Skip to content

Abdulkadir | Babi Na Uku

5
(1)

<< Previous

Tun da ya shiga gida ɓangaren Waheedah ya wuce, ɗakin baccin su ya shiga, ya zauna a gefen gadon. Kan shi sarawa yake tunda ya fito daga asibitin, bai san ta inda zai fara tarar matsalar da Waheedah take son janyowa rayuwar su ba, don bai san me ya shiga kanta ba, ƙafafuwan shi ya janyo da nufin ɗora su akan gadon ya ga takalman shi da bai kwance ba.

“Ba zan cire ba!”

Ya faɗa a fili, da Waheedah yake, don ita ce ba ta so yana shigo mata da takalma har ɗaki, abinda take so shi take mishi yau, shi ma abinda yake so zai yi, hannu ya sa ya dafe kan shi, yana kuma saukewa haɗi da ajiye numfashi mai nauyi. Idan matsalar ƙwaƙwalwa ce ta samu Waheedah, ya ga alama har shi take son gogawa tunda ya fara magana shi kaɗai. Hoton su da ke durowar gefen gadonta ya ɗauka ya tsayar da idanuwan shi akai. So yake ya gane wane kalar kaya ne a jikin Waheedah ɗin, yadai ga farare ne, ɗankwalin da ta naɗe kanta da shi ma farine, zai iya tuna da wayarta ta ɗauke su hoton, tana lafe a jikin shi, ya zagayo da hannunshi ɗaya kan cikinta da ta ɗora nata hannun akan nashi, ya ƙanƙance mata idanuwan shi da ba girman kirki ne da su ba dama, da dariyar nan tata a fuskar shi.

Ɗan yatsan shi ya saka ya shafi dai-dai fuskarta, ya sha ganin hoton a ajiye a gurin haɗe da sauran hotunan shi da ba zai ce ga lokacin da ta ɗauke su ba, amman zai yi ƙarya idan ya ce ya taɓa tsayawa ya kula da hoton da yake hannun shi, balle ya tambayeta lokacin da ta kai aka wanko hoton har aka saka shi a frame haka. Bai san me ya sa sai yanzu yake son tambayarta ba. Sake shafar fuskarta ya yi.

“Me yake damunki yau? Me kike son janyo mana Wahee? Me kike son janyo mana haka?”

Ya tsinci kan shi da tambaya. Shirun ɗakin na saukar mishi da wani irin yanayi daya saka shi ajiye hoton a inda ya ɗauka. Bai san abinda ya kamata ya yi ba, wani abu makamancin wannan bai taɓa faruwa da shi ba, asali ma yau ce rana ta farko da rikici ya soma haɗa shi da Waheedah, shi ya sa yake jin komai ya kwance mishi, ba zaice baya faɗa da ita ba, ita ɗin ce dai bata taɓa biye mishi, komai faɗan da zai sauke mata haƙuri kawai za ta ba shi , bai san me yake damunta ba yau.

Aljihun shi ya taɓa, wayarshi ba ta ciki, waige-waige ya fara yana neman inda ya ajiye ta, babu shiri ya miƙe, duka inda tunanin shi zai iya kaiwa cikin ɗakin sai da ya duba amma bai ganta ba, takawa yayi zuwa falon su, zuciyar shi na wani irin bugawa da ya sauke idanuwan shi kan table ɗin da Waheedah ta faɗa kai, ga jini da har ya fara bushewa akan kafet ɗin, ƙafafuwan shi da yake ji sun soma rawa ya ja zuwa hanyar kitchen, wani ƙaramin bokiti ya gani ya ɗauka ya tara ruwa a ciki, kan window ɗin kitchen ɗin ya ɗauki omo ya zazzaga a ciki. Abin goge-goge yake nema, bai gani ba sai wani towel ƙarami. Shi ya ɗauka ya saka a cikin bokitin ya ɗauko ya fito daga kitchen ɗin, gefen da jinin yake akan kafet ya ajiye bokitin tare da tsugunnawa, towel ɗin ya fiddo ya matse ya soma goge wurin. Jikin shi ya ɗauki ɗumi sosai, da alamar zazzaɓin yana da alaƙa da da na sanin da ya lulluɓe shi, yana mayar da towel ɗin cikin bokitin ya ga yadda ruwan ya sake launi ya ji wani abu na tattarowa daga zuciyar shi ya haɗu a wuyan shi ya shaƙe shi, a hankali kuma shige da ficen numfashin shi ya fara canzawa. Towel ɗin yake gogawa a wajen da dukkan ƙarfin shi.

