Skip to content

Akan So | Babi Na Arba’in Da Shida

0
(0)

<< Previous

Yana shigowa gidan da sallama ya ga bai ga Nuriyya ba. Ciki ya shiga ya duba bedroom ɗinta.

Don ya san bata cika zama falo ba. Ta fi gane ta yi kwance a bedroom ɗin in ba shi ya dawo ya zo ya fito da ita ba. Zuciyarshi ya ji tana dokawa babu dalili. A rikice ya fito yana faɗin,

“Nuriyyaaaa!”

Da saurinta ta fito daga cikin. Idanuwanta ta sauke cikin nashi. Wata ajiyar zuciya ya sauke yana tura hannunshi daya cikin sumar kanshi. Da mamakin ganin tsoron da har lokacin bai barshi ba ya sa ta faɗin,

“Yaya Farhan. Lafiya dai ko?”

Kai ya ɗaga mata yana ɗora murmushi a fuskarshi.

“Ina kitchen ne ban ji shigowarka ba.”

Ta faɗi a sanyaye tare da ɗoraawa da,

“Ka daina tunanin za ka nemeni ka rasa yaya Farhan. You are the only family da nake da.

Please bana jin daɗi.”

Kunyarta ya ji ta rufe shi. Har ranshi yana tsoron ya nemeta ya rasa. A yanzun shi ma ba shi da wani family bayan ita.

“Na daina. I am sorry.”

Kai ta ɗaga mishi alamar komai ya wuce.

“Na ce ki daina damuwa da dafa abinci. Zamu iya fita waje mu ci.”

Ɗan murmushi ta yi mishi tana jin wani ƙuna a zuciyarta. Nawaf ya koya mata ƙyamar abincin waje komin tsaftar restaurant ko hotel kuwa.

“Ba wani aiki bane. Tunda babu yawa.”

Kai ya ɗaga mata ya zagaya ya zauna kan kujerar.

“Zo mu zauna.”

“Bari in sauke girki sai in zo.”

Ta faɗi tana juyawa. Bata fi mintina goma ba ta fito. Waje ta samu gefenshi ta zauna.

Kallonta ya yi sosai. Muryarshi da fuskarshi tana nuna mata muhimmancin maganar da ya ke son faɗa.

“Na je gidan Anty ne yau. Na je in ji ko tana da wani abu da ya rage na lokacin da ta tsince ki. So ba a samu komai ba sai School back ɗinki. Na karɓo amma ban buɗe ba. Ban ma san yadda za ki yi handling abin ba na bari in fara faɗa miki.”

Kan Nuriyya a ƙasa tana jin hawayen da suka taru a idanuwanta suna zuba. Zuciyarta dokawa take.

“Nuriyya…”

Ya kira a hankali. Tun a hanya yake tababar faɗa mata. Ya ɗan samu a satin nan ta fara warwarewa har tana ɗan hira dashi. Zai jagula komai akan maganar da babu tabbas a cikinta. Babu ma wani hope ko za a samu wani clue cikin jakar. Hannunta ta kai ta kamo na Farhan ta dumtse. Karo na biyu da jikinsu ya haɗu tun zuwanta gidan. Kamar yadda ya yi mata alƙawarin zama duk abinda take son shi ya zame mata har sai ta shirya canzuwar hakan.

Bai karya ba. Beside, in ya kula bata son magana bata waje yake.

“Ina tsoron a buɗe jakar da ka ce ka karɓo a samu babu komai a ciki. Ina tsoron ko ba zan taɓa ganin dangina ba. Idan ina da su kenan. Ban san me ya kamata in yi ba.”
Ɗayan hannunshi ya sa ya haɗe nata cikin nashi duka biyun. Cikin idanuwa ya ke kallonta. Sannan ya ce,

“Rashin buɗewa a duba zai sa ki zama cikin tambaya a ko da yaushe. Buɗewar ba zai cutar da ke ba nuriyya.  Ƙila ma ki tuna wani abu. Allah kaɗai ya san me ya ɓoye miki a bayyanar gaskiyar nan. In kuma kina son magana da Anty ne directly sai mu je.”

Da sauri ta girgiza mishi kai. Wani irin tsoro na shigarta. In akwai abinda ta fi tsana bai wuce ta sake ɗora fuskarta kan azzalumar mata kamar Anty ba. Ko a mafarki bata fatan Allah ya sake haɗa su ballantana kuma idanuwa biyu.

“Bana son sake ganinta Yaya Farhan. Na tsaneta wallahi.”

“I understand…”

Da rauni a muryarta ta ce,

“Za mu buɗe jakar tare. In babu kai bazan iya ba.”

Kasa controlling emotions ɗinshi yayi. Ya ƙara matsawa ya sumbace ta a kunci sannan ya saki hannunta ya miƙe yana ficewa daga falon. Hannu ta sa ta goge fuskarta. Zuciyarta na wani irin dokawa. Tana jin ya shigo da sauri ta ɗaga kai ta kalle shi.

