Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Talatin Da Hudu

4
(1)

<< Previous

Bai san inda zai nufa ba, da duk daƙiƙa da yadda zuciyar shi take ƙara mishi zafi. Tsintar kanshi ya yi a ƙofar gidan su. Aka buɗe mishi ya shiga da motar shi ciki, kan shi tsaye ɓangaren Hajja ya nufa, ya shiga babu ko sallama. Fajr da ya rugo ya riƙe mishi ƙafafuwa ya kama yana ɗaga yaron cik ya sauke shi a gefe tare da faɗin,

“Fajr ka barni ni kam, ina Hajja?”

Shagwaɓe mishi fuska Fajr ya yi.

“Tana bacci.”

Kai Abdulƙadir ya jinjina ma Fajr ɗin yana wucewa ya barshi a wajen. Ɗakin Hajja ya nufa ya ƙwanƙwasa, ci gaba ya yi har sai da ya ji muryarta da ke cike da bacci ta amsa shi, tukunna ya tura ɗakin ya shiga. Kallo ɗaya ta yi mishi ta gane a hargitse yake.

“Abdulƙadir…”

Ta kira cike da damuwa tana ɗora mwa da,

“Lafiyar ka?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza mata yana kallon ta kamar zai fashe da kuka, yanayin da yasa Hajja miƙewa zaune.

“Me ya faru?”

Tsayen dai yake yana ƙara ƙanƙance mata idanuwan shi.

“Kai min magana mana Abdulƙadir.”

Takawa yayii ya zauna ƙasa yana ɗora kanshi akan ƙafar Hajjan kamar ƙaramin yaro.

“Hajja na yi kuskure…. Na sake biyewa zuciyata na yi kuskure babba.”

Cikin tashin hankali Hajja tace,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…me kai ma Waheedahr kuma?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza mata.

“Ba Waheedah bace ba, na saki Nuriyya…Hajja na sake ta.”

Numfashi Hajja ta sauke, duk da saki ba abin so bane, musamman ita mace da ta fahimci abinda hakan yake nufi. Amma zata yi ƙarya in ta ce bata ji wani sanyi a ƙasan zuciyarta da ta san ba Waheedah bace ba. Ta yi iya ƙoƙarinta na ganin ta bata kasance cikin irin iyayen mijin da ke ɗaukar tsana ta babu gaira babu dalili su ɗora akan matan yaransu ba, amma sam zuciyarta ta kasa aminta da auren Abdulƙadir ɗin da Nuriyya. Ko kaɗan bata son yarinyar, hakan dai ba zai hanata faɗa mishi gaskiya ba.

“Subhanallah, me ya faru Abdulƙadir? Cikin azumin nan? Yanzun ita tana ina?”

Kan shi ya ƙara kwantarwa a jikin cinyarta, ƙirjin shi zafi yake kamar ana hura mishi wuta. Maganganun Nuriyya sun ruguza wani abu a cikin zuciyar shi da bai ma san da shi ba. Komai ya yi mishi tsaye, ya kasa yarda cewar ya saketa ɗin, duk da ko ba gaba ɗaya ya datse igiyoyin auren su ba, ta faɗa mishi maganganun da yake da tabbacin alaƙarsu ta samu tangarɗa ta har abada, ba dai zai hana zuciyarshi jin zafin abinda ya faru ba.

“Bata sona, abinda aurena zai iya bata shi take so.”

Ya furta muryar shi na fitowa da wani irin yanayi da yasa Hajja runtsa idanuwanta tana sake buɗe su.

“Wannan kawai bai isa zama dalili ba.”

Ɗago kai ya yi yana kallon Hajja, kafaɗun shi ya ɗan ɗaga mata.

“Na riga na yi m, na saketa, saki uku Hajja, dalili ko babu dalili ba zai canza hakan ba.”

Wannan karon ware idanuwanta Hajja ta yi.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…. Abdulƙadir saki uku? Idan Allah ya jarabceka da son ta kuma fa?”