‘Jinin Waheedah ne duka anan.’

Wata karamar murya ta furta cikin kunnuwan shi, numfashin shi na fita da sauri-sauri kamar wanda ya yi gudu.

‘Ba na ɓata lokaci akan abinda ya riga ya wuce, ba na tunani akai saboda ba zan iya komawa in canza ba.’

Yake faɗa a cikin ƙwaƙwalwar shi ko zuciyar shi za ta taimaka ta ba shi haɗin kai. Iya abinda zai iya gogewa daga jikin kafet ɗin ya goge ya sake ɗaukar bokitin ya mayar kitchen. Wajen wanke-wanke ya juye ruwan, kalar shi na sa cikin shi yamutsawa, bai san lokacin da jini ya fara ɗaga mishi hankali haka ba, fanfo ya buɗe akan ruwan don ya wuce da wuri, ba ya son ganin shi, ya tara hannuwan shi a jiki ya wanke, har fuskar shi ya wanke ko za ta rage mishi zafin da ya ji tana yi, ya kashe fanfon ya fito. Tunawa ya yi wayar shi yake nema, ya ci gaba da duddubawa, bai san lokacin da yace,

“Waheedah! Ina wayata?”

Idanuwan shi ya runtse, bai gama tunanin yadda shi ma yake gab da samun taɓin hankali ba ya ji ƙarar wayar. Hakan ya sa shi buɗe idanuwan shi babu shiri, inda yake jin ƙarar wayar yake bi har kan kujera daga gefe, hannu ya saka ya janyo wayar da rabin ta ya fara shigewa cikin lokon kujerar, sai dai kiran har ya yanke, dangwala jikin gilashin wayar ya yi tunda babu wani mukulli a jiki ta kuwa buɗe, mamaki ne bayyane a fuskar shi ganin Abba ne ya kira, ba wai don ba ya kira ba, lokacin da ya kira ɗin ne ya ji ya mishi wani iri.

Yana shirin bin kiran sai ga shi ya sake shigowa, amsawa ya yi ya kai wayar kunnen shi da faɗin:

“Abba”

Daga ɗayan ɓangaren Abba ya amsa,

“Abdulkadir, ko me kake yi ka zo gida yanzun.”

Zuciyar shi ya ji ta yi wata irin bugawa.

“Abba lafiya?”

Ya buƙata yana jin sautin muryarshi da ya fito a tsorace.

“Ka dai zo…”

Kai ya girgiza.

“Ni dai ka fara faɗa min ko menene a waya tukunna.”

Abdulƙadir ya faɗa, don yadda zuciyar shi take bugawa sam bai aminta da kiran Abban ba.

“Abdulƙadir”

Abba ya kira cike da kashedi.

“Ba zan iya tuƙi a nutse bane idan ban san meye dalilin kiran ba Abba, ni dai ka faɗa min don Allah. Ka ji?”

Ya sake faɗa.
“Bari in aiko a ɗauke ka to.”

Cewar Abba da alamun ranshi ya fara ɓaci, kai Abdulkadir ya girgiza yana jin ko meye yake shaƙe da wuyan shi yana ƙara shaƙe shi.

“Akan Waheedah ne ko?”

Ya tambaya muryar shi can ƙasa, yana kuma jin bugun zuciyar shi har cikin kunnuwan shi, idanuwa ya runtse yana jiran amsar Abba, a ranshi kuwa roƙon Waheedah yake.

‘A’a Waheedah, ba ki min wannan tonon asirin ba, ba ki min haka ba, ba za ki taɓa min haka ba.’

Buɗe idanuwan shi ya yi da jin Abba yace,

“Akanta ne, ka zo yanzun ina jiran ka.”

