Skip to content

Akan So | Babi Na Ashirin Da Takwas

0
(0)

<< Previous

Tun jiya ya kasa samun wani wadattaccen bacci. Haka ya daure ya je aiki. Yana tasowa ya wuce gida. Wanka kaɗai ya yi.

Abincin ma don Zee ta tusa shi gaba ne babu inda zai fita babu komai a cikinshi ya sa shi ɗan ci kaɗan. Wani irin abu yake ji cikin zuciyarshi da ya jima da manta yadda ya ke.

Tunani da mamakin yiwuwar samun ‘ya a wajen Fu’ad kawai ya ke yi. Tunani ya ke zuwansu nawa da shi da Haneef gidan Fu’ad.

A kulle sai mai gadi. Ƙarshe ma ce musu ya yi an siyar wa da wasu gidan. Har Bichi suka je asalin gidan su Safiyya aka ce musu sun tashi.

Bai san ko Haneef ba. Amman shi ya sake gwadawa bai samu Safiyya ba sannan ya haƙura. Wayarshi ya ɗauko ya kira Haneef ya ji ko yana gida.

Don ba ya son ya ƙarasa kuma ya samu ba ya nan. Kanshi tsaye ya wuce Rijiyar Zaki in da gidan Haneef ya ke.

*****

“Wai Lukman sai ka ce wani baƙo.”

Cewar Haneef bayan sun gaisa da Lukman ɗin. Murmushi Lukman ya ɗan yi tare da faɗin,

“Ba jimawa zan yi ba ne shi ya sa. Ya su Ummi?”

Jingina da mota ya yi sannan ya amsa shi da,

“Suna nan lafiya. Ina Junior da Zainab?”

“Yana Islamiyya daga nan zan biya in ɗauke shi.”

Wayarshi Lukman ya sa hannu a aljihu ya ɗauko ya buɗo saƙon da Hamza ya turo mishi kafin ya miƙa wa Haneef.

Karɓa ya yi ya karanta saƙon. Cike da rashin fahimta da ƙin yarda da abinda idanuwanshi suke gani mishi, ya ɗago ya kalli Lukman.

Wani murmushin takaici Lukman ya yi tare da faɗin,

“Yar Fu’ad ce Haneef…”

Girgiza kai Haneef ya ke yi cikin rashin yarda.

“Bazai yiwu ba Lukman. Kawai dai wata ce daban. Ta ina?”

“Wallahi ‘yar shi ce. Na ganta da idanuwana. Idanuwanshi, fuskarshi komai Haneef…”

Sau uku Haneef na buɗe bakinshi yana mayarwa ya rufe. Ya rasa me ya kamata ya ce.

“Na kira shi jiya. Na faɗa mishi ya dawo kafin ya sake wani kuskuren. Ba mu kaɗai zai rasa ba wannan karon. Ina jin ba ta da lafiya yarinyar. Tana buƙatar shi.”

Wayar Haneef ya miƙa wa Lukman yana jin wani abu ya tsaya mishi a wuya.

“Da baka ɓata lokacinka ba. Ba dawowa zai yi ba Lukman. Kanshi kaɗai yasani. Ba na tunanin zai dawo saboda wannan yarinyar.”

Jinjina mishi kai Lukman ya yi. Don ya fi kowa sanin halin Fu’ad. Ga shi bai ma faɗa mishi dalilin da ya sa ya ce ya dawo ba.

Sai ka ce bai san yadda Fu’ad ya ke da umarni ba. Sauke numfashi ya yi ya ce,

“Safiyya na garin nan Haneef.”

Wani abu ne ya faɗo wa Haneef a rai. Kar dai ace Safiyya ba ta bar gidan nan ba. Kawai ta sa ace ba ta nan ne.

Kallon Lukman ya yi ya ce.

“Ka san me. Je ka ɗauko Junior daga Islamiyya. Zan dubo Safiyya, i will call you ko me ake ciki.

Zan manta yadda na tsani Fu’ad a yanzu saboda in dai wannan yarinyar ‘yarshi ce tana buƙatar family ɗinta.”

