Skip to content
Part 47 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Bai iya fita magrib masallaci ba. A gida ya ja musu shi da Safiyya da wata kalar ƙaunarta ke masa yawo.  Ga wata nutsuwa.

Tare suka shiga toilet ɗin da abin wankan da suka siyo wa Mimi. Safiyya ta yi mamakin ko uhm Mimi bata yi ba. Ta ce wa Fu’ad,

“Kasan Nana kukan wanka take?”

Ware idanuwa ya yi sannan ya kwashe da dariya.

“Nana da kukan wankan. Baki faɗamin ba ai da na tsokane ta.”

Murmushi Safiyya ta yi. Jin ya yi shiru yasa ta daagowa ta kalle shi. Ruwan ta ɗan ɗiba ta watsa mishi a fuska. Da sauri ya kawo hannunshi ya kare yana faɗin,

“Sofi mana…”

Ware mishi idanuwa ta ɗan yi kafin ta maida hankalinta kan Mimi da take sakawa a towel.

“Kai ka ce banda yawan tunanin.”

Kallonta ya yi ya ce,

“Ina jin kewarta sosai…”

“Na sani, nima haka. Allah ya ba mu Mimi. Duk da samunta ba zai hana mana kewar Nana ba.

Zai ba mu sabon farin ciki.”

Kai ya jinjina mata.

“Me za mu ci? Wani abu simple dai.”

Ita bata ma jin cin komai sai dai ta san in ta ƙi shi ma haka zai kwana tun breakfast ɗin da momma ta takura su suka ci da safe.

“Ka zauna da Mimi kar mu barta ita kaɗai. Sai in dafa mana indomie.”

Karɓar Mimi ɗin ya yi yana kallon yadda ta yi kyau cikin fararen kayan sanyin da aka saka mata. Wani irin Kaunarta ke shigarshi a hankali.

“Mi daughter.”

Ya faɗi a hankali kamar yana son sake tabbatarwa tashi ɗin ce. Babu mai ƙwace mishi wannan kyautar.

*****

Indomie ɗin suka ci. Suka yi sallar isha’i. Ya zauna da Mimi safiyya ta watsa ruwa sannan ta fito shi ma ya shiga. Tana kwance kan gadon ya hau ya kwanta gefenta yana nazarin fuskarta.

“Gadon ina jinshi very empty babu Nana.”

Bai ce komai ba ya sauka daga kan gadon. Mimi ya ɗauko daga nata gadon a hankali. Har mamakin ina ya iya ɗaukar jariri take.

Towel ɗinta ya miƙawa Safiyya yana nuna mata ta shimfiɗa. Bata yi musu ba ta shimfiɗa. Ya kwantar da Mimi tsakiyarsu sannan ya kwanta.

Murmushi ya ɗan yi mata.

“Better?”

Kallon Mimi ta yi ta lumshe idanuwa tana ma Allah godiya kafin ta buɗe su kan Fu’ad.

“Much better.”

Sake gyara kwanciya ya yi yana kallon fuskarta ya ce,

“Ya kika yi all the years da bana nan?”

Girgiza mishi kai ta yi.

“Bana son tuna baya. Ina son kallon gaba ne kawai.”

Shagwaɓe fuska ya yi.

“Ina son ji ne.”

Kai ta ɗaga a hankali ta fara mishi bayani da faɗin,
“Ba wani abu much fa. Sati biyu bayan na gama kukan na gama zuba idanuwa baka dawo ba.

Na koma school. Ina amfani da kuɗin da ke cikin gidan ina yin komai da nake buƙata kafin su ƙare.

Cikin Nana ba mai wahala bane. Don bana wani amai ko wani abu. Ina cin abinci sosai sosai dai. Anty Laurat ta fara ce min ina da ciki.

Kafin in yi noticing Changes ɗin da kaina. Sai na fara ɗibar kuɗin da ke banki. Muna zuwa da ita mu ɗauko. Tun ina mamakin yadda suka ƙi ƙarewa har na zo na san kai ne kake turowa. Really bana son tuna duk wannan.