Kafin ya furta wani abu Abba ya kashe wayar, ta yi ‘yar ƙara alamun an kashe daga ɗayan ɓangaren cikin kunnen shi, sauke wayar yayi yana faɗin,

“Abba mana, Abba ba na so ana kashe mun waya cikin kunne, da gaske bana so…”

Ya ƙarasa maganar da furta,

“Yaa Ilahee…”

Komai yake ji ya kwance mishi, takawa ya yi ya fita daga ɗakin, gurin motar shi ya nufa, buɗewa ya yi ya jefa wayar  ciki, har ya ɗaga ƙafar shi ɗaya ya saka a cikin motar ya ji an kira sallah.

“Ni sai na yi Sallah wallahi.”

Ya furta kamar wani ya ce kar ya yi sallah, cikin gida ya koma ya ɗaura alwala, sai dai ba ya jin yana da nutsuwar da zai iya zuwa masallaci, anan ɗakin baccin su ya nemi darduma ya shimfiɗa ya tayar da sallah. Sai dai ga mamakin shi kokawa ya soma yi sosai da nutsuwar shi, da ƙyar ya samu ya yi sallar tunani fal cikin ran shi, ko addu’a bai yi ba ya miƙe ya bar dardumar anan. Fita ya yi ya shiga motar ya kunna tare da janta ya juya, maigadin ƙofar nashi ya buɗe mishi gate ya fice ya nufi hanyar da za ta kaishi gidan nasu da yake a Ƙofar Ruwa.

*****

Da ƙyar Anty ta samu likitan ya bar su suka taho gida, shi ma da alƙawarin cewa za ta dawo da Waheedah a ranar, komai a asibitin suka baro shi. Ita kanta Antyn ta so koma menene abar shi sai Waheedah ta samu sauƙi sai a yi, amma ita da Abbanta sun ƙi yarda da hakan. Har suka shigo gida addu’ar Allah ya kawo musu sauƙi take yi. Waheedah da kanta ta fara jan Anty zuwa ɓangaren ta, ba don ba ta son ganin Mami ba, ba ta son kowa yace ta yi haƙuri ko ta bi komai a hankali, ba ta son jin duk wannan. Kujera ta samu ta yi zamanta a ɗakin Anty, lokaci zuwa lokaci take saka hannu ta share hawayen da ke biyo fuskarta, Ikram ma da ta ƙara ba ta tasha Anty ta miƙa wa yarinyar. Tana nan zaune Abba ya shigo da sallama, tana sauke idanuwan ta cikin nashi wani irin kuka ya ƙwace mata, a hankali Abba ya ƙaraso cikin falon ya nemi waje ya zauna.

“Waheedah”

Abba ya kira sunanta muryar shi cike da rauni, kanta da yake naɗe da bandeji ya fara bi da kallo, tukunna ya tsayar da idanuwan shi kan fuskarta da duk kumburin da ta yi da alamun kukan da ta sha bai hana yadda ta rame matuƙar nunawa ba. Kukan da take ya sa ta kasa amsa shi.

“Waheedah ki yi haƙuri kin ji…”

Abba ya furta yana jin yadda zuciyar shi take a jagule, muryar Waheedah a dishe ta ɗago jajayen idanuwanta tana kallon Abba, kai take girgiza mishi tana sauke ajiyar zuciya a hankali.

“Don Allah Abba…”

Ta soma faɗa tana jin zuciyarta kamar za ta faɗo.

“Don Allah… Kar ka ce in koma… Kar ka ce in yi haƙuri Abba… Wallahi na gaji … Ina jin idan na koma zuciya ta Abba…”

Ta yi maganar tana kai hannunta a ƙirji inda take jin zuciyarta kamar za ta fashe, numfashi take ja tana fitarwa amma iskar ba ta kai mata inda take so, da ƙyar take iya magana.

“Abba zuciyata ina jin kamar za ta faɗo, don Allah kar kace in yi haƙuri, kar ka tambayeni me ya faru… Ban san ta inda zan fara maka bayani ba, kawai na gaji ne, na gaji sosai.”

