Skip to content
Part 6 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Akan ce kwanaki na gudu, bai taɓa yarda da hakan ba sai bayan sunanshi ya fita cikin jerin mutanen da suka samu gurbi a makarantar horar da sojoji ta NDA da ke cikin garin Kaduna, bayan surutun da ake ta yi na cewar makarantar na da wahalar samu, sai kana da hanya. Zai yi ƙarya idan ya ce Abba bai san mutane ba, ko cikin kawunnan shi ba za a rasa wanda ya san wani da zai taimaka mishi wajen samun makarantar ba, bai dai nemi taimakon su bane kawai. Kuma da yake yana da rabo sai gashi Allah ya ba shi. Ranar wani sama-sama yake jin shi, sosai ya yarda ranaku na gudu.

Duka yaushe ya fara sakandire, ga shi har ya kammala yana shirin jefa takun farko a hanyar shi ta cikar burin shi. Ji yake kamar ya janyo lokacin tafiyar, ‘yan gidan kansu sun fahimci nishaɗin da yake ciki, don tunda suke ba su taɓa ganin ya wuni da murmushi a fuskar shi ba, ko gaishe shi ka yi ranar da murmushi yake amsawa. Idan ka tona ran kowa a gidan ƙal yake, musamman yaran da duk ya kasance akwai tazarar ko da satika ne a tsakanin shi da Abdulƙadir, har tambaya suka yi aka ce musu akan yi shekara ɗaya ma ba a zo gida ba, don sai hutun sallah da ba koyaushe yake kaiwa sati biyu ba ballantana ma ya shige hakan. Ran su ƙal suke jinshi, za su sakata su wala a gidan ba tare da tunanin Abdulƙadir ɗin ba.

Yanzun ma abinci suke ci a ɗakin Anty. Waheedah ta kalli Zahra ta ce,

“Wai da gaske daga shekara sai shekara Hamma Abdulƙadir zai dinga zuwa gida?”

Kai Zahra ta ɗaga mata tana haɗiye abincin da ta cika bakinta dashi.

“Haka na ji Hajja da Hamma Yazid na maganar…”

Kai Waheedah ta jinjina tana jin wani abu ya yi mata tsaye a wuya ba tare da sanin dalili ba.

“Kin san duk yadda nake murnar tafiyar nan…Zan yi kewar shi fa.”

Ta ƙarasa maganar tana ɗan yin jim.

“Babu wanda yake shan dukan Hamma Abdulkadir irinki duk gidan nan…kewar me za ki yi tashi? Jibgar da kike sha?”

Nabila ta yi maganar tana cakuɗa abincinta, dariya Zahra ta yi, don bata san ya za ta yi aa Nabila bayani ta fahimce ta ba, da gaske ne babu wanda yake shan dukan Abdulƙadir ɗin duk gidan kamar ita, sai dai ko shigowa ya yi bai ganta ba sai ya tambaya tana ina, idan abu ya shigo da shi ko bata nan sai yasa an ajiye mata, tana kula da ko aiki yake so ai mishi ita kaɗai ya fi matsawa, da wahala rana ta fito ta koma bai taɓa lafiyarta ba, duk da hakan tana jin Yayan nata har ƙasan ranta.

Abincin suka ci gaba daci suna hira abinsu, Anty ta fito daga ɗakin baccinta tana ganin yadda suka mayar mata da falo.

“Lallai yaran nan, falona ne haka? Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Ta ƙarasa ganin shinkafar da ke danƙare kan kafet ɗinta.

“Wallahi tas za ku share min ɗaki…ko Kjwayar shinkafa bana son gani.”

Turo baki Nabila ta yi don Allah ya ɗora mata son jiki na ban mamaki.

“Anty su Hamma ne fa…”

Hararta Anty ta yi.

“Ban ga su Hamma ba, ku na gani…”

Waheedah kam murmushi ta yi tare da faɗin,

“Za a share Anty… Da mun gama. Har wanke-wanke ma duk za mu yi.”