Kawai I was so happy bayan haihuwar Nana and sad da ba ka nan. Sad da ban san ko in kana nan zaka sota ba.

So koma ya na yi rayuwa ba abin dubawa bace a yanzun. Kasan abu ɗaya, ko da ka yi nisa. Ko yadda bana son in faɗa, da kulawarka na rayu. Da kulawarka muka rayu duk shekarun nan ni da Nana. If ba ka yi tunanin turo mkn kuɗaɗe ba…”

Sauke numfashi ta yi tana kasa ƙarasawa. Muryarta a sarƙe ta ce,

“Please mu bar maganar nan. Baya ta zauna a baya. Mu duba gaba kawai.”

Hannunta ya kamo ya dumtse yana jin wani abu ya tsaya mishi a wuyanshi.

“Ki sani wallahi da zan iya. Da ina da iko da na koma baya na canza komai.”

Ɗan murmushi ta yi.

“I know. I…I love you.”

Ta faɗi. Ware idanuwanshi ya yi da hakan ya yi mata yanayi da Nana sosai.

“Thank you.”

Ta ɗaga mishi kai tare da hamma. Dariya ya yi. Itama haka kafin suka yi addu’a suka kwanta. A karo na farko tun rasuwar Nana da suka samu bacci.

*****

“Ina za mu je baka faɗamin ba har yanzun Yaya Farhan.”

Kallonta ya ɗan yisannan ya maida hankalinshi kan tuƙin da yake da murmushi a fuskarshi.

“Home. Your home.”

Da rashin fahimta ta ce,

“Bangane ba.”

“Za ki gane Nuriyya.”

Girgiza kai kawai ta yi ta gyara kwanciya cikin kujerar. Ga mamakinta kwana suka shiga.

Bata sake mamaki ba sai da ta ga sun nufi wani ƙaton gida an buɗe musu. Kallon Farhan take har ya yi parking. Sannan ya juyo ya kalleta.

Fuskarshi da wani farin ciki ya ce mata,

“Kin shirya ganin family ɗinki?”

Hannu takai tana rufe bakinta cike da mamaki. Idanuwanta na kawo hawaye.

“Da gaske Yaya Farhan?”

Ya ɗaga mata kai.

“Da gaske Nuriyya. Family ɗinki na jiranki.”

Ko’ina jikinta rawa yake. Ta kasa cewa komai saboda gani take da ta sake buɗe baki zuciyarta fitowa za ta yi saboda dokawar da take yi.

Tana kallo har Farhan ya fita ya zagayo ya buɗe mata. Hannunta ya kamo ya fito da ita. Da ƙyar ƙafafuwanta ke ɗaukarta.

Dam ta riƙe hannun Farhan da ke cikin nata. Ta kasa yarda. Gani take da ta yi wani wrong motsi wannan mafarkin ɓacewa zai yi.

Kamata ya yi suka hau steps uku da zai kaika ƙofar gidan sannan suka tura ƙofar. Farhan ya shiga da sallama.

Muryoyi ta ji fiye da biyu sun amsawa Farhan. Idanuwanta cike suke taf da hawaye, ba sosai take ganinsu ba. Blinking ta yi tana fito da hawayen da suka taru mata.

Sannan ta ware idanuwanta tsakiyar falon. Kan wata mata idanuwanta suka fara sauka. Ta kuma kasa janye su saboda yadda take jin zuciyarta na wani irin abu.

Wata irin ƙaunar matar na shigarta da ta kasa fahimta. Kamar dama can an halicci zuciyarta ne kawai don ta ƙaunace ta.

A hankali take takawa zuwa inda matar take tsaye idanuwanta itama kafe kan Nuriyya da bata san tana ƙarasawa ba.

Tsakiyar falon suka haɗe da matar. Hannunta takait da yake rawa tana taɓa fuskar Nuriyya.

