Skip to content
Part 32 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Kan kafet ya zauna yana jiran Nuriyya ta fito daga ɗaki ta ɗauko musu kular doya. Ko yaji bata da shi, ta ajiye tana samun waje ta zauna tare da faɗin,

“Masoyi ko yaji bamu da shi, in karɓo mana wajen Waheedah?”

Tun kafin ta ƙarasa Abdulƙadir yake girgiza mata kai. Bada shi za’a yi wannan ɗanyen aikin ba, ba zata ja mishi jangwam daga ɗan samun natsuwar shi ba. Kai Nuriyya ta rausayar tana sake miƙewa, kofuna ta samu guda biyu, a kitchen ɗin ta haɗa musu tea ta fito da shi ta ajiyewa Abdulƙadir nashi, ɗauka yayi ya kurɓa don ya kora doyar da ta yi mishi tsayuwar mashi a maƙoshi. Yana ɗan ɓata rai jin kamar akwai abinda ya kamata ya kasance cikin shayin da babu, ya saba da Waheedah na saka kayan ƙamshi a shayinta, yanzun kam ruwan zafi ne sai madara da milo, ko lipton ɗin ma bai samu a ciki ba.

“Wacce irin doya ce wannan Nuriyya? Babu ƙwai fa.”

Abdulƙadir ya faɗi yana saka Nuriyya haɗiye doyar da ƙyar, gashi ta yi mata wani irin salaf, shi bai ga ƙoƙarin da ta yi ba, ko da bata soyu kamar yadda ya kamata ba, sai ya duba ƙoƙarin da ta yi yai shiru.

“Na saka ƙwai ni dai.”

Ta yi maganar tana saka Abdulƙadir ɗin ƙanƙance idanuwan shi a kanta.

“Bana gani ne? Ya za ki ce min kin saka ƙwai? Ƙafafuwa ya yi ya rabu da doyar kenan.”

Yai maganar a faɗa ce saboda yadda ya ji zuciyarshi na tafasa, ga yunwa yana ji ta fitar hankali, amma rabon shi da abinci makamancin mai munin wannan tun wani aiki da yaje Makodi, shi ma wajen abinda duk ka samu shi zaka aunawa cikinka. Amma ko wannan ɗin za ka ji alamun gishiri a jikin shi. Ganin ta yi shiru yasa shi jinjina kai kawai, ba zai ƙarar da ɗan ƙarfin shi akan doya da ƙwai ba. Haka ya ɗauka yana turawa sai ya danna da shayin ya haɗiye. Iya inda ya ji cikin shi ya cika ya tsaya yana ƙarasa kurɓe ruwan shayin ya miƙe, dai-dai lokacin da ‘yan Nepa suka zaɓi su ɗauke wutarsu.

Dogon tsaki Abdulƙadir ya ja, ya yi niyyar ya biya ya siyo mai ɗazun, kwana biyu ne bai damu da ya kunna gen ɗin ba shi yasa. Dama in dai ya biyewa Waheedah ba kunnawar zai dinga yi ba, zata ce ita babu abinda zata yi da wutar tana da caji, kuma tama fitilar ta ma, sai dai in ana zafi ne don su kunna fankoki. Da fitilar wayar shi ya yi amfani zuwa ɗaki ya ɗauko wa Nuriyya tata wayar ya kunna mata fitilar ya ajiye kan kujera ya kama hanya yana ficewa daga gidan ba tare da ya ce mata komai ba. Tana jin shi har ya fita bata dai ɗago bane ba, wani irin ƙunci na ban mamaki ya cika zuciyarta fam, ba zata tuna ranar ƙarshe da wani abu ya zo wuyanta ya yi tsaye ba haka.