Tana jin zungurin da Zahra ta yi mata.

“Na ganki don ubanki, wato ta ce wanke-wanke shi ne kike zungurinta ko?”

Cewar Antyn tana ɗorawa da,

“Maƙyuyatan banza da wofi, sai ka ce ba mata ba.”

Ta juya ta koma ɗakinta, harara Nabila da Zahra suka zabga mata, Nabila na faɗin,

“Adda Wahee ke za ki yi wanke-wanken?”

Kai Waheedah ta ɗaga musu tana ajiye cokalinta cikin abincin, don ta riga ta ƙoshi tuntuni, hanyar kitchen ɗin ta nufa tana ganin jibgin kwanonin wanke-wanken da ko kaɗan ba su ɗaga mata hankali ba, in dai aiki ne da za ta yi da jikinta ba ya mata wahala, duk da Mami kance ta cika yin abu da sanyin jiki. Sai da ta fara share kitchen ɗin tukunna ta fara wanke-wanken, tafiyar Abdulƙadir ta yi mata tsaye a maƙoshinta. Shekara ɗaya na mata wani irin nisa na ban mamaki, a wani ɓangaren kuma tana mata saurin zuwa, duka yaushe ya gama jarabawar aji shida har ta fito, ita kanta aji biyar take shirin shiga yanzun hakan.

*****

Ranar Lahadin da saura kwana ɗaya su koma makaranta, kuma ya yi dai-dai da litinin ɗin da Abdulƙadir ɗin ma zai tafi Kaduna. Wani iri take jinta, don haka tana yin wanka ta gama abinda take yi ta fito za ta shiga gidan su Nuriyya ko hira su yi , ta fito harabar gidan ta ci karo da Abba.

“Abba…”

Ta kira fuskarta ɗauke da fara’a cikin yanayin da ita kaɗai take kiran shi da hakan. Shi ma muryar shi ɗauke da fara’a ya ce,

“Waheedah…”

Murmushinta ya ƙara faɗaɗa.

“Ina kwana…”

Amsawa ya yi yana ɗorawa da,

“Har za’aje Islamiyya ne da wuri haka?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi, kafin ta amsa ya ce,

“Wajen Hassanarki za ki je kenan.”

Dariya Waheedah ta yi.

“Abba mana.”

Jinjina kai ya yi yana saka hannu a aljihu.

“Ai na sani….itama goben suke komawa makaranta ko?”

Kai Waheedah ta ɗan ɗaga mishi, dubu uku ya zaro daga aljihunshi yana miƙa wa Waheedah ɗin.

“Na manta ne wallahi, ki bata sai ta ɗinka sabon kayan makaranta itama, abin na raina tun ranar da na bayar da naku ɗinkin…”

Da fara’a a fuskar Waheedah ta karɓi kuɗin.

“Allah ya ƙara arziƙi Abba… An gode sosai.”

Murmushi kawai Abba ya yi, hankalin yarinyar yasa yake jinta kamar daga cikin shi ta fito, ko kaɗan baya so ta ji maraicin rashin mahaifinta, alƙawari ya ɗaukarwa mahaifiyarta na cewa zai riƙeta, ko da mahaifinta na raye, nauyin alƙawarin da ya ɗauka zai cigaba da danne shi.

“A dawo lafiya. Allah ya tsare mana kai.”

Waheedah ta faɗi, Abban ya amsata, tsaye ta yi sai da ta ga ya shiga mota ya juyata ya fice daga gidan tukunna ta ƙarasa takawa tana isa ƙofar gidan ta fice tana shiga gidan su Nuriyya ɗin. Bata ma sameta a gidan ba, Mama ta aiketa, kuɗin da Abban ya bata ta miƙa wa Mama tana mata bayani, sosai Mama ta nuna jin daɗinta tare da yin godiya mai yawa, tukunna Waheedah ta koma gida. Ɓangaren su ta nufa ta shiga ɗakinsu ta kwanta. Bata da abinda za ta yi , gashi sun ƙi kawo wuta balle ta yi kallo ta rage zafi