“Nuriyya.”

Ta faɗi. Hannunta da ke fuskarta Nuriyya ta kama ta dumtse tana jin wani yanayi da bata taɓa jin shi ba a rayuwarta.

Bata san lokacin da ta rungume matar ba. Kuka suke yi a tare. Ko ba a faɗa mata ba zuciyarta ta san wannan mahaifiyarta ce. Sosai suke kuka kafin wani babban mutum da ke tsaye ya ce,
“Hajiya ai kin saketa muma mu ganta ko?”

Sakinta Hajiya Karima ta yi. Tana goge fuska kawai, bata taɓa sa ran za ta sake ganin ‘yartata ba. Duk da kullum da tunanin halin da take ciki take kwana take wuni.

Takowa ya yi. Hannuwanshi ya sa ya tallabi fuskar Nuriyya. Yana kallon ‘yar tashi da suka cire rai da sake ganinta sai yau da Farhan ya same shi yake mishi tambayoyi.

Hawaye ya ji sun zubo mishi kafin ya rungume nurriya suna ma Allah godiya. Sun ɗauki mintina a hakan kafin ya ɗago Nuriyya yana goge mata fuska.

Hannunta ya kama ya shiga janta wajen yayyanta maza har biyar. Sai ƙannenta su biyu maza. Ita kaɗai ce ‘ya mace da Allah ya basu.

Yinin ranar cikin ‘yan uwanta ta yi shi. Don Farhan tafiyarshi ya yi. Sai dai bata yarda ta kwana ba. Duk yadda take so da yadda’ yan uwanta suka so.

Ba za ta iya barin Farhan shi kaɗai ba bayan wannan halaccin da ya yi mata. Ta Yi alƙawarin shi ma sai ta sa ya nemi nashi ‘yan uwan don ya ji abinda take ji itama.

Wannan farin cikin wajen shi da ban ne. Girman ƙaunar ‘yan uwantaka bata taɓa haɗuwa da wata. Allah ne ya haɗa jini ɗaya waje guda.

Shi kaɗai Ya san hikimar haka. Zumunci abune mai girman gaske.

Bayan Shekara Ɗaya

Wani irin zama su Jana suke yi mai natsuwa. Duk da wata doguwar hira bata haɗa ta da Aina.

Yara dai tunda ita ta ma fita zama da su, wani lokaci ma ko tana gidan Aina ke kula da su. Hakan bai dameta ba. Ta dai saka idanuwa ne saboda ta ga ko yanayin tarbiyar da ta ɗora yaranta akai ya sake. Ga mamakinta sai dai ya ƙaru.

Ƙananan abubuwan da bata tsayawa ta kula ko ma ta ce bata da lokacin kula da shi Aina na tsaya mata akan hakan.

Yau ma kamar kullum ta gama shirinta tsaf da yake ɗakinta Jabir yake kuma ya ma rigata shiryawa tare za su fita.

“Jana sai mun yi latti ko?”

Ya tambaya yana sake duba agogon da ke hannunshi. Da murmushi a fuskarta ta ce,

“Ka tafi in ka gaji da jira.”

“Zaki hau Napep kenan?”

Ya buƙata yana tabbatar da idanuwanshi sun sauka cikin nata kafin ya yi i tambayar. Yana kallon yadda take wani matse laɓɓa ya san tsokana ce fal cikinta.

“Ka dai hau Napep Honey J.”

Dafe ƙirji ya yi.

“Yes. Ka manta motata ce? In kuma Aina za ta ara maka tata ne to ka je ka amso.”

Rausayar da kai ya yi gefe.

“Allah ya hore min in sake siyan wata motar yadda in ɗayar ta samu matsala ba sai an min gori ba.”

Dariya Jana ta yi sosai.

“Amin. Ko in ara maka? Ka siya in ka samu ka biya ni?”