Har yunwar da take ji ta nemeta ta rasa, kwashe kwanonin ta yi tana mayarwa kitchen, acan ta tsaya da ƙyar ta shanye ruwan shayin tana ji kamar zata kama da wuta saboda ɓacin rai. Shinkafarta da ta ɗora ta duba ta ga ruwan ya tsane, ta kashe gas ɗin tana barinta a cikin tukunyar ta wuce ɗakin bacci, alwala ta sake yi jin har ana kiran Isha’i. A daddafe ta yi sallah tana idarwa ta janyo wayarta tana buɗe whatsapp ta lalubo chat ɗinsu da Asma, ita kaɗai ce ƙawarta da zata ce suna maganar komai a yanzun, kuma bazawara ce, a FCE suka haɗu. Ita Nuriyyar ma ce ta manne mata saboda ganin yadda ta fi kowa wayewa da kuɗi a ajin. Har suka zama ƙawaye, don Nuriyya na bala’in so ace tana tare da manyan mutane.

‘Asma mutumin nan bashi da kirki wallahi, kin san dai yadda azumi yake bani wahala ko da na yi sahur balle yau da muka makara, da ƙyar na soya doya kin ji masifar da ya sauke mun.’

Kafin kace meye Asma har ta karanta saƙon.

‘Ya ɗauko miki’ yar aiki kema, kina auren mutum kamar wannan za ki zauna kina shiga kitchen, ke banzar ina ce, narkewa za ki yi sai ya ɗauko miki ‘yar aiki.’

Numfashi Nuriyya ta sauke, duk yadda zata misalta wa Asma halin Abdulƙadir ɗin ba zata fahimta ba.

‘Kika san magana nawa nai mishi? Taurin kan shi yafi ƙarfina, ya ce ba zai ɗauko ba fa, kuma na san ba zai ɗauko ɗin ba.’

Kawunan mamaki Asma ta turo mata tana ɗorawa da rubuto,

‘Lallai ma, sai ki zauna kina kwasar baƙin ciki ai, shi yasa kin ganni, auren nan ya gama fita kaina wallahi, tunda na tungule aurena na biyu na ji ko zan yi wani ba nan kusa ba, ba zan zauna wani ƙaton banza na ɓata min rai ba. Ga mutane nan kaca-kaca suna lallaɓa ni, sha’anina kawai nake yi. Kuɗi na shigo min ta ko’ina.’

Shiru Nuriyya ta yi tana tauna maganar, da gaskiyar Asma, kafin igiyar aure ta ɗaureta da Abdulƙadir free take jinta, babu nauyi ko tunanin kowa, inda take so nan take zuwa, amma yanzun tana iya tambayar Abdulƙadir zata je waje ko baya gari ya ce ba zata ba, iya wannan ta kasa sabawa da shi, don auren Anas mayafi take ɗauka in yana nan ta ce mishi ta fita, idan baya nan ta yi gaba abinta. Balle kuma yanzun ga maganar girkin nan da sauran ayyuka, ta shiga wani irin matsatsi cikin kwanaki kaɗan da bata taɓa hangowa ba, ko kafin kwanakin nan, za su yi waya da Abdulƙadir, za su yi chatting ko yaya ne, zai zo su yi hira tana kwance a jikin shi. Amman tanajin wani abu can ƙasan ranta da ta rasa menene.

Sai yanzun take jin farin ciki ne cikakke bata da shi, ba zata ce ma ga asalin yadda yake ba, din in ta taɓa shigar shi a baya ma ta manta. Yanzun ne ƙuncinta ya ƙaru, rayuwar a cunkushe take jinta. Data ɗinta ta kashe ba tare da ta amsa Asma ba. Ta ja jiki ta haye gado ta kwanta, gara ko bacci ta samu ta yi wataƙila zuciyarta zata yi mata sanyi-sanyi. Tana nan kwance ta ji shigowar Abdulƙadir ɗin ya wuce banɗaki kanshi tsaye, ruwa ya watso ya fito ya saka gajeren wando don bai ga towel ɗinshi ba.

“Nuriyya ina towel ɗina?”

Ya buƙata, kai ta ɗan ɗago, bata ganin shi sosai saboda ta kashe fitilar wayarta, tashi kuma ya ajiye a banɗaki, ta ɗan hasko ɗakin kaɗan. Sai da ta ji zuciyarta ta doka, don tunda ta kwaso kayan daga wajen shanya, ƙulle su ta yi a cikin zanin gado ta ajiye can gefe.

“Magana nake da ke fa.”