Kafin ta maida kallon kan ‘yar jakar da ke hannunshi. Ƙurar da jakar ta yi ya hana asalin kalarta ya fito. Kamar ash colour. Ƙarasowa ya yi ya zauna.

Sannan ya miƙa mata jakar ta karɓa tana jujjuyata. Da duk wani abu na jikinta take son ta ji wani connection tsakaninta da jakar ko ta tuna wani abu ko ya yake amma ta kasa.

Muryarta na rawa ta ce,

“Na kasa tuna komai Yaya Farhan.”

Dafa hannunta ya yi. Ya karɓi jakar ya ajiye kan kujera.

“Maybe shekarunki ba masu yawa bane da za ki riƙe wani abu. Ki buɗe.”

Kai ta ɗaga mishi. Zuciyarta na wani irin dokawa. Ji take kamar in ta buɗe jakar za ta iya ganin wani abu da zai tuna mata asalinta.

Ta wani fannin kuma tana jin tsoron yadda ta ɗaga burinta har haka. Jin Farhan ya sake dafa hannunta ya sa ta jan wani numfashi sannan ta sa hannu kan zip ɗin jakar ta buɗe bugun zuciyarta na ƙaruwa. Hannu ta sa ta ɗaga jakar tare da zazzageta kan kujerar. Ta sa hannu tana taɓa kayyakin da suka zubo daga ciki kamar za su bata amsar da ta kasa samu. Books ne a ciki gaba ɗaya na ‘yan Nursery 1. Farhan ne yasa hannu ya ɗauki guda ɗaya daga ciki. Ya ga inda Anty ta ga asalin sunan Nuriyya kenan.

Gashi nan da manyan baƙi a rubuce. ‘Nuriyya Habeeb Danori’.

Habeeb Danori, Farhan ya ke maimaitawa cikin kanshi yana tunanin inda ya taɓa jin sunan.
Sosai yake dubawa. Ɗan ware idanuwa ya yi ya kalli Nuriyya da idanuwanta ke kafe kan littatafan da take ta shafawa.

Ya buɗe baki sai ya fasa. Gidan mai ne ya gani wajen Bachirawa. Sai dai zai iya yi wa Habeeb Danori da yawa cikin garin Kano.

Baya son ya ɗaga mata burinta sai ya tabbatar tukunna. Duk da yana da wani irin feeling mai ƙarfi kan hakan. Ba zai ɗaga mata buri ya zo ya tarwatsa shi ba.

Yana kallonta ta ɗauki littafi ɗaya tana sa hannu tana shafa wajen da sunan yake.

“Asalin sunana Nuriyya. Anty ta gani. Ta ga sunana ta kasa kai ni inda dangina za su nemeni.

Saboda me? Meye ribarta na tsintata ta kasa kaini inda za a ganni? Amfanin me na yi mata?”

Shiru Farhan ya yi, saboda bai san me ya kamata ya yi mata ba. Matsawa ya yi ya kama Hannuwanta. Ƙwacewa ta yi.

“Saboda me? Ina da family kaima ka gani. Kaga shaida Yaya Farhan me yasa za ta tarwatsa min rayuwa? Duk shekarun nan ina tunanin ko kalar mahaifina ba zan taɓa sani ba. Ina tunanin mahaifiyata karuwa ce.

Kasan tashin hankalin da ke cikin hakan?”

“Nuriyya please calm down…”

Farhan ya faɗi. Cikin hargowa ta ce,

“No! Yaya Farhan. Ba za ka taɓa ganewa ba saboda ka yi normal rayuwa ba irin tawa ba.”

Kallonta yake maganganun da ta faɗa suna masa wani irin zafi. Muryarshi can ƙasa ya ce,

“Nuriyya. Ki bar maganar nan. Zan nemo miki su in shaa Allah.”

Hawayen da suke zuba idanuwanta ta sa hannu ta goge.

“Idan kuma ba sa nan fa? Ba za ka taɓa ganewa ba.”

A tsawace ya ce,

“Yes bazan gane ba Nuriyya. Na ɗauka kin san kaɗan daga cikin rayuwata. Kin san waye Babana. Ban ce ya fi Anty ba. Ban kuma ce kalar su ɗaya ba. Ki kalle ni sosai.

Na miki kama da wanda ya yi rayuwa normal?”

Shiru ta yi tana kallonshi yadda ya birkice lokaci ɗaya.

“Ko kin taɓa tambayata ina ƙanwata da nake baki labari?

No, baki tambaya ba. Ni kuma ban faɗa miki ba saboda what is there to tell? In ce Nuriyya kin san me ya faru da Farhana kuwa? Ina kallo Babana ya sha giya ya bugu ya ce sai ta bishi sun fita unguwa.

Ina tsaye saboda ta ce tana son zuwa, gudun ma tashin hankalinshi na barta.