Ƙarasawa ya yi inda take ya zagaya hannuwanshi zai rungumeta ta miƙe da sauri.

“Na gama shiryawa.”

Girgiza mata kai yake alamar bai yarda ba.

“Zo nan ki ga in taya ki.”

Pillow ta ɗauka kan gadon ta jefa mishi tana ɗaukar jakarta. Ya riƙe yana dariya. Tare suka fita. Jana ta tsaya a falon ya wuce ɓangaren Aina ya faɗa mata sun wuce. Bata ɗaukar wa kanta gulmar yi ma Aina sallama ba don za ta tafi aiki.

Tana danne abubuwa da yawa. Sai dai bata takura kanta ba. Shi dai da yake wajibi akanshi ya yi. Sai dai Aina ta burgeta, yadda kullum ko da Jabir na ɗakinta sai ta zo da kanta sun yi sallama da Janar.

Fitowa ya yi ya ce ma Jana,

“Bata da lafiya. Zazzaɓi ne ruf jikin ta.”

“Subahanallah…”

Jana ta ƙarasa tana ture Jabir ɗin ta wuce ɗakin Aina ɗin. Karo na farko da ƙafafuwanta suka taɓa taka bedroom ɗin Aina a shekara ɗaya da ta yi a gidan.

Koma ta ce ɓangarenta gaba ɗaya. Sai dai in sun haɗu a babban falo sannan. Sosai ta dudduba Aina.

Sannan ta taimaka mata ta tashi daga kan gadon. Take faɗa ma Jabir sai sun je asibiti dole. Bai musa ba ya bata mukullin motarta ya ɗauki ta Aina ɗin.

*****

Abinda Jana take zato ne. Ta lumshe idanuwanta tana danne wani kishi da take jin ya taso mata. Wayarta ta ɗauko ta kira Jabir. Ringing ɗin farko ya ɗaga.

“Albishirinka, amma sai ka bani goro.”

Tana jin murmushin da yake cikin muryarshi.

“Sai kin zaɓi kalar goron da kike so. I promise.”

‘Yar dariya ta yi.

“Aina na da shigar ciki sati huɗu.”

Tana jin yadda ya ja numfashi tare da fitar da shi kafin addu’o’i su biyo baya. Sosai ta rintse idanuwanta. Hakan da ya yi ba baƙon abu bane, saboda ita ma ya yi duk cikin yaransu. Ta rasa ko menene na jin kishi a ciki.

“Thank you, Jana. I love you. Ki zaɓi goronki.”

Sai da ta ɗan yi jim tana son danne abinda take ji kafin ta ce,

“Sai na yi tunani tukunna. Bari in faɗa musu ina da patient mu koma gida. Babu daɗi in kaita in barta ita kaɗai.”

“You don’t have to do this Jana. Atika na nan ai.”

Girgiza kai ta yi.

“Badon kai na yi ba. Ko ni. Na yi saboda karamcin da ke tsakanin su da yarana.”

Shiru Jabir ya ɗan yi kafin ya yi mata sallama.

*****

Kamar yadda ta faɗa hakan ta yi kuwa. Har ɗaki ta raka Aina ta tambayeta ko tana buƙatar wani abun ta ce mata a’a.

Sosai ta yi mata godiya. Murmushi kawai ta yi ta faɗa mata tana ɗakinta in dai tana buƙatar wani abu ko flashing ta yi mata sannan ta fice. Gyara kwanciya Aina ta yi. Jana mutuniyar arziƙi ce. Ba kowa ne zai dace da kishiya irinta ba.

*****

Zaune suke tana yanke wa Farhan farce. Suka ji sallama da sauri ta saki ƙafarshi ta miƙe tana amsawa.

A faɗace ya ce,

“Nuriyya ki daina saurin miƙewa haka. Sai kin ji ma baby na ciwo ne ke kam?”