Abdulƙadir ya faɗi a ƙule, saukowa ta yi daga kan gadon ta kunna fitilar wayarta ta taka zuwa inda ta ajiye ƙullin kayan ta kama su tana kwancewa.

“Ki miƙo min gajeran wando da singlet.”

Ɗaukowa ta yi, duk sun zama kamfala, musamman gajeran wandon da yake ruwan madara, mayar da shi ta yi ta ɗauko mishi na kakin Sojoji shi ma duk ya yi roɗi-roɗi. Ta dunƙule su waje ɗaya ta ƙarasa ta miƙa mishi, kamar hakan yan nepa suke jira da bugun agogo na alamun cikar ƙarfe tara na dare suka kawo wuta, haske ya gauraye ɗakin, yana dai-dai da sauke idanuwan Abdulƙadir akan kayan ya kuwa ware su yana buɗe kayan sosai.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un!”

Ya faɗi yana jujjuya wandonshi.

“Bansan akwai kaya masu zuba ba, na haɗa duka.”

Kai Abdulƙadir yake girgizawa.

“Aikin ki kenan, kullum baki san abu ba, ko yaushe uzurinki baki sani ba. Hankalin ki bai baki ba’a haɗe gaba ɗaya kaya wajen wanki ba? Idan kin haɗa wandon nan da sauran kaya, me yasa zaki haɗa farare da masu kala? Ke mahaukaciya ce?”

Ya ƙarasa maganar yana kallonta.

“Kuskure ne kowa na yi.”

Nuriyya ta faɗi cike da gajiya.
“Karki fara min rashin kunya, wallahi karki fara cewa za ki faɗa min magana Nuriyya, baki sanni ba ko? Baki san halina ba har yanzun, shi yasa nake magana kina ƙoƙarin mayar min.”

Shiru ta yi idanuwanta na cika da hawaye, gefen gado ta koma ta zauna, ta ɗauka ya yi shiru, ai kamar lokacin ya fara faɗa, sai da ya yi mai isar shi tukunna ya koma banɗakin, ranta in ya yi dubu a ɓace yake, kwanciya ta yi tana tsiyayar hawaye masu zafin gaske, ko kaɗan ba wannan rayuwar ta hango ba, bata saba ana mata faɗa ba, duk bala’in Anas ba koyaushe yake kulata ba, sai ta kai shi ƙarshe, shi ma in ya ga ta hayayyaƙo mishi sai ya yi shiru ya ƙyale ta ko ya fice daga gidan. Amma yadda Abdulƙadir ya nuna yana gab da kwaɗa mata mari shi yasa ta yi shiru, ba sai kowa ya gaya mata ba zai ɗauki kaso ɗaya cikin abinda Anas ya ɗauka ba.

Fitowa ya yi har lokacin ran shi a ɓace yake ji shi yasa ya ƙara yin wanka. Ya zagaya kan gadon ya hau yana kwanciya, baya Nuriyya ta juya mishi, tsintar kan shi ya yi da bai damu da hakan ba, Waheedah ce dai bata isa ta juya mishi baya ba ko me ya yi mata, ko gajiya ta yi da kwanciyar zata juya hannu sai dai suyi musayar waje. Ko a jikin shi take kuwa, sai dai in bacci yayi, da ya tashi ya ganta sai ya kamata ya juyata.

“Ki kashe mana fitila.”

Ya faɗi yana juya kwanciyar shi, yana jinta ta sauka daga kan gadon ta kaso fitilar ta dawo. Alarm ya saka a wayar shi ya ajiyeta gefe, Addu’ar bacci ya tofa a jikin shi yana lumshe idanuwan shi duk da alamun yunwa da yake ji.

*****

Ƙarfe uku da rabi alarm ɗin da ya saka ya tashe shi, sai da yayo brush da alwala tukunna ya tashi Nuriyya. Rigar kirki ya ɗauka ya saka a jikin shi, yana ganin yadda ta koma kamar Kampala itama, sallar nafila ya tayar yanayin raka’a huɗu. Sai lokacin ma Nuriyya ta sauko daga kan gadon da ƙyar ta shiga banɗaki ta wanko fuskarta, ta wuce kitchen. Miƙewa Abdulƙadir ya yi yana fita shi ma ya nufi ɓangaren Waheedah ya tura tare da sallama ya kuwa same shi a buɗe, ƙwan ɗakin ya kunna yana sakata runtse idanuwanta sosai alamar hasken ya shigar mata cikin su, kafin ta buɗe su tana ƙanƙancewa akan Abdulƙadir.

