Skip to content
Part 26 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Tana yin sallar La’asar ta koma falo ta zauna tana kallo. Tun da suka ci abinci Fu’ad ya sake fita.

A nan ya sameta da ledoji a hannu da Safiyya ta san kayan ciye-ciye ne a ciki. Tun tana mamakin kalar cin abincin Fu’ad har ta daina.

Ƙasa ya zauna ya ajiye komai. Robobin ice cream ya fiddo guda huɗu ya ajiye. Ya kalli Safiyya da idanuwanta ke kanshi.

“Sakko mu sha.”

Ba ta yi mishi musu ba ta sakko. Ta ɗauko roba ɗaya ta buɗe. Har ya soma koya mata ‘yan ciye-ciyen nan. Ba ta ko shanye rabi ba ta ajiye. Don yanzun ta na iya fara tari. Sam ba sa shiri da sanyi.

“Kin yi me kenan?”

Fu’ad ya buƙata yana ajiye robar da ya shanye ya ɗauki wata ya buɗe.

“Na ƙoshi. Sai ka yi mura ko?”

Ware idanuwanshi ya yi akanta. Yana ci gaba da shan ice cream ɗinshi. Hankalinshi ya maida kan fim ɗin da ta ke kallo na Hausa Zuri’a.

“Wai duk yaranta ne wannan ukun?”

Ya tambayi Safiyya ta amsa shi da,

“Eh mana. Abin sha’awa ko?”

Yamutsa fuska ya yi tare da faɗin,

“OH-OH…”

Da mamaki ta ke kallonshi.

“Basu burgeka ba kenan.”

Girgiza mata kai ya yi.

“Ko kaɗan…”

Dariya ya ba ta.

“Inka haifi naka za su burgeka.”

Ware idanuwanshi ya yi akanta yana faɗin,

“Wa?  A duniyarmu babu yara Sofi. Daga ni sai ke.”

Dariya ya ba ta. Fu’ad akwai zolaya ta faɗi a ranta ba ta ce mishi komai ba har aka yi magriba. Sannan ya fice masallaci.

Kwashe robobin ice cream ɗin da ya shanye guda uku ta yi. Sauran nata kuma ta buɗe fridge ta saka in Mama Indo ta shigo ta ba ta.

Kafin ta wuce ɗakinta.

A kwance ta fito daga wanka ta same shi kan gadon yana danne-danne da wayarta.

Zama ta yi a gefenshi. Ya ɗago ya kalle ta. Sosai ya kai kanshi jikinta yana shaƙar ƙamshinta.

“Wane irin turaruka ne wannan?”

Dariya ta ɗan yi.

“Ban san sunan su ba. Anty Fatima ta haɗo min ranar da muka je gidan tan nan.”

Sake shaƙa ya yi yana wani sauke numfashi. Sun mishi daɗi sosai.

“Nima a shafa min.”

Hannunta ta goga a fuskarshi.

“Gashi nan.”

Riƙe hannun ya yi.

“Wayau ko Sofi?”

Ɓoye kanta ta yi a jikinshi. Sumbatarta ya yi sannan ya ja ta sosai suka koma tsakiyar gadon.

Wata irin soyayyarshi ya ke nuna mata mai tsayawa a zuciya. Da ƙyar ya kai hannu jikin switch ɗin ya kashe musu ƙwan…”

“I love you so so much Sofi.”

Na gode…”

Ya ke faɗi ya na sumbatar kanta. Ya wani riƙe ta kamar za a ƙwace mishi ita. Tun ɗazun ya faɗi mata i love you ɗin nan ya fi a ƙirga. Ta kasa cewa komai saboda son shi da kunyarshi da suka haɗe mata.

“Tashi mu yi wanka Sofi.”

Wani maƙalewa ta yi a jikinshi. Ko’ina ciwo ya ke mata. Kai ta girgiza mishi. ‘Yar dariya ya yi ya miƙe daga kan gadon.

Wanka ya shiga ya yi. Yana fitowa ya goge jikinshi ya hau kan gadon. Ɗago ta ya yi.

Sam ta ƙi haɗa idanuwa da shi. Cik ya ɗauke ta ya nufi toilet da ita.

“Zan iya zuwa da kaina…”

Cikin fuska ya kalleta.

“Kin tabbata?”