Dariya ta yi tana mamakin Farhan. Cikin da bai wuce sati uku ba ko motsin kirki bata da ikon yi sai ya yi faɗa. Sosai fara’arta ta ƙaru ganin Anty maimuna.

“Anty maimuna. Sannu da zuwa.”

Nuriyya ta Faɗi.

“Ki ƙaraso mana.”

Da fara’a a fuskar Anty Maimuna ta ƙaraso ɗakin. Farhan ya kalleta yana murmushi.

“Anty Maimuna. Ina wuni.”

Sai da ta samu waje ta zauna sannan ta ce mishi.

“Lafiya ƙalau Farhan. Ya mai jiki?”

Ya amsa da,

“Ta warware sosai Anty. Muna cewa mu samu lokaci mu shigo mu gaishe da ku.”

Zuwan Nuriyya ya katse musu hirar. Lemo da kofi ta ajiye wa Anty maimuna a ƙasa. Ta na samun waje gefe ta zauna.

“Aikam da kin bar drink ɗin nan. Daga gida nan nayo fa. Ya jiki?”

Murmushi Nuriyya ta yi a kunyace.
“Na ji sauƙi.”

“Allah ya ƙara sauƙi ya raba lafiya.”

Farhan da ke zaune kan kujera ya amsa da.

“Amin thumma amin.”

Zungurinshi Nuriyya ta yi tana mamakin rashin kunya irin ta Farhan. Anty Maimuna ƙanwar babanshi ce uwa ɗaya uba ɗaya.

Miƙewa Anty Maimuna ta yi.

“Bari ku ga in zo in wuce. Nan har gidan Hajja zan je.”

“Anty wannan irin zuwa da wuri haka?”

Cewar Farhan. Nuriyya ta karɓe da faɗin,

“Wallahi kuwa. Daga zuwa sai tafiya.”

Dariya Anty Maimuna ta yi.

“Daman jikinki na zo dubawa. Zumunci ai yanzun aka fara in banda abinku. Duk ana tare.”

Har ƙofa suka rakata suna shigowa Nuriyya ta sa kafaɗarta ta ture shi.

“Kai ko? Har da cewa amin. Ka sa inata jin kunya.”

Dariya sosai Farhan ya yi.

“Ji min ke please. An mana addu’a me kyau ba zan amsa ba?”

Turo baki ta yi tana daƙuna mishi fuska. Hannuwanta ya kamo yana janta jikinshi.

“Me nace kan turo bakin nan a gabana?”

Kanta ta ɓoye a ƙirjinshi tana dariya. Rungumeta ya yi tsam a jikinshi yana jin ɗuminta.

Yana gode wa Allah da ya tsara mishi rayuwarshi da ita a cikinta. Yana kuma sake gode wa Allah da yasa ya bi shawarar Nuriyya ya nemi dangin babanshi.

Laifin babanshi mai girma ne a gare shi. Waya sani wata rana ya iya yafe mishi. Ba zaka taɓa faɗar me zai faru da kai ba a rayuwarka.

Sosai ya sake matse Nuriyya a jikinshi. Ƙasa-ƙasa ta ce mishi.

“Idan mace muka haifa sunanta Farhana in sha Allah.”

Murmushi ya yi.

“Idan namiji ne sunanshi Nawaf.”

Ɗago wa ta yi daga jikinshi hawaye na taruwa a idanuwanta. Wasu irin emotions na mata yawo.

“Da gaske? You will name him that?”

Kai ya ɗaga mata yana sa hannu ya tallabi fuskarta.

“Da gaske sunanshi Nawaf. In dai muka haifi namiji ko ba wannan cikin ba.”

Sumbatarshi ta yi tana nuna mishi godiyarta. Kafin ta kwantar da kanta a ƙirjinshi.

“I love you. Thank you.”

“I love you more. Allah ya jiƙan Nawaf.”

Ta amsa da,

“Amin. Allah ya jiƙanmu muma. Mun fi Nawaf buƙatar wannnan addu’ar, saboda ƙarshen shi ya yi kyau. Namu ne abin tsoro.”