Ta ƙarasa maganar hankalinta a tashe, don sam abin bai mata daɗi ba, ko me ya faru kuwa, duk yadda bata son shi da Nuriyyar. Murmushi ya yi me sauti yana ɗan dafe kan shi da yake sarawa kafin ya sauke hannun shi yana ƙanƙance idanuwan shi akan Hajja, wanne soyayya kuma banda wadda ya yi mata tasa ƙafafuwa ta ture, itacee mace ta farko da zuciyar shi ta fara doka wa, ita ce mace ta farko da ya fara tunanin zaman aure da ita.

Baya jin akwai wata jarabta ta ɓangaren soyayyar Nuriyya da zai same shi ya bashi mamaki. Ita ce macen da ya so, sai dai ba ita bace macen da ta dace da shi. Yadda za ka so abu ya zamana ba alkhairinka bane ba zai daina bashi mamaki ba. Inda yasan hakan zai faru, da yana da ilimin sanin abinda gobe zata haifar ba zai soma auren Nuriyya ba, ciwon da zai ji na hakan ba zai taɓa kai wanda yake ji yanzun ba.

“Magana nake maka fa.”

Hajja ta ce tana saka Abdulƙadir ɗin miƙewa tsaye.

“Hajja ni ƙiirjina ciwo yake min, don Allah ki yi haƙuri…”

Ya ƙarasa maganar yana zagayawa ya miƙa hannu ya ɗauko pillow ɗaya daga kan gadonta ya jefa shi a ƙasa. Sai da ya cire takalman ƙafafuwan shi tukunna Hajja ta kula da su. Sabon shi ne shiga ko’ina da takalma tun yana da ƙarancin shekaru, bakinta har ya gaji da magana kan hakan. Yanzun ma da idanuwa take bin shi har ya zauna kan kafet ɗin ɗakin nata ya gyara pillow ɗin shi ya kwanta.

“Abdulƙadir…”

Ta kira.

“Hajja kunyar Hamma nake ji shi yasa nazoe wajen ki…Allah zan tafi in baki barni ba.”

Miƙewa ta yi, ta riga da ta san halin Abdulƙadir ɗin, duk da alamu sun nuna yana cikin hali, in ba da kanshi yake son yin maganar ba ba zai yi ba. Yana jinta ta fice daga ɗakin, gyara kwanciyar shi ya yi yana lumshe idanuwan shi ko ƙirjin shi zai rage zafin da yake yi. Bacci ya yi har la’asar, har ya je masallaci ya dawo yana jin ƙirjin shi bai daina zafi ba. Ɗakin Hajja ya sake komawa ya yi kwanciyar shi. Tana shigowa ta ganshi ta ce,

“Wai kai Abdulƙadir ba za ka tashi ka tafi gidan ka ba?”

Sake juya kwanciya ya yi.

“Yanzun Hajja don na yi aure shikenan bazan zo gida duk sa’adda nake so in kwanta in huta ba?”

Ya ƙarashe maganar kamar zai yi kuka, don bai ga dalilin da zai sa Hajja ta dinga korar shi shi da gidan Abban shi ba, amma da Waheedah ta zo babu wanda ya ce ta koma sai da ya zo ya dinga binta yana bata haƙuri.

“Idan kuma yaji na yo fa? Sai ki koreni ki ce in koma?”

Dariya Hajja take da Abdulƙadir ɗin bai ga dalilinta ba, don shi da dukkan gaskiyar shi yake maganar da yake yi ɗin.

“Allah ya shirya min kai Abdulƙadir.”

Hajja ta faɗi har lokacin tana dariya ta fice daga ɗakin, sai da ya gaji da kwanciyar tukunna ya fito zuwa falon yana zama Fajr na shigowa da nama a hannun shi yana ci.

“Paapi ka ga, Mami ta bani.”

Ya ƙarasa maganar yana zuwa ya zauna a jikin Abdulƙadir ɗin.

“Mami ta kyauta, ka gode.”

