Skip to content
Part 30 of 35 in the Series Abdulkadir by Lubna Sufyan

Ƙunshin hannunta da yake rike cikin na farin matashin saurayin ya fara bi da kallo, ƙirjin shi na zafi kamar zai buɗe, kafin ya ga saurayin ya miƙa kai saitin kunnen Waheedah yana raɗa mata wata magana da ta sa ta yin dariyar nan tata da take kashe mishi jiki. Bai san ya ƙarasa wajen ba saboda wani irin kishi da ya turnuƙe shi har duhu-duhu yake gani, tsakanin su ya shiga yana huci kamar kububuwa.

“Lafiya?”

Saurayin ya faɗa yana kallon Abdulƙadir ɗin kamar ya ga mahaukaci.

“Lafiya kake tambayata? Baka san matata bace don ubanka?”

Dariya saurayin ya yi da ta ƙara ɓata wa Abdulƙadir ɗin rai.

“Ka saketa ɗin, na aura kana faɗa min matar…”

Bai ƙarasa maganar ba Abdulƙadir ɗin ya kai mishi wani irin naushi a baki.

*****

Duka Yassar yakai wa Abdulƙadir ɗin da saura kaɗan ya gabje mishi hanci, duk da haka ya same shi kaɗan a gefen mummuƙe, wani dukan ya ƙara jibga mishi yana faɗin,

“Tashi…. Ka warke shi yasa za ka kwantar dani ba…”

Miƙewa Abdulƙadir ya yi yana dafe kan shi da yake sarawa, a zuciyar shi yake karanto

‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un’

Yana neman tsari daga muguwar ƙaddara, tari ya sarƙe shi da yasa Yassar ɗin miƙa hannu ya ɗauko robar ruwan da take gefe ya miƙa ea Abdulƙadir ɗin, da sauri ya karɓa yana sha. Kishi ne yake turnuƙe shi har lokacin, kowanne mahaukaci ne yake tunanin zai saki Waheedah ya aura yana fatan ya zo da bargo da filo, don zai ci gaba da kwana a wajen ne, in ya gaji ya ƙara gaba. Ƙarin ruwan da yake ɗaure a hannun shi ya kalla yana son tuna lokacin da suka zo asibiti.

“Karka ƙara tsoratani haka Abdulƙadir, idan kana so in goyi bayanka ka zama mai gaskiya, karka ƙara tsoratani haka.”

Yassar ya faɗi muryar shi can ƙasan maƙoshi, yana jin yadda har lokacin zuciyar shi bata daina rawa ba. Ganin Abdulƙadir ɗin a kwance ya tsorata shi fiye da tunani, ya tuna mishi duk wani dalili da yasa baya son uniform ɗin shi, a lokaci ɗaya kuma ya tuna mishi da Soja ko ba Soja ba, mutuwa babu ruwanta, ba zaɓe take yi ba, kowa nata ne, lokaci kawai take jira ta cika aikinta.

“Ashe kana sona?”

Cewar Abdulƙadir da murmushi a fuskar shi duk da ƙirjinshi da yake ciwo, hararar shi Yassar ya yi da yasa ya ƙara yin dariya, sautinta na dirar mishi a kunne da wani irin yanayi.

“Zuciyata na min ciwo Hamma.”

Abdulƙadir ya faɗi yana ɗorawa da,

“Kamar zata fito daga ƙirjina haka nake ji…amma Waheedah ta ce min haka ta dinga ji har na wata takwas, Hamma ta ina zan fara bata haƙuri? Ta ina? Yau kawai na fara jin hakan amma ina jin kamar lokacin mutuwa yazo gab… Wanne irin ƙarfin hali gare ta?”

Kallon shi Yassar yake, yana jin ƙuncin da ke tattare da muryar ƙanin nashi da yake taɓa shi sosai da sosai.

“Ka yi kuskure Abdulƙadir… Ban ce maka na yi dana sanin zama sanadin da ka auri Waheedah don bana son zaman ku ba… A karo na farko ka sa na ji da na sani na bar Hamma Yazid ya aure ta.”

Da mamaki Abdulƙadir yake kallon Yassar ɗin yana jin maganganun shi sun dirar mishi kamar saukar ruwan da babu hadari.

“Hamma Yazid?”

Ya maimaita cike da alamar tambaya, kai Yassar ya jinjina masa.