Bayan komai na jikina na min ihun kuskuren hakan. Ina kallo ya ja mota suka bar cikin gidan ban tsayar dasu ba. Yeah na ga kuskurena awa biyu tsakani da aka jeramin gawarsu a gabana.

Sai dai kinsan me? I deserve the pain na mutuwar Farhana saboda ni ne sila. Him? That Monster? I wish Bai yi mutuwa mai sauƙi ba…”

Innalillahi wa inna ilaihir raji’un kawai Nuriyya ke faɗi cikin zuciyarta. Sai yanzu ta ji dalilin da duk murmushin da Farhan zai yi akwai wani irin ƙunci a ƙarƙashin shi. Hannu tasa ta dafa mishi cinya. Amman kamar ma ba ya jinta.

“Yaya Farhan…”

Ta faɗi hawaye na zubo mata ganin yadda jikinshi ke kyarma. Yadda komai nashi ya canza. Yanayin ciwon abinda yake ji bayyane a fuskarshi.

Juyowa ya yi ya kalleta sosai.

“I don’t know exactly yadda kike ji. But ba ke kaɗai kike hurting ba. Ba ke kaɗai bace Nuriyya.”

Miƙewa ta yi ta matsa ta zauna kan cinyarshi. Kafin ya gama mamaki ta yi hugging ɗinshi sosai. Kuka take. Shi kam ya kasa. Yana jin kalar raunukan da yake da su zafinsu da ciwonsu ya girmi hawaye. Riƙeta ya yi a jikinshi yana jin yadda yanayin ke fifita mishi inda yake masa zafi. Sumba ya manna mata a gefen fuska.

“Ki daina kuka. In sha Allah zan nemo miki family ɗinki. Za a gansu.”

Kai take ɗagawa tana sake ƙanƙame shi. Cikin kunnenshi ta ce,

“Kaima ka gano naka please. Ka gano mana family ɗinmu.”
Shiru ya yi yana juya maganarta.

“No naki dai Nuriyya. Mum na bata da kowa. Shi kuma…Yeah sun yi gefe lokacin da yake abusing ɗinmu. Saboda yana da kuɗi babu wanda zai iya mishi magana.”

Sake riƙe shi ta yi.

“Na sani . Ka yafe musu, dukkanmu muna kuskure a rayuwarmu.”

Lumshe idanuwa Farhan ya yi.

“Mu bar maganar for now please.”

Ɗagowa ta yi daga jikinshi. Ta kalli fuskarshi sosai.

“For now.”

Ya ɗaga mata kai da yake nuna alƙawarin za su sake maganar amma ba yau ɗin ba. Komawa ta yi jikinshi ta kwanta luf.

Ya riƙeta yana lumshe idanuwanshi. Rayuwa makaranta…

*****

“Na ɗauka sai da yamma za mu tafi.”

Safiyya ta faɗi a sanyaye tana kallon Fu’ad. Girgiza mata kai ya yi.

“Mu koma gida kawai. Zama a nan ba zai sake komai ba.”

Kai ta ɗaga mishi tana ɗauke idanuwanta daga fuskarshi. Tana jin ciwon yadda za ta koma gidansu da ya ke cike da memories ɗin Nana.

Yau kwana huɗu kenan da rasuwar. Su dukansu kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci yadda rayuwa ta koya musu darasi da dama. Musamman Safiyya da Fu’ad da suka yi wata irin rama. Ya karanci me take gudu tsaf. Ya share ne saboda yasan gudu wa feelings ɗinsu ba zai canza komai ba. Da yawan gudun da suke da yawan yadda zai musu zafi idan ya kamo su. Ya riga da ya faɗa wa Momma za su koma gida tun ɗazun.

Itama da ta ga kamar ya yi sauri da ya yi mata bayani sai ta fahimta.

“Bari to in ɗauko mayafina sai in yi sallama da Momma.”

Kai kawai Fu’ad ya iya ɗaga mata. Bai ko zauna ba don ya san ba daɗewa za ta yi ba.

Shi kanshi zuciyarshi cike take da tsoron kalar ciwon da zai ji in suka ƙarasa gidan. Kewar Nana har cikin tsokarshi yake jinta.

A zuciyarshi wani irin fili ne ta bari da babu wanda zai iya maye shi. Wajenta ne ita kaɗai. Lumshe idanuwanshi ya yi hannuwanshi cikin aljihu.

Murmushinta ya tuna da yadda take buɗe idanuwanta idan ta ganshi. Bai san sanda murmushi ya ƙwace mishi ba. Cikin zuciyarshi yake faɗin,

“Allah ya haskaka kabarinki Nana. Kin bar mu da kewa ko? Na gode da tare da kewarki akwai moments irin waɗannan.”

Taɓa shi ya ji anyi. Da sauri ya buɗe idanuwanshi ya sauke su cikin na Safiyya. Lokaci ɗaya murmushin da ke fuskarshi ya ɓace.

“Murmushin me kake?”

Hannunta ya kama suka nufi hanyar fita. Cikin sanyin murya ya ce,

“Bakomai kawai na tuna yadda Nana take nata ne ban san sanda ya bayyana ba.”