Dariya Lukman ya yi ya girgiza kai kawai ya buɗe motarshi ya tafi. Tsanar Fu’ad ita ce abu na ƙarshe da zuciyarsu ba za ta iya ba. Haneef ɗin ma mota ya shiga ya fice. Text ya yi wa Ummie ya fada mata ya fita don ba zai iya komawa ciki ba.

Ko ya ya rufe idanuwanshi a hanya fuskar Fu’ad ya ke gani. Yanayin shi. Komai na ƙanin nashi. Sauke ajiyar zuciya ya yi. Yana marhabin da duk memories ɗin da suke dawo mishi. Yaushe rabon da ya bar su haka…!

*****

Zaune suke suna cin abinci a tsakiyar falon suna kallon Harry Potter a MBC2.

“Na ce miki wannan ne na ƙarshen fa Mummy. Inda suke canza kala su yi kamar Harry…”

Saida ta haɗiye abincinta sannan ta ce,

“To ni ban ganshi ba ma…”

Jinjina kai Nana ta yi abincin da ta ke ci na mata wani iri a baki. A hankali ta ajiye cokalin cikin plate ɗin da suke sharing ita da Sofi.

Abincin bakinta ta ke taunawa tana ƙoƙarin haɗiye shi a hankali a hankali. Amai ta ji yana neman taho mata.

Da gudu ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta. Sofi ta ajiye cokalin ta bi ta tana faɗin,

“Nana…”

Toilet ta sameta tana kwara amai kama zata fito da ‘yan cikinta. Dafa bayanta ta yi har ta gama aman tsaf tana mata sannu.

Zuba mata ruwa ta yi ta wanke bakinta da fuskarta. Ta taimaka mata ta cire kayan jikinta. Saboda galaɓaitar da ta Sofi ta yi mata wanka. Ta naɗota da towel ta kamota suka fito. Wata doguwar riga marar nauyi ta ɗauko mata ta bata ta saka.

Kallonta Sofi ta ke yi. Yadda idanuwanta suka shiga ciki. A satin nan ta ƙara ramewa. Sai hasken fatar. A sanyaye ta ce,

“Mu je asibiti Nana.”

Ware idanuwanta ta yi akan fuskar Sofi da sai da ta ji gabanta ya faɗi. Ko a zuciyarta ba ta son kiran sunan shi saboda ciwon da ta ke ji.

“Ba sai mun je ba. Ni kam kwanciya kawai zan yi in huta.”

Sam ba ta son takura mata. Taɓa jikinta ta yi ta ji babu zazzaɓi. Hankalinta ya ɗan kwanta kaɗan.

Kwanciya Nana ta yi. Sofi ta gyara mata blanket sannan ta zauna gefen gadon tana sauke numfashi.

Ji ta yi kamar ana kwanƙwasa ƙofa. Ta ɗan ƙara saurarawa. Ƙwanƙwasawa ne. Da mamaki a fuskarta ta miƙe.

Waye zai zo a wannan lokacin. Ta san dai idan Ansar ne kiranta zai yi a waya kafin ya zo. Miƙewa ta yi ta ce wa Nana,

“Bari in ga waye ya ke buga ƙofa…”

Ba ta jira amsar Nana ba ta fice daga ɗakin tana faɗin,

“Ana zuwa…”

Ƙarasawa ta yi wajen ƙofar ba tare da tunanin komai ba ta buɗe. Wani irin tsalle zuciyarta ta yi tana shirin fitowa daga ƙirjinta.

Ba ta san lokacin da ƙafarta ta ja da baya ba. Da mamaki ƙarara a fuskar Haneef na ganinta.

Ita ce kuwa. Safiyya ce. Lokaci ɗaya ya hango ta tana ‘yar ƙaramarta wannan kuma ta zama babbar mace. Banbancin waccan Safiyyar da wannan a bayyane ya ke. Waccan akwai yarinta. Tsoro da ƙauyanci a tattare da ita.

Wannan Safiyyar babu alamar yarinta ko kaɗan a tattare da ita. Wannan safiyyar ta mishi kwarjini saboda ta yi kama da wadda wani abu ba zai razana ba.

