Skip to content
Part 27 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

“Ni dai ba surutu ba. Yunwa nake ji ka zo ka ɗauke ni please.”

Dariya Lukman ya yi ta cikin wayar sannan ya amsa da,

“Ni na ce ka zo babu sanarwa. But seriously ban sa ran zuwan ka yau ba. Duka satinka uku ko?”

Daƙuna fuska Fu’ad ya yi tare da faɗin,

“Oww Lukman. Surutun nan in ka zo mun yi. Ka taho ni dai.”

Ɗan jim Lukman ya yi kafin ya ce,

“Ba wani ɗan ladabi?”

“Please…”

Fu’ad ya faɗi yana kashe wayar da alƙawarin shaƙe Lukman in ya ƙaraso.

So ya ke ya ga fuskar Sofin shi saboda sam ba ta sa ranshi ba. Da ya kirata jiya har da kukanta saboda ya ce ba zai daɗe ba yana kuma gaya mata sai ya ƙara kwana goma.

Murmushi ya ke ta yi shi kaɗai. Yana hango soyayyar da zai nuna mata yau ɗin nan. Ji ya ke kamar ya yi tsuntsuwa ya ƙarasa gida.

Motar Lukman ya hango. Ya miƙe, ba shi da kayan komai sai jakar system ɗin shi.  Hannunshi cikin aljihun 3-quarter ɗin shi ya taka zuwa inda Lukman ya yi parking.

Ya buɗe motar yana faɗin,

“Allah ya yi maka yadda ka min Lukman.”

Dariya ya yi ya ja motar.

“Ya hanya?”

Lukman ya buƙata. Hararar shi Fu’ad ya yi ya sake yin dariya.

“Da na taimaka na zo? Bacci na ke wallahi ka wani tashe ni.”

Wannan karon Fu’ad ɗin ne ya yi dariya.

“Haneef na kira na ce ya zo ya ɗauke ni. Zagina ma ya yi.”

“Madallah. Ni ma kawai saboda Safiyya. Da sai dai ka shiga taxi.”

Hira suke jefi-jefi da Lukman har suka ƙarasa. Bai shiga da motar ba iya kofar gidan ya tsaya.

“Zan shigo anjima in shaa Allah.  Ka gaishe min da Hajiya please.”

Taɓe baki lukman ya yi.

“In ka shigo ka je da kanka.”

Ficewa Fu’ad ya yi daga motar yana faɗin,

“Zanzo ɗin ne ai. Sai anjima.”

“Ka gaida Safiyya…”

Wucewa Fu’ad ɗin ya yi. Lukman ya juya da motar.

*****

Zaune ta ke kan kafet tana yanke farce. Ƙwanƙwasa ƙofa ta ji an yi. Ba ta kawo ma ranta komai ba ta ce,

“Shigo…”

Zatonta ma Anty Laurat ce. Tunda suna hutu yanzun. Wani lokacin in dai ta fito ta kan biyo su gaisa da Safiyya. Ɗago kai ta yi da ta ji an turo ƙofar. Wani ihun murna ta saki ta tashi da gudu ta ƙarasa ta ruƙunƙume shi.

Dariya ya ke yi, shi ma hugging ɗinta ya yi sosai. Sun jima a haka sannan ya sake ta yana sumbatarta.

“I miss you sosai, Sofi.”

Ta kasa daina fara’a da ta ke yi. Hannu ta sa tana jan kumatunshi.

“Shine ka ce min sai nan da kwana goma ko?”

Riƙe hannunta ya yi yana faɗin,

“Wayyo Sofi. Yi haƙuri ina son surprising ɗinki ne fa.”

Jakarshi ta sa hannu ta cire daga bayan shi ta na kama hannunshi. Kan kujera ta ajiye jakar a hankali don ta san system ɗin shi ce a ciki.

Zama ya yi yana kwance igiyar takalminshi. Ya ajiye su gefe ya sauke mata idanuwanshi da ke cike da gajiya.

“Yunwa Sofi.”

Hannunta riƙe da ƙugu ta harare shi a zolayen ce tare da faɗin,

“Bansan da zuwanka ba ai. Banda abinci.”

Ware idanuwanshi ya yi a kanta. Ya yamutsa fuska.

“Da gaske?”

Kai ta ɗaga mishi alamar eh. Kai ya dafe don in ya ce har sai ya fita ya siyo abinci yunwar nan ta gama wahalar dashi.

Coffee ne kawai a cikinshi. Shi ma ɗan baccin da ya ji yana ji ne ya sha. Bai ci komai ba.

