Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Talatin Da Uku

0
(0)

<< Previous

Tunda ta gama baccin safenta ta gyara ɓangarenta tsaf, sannan ta yi wanka ta shiga kitchen. Ɗan wanke-wanken da take da shi ta yi. Ikram na kwance cikin kekenta tana bacci. Fridge ɗin ta duba ta ga tana da naman rago, kawai sai marmarin tuwon semo da miyar ɗanyar kuɓewa ya kamata. Fito da shi ta yi don ya huce, ya yi ƙanƙara, ta ɗauki Ikram suka fito ta kulle kitchen ɗinta. Ɗaki ta koma ta kira Naziru a waya ta ce ya je ya siyo mata ɗanyar kuɓewa ya kawo mata in ya zo sai ta bashi kuɗin. Hakan kuwa aka yi, daɗewar da ya yi har bayan Azahar yasa ta ɗauka ma ya manta don ta san shiriritar shi.

Kitchen ɗin ta koma ta samu kwando ta juye kuɓewar a ciki, tana da yawa, in ta ajiyeta ma kafin ta sake yin wani tuwon zata iya yin yaushi, gara ta yi miyar ta saka a fridge. Tasan zata waiwayeta. Ajiyewa ta yi ta wuce ɗaki ta ɗauko wayarta ta dawo, Tafsir ɗin Sheikh Albani ta kunna kan yadda zaka ƙara gyara ibadunka. Ta rage ƙarar dai-dai kunnenta tunda ba earpiece ta saka ba, duk da ita kaɗai ce ta riga ta saba. In akwai abinda yake saurin sosa mata rai bai wuce tana zaune waje wani ya kunna waƙa ko wani abin ya ƙure sauti ba. Sam mutane basa tunanin ko wanda yake kusa da su baya jin daɗin su abinda suke saurara ɗin, ko baya cikin yanayin son saurarar komai.

Wasu suna ganin ai karatun Qur’ani ne, musamman lokacin azumi, kuma za ka iya shiga haƙƙin wani, shi yasa aka sauƙaƙa da akai earpiece, ka saka ka ji duk abinda kake so dai-dai kunnuwanka ba tare da ka takura kowa ba. Kuɓewarta ta wanke ta ɗauko abin gogawa ta ɗauraye shi ma ta ajiye su gefe don ta ga naman ya saki, gara ta ɗora shi ta dafa, har cefane ta ɗauko, lokacin ba wahala gare shi ba, gashi tana son dafa zoɓo. Aikinta take a nutse ta ga giccin Abdulƙadir da wani irin sauri da ya saka ta leƙawa, yanayin tafiyar shi ya tabbatar mata da ranshi a ɓace yake sosai.

“Allah ya rufa asiri.”

Ta furta a hankali tana komawa ta ci gaba da aikinta. Abdulƙadir kuwa duk azumin da yake bai hana shi zira kai ta murfin mota yana wa mutane masifa a hanyar shi ta zuwa gida ba, don gani yake sun tare mishi hanya, sun hana shi isowa da wuri, wayar shi ma da Yassar ya ishe shi da kira kasheta ya yi. Ba zai tuna ranar ƙarshe da ya ji kunyar Yassar irin yadda ya ji ba yau. Tunda can ma akan Yassar ne ya fara sanin yana iya jin nauyin wani ɗan adam haka, kan shi tsaye zai iya faɗa wa Hajja abu, har Abba ma, ko ya tambaye su abu, amma Yassar sai ya jima yana juya maganar kafin ya samu ya fito da ita. Lokuta da dama yana jin kamar shi ne ya kamata ya fito ciki ɗaya da Yassar, su kwanta a mahaifa ɗaya saboda kusancin da yake tsakanin su.