Anty da ke tsaye hannu tasa tana share hawayen da ta ji suna shirin zubo mata, a muryar Waheedah take karantar ƙuncin da Allah kaɗai ya san tun yaushe take danne shi, a muryar Waheedah take jin ciwon da take ciki, ya kuma taɓa zuciyarta ba kaɗan ba, sosai ta yi niyyar lallaɓa yarinyar ta koma ɗakin mijinta domin shi aure ɗan haƙuri ne, kowa ka ganshi zaune a gidan mijin shi komin daɗin zaman su akwai haƙurin da suke yi da juna ta fannin da ba zai bayyanu ba.

Sai dai kuma ba ta san har yaushe za a dinga laɓewa a bayan haƙuri ana cutar mata a zamantakewa ta auratayya ba, ba ta san sai yaushe mutane za su fahimta shi kan shi haƙurin yana da ƙa’ida ba, a al’adance ma haƙuri na da iyaka, balle addini da ya sauƙaƙa matakin komai. Ba ta san lokacin da mutane za su fahimci duk da haƙuri jigo ne na zaman aure bai sa ya zama ibadar auren gaba ɗayan ta ba.

“Don Allah Abba”

Roƙon da Waheedah ta yi ya katse wa Anty dogon tunanin da take yi, wani raɗaɗi take ji zuciyarta na yi, ƙuncin Waheedah na tuna mata da duk haƙurin da ta yi a nata gidan auren, yana sa tana tuna rashin sauƙin da yake tattare da haƙuri, sai mai matuƙar ƙarfin zuciya ake yi wa ya kauda kai. Abba kan shi numfashi ya sauke yana furta,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Abdulkadir…Halima kin ga yaron nan sai da ya ƙure haƙurin ta ko?”

Abba ya ƙarasa maganar yana jinjina kanshi, a raunane Anty ta amsa shi da,

“Ai shikenan, ya kyauta, ya kuma yi wa kan shi wallahi.”

Hajja ce ta shigo ɗakin da sallama, tana ƙare musu kallo, don sallah take lokacin da Abba ya aika a kirata. Mami dama da Anty taje da kanta cewa ta yi tunda duk suna wajen ita kam ba ta ga zuwan me za ta yi ba, ta san za su iya yanke duk abinda ya kamata akan Waheedah ɗin. Duk kawaicin Mami, Anty tasan Waheedah ta ninka ta, yau kam tura ta kai bango.

“Allah dai ya sa lafiya…”

Hajja ta faɗa bayan Anty ta amsa mata sallamarta, kafin ta zagayo ta samu waje gefen Abba ta zauna, sai lokacin ta kula da Waheedah da tun shigowar Abba ta sauko daga kujerar da take ta zauna akan kafet ɗin ɗakin.

“Subhanallah, Waheedah? Ashe dai ciwon da yawa haka… Zainab ta zo tana faɗa min, yanzun nake shirin in idar da sallah sai mu koma asibitin gaba ɗaya. Amma kamar bai kamata su baki sallama da wuri haka ba…”

Anty ce ta amsa Hajja da,

“Ba su bayar da sallama ba su ma, zamu koma zuwa anjima.”

Da mamaki Hajja tace,

“Ikon Allah… Lafiya dai ko?”

Ta yi tambayar tana kallon Abba da ya girgiza mata kai.

“Abdulƙadir ne”

Zuciyarta Hajja ta ji ta yi wata irin bugawa jin sunan ɗan nata.

“Yau kam dai ya ƙure haƙurin yarinyar nan. Saki take nema.”

Cikin tashin hankali Hajja tace,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…saki kuma Alhaji? Meya faru? Me ya yi mata?”

Ɗan rausayar da kai Abba ya yi, don ba shi da wannan amsar, ba kuma shi da ƙarfin zuciyar da zai tambayi Waheedah ɗin tunda har roƙon shi ta yi da kar ya tambaya. Waheedah dake share ƙwalla Hajja ta kalla.

“Waheedah me ya faru?”