Ganin yadda ya yi da fuska ya sa ta kwashewa da dariya. Kitchen ta wuce ta samu plate ta zubo mishi taliyar da ta yi jalof da dankalin turawa.

Duka ta juyo mishi don ta san da wahala ma ta ishe shi. Tana gamawa ta zuba ma maigadi da Mama Indo nasu ta juye nata a warmer.

Ba ma ta ci ba ashe rabonshi ce. Da cokali ta taho mishi da cup. Ta soma ajiye abincin kan table ta ja shi zuwa inda yake.

Sannan ta wuce ta zubo mishi lemo a kofin ta haɗo da robar ruwa. Tana faɗin,

“Bari ko dankali in ƙara soya maka…”

Da sauri ya ce,

“Dawo please. Wannan zai iya riƙe ni na wani lokaci. Zauna kawai in ganki.”

Murmushi ta yi. Ta samu waje ta zauna tana kallonshi yana cin abincin cike da yanayin nan da ya ke burgeta.

Hira suke ɗan yi kaɗan-kaɗan har ya gama. Raka shi ta yi ya shiga wanka ta zauna ta jirashi ya fito.

Ita ta tayashi shiryawa ya gama tsaf sannan ya yi kissing ɗinta.

“Bari in je gida Sofi. In ma ɗauko mana wata motar na gaji da wannan.”

Murmushi ta yi mishi.

“A dawo lafiya. Ka gaishe da su.”

Tare suka fita falo ya ɗauki jakar system ɗin shi ya fice. Kitchen ta shiga ta ɗora indomie.

*****

Su Hussaina na Islamiyya. Bai samu kowa a gidan ba sai Momma da Haneef. Momma ta ke faɗa mishi Babban Yaya ma ya yi hatsari amma da sauƙi tunda babu karaya sai ciwuka.

Sama ya hau ya samu Haneef suka gaisa.

“Mu je gidan Babban Yaya mana in duba shi.”

Gyara kwanciya Haneef ya yi.

“Sa’anka ne ni da za mu jera muna zuwa unguwa tare.”

Dariya Fu’ad ya yi.

“Don Allah.”

“Ka ƙyale ni Fu’ad bacci zan yi.”

Daga nan saman Fu’ad ya wage baki yana kiran,

“Mommaaa!  Ki ce Haneef ya rakani!”

Miƙewa Haneef ya yi yana toshe Kunnuwa Fu’ad ya kama dariya.

“Wallahi ranka zai yi mugun ɓaci. Ka je ku tafi da Lukman mana.”

Juya idanuwanshi Fu’ad ya yi.

“Hajiya ta aiki Lukman. Ka tashi mu je tare.”

Ya san halin Fu’ad sarai, ba zai bar shi ya huta ba in ba tashi ya yi ba. Dole ya miƙe suka fito tare.

Motar Fu’ad ɗin suka shiga. Haneef ya ɗauke jakar system ɗin shi da ke ajiye a inda zai zauna.

Sai da ya zauna ya ɗora jakar akan cinyarshi. Fu’ad ya ja motar suka tafi.

*****

Basu wani daɗe a gidan Babban Yaya ba. Don ya ma fita sai matarshi kawai suka gaisa da ita.

Fu’ad ɗin ya ce a gaishe masa da shi za su dawo ko zuwa gobe ne in Allah ya kaimu.

Sun fito suna hanya ne Fu’ad a dole sai ya tsaya ya siya shawarma. Biris ya yi da tsegumin da Haneef ya ke mishi.

Ya yi parking ɗin motar ya fice. Siyowa ya yi ya dawo suka wuce gida zai ajiye Haneef ɗin.

Fu’ad ya fara fitowa daga motar. Haneef ya buɗe motar shi ma yana fitowa jakar dake hannunshi ya kai zai ajiye zip ɗin ya buɗe.

Da sauri ya tare system ɗin da takardun da suke ƙoƙarin zubowa yana faɗin.

“Ya Rabb….”

Komai ya ke ƙoƙarin gyarawa yadda ya ke, wasu takardun asibiti suka ja hankalinshi. Zaro su ya yi ya rufe motar yana dubawa.

Fu’ad ya zagayo ɓangaren Haneef ɗin. Das! Ya ji gabanshi ya wani faɗi ganin takardun da su ke hannun Haneef.

Har ranshi ya yi niyyar gaya mishi amma ba yanzun ba. Sam ba ta haka ya so Haneef ya gani ba.

A hankali ya ce,

“Haneef…”

Hannu kawai Haneef ya ɗaga mishi fuskarshi kafe kan takardun da ke hannunshi. Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi.