“Na ce ki dinga kulle kofa, bakya jin magana ko Wahee?”

Cikin bacci ta turo mishi bakinta da har lokacin da alamun janbaki ja, miƙa ta yi , muryarta cike da bacci ta ce,

“Na manta ne.”

Hararar ta Abdulƙadir ɗin ya yi yana sakata yin murmushi.

“Kinfi so in ta surutu kan abu ɗaya ne kawai.”

Ya ƙarasa ya ɗauki Qur’ani dama shi ya je ɗauka, ya tako ya kashe fitilar.

“Kabar min a kunne.”

Waheedah ta faɗi, sake kunna mata ya yi yana jan numfashi kamar yana son zuƙar iya ƙamshin da zai iya da yake cikin ɗakin kafin ya fita tare da ja mata ƙofar. Ɗakin Nuriyya ya koma ya samu waje ya zauna ya buɗe Qur’anin shi ya soma karantawa cikin sanyin murya, yana wajen har Nuriyya ta shigo ta ajiye musu plate ɗin shinkafa sai miya da ta zuba a wani kwanon, sai da Abdulƙadir ya ƙarasa shafin da yake karantawa tukunna ya rufe Qur’anin, su Hajja kawai ya yi wa Addu’a sai iyalan shi da ‘yan uwan shi, Yassar ne na farko. Janyo jikin shi yayi yana matsowa inda Nuriyya take zaune, yanayin shinkafar a idanuwan shi ya ga kamar bata dahu ba, hakan yasa shi ɗan ɗibowa da cokali ya saka a bakinshi ya ɗan tauna ya ji ta giri-giri.

“Wallahi ba zan ci shinkafa a tsai-tsaye haka cikina ya kumbura ba, bata dahu ba.”

Ya faɗi yana ajiye cokalin, kallon shi Nuriyya ta yi.

“Ki ci a bakin ki, da tun jiya kika dafa mana yanzun sai ki yi warming kawai.”

Plate ɗin Nuriyya ta ɗauka tana miƙewa da sauri ta fice daga ɗakin, don duk wani abu na zuciyarta gaya mata yake ta juye mishi shinkafar sannan ta kwantara mishi farantin tangaran ɗin a saman kai kowa ma ya huta.

“Kece da asara Waheedah, don ni bawai ya dameni bane.”

Nuriyyar ta faɗi a fili da bala’in ɓacin rai, da ta yi tunanin kwantara mai faranti ya mutu duk su huta. Cikin tukunya ta mayar da shinkafar ta ƙara ruwa ta yi tsaye. Idan ta koma ɗakin ya sake magana tana jin ko me ya fito daga bakinta faɗa mishi zata yi sai dai in gabas zai saka kanta ya yanka yayi. Ta gaji har cikin ƙasusuwan ta, ya fara fita daga ranta daga shi har auren, a wuya take jin su sun mata tsaye. Takai mintina sha biyar har sai da ta fara jin ƙaurin shinkafar tukunna ta kashe gas ɗin, ko ta dahu ko bata dahu ba haka zai haƙura ya ci, ko ya fito ya dafa wata.

Sake zubawa ta yi ta ɗauka tana komawa ɗakin ta ajiye. Ɗan ɗiba Abdulƙadir ya yi yana sakawa a bakin shi, ta ɗan rissina ba kamar ɗazun ba. Duk da bata kai yadda Waheedah take dafa musu laushi ba, kallon shi Nuriyya take yi tana jiran ta ji ya sake cewa bata dahu ba, don tabbas wannan karon zata kwantara mishi farantin tangaran ɗin. Sai ta ga bai ce komai ba, miyar ya ɗibo yana zubawa a gaban shi tare da cakuɗawa, ba sosai yake son abinci mai zafi ba, hakan ne yasa shi bai yi saurin kaiwa bakin shi ba, ta riga shi zuba miyar ta juya ta ɗiba ta saka a baki. Wani irin ƙarni ta ji cikin ƙofofin da suka haɗa bakinta da hancinta, sannan miyar ta sauka cikin bakinta da wani ɗanɗano marar kan gado, tana taunawa da ƙyar ta haɗiye.