Sai dai haka Allah Yakan tsara lamurra, wani lokacin ma sai ka ga shaƙuwa a tsakanin mutanen da ba su haɗa jini ba, Yassar na ɗaya daga cikin abinda yake godewa Allah da samu a duk sallar shi ta duniya tunda ya mallaki hankalin shi. Ta ina Nuriyya take so ya fara haɗa idanuwa da Yassar ɗin? Me take so ya ce mishi bayan yau? Ta mishi abubuwa da yawa, ƙanana da manya da ya ɗauki idanuwa ya saka mata, abubuwan da duk ya tsara wa kanshi ba zai ɗauke su a wajen macen da yake aure ba. Sai dai ita ɗin ba Waheedah bace ba, yana jin ranar da duk zai waiwayi abinda ta yi mishi da wahala alaƙarsu ba zata samu tangarɗa ba, shi yasa yake kauda kai yana ƙyaleta.

Yau ne ta kai shi saman kanta ba jikin bango ba ma, da shi ta taɓa, da kuɗin shi ne, wataƙila ba zai ji abinda yake ji ba yanzun, da kuɗin ma na wani ne daban da yasan in ya mayar mishi zai karɓa duk abin zai zo da sauƙi. Kuɗin na Yassar ne, kuma ko jiya sai da ya yi mishi mitar bashi da kuɗi, ya yi wa Hauwa gyaran mota, yana so ya ƙara tara wasu kuɗin itama ya sake mata wata, zai iya yin abubuwa da dubu arba’in da biyun shi, ko kayan abinci zai siya ya ajiye, ko ya yi hidimar sallah da take gaban shi cikin kwanaki ƙasa da talatin. Abdulƙadir na da tabbacin ba shi kaɗai bane yake tsara komai na rayuwar shi. Ciki har da yadda kashe kuɗin shi yake tafiya.

Bakin ƙofar ɗakin Nuriyyar ya tsaya yana riƙe da handle ɗin ƙofar, idanuwan shi ya lumshe ko zai tuna wani dalili da yasa zuciyar shi doka mata tun daga farko amma ya rasa, ba halayenta bane, saboda bai san su ba lokacin da ya fara sonta, bai san su ba lokacin da zuciyar shi ta sake doka mata bayan ya rufe shafinta daga rayuwar shi. Bai san ko kaɗan cikin halayyarta ba lokacin da ya amince ma aurenta, halayenta sun fito mishi ne bayan ya aureta, a ƙasa da sati ɗaya bayan ya aureta ya fara kula da su, sun sake fito mishi bayan ta tare a cikin gidan shi, zama ya haɗa su, tana saka shi fahimtar dalilin da yasa mutane ke cewa zaka iya shafe shekaru da mutum ba ka san ko da kashi ashirin cikin halayen shi ba, saboda akwai ɓoyayyayun halayen da ba mutum bane yake ɓoye su don kar a sani, basa fitowa ne sai zama na a kwana a tashi ƙarƙashin inuwa ɗaya ya kama suke bayyana.

Auren Nuriyya ya saka shi fahimtar abubuwa da dama duk da ba zama yakan yi yai tunani akan hakan ba. Akwai kuma dalilin da yasa akan auren Nuriyyar bayan ta tare Hajja ta kira shi a waya tana ce mishi,

‘Soyayya ce take ɗibarka yanzun Abdulƙadir, kuma ita kaɗai bata isa ta riƙe aure ba, akwai lokacin da za kui tashi ku duka ku nemi ɗigon soyayyar nan ku rasa, wallahi idan har ba ku gina zaman ku akan abinda ya girmi soyayya ba, in kuka shiga cikin irin yanayin nan zai muku wahala ku samu daidaito. Ba zance maka kacokan zaman aure kan ginu akan halaye bane kawai, amma su ɗin kan zama ginshiƙi mai girma na zaman aure. Ga ka ga Nuriyyar nan, itama ga ta ga ka nan, ba baki zan maka ba, amma akwai halayenka da nake da yaƙinin Waheedah ce kaɗai macen da zata iya jurewa.’