Ba ya son damuwa da wani ciwon kai. Fuska Haneef ya ɗago ya kall Fu’ad da wani irin yanayi da ya sa zuciyar Fu’ad dokawa.

Kallon shi Haneef ya ke yana so ya ga ina ƙaninshi ya ke. Ƙaninshi da ya san ba zai taɓa aikata irin wannan abin bai shawarce shi ba.

Ƙaninshi da ba zai yi wannan rashin hankalin ba. Wannan ba Fu’ad ɗin da ya sani ba ne. Wani Fu’ad ne a tsaye a gabanshi da bai san daga inda ya fito ba.

A tsorace Fu’ad ya ce,

“Haneef ni ne…”

Saboda ya karanci kallon da Haneef ɗin ke mishi. Takardun ya sake kallo ya ɗago ya kalli Fu’ad. Girgiza kai Fu’ad ya ke yi ganin katangar da ke ginuwa tsakanin shi da Haneef ɗin lokaci ɗaya.

Tunda ya ke a rayuwarshi bai taɓa jin yayii kuskure har cikin ranshi ba kamar yanzun. Kuskuren da ya shiga tsakanin shi da ɗan uwanshi.

Cikin gida Haneef ya yi da takardun a hannu. Da gudu Fu’ad ya bi shi yana faɗin,

“Haneef. Ka saurareni don Allah…”

“Mommaaaaaa!”

Haneef ke kiranta. Hannunshi Fu’ad ya riƙo ya fisge yana ture Fu’ad ɗin.

“Don’t. Just don’t…”

Fuskar Haneef da ya kalla ya sa shi tsayawa kawai yana dafe kai.

“Damn…!”

Momma ce ta fito daga ɗaki da sauri kallo ɗaya ta yi wa yanayinsu ta ce wa Haneef,

“Lafiya? Me ya faru?”

Dai dai lokacin da Abba ya yi sallama. Momma ta amsa mishi. Ganin su cirko-cirko ya sa shi cewa,

“Me ke faruwa ne?”

Kallon Haneef momma ta yi Shi kuma ya kalli Fu’ad idanuwanshi da wani irin distant look a ciki. Har yanzu ya kasa yarda da abinda ya ke gani.

Takardun ya sake dubawa don ya tabbatar da gaske ne abinda ya ke gani Fu’ad ya aikata.

“Fu’ad wai lafiyarku kuwa? Kuna ji ana ta magana kun yi shiru.”

Cewar momma a tsawace. Idanuwa Fu’ad ya sauke a kanta. Shi bai ma yi niyyar gaya musu ba. Daga Lukman sai Haneef.

Sake kallon Haneef ya yi, da idanuwanshi ya ke roƙonshi da abin ya tsaya tsakaninsu. Kai ya girgiza mishi ya maida hankalinshi kan Momma.

Sannan ya dubi Abba. Fa’iza ce ta fito daga kitchen ita ma ta yi tsaye tana ƙoƙarin fahimtar abinda ke faruwa.

Cikin wata irin murya da wani yanayi a fuskarshi Haneef ya ce,

“Momma Fu’ad. Fu’ad ba shi da hankali ko kaɗan…”

Kanshi ya nuna da duk hannayenshi ya ci gaba da faɗin,

“Ni banda wata daraja a idanuwan Fu’ad ban isa ya faɗa min ba kafin ya yi wannan haukan.”

Ya ƙarasa yana miƙa wa Momma takardun da ta karɓa baki a sake. Lumshe idanuwa Fu’ad ya yi tare da faɗin,

“Haneef….”

Hannu ya ɗaga mishi alamar ba ya son ji. Sannan ya juya ya sauke idanuwanshi kan fuskar Fu’ad.

“Ba na son ji. Ba na son jin duk wani abu da zai fito daga bakinka…”

Takardun Momma ke dubawa hannunta har rawa ya ke yi. Idanuwanta sun tsaya kan kalma ɗaya VASECTOMY.

Cikin kanta ta ke duddubawa inda ta adana bokonta ta ke son fahimtar kalmar. Kai take girgizawa. Abba da ke tsaye ya ƙaraso ya karɓi takardun daga hannunta yana faɗin,

“Wai menene?”

Dubawa ya shiga yi. Jingina da bango Fu’ad ya yi yana jin kamar a ce yana da wani sihiri da zai iya ɓacewa ɓat su neme shi su rasa da su tirke shi kan abinda ya ke tunanin bai shafe su ba. Rayuwarshi ce ba tasu ba.

Wani irin kallo Momma ta ke ma Fu’ad muryarta na rawa ta ce,

“Kace min ƙoƙarin yi ka ke ba ka aikata ba…”

Abba ma idanuwa ya zuba mishi. Yana jiran ya ji amsar da zai bayar don ji ya ke zuciyarshi har wani ɗaci ta ke yi saboda takaici.