Sake shigewa jikin Abdulƙadir ɗin Fajr ya yi yana kwanciya sosai, yana sa Abdulƙadir ɗin faɗin,

“Kaifa ka cika son jiki Fajr, baka azumi za ka bini ka danne ni”

Baisan inda yaron ya koyi son jiki ba, gashi ɗan mitsitsi da shi abinda yake so shi zai yi, maganar shi ba zata sa Fajr ɗin ya sauka daga jikin shi ba, sai dai in dukan shi zai yi. Amma wani ido ko magana ba ko yaushe suke tasiri akan Fajr ba, bai san inda ya kwaso halayen nan ba, don shi ba haka yake ba. Anan ya zauna har aka kira sallah, dabino da kankana ya ɗan sha ya yi alwala, Fajr na rigimar sai ya bi shi.

“Ka tafi da shi mana.”

Cewar Hajja.

“Bai ga takalmin shi ɗaya ba, har an yi raka’a ɗaya.”

Abdulƙadir ya faɗi yana zame hannun Fajr ɗin daga cikin nashi, yaron na buɗe baki ya fara kuka, wani irin mari Abdulƙadir ya ɗauke shi dashi da yasa Hajja fitowa daga kitchen ta kama Fajr ɗin.

“Abdulƙadir baka da hankali? Wannan ai sai ka ji mishi ciwo.”

Ta ƙarasa tana ɗaukan Fajr da jikin shi ko ina ke ɓari, yama kasa fitar da sautin kuka. Ficewa daga gidan Abdulƙadir ya yi don bai da amsar ba Hajja, baya son kukan banza marar dalili, Fajr ya cika rigima har ta banza, inda Hajja ta san dukan da yake sha da ba zata yi magana don ya mare shi ba. Da ya dawo masallaci ma ruwan shayi kawai ya iya sha, don ko yunwar ma baya ji, tukunna ya yi ma Hajja sallama ya sake ficewa ya shiga motar shi yana nufar gida. 

*****

Ba zata ce ga iya lokacin da ta ɗauka a ƙofar gidan ba, zafin ranar da ake ƙwallawa shi yasa ta yanke hukuncin takawa zuwa bakin hanya ta tare wata napep ɗin ta shiga zuwa gidansu. Lokaci zuwa lokaci take saka hannu tana share ƙwallar da ke zubo mata. Bayan kayanta da aka gudu dasu, tasan akwai wani abin da yake nuƙurƙusarta da bata son tsawaita tunani a kai. Ɗari biyu ta ba mai adaidaita sahun tana wucewa ta shiga gida da sallamar da Mama ta amsa mata. Tana zaune kan kujera a ƙofar ɗaki tana tsintar shinkafa.

“Ki ɗauko tabarma mana.”

Mama tace mata ganin Nuriyya ɗin na shirin zama ƙasa kan siminti, bata yi musu ba ta shiga ɗaki ta ɗauko tabarma ta zo ta shimfiɗa. Gaisawa suka yi, Mama ta ci gaba da tsintar shinkafarta ba tare da ta ko kalli inda Nuriyyar take ba, ballantana kuma ta ce mata wani abu. Gaba ɗaya jikinta Nuriyya ta ji ya ƙara mutuwa, wasu sabbin hawayen na ƙara zubo mata da ba zata ce ga dalilinsu ba.

“Mama ya sakeni, Abdulƙadir ya sake ni.”

Ta furta wani abu na tasowa daga ɗan yatsan ƙafarta yana zuwa ƙirjinta ya samu wajen zama. Sosai yanzun abinda hakan yake nufi ke zauna mata, ga yunwar azumin da ke bakinta data fara ƙulle mata ciki, ga shinkafar da ta ga Mama na tsinta ta kuma tabbatar da ita ɗin ce abincin buɗa bakinsu, sai ɗan kunu da ƙosai da ba kullum ake samu ba. Da yanzun tana ɗaki a kwance da fanka in sun kawo wuta, komin ta lalace kuma akwai nama a fridge ɗinta, ko soyawa zata iya yi. Watanta kusan tara rabonta da shinkafar hausa.

“Allah ya rufa asiri ya kuma kyauta.”

