Skip to content
Part 8 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Idan akwai abinda yake yi a nutse a rayuwar shi bai wuce tuƙi ba, ko Yassar da ya koya mishi tuƙin idan za su je wani waje yakan ce mishi,

‘Abdulkadir kana taka mota kamar za ta cije ka. Don Allah ka ƙara gudu.’

Shi kam bai ga saurin da yake ba. Yanzun ma a nutse yake tuƙinshi, kamar yana da duka lokacin da yake buƙata. Waheedah kuwa ta nutsu a gefe tana wasa da wallet ɗinshi da take hannunta, zuciyarta na doka mata a ƙirjinta kamar za ta fito waje. Ga shirun da yake cikin motar da take jin kaurinshi kamar ta sa hannu ta dangwalo, ya yi mata yawa. Rasa abin yi yasa ta ɓalle maɓallin da yake jikin wallet ɗin tana wasa dashi.

“In kika lalata min sai na zane jikinki.”

Abdulƙadir ya yi i maganar hankalinshi na kan tuƙin da yake yi. Don yana jin yadda maɓallin yake ɓas-ɓas duk idan ta buɗe ta sake rufewa, yasan wasa take da shi. Ba don ba zai yi abinda ya ce ɗin ba, ya zaneta ta san ba wani abu bane, ba zai zama ma farko ba, bata dai san dalilin da yasa maganar shi ta bata dariya ba.

“Na zama sa’anki ko?”

Ya buƙata jin sautin dariyarta, bata amsa ba, bai kalleta ba kuma har lokacin, amma yasan kai take girgiza mishi. Bata mayar da maɓallin jikin wallet ɗin ba, hakan yasa ta buɗewa tana sa hannu ta shafa wajen da ta ga alamar I.D card ɗinshi ne, hannu ta sa ta janyo tana ƙoƙarin ganin hoton da yake jiki, sai lokacin Abdulƙadir ya ɗan juya ya kalleta, yana mayar da hankalin kan tuƙin da yake yi. Ya ga yadda take ɗaga I.D card ɗin wajen gilas ɗin ƙofar don ta gani, hannu ya miƙa ya kunna fitilar da ke cikin motar yana sata rufe idanuwanta ta sake buɗesu da wani yanayi da yake nuna bata tsammaci hasken da ya gauraye gaban motar ba.

Tukunna ta kalli Abdulƙadir ɗin da idanuwanshi suke kafe kan titi, numfashin da batasan dalilin shi ba ta sauke tana mayar da hankalinta kan ID card ɗin da yake hannunta ta ci gaba da dubawa. Ɗan yatsanta babba na shafa kan hoton shi da yake manne a gefe. Mayar mishi da ID card ɗin za ta yi wajen data ciro shi ta ga ɗan ƙaramin hoto a wajen ta sa hannu ta zaro tana ƙare wa hoton da alamu suka nuna bai jima da ɗaukar shi ba kallo, don askin da yake kanshi yanzun shi ne a jikin hoton. Wani abu da ya yi mata tsaye a maƙoshinta take ƙoƙarin haɗiyewa amman ya ƙi tafiya.

“Hamma…”

Ta kira muryarta can ƙasan maƙoshi, sai da ta yi tunanin ba zai amsa ba tukunna ya ce,

“Menene?”

Don yaji ta kira sunan shi, bai amsa bane yana jiran ta ci gaba da magana, jin ta yi shiru yasa shi amsawa, ya san za su iya kaiwa inda zasu kai bata yi maganar ba tana jiran sai ya amsa ta. Ɗan gyara zamanta ta yi tana kallon Abdulƙadir ɗin, gudun zuciyarta na ƙaruwa da tambayar da take shirin yi mishi, kafin ta tattaro duk wani ƙwarin gwiwar da za ta iya ta ce,

“In dauka?”

Ɗan daƙuna fuska ya yi duk da bai kalleta ba, yanayin na sa idanuwan shi ƙara ƙanƙancewa.

“Meye?”

Numfashi ta ja a hankali tana sauke shi da faɗin,

“Wannan hoton?”