Duk wata ƙaddara mai muni da za ta auka mishi daga fannin Fu’ad ta ke tasowa. Yau shi ya haifi yaron da baya son haihuwa.

Ɗaya bayan ɗaya Fu’ad ke kallon fuskokinsu. Cikin sanyin murya ya ce,

“Na riga na yi momma. Shi ya mayar da ni wannan karon. Ina jin cikin ku Abba ne kawai bai san ba na son yara ba.

Na sha faɗa ba sau ɗaya ba. Kuma a gabanku. Ban ɗauka don na yi wannan zai zama wani babban abu ba…”

Wannan karon Momma ce ta ƙarasa inda Fu’ad ya ke ta ɗauke shi da mari. Riƙe kunci ya yi yana kallonta cike da mamaki.

Abinda ba ta taɓa mishi ba tun daga yarinta sai yau. A ƙufule ta ce,

“Fu’ad ka fita idona wallahi. Har yaushe kai hankalin da za ka yanke irin wannan hukuncin.”

Fa’iza kuwa ta ware idanuwa jin Fu’ad ya ce,

“Banga wani abu a vasectomy ba Momma. Rayuwata ce wannan saboda me za ku kasa fahimta…”

Da mamaki da wani yanayi Momma ke kallon Fu’ad. Ɗaga hannu ta yi za ta sake marin shi Abba ya yi sauri ya riƙe hannunta da faɗin,

“Ki rabu da shi kawai. Ba zamu zauna shi kaɗai yana ɓata mana rai ba. Alhamdulillah tunda ba shi kaɗai muka haifa ba. Kai da ba a haihuwa za a haifoka ne.

Duka shekarunka nawa da har za ka yanke hukuncin ba ka son zuri’a?”

In ran Fu’ad ya yi dubu ya ɓaci. Ya rasa meye abin ɗaga hankali cikin wanna abin. Jikinshi ne, fayuwarshi ce idan basue bashi goyon baya ba sai su zuba mishi ido.

Kanshi a ƙasa ya ce,

“Abbah ba ni da wajen su ne a rayuwata. Yanzun na ke ƙoƙarin building career ta. Da me zan ji? Me…”

Hannu Abba ya ɗaga mishi yana jin kamar ya shaƙe shi ya huta kawai. Muryarshi a dake ya ce,

“Duk wani abu da ka sani naka ne a gidan nan ka kwashe. Aje ai building ɗin career lafiya.

Kar ƙafarka ta ƙara shigo min cikin gida.”

Gaba ɗayansu ware idanuwa suka yi akan Abba. Momma kanta kallonshi ta ke yi tana ganin tsaurin hukuncin da ya yanke.

Su Hussaina ne suka shigo da sallama an rasa me bakin amsa musu. Abba suka fara riƙewa da murna kafin Hussaina ta ga Fu’ad.

Da gudunta ta ƙarasa inda ya ke ta riƙo mishi hannu. Duk da abinda ya ke ji bai hana shi yi mata wani guntun murmushi ba kafin ya maida dubanshi zuwa Abba da ya ce,

“Ka ji abinda na ce. Kabar min gida Fu’ad, ka bar min gida karka sake shigo mon ballantana inganka raina ya ɓaci.”

Momma ta kalli Abba, kafin ta yi magana ya ce,

“Zaɓi biyu ki ke da shi. Ko ni ko ðanki. Na gaji da halinshi. Ban haifi yaron da zai samun hawan jini ba. Tunda ban saka wa nawa iyayen ba.”

Yana rufe baki ya juya ya nufi sashin shi.  Wasu hawaye suka zubo wa Momma, ta kalli Fu’ad ta ce,

“Ka ga abinda rashin hankalinka ya janyo ko?”

Hussaina da ba ta fahimci me ke faruwa ba ganin Momma na kuka ya sa ta kama ita ma. Fa’iza ma kukan ta ke yi.

Wani numfashi Fu’ad ya ja yana jin gaba ɗaya duniyar ta mishi zafi. Zuciyarshi ya ji ta wani bushe. Saboda me Abba zai mishi haka.

Akan ya zaɓi ya tsara rayuwarshi ba tare da ra’ayin kowa ba. Hussaina da ke riƙe da hannunshi ya kalla. Ya sa hannu ya cire nata ya nufi sashinsu.

Kowa kallo ya bi shi da shi har ya ɓace wa ganinsu. Ɗakin shi ya shiga. Jaka ya ɗauka ya buɗe wardrobe ɗin shi.