“Shhhhhhhhh. Za ki kashe min jiki.”

Farhan ya faɗi. Don maganganunta sun tsorata shi lokaci ɗaya. Kuma sun shige shi. Dariya Nuriyya ta yi.

“Idan jikinmu yana sanyi lokaci lokaci ƙila yasa mu shirya wa mutuwarmu kafin ta same mu.”

Sauke numfashi ya yi. Ya yi shiru yana jin ɗuminta da ƙamshinta. Lokaci ɗaya kuma maganganunta na zauna mishi.

****

Blocks ɗin robar da ke gabanta take shiryawa kamar katanga. Mimi da ke zaune sai ta sa hannu ta tarwatsa su tana wata dariya da ke saka Safiyya dariyar itama.

Sun kai rabin awa zaune suna wannan shiriritar. In ta yi dariya sai ta yi wani gwaranci da ita kaɗai take son faɗa.

A shekara ɗaya Mimi yarinya ce mai cikakkiyar lafiya. Gashi bata da rikici sam. In dai ta yi kuka to bata da lafiya. In dai da kayan wasa to bata da matsala.

Tun ranar sunan Mimi Safiyya ta yi resigning. Ta gaji da aiki. Tunda Fu’ad na tsare mata duk abinda take so. Tana son ba wa Mimi dukkan kulawar da take buƙata.

Sallama Safiyya ta ji. Sake baki ta yi tana kallon Fu’ad da ya turo ƙofar ya shigo. Ware mata idanuwa ya yi.

“Ki amsa sallamata ba kina min wannan kallon ba.”

“Seriously ka gudo daga kasuwa ne ko?”

Daƙuna fuska ya yi.

“Ni ban gudo ba. Kuma akwai su Lawal a shagon. Missing ‘yata nake na zo in ganta.”

Ƙarasowa ya yi falon tare da faɗin,

“Hey sweetheart. Dad is home.”

Tana jin muryarshi ta ci gaba da doka hannuwanta tana tarwatsa blocks ɗin tana dariya. Kallon Safiyya ya yi da ke fassara Kin gani itama ta yi kewata.

Girgiza kai Safiyya ta yi da murmushi a fuskarta. Fu’ad sai abarshi. Haka yake yi daga kasuwa zai gudo gida ya ga Mimi sannan ya koma. Wani lokacin ma ɗaukarta yake yi. Sai safiyya ta yi ta faɗa tukunna. Wasu ranakun sai dai ta gaji ta barshi.

Hannu ya sa ya ɗauki Mimi yana haɗa goshinshi da nata. Yarinyar ta saba wasan da yake mata. Ita ta soma girgiza kanta jikin nashi suna dariya tare.

“Mimi is so cute. She is so cute.”

Dariyarsu ta ba wa Safiyya dariya sosai.

“In zubo maka abinci ko?”

Ta buƙata. Ya girgiza kai.

“Restaurant na je na ci delicious.”

Miƙewa Safiyya ta yi tana kallon shi.

“Res….  Me? Ai da ka kirani ka ce kar in sa abinci da kai za ka je ka ci wanda ya fi shi daɗi.”

A kasalance ya kalleta.

“Nikam bana jin yin ringima Sofi. Yunwa na ji and restaurant ɗin yana kusa damu. Muka je muka ci abinci. Ba sai ki barshi da dare mu ci ba?”

Sosai take kallonshi.

“Da daren ma ka je restaurant. Akwai wani a kusa da mu.”

Ta fadi ta na matsawa tare da karɓe Mimi daga hannunshi ta juya da ‘yarta a hannu tana barin falon. Dariya Fu’ad yake sosai. Yana so ya ga Safiyya na faɗan nan. Kyau take ƙara mishi kamar ya mayar da ita cikin shi.

