Skip to content

Akan So | Babi Na Ashirin Da Tara

0
(0)

<< Previous

Fu’ad na nan yadda ya ke. Ba zai taɓa canza halinshi ba. Ya ɗauka a shekarun nan ya karanci kuskuren shi. Saima abinda ya ƙaru. Son kanshi yana nan. Shekaru goma sha ɗaya babu abinda ya canza Fu’ad da shi.

Zee ce ta fito da cikinta da ya turo. Murmushi ya yi mata a kasalance. Ta mayar masa da martani.

“Ki bi min yarinya a hankali Zee.”

Dariya ta yi.

“Wa ya ce maka yarinya ce?”

Ta ƙarasa ta dafa cinyar Lukman ɗin kafin ta zauna gefen shi. Kanta ta kwantar kan kafaɗarshi.

“Inaji a jikina ne kawai. Kinsan zuciyata bata min ƙarya.”

Ɗaga mishi gira ta yi tare da faɗin,

“Ko?”

Sarai ya san me hakan ke nufi. Kan Junior har kayan mata yai ta kwasowa shi a dole jikinshi ya ba shi mace za a haifo sai gashi ta haifo namiji.

“Wannan karon fa da gaske na ke.”

Dariya kawai ta yi. Tambayar da take son yi mishi na ci mata zuciya. Kafin ta san Fu’ad na da wani muhimmanci a rayuwarshi ta ɗauka haka kawai ya sama Junior sunan don yana burge shi.

Sai daga baya ta gane sunan Fu’ad ɗin ya mayarwa Junior. Kuma tun yana jariri ba ya kiranshi da Fu’ad ɗin.

Shi ya fara ce masa Junior kafin kowa ma ya ɗauka. In ba a makaranta ba babu mai kiranshi da Fu’ad. Ta na son jin labarin shi da Fu’ad ko yaya ne.

Don duk abinda ke da muhimmanci a rayuwarshi ta sani. Ya ɓoye mata Fu’ad ta rasa dalilinshi.

“Ina son tambayarka ne fa. Amman ina tsoron ɓata maka rai.”

Kallonta ya ɗan yi tare da faɗin,

“Ki yi tambayarki babu damuwa.”

Sai da ta nisa sannan ta ce,

“Na san ka roƙe ni kar na zurfafa tambaya. Kawai ina son sanin duk wani abu da ke da muhimmanci ne a rayuwarka.

Waye Fu’ad a wajenka?”

Wata ajiyar zuciya Lukman ya yi. Wayar da suka yi da Fu’ad ɗin ‘yan mintinan da suka wuce na ƙara yi mishi wani iri. Jin ya yi shiru ya sa zee cewa,

“Ka yi haƙuri. Ban san ranka zai ɓaci ba wallahi. In shaa Allah ba zan sake tambayar komai a kanshi ba.

Kanshi ya jingina da nata da ke kafaɗarshi cikin sanyin murya ya ce,

“Yau za ki san komai game da ni da Fu’ad Zee…

*****

Kai kawo ya ke ta yi a cikin ɗakin tunda ya dawo aiki. Kira uku ya yi wa Nuri wayarta a kashe. Ita da ta ce mishi ba daɗewa za ta yi ba. Duk da ya san inda ta je bai hana ranshi ɓaci ba.

Wani abu ya ke ji na mishi yawo cikin kai. Yakan tsinci kanshi cikin wannan halin in har Nuri ta yi mishi nisa.

Waje ya samu ya zauna yana running hannuwanshi cikin kai. Kallo ɗaya za ka yi wa yanayin Nawaf ka san yana da matsala ba ƙarama ba.

Jin ƙarar mota ya sa shi miƙewa ya ƙarasa jikin window ɗin. Nuri ce gaban mota da wani wanda yake tunanin ya taɓa ganinshi amma ya rasa ko a ina.

Murmushin da ya ga Nuri ta mai ya sa shi jin wani abu ya soki zuciyarshi. Yana kallo ta buɗe motar ta fito ta faɗa wa matashin wani abu da bai san ko meye ba.

Amman ya ji yana son cire mishi haƙoran can da ya ke ta buɗe wa Nuri. Kanshi zafi ya ke. Yana kallo ya ja motar ya yi baya da ita.

Nuri kuma ta yo hanyar shigowa gidan. Da sallama ta turo ƙofar. Ganin Nawaf tsaya ya sa ta sakin mishi wani murmushi.

Fuskarshi a haɗe ya ke kallonta.

“Waye wancan Nuri?”.

Ba tare da tunanin komai ba ta ce mishi.

“Mijin Amal ne. Da zan kira ka ka zo ka ɗaukeni ya ce bari ya saukeni ma. Sannu da gida ka ga na daɗe ko?”

A tsawace ya ce,

“Shi ne ki ke buɗe mishi hakora? Don yana mijin Amal sai aka ce ya kawoki gida?