Kayane kawai a ciki. Gani ya yi babu abinda zai ɗauka ciki. Karewa ɗakin kallo ya ke yi. Wani pink ɗin hanky ya hango kan gadon shi.

Hussaina ta bashi shi. Ba zai manta ba har yana ce mata na mata ne ta ce ta rubuta sunanshi a jiki da hannunta har cakewa ta yi da allura zai ce baya so.

Hannu ya sa ya ɗauki hankyn  yana jin kamar ya ciro zuciyarshi ya ajiyeta gefe ɗaya ya ɗan huta. Ɗakin ya ke ƙare wa kallo.

Yana ma kanshi da zuciyarshi alƙawarin ƙin sake tako gidan ma ballantana ɗakin. Ba zai saka wa Abba hawan jini ba kamar yadda ya ce.

Lumshe idanuwanshi ya yi tamkar wanda ya ke son ɗibar duk wani memory da ya taɓa spending cikin ɗakin ya adana su don kar su ɓace mishi.

Jakar ya ajiye kan gadon saboda babu abinda zai zuba a ciki. Wardrobe ɗin shi ya sake buɗewa ya ɗauki wata riga da momma ta taɓa siyo mishi.

Bai taɓa sakawa ba saboda ta mishi girma sosai. Ya ajiyene saboda ya san yafda ta siyo mishi rigar cike da ƙaunarta a wajenshi.

Ƙafarshi da wani irin nauyi ya ke takawa ya fito daga ɗakin. A hankali ya janyo ƙofar, ƙarar rufeta na rufewa da wani ƙyaure a zuciyarshi da bai san inda ya samo shi ba.

Da ƙyar ƙafafunshi suka kai falon. Suna tsaye inda ya bar su. Fa’iza ya fara samu. Tana tsaye tana kuka. Kallonta ya ke yi.

Muryarshi a dakushe da ɗacin abinda ya ke ji ya ce,

“Be safe. I will always love you.”

Riƙe mishi hannu ta yi tana wani irin kuka saboda ta kasa ma magana. A hankali ya zame hannunshi daga nata ta durƙushe a wajen tana wani irin kuka.

Ko me Fu’ad ya aikata. Ba ta ga dalilin da zai sa a kore shi daga gidan ba. Abba ba kanshi kaɗai ya kamata ya duba ba har da su.

Wajen Momma ya ƙarasa ya zuba mata idanuwa. So yake ya kalleta sosai don zai musu nisan da bai san ranar da zai sake ganin fuskarta ba.

Cikin kuka ta ce,

“Karka yi Fu’ad karka sake wani kuskuren. Ka je gida zan shawo kanshi…”

Kai ya girgiza mata yana jin wani abu game da Abba da ya kasa fahimtar ko mene ne. Zuciyarshi ya ji ta ƙara bushewa.

“Momma ki yafe min. Zamana zai iya samar miki da matsala…”

Kasa ƙarasawa ya yi saboda wani abu da ya tsaya mishi a wuya. Wuce ta ya yi ya ƙarasa inda Haneef ya ke. Ba ya ƙaunar abinda ya ke gani cikin idanuwan Haneef sam. Ba ya son yadda ya ke kallonshi.

Karantar rungume shi ɗin shi da Fu’ad ke shirin yi ya sa Haneef ɗan matsawa baya. Ware idanuwa Fu’ad ya yi da mamaki.

Cikin wata irin murya Haneef ya ce,

“In har ka tafi karka dawo. In ka tafi ka tabbatar da ka bar mu kenan. Ka tabbata shi ne kuskure na biyu mafi girma da za ka aikata…”

Wani abu da ya tsaya mishi a wuya yake kokarin haɗiyewa amma ya ƙi wucewa sam. Shi ma Haneef ɗin ya tsane shi kenan.

Kallon shi ya yi sosai bai ce komai ba ya nufi hanyar waje. Da gudu Hussaina ta bishi ta riƙe masa riga tana kuka.

“Ina za ka tafi wai?  Momma ku ce ya tsaya.”

Lumshe idanuwanshi ya yi. Ya juyo ya tallabi fuskarta da ke jiƙe da hawaye. Ranƙwafawa ya yi ya sumbaci goshinta.

“Duk nisan da zan yi kina zuciyata Hussaina…”

Hassan ya kalla. Ya girgiza mishi kai tare da faɗin,

“Karka tafi. Ko me ka yi muna buƙatar ka. Wa zai je ya ga ko zan iya zama ɗan ball ni ma?

Wa zai rabani faɗa da Hussaina?”