Safiyyar nan babu ƙauyanci a tare da ita. Sosai take kallonshi tana girgiza kai. Shekaru goma sha ɗaya ta ɓoye musu.

Sai yau ne za a ce kwatsam sun ganota. Muryarshi a sarƙe ya ce,

“Why Safiyya? Saboda me ki kai mana haka?”

Ba ta ji taruwar hawayen ba. Zubar su kawai ta ji. Muryarta na rawa ta ce,

“Kai min adalci Haneef. Bayan abinda kaninka ya yi min wanda ya taɓa ganinshi ma ba na son alaƙa da shi…”

Lumshe idanuwa Haneef ya yi yana jin nauyin tambayar da ya yi mata. Kawai ya kasa jurewa ne.

Saboda yana jin kamar da hannunshi a abinda Fu’ad ɗin ya aikata don haka ya so ya nemo Safiyya ya taimaka mata ko zai rage yawan laifukanshi.

Buɗe baki ya yi zai yi magana ta maƙale. Idanuwanshi suka kafe kan yarinyar da ke tahowa.

Bin inda yake kallo Safiyya ta yi ta ga Nana da ta ke kallon Haneef ita ma. Sannan ta maida kallonta kan Sofi tana ƙarasawa kusa da ita.

Riƙeta a jikinta Sofi ta yi tana kallon Haneef da ƙyar ya iya janye idanuwanshi daga kan Nana.

Saboda duk wani shakku kan maganar da Lukman ya faɗa mishi ya gama gogewa da ganin Nana da ya yi.

Wata kewar Fu’ad ta ziyarce shi. A hankali Nana ta ce,

“Mummy?”

Tana son tambayarta waye Haneef ɗin don ba ta taɓa ganinshi ba.

Kallonta Safiyya ta yi ta ɗan ɗaga mata kai. Alamar babu damuwa za ta iya ƙarasawa wajen Haneef ta yi mishi magana.

A hankali ta taka zuwa inda Haneef ya ke saboda ba ta jin ƙarfin jikinta. Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi tare da faɗin,

“Ina wuni…”

Ya kasa magana. Ya kasa cewa komai da irin abinda ya ke ji. Tsugunnawa ya yi don tsawonshi ya zo daidai da Nana.

Hannuwa ya sa ya tallabi fuskarta yana son ganin da gaske ne ko mafarki ya ke. Idanuwanshi ke yawo a fuskar Nana.

Kafin ya kalli Safiyya da ƙyar ya ce,

“Ya sunanta?”

Fuskarta ta goge kafin a sanyaye ta ce, “Safiyya. Muna kiranta Nana.”

Jinjina kai Haneef ya yi yana jin yadda lokaci ɗaya son yarinyar ya shigar mishi rai. Miƙewa ya yi ya kalli Safiyya.

Ta fahimci yana son magana da ita ne. Hannun Nana ta kamo ta na faɗin,

“Kije ki kwanta ki huta Nana. Zan zo yanzun.”

Haneef ta kalla ta yi masa murmushi tare da faɗin,

“Sai anjima…”

“Ya Rabb…”

Haneef ya faɗi yana binta da kallo har ta shige ciki. Kamar ta ɗaya da Fu’ad. Komai nata.

“Ka shigo.”

Safiyya ta buƙata a hankali ta na wucewa cikin falon. Bakin ƙofa Haneef ya ajiye takalminshi sannan ya bita..!

*****

Necktie ɗin shi ya warware ya jefar da shi gefe. Ya cillar da suit ɗin da ke hannunshi kan gado.

Gidan ya yi wani shiru ya san duka yaran suna Islamiyya. Jana kuma tana wajen aiki.

Waje ya samu gefen gadon ya zauna yana dafe kai. Kwata-kwata jinshi ya ke ba dai dai ba. Bai san haka Aina ta kai a zuciyarshi ba sai yau.

Sau shida yana zuwa office ɗin su su ce mishi ba ta zo ba. Tun ɗazun ya ke kokawa da zuciyarshi kan kiranta a waya.

Dawowar da ya yi ya samu gidan ba kowa ya ƙara mishi damuwa. Waya ya ɗauko ya lalubo lambarta ya kira.