Mama ta faɗi tana miƙewa da farantinta ta kai ɗan ƙaramin kitchen ɗin gidan ta ajiye. Itacen ta iza tana buɗe waken ta ga ko alamar dahuwa bai yi ba, shi yasa ta ɗora shi da wuri in ta dafa sai ta ajiye. Anjima ruwa zata ƙara da ya tafaso ta zuba shinkafa. Ba don ta yi wa auren Nuriyya da Abdulƙadir ɗin baki ba, amma har a ƙasan ranta ta ji alamun babu inda zai je, ko ba don auren cin amana ba ne, Nuriyya na da son zuciya da son abin duniya da in bata bi a hankali ba zai hanata zaman aure, don zata ci gaba da gina aurenta akan hakan, duk namijin da ya gane kuwa da wahalar gaske ya ci gaba da zama da ita.

Hidimarta Mama ta ƙarasa ta shige ɗaki tana barin Nuriyya anan zaune, ganin hakan yasa itama ta tashi tana komawa ɗakinta na da, yana nan yadda yake babu abinda ya canza, banda ‘yan kayan sawa da aka ajiye. Ta kuma san na Mama ne, tunda ita bata da yara mata, nata duk maza ne, ɗakinsu kuma daban yake. Jakarta ta ajiye ta samu waje kan katifa tana kwanciya, a jikinta take jin banbancin katifar da ta gidan Abdulƙadir. Wasu sabbin hawayen na sake silalo mata, musamman da tunanin Waheedah na can kwance a ɗaki tana jin daɗin ta bar mata gidan, sai ta ji wani malolon baƙin ciki ya taso mata kamar zata haɗiyi zuciya ta mutu ta huta.

Kafin yamma wani zazzaɓin tashin hankali ya rufe ta, banda tsinuwa da fatan tsiya da take mai napep ɗin da ya yi mata ɗibar albarka babu abinda take yi. Ga kuma tashin hankalin abinda zai faru idan Baba ya dawo gidan ya ganta, don sosai kashedin shi yake dawo mata. Ita kam bata ga inda zata fara zuwa ba a yanzun, bata da wani waje da ya wuce nan ɗin, haka ta wuni juye-juye. Ta ƙulla ta saƙa, tare da addu’o’i kala-kala, cikin su har da na samun mijin da ya fi Abdulƙadir komai tana gama iddarta ta yi aure inda zata huta ta shaƙata, amma ta san hakan ba zai yiwu babu suttura ba. Ta yanke hukuncin siyar da duka kayan kitchen ɗinta, ta siyi kaya sai ta ajiye sauran kuɗin tana kashewa a hankali kafin ta samu garan da zata wanka.

Wannan tunanin shi ya nutsar da ita har aka kira sallar Magriba, tukunna ta fito daga ɗakin ta yi alwala tana sake komawa, sa’adda ta idar da sallah, Mama ta kawo mata kunu da ƙosai da take ta jin ƙamshin shi tana kwance, hakan ya tabbatar mata da ba siyowa aka yi ba, Mama ta soya da kanta. Ci ta yi don ya mata daɗi sosai, rabon da ta ci abu mai nutsuwar wannan tun girkin Waheedah. Tas ta shanye kunun ma da ya sha kayan ƙamshi ta samu waje ta zauna, wata nutsuwa da ƙoshi ne kaɗai ke samar da ita na saukar mata.

Tana jin sallamar Baba ta ji hanjin cikinta ya hautsina, komai ya tsaya mata. Tashi zaune ta yi, dama ɗakin fitilar wayarta ce ta haska, itama kashewa ta yi, ta yi zaune cikin duhun tana jin zazzaɓinta ya dawo sabo. Ba zata ce ga iya lokacin da ta ɗauka a ɗakin ba kafin ta ji Baba na faɗin,

“Auren ta kaso? Shi ne kika barta ta zauna min a gida? Ban gaya mata ta nemi wani wajen ba?”

Baba ya ƙarasa maganar yana ɗaga labulen ɗakin da Nuriyyar take ciki.