Baya son ya tsaya tunanin hakanne a baya, don zai saka tunanin cewa sai da kowa da yake son shi ya yi mishi magana akan auren Nuriyya ɗin ya yi biris da su, ko Yasir da ba shiga harkar juna suke ba sai dole sai da yace mishi,

‘Da yawan lokuta mukan so abinda ba alkhairin mu bane ba, za ka iya son abu ka rayu babu shi, za ka iya ƙin abu ka rayu da shi Abdulƙadir. Don kana son yarinyar nan baya nufin in baka aureta ba wani abu zai sameka, da yawan lokuta mukan yi haƙuri da abinda muke so don zaman lafiyar mu.’

Shima ya yi watsi da shi, kashe wayar shi ma ya yi. Shi yasa duk wani ƙaramin abu da Nuriyyar zata yi mishi baya ɗaga kai, yasan tunanin maganganun da kowa ya faɗa mishi kan aurenta ne zai danne shi. Ya kuma tsani kalaman da ke biyo bayan da na sani na ‘Sai da wane ko wance suka faɗa min ban ji ba’ wani lokuttan kuma sai ka ji ana ‘Dama ance min kaza da kaza’.  Duk baya son wannan tunda ba za su canza abinda ya riga da ya faru ba, shi yasa yau yake tsaye bakin ƙofar yana so ya tuna koma menene da zai saka shi ya ɗan sauka daga dokin zuciyar da yake kai, ko da kuwa sharrin shaiɗan ne, amma azumi ake yi, babu wani shaiɗan a cikin abinda yake ji sai Nuriyya. Numfashi ya ja yana fitar da shi da wani irin ɓacin rai ya tura ƙofar, a tsaye ya sameta tana linke hijab. Kan lace ɗin da ta yi saurin jefa hijab ɗin sama idanuwan shi ya fara sauka kafin ya ji kamar ta watsa ma wutar da take ci a zuciyar shi galan ɗin fetir.

“Me yasa?”

Ya tambaya muryar shi can ƙasan maƙoshi yana kafeta da idanuwa.

“Me yasa me?”

Nuriyya ta tambaya tana son yin kamar bata fahimci abinda yake nufi ɗin ba, duk da yanayin shigowar shi yasa ta gane yasan ta ɗibi kuɗin, ita tabarmar kunya da hauka akan naɗeta. Tana bacci ma wayarta ta fara ihu, ta ɗauka ta ga Hajiya Kaltume ce tana faɗa mata yanzun za’a kawo lace ɗin ma, don ya iso, ta ɗauka sai dare. Ta karɓo kenan ta shigo ta tsaya waya da Asma, ta manta shaf bata kulle ƙofar ta ɗauke lace ɗin ba ta ji shigowar shi, da yasa zuciyarta yin wani irin tsalle, shi yasa ta jefa hijabin a sama tana fatan Allah yasa bai gani ba. Tana kallon yadda yasa hannun shi ya dafe goshin shi yana runtsa idanuwan shi kafin ya sauke hannun yana ware su a kanta.

Sosai yake kokawa da duk wani abu dake zuciyar shi yana tuna mata da in ta manta akwai igiyar aure a tsakanin su da Nuriyya da ta hana mishi dukanta sai ya fitar mata da yadda ko a gaba ba zata yi ƙoƙarin raina hankalin wani mai suna irin nashi ba, akwai azumi a bakin shi, watan Ramadan ne, wata mai albarka da yake cike da son yafiya da aikata alkhairai. Amma tafin hannun shi har ƙaiƙayi yake ya amsa tambayar rainin hankalin da ta yi mishi akan kuncinta, marin da sai ta ga taurari.

“Ki tauna maganar da za ki faɗa min Nuriyya, Wallahi gab nake da wanka miki mari. Karki gwada wasan banzan ki a kaina yau, ba zai mana daɗi ba. Me yasa kika ɗaukar min kuɗi?”