“Yana son ta, ya sota a lokacin, ni na faɗa mishi kuna soyayya sai ya haƙura… Shi yasa ya yi nisa da Kano…”

Wannan karon ruwan da yake hannun shi Abdulƙadir ya fisge, duk yadda Yassar ɗin ya kira sunan shi, ƙafafuwan shi ya sakko daga kan gadon yana jin shi wani sama-sama. Yazid ya so Waheedah? Ko kaɗan ƙwaƙwalwar shi ta kasa yardar mishi da maganar, muryar shi can nesa cike da tuƙuƙin kishi ya ce,

“Me yasa ta aure ni to? Tunda yana sonta.”

Ya ƙarasa maganar yana kallon Yassar ɗin kamar zai rufe shi da duka, numfashi Yassar ya sauke.

“Ka taɓa ganin son wani a idanuwan ta? Bai taɓa faɗa mata ba, bata taɓa son shi ba, kishin banza da wofi za ka nuna yanzun? Kana kishinta amma baka iya kula da damuwarta ba.”

Runtse idanuwa Abdulƙadir ya yi yana jin n kamar Yassar ya watsa mishi ruwan zafi, kafin ya buɗe su a kan shi da faɗin,

“Karka ƙara min ciwon da nake ji.”

Kujerar shi Yassar ya ja yana matsawa gab da Abdulƙadir ɗin sosai.

“Ba Hamma Yazid ya so Waheedah zaka duba ba Abdulƙadir, ka duba yanda ya zaɓi farin cikinka a kan nashi, ka duba yadda mu duka muke a shirye da ɗora farin cikinka akan namu, ka fara yarda da faɗanmu ba nuna isa ba ne a kanka, faɗan mu na tare da yadda muke sonka.”

Wannan karon kamar AbdulKadir ɗin zai yi kuka yake kallon Yassar, idanuwan shi sun ƙara ƙanƙancewa.

“Sau nawa abin mda na yi yai hurting ɗin ku? Rashin tunani da rashin duba abinda halayena suke yi wa na kusa dani, Hamma sau nawa?”

Ɗan murmushi Yassar ya yi.

“Ba zai lissafu ba.”

Ya amsa a taƙaice yana sa Abdulƙadir ɗin runtse idanuwan shi yana buɗe su, zuciyar shi na wani irin ciwo.

“Har da su Hajja ko? Halayena na taɓa su suma.”

Kai Yassar ya ɗaga wa Abdulƙadir ɗin da ɗan murmushin ƙarfin hali a fuskar shi.

“Ta ina zan fara? Ta yaya zan fara baku haƙuri Hamma? Ban taɓa tunanin nan ba, ban taɓa tunanin don na yi abinda ni ya shafa zai taɓa mutanen da na fi kusanci da su ba, mutanen da nake ƙauna da dukkan zuciyata.”

Numfashi Yassar ya sauke.

“Ka fara da sauraren shawarwarin mu, ko da baka ɗauka ba, ka nuna mana yadda muka isa ka saurara.”

Kai Abdulƙadir yake jinjina, ko me suke so shi kam zai yi, tunanin yana cutar da su ba ƙaramin karyar mishi da zuciya yake ba.

“Ka buɗe bakinka ka ba Waheedah haƙuri, tana sonka, shi yasa kishinka ya yi mata yawa…”

Kai Abdulƙadir ɗin ya sake jinjina, muryar shi a karye ya ce,

“Bansan ya akai kuke sona ba har yanzun Hamma, bana tunanin idan ni ne a matsayin ku zan manta duk abubuwan nan in ci gaba da zama da ku.”

Wannan karon murmushin Yassar daga zuciyar shi ya fito.

“Ba zaɓi aka bamu ba kafin ka kasance ɗan uwan mu, akwai alaƙar da bata baka wannan zaɓin, haka ƙaunar da muke maka, ba muna tare da kai don mun manta abubuwan da ka yi da bamu so ba, muna tare da kai saboda mun yafe maka hakan tun kafin ka gane kuskure ne ka roƙe mu.”

Hannu Abdulƙadir din ya kai yana jin kamar maiƙo a gefe-gefen idanuwan shi, yasa yatsun shi yana dangwalowa, Yassar ɗin na ci gaba da faɗin,

“A ƙasan duk rashin kunyar ka, ɗan uwane kai da ko an bani zaɓi ba zan taɓa ɗaukar irin shi ba, kana da halaye da bana so, halayen da zan so ka sake su, amma shi ne cikar ɗan adam ɗin, duk idan zamu faɗa wa kanmu gaskiya akwai halayen da muke da su da muke son canzawa saboda ba masu kyau bane ba.”