“Fito….ai na faɗa miki idan kika kaso auren nan ki nemi wani wajen, na faɗa miki bazan kaffarar rantsuwa ta ba.”

Wani irin kuka Nuriyya take tunda Baba ya fara magana. Mama ce ta kama labulen daga hannun shi tana saukewa da faɗin,

“Ai kam haƙuri za ka yi kai azumin kaffara saboda babu inda zata je.”

Da matuƙar mamaki Baba yake kallon Mama, kai ta ɗaga mishi, don sosai iyaye suke wannan kuskuren, ta san ɓacin rai abu ne da ba’a iya guje mishi idan ya zo. Amman bata ga dalilin da zai sa iyaye su gindaya sharaɗi kan cewar idan yara suka tsallake su nemi wasu iyayen ko kuma su bar musu gida ba. Akwai dalilin da yasa Allah ya zaɓi ya basu amanar yaran, bata ce babu haƙƙin iyaye akan yaransu ba, amma akwai haƙƙin yara akan iyaye suma. Amana ce mai wahalar riƙewa, amana ce da riƙonta yake cike da ƙalubale kala-kala.

Amma korar yara daga gida da nufin son su gane kuskurensu ba hanyar gyara bace ba, lokuta da dama hakan baya janyo komai banda ƙara lalacewar su, ga fushin iyaye da ko basu kore su ba zai ci gaba da bibiyarsu har sai lokacin da suka furta sun yafe ko suka ƙudurta a ransu, ga tangaririya a filin duniya ba tare da tudun dafawa ba. Ba mata kaɗai hakan yake faruwa da su ba, har mazan, da yawa in ba su faɗa sace-sace don su sami abin ciyar da kansu ba, za su fara shaye-shaye don rage damuwa, da duk wani abin ƙi da zai iya fin wanda ya yi sanadin korar su daga gida muni. Akwai ƙaddarar da take tafiya da son zuciya, kamar ta Nuriyya, halin da take ciki laifinta ne, amma hakan baya nufin ba ƙaddararta bace ba.

Da yawan mutanen da za su zage ta idan sun ji halayenta marasa kyau su kansu basu wuce jarabta da irin ƙaddararta ba, bata saka musu baki a cikin al’amuran su, amma tana da yara, duk da maza ne, ba za’a haɗu da ita a yi wannan kuskuren da Baba yake shirin yi ba.

“Ina kake so ta je? Idan ta bar gidan nan ina kake so ta je? Bazan maka magana akan cewa hannunka baya ruɓewa ka yanke ka yarda ba, saboda ban taɓa yarda da wannan kalaman ba, lokacin da azaba zata isheka, idan baka roƙi wani ya yanke maka ba, za ka samu wuƙa ka yanke da kanka, neman sauƙi abu ne mai ban mamaki.”

Cewar Mama tana ɗorawa da,

“Amma na san yara amana ne a wajen iyayen su, na san idan ta sa ƙafa ta fita daga gidan nan ka gaza a riƙon wannan amanar. Ban taɓa saka maka baki akan Nuriyya ba, yaune na farko saboda yau ɗin ne nake ganin za ka yi kuskure mai girma, in kuma ina da wani muhimmanci a wajenka za ka haƙura ka barta tunda bata da inda ya fi nan ɗin, babu kuma wanda ya wuce ƙaddara daga ni har kai.”

Jim Baba ya yi yana tattauna maganganun Mama ɗin, zuciyar shi na tafasa sosai, amma ya san gaskiya ce ta fada mishi. Babu inda Nuriyya take da shi da zata je, bakuma zai kyauta wa mahafiyarta ba, don sun yi zaman da baya manta ta a duk ɗaga hannuwan shi da zai yi don gabatar da addu’a. Wucewa ya yi ɗakin ba tare da ya ce komai ba sai addu’ar neman shiriya da yake wa Nuriyyar a ran shi. Numfashi Mama ta sauke tana ɗaga labulen tare da faɗin,

“In ya huce ki je ki same shi ki bashi haƙuri, sai a kira Abdulƙadir ɗin a ji idan abinda zai gyaru ne.”