Kallon shi Nuriyya ta yi tana jin zuciyarta na ci gaba da dokawa, bata taɓa ganin shi cikin irin wannan yanayin ba, amma a ƙasan tsoronta akwai yadda maganganun shi suka ɓata mata rai, ta ya zai ce zai mareta tana matar shi, ita alƙawari ta yi wa kanta daga ranar da namiji zai taɓa ta ya taɓa auren shi tunda ita ba jaka bace da zai kamata yana duka.

“Wai wanne kuɗi?”

Ta tambaya tana ƙarasa kwance sauran hankalin da Abdulƙadir yake ji yana riƙe da ƙwaƙwalwar shi ya kuwa ɗauke ta da wani irin mari da yasa ta jin kamar idonta ɗaya ya faɗo, da sauri ta saka hannu ta dafe idon tana lalubawa ta ji ƙwayar na cikin shi, wani irin numfashi take ja tana son kukan ya ƙwace mata ko zai rage mata raɗaɗin da take ji, Abdulƙadir na kallon ta, wani irin dana sani yake ji yana shirin lulluɓe shi, alƙawari ya yi wa kan shi da ba zai sake taɓa wata mace da zata kasance ƙarƙashin igiyar auren shi ba, saboda yadda addini ya haramta mishi hakan, yadda al’ada bata yardar mishi da hakan ba, amma Nuriyya ta saka shi ya karya alƙawarin nan da azumi a bakin shi.

“Na faɗa miki ki tauna maganar da za ki faɗa min baki ji ni ba, uban me yasa ni da gidana ba zan ajiye kuɗi inda nake so ba? Me yasa za ki ɗauka? Me yasa za ki ɗaukar min? Rashin hankalin ki bai faɗa miki kuɗin zai iya kasancewa ba nawa bane? Ban nuna miki salary na ba Nuriyya?”

Ba sosai take jin maganganun Abdulƙadir ɗin ba duk da hargowar da yake yi kamar ƙiris yake jira ya rufeta da duka.

“Abinda nake miki bai isheki ba sai kin ɗaukar min kuɗi? Kin ɗauka ban san kina zarar min ba duk idan na ajiye? Ban miki magana bane saboda ina guje mana zuwa inda muke yanzun. Kin san kuɗin wa kika ɗauka? Kin san kunyar da kika sakani a ciki? Me kike so in ce mishi? Ni na ɗauki kuɗin? Ko ke kika ɗauka? Me yasa za ki min haka?”

Zuwa lokacin raɗaɗin da take ji ya fara yin ƙasa, sai hawayen baƙin cikin da suke silalo mata suna busar da tsoron shin da take ji, tunda ba mala’ikan mutuwa ba ne ba, ta ɗauka ya fi ƙarfin dubu arba’in da biyu da har zai zauna yana mata tijara akan su.

“Ni na ɗauka, saboda na tambayeka ka hanani shi yasa na gani na ɗauka, me yasa kai baka faɗa min ka ajiye kuɗin ba? Me yasa kai baka faɗa min ba naka ba ne ba?”

Nuriyya ta tambaya cike da tsantsar rashin kunya tana saka wani murmushin takaici ƙwace wa Abdulƙadir ɗin.

“Akan dubu arba’in da biyu ne zaka mareni? Ni ba jaka bace da zan zauna kana jibgata.”

Kai Abdulƙadir ya girgiza, idan yana ganinta a gaban shi, idan ta ci gaba da magana zai daketa sai ya ji wani daga cikin ƙasusuwanta ya yi ƙara alamar karyewa, zai daketa sai ta kasa ko nishi balle alamar kuka, ballantana ta sami bakin da zata tsaya tana kallon shi cikin idanuwa tana mishi rashin kunya, zai zaɓar musu abinda zai fi musu sauƙi, muryar shi a hankali ta fito kamar yana ɗanɗana duka kalaman shi.

“Kije gida Nuriyya, ki je gidan ku ki ɗan huta, nima in huta.”