Ga mamakinsu duka biyun dariya safiyya ta yi. A karo na farko tun rasuwar Nana.

“Ka san akwai lokacin da ina fever. Na ji Nana shiru ina ta kira ashe tana kitchen.

Kasan me take?”

Da murmushi a fuskarshi ya girgiza mata kai. Dariya ta sake yi lokacin sun ƙarasa bakin motar. Tsaye Fu’ad ya yi yana kallonta yana son ta ƙarasa bashi labari.

Cikin fuska take kallonshi.

“Ƙwai ta soya min ta haɗo tea. She was 7 lokacin. Karka ga fuskata sanda ta shigo ɗakin. Ranar na fara jin tsoro a rayuwata. Ina tunanin da ta ƙone fa? Ko ta zubo ma kanta ruwan zafi.

Abinda ta yi ya taɓa ni sosai, na kasa mata faɗa. Karka ga fuskata lokacin da na yi tasting wainar ƙwan.

Goodness. It was awful.”

Wanna karon Fu’ad ne ya yi mamakin daga inda dariyarshi ta fito. Daga shi har ita dariya suke. Kafin wasu hawaye masu zafi su zubo ma safiyya.

“I miss her. Every second da bata nan ina jinshi a ko’ina nawa wallahi.”

Riƙota ya yi jikinshi yana matse ta dam. Shi kanshi yanajin irin ciwon da take ji.

“Sofi kina da memories irin wannan ke. Banda su da yawa. Don Allah ki dinga sharing min nima in samu? Zamu saba da kewarta a hankali. Komai zai yi mana sauƙi”

Ɗagowa ta yi daga jikinshi tana goge fuskarta.

“Zan sharing maka duka. Duk wani babban abu da ƙarami da zan iya tunawa.”

Kai ya ɗaga da murmushi a fuskarsa. Itama kasa ɓoye nata murmushin ta yi. Ta ce mishi,

“As much as tunanin Nana zai mana ciwo. Farincikin da ke tattare da shi mai girma ne.”

“Ta tafi ta bar mu da kewarta ne. Shi ya sa zai yi ciwo. Amma kuma ta bar mana abubuwan farin ciki da yawa. Ina jina da sa’a sosai da na santa a rayuwata.”

“Nima haka… Mu je gida dai.”

Kai Fu’ad ya ɗaga yana sauke numfashi tare da buɗe wa Safiyya motar. Shiga ta yi ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shi ma.

*****

Suna hanya sun kusa kai gida ma wayarshi ta hau ihu. Sai da ya rage gudun da yake sannan ya lalubota daga aljihunshi.

Dubawa ya yi ya ga Lukman ne. Ya ɗaga ya kara a kunnenshi. Kafin ya ce wani abu Lukman ya ce,

“Fu’ad please ka gaya wa Hajiya muna nan Aminu Kano. Zainab ke labour. Inata kiran wayarta ba ya zuwa.”

Ware idanuwa Fu’ad ya yi.

“Wallahi nima na fito. Bari na kira Momma sai ta je su taho.”

Kamar Lukman zai yi kuka ya ce,

“Please ka yi sauri. Ni kaɗai ne a wajenta.”

Katse wayar ya yi. Fu’ad ya miƙa wa Safiyya wayar.

“Lukman ne. Kira Momma ki ce su taho ita da Hajiya. Zainab ke naƙuda kuma ba kowa wajenta.”

Da sauri Safiyya ta lalubo lambar Momma. Allah ya taimaka ringing ɗaya Momma ta ɗauka. Faɗa mata ta yi. Sannan ta ce wa Fu’ad.

“Da mun je asibitin ma ai.”

“Are you sure?”

Kai ta ɗaga mishi tana masa kallon da ke fassara tambayata ma kake. Lukman da Zainab ake magana ba wasu ba.

*****

Sun riga su Momma zuwa asibitin. Lukman suka samu, kallo ɗaya za ka yi masa ka san yana cikin tashin hankali.

“Ya Zainab ɗin?”

Safiyya ta tambaya. Kai ya girgiza mata alamar bai sani ba. Kallon wajen Fu’ad yake yana mamakin ganin Lukman ɗin ne kawai.

“Ina family ɗinta. Ka kira mamanta?”

Kallonshi Lukman ya yi. A sanyaye ya ce,

“Bata san babanta ba. Da cikinta ya rasu. Wajen haihuwarta mamanta ta rasu. Ita kaɗai ce wajensu.”

Kai Fu’ad ya girgiza. Yana jin wani abu da ya tsaya mishi a wuya. Har Safiyya kasa cewa komai suka yi. Lukman ya yatsina fuska.

“Basu damu da ita ba. Lokacin da na je neman aurenta yi sukai kamar sun gaji da ita. Kamar dama jira suke su samu maraba da ita.”

“Hmm duniya kenan. Rayuwar duka guda nawa ce.”