Miyau Fu’ad ya ƙara haɗiya. Da ƙyar ya iya cewa,

“Ga Haneef nan. Ga Fa’iza ga su Babban Yaya.”

Girgiza mishi kai Hussaina ta ke yi.

“Babu wanda zai so mu kamar ka. Don Allah karka tafi.”

Ɓanbare Hussaina ya ke ƙoƙarin yi daga jikinshi. Fa’iza ta ƙaraso inda suke idanuwanta a bushe.

Hussaina ta kama ta janye ta ce,

“Tunda ya zaɓi ya bar mu ki ƙyale shi mana. Sai mu fasa rayuwa don ba ya nan?”

A hankali ya ce,

“Fa’iza…”

Ware idanuwanta ta yi akanshi. Irin kallon da Haneef ya ke masa ya ke gani cikin idanuwanta. Wani numfashi ya ja kafin ta ce,”

Ka tafi abinka. Ƙaunarka ba za ta kashe mu ba.”

Jan Hussaina ta yi da ta ke wani irin kuka tana ƙoƙarin ƙwacewa. Momma ya kalla ta kauda kai gefe.

Ita ma ya karanci zaɓin da su Haneef suka bashi ta ke bashi ba tare da ta furta ba. Wucewa ya yi da duk takun da ya ke yi zuwa fita daga gidan yana jin yadda ya ke barin wani ɓangare na zuciyarshi.

Da ƙyar ya kai mota. Ya buɗe ya shiga. Wani dishi-dishi ya ke gani..!

*****

Ta rasa me ya sa gabanta ya ke ta faɗuwa tun ɗazun. Wayarta ta ɗauko ta kira Fu’ad har sau uku bai ɗauka ba.

Miƙewa ta yi ta je wajen window ta tsaya saboda haka kawai ta ji hankalinta ya kasa kwanciya. Tana nan tsaye ta ga motarshi ta ƙaraso. Wata ajiyar zuciya ta sauke saboda yadda ta ji hankalinta ya kwanta. Tana ganin ya fito daga mota ta ƙarasa ta buɗe ƙofar. Dai dai shigowarshi. Bai ko yi sallama ba ya ja ta jikinshi ya rungume ta. Wani sauƙi-sauƙi ya ke ji a zuciyarshi.

Rungume shi ta yi itama tana karantar akwai abinda ke faruwa. A hankali ta zame jikinta ta ɗaga kai tana kallon fuskarshi.

Wani irin haske ta ga idanuwanshi sun yi. Gaba ɗaya ya canza kamar ba Fu’ad ɗin da ta saba gani ba. A tsorace ta kai hannu ta taɓa kuncin shi.

“Mene ne?”

Ta tambaya da wani yanayi a muryarta. Hannunta ya riƙe ya sauke numfashi kafin ya ce,

“Abbah ya koreni Sofi. Baya son in sake shigar mishi gida.”

Ware idanuwa ta yi ta riƙe baki tare da faɗin,

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Me ka yi mishi? Ko akan aurenmu ne? Ba ka ce ya haƙura ba….”

Ganin yadda ta rikice ya sa shi riƙota jikinshi. Kuka ta ke wanda baya so saboda tana ƙara rikita mishi lissafi.

Tana ƙirjinshi kwance luf ta ce,

“Me ka yi?”

A hankali ya ce mata,

“Vasectomy…”

Da rashin fahimta ta ce,

“Mene ne shi ɗin?”

Don ba ta san ma’anar abin ba ba kuma ta ga alaƙarshi da korarshi da Abba ya yi ba. Muryarshi can ƙasa ta ji ya ce,

“ƙwayayen haihuwata na kashe gaba ɗaya.”

Kamar wadda aka yi wa allurar rashin kuzari ta ke ɗagowa daga jikinshi. Yana jin yadda ta ke zamewa daga jikinshi.

Wani irin ihu zuciyarshi ke yi. Kallon Safiyya ya ke yi har ta bar jikinshi ta sauke idanuwanta cikin nashi da wani yanayi.

Kunnuwanta ke amsa maganar da ya yi. Takai mintina biyu tana tauna nauyinta. A hankali maganar ke yawata zuciyarta.

Tana gaya wa duk wani waje da ya yarda da Fu’ad cewar ƙarya ne. Son shi da ya ke mata na ƙarya ne in har ba ya son haɗa jini da ita.

Inna!  Baba!  Yaya!  Usman!

Zuciyarta ke jero mata a hankali.  Duk danginta duk wata rayuwa tata. Yadda ta fito daga gida ta bi Fu’ad ta ke gani cikin idanuwanta.  Yadda ta bar komai ta biyo soyayyarshi ta ƙarya ta ke hangowa. Komai ƙarya ne. Duniyarshi tashi ce shi kaɗai. Ƙarya ya ke da ya ce ta shigo ciki. A bakin ƙofa ya ajiyeta saboda babu wani waje a zuciyarshi da duniyar shi sai son kanshi.