Ya ɗauka zuciyar shi ta gama karyewa da maganganun Waheedah, sai yanzun da yake jin hawayen da ya ɗauka sun yi bankwana da shi cike taf da idanuwan shi, ƙaunar Yassar ɗin na taɓa shi tana karya sauran abinda ya rage a zuciyar shi, ko yau rayuwa ta ƙare mishi yana da tabbacin ƙaunar su zata cigaba da samun shi a kabarin shi, saboda addu’o’in su ba za su taɓa yankewa ba. Bai san ya miƙe daga kan gadon ba sai da ya ji Yassar ya sa hannu yana ture shi ya mayar dashi ya zaunar.

“Rungume ni za ka yi don ubanka? Meye haka? A India muke ko America? Bana son iskancin banza da wofi fa.”

Dariya Abdulƙadir yake sosai yana goge idanuwan shi da yake ji cike da hawaye.

“Na gode Hamma.”

Ya faɗi da dukkan zuciyar shi, kai Yassar ya ɗaga mishi, Abdulƙadir ɗin na ɗorawa da,

“Kai musu magana su zo su sallameni, ni bazan kwana anan ba.”

Kallon shi Yassar ya yi.

“Faɗuwa fa ka yi Abdulƙadir…”

Kafaɗun shi duka biyun ya maƙale ma Yassar.

“Wallahi Hamma bazan kwana ba, in basu sallameni ba zan tafi da kaina.”

Kai kawai Yassar ya girgiza tare da sauke numfashi ya miƙe, mai hali aka ce baya taɓa canzawa, akwai halayyar Abdulƙadir ɗin da a jinin shi yake, ba zai iya canzawa ba, taurin kai na cikin wannan.

“Kai kam ko Sheikh Mufti aka saka a ruwa aka girgiza aka baka ka sha ka yi wanka ba za ka canza hali ba Wallahi.”

Daƙuna mishi fuska Abdulƙadir ɗin ya yi yana haɗe girar sama da ta ƙasa, babu wanda zai saka shi zama a asibiti, banda zazzaɓi baya jin komai, sai ciwon kai sama-sama, ƙirjin shi da yake yi kamar zai buɗe ba asibiti yake buƙata ba, Waheedah yake buƙata, in ya riƙe ta a jikin shi zai samu sauƙin duk wannan abubuwan da yake ji. Da ido ya bi Yassar ɗin har ya fice daga ɗakin, kafin ya sauke ajiyar zuciya yana jin tunanin Waheedah da ya baibaye shi.

*****

Ruwa ta watsa bayan tafiyar Hajja, ta sake kaya. Wata nutsuwa take ji da ta kwana biyu bata ji irin ta ba, WhatsApp ɗinta ta buɗe tana shiga saƙon da Hauwa ta turo mata na littafin Farin Wata na Zahra Tabi’u.

‘An saka mata sunan mace ba don ana tunanin ita ɗin cikakkiyar mace bace’

Ta karanta layin farko, maganganun na saka ta tunani barkatai, tun daga kan maitafiya take son marubuciyar, saboda tana taɓo labaran da ba ko yaushe ake taɓo su ba a cikin duniyar rubutu, tallar kawai ta ja hankalinta sosai. Ɗari uku bata yi mata tsada ba, account number ɗin ta ɗauka tana tura kudin kafin ta dauki lambar marubuciyar don ta tura mata shaidar biya. Tana gamawa ta miƙe, tana tunanin shiga kasuwa ne don ta yi siyayyar azumi tunda yau ɗin ne ake sa ran fara duban fitowar watan, duk da ana ta gardama kan hakan kamar ko da yaushe.

Abin na ɗaure wa Waheedah kai, yadda ake shafe watanni goma cir ana tafiya kai a haɗe, sai ance watan Ramadan ya gabato sai a fara rikici kan lissafi, yadda aka saki sunnah da Manzo (S.A.W) ya ɗora mu a kai na tsoratar da ita, shi yasa abubuwa sukai mana yawa, wahalhalun mu suka yawaita. Shagon da takanyi siyayyarta guda ɗaya ne, don sun saba sosai, lokuta da dama duk abinda take so ma list take yi sai ta tura musu text, wanda sai an shiga kasuwa cikin yaran shagon ake sakawa yaje ya siyo mata, kafin ta shiga duk sun haɗa mata kayayyakinta, kuɗin kawa za ta yi musu transfer, sai a nemo mata mai napep a saka mata kayan a baya. Wasu lokuttan kuma mai napep ɗin da ta je da shi ne bata sallama.