Kai ta ɗaga mishi. Bai sauketa ba sai da ya kai ta cikin banɗakin sannan ya janyo mata ƙofar a hankali. Wardrobe ya buɗe ya ɗauko mata wata rigar baccin. A hankali ya tura banɗakin ya miƙa mata. Sanda ta fito bakin ƙofar banɗakin ta same shi a tsaye. Hannunta ya kama suka hau gadon tare.

Riƙeta ya yi a jikinshi. Wata sumba mai taushi ya manna mata. Hannu ta sa tana ture shi.

“Yi haƙuri…”

Ya faɗi yana sauke numfashi.

“Bacci na ke ji…”

Ta ƙarasa muryarta can ƙasa. Gyara musu blanket ya yi tare da yi musu addu’a. Cikin sanyin murya ya ji ta sake riƙe shi ta ce.

“Tun daga ranar daka shigo rayuwata komai ya daidaita…”

Da murmushi a fuskarshi ya ce,

“Ban san akwai abinda na rasa ba a tawa rayuwar sai da na mallake ki…”

Sumbatarta ya yi a goshi yana jin numfashinta ya canza alamar bacci ya ɗauketa kafin shi ma wani ni’imtaccen bacci ya yi gaba da shi.

****

Sama-sama ya ke jin kiran Asuba. Da ƙyar ya iya tashi ya shiga banɗaki ya yi alwala. Bai tashi Sofi ba don ya san shi ya hana mata baccin kirki jiya.

Ya fita masallaci. Ya yi mamaki da ya dawo ya sameta zaune kan kafet. Ƙarasawa ya yi ya zauna a gefe.

 A kunyace ta ce mishi.

“Ina kwana…”

Ɗan ranƙwafa kanshi ya yi yana kallon fuskarta da ta ƙi ɗagowa.

“Sofi ki kalle ni mana.”

Hannu ma tasa ta rufe fuskarta tana dariya. Janta ya yi jikinshi.

“Na gaji da kunyar nan fa. Taso ki ga in ƙara rage ta…”

Ture shi ta yi tana dariya.

“Kin tashi lafiya? Ba inda ke miki ciwo ko?”

Kai ta ɗaga mishi alamar babu. Tana miƙewa.

“Ina za ki?”

“Zan shiga kitchen in haɗa maka abinda za ka karya kafin ka tafi.”

Riƙo mata hannu ya yi.

“Sai sha goma zan fita. Barshi Sofi mu ɗan kwanta. Anjima in na shirya zan siyo mana wani abu.”

Hamma ta yi kafin ta ce,

“Allah ya kaimu.”

Kallonta ya ke yi sosai. Yana sake gode wa Allah da ya ba shi ita.

“Bacci ko?”

Ya buƙata. Ɗaga mishi kai ta yi alamar eh. Miƙewa ya yi ya kama hijabinta ya cire ya ajiye gefe ɗaya yana faɗin,

“Kuma haƙuri zai min saboda na fi shi buƙatarki.”

Murmushi ta yi tana sadda kanta ƙasa. Hannunshi ya ɗora a saman kafaɗunta yana mata wani irin kallo.

“Say mi’ name Sofi. Ina son ji akan lips ɗinki.”

Murmushin dai ta sake yi. Haɗe wurin da ke tsakaninsu ya yi. Cikin kunne ya ke gaya mata kalaman da sirri ne tsakaninsu.

Kanta ta ɓoye cikin ƙirjinshi tana dariya kafin ya soma aika mata saƙon da ya sa daga shi har ita tsayuwar ta gagare su. Don haka ya ja ta kan gadon..!

Takalminshi ya ke ɗaurawa, Sofi da comb ɗin shi a hannu yana jin yadda ta ke yamutsa mishi sumar kanshi da comb ɗin.

A dole taje mishi ta ke tana ƙoƙarin kwantar da ita baya. Ƙarasa ɗaura takalmin ya yi ya riƙo hannayenta duk yana sauke idanuwanshi cikin nata.

“Kwana biyu sun min kaɗan…”

Ta faɗi can ƙasan maƙoshi. Ya lumshe idanuwa. Tun kafin su haɗa gado ma kewarta na azabtar da shi ballantana yanzun.

Ya san sai ya fi ta shiga damuwa. Miƙewa ya yi ya zaro wayarshi daga aljihu.