Fu’ad ya faɗa yana jin wani tausayin Zainab ɗin ya cika zuciyarshi. Safiyya ta buɗe baki za ta yi magana su Momma suka ƙaraso.

Kamar zuwansu wajen ya taho da sa’a, kafin ma su ce wani abu Nurse ta fito tana tambayar wanda suka kawo Zainab. Su dukansu suka nufe ta suna tambayar yaya. Murmushi ta yi.

“Ta sauka lafiya. Ta samu baby girl. Suna cikin ƙoshin lafiya. Za ku iya ganinta nan da mintina sha biyar in an shiga da ita ɗakin hutu.”

Su duka hamdala suke. Cikin yanayin murnarsu Fu’ad ya matsa ya kamo hannun Safiyya ya riƙe. Dumtsewa nashi ta yi ta san tambayarta yake ko she is okay.

Shi ya sa ta amsa shi itama. Duk da halin rashi da take ciki bai hanata taya su Zainab farin ciki ba. Haihuwa kyautar Allah.

Momma ta buɗe jaka ta zaro kuɗi ta ba Nurse ɗin tare  da yi mata godiya. Nan suka tsaya suna jira a fito da Zainab ɗin don su shiga su ganta.

Aikam ana zuwa aka faɗa musu za su iya shiga su ganta. Suka ɗunguma su dukansu. Tana kwance babyn na gefenta.

Momma ta fara ɗaukar babyn ta miƙa wa Lukman ya karɓa. Hamdala ya yi ga da ya saukar da matarshi lafiya kafin ya kai kunnen babyn saitin bakinshi.

Kiran sallah ya yi mata cikin kunnen kafin ya biyo da addu’o’i sannan ya matsa wajen Fu’ad miƙa mishi ita.

“Ka yi mata huɗuba.”

Ware idanuwanshi Fu’ad ya yi cike da alamar tambaya.

“Ko wanne suna ya yi maka.”

Lukman ya faɗi ƙasa-ƙasa.

“Ya sunan Maman Zainab?”

Fu’ad ya faɗi yana karɓar yarinyar da yake jinta ‘yar ƙararrama a hannunshi. Kallonta yake so cute. Yana jin wani abu a zuciyarshi da ya kasa ba wa suna.

“Aisha.”

Kai Fu’ad ya ɗaga wa Lukman, saboda ba zai iya magana ba a yanayin da yake ji. Addu’o’i sosai ya yi wa yarinyar ya miƙa wa Lukman ita.

Yana jin yadda ya yi kewar ɗan nauyinta a hannunshi a iya mintinan da ta yi wajen shi. Hajiya Lukman ya miƙa wa yarinyar.

Ta karɓe ta itama ta yi mata addu’a sannan ta ba wa Safiyya. Idanuwanta cike da tausayawa. Karɓarta Safiyya ta yi ta ƙura mata idanuwa kafin ta ce,

“Zainab kamarku ɗaya, Lukman ka ɓata min daughter da guntun hanci.”

Dariya suka yi. Suna jinjina wa ƙarfin halin Safiyya ɗin. Da idanuwa Lukman ya ke roƙon Hajiya da su ɗan bashi waje da Zainab. Ta san dalilin hakan ta dafa Momma kafin ta miƙe. Ta fahimci so take subar ɗakin. Don haka babu wani ɓata lokaci ita da Momma suka fice.

Fitarsu ta fahimtar da su Safiyya. Ta miƙe tare da ba wa Zainab babyn.

“Allah ya raya, ya sanya mata albarka.”

Ƙasa da kai Zainab ta yi. Tana jin kunyar Safiyya ɗin. Ɗan murmushi ta yi ta kalli Fu’ad suka fice daga ɗakin suma.

Ƙarasawa gefen gadon Lukman ya yi. A tsorace yake kallon Zainab. Hannu yakai ya taɓa fuskarta.

“Sannu Zee na. Allah ya miki albarka. Allah yasa kece matata har a Aljanna.”

Cike da jin daɗin addu’ar shi ta dafa hannunshi da ke kan fuskarta ta ce,

“Amin. Zan yi alfahari Dee. Samun miji irinka sai an tona. Ba zan taɓa manta karamcin da kai min ba.

Kai ne komai nawa kai…”

Saurin janye hannunshi ya yi daga fuskarta yana rufe mata baki.

“Shhhhh. Bana so. Bana so kina faɗar haka. Abinda na yi miki in kyauta ce kin bani linkinta da Junior. Idan bashi ne kin riɓanya min riba mai girma.

Ina sonki Zee. Zan fahimta in kin fasa niyyarmu. Wallahi ba zan taɓa kallonki da abin ba.

Saboda cikin ba a jikina ya zauna wata tara ba. Ba ni na yi miki naƙudarshi ba.

Bana so ki yi abinda za ki yi nadamarshi don farincikina ba…”

Wannan karon ita ta rufe mishi baki.
“Ko da nake naƙuda da niyyarmu daram take a zuciyata Dee.”