Yanzun ma komawa ta yi ta zauna tana tunanin abubuwan da take buƙata, list ɗinsu ta yi gaba ɗayan su, sai doya da dankali da ta saka na adadin da za su siyo mata, ɗaya daga cikin yaran shagon Tasi’u ta kira, ba zai wuce shekaru sha tara ba, amma hankalin shi har mamaki yake bata, ga girmama mutane, ta ce ya duba whatsapp ɗin shi ga kayyakin da za’a haɗa mata nan, yanzun zata shigo kasuwar, ya kuma taimaka inda yakan siyo mata doya da dankali ya siyo mata doya ta dubu biyu sai dankali na dubu uku. Ta san zata kwana biyu bata nema ba.

Kayan su ta haɗa a jakar da Yassar ya kawo musu. Ta ƙara gyara ɗakin tsaf tukunna ta saka Ikram a jakar goyanta, ta sa hijab ta goya yarinyarta, ta ɗauki jakar da mukulli ta wuce, a falo suka ci karo da Hauwa, da mamakin ganin ta dawo da wuri a tattare da Waheedah ta ce,

“Yau da wuri haka?”

Dariya Hauwa ta yi.

“Na gaji fa, gudowa na yi nace banda lafiya.”

Murmushi Waheedah tayi, dama ta yi niyyar karɓar kayanta a kasuwa ta sauke a gida ta dawo, sai ta yi musu sallama tukunna ta wuce. Cikin sanyin murya ta ce,

“Ina son zuwa kasuwa ne, sai in biya gida in kai kayan nan.”

Hauwa bata san lokacin da ta haɗe space ɗin da ke tsakanin su da Waheedah ta rungumeta ta gefe ba, saboda Ikram da take riƙe da ita, tukunna ta ɗago ta ce,

“Inata ƙoƙari kar in miki magana Wallahi, ina kuma ƙoƙarin kar in wuce gidanki daga wajen aiki in jibgi Nuriyya ko zan huce haushina… In kika bar mata gidan har ni kin cuceni, bata isa ki bar mata gidanki ba wallahi.”

Dariyar ƙarfin hali Waheedah ta yi, Yassar yasa ta sami ƙawa a tare da Hauwa.

“Na gode Hauwa.”

Ta faɗi a sanyaye, kai Hauwa ta jinjina mata.

“Muje in kai ki, ba abinda zan yi sai kwanciya ko na zauna gidan dama. “

Tare suka fita da Hauwa ɗin, har kasuwa suka je tare tana ta tsegumin yadda motarta take buƙatar ganin bakanike saboda tana mata wata Kjara da Waheedah bata ji ba, tunda ba sanin kan mota ta yi ba. Da suka ɗauki kayan gidan Waheedah ɗin suka wuce ta kai, bata ga Nuriyya ba, bata kuma damu da hakan ba, har bedroom ɗinta ta wuce ta ajiye jakar kayansu, ta ɗauki mukullan da ta manta ranar ƙarshe da ta yi amfani da su l, ta kulle ɗakin baccin nata da sauran ɗakunan da suke ɓangarenta, dawowa ta yi ta rufe kitchen ɗinta ma, don siyayyar duk da ta yi a tsakiyar kitchen ɗin ta ajiye su, in ta dawo ta shirya komai. Suka sake ficewa da Hauwa ɗin.

Saloon ta ce zata je ta wanke kai, tare suka je, ita ma Waheedah kan aka wanke mata aka yi mata kitso, yadda suka dame ta da a saka mata baƙin lalle akan jan da yake hannunta zai yi kyau, har da Hauwa ɗin yasa ta bari, da yake babban saloon ne, har su gyaran jiki ana yi. Lokacin da suka gama, wani yawon Hauwa ta sake janta, wai zata kai ɗinki. Gidansu Waheedah ta ce ta sauketa, lokacin gab da magriba, don anan Hauwa ta yi magriba tana ta sauri.

“Yau zan sha faɗa na sani Wallahi.”

Hauwa ta faɗi hankalinta a tashe, bakomai Yassar yake magana a kai ba, amma Allah ya mata son yawo, shi kuma ya tsani ta je unguwa ta yo dare, ta sani kawai taurin kai ne irin na mata, dariya Waheedah ta dinga mata, har bakin mota ta rakata tukunna ta koma ciki tana samun Mami a ɗakinta, gefen gado ta zauna tana faɗin,

“Mami zan koma.”

Numfashi mai nauyi Mami ta sauke.

“Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, kar ki yi wasa da addu’a, kin san in kina da matsala waya kawai za ki ɗauka ki kira ni ko?”

Kai Waheedah ta jinjina mata, addu’o’inta Mami ta sake yi musu tana ƙara binta da nasiha mai ratsa jiki, tukunna ta dauki Hijabinta ta bar Ikram ta wuce ɓangaren Abba, shi yasa ta kira shi kar ya je gidan Yassar zata taho gida ita ma. Da sallama ta tura ƙofar tana shiga falon Abban da murmushin da ke fuskar shi ya nutsa wani abu a zuciyarta.