Tunawa ta yi da wani littafi da ta fi wata shida da karɓa wajen Nuriyya, amma bata karanta ba, don har yanzun ita karance-karancen littafin Hausar nan basa kanta, saukowa ta yi daga kan gado tana ɗauko tsohuwar jakar makarantarta, ai kam tana saka hannu ta bincika ta janyo littafin, kan gado ta ɗora shi tana mayar da jakar tukunna ta koma ta hau gadon ta kishingiɗa tana ɗaukar littafin. ABIN DA AKE GUDU na Batul Mamman ta duba sunan littafin da marubuciyar, sosai takan ji Nuriyya na maganar marubuciyar da yadda tsarin rubutunta yake tafiya a nutse, don takan ce bata da gwana a marubutan Hausa kamar matar. Shafin farko ta buɗe tana nutsawa cikin labarin Asma’u.

****

Ko da suka dawo Islamiyya so take kawai ta gama duk wata hidima da za ta yi tai sallar isha’i ta koma ɗaki ta ƙarasa jin yanda za a ƙare da labarin Asma’u, da ta ɗauka Nuriyya zuzuta marubuciyar kawai take yi, sai yanzun da labarin ya taɓa ta fiye da tunani. Ga tarin darussan da iya tsayin rayuwarta bata taɓa hango faruwar su ba, tashin hankali abune da sai dai ta ji labarin shi a waje ko a fina-finai, sai kuma yanzun da take karanta shi a littafin Batul Mamman. Kayan makarantar su duk ta haɗa ta goge. Ɗauka ta yi tana nufar ɗaki, ta ga Amatullah a kwance a ƙasa kan kafet.

Tun da za su fita Islamiyya take faɗin cikinta na ciwo, har suka dawo, don Waheedah ba zata ce ta ga ta ci abinci ba.

“Ki tashi ki faɗa wa Mami ko magani sai ta baki… Ya za ka zauna ciwo na cinka?”

Waheedah ta faɗi tana ajiye uniform ɗin a gefen gado tare da taɓa Amatullah ɗin, zuciyarta ta yi wata irin dokawa ganin kamar bata motsi, tsugunnawa ta yi tana kamota.

“Amatu… Amatullah…”

Take faɗi tana jijjigata, idanuwanta cike taf da hawaye, da ƙyar Amatullah ta ɗaga idonta.

“Adda Wahee cikina, cikina ciwo yake…”

Hannu Waheedah ta sa tana share Kjwallar da take shirin zubo mata, muryarta a karye ta ce,

“Bari in kira Mami…sannu.”

Ta ƙarasa maganar tana zame Amatullah daga jikinta, ta fice daga ɗakin da sauri, ko da ta je wajen Mami ɗin ma hannunta kawai ta kamo don ta kasa magana, saboda kukan da take yi, ɗakin nasu Mami ta bita hankali a tashe, a kafaɗa ta saɓa Amatullah ɗin tana ɗaukar hijabin Waheedah da ta gani inda ta yi sallar Magrib tana nufar hanyar fita daga ɓangaren nasu. Waheedah ta rufa mata baya. Ɓangaren Hajja ta nufa da Amatullah don tasan Abban su bai isa dawowa ba.

“Subhanallah, me ya faru haka?”

Hajja ta tambaya, Mami na amsata da,

“Cikinta ne yake ciwo…”

Hajja bata ce komai ba ta koma cikin ɗakin da hanzari, Hijabinta ta daauko itama ta saka ta ɗauko mukullin motarta tana faɗin,

“Mu je… Bari in dubo cikin yaran nan, ko wani yana nan. Tafiya asibiti da namiji na da daɗi, ko don zirga-zirga…”

Basu ma ƙarasa bangaren nasu ba sai ga Muhsin ya shigo gidan. Motar Hajja ta buɗe tana karɓar Amatullah da take fitar da numfashin wahala ta sakata a bayan motar tana shiga. Ganin Waheedah da ke kuka ta kama murfin motar ya sa Mami faɗin,