Sheƙeƙe Nuriyya take kallon shi, tana jin auren shi yau kamar sartse a maƙoshinta, bambancin su da Anas na bayyanar mata.

“Ni babu inda zanje babu wata shaida, sai inje musu saƙaƙa in ce me? Yaji na yo? Ka sake ni mana sai in tafi da Hujja.”

Ta ƙarashe maganar tana watsa mishi wani kallo kafin ta ɗora da,

“Ni ba kai bane mijin dana ɗauka na aura, ba haka Waheedah take faɗarka ba, ba haka take nuna ka ba.”

Da mamaki Abdulƙadir yake kallon ta.

“Kin aureni akan abinda Waheedah take faɗa ne dama?”

Don sosai yake son ya kwantar da ɓacin rai ya fahimci maganganunta, amma su kansu tunzura shi suke yi, ba shi ta aura ba, mijin Waheedah ta aura shi ne abinda take son faɗa mishi.

“Me zan yi da kai? Wallahi Abdulƙadir ba kai bane mijin da nake burin aure, kuɗinka da halayenka ba su yi min ba, ba zan iya zama da kai da wannan baƙaƙen halayen ba.”

Nuriyya ta ƙarasa maganar tana jin zugin da kuncinta yake na marinta da ya yi, gara ma ya sauƙaƙe mata auren shi, Asma tace mata da kyawunta ta zauna namiji na wahalar da ita, kuma gaskiya ne, in yau ta gama iddarta tana da tabbacin samari ne za su dinga mata layi. Numfashi Abdulƙadir yake ja yana fitarwa, idan ta ci gaba da magana tabbas zai datse igiyar da ke tsakanin su, maganganun da take faɗa ɗin na ƙara tunzura shi sosai da sosai, don bai ƙara sanin yadda zuciyar shi take doka mata ba sai yanzun da take faɗa mishi maganganun da yasa shi jin kamar ita ɗin bata taɓa sonshi ba. Abinda take tunanin auren shi zai samar mata shi take so. Abinda ta ga kamar auren shi ne ya samarwa Waheedah shi ta biyo.

Lokuta da dama kuma ba mata kawai ba, har maza na wannan wautar, ba a ƙarin mata ta biyu ba maza kan yi kuskuren nan, a ta farkon ma, da yawa kan ɗauka auren wata mace shi ne cikar farin ciki, idan har baka da farin cikin da kaine silar samarwa kanka shi, cikar shi zata yi maka wahala idan wani ya zama sanadin farin cikin ka, ko da zama na yau da gobe bai taɓa wannan farin cikin naku ba, rabuwa ta ƙaddarar rayuwa ko mutuwa kan iya giftawa, sai ka yi yaya? Aure kan samar da farin ciki, amma baya nufin duka farin cikin naka zai zamana a zagaye da shi auren. Mata sun fi kowa yin wautar nan, musamman a zamanin da muka tsinci kan mu a ciki.

Zamanin da yasa idan mace ta samu jinkirin auren da ba laifinta bane za’a dameta da yawan surutai har ya sa ta jin yin auren ne kawai hanya ɗaya ta samun farin ciki, a wasu lokutan kuma idan yarinya bata tashi cikin wadata ba, bata kuma da wadatar zuciya sai ta dora ginshiƙin aurenta da samun farin ciki akan auren mai kuɗi, wasu kuma hange-gange shi ne yake halakar da su, ki ga mace cikin rufin asiri, kin ganta daga sama da mijinta suna cin me kyau su sha me kyau, sai wannan ƙyallin ya haska miki shi, sai ki ga kamar ta samu duk wani abu da shi ne burinki a zaman aure.