“Abba…”

Waheedah ta faɗi cike da farin ciki, bata taɓa tunanin zata ƙaunaci wani da jinin shi baya yawo a jikinta da yawa haka ba, tana son Abba da dukkan zuciyarta. Babu jinin shi a jikinta, amma ƙaunar shi na ciki ta gauraye, ƙarasawa ta yi ta zauna a gefen shi kan kafet bayan sun gaisa.

“Kina lafiya ko?”

Abba ya buƙata, yana jin daɗin ganin murmushin da yake kan fuskarta.

“Ina lafiya Abba…”

Numfashi mai nauyi Abba ya sauke.

“Kin yi magana da Abdulƙadir ɗin?”

Kai ta jinjina wa Abba a kunyace, murmushi ya yi ba saita faɗa mishi ba, ya san sun shirya da Abdulƙadir ɗin, tsakanin mata da miji dama an ce sai Allah.

“Babu inda haƙuri ya tashi a banza Waheedah, kar wani ya taɓa sa ki ji haƙurinki ya yi yawa. Karki bari halayen kowa ya canza naki masu kyau. Da yawan lokaci rashin kirkin mutane na gurɓata na masu kirki….karki bari hakan ya faru da ke kin ji?”

Kai ta sake jinjina wa tana furta

“In shaa Allah.”

Numfashi Abba ya sauke yana cigaba da faɗin

“A lokaci da ya kuma karki bari haƙurin ki ya ja miki raini, ko da za ki yafe in an miki kuskure ki nuna hakan, ba saikin yi da hayaniya ba, tunda ba halinki bane, ki yi a nutse, karki barshi a cikin ki zai cutar da ke. Allah ya yi miki albarka, Allah ya shirya miki zuri’arki.”

Da wani yanayi a muryarta ta ce,

“Amin Abba, Allah ya bamu aron rayuwa mai tsayi tare da kai.”

Da murmushi a fuskar shi ya amsa ta da

“Amin…”

Yana ɗorawa da,

“Ba gidan ki za ki koma ba?”

Kai ta sake sunkuyar wa cike da kunyar shi da ta lulluɓe ta, hakan yasa Abba faɗin,

“Ki je ki shirya ki fito in kai ki.”

Mikewa ta yi don ji take kamar zata nutse a wajen saboda kunya. Babu abinda zata ɗauka banda Ikram, Fajr na wajen Hajja, kunyar Hajja ɗin take ji don ɗazun bata san bakinta ya suɓuce ta mayar mata da magana ba. Duk gidan ita ce ta farko da ta sameta har gidanta bayan ta ji Nuriyya ta tare ta bata haƙuri, ita ta fara nuna mata ko kaɗan ba da son ranta akai auren Abdulƙadir ɗin da Nuriyya ba, duk da a lokacin ta nuna wa Hajjan babu komai, bata kwana uku ba ta kirata ta ji lafiyarta ba, matar bata nuna mata komai banda ƙauna ba. Sallama ta yi da Mami tana goya Ikram, ta samu Abba har ya fito ma yana motar shi a zaune. Buɗewa ta yi ta shiga gaba ta zauna tana mayar da murfin ta rufe.

*****

A ƙofar gida Abba ya yi parking yana kiran wayar Abdulƙadir ɗin, da ya fito ko takalma babu a ƙafafuwan shi, kamar bai ga Abba a tsaye ba ya ce,

“Waheedah…”

Yana kasa ɓoye farin cikin shi, kunya ta sa Waheedah raɓa Abdulƙadir ɗin ta wuce cikin gidan da sauri. Sai lokacin Abdulƙadir ya kalli Abba yana faɗin,

“Abba… Ina wuni”

Hararar shi Abba ya yi.

“Sai yanzun ka ganni?”

Ɗan sosa kai Abdulƙadir ya yi yana ƙarasawa wajen motar Abban ya jingina, yana jin tsakuwoyin da yake takawa da suke tunasar da shi bai ko saka takalma ba.

“Ba yaro bane kai da zan zauna ina maka faɗa akan duk wani abu na rayuwa, ya kamata ace ka hutar da ni haka Abdulƙadir, kasan wasu abubuwan sun kamata ko basu kamata ba, bansan me kai mata ba wannan karon, ban kuma san inda ta sami ƙarfin zuciyar yafe maka ba. Amma bana jin ni zan yafe maka idan ka sake taɓa ta haka, Hajiya Safiyya ta ce min Fajr ya faɗa mata ka ture Waheedah har ta faɗi, ya kuma yi ƙanƙanta ya shirya ƙaryar da bai gani ba haka.”