Ba tare da ta ɗago ba ko hawayenta ya daina zuba tace,

“Don Allah Hajja kar ki tambayeni me ya faru, kiyi haƙuri, duk ku yi haƙuri, takardata kawai nake son a karɓar min a wajen shi…”

Maganar daga zuciyar ta takejin tana fitowa, ta ɗauka rashin Abdulƙadir a kusa da ita zai zama barazana ga rayuwarta, ba ta taɓa tunanin shi ne zai zama abinda zai haifar da hakan ba, in ba ya kusa da ita ko numfashi ba ta jin tana fitarwa dai-dai, amma yanzu tunanin kusanci da shi ne yake barazana da dai-daiton numfashin ta. Ba ta san lokacin da rayuwa ta buɗe musu wannan shafin ba, sai dai ko ba za ta iya wuce shi ba, za ta yi duk wani ƙoƙari da za ta iya ko don su Fajr. Salati Hajja take tana ƙarawa da,

“Ke kam Waheedah ki yi haƙuri mana, kin ji? tun da duk muna nan ki bari a kira shi in shaa Allah koma menene yake faruwa za mu ji sai a dai-daita ku…tunda haihuwa ta shiga tsakani ko don yara sai a duba lamarin.”

Kai Abba ya girgiza wa Hajja.

“Kar ku yi amfani da yaranta ku danne ta.”
Rai a jagule Hajja ta kalle shi.

“Kar ka ce min kana tunanin yin abinda take so ne ba tare da ka duba lamarin ba?”

Kafin ya amsa Abdulƙadir ya shigo ɗakin, kallo ɗaya za ka yi mishi ka san babu nutsuwa a tattare da shi ballantana a yi maganar kwanciyar hankali. Ko sallama bai yi ba, zagayowa yayi ya zauna akan hannun kujera, zuciyar shi kamar za ta fito daga ƙirjin shi saboda tsallen da take yi.

“Abba me tace na mata?”

Ya tambaya, rashin gaskiya shimfiɗe a fuskar shi. Kallon shi kawai Abba yake yi, Hajja ce ta watsa mishi harara.

“Me ka yi mata Abdulƙadir? Me ka sake yi mata?”

Cike da rashin fahimta yace,

“Bangane me na sake mata ba Hajja? Na mata wani abu ne banda na yau?”

Girgiza kai Anty ta yi tana faɗin,

“Hmm…”

Don ba ta son ta yi magana, Abdulƙadir rashin kunya zai yi mata ta san shi sarai.

“Dan ubanka baka san me ka yi mata ba?”

Fuskar shi babu walwala yace,

“Hajja mana.”

Ko kaɗan ba ya so a saka shi a gaba ana mishi faɗa, ko da can ma ba ya so balle yanzun da ba yaro bane shi, sai dai bai ga laifin su ba, Waheedah ce, duk laifin nata ne da ta yi mishi wannan tonon sililin, ta fi kowa sanin yadda yake son sirri a rayuwar shi, abin da ya faru yau ɗin tsautsayi ne da za su iya magance shi tsakanin su, bai san me yake damunta da ta kwaso matsalar su tana faɗa wa su Abba da bai ga ta inda abin ya shafe su ba.

“Ka kyauta Abdulƙadir…Ka ji… Ka kyauta.”

Hajja ta ƙarasa muryarta na karyewa, idan ranta ya yi dubu a ɓace yake. Abba ya sake kallo.

“Don Allah Abba me ta ce na yi mata?”

Kai Abba ya girgiza mishi.

“Ba ta ce ka yi mata wani abu ba, aurenka ne kawai ta gaji dashi.”

Cikin wani irin tashin hankali Abdulƙadir ya kalli Waheedah da ta sauke mishi rinannun idanuwanta. Da nashi idanuwan yake tambayar ta me take yi? Me take yi musu haka?

“Abba zan yi magana da ita… Ka ji… Hajja kun ji…”

Ganin suna kallon shi ya sa shi ɗorawa da,

“Don Allah…”

Abba ya fara miƙewa, shi kam ba tun yanzu ya sallama da lamuran Abdulƙadir ba, tsakanin shi da yaron ido ne da addu’a, amma shi kam ya ce ya yi ko kar ya yi bakin shi ya daina wannan asarar. Ganin da gaske bar musu ɗakin za su yi ya sa Waheedah faɗin,

“Abba da kun zauna… Ko me zai ce ba zai canza komai ba… Takardata kawai nake so ku amsar min tun da ni na mishi magana ya ƙi…”

Ba su ce komai ba suka fita, ko ƙarasa barin ɗakin Hajja ba ta yi ba, Abdulƙadir ya bar inda yake zaune ya dawo kusa da Waheedah ya tsugunna, hannu ya sa ya tallabo fuskar ta.