AbdulKadir ta kalla daya ciko cokali tanajin kamar ta ce mishi karya ci, ya kuwa auna cikin bakin shi, lokaci ɗaya yanayin fuskar shi ya sauya, bai tauna shinkafar ba ya haɗiye yana wani irin sauke numfashi har lokacin bakin shi a gauraye yake jin shi. Mama na musu abinci marar daɗi, amma yana ciyuwa, bakajiny kamar za ka shaƙe ka wuce lahira.

“Kasheni kike so ki yi Nuriyya… Da raina kike so ki kashe ni.”

Abdulƙadir ya faɗi yana ɗorawa da,

“Baki iya abinci ba, bansan ya akai ban taɓa sani ba sai yanzun… Wacce irin miya ce wannan?”

Kai Nuriyya ta saddar ƙasa tana jin kunyar da ta shiga ta danne ɓacin ran da take ciki.

“Shi yasa kike cewa in ɗaukar miki ‘yar aiki?”

Kai ta ɗan ɗaga mishi a hankali, kai Abdulƙadir ya jinjina don abinda ba zai taɓa yiwuwa ba ne ba, ba don kar a tayata aiki ba, ko don baya goyon bayan mazan da suke ɗaukar wa matan su ‘yan aiki ba, ko da babbar sallah yana wa Hajja magana a ɗauko ma Waheedah ta soya mata nama. Bai ga dalilin da zai sa shi ya ci abincin ‘yar aiki ba.

“Ki koya don ni ba zan ci abincin’ yar aiki ba.”

Kallon shi Nuriyya ta yi sosai, tana tunanin ta inda yake so ta fara koyon girki, kowa yake so ta je ta samu ya koya mata.

“Kafin ki kashe ni don Allah ki dinga mana mai da maggi.”

Abdulƙadir ya ƙarasa maganar da sigar roƙo yana ɗorawa da,

“Yanzun ma tashi za ki yi ki zubo min da mai…”

Bata yi musu ba ta miƙe, numfashi Abdulƙadir ya sauke yana jin komai ya birkice mishi, faɗa ya so ya yi sosai, amma ƙananun maganganu ba halayyar shi bace ba, bai kuma saba komai sai ya yi magana a kai ba, sun samu matsala da yawa yau da Nuriyyar baya so su ƙara samun wata cikin daren nan. Don ya san halinsu ne, ko me zai faru iya su ne, babu shaiɗan ɗin da za su laɓe a bayan shi tunda watan azumi ne. Bai shirya sanin yana da halaye marassa kyau ba, gara ta san yadda zata yi ta koya, ya dai cika da mamaki, ya ɗauka ko yaya ne mata sun iya girki tunda abune da suke yi yau da kullum.

Da mai ya ci kuwa yana mayarwa da ruwa ya miƙe, yana jin yadda idanuwan shi sukai zuru-zuru duk da bai kalli mudubi ba. Bacci suka ɗan koma kafin Asuba. Sa’adda ya dawo masallaci Nuriyya har ta sake komawa bacci. Shi kam zama ya yi yana yin azkar har rana ta fito ya mayar da sallah raka’a biyu ta nafila. Sai daya wuce ɗakin Waheedah yana samunta tana linke dardumar ta da alama ita ma sai lokacin ta tashi. Don ita ta saba mishi da yin nafilar bayan Asuba, ko kaɗan bata wuce ta, ta tunasar da shi tarin ladan da yake cikin hakan.

Yanzun har ta zame mishi jiki, cikin sanyin muryarta ta gaishe da shi, ya amsa da,

“Kun tashi lafiya?”

Sai da ta fara jinjina mishi kai tukunna ta amsa tana ɗorawa da,

“In ka je gida yau ka taho da Fajr.”