Kanshi Abdulƙadir ya sadda ƙasa yana jin maganganun Abban na shigar shi sosai.

“Bansan inda ka sami tarbiyar ɗaga wa matar aurenka hannu ba, ni kam ba daga wajena ka ɗauka ba…”

Abba ya Kjarashe maganar cikin sanyin murya kafin ya ce,

“Abdulƙadir…”

Yana saka Abdulƙadir ɗin ɗagowa ya kalli Abba.

“Ranar da duk ka sake ɗaga wa yarinyata hannu, ka kalli fuskata ba wasa nake da kai ba, wallahi ka daki aurenka.”

Rufe fuskar shi Abdulƙadir ya yi da hannuwan shi biyu yana buɗe ta, ƙirjin shi na ɗaukar ɗumi kamar ana gobara a cikin shi, muryar shi a karye ya ce,

“Abba nima ɗanka ne… Ita ma ka ce mata idan na yi mata abu ta dinga faɗa min ina bata haƙuri, ka ce mata ta daina bari a ranta babu kyau. Abba ka kalli yadda duk ka tsorata ni.”

Ya ƙarasa yana goge zufar da take tsatssafo mishi a goshi, amma fuskar Abban babu wani alamar wasa, shi kam yanzun kowa ya gane raunin shi, rabuwa da Waheedah ne raunin shi, shi yasa suke son kashe shi duk su huta, ya san da ya yi abu za su dinga mishi barazanar raba shi da Waheedah ɗin tunda sun san hankalinshi tashi zai yi.

“Ita ma in kirata ka ce mata a bakin aurena idan tana ƙullata ta”

Mota Abba  ya buɗe ya shiga yana mayar da murfin ya wuce, ya yarda akwai mutanen da duk shekarun da za su yi a duniya rashin hankali ba zai taɓa barin su ba, ciki har da Abdulƙadir.

“Ka ji Abba…”

Bai ko kalle shi ba, ya tayar da motar, murmushi Abdulƙadir ɗin ya yi.

“Na gode Abba… Zan kiyaye in shaa Allah, zan kiyaye.”

Ya sake jaddada wa Abban, kafin ya ja motar shi ya wuce. Numfashi Abdulƙadir ya sauke yana wucewa cikin gidan. Shi ma da magriba Yassar ya dawo da shi, don asibitin ƙin sallamar shi suka yi sai da suka ƙarasa mishi wani ruwan da allurar da ta saka shi bacci har kusan magribar, bai jima da dawowa ba, wanka kawai ya yi tunda sun yi sallah a hanya. Har haushin Yassar ya ji da ya ce,

‘Matarka bata da hankalin da za ka wuni baka koma gida ta nemeka ba ko?’

Duk da gaskiya ce ya faɗa, Nuriyya ɗin ko flashing bata yi mishi ba, ya kuma ji haushi sosai, don shi mutum ne mai bala’in son kulawa, shi yasa tunda ya dawo yake shashshareta, ya kuma ga bata damu ba, hidimarta kawai take yi, ya yi alƙawarin zai dafata a ruwan sanyi, don ba zai ɗauki wannan halin ko in kula ɗin nata ba, in ma ba da gangan take yi ba, ɓangaren Waheedah ya shiga yana samun ta ta fito daga banɗaki, da alama alwala ta yi, bata ce mishi komai ba ta ɗauki hijabinta, shi ma banɗakin ya shiga ya ɗaura alwala yana fita masallaci, zuciyar shi a nutse yake jinta har aka idar da sallah. Ko Azkar bai tsaya yi ba ya dawo gida, don so yake ya ganshi a kusa da ita.

Ita kam Waheedah zafi ta ji ya isheta ta sake watsa ruwa tana idar da sallah, doguwar riga ta saka ta material ɗinkin bubu, yadin blue mai haske, ta ɗauki hula kalar shi mai cizawa ta saka a kanta, tana jin daɗin wutar da suka dawo da ita, don fitilar waya take ta amfani da ita a ɗakin, torchlight ɗinta babu caji a jiki. Duk da dare ne jambaki ta tsinci kanta da shafawa a laɓɓanta, tana ɗan murza mai a hannuwanta, ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin ƙamshi. Sa’da Abdulƙadir ya shigo ta sauke ikram kan katifarta, tana ƙara gyara gadon da yake a hargitse. Tsaye ya yi a tsakiyar ɗakin, ƙamshinta na saka shi lumshe ido, wata irin kewarta na dabaibaye shi.