Baki san yadda zaman aurenta yake tare da mijinta ba, baki san me take jurewa ba, baki san shi ma me yake jurewa a zama da ita ba, zamantakewa ta tsakanin ma’aurata sirri ne da yake a lulluɓe, abinda idanuwanki suka gani baya nufin shi ne komai, zai iya yiwuwa mijin wadda kika ƙyalla idanuwanki a kai ba shi ba ne abinda burinki yake buƙata. Karki so mutum don abinda kike tunanin kin ga matar shi ta samu a tare da shi, ko da zatonki ya zama gaskiya ba ki da tabbas ke za ki samu irin wannan a tare da shi. Duk da wasu matan ma na da laifin ganin mijin su nasu ne su kaɗai, wasu kance ‘Ta auri mijin wata’. Don kawai ta shiga a ta biyu.

Babu wani abu mijin wata daga lokacin da musulunci ya halarta ƙarin uku bayan ke tun kafin wanzuwarki, mijinki nata ne itama. Wahalhalu da yawa mutane su suke ɗora wa kansu ita, kwanciyar hankali baya zuwa idan baka neme shi ba. Abdulƙadir ko kaɗan bai zaci ta aure shi da wata manufa da ta wuce ta son zama da shi kamar yadda yake son zama da ita ba, shi yasa ya juya yana ficewa daga ɗakin. Takawa yake don ya fita daga gidan ya tafi wani waje, koma ina ne inda ba zai ga Nuriyya na wani lokaci ba kafin ta tunzura shi ya yanke musu hukuncin da su duka ba zai musu daɗi ba.

Amma sai ta biyo shi, a falon Waheedah ta same shi zai wuce ta gaban kitchen ɗin shi ta kama mishi riga ta janyo shi sai da ya juyo.

“Nuriyyaa!”

Ya sake kira cikin wani sabon kashedin, Waheedah ta ji takun tafiyar shi tun kafin ya fito, ta kuma ji muryar su don tana hango ƙafar shi guda ɗaya, da yake kujera ta saka ta zauna a kitchen ɗin ta jingina bayanta da lokar kitchen ɗin ta ɗora roba kan cinyarta tana gurza kuɓewa.

“Ka dawo ka sauƙaƙe min wannan ƙaddararren auren naka, don wallahi ba zan je gidanmu babu wata shaida ba, ni dama na gaji da zama da kai…”

Numfashi Abdulƙadir ya sauke ya kama hannunta yana ɓanɓarewa daga rigar shi yana faɗin,

“Kin gaji da zama da ni right? Ki jira ni Nuriyya, duk mu huta da rashin albarkar da take bin mu.”

Abdulƙadir ya ƙarasa don shi kanshi yana jin ya gaji da bala’in nan, yanzun nan kuma yanajin rashin albarkar iyaye ce take bibiyar shi shi yasa ƙasa da sati biyu komai ya jagule musu shi da Nuriyyar, shi ma a gajiyen yake jin shi, maganganun kowa da suka faɗa mishi sun tabbata, hankalin su ya kwanta, sai su kalli idanuwan shi su yi mishi dariya su faɗa mishi da ya ji maganar su daga farko da bai zo inda yake ba yanzun. Ɗakin Waheedah ya wuce, Nuriyya na tsaye bakin ƙofar kitchen ɗin Waheedah ɗin tana girgije-girgije, ta wutsiyar ido Waheedah ta ganta, ko ɗagowa bata yi ba, kuɓewarta take gurzawa a hankali tana bin karatun daya shigo na Suratul-Mulk cikin muryar Qari Sheikh Ghamdi da ke nutsar da abubuwan da bata san a tashe suke a tattare da ita ba.

Bata kalle su ba ne saboda basu bane a gabanta, saboda faɗan su bai shafeta ba, asalima bata da alaƙa da shi. Nuriyya na nan tsaye Abdulƙadir ya dawo da takarda a hannun shi, ɗayan da biro riƙe, fuskar shi kawai za ka kalla kasan ran shi a matuƙar ɓace yake.

“Gashi nan, na sake ki saki ɗaya.”