Kallonta Abdulƙadir ya yi, sosai take kewar yaron nata.

“Ni na ce miki zan je gida ne? Ki kirasu a kawo miki shi.”

Kai ta girgiza mishi.

“Ni kunya nake ji ai.”

Ɗan murmushi ya yi.

“Lallai yarinyar nan, ni ne sarkin rashin kunya ko?”

Dariya Waheedah ta tsinci kanta da yi tana girgiza mishi kai.

“Haka kike nufi mana, ba zan je ba to, in kina kewar shi ne ki kira su da kanki.”

Ya ƙarasa maganar yana juyawa don bacci zai je ya yi dama zai duba ya suka tashi ne.

“Don Allah ka ɗauko min yaron.”

Juyawa Abdulƙadir ɗin ya yi yana harararta ya fice daga ɗakin ya ja mata ƙofa, dariya take sosai, har ranshi ta san harara ce yake ganin yana yi, amman idanuwan shi basu da girman da za su juyu har su yi hararar, bata taɓa gaya mishi baya yi dai-dai ba. Sai dai tasha dariyarta kawai. Ikram ta ɗauka tana cire mata kaya, don wanka zata yi mata, itama ta yi, sai su zo su yi baccin.

*****

Bacci yayi har wajen sha biyu sannan ya tashi, ya watsa ruwa ya fito yana zaune a bakin gado, Nuriyya na kai tana danne-danne a waya, don group ɗinsu an turo wasu laces masu bala’in kyau. Kuma duk wanda yake cikin group ɗin ya ce yana son guda ɗaya, ita kaɗai ce bata ce a ajiye mata ba, don ta ji Hajiya Kaltume mai siyar da kayan ta ce kuɗi hannu ne, ba zata bayar da bashi ba wannan karon, da sai ta ɗauka sai ƙarshen wata. Gashi kowa sai magana yakeyi ita ba zata siya ba, tana ta kallon su ne bata san me zata ce ba, har a rainata.

“Masoyi.”

Ta kira cikin sanyin murya, tana saka Abdulƙadir ɗin kallon ta.

“Ka ga wani lace.”

Ta faɗi tana nuna mishi wayar, kallo ya yi yana jinjina mata kai.

“Ya yi kyau.”

Ya amsa a taƙaice yana ɗaukar tashi wayar da take ajiye a gefe. Murmushi Nuriyya ta yi don ta ga alamar zata yi nasara.

“Dubu arba’in da biyu.”

Kai kawai Abdulƙadir ya jinjina mata bai ce komai ba ya ci gaba da danna wayar shi, da sauri ta ce,

“In ɗauka za ka biya kuɗin?”

Ɗago idanuwan shi Abdulƙadir ya yi yana kallonta kamar bata da hankali.

“Wai me kika ɗauke ni ne Nuriyya? A bishiya nake tsinko kuɗi ko me? Kin manta kuɗina da kika kashe min, kin sani sai da na taɓa wasu dana ajiye don wani abin, har kina min maganar in sai miki abin dubu arba’in da biyu. Ina nagan su?”

Kallon shi take don in jikinta zai zama kunnuwa ba zata tabae yarda ba shi da su ba, da ce mata ya yi ma bazaie bayar ba sai ya fi mata sauƙin yarda. Wayar shi Abdulƙadir ya ci gaba da dannawa yana nemo text ɗin albashin shi ya ajiye wayar kan gadon yana tura wa Nuriyya data ɗauka.

“Bansan kallon me kike min ba, amma ni ba wasu kuɗi gareni ba, kin ga albashina nan duk watan duniya, a ciki nake duk hidimata, ƙaton gidan nan kuɗin allowance ne na wasu ayyuka, haka motata, bawai albashina bane, su kuma sai ayi shekaru ba’a same su ba. Idan ban taɓa faɗa miki ba yau ki sani, ni bamair kuɗi bane, cikin layin masu rufin asiri ma a tsakiya za’a sakani.”