Sauke numfashi ya yi ya miƙe. Sumbatarta ya yi yana nuna mata godiyarshi. Yana ɗaukar mata alƙawarin ƙin manta wannan karamcin.

*****

Leƙo da kanshi ya yi wajen ɗakin ya ce,

“Momma ku shigo. Fu’ad…”

Su Momma wucewa suka yi. Ganin su Fu’ad sun tsaya ya sa shi fitowa daga ɗakin gaba ɗaya.

“Ku shigo mana.”

“Zamu dawo Lukman. Gida za mu tafi yanzun.”

Girgiza kai ya yi alamar bai yarda ba.

“Nidai ku shigo. Safiyya kema biye wa Fu’ad za ki yi ko?”

Kallon Fu’ad Safiyya ta yi da idanuwa take roƙonshi da su koma ɗin. Gani yake kamar ba za ta iya handling emotions ɗin ba shi yasa yake cewa su tafi gida.

Kai ya ɗan ɗaga mata. Ta saki hannunshi da ke cikin nata. Suka shiga ɗakin a tare Lukman na gabansu.

Tsaye suka yi daga ɗan nesa su duka, wannan karon sun rasa me ya kamata suyi. Haɗa idanuwa Safiyya ta yi da Zainab. Zainab ɗin ta yii mata wani murmushi da ta kasa fahimtarshi. Kasa mayarwa ta yi don yanda take jinta.

Suna kallo Lukman ya je wajen Zainab ta sa hannu ta miƙo mishi babyn. A hankali ya tako inda su Fu’ad suke ya tsaya da babyn a hannunshi. Juyawa ya yi ya kalli Hajiya. Ya ga alfaharin da ke cike da idanuwanta. Farincikin da ke kan fuskarta da zai jima tunosu kawai na saukar mishi da nishaɗi.

Ɗan ɗaga mishi kai ta yi da ke nuna me yake jira? Ya yi kawai. Juyawa ya yi ya sauke idanuwanshi cikin na Fu’ad.

Fuskarshi ɗauke da wani yanayi ya ce,

“Lukman ni me zan yi da yara? Idan ina buƙatarsu ga naka nan za ka haifa. Ga  Haneef ga su Fa’iza zan gansu.”

Sosai yake kallon idanuwan Fu’ad ɗin, sai da ya ga alamar ya tuna exact maganganunshi shekarun da suka wuce. Yaga dana sani da nadama da ke cikin idanuwanshi.

Sannan ya ce,

“Yes, rabin maganarka babu ƙarya a ciki Fu’ad. kana da mu. Kuma yanzun kana buƙatar ya’ya. Sai dai ɗaya kawai za mu iya haifa maka…”

Lukman ya ƙarasa maganar yana miƙa mishi babyn. Kallon Safiyya Fu’ad ya yi sannan ya kalli Lukman ya kalli babyn.

Muryarshi na rawa ya ce,

“Me kake nufi?”

Don ya kasa fahimta. Duk da kunnuwanshi sun ji maganganun Lukman. Zuciyarshi ta ƙi yarda ta karɓe su.

“Ka ji ni ai. Baby muka haifo maka ni da Zainab…”

Hannu Fu’ad ya kai kan ƙirjinshi yana dafe inda zuciyarshi ke wani irin tsalle kamar za ta faɗo.

Momma ya kalla ita kanta mamaki ne ƙarara a fuskarta. Ta kalli Hajiya idanuwanta cike da tambaya da hawaye.

Tana so ta ji ko da saninta Lukman zai yi wannan abin. Kai Hajiya ta ɗaga mata tare da faɗin,

“Wacece ni in shiga tsakanin ‘yan uwa?”

Hawayen da suka zubo wa Momma ta goge tana faɗin,

“Na rasa abinda zan faɗa.”

“Ki sanya musu albarka.”

Kai momma ta ɗaga wa Hajiya tana kallon su Fu’ad wanda da ƙyar ya iya cewa,

“Lukman please. Ka daina min irin wasan nan.”

Kallon ba ka da hankali ko? Lukman ya yi mishi kafin ya sake miƙa mishi babyn.

“Ka karɓeta Fu’ad…”

Jikinshi ko ina ɓari yake. Idanuwanshi cike taf da hawaye ya miƙa hannu ya karɓi babyn.

Safiyya ya kalla. Ta matso kusa da shi tana sa hannuwanta jikin nashi suna riƙe babyn tare. Ta kasa tsaida hawayenta.

Sun kuma kasa daina kallon babyn. Da ƙyar Fu’ad ya ɗago da kanshi ya ce wa Lukman.

“Wallahi za mu riƙeta da kyau. Za mu kula muku da ita.”

Zainab da ta dafa gadon ta miƙe zaune ta ce.

“Mu a suwa? Za ku kula da ‘yarku dai.”

Kallon ta sukayi sannan suka kalli lukman. Suna son jin ko gaskiya ne abinda ta faɗa.