“Me na yi miki da zafi haka Waheedah? Don Allah me nayi miki haka? Hankalina kike son ganin ya tashi? Nutsuwata kike son rabani da ita? Duk kinyi nasara, wallahi kinyi nasara, ki bari haka ki tashi mukoma gida… Idan ma kina so raina ya ɓaci ne kamar yadda na ɓata miki rai duk ya faru…”

Sai da hawaye suka zubo mata tukunna ta sa hannuwanta ta zame nashi daga fuskarta, kallonta yake yana ganin kamanninta nata ne, amma gaba ɗaya yanayinta ya sa ta zame mishi baƙuwa, bai taɓa sanin tana da wannan ɓangaren ba ma balle ya yi tunanin ganin shi watarana.

“Aurenka nake so ka sauƙaƙe min.”

Ta furta da wani irin yanayi da ya sa shi zama. Ko dai Waheedah na da aljanun da bai sani bane sai yau, ko kuma wataƙila ba ta san yadda kalamanta suke mishi kamar ta watsa mishi garwashin wuta bane shi ya sa.

“You are hurting me…Waheedah don Allah… Ki yi haƙuri… Shikenan? Haƙuri kike so in baki?”

Kalaman suka ƙwace mishi ba tare da ya sani bama, kallon shi take, yau ce rana ta farko a tsawon shekarun da ta san shi da ta ji kalmar haƙuri ta neman afuwa akan laɓɓan shi, sai dai zuciyarta kamar dutse take jinta, babu abinda haƙurin shi ya motsa

Ƙirjinta balle ya yi tasiri. Muryarta na rawa tace,

“Ka sakeni… Shi nake so.”

Ciwon kan da yake ta fama da shi ya ji yana ƙaruwa, ya kasa gane kanta, ko kaɗan ya kasa gane kanta balle ya san ta inda zai ɓullo ma abinda yake faruwa.

“Kin san girman kalmar da kike faɗa? Kin san babu kyau mace ta furta wa namiji kalaman nan?”

Duk da hawayen dakee zubar mata sai da murmushi ya ƙwace mata.

“Za ka fi kowa bada tabbacin na je islamiyya Sadauki, kamar yadda zan bayar akanka, an halarta min neman sakina idan bazane iya zama da kai ba… Zan biya ka sadakinka kar ka damu…”

Ta ƙarasa tana sa wata irin dariya kuɓce mishi, ya lallaɓata, yayio duk iya abinda zai iya, bai san me take son samu daga wajen shi haka da ta zaɓi wannan hanyar ba, mamakinta yake yi sosai, ance kana sanin halayen mutum fiye da ko yaushe idan zamantakewa ta aure ta haɗa ku, Waheedah na son ƙaryata kowaye ya fara faɗin kalaman, din yanzun ba zai iya bada shaida akan halayyarta ba, da wani yanayi a muryar shi yace,

“Me kike so daga wajena?”

Dan in ba yau ba, shi bai mata komai ba, wata rigima ba ta haɗa su da za ta zaɓi ɗaga mishi hankali haka ba. A gajiye ta amsa shi da,

“Sau nawa zan maimaita? Ka sauƙaƙe min auren ka.”

Tashi ya yi daga ƙasa ya koma kan kujera, ya ga alamar tashin hankalin shi take son yi, nata kuma babu yadda za’ai ya kwanta, baisan kalar wasan da take yi da shi ba, amma zai biye mata har ya gane kan wasan, sai ya san hanyar da zai bi ya yi nasara akanta.

“Ko meye yake faɗa miki za ki samu abinda kike nema yaudararki yake yi…”

Ya faɗa mata yana tabbatar da kalaman sun zauna mata, zai ga wanda ya isa yasa shi sakinta tunda igiyoyin a hannun shi suke.