Cikin muryar da ba ta gane tata ba ce idanuwanta cikin nashi ta ce,

“Sai ka baro gidan? Ka bar kowa?”

Cikin rashin fahimtar tambayar ta ya ce,

“Me zan zauna in yi Sofi? Ba ni na zaɓi in tafi ba?  Abba ya koreni saboda na zaɓi tsara rayuwata ba tare da shawararsu ba.”

Sai yanzun ta gane. Sai yanzun ta ga Fu’ad sosai. Sai yanzun ta ga babu komai a tare dashi sai son kanshi. Shi ya sa ya aureta. Shi ya sa ya yanke musu hukunci kamar shi kaɗai ya ke yi da haƙƙi akan hakan. Kallon safiyya ya ke yi. Yadda ta ke matsawa baya. Riƙo ta ya kai hannu ya yi ta ture shi da wani irin ƙarfi.

“Ashe ba ka sona?”

Wata guduma ya ji ta doka cikin kanshi.

“Ashe ƙarya ne duk kalamanka?”

Wanna karon zuciyarshi ce ya ji ta rabe gida biyu. Da ƙyar ya iya cewa,

“Sofi…”

Cikin tsawa ta na wani dafe kai, ta ce,

“Ba na son ji Fu’ad!!! Wa ya baka ikon yanke mana wannan hukuncin? Ka taɓa tunanin in kai ba ka son yara ni ina so?

Ashe duk ƙarya ne. Duk ƙarya ne komai?”

Sauran lemar da ke cikin zuciyarshi ya ji ta ƙarasa bushewa tsaf. Dariyar takaici ya yi ya ce,

“Akan sonki na yi wannan abin. Saboda ba na so ke ki yi ne jikinki ki ya cutu. Ki rasa inda za ki ɗora darajar sona sai kan ƙarya Sofi?”

Girgiza kai ta ke wasu hawaye na bin fuskarta.

“Karka gaya min me kai Akan so, ni Safiyya ya kamata in ba da wannan labarin Fu’ad.

Na bar komai Akan so ashe ƙarya ne ba ka son haɗa jini da ni.”

Kai ya dafe a tsawace ya ce,

“Enough Safiyya!”

Sai da ta razana. Ji ya ke kamar kanshi zai yi bindiga. Wai da me zai ji ne. Kallonta ya ke kamar bai taɓa ganinta ba. Kafin ya ce,

“I don’t do happily ever after. Daga ranar da kika yarda da soyayyata ya kamata ki san ban yi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba. Ban yi kama da wanda zai yi asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Ina da su Haneef. Ina da su Fa’iza. A duk sanda na ji marmarin ganin yara zan je gidansu in ga na su.”

Karasawa ta yi inda ya ke ta cakumi wuyan rigarshi. Tana wani kukan da na sani.

“Ban san ba ka da soyayyar bawa kowa ba sai kanka da ban yi kuskuren yarda da ƙaryarka ba.

Ka cuce ni Fu’ad. ka raba ni da kowa. Ka sa zuciyata ta yarda da dukkan alƙawurranka.”

Hannunta ya kama yana jin yadda zuciyarshi ke tarwatsewa. Bai taɓa zaton Safiyya za ta yi mishi haka ba. Cikin idanuwa ya kalleta ya ce,

“Baki san me ki ke faɗa ba Sofi. Za mu yi magana in kin nutsu.”

Wucewa ya zo yi ya fita daga gidan, don ya ɗan sha iska ta riƙo shi gam. Wata irin tsanar shi da ba ta san cewar akwai irinta ba a duniya na ziyartarta.

“Ba na son ganinka wallahi. Ba na son sake ganinka.”

Ƙafafuwanshi ya ji suna wani irin rawa. Riƙe hannayenta ya yi muryarshi na rawa ya ce,

“Sofi…”

Kai ta ke girgiza mishi tana wani irin kuka.

“Na san ba zaka taɓa iya ba ni soyayyarka ba saboda ban taɓa ganin mai son kai irinka ba.

Ba kuma za ka iya ba ni yaran da zan sami soyayarsu ba. Na rabu da iyayen da suke sona na biyoka bayan ba ka da abinda za ka bani.”

Kallonta ya ke yi. Kallonta ya ke sosai yana auna maganganunta yana ganin tsantsar sonkan da ya yi mata.