Hawayen fuskarta Nuriyya ta share tana girgizawa Mama kai.

“Saki uku ne.”

Labulen Mama ta saki tana girgiza kanta kawai. Addu’a ce kawai abinda ya rage tsakaninta da Nuriyya, alwalar isha’i ta ɗaura ta shige ɗaki kawai. Nuriyya kuwa kwanciya ta yi, bata fi mintina goma ba aka kawo wuta. Cajin wayarta ta saka ta fito tsakar gida ta wanke fuskarta ta koma ta yi sallar isha’i. Sai take jin ta ɗan samu natsuwa yanzun da tasan babu inda zataje. Baba ba zai koreta ba, zata samu ta san yadda zata yi ta kwaso kayanta ta siyar da su, don bata son shigowa da komai gidan sai kuɗinta da kayan sawa.

Lambar wayar telanta ta laluba ta yi mishi magana ta whatapp don akwai kayanta wajen kala biyar da zai kai mata gida washegari, ta yi mishi kwatancen nan gidan ta ce ya kawo mata, su zata samu ta ɗan yi amfani da su kafin ta je ta kwashe kayanta ta siyar ta siyi wasu na kece raini. Ta kuma yanke hukuncin Asma ce kaɗai zata san aurenta ya mutu, itama don ta tayata siyar da kayan kitchen ɗin ne, sauran sai ta samu mijin da za su girgiza da jin shi tukunna zata sanar da su don su zo biki. Biki zata yi na alfarma ba irin na Abdulƙadir da akai ta yi mata tsegumin ko ‘yar walima bata yi ba. Da wannan tunanin na sabuwar rayuwar da zata yi bacci mai ƙarfi ya yi awon gaba da ita.

*****

Yana shiga gida ya hango Yassar tsaye da waya a hannun shi yana dannawa, parking yayi ya fito daga motar.

“Kai nake shirin kira, Waheedah ta ce min ka fita tun ɗazun ba ka dawo ba…kar in sake ina maka magana kana kama hanya ka wuce, don ubanka kasan yadda ka ɗaga min hankali? Yanzun ma mashin na hau na zo.”

Juya mishi idanuwa Abdulƙadir ya yi.
“Na sha ruwa lafiya… Kai fa?”

Ya faɗi yana saka Yassar ɗin watsa mishi wani kallo.

“Bana son iskancin banza… Me ya faru?”

Numfashi Abdulƙadir ya ja yana fitarwa tare da jingina bayan shi da motar shi, sosai yake jin kunyar Yassar ɗin, muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Don Allah Hamma ka yi haƙuri, tun ɗazun na so in je amma kunyarka nake ji shi yasa na kasa zuwa…. Wallahi kunyarka nake ji har yanzun… Don Allah ka yi haƙuri.”

Kai Yassar yake girgiza mishi tunda ya fara magana, in duka kuɗin Abdulƙadir ya kashe zai haƙura da sake motar, idan fiye da hakan yake buƙata zai siyar da motar ya ba shi duka kuɗin, ya fi ƙarfin wata dukiya a wajen shi, ballantana dubu arba’in da biyu, shi ya biyo bayan shi ne saboda ya ga yanayin ɓacin ran da ya shiga.

“Don Allah ka daina wannan maganar Abdulƙadir, kasan ka fi ƙarfin wannan kuɗin a wajen ai.”

Kai Abdulƙadir ya jinjina.

“Na sani, amma ajiya ka ba ni saboda baka son taɓa kuɗin.”

Abdulƙadir ya ƙarasa yana kallon Yassar ɗin.

“Ni kam kabar maganar kuɗin nan, ka yi zuru-zuru, duk azumin ne?”

Kai Abdulƙadir ya girgiza wa Yassar ɗin.

“Banajin daɗi Hamma, ƙirjina ciwo yake min.”

Cike da damuwa Yassar ya ce

“Ko za mu koma asibitin ne? Ka ga shi yasa suka so ka kwana rannan don su ga yanayin jikin, kuma baka shan magungunan ko?”