Kumatunshi ya haɗa da nata ya ɗaga kyamarar yana ɗaukarsu hoto. Wani kuma ya rungumota ta baya. Sannan ya mayar da ita aljihu. Ya tallabo fuskarta.

“Tafiyar lokaci ne kawai abinda ke riƙe ni in har na bar nan. Saboda na san da duk mintin da zai wuce da kusantar kwanakin da suka rage min in sake ganinki.”

Hannunta ta ɗora kan nashi tana ƙoƙarin tarbe hawayen fuskarta.

“Banda kallon turawa wanda suka fi ni kyau…”

Dariya ta ba shi ba kaɗan ba. Yana dariya ya ce,

“Sofi idanuwana kaɗai za su kalle su. Na miki alƙawari zuciyata na tare da ke komin nisa.”

Har ranta ta yarda da maganarshi. Tana jin tsakanin jiya da dare da yau da safe soyayyar da ya nuna mata babu shakku a cikinta.

Hannunta ya kama ya ɗora kan ƙirjinshi daidai inda zuciyarshi ta ke,

“Ƙarfin bugawarta zaman ki ne a ciki.”

Ba ta san lokacin da ta cire hannunta ba ta sumbaci inda ya bari. Cikin idanuwa ta kalle shi.

“Ina sonka. Ina sonka sosai.”

Rungume ta ya yi yana jin wani irin emotion da bai san ta yadda zai fara fassara shi ba.

Ƙofa ta raka shi.

“Allah ya tsare min kai a duk inda ka ke. Allah ya ba da sa’a ya dawo min da kai lafiya…”

Ta ƙarasa maganar muryarta na rawa. Girgiza mata kai ya ke yi. Ba ya son hawayen da ya ke gani cikin idanuwanta.

Sumbatarta ya sake yi sosai yana ƙoƙarin shanye duk wata damuwa da ta ke ciki.

“Sai mun yi waya.”

Kai ta ɗaga mishi tana kallo har ya fice ya yi wajen mota inda driver ke jiranshi. Ajiyar zuciya ta sauke ta sa hannu ta goge hawayen da suka zubo mata. Sannan ta koma cikin ɗaki ta kwanta.

Kiran Fu’ad kawai ta tsaya jira su sake yin sallama kafin wani bacci mai nauyi ya ɗauke ta cike da mafarkin Fu’ad.

*****

In ta duba yadda kwanaki suke wucewa suna zama satittika. Yadda satittika ke wucewa zuwa watanni abin har mamaki ya ke ba ta. Wai yanzu har sun yi watanni bakwai suna cikin na takwas da Fu’ad.

Kusancin su na ba ta mamaki sosai. Don ji ta ke yi kamar sunyi shekaru ne ba watanni ba. Banda kewar su Inna da ta ke manne a zuciyarta tana tunasar da ita abinda suka rasa na cikar farin cikinsu.

Za ta iya rantsewa babu matar da ta kai ta sa’ar miji. Don ma lokaci na musu kaɗan. Duk da hakan ba ya hana Fu’ad nuna mata soyayarshi.

A watannin nan duk bayan sati takwas ya ke zuwa ya yi kwana biyu. A dawowarshi ta biyu ne ya buɗe mata account.

Da kanshi suka je ya koya mata yadda za ta cire kuɗi ta ATM wanda bai mata wuya ba saboda ci gaba sosai da ta samu a ɓangaren karatu.

Su Khadija ke ba ta shawarar ta tafi Account Class don abu biyu za ka ɗauka dama a aji huɗu.

Safiyya Art ne da Account nata combination ɗin kuma sun ga ta fi gane lisasfi.

*****

Wannan dawowar ya karanci akwai damuwa tattare da Safiyya. Ƙyaleta ya yi sai da ya nutsu ya huta sannan.

A hankali ya ce mata,

“Sofi me ke damunki?”

Kallonshi ta yi a sanyaye ta girgiza kai alamar babu komai.

Tashi ya yi daga kujerar da ya ke ya koma ya tsugunna a gabanta ya kalle ta sosai.

“Wa ki ke da shi da zai ji damuwarki fiye da ni?”

Wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata. Ware idanuwa Fu’ad ya yi.

“Subahanallah Sofi don Allah menene?  Ko na miki wani abu ne?”

Kai ta girgiza mishi alamar a’a. Ya koma gefenta ya zauna ya riƙo hannunta.