Sake rage gudun motar ya yi yana ɗan kallon hoton da ta nuna mishi, don yasan akwai ƙananun hotuna da yawa a cikin wallet ɗin tashi, bai san ko wanne take cewa ta ɗauka ba, hoton ya kalla, da alamu a kafaɗarshi da yake nuna yana Therma III yanzun a NDA, hoton bai daɗe ba, kafin ya taho ɗin nan ne ya ɗauka, shine hoton shi na ƙarshe da ya yi zuwa yanzun. Fuskar shi har lokacin a daƙune take, kan titi ya mayar da hankalinshi yana ƙara gudun motar yadda yake da kafin ya rage. Ba tambayarta bace ta bashi mamaki, bai ga me za ta yi da passport ɗinshi bane ba, hoton da ko kyau bai yi ba.

Zuciyarta take ji ta dawo maƙoshi saboda gudun da take, amsar shi take jira, in ya ce karta ɗauka za ta mayar ta ajiye mishi, tun da daga farko ma bata san me yasa ta tambaye shi ta ɗauka ɗin ba, ta ciro hoton kuma ta ji tana son kasancewa da shi, tana son samun wani abu daga wajenshi kafin ya sake tafiya, tunda ba ranar dawowa gare shi ba. Wani abu da zai riƙeta har ya sake dawowa. Bata san kalaman da za ta yi amfani da su su fassara dalilinta ba, kusan hakan dai shi ne abinda take ji.

“Ka ji Hamma… In ɗauka?”

Ta tsinci kanta da sake faɗi, ɗany ɗaga mata kafaɗa Abdulƙadir ya yi yana juya steering wheel ɗin ya sha roundabout ɗin da ke gaban shi, ji ta yi wani abu na narkewa a zuciyarta da bata san akwai shi ba, yanayin shi da abinda ya yi da kafaɗa na sa numfashinta yi mata barazana. Da ƙyar ta iya cewa,

“In ɗauka?”

Wannan karon Abdulƙadir ɗin ne ya sauke numfashi.

“Komai ne sai na yi surutu?”

Ɗan murmushi ta yi.

“Baka ce in ɗauka ba ai…haka kayi da kafaɗunka.”

Ta ƙarasa tana ɗaga nata cikin son nuna yadda ya yi da nashin. Kai kawai Abdulƙadir ya girgiza don sun ƙaraso wajen da Yazid ɗin ya yi mishi kwatance za a yi dinner. Bai yi tunanin zai gane ba, sai dai yawon da suke sha a garin Kano ba ɗan kaɗan bane ba. Waje ya samu ya yi parking yana buɗe motar ya fice. Hoton Waheedah ta mayar inda ta ɗauko shi, tukunna ta buɗe murfin motar itama tana ficewa. Sai da ya ga ta fito tukunna ya rufe motar ya soma tafiya, bin bayan shi Waheedah ta yi don gani ta yi yana sauri sosai.

“Ka ji Hamma, in ɗauka?”

Take faɗi tana mayar da numfashin da ya sa shi juyawa ya kalleta, sauri take kamar za ta faɗi tana kai hannu ɗaya ta dafe mayafin da ke jikinta, ɗayan riƙe da wallet ɗinshi tana ƙoƙarin tattare doguwar rigarta ko za ta ƙara sauri, juyawa ya yi yana jin murmushi na shirin ƙwace mishi, bai taɓa ganin kalar Waheedah ba, bai san me yasa ya ji yana so ya ƙure rashin hankalinta ba. Sauri ya ƙara yana bi ta duk inda ya ga turmutsun jama’a duk da ga hanya nan da zai iya wucewa, sai da ya yi wajen mintina biyar a hakan har yana hango ƙofar wajen tukunna ya tsaya yana juyawa, hangota ya yi can cikin jama’a an matse ta, sai ƙoƙarin turmutsowa take da hannuwanta da suke mishi kama da sandar siririn rake.

Murmushin da yake ta dannewa ne ya ƙwace mishi, kai ya girgiza.