Abdulƙadir ya ƙarasa yana miƙewa ya fisge wayar shi daga hannun Nuriyya yana ficewa daga ɗakin ya barta a zaune gaba ɗaya jikinta ya gama mutuwa. Tabbas yau kallon kitse ake ma rogo ne ya tabbata a kanta, wannan albashin na Abdulƙadir sam-sam ba shi bane burinta na hamshaƙin mijin da take son aure.

“Taɓɗi…”

Ta faɗa ranta a jagule, kwata-kwata yadda ta hango Abdulƙadir ba haka yake ba. Daga halayen shi har kuɗin shi, ita da bata hango cikarta shekara ɗaya a gidan ba tare da ta yi motar kanta ba. Da wannan yagalgalallen albashin yaushe har ya tara kuɗin da zai siya mata mota. Wani ƙunci take ji yana taso mata tun daga yatsan ƙafarta yana mata zaune a ƙirjinta. Har ma faɗa mata yake shi ba kuɗi yake da su ba don karta sa ran zai mata wani abin arziƙi. Har ranta take jin babu wanda ya cuceta sai Waheedah, babu babbar makira irinta, ita ta dinga nuna mata kamar tana cikin daular rayuwa, ita kuma ta dinga mata hidima kamar Abdulƙadir ɗin wani hamshaƙin mai kuɗi ne, ita taja mata duk wannan abin da take ciki, don ita ta haska mata Abdulƙadir ɗin ta ga ƙyallin shi har ta kwaɗaitu da auren shi, amma da duk mintina take ganin abinda bata so a tattare da shi.

Gani ta yi baƙin ciki zai mata katutu, ga whatsapp ɗin da ta buɗe har ta private Hajiya Kaltume ta mata maganar siyan lace ɗin nan, hankalinta ya ƙara tashi, hakan yasa ta janyo system ɗinta, drawer ɗin gefen gado ta janyo ko ta saka earpiece ɗinta a ciki, taga wata leda da batasan ta ajiye ba, ɗagota ta yi ta ga kuɗi ne a ciki, sai da zuciyarta ta yi wata irin dokawa, warware ledar ta yi tana zazzago kuɗin kan gadon, ganin su tayi da yawa sosai, da sauri ta tashi ta saka mukulli ta kulle ƙofar ta dawo, kuɗi ne masu yawan gaske don ba’a ɗaure su ba, hakan ya sa ta tunanin da alama ana zararsu ne. Tasan Abdulƙadir ɗin kan ciro kuɗi ya ajiye ana ɗiba, don ta sha zara kuma bai taɓa ganewa ba tunda bai mata maganar ba.

Duk da zuciyarta na dokawa, wani abu ƙasan ranta na faɗa mata kar ta yi, dubu arba’in da biyu ta ƙirga ta ware su a gefe, ko kwatar kuɗin bata ga alama sun girgiza ba, tasan ba ƙirgawa zai yi ba, da sauri ta gyaggyara su ta mayar cikin ledar tana nannaɗewa kamar yadda ta gani ta mayar ta rufe drawer ɗin. Wanda ta ɗiba ɗin ta miƙe ta samu jaka ta zuba su a ciki. Kafin ta zauna ta ji ana ƙwanƙwasawa, da yake ta saba ɗibar kuɗin Anas ko ɗar bata ji ba, ta je ta buɗe mishi ƙofa, bai ce mata komai ba ya raɓata ya wuce.

‘Namiji munafuki.’

Ta faɗi a ranta, dama akance namiji ba zai taɓa nuna maka samun shi ba, yau ta ƙara yarda, yanzun ya nuna mata wani alert kamar mai gaskiya, jibi kuɗin da ta gano. Dama tanata tararrabi anya ace ba shi da kuɗin da take tunani. Tana kallo ya buɗe drawer ɗin ya ɗauki ledar ya sake zuwa ya fice, ɗakin ta tura. Ta koma kan gado tana ɗaukar wayarta ta ba Hajiya Kaltume amsa,

‘Ni banda kudi a banki, Cash ne bansan ya za’a yi ba, gashi yau ba zan fita ba, ni nake da girki.’

Ba’ayi mintina biyu ba Hajiya Kaltume ta amsa ta,

‘Ki bani address ɗin zan turo yaro ya zo ya karɓa.’