Hannu yasa ya tallabi fuskarta dam. Ƙwacewa take so ta yi, saidai ba ta da ƙarfin hakan.

“Ina sonki sofi. Wallah ina sonki.”

Kallonshi ta ke yi hawaye na sake bin fuskarta.

“Ka ba ni yara. In har ka na sona da gaske ba ƙarya kake ba.”

Numfashin shi da ke ƙoƙarin ƙwacewa ya ke ƙoƙarin kamawa. Zai iya ba ta yara ne ta hanya ɗaya. Kallonta ya ke yana girgiza kai. Sai lokacin wasu hawaye suka zubo mishi. Sosai yake girgiza mata kai.

“Kabani yara in kana sona Fu’ad…”

Lumshe idanuwanshi ya yi wasu hawayen suka sake zubowa yana jin dirarsu tare da dukkan zuciyarshi.

A maimakonta wani irin abu na maye gurbin da ta bari. Da ƙyar ya iya fito da kalaman da suke shirin kashe shi har lahira.

“Na sake ki saki ɗaya sofi…”

Ƙwacewa ta yi daga hannunshi tana yin Kasa. Saboda yadda Kafafuwanta suka kasa ɗaukarta.

Ba ya son sake kallonta kar ya kasa tafiya. Kar ya kasa ba ta abinda ta nema saboda yana da son kanshi kamar yadda ta faɗa.

Wani irin gunjin ihunta ya daki kunnen shi.

“I hate you Fu’ad. Ba na fatan sake ganinka a rayuwta.”

Wani numfashi ya ja ya na takawa zuwa waje.

“Mayaudari…!”

Takawa ya sake yi .

“Na tsaneka Fu’ad na yi da na sanin ƙaddarar da duk ta sa na fara ganin fuskarka a rayuwata…”

Ƙofa ya buɗe ba tare da ya juya ba. Ko kalamanta ba su kashe shi ba sun kashe abinda ya yi saura a zuciyarshi.

Motarshi ya buɗe ya ɗauki jakar system ɗinshi. Komai da ya ke buƙata yana ciki. Fita ya yi daga gate ɗin gidan ya miƙe hanya yana jin shi kamar ba shi ba.

Ya fita titi bai ma kula da motar Lukman ba sai da ya yi parking ya fito ya biyoshi ya dafa shi.

Juyowa ya yi. Gaba ɗaya a firgice yake. Lukman ya ce,

“Yanzun Haneef ya kira ni. Fu’ad me kayi?”

Murza kanshi ya yi kafin ya kalli Lukman sosai.

“It is my life saboda me kowa zai kasa fahimta ta.”

Fu’ad ya ke faɗi cikin hargowa.

Girgiza kai Lukman yake yi cikin ganin wauta da rashin hankalin abinda Fu’ad ɗin ya aikata.

“Wallahi duk yadda kake faɗar rashin son haihuwa ban taɓa kawowa ya yi ƙamari haka ba Fu’ad. Ban kuma taɓa zaton cewa a zamanmu za ka yanke hukunci irin haka ba tare da ka shawarce ni ba.”

saima ka ji abinda na sake yi za ka yi mamaki tunda rayuwata ce ba ta wani ba. Faɗar fu.ad ɗin cikin ranshi a fili kuma ya ce,

“Na saki sofi!!!”

Lukman baisan sanda ya ɗauke Fu’ad da wani irin mari ba. Fuskarshi ɗauke da wani yanayi da ya girmi tsana da kuyamata ya ce,

“Fu’ad anya ba ka haukace ba? Ko dai maƙiya sun maka asiri ne?

Na ɗauka akan auren Sofi kawai Allah ya gama jarabtarka.

Na ɗauka ka gama girbar mugayen halayenka. “

Wata irin dariyar takaici Fu’ad ya yi tare da faɗin,

“Zan bar muku ƙasar gaba ɗaya. I have set her free. Ta auri wanda zai iya bata yara. Kai ma bankwana na zo in yi maka.”

Kallonshi lukman yake. Ya zo ya raɓa shi yana wucewa. Murya a dake ya ce,

“We are done Fu’ad. Ban ga me ya rage ba. Be safe.”

Kallonshi kawai Fu’ad ya yi ya wuce abinshi. Yana ganin motar Lukman ɗin ta zo ta wuce shi fuuu.

Wata irin dariya Fu’ad ya kwashe da ita yana jin cewar ya samu matsala. Dariya yake sosai kamar mahaukaci…!!!”

21 February 2017

Yanzu ma dariyar ya kwashe da ita saboda bai ga haukan da ya sake tako da ƙafarshi Nigeria ba bayan shekaru sha ɗaya!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 26Akan So 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×