“To mene ne?”

Kallonshi ta yi wasu hawayen na sake zubo mata.

“Ina kewar su Inna sosai. Kuma kwana biyun nan ina yawan mafarkinsu. Kawai ina son sanin halin da suke ciki ne……”

Ta ƙarasa tana kwantar da kanta a jikinshi. Kama ta ya yi yana jin wani iri a zuciyarshi. Kama ta ya yi ya miƙar da ita tsaye.

“Mu je ki shirya mu tafi.”

Da sauri ta ce,

“Ina?…..”

Ba wani alamar razana ya ce,

“Wajen su Inna. Abinda ya kamata in yi ne tuntuni. Rashin son ganinki cikin damuwa ya hana.”

A tsorace ta ke girgiza mishi kai. Riƙe ta ya yi a jikinshi. Kuka ta ke tana tuno yadda su Inna suka koreta.

“Sofi please. Ba na son kukan nan ko kaɗan. In ba mu je ba ba zaki daina ba.”

Ƙanƙame shi ta yi tana girgiza kai.

“Tsoro na ke ji.”

Kissing ɗinta ya yi a goshi yana kama ta zuwa bedroom.

“Ina tare da ke. Ni da ke zamu iya yin komai a tare. Za mu je in su Inna sun karɓe mu fine. In ba su karɓe mu ba za mu dawo.

Za mu sake komawa wani lokaci. Za mu yi ta komawa har sai sun karɓe mu.”

Da maganar shi ta samu ɗan ƙwarin gwiwa ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta. Ta fito ta ɗauki mayafinta ta sa takalmi suka fita.

*****

Wani irin bugawa zuciyarta ta ke yi saboda tsoron da ta ke ji. Tun Fu’ad na ƙoƙarin janta da hira har ya haƙura.

Sai dai lokaci-lokaci zai kai hannu ya ɗan taɓa nata yana son nuna mata yana tare da ita a duk abinda zai faru. Zuciyarta ci gaba ta yi da bugawa fiye da na da ganin anyo kwanar layinsu. Komai ta ke ji yana kwance mata.

Har ya ƙarasa ƙofar gidansu ya yi parking. A tsorace ta kalle shi idanuwanta cike da hawaye. Hannu yakai ya riƙe nata. Cikin sanyin murya ya ce,

“Be strong sofi. In shaa Allah komai zai zo da sauƙi.”

Hawayen da suka zubo mata ta goge. Tana kallo ya fita daga motar ya rufo. Zagayowa ya yi ya buɗe mata. Ganin ta ƙi fitowa ne ya sa ya kamo hannunta ya fito da ita. Gabanta faɗuwa ya ke. Ji ta ke kamar ta ruga ta koma mota.

Idan su Inna suka sake korarta fa? Suka sake mata abinda ya fi na farko. Wani ɓangare na zuciyarta kuma ya ke faɗa mata bakomai ai. Ko dai sun sake korarta ta gansu.

Ta ga suna nan lafiya. Hankalinta sai ya ɗan kwanta. Tare suka taka har ƙofar gidansu. Ƙafafuwanta sun mata wani irin nauyi.

Buɗe baki Safiyya ta yi za ta yi masa magana daidai fitowar wata yarinya daga gidan da za ta kai shekaru sha biyar.

Da mamaki Safiyya ke kallonta don za ta rantse ba ta taɓa ganinta ba kamar yadda ita ma ta ke kallon Safiyyar.

Wani miyau ta haɗiye sannan ta ce wa yarinyar.

“Sannunki….”

Ta amsa da,

“Ina wuni.”

A tsorace Safiyya ta kali Fu’ad sannan ta maida dubanta zuwa ga yarinyar.

“Su Inna suna ciki?”

Da mamaki yarinyar ta ce,

“Innarmu ki ke nufi?”

Safiyya ta girgiza mata kai.

“Aa masu gidan.”

Cikin rashin fahimta yarinyar ta ce,

“Mu ne masu gidan ai.”

Da sauri safiyya ta tureta ta shige cikin gidan ba ta damu da yadda Fu’ad ke ƙwala mata kira ba.

Wata mata ta samu tana jan ruwa. A tsorace ta saki gugar ya koma ciki ganin Safiyya babu ko sallama.

“Ina inna?”