“Ina za ki ke kuma? Wuce ki koma gida…”

Rau-rau ta sake yi da ido, wani kallo Mami ta watsa mata da yasa ta sakin murfin motar, tana kallo suka rufe, gefe ta matsa, Muhsin ɗin ya juya motar suka fice. Tsaye ta yi a wajen tana share hawaye, tare da sauke ajiyar zuciyar da take jin tana mata zafi. Ita kam da sun tafi da ita hankalinta zai fi kwanciya. A wajen ta zauna ko sauron da ke gartsa mata cizo bata ji, don ma da haske, kasancewar an kunna musu generator. Bata san iya lokacin da ta ɗauka a wajen ba, ta haɗa kai da gwiwa, kuka kawai take sharɓa.

Abdulƙadir ne ya zo wucewa, don ranar ya wuni ne da su Nawaf tunda washegari da sassafe zai wuce, ajiyar numfashinta ya soma ji, kafin ya tsaya yana daƙuna fuska, sosai ya saurara ya ji daga inda kukan yake fitowa, dube-dube ya shiga yi, yana hangota rakuɓe wajen ajiye motocin, daga hannuwanta ya gane ita ce.

‘Me yarinyar nan take yi anan?’

Ya tambayi kanshi yana ƙarasawa wajen, ta haɗe kanta da gwiwa da alama kuka take yi.

“Waheedah…”

Ya kira, muryarshi na dukan dodon kunnenta da wani irin yanayi da yasa ta ɗagowa, fuskarta ta ƙara yin ja, idanuwanta duk sun kumbura saboda kukan da take yi, sai ya tsinci kanshi da kasa yi mata faɗa. Muryarshi ɗauke da wani yanayi ya ce,

“Menene? Wa ya dake ki?”

Kai Waheedah ta girgiza mishi, wani rauni take jin yana ƙara danneta da ganin shi, hawayen ta na ƙara zubowa.

“Me kike yi anan to? Me ya faru? Mutuwa akai?”

Abdulƙadir ya tambaya, wannan karon da damuwa a muryarshi. Kan dai ta sake girgiza mishi.

“Ki min magana Waheedah, kina son ɓata min rai ne ko me?”

Ya ƙarasa maganar a faɗace, da ƙyar, muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,

“Amatu…Amatullah ce bata da lafiya.”

Numfashi ya sauke.

“Shi ne kika zo nan kina kuka…ina Amatu ɗin yanzun?”

Hannu ta sa ta goge hawayen da ke shimfiɗe kan fuskarta tana jan hanci.

“Sun je asibiti…”

Ta amsa muryarta na sake karyewa.

“Me yasa ba su tafi da ke ba? Mtswww.”

Abdulƙadir ya ƙarasa maganar da jan ƙaramin tsaki. Kukan da take yana mishi wani iri.

“Tashi daga nan.”

Ya umarta, idanuwanta cike da hawaye take kallon shi.

“Zan jira su dawo ne Hamma…”

Wani irin kallo ya yi mata yana faɗin,

“Za ki tashi ko sai na watsa miki mari? Cikin sauron za ki zauna da yake baki da hankali ko?”

Miƙewa Waheedah ta yi babu shiri, tana ganinta ‘yar mitsitsiya a gaban shi, duk da halin damuwar da take ciki bai hanata jin yadda zuciyarta take dokawa ba.

“Ki koma cikin gida. Idan na ganki a wajen nan sai na zane ki…”

Wasu sabbin hawayen ta ji sun zubo mata, duk da ba su hanata ƙin bin umarnin shi ba, tsaye ya yi a wajen yana kallonta har ta sha kwana, ɗan dafe kanshi ya yi, yana jin ranshi na ɓaci babu dalili, ɓangaren su ya nufa, ko sallama bai yi ba ya wuce su Yassar da suke cin abinci.

“Ko shi da wa kuma?”