Sai da ya yi mai isarshi sannan ya tashi ya bita bedroom ɗin. Tana zaune kan gado da Mimi a tsakiyar gadon. Sarai ta ji shigowarshi. Ta ƙii juyowa. Tsayawa ya yi wajen ƙaton hoton Nana da yake cike da bangon ɗakin ya kalleta. Yana jin wata irin kewarta ta ban mamaki.

Hannu yasa ya shafi kumatunta a jikin hoton. Sannan ya ɗan ɗaga kafaɗarshi.

“Mumynki fushi take min. Har da ƙwace Mimi daga hannu na bayan ta san saboda ita kawai na baro kasuwa.”

Shiru ya yi. Zai iya rantsewa ya ji sautin dariyar nan ta Nana da ke saka shi farin ciki na daban.

“Yeah mumynki akwai rigima sosai.”

Juyowa Safiyya ta yi.

“Dadynki akwai son kai sosai. Ya faɗa miki ko me ya yi min. Abinci fa a restaurant bayan ya san ni kaina bana iya ci sai ya dawo.”

Kallon hoton Fu’ad ya yi ya ɗaga girarshi da ke fassara mumynki bata karantata kamar yadda kike yi. Yasan da tana nan tunda ya buɗe baki za ta gane wasa yake.

Sannan ya juya ya taka har inda take. Gefen gadon ya zauna. Ya ɗauko Mimi ya ɗorata kan cinyarshi sannan ya kalli Safiyya da take wani basar da shi.

“Ki kalle ni Sofi.”

Kauda kai ta yi gefe.

“Please… Sofi.”

Ya faɗi yana jan sunanta yadda ya san ba za ta iya mishi gardama ba. Juyowa ta yi ta sauke idanuwanta cikin nashi.

“Goodness. Kina kyau da faɗa.”

Naushinshi tai a kafaɗa. Ya wani daƙuna fuska yana faɗin,

“Ouchhh yi haƙuri Sofi.”

Hannuwanta ta sa ta matse mishi kumatu tana faɗin,

“Kasan in akwai abinda na tsana bai fi ka ci abinci a wani waje ba.”

Ture hannunta ya yi yana gyara wa Mimi zama kan cinyarshi.

“Ki ƙyale ni ni kam. Yunwa nake ji cikina sai ihu yake tun ɗazun.”

Dariya ta yi tana miƙewa. Wani irin jiri ya ɗibeta ta tafi luuu. Da zafin nama Fu’ad ya fizgota yana zaunar da ita kan gadon.

Kanta ta dafe da hannuwa biyu tana jin yadda ɗakin ke wulwula mata. A rikice Fu’ad ke faɗin,

“Subahanallah. Sofi menene? Lafiyarki kuwa?”

Gaba ɗaya hankalinshi ya tashi. Saida ta ɗan ji jirin ya fara tsayawa sannan ta ce mishi,

“Bakomai fa. Kawai ina jin jiriri ne wasu lokutan.”

Muryarshi babu alamun wasa a ciki ya ce,

“Tun yaushe?”

“Wajen sati biyu. Amma bai fara damuna ba sai kwana biyun nan.”

A ƙufule ya ce,

“Sati biyu sai yanzun nake ji? Damn it Sofi in wani abu ya same ki fa?”

Ganin yadda ya birkice yasa ta dafa hannunshi.

“Really ba wani babban abu bane ba. Kawai jiri ne. Babu inda ke min ciwo banda shi.”

Ture hannunta ya yi.

“Tashi mu tafi asibiti.”

“Ba wani…”

Kallon da ya yi mata ya sa ta katse maganar.

“Ka ci abinci sai mu je.”

Muryarshi a dake ya miƙe da Mimi a hannunshi.

“Bana jin yunwa.”

Miƙewa Ta yi tana dafa shi da faɗin,

“Ka yi haƙuri.”

Kallonta ya yi taga yanayin da ke cikin idanuwanshi.