“Wallahi yarinyar nan bata da hankali…”

Abdulƙadir ya faɗi yana jin nishaɗin da ya rasa daga inda yake fitowa, komawa ya yi baya don ya ga alamar mutane na gab da ture Waheedah ta faɗi ƙasa, in wani ya takata yana da tabbacin karyewa za ta yi ɓal, hannunta ya kama yana janta, banda maida numfashi babu abinda take yi, hanyar da babu mutane ya bi da ita, da ƙyar take tafiya saboda bata san wahala irin wannan a rayuwarta, da ƙyar ta iya cewa,

“Hamma sauri kake kamar za ka tashi sama wallahi….”

Dariya ya ji ta kuɓce mishi.

“Lalaci ne ya yi miki yawa.”

Ya faɗi yana ci gaba da janta, binshi take da duk saurin da za ta iya har suka shiga wajen da ya ƙawatu babu laifi tukunna Abdulƙadir ɗin ya rage saurin da yake yi yana sakin hannunta, numfashi ta mayar tana fifita fuskarta da wallet din shi saboda zufar wahalar da take jin tana yi. Ƙanƙance idanuwanshi ya yi a kanta, kafin ya mayar da hankalinshi kan harabar wajen yana nemo tebir ɗin da ya ga babu kowa da kuma kujerar mutum huɗu tukunna ya ja hannun Waheedah ba tare da ya damu da mutanen dake binsu da kallo ba suka ƙarasa wajen, kujera ɗaya ya ɗan ja baya yana jan hannunta ya zagaya da ita, zama ta yi don tagaji kam.

Ta gefenta Abdulƙadir ya zagaya ya zauna yana kallon yadda take mayar da numfashi. Hannunta Waheedah ta sauke ƙasan tebur ɗin tana murzawa da ɗayan, tana jin kamar Abdulƙadir ya bar mata shatin nashi hannun a wajen da yanayin da ya yi mata tsaye a zuciya.

“Baka ce in ɗauka ba fa.”

Ta faɗi tana kallon Abdulƙadir da ya ɗauki robar ruwan da take ajiye a wajen yana murzawa da nufin buɗewa da alama. Ƙananun idanuwanshi ya kafeta da su da yasa ta sauke nata idanuwan, zuciyarta na ci gaba da tsalle a cikin ƙirjinta. Ruwan shi Abdulƙadir ya kwance, yana son ganin yadda tsoro kan cika idanuwanta, kai robar ya yi bakinshi yana shan ruwan sosai tukunna ya miƙa robar kusa da Waheedah yana faɗin,

“Ki sha ruwa…”

Hannu ta sa ta ɗauki robar ta cire murfin da bai ɗaure ba sosai tana kaiwa bakinta ta kurɓi ruwan tukunna ta mayar ta rufe, ba ƙishi take ji ba, ta sha ne kawai don ya ce tasha, don shi ne ya bata ba za ta iya ce mishi bata jin ƙishi ba. A hankali ta ajiye robar tana soma kalle-kalle ko za ta hango su Nuriyya. Amma ko alamunsu ba ta gani ba. Yazid ne ya ƙaraso wajen yana jan kujera ya zauna tare da faɗin,

“Kai jama’a, wallahi jikina ciwo yake min.”

Kallon shi Waheedah ta yi cike da tausayawa, abinda ya fi ciwon jiki ma tasan zai yi, tunda hidimar bikin ta fara shi yake zirga-zirga. Cikin sanyin muryarta ta ce,

“Sannu… Kaine baka huta ba ai Hamma…”

Murmushi ya yi yana sauke idanuwan shi akanta, tun ɗazun ya kula da yanayin fuskarta kafin su taho, bai san lokacin da abinda yake ji ya fara ba, kawai ta gitta ta gaban shi ya tsinci zuciyar shi da doka mata. Tunda ya zo wajen yake cin karo da ‘yan mata kala daban-daban, dukkansu fuskokinsu ɗauke suke da kwalliya ta ban mamaki. Yadda tata take fayau ya mishi, lokaci zuwa lokaci takan sake gyara zaman mayafinta a kafaɗarta, ya kula da a takure take jinta saboda rashin hijabinta.

“Me yasa baki saka hijab ba?”