Yazid ya tambaya, Yasir ya amsa shi da,

“In dai baƙin ran Abdulƙadir ya motsa ko babu dalili yin shi yake…”

Dariya suka yi, sai gashi ya fito, ƙaramin tsaki ya ja, don bai ga abinda zai basu dariya ba, ranshi yana ɓaci suna dariya.

“Ku komai na dariya ne?”

Ya faɗi yana ƙara jan tsaki.

“Kai da uban wa?”

Yassar ya tambaya, bai samu amsa ba, Abdulƙadir ɗin ya zo ya wuce yana yin ciki da kƙafafuwan Yazid da ya ce,

“Ikon Allah…ba ni na kar zomon ba.”

Shima bai samu amsa ba, Abdulƙadir ɗin ya fice daga ɗakin, yana doko musu ƙofar kamar zai karyata. Haka kawai ya tsinci kanshi da nufar ɓangaren su Waheedah don bai yarda cewar ta koma ba, hangota ya yi tsaye bakin ƙofa tana kai hannu tana goge fuskarta.

“Yarinyar nan bata da hankali.”

Ya furta a hankali, kukan da take yi ma zai saka mata wani ciwon kan, ga sauro da ya gama moreta a wajen da ta zauna. Da alama bata ganshi ba, don sai da ya ƙure mata tukunna ta ruga da gudu tana shirin komawa cikin ɗakin, Abdulƙadir ya damƙo hannunta.

“Hamma don Allah…”

Waheedah ta faɗi idanuwanta kamar za su faɗo, ga wani lugude da zuciyarta take mata.

“Me nace?”

Kai ta girgiza mishi, hawaye na silalowa daga idanuwanta.

“Me nace miki?”

Ya tambaya a tsawace.

“Kar in fito… Haka kace kar in fito…”

Idanuwa Abdulƙadir ya tsura mata, bai yi niyyar dukanta ba, haka kawai ya ji yana son ganin ta tsorata haka.

“Wallahi Hamma ƙafata ɗaya na cikin ɗaki… Ɗaya ce kawai a waje… Wallahi.”

Waheedah ta faɗi, bai san dariya ta kuɓce mishi ba sai da ya ji sautinta cikin kunnen shi. Zahra na da wauta, baya jin kuma a cikin gidan akwai wanda ya kai Nabila rawar kai, amma Waheedah cikin sanyi take nata rashin hankalin, dariya yake da ya kwana biyu bai yi ba, ita kanta Waheedah ɗin kallon shi take da mamaki, ba wai baya dariya bane, amman dariya irin haka da sauti ba, ba za ta tuna ranar ƙarshe da ta ga hakan ya faru da shi ba. Ɗayan hannunta ta sa tana share hawayenta, ɗan ƙaramin murmushi na ƙwace mata.

Hannunta Abdulƙadir ya ja zuwa cikin ɗakin, ya zaunar da ita kan kujera, da murmushi a fuskarshi ya nufi kitchen ɗin, ruwa ya ɗibo a kofi ya zo ya kawo mata, karɓa ta yi tana mamakin yadda bata san tana jin ƙishi haka ba, ta kusan shanye ruwan, ta ajiye kofin tare da sauke numfashi, miƙewa ta yi.

“Ina za ki je?”

Abdulƙadir da yake tsaye ya tambaya, muryarta a dishe ta ce,

“Fuskata zan wanke.”

Kai ya ɗaga mata, ta zagaya ta bayan kujerar ta wuce, don gani take in ta wuce ta gabanshi zai ji yadda zuciyarta take dokawa. Kofin ruwan ya ɗauke yana mayarwa kitchen ya fito ya koma kan hannun kujerar da ke kusa da ƙofa ya zauna. Fitowa Waheedah ta yi, yabi fuskarta da ta ƙara mishi ja saboda kukan da ta yi, yana tunanin kar ta yi ciwon ido da yadda ya ga idanuwan sun kumbura. Wajen da ta tashi ta koma tana zama, wasa take da hannuwanta, ko zuciyarta za ta rage gudun da take, lokaci zuwa lokaci takan dan ɗago ta saci kallon Abdulƙadir ɗin da yake zaune, ƙananun idanuwan shi na kafe a kanta, duk da alamun shi sun nuna yayi nisa a duniyar tunani.