Tura mata ta yi kuwa tana komawa kan gado ta zauna. Ko da ƙirgawa Abdulƙadir ya yi ya gane an ɗiba sai ta bashi haƙuri, faɗa ne zai yi sai ta toshe kunnuwanta ta ƙyale shi, in aka kawo lace ɗin ta ɗaura a jikinta zai wanke mata haushin shi da zata ji na ɗan wani lokaci. Ko mintina sha biyar ba a yi ba, ta ga kira yaron har ya iso ƙofar gida. Kuɗin ta ɗauka ta saka hijabi ta leƙa ta kai mishi, saidar ya ƙirga a gabanta tukunna ta dawo gida, tana jin wani abu ya ɗan kwanta cikin ɓacin ran da ta shiga.

*****

“Hamma kasan fa bani da lafiya, gashi ana rana, ina azumi ka fito da ni.”

Abdulƙadir ya faɗi yana miƙa mishi ledar kuɗin da sun kai kwana goma a ajiye a wajen shi, don Yassar ɗin ya yi cinikin mota zai sake wata, tashi na ta bashi matsala, daya ciro kuɗin sai cinikin bai yiwuwa ba, yana jin ƙyuyar komawa banki ya kuma san halin shi, ko Hauwa yaba ta ajiye sai ya bi ya karɓa ya kashe. Amma idan Abdulƙadir ɗin ne ba zai bashi ba sai dai ko in lalura. Yanzun ma dan yacee ga motar an kawone an gama komai, kuɗin ne kawai zai basu, tashi motar ma har wanda ya siya ya ɗauka tukunna Abdulƙadir ɗin ya fito da kuɗin.

Ya ɗauka ma ɗakin Waheedah ya ajiye, don ya je yana nema, ta taya shi basu gani ba, kafin ya tuna ɗakin Nuriyya ya ajiye.

“Kai kamar ba soja ba.”

Ƙanƙance mishi idanuwa Abdulƙadir ya yi.

“Ina gida yanzun, ka barni. Kuma ma don ina soja sai akace duk wahala in dinga jureta?”

Kai kawai Yassar ya girgiza mishi yana karɓar kuɗin ya basu. Suna tsaye aka ƙirga

“Dubu ɗari huɗu ne babu arba’in da biyu.”

Da mamaki Yassar ya ce,

“Ban gane ba.”

Don yasan kuɗin shi ya ciro su da kan shi.

“Eh babu dubu arba’in da biyu”

Abdulƙadir ya kalla yana faɗin,

“Ka taɓa kuɗin nan ne Abdulƙadir?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza don bai ma ji me suke faɗa ba, hankalin shi na kan wayar shi da yake duba saƙo.

“Me ya faru?”

Ya buƙata yana mayar da hankalin shi kan Yassar ɗin.

“Wai basu cika ba, babu dubu arba’in da biyu.”

Ɗagowa Abdulƙadir ya yi daga jikin motar shi.

“A ƙara ƙirgawa dai.”

Ya faɗi saboda baya son abinda ya fara zuwa kan shi ya tabbata, sam baya so, mutumin kuwa bai musu gardama ba, wannan karon duk a tare suka ƙirga kuɗin, babu dubu arba’in da biyun. Wallet ɗin shi Abdulƙadir ya zaro ya ɗauko ATM ɗin shi ya miƙa wa Yassar.

“Kasan password ɗin.”

Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi kafin ya ce,

“Bana son iskancin banza da wofi.”

Kai kawai Abdulƙadir ya jinjina yana mayar da ATM ɗin inda ya ɗauko shi, ba tare da ya ce komai ba ya buɗe murfin motar shi, ran shi ya daɗe bai ɓaci ba irin haka.

“Abdulƙadir me ya faru? Ka fito daga motar nan mu yi magana.”

Yassar ya faɗi ganin yanayin fuskar Abdulƙadir din, amma mukullin motar shi ya murza yana tayar da ita, duk maganar da Yassar ɗin yake mishi bai ji ba ya fisgi motar yana hawa titi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 31Abdulkadir 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×