Ya buƙata, baya son ganin yadda take a takure, ɗan murmushi ta yi mishi cikin yanayin sanyinta. Bai san ko shi kaɗai yake ganin kyanta ba, da ɗan bakinta da yasan mata da yawa zasu shafa abubuwa da dama don kalar laɓɓaansu ta yi ruwan hoda haka kamar nata, idanuwanta sun fi komai ɗaukar hankalinshi a fuskarta, yadda suke maiƙo kamar da hawaye a cikin su koda yaushe kan saka shi murmushi ko shi kaɗai ne.

“Su Zahra za su dame ni.”

Kai Yazid ya jinjina.

“Ki daina yin abinda za ki takura saboda mutane…”

Kai Waheedah ta rausayar gefe, ba zai fahimta ba, bata takura kanta bane saboda su, idan ta saka hijab ɗin yadda za su takurata zai fi yadda take a takure yanzun, ta zaɓi abinda ya fi mata sauƙi ne kawai. Abdulkadir hankalinshi ya mayar kan hidimar da ake wajen dinner ɗin, ganin hirar Yazid ɗin da Waheedah ta fara dakushe mishi nishaɗin da yake ciki.

*****

Dan mudubin da ta saka a cikin ‘yar jakar hannunta ta ɗauko tana saka shi ta ƙarƙashin teburin wajen ta duba fuskarta, kowa ya ce mata ta yi kyau, daga ‘yan gidansu Waheedah zuwa abokan wasansu da suka zo bikin, sai dai kamar koda yaushe akwai murya a ƙasan ranta da take faɗa mata kyawunta bai kai ba, kyawunta ba zai taɓa isa ba, kamar yadda ba zai cike mata gurbin abubuwa da yawa da bata da shi a rayuwarta ba. Ta jima tana tsara kwalliyarta yau, amman Waheedah na fitowa sai ta raina duk wani kyau da take tunanin ta yi. Bata san menene a tattare da fuskar Waheedah ɗin da ko hodar kirki bata ji ba.

Tana da tabbacin ba ita kaɗai take ganin wani sanyi da yake cikin idanuwan Waheedah a koda yaushe ba, yau ɗin ma ba tare da wani yunƙuri ba ta ga Waheedah ɗin ta yi kyau, da pink lips ɗinta da take jin kamar ta cire ta mayar a tata fuskar, duk da in ta kalli yadda zubin ƙirarta yake takan ji sanyi ta wani fannin, duk kyan Waheedah da hasken fatarta ba zata nuna mata dirin jiki ba, duk da ita ma a sirantakarta Allah yai mata wadattacen cikar ƙirji da Nuriyya take jin bai kamaceta ba, yadda take siririya ya kamata komai nata ya zamana a shafe, ta fito a asalin zanen lamba ɗayan ta.

Tunda suka zo takan tashi ta yawata a cikin wajen ko za ta ga Waheedah ɗin, amma ko alamunta bata gani ba, yanzun ma zagayawar take tana dube-dube, kafin idanuwanta su sauka kan Waheedah ɗin da take murmushi cikin yanayin da yakan ƙara mata kyau. Ƙaramin tsaki Nuriyya ta ja, tana jin wani ɗaci har a ƙasan zuciyarta da bata san daga inda yake taso mata ba. A hankali take ƙarasawa, idanuwan mazan duk da ta gitta yana kanta, amman ko kaɗan bata kula da su ba, gaba ɗaya hankalinta yana kan Waheedah da Yazid da alamu ya nuna hira suke yi, akwai wani namijin tare da su da bata san ko waye ba, saboda ya bata baya.

Takawa ta yi har ta ƙarasa inda teburin yake tana faɗin,

“Inata nemanki tun ɗazun.”

Saukar maganar Abdulƙadir ya ji a saman kanshi, din a bayan shi Nuriyya ta tsaya, gyara zamanshi ya yi tukunna ya juya a hankali don ya ga wacce marar tunanin ce take mishi magana tsakiyar kai, ba tare da ko sallama ta yi musu ba ballantana ta gaishe su tukunna ta yi maganar da za ta yi, idanuwan shi ya fara saukewa kan fuskarta, kafin ya ƙanƙance su yana ƙare mata kallo, wani abu yake ji yana dokawa cikin kunnuwan shi daya rasa daga inda yake jin sautinshi, don ba shi da alaƙa ko kaɗan da kiɗan da yake tashi a wajen.