Ɗaga mishi kai Lukman ya yi.

“Ba riƙo muka baku ba Fu’ad. Aisha Fu’ad Arabi. Mu muka haifeta. Amman ‘yarka ce Fu’ad.

Allah ne shaidar mu akan wannan. Zamu amsa sunan masu haihuwarta ne kawai.”

Hawayen da suke idanuwan Fu’ad suka zubo. Bai yi ƙoƙarin gogesu ba saboda yana jin yadda wasu ke sake fitowa. Kuka suke sosai shi da Safiyya suna riƙe da yarinyar har lokacin. Shi kanshi Lukman kukan su ya sa hawayen zubo mishi.

Har su Hajiya ma da Zainab ɗin. Hannu Lukman yasa ya goge fuskarshi.

“Enough please.”

Girgiza kai Fu’ad yake. Saboda ya kasa tsaida su. Bai taɓa tunanin wannan karamcin daga wajen Lukman ba. Bai taɓa tunaninshi daga wajen Haneef ba ma balle Lukman. Allah kenan. Ya karɓi Nana, cikin hikimar shi kuma ya basu wata kyautar. Kyautar da ko a mafarki basu taɓa zatonta ba. Miƙa wa Safiya babyn Fu’ad ya yi duka yasa hannu yana goge hawayen dake bin fuskarshi.

“Lukman…”

“Shhhh in har zumuncin mu ya kai inda na ɗauke shi za ka yi shiru ba za ka ce komai ba.”

Shiru Fu’ad ya ui yana runtse idanuwanshi. Takawa ya yi ya ƙarasa wajen Zainab. Tsugunnawa ya yi kan gwiwoyinshi.

Hannuwanshi na riƙe da gefen gadon. Kasa ce mata komai ya yi. Ya kife kanshi jikin gadon kawai hawaye na ci gaba da zubo mishi.

Me zaka ce ma wanda ya ɗauki farin ciki ya baka? Babu wasu kalamai.

Muryar Zainab na rawa ta ce,

“Na gode da karamcin da ka yi min. Na gode da ka sakawa ‘yarka sunan mahaifiyata. Allah ya raya muku ita.”

Ðago kai ya yi ya kalli Momma ya ce,

“Momma kin ji ita ce take min godiya wai. Really? Wai ni ne na yi mata karamci. Momma da wane baki zan musu godiya? Wallahi ban cancanci wannan karamcin daga wajensu ba sam.”

Hajiya ce ta yi mishi daƙuwa.

“Gidanku Fu’ad da irin maganganun nan. Kar in sake ji. Ka tashi ku wuce gida ma.

Mu ma da Zainab ta warware gidan za mu tafi.”

Miƙewa Fu’ad ya yi. Ya ƙarasa inda Lukman yake tsaye. Hugging ɗinshi ya yi. Lukman ya ture shi yana ɗan tari,

“Maza ragargazamun ƙashi kar in ci naman suna da kyau.”

Dariya Fu’ad ya yi yana girgiza kai. Safiyya ya kalla da take takowa ta ƙaraso wajensu.

Lukman ta kalla.

“Allah ya karramaka linkin yadda kai mana. Allah ya baka aljanna.”

“Amin Safiyya. Allah ya jiƙan Nana.”

Kai ta ɗaga mishi hawaye na zubo mata. Ƙarasawa ta yi ta zauna gefen Zainab. Hannunta ɗaya riƙe da babyn ɗayan kuma ta saka shi cikin na Zainab.

“Mahaifiyata ce kaɗai za ta yi min irin abinda kika yi min.

Allah ya barki da mijinki yasa zamanku har a aljanna. Za mu kula da ita, na miki alƙawari.”

Murmushi Zainab ta yi mata.

“Ko me zai sa Lukman farin ciki. Amin Allah ya jiƙan Nana ya raya muku baby.”

Kai safiyya ta ɗaga tana jin hawayen na sake zubo mata kafin ta ce,

“Ki shayar da ita. Kar a ɗauki alhakinta. In yaso sai mu karɓa in…”

Katse ta Zainab ta yi.

“Banda enough milk. Ko Junior madara ya sha. Karki damu.”

Lumshe idanuwa Safiyya ta yi tana sauke ajiyar zuciya. Kai kawai ta ɗaga wa zainab ta miƙe. Fu’ad ta kalla. Basu da sauran abinda za su faɗa. Wannan karon sun manta da su Momma da ke wajen. Hannunta Safiyya ta sa cikin nashi suka juya suka fice.

Zainab ta kalle su tana sauke numfashi. Tana jin kewar ‘yarta har ranta. Sai dai tana da yaƙinin za su kula da ita fiye da su ma ƙila.

Kallon Lukman ta yi. Kalar yadda ya kalleta ya wanke mata duk wani shakku daga zuciya.

*****

Basu bar asibitin ba sai da suka nemo  Doctor ɗin yara ya basu shawarwarin da zai basu tukunna.