Runtse idanuwanta Waheedah ta yi tana jiran ta ji ko zata girgiza tare da abinda ya girgiza daga kalaman sakin aure da Abdulƙadir ya furta, asalima tana buɗe idanuwanta ji ta yi kamar tare da sakin Nuriyyar ya ɗauke mata wani ƙaton dutse daga saman kai.

Nuriyya kuwa bata karɓi takardar ba, kallon Abdulƙadir ɗin take yi bata son sake haɗa wata hanya da shi ko ta wasa ce, wani auren zata yi na mai kuɗi inda ba za’a yi mata tijara kan dubu arba’in da biyu ba.

“Da ka haihu cikin Hajja da ka ƙarashe biyun ai, ka ga duk sai ka hutar da mu.”

Sosai Abdulƙadir yake kallon ta, a duniya babu wanda ya taɓa zagin shi haka, babu wanda ya taɓa kallon shi ya zage shi haka, saki ɗaya ko uku, har a bayan zuciyar shi yana jin kamar yadda ya nuna babu wanda ya isa ya hana shi lokacin da ya aureta, sai wata ƙaddarar da bai yi fata ba, haka yake jin yanzun ma babu wanda ya isa ya saka shi sake zaman aure da ita ko da su kaɗai suka rage a faɗin duniya, saboda baya son gauraya yaran shi da matar da ta faɗa mishi maganganun da Nuriyya ta faɗa mishi. Takardar ya yaga yana komawa cikin ɗakin, ko mintina biyu bai yi ba ya fito da duka littafin a hannun shi ya ɗago ƙafar shi ɗaya ya ɗora littafin a jiki ya yi rubutu ya yago ya miƙa mata.

“Na sake ki saki uku…na sauƙaƙe miki gaba daya ƙaddararren aurena Nuriyya.”

Abdulƙadir ɗin ya ƙarashe yana miƙa mata takardar da ta karɓa ta linke bata jin ɗigon da na sani ko ɗaya, asalima wani irin saƙat ta ji ta, tana kallon shi ya ajiye takardar da biron akan kujera ya taka ya fice daga gidan, ta ɗauke idanuwanta daga kan ƙofar tana kallon kitchen inda Waheedah take gurza kuɓewa kamar bata da wata damuwa a duniya, sai Nuriyyar ta ji shi ne abinda ya yi mata tsaye a maƙoshi, yadda Waheedah take nuna kamar bata da wata damuwa a duniya.

“Za ki iya nuna farin cikin ki, ga mijinki nan na bar miki sai ki jiƙa ki sha.”

Nuriyya ta faɗi da wani malolon baƙin ciki ɗaya taso ya danne mata zuciya, amma inda take ma Waheedah bata kalla ba.

“Banza wawiya kawai.”

Ta ƙara faɗi tana jan wani irin tsaki ta wuce ciki don ta haɗa akwatunanta. Waheedah bata kulata ba ne duk yadda zuciyarta take tunzurata da ta yi hakan, ta faɗa mata maganganu, ta gaya mata yadda ta ture amintar su ta aure mata miji, ta zageta kamar yadda take so, amma azumi take yi, ita ko bata azumi ma bata jin akwai wasu maganganu da Nuriyya zata faɗa mata da zai tunzurata kuma, babu wani abu a tattare da ita da zai bata mamaki, daga ranar da ta iya auren Abdulƙadir bata ƙara bata mamaki ba. Ta ji maganganun Abba da yace mata kar ta taɓa bari baƙin halin mutane ya canza kyakkyawar ɗabi’arta, ko jiya ta ƙara jin wa’azin Mufti Menk akan mu’amala da mutane.