Zai yi ƙarya idan ya ce bai manta da wata Nuriyya a shekarun nan ba, saurarawa ya yi don gane inda yake jiyo sautin, kafin ya gane zuciyarshi ce take dokawa a ƙirjinshi, alaƙanta hakan yake da mamakin girman da yarinyar ta yi.

“Baki iya sallama ba?”

Abdulƙadir ya faɗi har lokacin yana rasa dalilin da zai sa zuciyar shi ba zata daina bugawar da take ba. Ware idanuwanta Nuriyya take akan Abdulƙadir ɗin, bata san ya zo ba, Waheedah bata ce mata ya zo ba, duk da a shekarun nan biyu da ya tafi, ta tabbatar babu wanda Waheedah take damu da zancen shi idan ba ita ba. Bata taɓa ganinshi cikin manyan kaya ba tunda take, ba tun yanzun yake mata kyau ba, hankalin da ta ƙara yasa kyawun nashi bayyannar mata sosai yanzun. Gashi ya yi wani irin girma.

“Hamma…”

Nuriyya ta faɗi tana murmushin da Abdulƙadir din ya ji zuciyarshi ta ƙara gudun dokawar da take yi.

‘Tana da kyau.’
Wata murya ta faɗa a cikin kanshi. Sake ƙanƙance idanuwanshi ya yi kamar za ta iya karantar abinda yake tunani akan fuskar shi, idan akwai abinda ya tsana a rayuwar shi bai wuce raini ba, yara kuma a shekarun su Nuriyya suka fi jin tashen raini, saboda ƙuruciyar girma na ɗibarsu, shi bai saba yi wa kanshi ƙarya bane kawai, ya ga tana da kyau, ya kuma yi acknowledging kyan nata a ranshi.

“Sannu da dawowa.”

Nuriyya ta faɗi tana shirin dorawa da,

‘Yaushe ka zo?’

Yadda Abdulƙadir ɗin ya ɗaure fuska ya hanata fito da maganar a fili, juyawa ya yi ba tare da ya amsa Nuriyyar ba tare da gyara zamanshi, tukunna kamar an mishi dole ya ce,

“Yawwa.”

Wani abu Nuriyya ta ji ya tsaya mata a maƙoshi, har ranta ta ji daɗin ganin nashi, ya tuna mata yadda yake mata kyau na ban mamaki, a lokaci ɗaya kuma ya tuna mata yadda daga ƙawar Waheedah da suke gaisawa kan dole bata wuce nan ba, ba kuma za ta taɓa wuce nan ba, bata san me yasa yanayin ya yi mata ciwo na gaske ba. Waheedah kuma Abdulƙadir ɗin take kallo, yanayin shi na nuna alamar gajiyar da ya yi da zaman wajen.

In da idanuwan Waheedah suke Yazid ya bi da kallo, kafin ya sake mayar da kallon shi kan fuskarta, yana runtse idanuwanshi ya buɗe su tare da kauda tunanin da yake shirin dirar mishi.

‘Duka nawa Waheedah ɗin take.’

Ya faɗi a ranshi yana miƙewa.

“Ina za ka je? Yanzun fa kake faɗin ka gaji.”

Waheedah ta yi maganar tana ɗauke idanuwanta daga kan Abdulkadir ɗin.

“Zan huta Waheedah…bari in zo.”

Yazid ya ƙarasa don ya ga ba a fara rarraba abinci a wajen ba, dare na yi, sun ce kuma ba za su jima ba sosai, ya kamata a yi abinda za a yi a tashi kowa ya kama gabanshi.

“Wai ta ina kuka zauna, ni ma ina ta duba ku.”

Waheedah ta tambaya, harararta Nuriyya ta yi tana matsawa ta zauna inda Yazid ya tashi ta ja kujerar kusa da Waheedah sosai, dai-dai kunnenta ta ce,

“Ko ki faɗa min Hamma ya dawo.”