Suna mota Safiyya rungume da babyn. Lokaci-lokaci Fu’ad na juyowa ya kalle su. Sun kasa cewa komai har yanzun.

Kafin Fu’ad ya kori shirun da faɗin,

“Mu je mu siya wa Mimi kaya tukunna.”

Kallonshi Safiyya ta yi.

“Mimi?”

Kai ya ɗaga mata tare da faɗin,

“Sunan maman Zainab ne. So za mu ɓoye ko dama. Kuma Nana tace inda tana da ƙanwa za ta dinga kiranta Mimi.”

Murmushi Safiyya ta yi.

“Nana ga ƙanwa kin samu. Sai dai Allah bai yi za ki ganta ba.”

Jin rawar da muryar Safiyya ta ke yasa Fu’ad faɗin,

“Mimi kin ji mumynki ko? Big sis ɗinki ba za ta taɓa ganinki ba. Amma ke za ki ganta. Ina da pictures da labarai da yawa.”

Murmushi Safiyya ta sake yi. Tana jin su Inna kawai take son ta yi magana da su ta faɗa musu sauyin da ya shigo rayuwarta.

Ta nuna musu kyautar Allah yawane da ita. In ya jarabceka ba don ya manta da kai bane. Sai don Ya fi kowa sonka ne.

*****

Aikam biyawa suka yi. Siyayya kawai Fu’ad yake kamar baisan wahalar neman kuɗi ba.

“Ya isa haka.”

Cewar Safiyya. Girgiza mata kai ya yi yana daƙuna fuska.

“Ba fa a baby za ta zauna ba. In ta ƙara girma za mu dawo. Ka ga wanna za su zama waste. Abarsu haka.”

Jim ya ɗan yi kafin ya jinjina mata kai cikin yarda da abinda ta ce ɗin. Zuwa suka yi suka biya kuɗin kayan aka ɗiba aka zuba musu.

Boot ya cika dam. Kaya har bayan motar. Suka shiga sannan Safiyya ta ce,

“Mimi akwai haƙuri. Har yanzun bata yi kuka ba. Bacci take ta yi ma. Da na so mu je gidansu Inna mu nuna musu ita. Mu dai je gida in haɗa mata madara tukunna.

In mun huta sai mu je ko?”

Kai ya ɗaga ya ce mata,

“Ke kika riƙeta ɗazun. Yanzun ni zan riƙeta kiyi driving.”

Kafaɗa ta maƙale alamar bata yarda ba.

“In ji waye? Kai za ka yi driving”

Shagwaɓe fuska Fu’ad ya yi.

“Please…”

Buɗe motar ta yi ta fita tana zagayawa ta buɗe shi. Fitowa ya yi ta bashi Mimi sannan ta shiga wajen da ya fito shikuma ya za gaya. A hankali ya shiga yana rufe ƙofar tare da kallon Mimi da take ta baccinta kafin Safiyya ta tayar da motar su tafi.

*****

Fitowa ta yi da madara a hannunta ta samu Fu’ad a tsaye inda ta barshi tun shigowarsu.

Hankalinshi kwance yake zuba wa Mimi labari. Ɗan murmushi ta yi. Yanayin da take ji ba zai barta ta faɗa mishi Mimi bata jin me yake faɗa ba. Karɓarta ta yi ya shiga bedroom ɗin ya yo alwalar sallar la’asar ya fito ya wuce masallaci. Jin gidan take yi shiru.

Ta san da gaske Nana ta rasu. Ta Yi accepting hakan. Amma wani ɓangare na zuciyarta gani yake kamar Nana za ta fito daga ɗaki ne tana tambayarta inda ta samo baby. Lumshe idanuwanta ta yi tana maida hawayen da take ji.  Addu’a sosai ta yi wa Nana. Mimi na gama shan madarar ta sake komawa bacci.

Ta so ta sake mata wankane. Sai ta haƙura ta barta ta huta. Ɗan gadonta da suka siyo ta ɗauka  sannan ta wuce bedroom ɗin.

Sai da ta saka ta a ciki ta lulluɓeta sannan ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala ta fito ta yi sallar la’asar.

*****

Tana kwance kan gadon abinta hannunta ɗaya kan gadon Mimi ta ɗora shi. Sosai tunanin rayuwa take da abinda ke cikinta.

Ta ji an hawo gadon an riƙeta ta baya. Sauke numfashi ta yi.

“Ban ji shigowarka ba.”

Sumbatarta ya yi a kai ta baya sannan ya amsa da,

“Bana son tunanin nan please.”

Shiru ta yi. Tunani kam dole ne sai a hankali tukunna. Jin yadda ya riƙeta yasa ta ɗora hannunta kan nashi tana shirin zame jikinta.

“Sofi. I miss us. Please…”

Shirun da ta yi ya bashi amsar da yake buƙata. Cikin mintina ya fara nuna mata kalar kewarta da ya yi shekarun nan. Yake nuna mata yadda soyayyarta take tare da shi duk nisan da suka yi.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×