Hakan ne a ɓangaren Abdulƙadir ɗin, in da za ka taɓa shi ka tambayeshi tunanin da yake yi bai sani ba, balle kuma a zo dalilin da ya sa shi yake zaune a wajen, kukan da ya ga tana yi ne ya dame shi, shi yasa ya dawo kota sake fitowa, yanzun ɗin ma yana zaune ne kar ya tafi ta sake fita, yana kuma so ya ga dawowar su Mami ɗin ya duba jikin Amatullah, dalilan duka sun zauna mishi, don baya tunanin akwai wani dalili bayan hakan, numfashi ya ja a hankali yana fitarwa, yana jinjina ikon Allah akan Waheedah ɗin, yadda ta kuɓcewa fitowa a zabaya abin al’ajabine, hannuwanta da take wasa da su ya tsayar da idanuwan shi akai, har faratan yatsunta farare ne.

‘Wannan wanne irin haske ne?’

Ya tambayi kanshi yana sake sauke numfashin da yasa Waheedah kallon shi, duk cikin yayyen nasu shine ba sa hira da shi, ba ka ma ga wannan fuskar ba, in ba gaisuwa ba, sai dai in shi da kanshi ya tambayeka abu za ka amsa, amma hira kam baya yi da su, wani irin gudu ta ji zuciyarta ta ƙara, sautin na bugawa har cikin kunnuwanta, da laɓɓanta da ta ɗaga su da ƙyar tana faɗin,

“Gobe In Allah ya kai mu za ka tafi ko?”

Da mamaki Abdulƙadir ɗin ya kalleta, yana ɗan daƙuna fuskar shi tare da jinjina mata kai, wani abu Waheedah ta haɗiye da take jin shi tsaye a maƙoshinta, bata san ya akai take son tambayar shi ba.

“Hamma sai ka yi shekara baka dawo ba ko?”

Kai ya sake jinjina mata, kamar ba zai yi magana ba kafin ya ce,

“Menene? Ba murna kuke zan tafi ba.”

Wannan karon ita ta girgiza mishi kai, tana kallo ya sake ƙanƙance mata idanuwanshi kafin ya ce,

“Ƙarya ne…”

Yana saka ta yin ƙaramin murmushi.

“Ki ban ruwa in sha Waheedah…”

Abdulƙadir ya faɗi yana ƙara gyara zaman shi akan kujerar, miƙewa Waheedah ta yi tana zuwa kitchen ta ɗibo ruwan ta kawo mishi, karɓa ya yi yana shanyewa tas ya miƙa mata kofin da ta mayar kitchen, ta kai mintina uku a ciki tsaye ba tare da ta san tunanin me take yi ba. Kafin ta fito tana komawa kan kujerar ta zauna, wannan karon tana kwantar da kanta a jikin hannun kujerar, agogon dake ɗaure a hannun shi ya duba yana mamakin gudun da lokaci ya yi don har tara da rabi ta gota.

“Kin ci abinci?”

Ya tsinci kanshi da tambayarta, don yadda ta langaɓar da kai a jikin hannun kujerar ya sa shi tunanin ko yunwa take ji, shi kanshi bai ci abincin ba. A hankali Waheeda ta ɗaga mishi kai, gyara zaman shi ya ƙara yi kan hannun kujerar. Lumshe idanuwanta Waheedah ta yi, bata san iya lokacin da suka ɗauka a haka ba, balle ta san bacci ya ɗauke ta, cikin bacci ta ji muryar Abdulƙadir ɗin na faɗin,

“Ya jikin nata yanzun?”

A hankali ta buɗe idanuwanta tana kallon Mami, da sauri ta miƙe tana murza fuskarta.