Ɗan murmushi Waheedah ɗin ta yi, muryarta can ƙasa ta amsa Nuriyyar.

“Ba mu zauna bane shi ya sa, kuma dawowar bazata ya yi.”

Ɗan taɓe baki Nuriyya ta yi, kamar rashin zaman su na hana Waheedah ɗin mata zancen Abdulƙadir, ba tun yanzun ta gane Waheedah na son Abdulƙadir ɗin ba, ita dai ce har yanzun take son raina mata hankali kamar yadda ta saba, take nuna kamar bata san abinda take ji akan Abdulƙadir ɗin so bane. Ko don ta san ba samun shi za ta yi ba shi yasa take son nuna kamar bata san tana sonshi ba oho. Duk idan Nuriyya ta yi wannan tunanin takan ji sanyi a ranta, a karo na farko Waheedah bata samu abinda take so ba, wannan karon itama zataji yanda zafin rashin samun komai da kake so yake.

Abdulƙadir zai ce ya kwana biyu wani abu bai gwada ƙarfin halinshi irin yau ba, kokawa yake da idanuwan shi kar su kalli inda Nuriyya take zaune amma hakan na neman gagarar shi. Ita kanta Nuriyyan ta ƙasan idanuwanta take ƙare mishi kallo tana ganin yadda fuskarshi take a daƙune babu alamar wasa ko kaɗan akanta. Zungurin Waheedah ta yi da alamar su tashi su bar wajen. Ɗan kallon Abdulƙadir ta yi ita ma, tana son zama da shi ɗin ko ba za su yi magana ba, tana kuma son zagayawa ta zauna cikin su Zahra don nan ne kawai za ta fi more bikin, wannan ne karonta na farko da ta taɓa zuwa wata hidimar biki.

Duk da ana yi a dangin Abba sosai, su Amatullah kan je harsu kwana, ita kam tana zama gida, duk da ko a fuska babu wanda ya taɓa nuna mata banbanci, kawai dai hayaniyar ce bata cika so ba. Miƙewa Nuriyya ta yi tana ƙara taɓa kafaɗar Waheedah ɗin da ta miƙe ita ma, hakan ya ba Abdulƙadir damar da yake nema ta kallon su biyun, sai dai idanuwan shi na kan Waheedah.

“Za mu je wajen su Amatu…”

Ta faɗi tana kallon shi, kai Abdulƙadir ya girgiza mata yana faɗin,

“Idan na tashi tafiya wallet ɗina fa?”

Sai lokacin Waheedah ma ta tuna wallet ɗinshi ce a hannunta, bin hannun nata da kallo Nuriyya ta yi wani abu na tokare mata ƙahon zuciya don alamu sun nuna tare suka zo da Abdulƙadir ɗin.

‘Allah ya rabaki da naci Waheedah.’

Nuriyya ta faɗi a ƙasan zuciyarta. Wallet ɗin Waheedah take shirin miƙa mishi, yadda ya kafeta da ƙananun idanuwanshi na sa ta kasa motsa hannunta, kallonta Abdulƙadir yake har sai da ta koma ta zauna. Bai san dalilin shi na hanata tafiya ba, kawai yadda yake jin zuciyarshi na dokawa har lokacin cikin baƙon yanayin da ya kasa fahimta yasa baya son ya zauna shi kaɗai. Ganin Waheedah ta koma ta zauna yasa Nuriyya ɗin fara shirin zama ita ma.

“Ki wuce inda za ki je.”

Abdulƙadir ya faɗi yana watsa mata wani kallo da ya sa ta barin wajen ba tare da ta ko yi wa Waheedah sallama ba, ta tsorata sosai, ranta kuma in ya yi dubu ya gama ɓaci, me yasa zai ma Waheedah magana kamar tana da muhimmanci a wajen shi, ita kuma ya yi mata magana kamar ita ɗin ba komai bace, yana nuna kamar Waheedah ‘yar uwarshi ce, bayan babu wanda bai san agola bace a gidan nasu, itama ɗin ba komai bace a wajen shi. Har ta koma inda ta fito ta zauna ranta a ɓace take jinshi, bikin gaba ɗaya ya gama fita daga ranta.