Sai dai wani lokacin zuciya bata da ƙashi, mutane basu da kirki, babu uzuri a cikin lamurran su, kai sai su yi ta maka rashin arziƙi, idan ka ware rana ɗaya kai magana akan hakan sai ace da haƙuri aka sanka, ba’a tunanin yadda akwai zuciya a ƙirjinka kaima, babu wanda zai maka uzurin cewa kaima ɗin fa ɗan adam ne kamar kowa, amma kai mutane sai su saka ransu a cewar yi musu uzuri ya zame maka dole. Yanzun dai ta zaɓi ƙin kula Nuriyya ɗin ne, daga yau zata fara addu’ar yadda ta fita daga rayuwar su, ko a hanya kar ƙaddara ta sake haɗa su da ita, miƙewa ta yi da kuɓewar da ta gama gurzawa ta ajiyeta ta share wajen ta wanke hannuwan ta, sai take jin iskar da take shaƙa ma daban take dirar mata.

Nuriyya kuwa data wuce ɗaki ta sauko akwatinanta ta fara haɗa kayanta, har da ‘Ghana Must Go’ ta zuba takalmanta da jakunkunanta a ciki. Sai da ta gama haɗa kayan tsaf ta ɗauki hijab ta saka tukunna ta fita daga gidan, bakin hanya ta je ta taro mai napep ta dawo, ta kula da kitchen ɗin Waheedah ɗin a kulle yake kamar bata ciki, munafukar ta faɗi a ranta. Akwatinan ta dinga janyowa tana fitowa dasu tana loda wa mai napep ɗin da ta ajiye a ƙofar gida, har maigadi ya yi ƙoƙarin tayata fita da akwatin da ta fara fitowa da shi.

“Na roƙe ka ne? Bana son tsinanniyar gulma da baƙin munafunci kamar baka gane sakina aka yi zan bar gidan ba.”

Cewar Nuriyya tana saka shi ya koma inda yake ya zauna, haka ta dinga fitowa da kayan tana ɗirka nishi, kayan kitchen ɗinta ta zo da akori kura ta kwashe abinta don ba barinsu zata yi ba, ko siyarwa ta yi tai amfani da kuɗin, wani sama-sama take jin kanta da take alaƙantawa da nishin da take saboda fito da kayan. Komawa ciki ta yi don ta ɗauko ƙaramar jakarta. Tana ɗaukowa ta fito ta ga wayam, babu mai napep babu alamar shi, rasa inda zata nufa ta yi, titin haggu ko na dama, dawowa ta yi tana turo ƙofar muryarta a karye take kallon mai gadin.

“Dan Allah ka ga inda mai napep ɗin nan ya nufa?”

Wani irin kallo yake mata, dama kayan da zai taya ta ɗauka don ya zata matar gidance har lokacin, ba hurumin shi bane tsoma baki a al’amuran gidan Abdulƙadir ɗin, amma har ranshi ya tsani Nuriyya, saboda yasha ganinta ita da Waheedah ɗin idan ta zo gidan ta rakota, lokaci ɗaya yaga ta shigo gidan a matsayin matar gidan, ko ba’a faɗa mishi ba yasan auren cin amana ne aka yi, ga ta da wulaƙanci kuma, sai ya gaisheta ta watsa mai mugun kallo tana amsawa da ƙyar, ga aiken rashin daraja da take mishi.

“Tsinanniyar gulma da baƙin munafunci bai barni na ga inda yai ba.”

Kallon maigadin ta yi hawayen baƙin ciki na tarar mata a ido, kafin ya tura ƙofar har yana bige mata yatsun da take yarfewa don azaba. Hawayenta na samun damar zubowa, gaba ɗaya sutturarta ce ya tattara yai gaba da ita, ƙaryarta da mutuncin da take shiga ƙawaye na ganinta da shi duk ta silar kayan ce. Sai yanzun wani abu kamar guduma ya dakar mata tsakiyar kai, da asalin abinda barinta gidan Abdulƙadir ɗin zai haifar, ina zata je yanzun, bata manta kashedin da Baba yai mata ba, duk da watannin nan idan ta je gida ta gaishe da shi yakan amsata babu yabo babu fallasa, ta ina zata fara?

“Na shiga uku na.”

Ta faɗi wasu sababbin hawayen na zubo mata.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×