“Mami… Ina Amatullah ɗin?”

Kallon ta Mami ta yi.

“Suna asibitin ita da Hajja, bacci take yi, da sauƙi ma sosai, za su dawo da safe in sha Allah…”

Numfashi Waheedah ta sauke, Abdulƙadir da yake tsaye ya kalli Mami yana faɗin,

“Me yasa ba ku tafi da ita ba?”

Ware idanuwa Mami tayi tana kallon Abdulƙadir ɗin.

“Asibitin sai mun yi gayya Abdulƙadir?”

Daƙuna fuska ya yi.

“Da kun tafi da ita ai, ta zauna tanata kuka a waje.”

Kallon ta Mami ta yi, tana sakata sadda kanta kasa, sai yanzun take jin kunya ta lulluɓeta.

“Harabar motoci Mami, ga sauro a wajen…ni kam da kun tafi da ita.”

Ya sake maimaitawa, yana ƙoƙarin tausasa harshen shi saboda Mami ce, ɗan murmushi Mami ta yi, tasan halin yaron sarai, ta kuma san ƙoƙari yake kar maganar da yake ta yi kamar yana mata faɗa ne.

“Ai mun dawo yanzun.”

Mami ta faɗi da murmushi a fuskarta. Kai Abdulƙadir ya jinjina mata.

“Sai da safen ku. Allah ya ƙara sauƙi.”

Ya yi maganar yana ficewa daga ɗakin kafin ya ce komai, kamar hakan Waheedah take jira ta ƙaraso tana kwantar da kanta a jikin Mami da ta tureta tana faɗin,

“Ke yanzun meye na kuka? Ke da za ki yi mata addu’a? Ke komai na kuka ne?”

Dariya Waheedah ɗin ta yi tana jin hankalinta ya kwanta, bin Mamin ta yi suna hira, kafin ta yi mata sallama ta wuce ɗakinsu. Sai ta ji ɗakin ya yi mata shiru, musamman da ta kwanta, da yanzun Amatullah ɗin tana mata tsegumin juye-jujen da take in ta yi bacci, don da yawan lokuta tana cikin bacci za ta ji Amatullah ta ɗaka mata duka, ta kwashe ƙafafuwanta da ta jibga mata ta warɓar gefe tana faɗin,

“Adda Wahee ki kasheni sai ki huta.”

Dariya ta yi ita kaɗai, miƙewa ta yi ta kashe wutar ɗakin, tana ɗaukar ‘yar karamar fitila mai batir ta maƙala a cikin hular da ke saman kanta, tukunna ta kwanta ta janyo littafinta don ta ci gaba da karantawa. Idanuwanta da ta ji har zafi suke mata yasa ta lanƙwasa shafin da ta tsaya ɗin, ta yi addu’ar bacci ta rufe idanuwanta, soyayyar Asma’u da Jiƙamshi na mata tsaye, soyayyar tasu na sata tunani kala-kala, kafin bacci ya yi awon gaba da ita cike da mafarkin su.

*****

Ɓangaren su ya nufa ya shiga kitchen tunda girkin Hajja ne ranar, tuwon shinkafa ne ta yi da miyar taushe da ta sha albasa mai lawashi sai ƙamshi take. Yana jin daɗin girkin Anty da Mami, amma abincin Hajja daban yake jin shi, a wajen shi duk wani abinci da zai ci bayan na Hajja zai biyo, bai san ko ƙaunar da ke tsakanin su bace ta rufe mishi ido. Anan kitchen ɗin ya tsaya yana ɗora abincin kan kantar kitchen ɗin, hannun shi ya ɗauraye jikin famfon da ke gurbin wanke-wanke. A tsayen ya ci abincin.

‘Ka ga za ka tafi wani gari da babu idanuwan mu akan ka, don Allah ka riƙe addininka, kar ka yi wasa da sallah, in har kana yinta cikin lokaci, kana ƙoƙarin yinta yadda ya kamata za ta kare maka aikata abubuwan da bai kamata ba. Kuma ka rage zafin zuciya, don Allah Abdulƙadir ka dinga saka wa ranka salama.’