*****

Numfashi Abdulƙadir ya sauke da barin Nuriyya wajen, gaba ɗaya abinda yake ji baƙo ne a wajen shi, ba kuma zai yiwu ‘yar mitsitsiyar yarinya kamar Nuriyya ta saka zuciyarshi wannan gudun ba, kawai don tana da kyau. Baya son raini, komai tattare da Nuriyya na nuna mishi idan ta samu fuska za ta raina shi.

“Sai mu zo tare ki ta fi ki bar ni…”

Ya yi maganar yana kallonta, a lokaci ɗaya yana rasa yadda akai ita kaɗai take ganin ɓangaren shi haka, yadda yake jin ita kaɗai zai iya nuna wa ɓangarenshi haka ba tare da tunanin za ta raina shi ba. Ɗan kallonshi Waheedah ta yi tana sauke idanuwanta, don akwai wani abu tattare da nashi idanuwan da yake karya duk wata garkuwa ta jikinta, komai tattare da Abdulƙadir daban take ganin shi. Bata san me za ta ce mishi ba, don haka shiru ta yi kawai tana lafewa cikin kujerar da take zaune a wajen.

Abinci aka kawo aka ajiye kan teburin da suke zaune, abinci ne wajen kala uku a cikin faranti ɗaya, sai tsire a tsinke, har da haɗin salad a gefe, a ƙoshe Abdulƙadir yake jin shi don ya ci abinci kafin ya fito, tsiren kawai ya ɗauka yana ci, kallon shi Waheedah take yi har ya cinye, nata tsiren ta ɗauka daga cikin plate ɗin ta ta sake ɗorawa a nashi ba tare da ta ce komai ba, kallonta Abdulƙadir ya yi, ba dokawa zuciyar shi ta yi ba, ɗumi ya ji ta ɗauka wannan karon, hannu yasa ya ɗauki tsiren bai ce komai ba ya fara ci.

Lemo Waheedah ta ɗauka na roba da aka ajiye musu guda biyu, bata taɓa ganin shi da coca-cola ba tunda take, hakan yasa ta sanin ba zaɓinshi bane, don haka ta buɗe mishi Sprite ɗin tana ɗaukar abin zuƙa ta saka a ciki tana turawa gaban shi. Ɗauka Abdulƙadir ya yi, banda Hajja da Yassar, babu wanda ya taɓa mishi abinda Waheedah ɗin take mishi yanzun. Kowa a gida yana ɗaukar baya buƙatar kulawa, ko Hajja takan yi wannan tunanin wasu lokutan. Sosai zuciyar shi ta sake ɗaukar ɗumi, bai ce komai ba. Tsiren ya cinye, yana ganin Waheedah ta ɗauki abin goge hannu tana miƙa mishi, karɓa ya yi ya goge hannunshi tukunna ya ɗauki robar lemon ya sha kusan rabi ya ajiye.

“Ruwa fa?”

Ta buƙata, kai ya girgiza mata a hankali, yana kallo ta gyara zamanta kamar shi ɗin da ya ci wani abu kawai ya isheta, ita ba sai ta ci ba, numfashi ya sauke, yana kallon yadda fitilar wajen ta ƙara wa fuskarta haske. Haka suka zauna shiru, ita tunaninshi nne fal cikin ranta, shi kuma ba zai ce ga abinda yake tunani ba har mutane suka fara hada-hadar fita, da alamu an yi abinda za a yi an fara shirin tashi. Yazid ne yazo yana jansu biyun a cewar shi za a yi hotuna, binshi suka yi aka yi hotuna sosai da su tukunna Abdulƙadir ɗin ya damƙi hannunta yana fara janta. Binshi take tana kallon hannun shi da yake riƙe da nata, zuciyarta kamar zata fito waje take jinta.