Ringing biyu ta yi ta ɗaga tare da mishi sallama cikin sanyin muryar nan tata da ke saukar mishi da kasala tare da gaishe da shi.

“Lafiya ƙalau. Yau dai lafiya ko? Ba ki zo wajen aiki ba.”

Ya buƙata. Ta amsa shi da faɗin,

“Mama ce ba ta jin daɗi. Ga gidan sai mu kaɗai da muka dawo asibiti shi ne na zauna kar in bar ta ita kaɗai.”

Lumshe idanuwa Jabir ya yi yana jin wata nutsuwa. Har hankalinshi ya ɗan kwanta.

“Allah sarki. Ya jikin nata yanzun?”

“Da sauƙi sosai. Na gode da kulawa.”

Murmushi ya ji ya ɗan ƙwace mishi.

“Allah ya ba ta lafiya. Ki min text na address ɗin in zo in duba ta.”

A hankali ta ce,

“Da ka barshi kar ɗawainiyar ta yi yawa.”

“Haba ba komai. Ki turo min yanzun fa.”

Ta amsa da,

“In shaa Allah. Na gode.”

Ya kashe wayar yana miƙewa. Jinshi ya ke wani iri. Har ya ajiye wayar ya ɗauka. Jana ya kira har ta gama ringing ba ta ɗauka ba.

Jefar da wayar ya yi kan gado. Ya shiga wanka.

*****

Wata shadda ya saka me ruwan ƙasa da cizawa. Ya ɗora hula da ba ta kai shaddar haske ba da takalmi ya kuma ɗaura agogonshi.

A shekaru talatin da takwas Jabir na da wani kwarjini na ban mamaki. Mutum ne shi mai son riƙe girmanshi da ba wa kowa haƙƙin shi.

Baƙi ne. Sai dai yana da kyau dai dai nashi da tsayi matsakaici. Sajen da ke fuskarshi ya ƙara mishi wani kwarjini na daban.

Kasancewar shi ɗa na farko a gidansu ya riga ya saba da ɗawainiyar ƙannenshi guda biyu da duk maza ne tun bayan rasuwar mahaifinsu.

Kusan komai shi ya ke musu musamman da mamansu ta rasu. Shi ne uwa da ubansu duka. Ya auri Murjanatu tana level 2 tana karantar medicine.

Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya da ci gaba mai inganci. Duk da ba za a kira Jabir mai kuɗi ba yana da rufin asiri daidai gwargwado.

Wannan kenan.

*****

Sai da ya tsaya ya siyi kayan marmari leda biyu mai layi-layi sannan ya wuce unguwar Court Road inda Aina ta yi mishi text.

Gidan su bai mishi wahalar ganewa ba. Yana zuwa ya kirata a waya ta fito. Sanye ta ke da atamfa da ba zai iya faɗar skirt ba ne ko zani saboda hijabinta da ta ke sanye da shi dogo ne har ya kai ƙwaurinta.

Murmushin nan ta tarbe shi da shi da har sai da kumatunta ya lotsa duka biyun. Komai na Aina burge shi ya ke matuƙa.

Gaisawa suka yi ya sake tambayarta jikin mama. Ta ce su shiga ciki ya dubata. Haka kuwa aka yi, ya ɗauki kayan marmarin da ya siyo.

Mamansu Aina ta karɓe shi da karamci abin har mamaki ya ba shi m. Daga ita har Aina godiya sukai ta mishi kamar ya kai musu wani abu mai girma.

Sannan aina ta rakoshi har wajen motarshi.

“Nagode sosai Yallaɓai. Allah ya saka da alkhairi.”

Murmushi Jabir ya yi.

“Yallabai ɗin nan ya ƙi fita bakinki ko Aina?”

Murmushin nan dai ta yi da ya ji shi har zuciyarshi. Ya san lokaci ya yi da ya kamata ya faɗa wa Aina yana sonta. Kuma da aure.

Sai dai yana auna nauyi da ma’anar hakan a rayuwarsu shi da Jana. Farko gani ya ke kamar yawan nisantar shi da Jana ta ke yi ne ya sa son Aina ya shiga zuciyarshi.