Nasihar da Abba ya yi mishi ta dawo mishi, kai ya ɗan jinjina yana karasa cinye abincin ya wanke hannun shi ya fice daga ɗakin. Ɓangaren su ya koma, babu kowa a falon sai Yassar da ya kalle shi cike da mamaki.

“Daga ina kake haka kai kuma?”

Saida ya zauna tukunna ya daƙuna wa Yassar ɗin fuska.

“Hamma kana tsareni da tambaya kamar yaro.”

Dariya Yassar ya yi.

“Na kai shekarun da zan fita in dawo sanda naga dama.”

Dare yayi, don sha ɗaya har da rabi, gashi baya jin yana da ƙarfin biyewa rashin kunyar Abdulƙadir ɗin da zuwa yanzun inda sabo ya kamata ace ya saba, in wani ya yi wa a waje su Hajja yake ja wa zagi, mutane na ganin bai samu wadatacciyar tarbiya ba. Abin na wa Yassar takaici, mutane na bashi mamaki, yadda sukan ɗora laifin yara akan iyayensu ba tare da kwakwwarar shaidar cewa laifin na iyayen bane na ci mishi rai. A ganin shi burin kowanne iyaye ɗansu ya zamo nagartacce, ya zamo abinda za su yi alfahari da shi.

Bai ce wasu lokutan ba a samun ɓaraka daga ɓangaren iyayen ba, bai ce ba a samun sakacin iyaye a kan tarbiyar yaransu ba, amma hakan ba ya nufin duk wani abu da yaro zai yi sai ya zamana laifin iyayenshi ne , kowanne ɗan Adam yana da zaɓi a rayuwa, cikin zaɓin har da fatali da tarbiyar da iyaye kan ɗora yaransu akai, a ɓangaren Abdulƙadir ɗin kusan zai ce hakane, tun yana da ƙarancin shekaru yake da wata irin zuciya, da ko laifi ya yi in zaka kashe shi da duka ba zai ko motsa ba ballantana ya yi tunanin gudu, ko wani ya zo da nufin janye shi zai nuna baya so.

Yana tuna lokutan da Hajja ke dukan shi akan abubuwa da dama, kafin Abba yace tana binshi da addu’ar shiriya tunda dukan baya aiki, ga bakin shi ba zai yi shiru ba, in ka faɗi ɗaya sai ya faɗi goma, musamman in yana ganin akan gaskiyar shi ne, komin girmanka baka wuce Abdulƙadir ya datsa maka maganar duk da ta zo kan shi ba. Kallon shi Yassar ya yi yana faɗin,

“Don Allah ka kula da kanka, banda faɗa da mutane, banda rashin kunya…”

Murmushi Abdulƙadir ɗin ya yi yana sa Yassar tashi daga kishingiɗar da ya yi a jikin kujerar yana gyara zaman shi sosai.

“Nasan faɗa dai sai ka yi, don Allah banda faɗan da babu dalili.”

Ƙanƙance mishi idanuwa Abdulƙadir ya yi.

“Nasiha kake min?

Duka Yassar ya kai mishi da yasa shi ture Yassar ɗin yana faɗin,

“Cin zali babu kyau.”

Tare da miƙewa don kan shi yake ji ya mishi nauyi.

“Idan na bar gidan sai ka nemi wanda za ka ci zali.”

Ya ƙarasa maganar yana wucewa tare da turo ƙofar ɗakin shi, murmushi Yassar ɗin ya yi yana komawa kan kujerar ya kwanta yana sauke numfashi. Addu’ar Allah ya tsare da ta neman sauƙin zafin rai yake nemawa Abdulƙadir ɗin, da damuwar yadda ƙanin nashi zai rayuwa shi kaɗai a wani gari ba tare da kulawar wani nashi a kusa ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 5Abdulkadir 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×