da yake ji yanzun daban ne a rayuwarshi, yanayi ne da baya fatan ya sake jin shi har abada, don haka ba zai bari ya dame shi ba, zai daki wani abu har sai ya daina jin ƙirjinshi na mishi kamar zai buɗe.

“A. Bugaje…”

Ahmad ya kira cike da damuwa a muryarshi, Allah ne shaida yana jin Abdulƙadir ɗin kamar ɗan uwanshi. Bai kuma taɓa ganin yanayin da yake gani a fuskarshi ba, bai kula shi ba, punching bag ɗin ya soma duka kamar zai jijjigota, da dukkan ƙarfin shi yake dukanta, amma ji yake kamar yanayin da yake ji na ƙaruwa da duk dukan, kamar da tunanin Nuriyya a matsayin matar wani zuciyarshi na ƙara buɗewa. Sai da ya ji numfashin shi na barazanar ɗaukewa tukunna ya daina dukan yana ɗora hannuwan shi da gwiwoyin shi tare da wani irin sauke numfashi, tukunna ya ɗago ya haɗa wata irin zufa.

Ƙanƙance idanuwan shi yayie yana kallon Ahmad, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Ta yi aure. Ahmad ta yi aure…”
Kai Ahmad ya jinjina mishi yana fahimtar dalilin da ya sa Abdulƙadir ɗin shiga yanayi, bai yi magana ba, don yaune karo na farko da Abdulƙadir ɗin yake faɗa mishi wani abu mai girma haka.

“Ta jirani fa in nutsu ne… Shi ne ta yi aure. Ni na ce ban yi tunanin aurenta bane? Me yasa za ta yi aure?”

Ya ƙarasa yana sauke numfashi, hannu Ahmad ya kai ya taɓa kafaɗar shi cikin son nuna mishi yana tare da shi, ya fahimta. Abdulƙadir ɗin ya kauce yana faɗin,

“Don’t… Ka bar ni.”

Ya juya yana ficewa daga wajen motsa jikin, don iskar da take wajen ta mishi kaɗan, kanshi kamar zai buɗe saboda ɓacin ran da yake ji a cike da shi. Har wani ja-ja yake gani yana gilmawa ta cikin idanuwan shi. Ta yi aure bata jira shi ba, shi ne tunanin da yake cike da shi, yana jin wani yanayi na maye gurbin koma meye yake ji akan Nuriyya.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×