Har inda take ya taka yana rungumeta ta baya ya sumbaci kuncinta, cikin kunnenta ya ce,

“Ki yafe min Waheedah, don Allah ki yafe min.”

Tana jin yadda maganar ta fito daga zuciyar shi, zame jikinta ta yi daga nashi, tana juyowa ta fuskance shi, fuskar shi take kallo sosai, tana saka hannuwanta ta riƙe kuncin shi, tana jin yafda sai da ta ɗan ɗaga ƙafafuwanta, girman shi har ya daina bata mamaki, kallon shi ta yi na wasu daƙiƙu kafin ta sauke hannunta ba tare da ta ce mishi komai ba, a shirunta yake karantar yafiya, duk yadda idanuwanta suke tabbatar mishi yana da sauran lokaci kafin ta sauka daga fushin da take, zai yi komai, in dai tana kusa da shi duk mai sauƙi ne.

Gadon ta ƙarasa gyarawa, ta ɗauki Ikram da ke ta bacci ta mayar da ita kan gadon tana ficewa daga ɗakin zuwa kitchen, tana jin Abdulƙadir na biye da ita, mukulli ta sa ta buɗe kitchen ɗin tana turawa, ta bar mukullin a jiki, tsugunnawa ta yi tana buɗe kwalaye da ledojin siyayyarta, Abdulƙadir na tsaye yanata binta da idanuwa kamar bai taɓa ganinta ba, ta mishi kyau sosai.  Da an ce mishi lokaci zai zo da zai ji shakkarta zai ƙaryata, amma yanayin da ke fuskarta yasa shi haƙura da duk yadda yake son sumbatarta. Yanzun ma kasa haƙura ya yi ya tsugunna kamar zai taya ta fiffito da kayayyakin da take ya kamo hannunta da ya sha lalle ya ɗago shi ya sumbata.

Kallon shi Waheedah ta yi tanajin yanda ko meye tasa ta lulluɓe ƙaunar shi da shi yana soma buɗewa, hakan yasa ta zame hannunta daga cikin nashi.

“Aiki nake Sadauki.”

Ta faɗi tana ɗauke idanuwanta daga kan shi, ta ɗauki ledojin maggi tana ɗorawa kan kantar kitchen ɗin ta ɗauko robobinsu ta buɗe kowanne tana juye shi a mazaunin shi. Bai ce mata komai ba, kayan ya taya ta shiryawa, suna cikin aikin Nuriyya ta ƙaraso wajen da murmushi a fuskarta, wutar da aka kawo yasa ta fitowa falon sai ta ji motsin ya yi yawa shi yasa ta fito, sosai ta ji sanyi a ranta na ganin Waheedah ɗin, taliya ce ta samu ta dafa fara, tana yin miyar da ko a ido bata yi mata kyau ba.

Tunanin abinda za su yi sahur da shi take yi da yadda zata kaya musu washegari, ranta duk baya mata daɗi, amma yanzun ta san indai girki ne ta ƙare, faɗansu da ta hango ita da Abdulƙadir kan hakan ya wuce. Sosai hankalinta ya kwanta.

“Waheedah… Ashe kin dawo.”

Ta faɗi tana saka Waheedah ɗin da Abdulƙadir juyawa a tare, Waheedah na jin wani abu ya taso mata daga ɗan yatsan ƙafarta zuwa tsakiyar kanta yana dawowa ƙirjinta ya tokare, Abdulƙadir kuwa wani irin tsoro da bai yi tsammani ba ya ji ya lulluɓe shi, kar Nuriyya ɗin ta yi ƙoƙarin riƙe shi a gaban Waheedah, da sauri ya zo ya raɓata ya fice daga kitchen ɗin yana wucewa bedroom ɗin Waheedah ya turo ƙofar, jikin shi yake ji har ɓari yake mai, don bai san ya zai yi ba, a karo na farko a rayuwar shi da komai ya kwance mishi.

Waheedah kuwa wani kallo ta yi wa Nuriyya ɗin da yasa ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi. Ba zata ce tun zuwanta gidan suna hira da Waheedah ɗin ba, ko kuma sun ci gaba da zama ƙawaye, amma suna gaisawa kullum, kuma tana shigowa ɓangaren Waheedah ɗin ta zauna a falo, har remote take ɗauka ta yi kallo, musamman in ta jiyo ƙamshin girki, da ta kula ko bata zo ba tana bata abinci sai ta rage zuwa sai Abdulƙadir na nan. Amma Waheedah dama ta daina fara’a a gabanta, sai dai bata mata irin wannan kallon, bata mata kowanne kallo ma.