“Abba…”

Waheedah ta kira idanuwanta cike da hawaye, zaman shi Abdulƙadir ya gyara akan kujera yana jin shigowar su. Suka zazzauna amma banda Anty da ta yi tsaye inda take kafin ta fita daga ɗakin. Kallon su Abba yayi, fuskar Abdulƙadir tana tabbatar mishi ba su cimma wata matsaya mai kyau ba, duk da ya yi wannan addu’ar, ba ya son Abdulƙadir ya rasa Waheedah ɗin, amma ba za a haɗu da shi aci gaba da zaluntar marainiya ba. Bai da ƙarfin ɗaukar zunuban nan kam.
“Abba ku faɗa mata, ni ban shirya rabuwa da ita ba… Ku faɗamata.”

Abdulƙadir ya faɗa yana ƙara gyara zaman shi, ƙaryar hauka Waheedah take, aure yanzun yake jin ya fara yin shi da ita, don bai amsa karɓar aurenta a masallaci ba sai da niyyar mutuwa ce kawai abinda zai raba igiyoyin da suka ƙulle su a ranar. Bai ga dalilin da zai canza wannan ba.

“Ka ji shi ko Abba? Ba zan iya komawa gidan shi ba nikam… Don Allah ku bashi haƙuri ya sauƙaƙe min…”

Waheedah ta faɗa cikin tashin hankali, cikinta har yamutsawa yake da tunanin komawa gidan shi, ƙarfin ta ya gama ƙarewa gabak ɗaya.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Anty ta faɗa, hakan ya sa Abdulƙadir juyawa ya kalle ta.

“Ki fa daina salati tunda auren bai mutu ba, ba kuma mutuwar zai yi ba.”

Idanuwan Hajja a waje tace,

“Abdulƙadir…”

Ranshi a ɓace yake, so sai ranshi ya jima bai yi ɓaci irin na yau ba.

“Salatin me take yi to Hajja? Ni ban ma san me takeyi anan ba wallahi.”

Abba ne ya kalle shi yana girgiza kai.

“Ai ba za ka taɓa sake halin ka ba, ba za ka sake halinka ba Abdulƙadir…ni ba zan ba ta haƙuri ba, Allah kaɗai ya san me take ƙunsa a zama da kai…tunda ta nemi ka bata takardarra ai shikenan…”

Wata ‘yar gajerar dariya Abdulƙadir ya yi da ba ta da alaƙa da nishaɗi, ya san Abba ba son shi yake wani yi ba, ba tun yanzu ba, yadda ya goyi bayan Waheedah bai ba shi mamaki ba, bai bi takan Anty ba, ra’ayinta ko abinda take tunani ba shi da muhimmanci a wajen shi. Hajja ya kalla da yake ganin hawaye cike da idanuwana.

“Abin nan bai min daɗi ba sam…ni dai ko meye ya faru don Allah ku yi haƙuri, ku ba abin kwana biyu tunda duk kun hau dokin zuciya… Idan kuka sauko sai a yi magana.”

Kai Waheedah ta girgiza ma Hajja.

“Ko an kwana biyu ba zai canza wani abu ba…gara ni dai ya bani takardata yau, Abba zan mayar mishi da sadakin shi…”

Rai a ɓace Abdulƙadir yake kallon ta.

“Za kuma ki bani yarana…”

Wannan karon zuciyarta ta ji ta motsa, da ƙarfin gaske, idanuwan shi ya tsayar cikin nata.

“Ba Fajr kaɗai ba, har Ikram…”

Da wani irin tashin hankali take kallon shi.

“Alhaji kana jin su, a gabanka suke wannan rashin hankalin…”

Hajja ta ƙarasa maganar wani hawayen baƙin ciki na zubo mata.

“Kasan me kake faɗa Abdulƙadir? Jaririyar kake cewa za ta baka? Ka yi yaya da ita to?”

Abba yake tambaya yana kallon shi.

“Wallahi har ita sai ta bani, Abba ka ji ita me take furta min ai ba ka yi magana ba, sai ni don na ce ta ban yarana zai zama rashin hankali?”

Numfashi Abba ya sauke.