Su duka biyun basu kula da Nuriyya da take bin bayansu tanajin kamar zuciyarta zata faɗo, ƙarshen abinda zai faru shi ne Waheedah ta samu abinda take so, fuskar Abdulƙadir ɗin take kallo ko zata ga alamun so, kamar yadda yake bayyane a fuskar Waheedah, amma bata ga komai ba, asalima kamar ranshi a ɓace yake. Ita dai komai zai faru kar Waheedah ta taɓa samun Abdulƙadir ɗin. Tana jin za ta yi komai don kar hakan ya faru. Wajen motar shi suka ƙarasa tukunna ya saki hannun Waheedah ɗin, ya buɗe motar da mukullin, har lokacin ba su ga Nuriyya da take tsaye a gefe ba.
Zagayawa Abdulƙadir ya yi ya shiga motar, ya miƙa hannu ya buɗe wa Waheedah daga ciki, jikinta babu ƙarfi ta shiga cikin motar tana rufe murfin, su dukansu juyawa suka yi ita da Abdulƙadir ɗin ganin an buɗe murfin bayan motar.

“Nuriyya…”

Waheedah ta fadi cike da mamaki tana ɗorawa da,

“Banganki ba.”

Cikin takaici Nuriyya ta ce,

“Ya za ki yi ki ganni dama.”

Sai da ta ji sautin muryarta tukunna ta san a fili ta yi maganar da ta yi. Yanayin muryarta Abdulƙadir ya ji bayaso, yadda ta yi maganar kamar Waheedah ta mata wani laifi ya mishi wani iri, saboda yana tare da Waheedah ɗin bai kuma ga abinda ta yi mata ba. Bai san dalilin da yasa ta buɗe mishi mota tana shirin shigowa ba, shi yasa yake da tabbacin idan ta samu fuska za ta raina shi, ga zuciyar shi da ya ji tana shirin ci gaba da dokawa.

“Ki rufe min mota…”

Ya faɗi a tsawace, yana saka Nuriyya mayar da ƙafarta da ta ɗago, tana jin wasu hawayen baƙin ciki sun tarar mata lokacin da ta rufe mishi ƙofar tana matsawa gefe ganin ya fisgi motar kamar zai bigeta. Cike da rashin jin daɗi Waheedah ta ce,

“Hamma…”

Sai da ya yi baya da motar sosai ya yi kwana tukunna ya kalli Waheedah ɗin idanuwanshi cike da rikici.

“Tare na zo da ita? Me yasa za ta buɗe min mota? Sa’anta ne ni?”

Kai Waheedah take girgiza mishi idanuwanta cike da tsoro, bata son faɗa, musamman nashi.

“Me yasa za ki kira ni kamar ban kyauta ba then? Sa’anki ne ni da za ki kira sunana kina tsareni da idanuwa kamar ban kyauta miki ba?”

Kai Waheedah ta sake girgiza mishi, yadda take jin ranshi ya ɓaci na sa idanuwanta cika da hawaye. Tsaki Abdulƙadir ya ja, shi kanshi idan za a tambaye shi asalin abinda ya ɓata mishi rai ba zai ce gashi ba. Yasan Nuriyya na da hannu a cikin ɓacin ran nashi, bai san ta yaya bane kawai. Tunda Waheedah ta lafe cikin kujerar motar ko motsin kirki bata yi ba, ta gefen idanuwanshi yake kallon tana goge fuska, yasan kuka take yi. In ya yi magana ta amsa ya ji kuka take tabbas zai watsa mata mari ya bata dalilin da zata saka shi a gaba tana mishi kuka, shi yasa bai ce mata komai ha har suka ƙarasa gida.

Ita ta fara fita daga motar, tukunna ya fito shi ma, zagayawa ya yi ta gefen da take, cikin sanyinta ta ɗago da hannu tana miƙa mishi wallet ɗinshi, karɓa ya yi yana jinshi wani iri. Buɗe wallet ɗin ya yi tukunna ya sa hannu yana zaro duka ƙananun hotunan da suke cikinta, sosai ya matsa daf da Waheedah ɗin ya kamo hannunta yana ware tafin ya saka mata hotunan a ciki tukunna yasa ɗayan hannunshi yana rufe yatsunta akan hotunan ya saki hannunta yana juyawa abinshi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 7Abdulkadir 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×