Numfashi Abdulƙadir ya sake saukewa, kafin ya sauke muryar shi yana faɗin,

“Na saki Nuriyya… Saki uku.”

Cike da rashin fahimta Yassar yake kallon shi, don kamar daga sama haka ya ji maganar.

“Bangane ka saketa saki uku ba, baka da hankali ne kai? Ina tunanin ka ya tafi? Rashin hankalin naka har ya kai haka?”

Kai Abdulƙadir yake girgiza mishi.

“Baka san me ta yi min ba Hamma, baka tambayi me ta yi min ba, kar kai min faɗa ba ka ji duka abinda ya faru ba.”

Sosai Yassar yake kallon Abdulƙadir ɗin, sam bai ji daɗin jin maganar ba, ba don yana son Nuriyya ba, sai don saki abu ne mai girman gaske.

“Koma me ta yi maka, shi yasa addini ya ba da maslaha akan ka fita ka bar mata gidan idan ka ga zata tunzuraka, karka yanke hukunci sai ka samu nutsuwa ka sauka daga fushin da ka ɗauka. Macece ita, ba ko yaushe take da hankali ba, komai ya fito daga bakinta faɗa maka zata yi.”

Shiru Abdulƙadir ya yi, don maganganun Yassar ɗin ciwon da yake ji suke ƙara mishi, cikin taushin murya Yassar ya ci gaba da faɗin,

“Ni kam sam ban ji daɗi ba, kuma baka kyauta min ba Wallahi, na ɗauka mun yi magana ta fahimta akan wannan zuciyar taka da rashin neman shawara?”

Wani abu Abdulƙadir ya haɗiye da ya yi mishi tsaye a wuya.

“Ka yi haƙuri.”

Ya faɗi yana sa Yassar ɗin kallon shi, yanayin Abdulƙadir ɗin na karya mishi zuciya, da ka ga alamun shi kasan yana cikin jimamin rabuwa da Nuriyya ɗin, amma ƙaddarar su ce ta zo da haka. Da yawan lokuta mutane biyu kan haɗu don su koyar da juna wani darasi kafin ƙaddara ta raba hanyar su, hakan ne abinda ya faru da zaman Abdulƙadir ɗin da Nuriyya.

“Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi.”

Cewar Yassar yana ɗorawa da,

“Karka saka damuwa sosai a ranka, babu wanda yake wuce ƙaddarar shi, yin aure da mutuwar shi lokaci gare su, Allah bai nufi zamanku zai tsawaita ba.”

Kai Abdulƙadir ɗin ya jinjina.

“Hakane Hamma… Na gode.”

Sallama Yassar ɗin ya yi mishi, babu yanda bai yi da ya sauke shi gida ba, amma ya ƙi, cewa ya yi ya je ya kwanta ya huta, yana buƙatar ya samu wadataccen hutu. Bai wani ja maganar ba, don kan shi ciwo yake sosai, har bakin ƙofa dai ya raka Yassar ɗin tukunna ya dawo ya shiga gida da sallama. Bai ga Waheedah a falo ba, hakan yasa shi ya wuce cikin ɗaki ya sameta a kwance. Kan gadon ya ƙarasa ya ɗauki Ikram da ke bacci ya sauketa ƙasa kan nata gadon, ya matsa sosai ya rungume Waheedah ta baya yana sauke wani irin numfashi da bai san yana riƙe da shi ba.

Hannunta ta ɗora kan nashi da ke cikinta, ta lumshe idanuwanta, tana jin yadda zuciyarta ke buɗe mata duk wata ƙofa da ta taɓa son shi tare da dokawa da ƙarfin gaske, tana jin yanayin ƙaunar shi da kusancin shi da ita hakane kawai yake haifar da ita, tana jin yadda ta yi kewar yanayin sosai.

“Sadauki.”