Ta tambaya tana ƙarewa gidan kallo. Cike da tsoro matar ta ce,

“Wacece ke? Daga ina haka babu ko sallama wacce Innar?”

Girgiza kai safiyya ta ke yi. Zuciyarta na barazanar barin ƙirjinta. Kallon matar ta yi idanuwanta cike da hawaye ta ce,

“Dan Allah masu gidan na ke nema.”

Sai lokacin matar ta gane inda ta dosa.

“Allah sarki. Mu muka siya gidan. Watansu biyu kenan da tashi.”

Wani abu Safiyya ke ji yana mata yawo cikin kunnuwa. Da gudu ta fito ta samu Fu’ad da ya ke kai kawo a ƙofar gidan.

Da sauri ya kamata ganin tana shirin shiɗewa. Fuskarta ya ke ɗan bubbugawa.

“Sofi mene ne?”

Da ƙyar numfashinta na wani sama sama ta ce,

“Sun tashi. Ba sa gidan…… Wallahi ba sa nan.”

Ware idanuwa Fu’ad ya yi. Kafin ya ɗan saita kanshi sanin tana buƙatar shi.

“A’a sofi. Ki kwantar da hankalinki. Babu inda suka je. Ki jira ni a nan bari in tambayo mutanen can.”

Kai kawai ta ɗaga mishi tana kallonshi ya tsallaka inda majalissar ta ke yana magana da su. Wani irin dokawa zuciyarta ta ke yi. Yana tahowa ta kasa jira ya ƙaraso ta taka suka haɗe a hanya.

Fuskarshi kawai ta kalla zarginta ya tabbata. Tsuggunnawa ta yi a wajen tana sakin wani irin kuka.

Riƙota ya yi da ƙyar . Ya ja ta ya buɗe motar ya rufe saboda mutane sun soma kallonsu sannan ya zagaya ya shiga shi ma.

Sai da ya ja motar suka fita daga unguwar gaba ɗaya suka hau titi tukunna ya yi parking ya nusar hankalinshi kan Safiyya da ke zaune ta haɗe jiki tana wani irin kuka.

Dafe kai ya yi. Tuƙa motar ya yi saboda yamma ta soma yi liƙis. Yanzun a kira magriba. In sun je gida ya san yadda zai yi da ita.

*****

Da zazzaɓi ta kwana ruf a jikinta. Da ya yi maganar su je asibiti ma kuka ta sake saka mishi dole ya haƙura ya ƙyale ta.

Da safe ma shi ya taya ta har ta wanka, sai dai fuskar nan ta kumbura. Shi ma ya yi wanka tunda ranar ta zai afi.

Sai da ya gama shiryawa tsaf tukunna ya dawo inda ta ke kwance.

“Kina so in yi menene?  In tafi in bar ki da wannan damuwar?”

Shiru ta yi ta na kallonshi. Saboda ba zai taɓa fahimtar abinda ta ke ji ba.

Ya ci gaba da faɗin,

“Na gaya miki ba jimawa zan yi ba. Idan na daɗe sosai sati huɗu. Kuma ina da kwanaki da yawa.

Na miki alƙawari zan nemo su Sofi. Duk inda suka je ni zan nemo su. Ko ba ki yarda da ni bane?”

Da sauri ta ɗago ta kalle shi. Ta kasa magana. Kawai so ta ke ya mantar da ita ciwon da ta ke ji a zuciyarta ko na awa ɗaya ne.

“Please……”

Kawai ta furta tana barin idanuwanta na nuna mishi buƙatarta. Lokaci ya kalla. Awa ɗaya da rabi ya ke da shi kafin jirginsu ya tashi.

Hannunshi ta kamo ta na mishi wanni kallo da ya ɓatar mishi da tunanin da ya ke yi…….!”

*****

Tun yana wanka ya ke jinjina kuskuren da ya yi. Son Safiyya ya rufe mishi ido. Ko da yake babu yadda za a yi a ce rabo ya gifta a daidai lokacin nan. Beside, yadai kusa maganin matsalar gaba ɗaya.

A gurguje ya shirya. Kissing Safiyya kawai ya yi yana faɗin,

“Sai mun yi waya. I love you…”

Sannan ya fice daga ɗakin da sauri. Ajiyar zuciya ta sauke tana lumse idanuwanta!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 25Akan So 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×