“Har yau inajin cewa kamar da nazo da wuri nana za ta kasance tare da mu. Na sani ba tunani me kyau bane ba. Amma na kasa dainawa. What if wani abu ya sameki? Don Allah karki sake min irin wannan. Da ciwo sosai.”

Jikinta a sanyaye ta ce,

“Bazan sake ba. Please ka yi haƙuri.”

Ɗan dafe kai ya yi.

“Ya wuce. Ɗauko mayafinki mu je mu dawo.”

“Da ka ci abincin sannan.”

“Abinci can wait. Sai mun dawo.”

Tasan halinshi.  Tsayawa gardama babu amfanin da zai yi, don haka ta wuce ta ɗauki hijabinta ta saka. Suka fita.

*****

Kallon Jana suke su dukansu. Kallonta suke kamar ƙaho ne ya fito mata tsakiyar kai da maganar da ta gaya musu.

Kallon da suke mata ya bata dariya sosai.

“Wai menene kuke kallona haka? Nace matarka na da ciki na wata ɗaya da sati biyu. In ba ku gane turancin ba.”

Safiyya kallon Fu’ad take zuciyarta na wani irin dokawa. Shi ma kallonta yake lokaci ɗaya maganganun Doctor ɗin da ya jagoranci yi mishi surgery na vasectomy suka dawo mishi.

Cikin harshen turanci yake faɗa wa Fu’ad ɗin cewar,

“Ko da bayan shekaru ko watanni matarka ta samu ciki karka zargeta. Ka ɗauka jikinka ya warkar da kanshi.

Yana faruwa ga wasu mutanen.”

Hannu Fu’ad ya kai yana tsane gumin da ya tsattsafo mishi. Zufa yake ta ko’ina. Ta bakinshi yake jan iska saboda ya daina jin shigarta na wani lokaci. Mimi ya sake gyara wa zama kan jikinshi.

Su dukansu sun kasa magana. Hawaye ke zubo wa Safiyya wasu na bin wani. Tunani take wanne kyakkyawan aiki ta yi da Allah ya bata wannan kyautar.

Shi kanshi Fu’ad tunanin da yake kenan.

“Oh Allah. Ina bayin da suka sake ka suka kama waninka? Haƙiƙa suna cikin ɓata mai muni.”

Ya ƙarasa maganar yana jin wasu hawaye masu ɗumi sun zubo mishi. Hannunshi Safiyya ta kamo da nata duka biyun.

Ya ɗago da su ya sumbace su saboda mimi da ke hannunshi. Ya kasa tsaida hawayenshi. Allah Ya dube shi da Rahma ya mishi kyauta da ya yanke rai da samunta. Haƙiƙa indai kana da rai. Baka fidda rabo. Sai dai rabonka ya yi jinkiri. Inda Allah ya rubuta maka shi to sai ka samu.

Mimi kamar tasan farin cikin da suke. Ta ƙyalƙyale da dariya. Kallonta suka yi a tare suna murmushi duk da hawayen da suke zubdawa.

Dr. Jana kuwa gyara zama ta yi tana kallon su tana koyln darussa masu dama daga rayuwarsu. Da murmushi a fuskarta.

Kallon cikin Safiyya Fu’ad ya yi ya kalli Mimi. Ita kuma kallonshi take. Lokaci ɗaya abinda su duka biyun suke tunani ya bayyana a fuskarsu. Hannu Safiyya ta kai da sauri ta karɓi mimi tana rungumeta. Hawaye na sake zubo mata.

“No please. Ba za su yi mana haka ba.”

Yadda ta yi maganar ya gane so take ya tabbatar mata. Sadda kanshi ƙasa ya yi da wannan sabon farin cikin da ya same shi fargaba na rabuwa kusa dashi.

Miƙewa ya yi ya miƙa mata hannunshi ta sa nata ciki suka juya. Jana murmushi ta sake yi dan ganin sun tafi wata duniya ta daban. Sanda suka samu natsuwa sun nemeta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 46Akan So 48 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×