“Sannun ki.”

Waheedah ta faɗi tana juyawa ta ci gaba da abinda take yi, wataƙila ko don bata jin daɗi ne, Nuriyyar ta yi tunani, hakan yasa ta wuce ta koma ɓangarenta don bata kula da sa’adda Abdulƙadir ya fice ba. Tsaf Waheedah ta ƙarasa gyara kitchen ɗin tana share shi, fridge ɗinta ta buɗe taga an ɗibar mata robobin kayan miya, ta kuma san Nuriyya ce, daga yau kuma ta ƙare, can gidan ƙasa ta tsugunna, tana janyo kwami ta ciro roba fara mai murfi, da ƙyar ma ta fito da ita don ta yi ƙanƙara. Farfesun kayan ciki ne a ciki, tukunya ta ɗauko ta saka robar a sink tana sakar mata ruwa don ya ɗan saki.

Doya ta yanka da za ta isheta iya cikinta, ta fere tana zuba ɗan mai a abin suya, ta soyata fararta, tana kwashewa a plate. Lokacin farfesun ya saki, iya wanda zai isheta ta ɗiba ta zuba a tukunya ta mayar da sauran a fridge. Ta ɗora, da yake ya sha kayan ƙamshi, kafin ka ce wani abu gidan ya buɗaɗe da ƙamshin da ya fito da Abdulƙadir ya zo kitchen ɗin yana faɗin,

“Me kike dafa mana?”

Juyowa ta yi tana kallon shi

“Daga dawowata zan karɓi girki? Banda lafiya ko ka manta, sai jibi ni kam.”

Da mamaki Abdulƙadir yake kallonta.

“A’a ba abin tashin hankali bane ba, sai in koma gida, jibin in dawo.”

Kai ya girgiza mata da sauri, shi ba shi da ƙarfin faɗa ko yin gardama da ita. Duk da ya so jinta a jikin shi daren yau, kwana biyu ba zai canza wani abu ba, sanin tana cikin gidan ya ishe shi, ranshi ya biya da abincin sosai, wata yunwa da bai san yana jinta ba ta taso mishi. Ɗan waje ta samu ta juye farfesun a ciki, Abdulƙadir ɗin ya kai hannu zai ɗauki guda ɗaya ta doke hannun shi.

“Ni ban dafa da kai ba Wallahi.”

Tana janye kwanon ta ajiye gefe, kallonta yake, yayi mata laifi ya sani, ya bata haƙuri kuma.

“Ba kyau horon yunwa”

Ya faɗi can ƙasan maƙoshi, Waheedah ta yi kamar bata ji shi ba, duk abin ya mishi wani iri sosai don bai saba ba, sau nawa take haƙura da abu ta bar mishi, amma yau ita ce take cewa ta yi girki banda shi, zuciyar shi bata yi mishi daɗi ba sam, tukunyar data ɓata take wankewa. Sai ga Nuriyya ta shigo kitchen ɗin tana ta washe baki, don tana sallar isha’i take jiyo ƙamshin, yawunta sai tsinkewa yake, kwana biyu bata ci abu mai galmi-galmi ba.

“Ƙamshi duk ya cika gidan, me ake dafa mana ne?”

Ta faɗi kamar yadda ta saba, Abdulƙadir na kallonta a karo na farko ya ga kwa&ayi a fuskarta, bai san ko don shi ma an hanashi bane yasa shi jin haushin kwaɗayin nata. Ga mamakinta ko inda take Waheedah bata kalla ba, asalima plate ɗin doyar ta ɗauka da kwanon farfesun tana zuwa ta gaban su,

“Ku ɗan fita zan rufe kitchen ɗin.”

Ta faɗi tana ganin suka fita bakin kitchen ɗin suna ta kallonta, sai da ta janyo kitchen ɗin ta sa mukulli ta rufe tukunna ta wuce da faɗin,

“Sai da safen ku.”

Su biyun suna binta da kallo cike da mamaki.

“Ina namu?”

Nuriyya ta faɗi bayan Waheedah ta shige lungun da zai kaita ɗakin baccinta, daƙuna fuska Abdulƙadir ya yi.

“Nima bata bani ba.”

Ya amsa ranshi a jagule yana wucewa ɓangaren Nuriyya ɗin, da duk da mamakin da take bai hanata jijjiga kitchen ɗin ba ta ji da gaske a kulle yake, don Waheedah bata taɓa rufe kitchen ɗinta ba. Tsaye ta yi a wajen ta kasa yarda da abinda ya faru.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abdulkadir 29Abdulkadir 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×