A yau kam ya gane ko ya yaso ya ƙaryata zuciyarshi son Aina ya samu waje daram. Kuma dole ya sanar da wuri kar a samu matsala.

Harya buɗe ba ki zai furta mata sai kuma ya ce,

“Shikenan. Ni zan wuce Allah ya ƙara sauƙi. Za ki samu shigowa gobe in Allah ya kaimu ne?”

Kai ta ɗaga mishi tare da faɗin,

“Eh in shaa Allah. Ai ta warware ma. Ka gaishe da su Ikram da madam. Na gode.”

Ya amsa da,

“Za su ji. Sai mun yi waya.”

Ya shiga motar ya tayar ya tafi. A hanya ya yanke hukuncin fara sanar da Jana kafin ya gaya wa Aina.

Ba zai iya ci gaba da jan rigima da ita ba kan aikinta tunda ya san karya ya ke wa kanshi cewar aikinta ne ya sa shi son Aina.

*****

A daddafe Nuriyya ta gama girki. Ta jera komai a dining table ɗin sannan ta koma kitchen ta wanke kayan duk da ta ɓata.

Tana maida komai wajenshi ne ta ji takun tafiya a bayanta. A tsorace ta juya. Ta sauke idanuwanta kan kyakkyawar fuskar Nawaf.

Murmushi ya yi mata da shakku a idanuwanshi. Ɗan matsawa ta yi baya kaɗan. Tana tsoron kowanne kalar Nawaf ne ya shigo tunda ba tantancewa ta ke ba.

A hankali ya taka har inda ta ke. Ya ɗora hannayenshi akan kafadarta. Goshin shi ya haɗa da nata. Kamar zai yi kuka ya ce,

“Ki yafe min Nuri. Ba zan sake ba. Don Allah ki yafe min.”

Hannunta ta ɗora kan nashi da ke kafaarta ta riƙe sosai.

“Ina sonka Nawaf. Kai ma ka san ina sonka sau nawa za kai min alƙawarin ba za ka sake ba? Sau…”

Ɗan yatsan shi ya ɗora kan laɓɓanta yana faɗin,

“Shhhhhh. Kin fi kowa sanin matsalata. Kin san ba na iya controlling fushina. Musamman Akan sonki. Ba na son jin sunan Farhan a laɓɓanki ko kaɗan.”

Kau da kai ta yi gefe, ba ta son ya ga hawayen da ke taruwa a idanuwanta. Ta rasa me ya sa ya kasa gane girman Farhan a rayuwarta.

Fuskarta ya kama ya juyo da ita yana sauke idanuwanshi cikin nata. So ya ke ya ga ko tunanin Farhan ɗin banzan nan ta ke yi. Ya rasa me ya ke da shi da shi Nawaf ba shi da.

Me ya yi mata da shi bai mata ba? Makaranta ce. Sai me kuma?  Yana ina lokacin da ya sha ƙwatarta a hannun mazan da ke son lalata mata rayuwa?

Farhan ba shi ba ne ya fito da ita daga gidan karuwan nan. Shi ne. Ya rasa me zai sa ta dinga fifita Farhan da ya tafi ya bar ta akan shi.

Yanayin idanuwanshi Nuri ta kalla. Ta san abu kaɗan zai iya birkita mishi sauran tunanin da ya ke da shi. Kuskure ƙalilan ya ke jira

Light kiss ta manna mishi a laɓɓanshi sannan ta ce,

“Ka yi haƙuri, ni ma ba zan sake ba. Mu je mu ci abinci.”

Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin wucewa. Hannunta ya riƙo ya janyota ta na komawa.

Kallon fuskarta ya ke. A hankali ya sa hannu ya shafi inda jini ya kwanta. Da sauri ta riƙe hannunshi ta na janye fuskarta.

“Da zafi ko?”

Ya tambaya. A hankali ta ɗaga mishi kai. Ji ya yi ya tsani kanshi gaba ɗaya. Rungumeta ya yi a jikin shi, cikin kunnenta ya ke faɗin,

“I am so so sorry Nuri. Don Allah ki yafe min.”