“Kar ka ƙara ɓata min rai fiye da wanda nake ciki, ba na son furta wasu kalamai marasa daɗi a kanka Abdulƙadir, ba tun yanzun kake ƙure haƙurina ba…”

Jikin shi Abdulƙadir yake ji har ɓari yake saboda ɓacin rai, wani irin kallo ya watsa ma Waheedah da duk ita ta ja mishi wannan tijarar, ya kuma ƙudurta a ranshi ba zai ɓaci shi kaɗai ba, tashin hankali take nema ta kuma samu, ya ga alamun duka laifin komai suke so su ɗora mishi, da ya yi wani abu mai girma ne ma ranshi ba zai ɓaci har haka ba, babu abinda ya yi da za a saka shi a gaba haka.

“Abba na san ba wani sona kake ba dama, ba tun yanzu ba na sani, amma duk da haka ya kamata a yi min adalci, sai ka tambayeta idan na mata wani abu.”

Da mamaki Abba yake kallon shi, cikin yaran shi zai ce daga shi sai Waheedah ya fi kula da lamuran su, yake kuma jin shaƙuwa ta ban mamaki da su, Waheedah saboda haƙuri da hankalinta, Abdulƙadir saboda yawan kawo mishi ƙarar shi da akan yi, da kuma zuciyar da Allah ya halitta mishi ta saurin fushi, ya sa babu ranar da yake gidan da ba ya kiran shi ɗakin shi don sulhunta tsakanin shi da wani a cikin gida, ko kuma yi mishi faɗa kan koyon haƙuri, amma shi yau yaron zai kalla yace ba ya son shi, wane kalar soyayya ce bai nuna wa Abdulƙadir ba.

“Abdulƙadir…”

Hajja ta kira, Abba ya katse ta da,

“Ki ƙyale shi Hajiya Furaira….ki ƙyale shi.”

Miƙewa Abdulƙadir ya yi yana kallon su gaba ɗaya.

“Ni dai ku faɗa mata, za ta bani yarana…”

Wannan karon hawayen da Waheedah ta ji ya zubo mata daga abinda ya yi saura mai motsi a zuciyarta ya fito, don sai da ta ja ƙafafuwanta ta haɗe su da jikinta ko zata samu sauƙin ciwon da fitowarsu ya bar mata, idanuwanta ta sauke cikin nashi da suke fal da kwantanccen rikici, muryarta ɗauke da wani irin yanayi tace,

“Wannan shi ne sharaɗin ka? Yarana kake son amfani da su Sadauki? Shikenan…na ji na ɗauka, ka sauƙaƙe min, ga Ikram nan bayan Anty ta baka ita, Fajr na cikin gida nake tunani sai ka ɗauke shi, Allahu ya rayasu cikin aminci…”

Anty da take tsaye ba ta san lokacin da ta juya ta nufi hanyar ɗakin baccin ta ba, don wani kuka ne ya ƙwace mata, zuciyarta ta gama karyewa da abinda yake faruwa, Hajja ma miƙewa ta yi tana kallon Abba kamar shi ne sanadin komai tunda ya ƙi musu magana, ba a gabanta za su yi wannan rashin hankalin ba. Ficewa ta yi daga falon, Abba ma miƙewa ya yi ya ba su waje ganin kallon da suke ma juna da alama sun ma manta ba su kaɗai bane a ɗakin.

Tunda ta fara magana, yanayin muryarta ya sa ko numfashin shi a hankali yake zarya, iskar wajen kanta tsaye Abdulƙadir ya ji ta yi, kamar ita ma tana son taya shi mamakin Waheedah, don ya tabbatar ba shi kaɗai yake mamaki ba, ba zai haɗa yadda yake ganin soyayyar shi da ta yaransu a idanuwanta ba, ta sha nuna mishi yadda yake da muhimmanci akan komai na rayuwarta, sai dai bai taɓa tunanin za ta iya ce mishi ya ɗauki yaran don ya rabata da auren shi ba, girgiza kai ta yi kaɗan, ya ɗora halin da yake ciki a yanzun, a cikin idanuwanta yake ganin yanda komai ya fara.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×