Ta furta cikin yanayin da ya manta rabon da ya ji ta faɗi, da sauri ya kamata yana juyo da ita, sosai ya ji daɗin hasken da yake gauraye da ɗakin, idanuwanta yake kallo yana ganin soyayyar shi a ciki, yana ganin yanayin daya manta rabon da ya ganshi a tare da ita. Wata ajiyar zuciya ya sauke yanajin ciwon da yake ji ya rage mishi, rungumeta yayi sosai a jikin shi.

“Na gode…”

Ya faɗi ba tare da yasan dalilin yin godiyar ba, kawai ya tsinci kan shi da son yi mata godiyar ne. Ɗumin jikin shi ne ta ji kamar ya wuce misali, hakan yasa ta taɓa wuyan shi, tana sauko da hannunta ta saka cikin rigar shi tana taɓa jikin shi sosai.

“Zazzaɓi kake yi.”

Ta furta tana ɗago kanta daga jikin shi tana kallon idanuwan shi da yake ƙara ƙanƙance mata.

“Tashi ka sha magani.”

Daƙuna fuska ya yi yana girgiza mata kai.

“Ba zazzaɓi nake yi ba, bana jin daɗi ne kawai.”

Ɗan ɗaga mishi girarta ta yi duka biyun, duk da sanin dalilin rashin jin daɗin nashi na saka wani irin kishi na ban mamaki tsirga mata.

“Shi ne zazzaɓin ai, ka ci abinci?”

Kai ya sake girgiza mata.

“Banajin yunwa, na sha shayi a wajen Hajja.”

Wannan karon zame jikinta Waheedah ta yi daga nashi.

“Ka je gidan shi ne baka taho da Fajr ba Sadauki?”

Hararar ta ya yi.

“Ni ne bani da kunya ai, ki je ki ɗauko shi da kanki.”

Murmushi ta yi kawai tana sauka daga kan gadon.

“Karki wahalar da kanki, ni babu maganin da zan sha.”

Abdulƙadir ya faɗi, komawa kan gadon ta yi tahau tana saka hannunta cikin aljihun shi ta ɗauki mukullin motar shi, Hajja ta ce mata yana asibiti rannan, ta tabbatar an bashi magunguna, suna mota don in ya shigo da su gida zata sa ya sha. Aikam magungunan ta ɗauko a mota tana dawowa da su ɗakin ta ajiye kan gado.

“Ba fa zan sha magani ba saboda lafiyata ƙalau.”

Har lokacin bata yi mishi magana ba, fitowa da magungunan ta yi kala huɗu, akwai paracetamol a ciki, shi kaɗai ta ballo guda biyu tana sakawa a hannunta ta miƙa mishi, akwai ruwa a roba kusa da ita da ta shigo da shi ta ɗauko ruwan, ƙunshin hannunta yake kallo, shi yasa shi karɓar maganin yana haɗawa da hannunta ya riƙe.

“Ka sha don Allah, shi kaɗai ne ai.”

Ɗauke idanuwan shi ya yi daga hannunta yana sauke su cikin nata.

“Bazan sha ba gobe.”

Ya yi maganar cike da tabbaci, kai kawai Waheedah ta ɗaga mishi, tana kallon shi ya shanye maganin yana haɗe fuska kamar zai yi amai, sosai ya daƙuna fuskar shi yana turo mata laɓɓan shi, murmushi kawai ta yi, fushi yake dole saboda ta sa shi ya sha magani. Ko Fajr in ta bashi magani da kuka da komai yake sha, ko Abdulƙadir ɗin yana nan baya tayata, ce mata zai yi magani ba shi da daɗi. Tsaf halayen shi yaron ya kwashe. Bata matsa mishi ya ci abinci ba, don ta san in har da kanshi zai ce mata baya jin yunwar to ba zai iya cin abincin bane ba. Ita ta kashe musu fitilar ɗakin tukunna ta hau gadon, duk da tana riƙe a jikin shi, ko kaɗan ya nemi bacci ya rasa, ita kanta ba baccin take yi ba, rashin baccin shi ya hanata yin nashi, suna kwance har ƙarfe uku kafin su tashi su ƙarasa raya daren ta hanyar gabatar da sallolin nafila.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×