Matse shi ta yi sosai. Zaman gidanshi ya fiye mata inda ta fito. Ko banza ta san babu mai cutar da ita sai shi.

“Na yafe maka. Mu je mu ci abinci.”

Sakinta ya yi. Ya kama hannunta suka wuce dining ɗin tare.

*****

Taxi ya tara ya ce ya kai shi wani hotel me kyau. Har lokacin mamaki ya ke ba kaɗan ba.

Ya rasa tsautsayin da ya sa ya yi abinda Lukman ya ce.  Meye ya ke da shi ma a Nigeria da ya dawo ma?

Momma kaɗai ke son shi. Ita kaɗai ce ta neme shi bayan watanni shida da tafiyarshi. Har su Haneef babu wanda ya taɓa nemanshi ya ji yana da rai ko ya mutu.

Duk yadda ya ke ƙaunarsu suka watsar da shi. Suka ƙi fahimtarshi ko kaɗan. Saboda sun cika son kansu.

Haka ya biya kuɗin kwana biyu a hotel ɗin ya wuce ɗakin shi. Wanka ya fara yi. Ya yi Sallar azahar da bai yi ba ya mayar da la’asar don ya ga uku har da rabi.

Ordering abinci ya yi. Da ƙyar ma ya iya ci don ji yayi taste ɗin na mishi wani iri saboda ya jima rabonshi da jin shi. Sannan ya fito.

Yana tunanin me ya kamata ya yi daga farko. Da ƙafarshi ya taka yana kallon yadda garin kano yabi ya canza gaba ɗaya.

Wani waje ya gani da ake siyar da Simcard ya ƙarasa ya siya don bashi da sim ɗin Nigeria. Ya riga ya karya shi tuntuni. Ya siya kati.

Sannan ya saka. Lambar da Lukman ya kira shi da ita jiya ya sake trying. A kunne take wannan karon. Ya lumshe idanuwa yana jin ringing ɗin wayar.

Sake jin muryar Lukman ya sa shi jin wani ɗaci-ɗaci a zuciyarshi. Da na sanin bin abinda Lukman ya buƙata bayan duk sun guje shi.

“Hello…”

Lukman ya sake faɗi a karo na biyu kafin Fu’ad ya haɗiye wani abu da ya tsaya mishi a wuya ya ce,

“Ban san me ya sa ni yin abinda ka ce ba. Ban kuma san dalilinka na nemana bayan duk shekarun nan ba. But, koma meye gani a Nigeria…”

Da sauri Lukman ya ce,

“Fu’ad? Da gaske ka zo?

Alhamdulillah.”

“Hmm…”

Kawai Fu’ad ya faɗi yana sauraren Lukman ɗin kafin ya ji ya ɗora da faɗin,

“Ka je gidanka. Koma mene ne dalilin za ka gani.”

Yamutsa fuska Fu’ad ya yi.

“Wane gidana kuma?”

“Wane gida ka ke da?”

A ƙufule ya ce,

“Lukman ba na son rainin hankali ka sani. Kawai kamin bayani yadda zan fahimta.”

Shiru Lukman ya yi. Fu’ad ya duba wayar ya ga tana reading. Don zatonshi ma ko network ya katse kiran.

“Ka na jina fa Lukman.”

Cikin sanyin murya ya ce,

“Wai ka gama masifar. Don na fara da na sanin kiranka da na yi.”

Dafe goshi Fu’ad ya yi yana jin alamar ciwon kai ya fara mishi sallama.

“Da yake ma ban roƙi ka kirani ba. Duk tsawon shekarun nan sai na fasa rayuwata da babu kiranku a ciki?”

Wani numfashi Lukman ya sauke. Kafin ya ce,

“Allah ya sa abinda za ka samu ya canza rayuwarka gaba ɗaya. Ka je gidanku kai da safiyya…!”

Kashe wayar Lukman ya yi. Gaba ɗaya Fu’ad ya ji jikinshi ya yi wani sanyi. Jin sunanta a bakin Lukman.

Gidansu shi da Safiyya. Sofinshi ta na gidansu..!

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×