Cike da mamaki Nuri ke kallonshi.

“Nawaf? Karka cemun kishinka har da mijin Amal.”

Bai san lokacin da ya ɗauke ta da mari ba. Wani ihu ta saka tana matsawa da baya riƙe da fuskarta.

“Babu namijin da ya ke da hurumin zama mota ɗaya da ke banda ni. I don’t care ko wanene shi.”

Wasu hawaye ta ji sun zubo mata. Wai me ke damun Nawaf ne? Ta ɗauka shaye-shaye ne kaɗai matsalarshi kuma ya daina.

Za ta iya rantsewa abinda ya ke yanzun marar hankali ne kawai zai yishi. Muryarta na rawa ta ce mishi.

“Ka yi haƙuri. Ba zan sake ba.”

Lumshe idanuwa ya yi. Da na sanin marin da ya yi mata na ziyartar shi. Ƙarasawa ya yi ya kamata ya rungume tsam a jikinshi.

“Ba na son ganinki da kowa. Ba ki da kowa sai ni Nuri. Ba ki da inda za ki je sai nan…”

Sake matse shi ta yi. Ta sani. Basaiya tuna mata ba. Ta san ba ta da kowa sai shi. Ba ta da inda za ta je sai gidanshi.

Ba ta da inda ya fi nan ɗin. Shi ne bargonta. Shine makangin da take da shi tsakaninta da zama da matar da ta fi tsana fiye da komai a duniya.

Matar da zata iya bada ranta in za a canza ƙaddarar da ta zo da ita a matsayin ‘yarta. Gara ko wacce wahala da koma ma rayuwa da ita.

Zata iya jure duk wani duka na Nawaf in dai hakan na nufin rashin komawa rayuwar da ta riga  ta yi wa bankwana..!

*****

“Dady…”

Khadee ta faɗi tana rugawa da gudu ta riƙe ƙafafuwan Haneef. Lumshe idanuwanshi ya yi yana jin wani sauƙi a zuciyarshi.

Tsugunnawa ya yi ya tallabi fuskar ‘yar tashi yana kallonta. Ji ya ke kamar ya buɗe ƙirjinshi ya sakata ciki ya ɓoye ta kar wani abu ya samar mishi ita.

Yau ganin Nana da jin matsalarta ba ƙaramin ɗaga mishi hankali ya yi ba. Tunanin wani abu ya raba shi da Khadee kawai ya sa yana jin numfashin shi na wani tsaitsayawa.

Riƙeta ya yi a jikinshi yana matseta gam. Fu’ad ya yi kuskure. Duk da haushin yadda ya bar su da ya ke ji bai hana shi hango mishi kuskuren da ya aikata ba.

Bai hana shi tausaya wa halin dazai shiga da wannan jarabtar da Allah ya ɗora masa ba.

A haka Ummi ta shigo ta same su tana riƙe da Alhaji da ya ke da sunan mahaifinsu Haneef ɗin wato Muhammad.

Ɗaukar Khadee ya yi ya ƙarasa inda ta ke tsaye ya haɗa su su duka ya rungume yana godewa Allah da ni’imar da ya yi masa ta kyautar iyali masu cikakkiyar lafiya.

Cikin kunnenshi Ummi ke cewa,

“Lafiya?”

Don ba ta taɓa ganinshi haka ba. Sumbatar goshinta ya yi. Sannan ya sumbaci Alhaji da ke ta ƙyaƙyata dariya abinshi. Ya sumbaci Khadee ma yana ƙara riƙe su a jikinshi sosai.

“Ina Kaunarku da yawa Ummi. Ina son ku. Allah ya ƙara muku lafiya.”

A hankali ta amsa da,

“Amin…”

Tana ƙara riƙe shi don ko bai faɗa mata ba ta san akwai abinda ke damunshi. Sai dai ya na da zurfin ciki.Ko ita ba ko yaushe ta ke jin damuwarshi ba. Sai dai yanayin ƙaunarshi dabanne a wajen su.

*****

Ko da dare fir Haneef ya ce da su Khadee za su kwana kar ta kai mishi yara ko’ina. Ba ta yi musu ba ta kwantar da su tsakiyarsu.

Hannu ya sa akansu Khadee kamar wani zai ƙwace su. Kallonshi ta ke da mamakin shi yau.

“Habibi ba za ka faɗa min damuwarka ba ko?”

Cikin sanyin murya ya ce,

“Kawai ina buƙatar yarana a kusa da ni ne ummi. Ko na yi laifi?”

Hannu ta kai ta shafi sumar kanshi da murmushi tare da faɗin,

“Ba ka yi komai ba. In ba za ka iya fada min damuwarka ba karka yi ƙoƙarin nunamun babu ita.

Saboda zan iya karantarka a duk yanayi Habibi.”

Murmushin ya mayar mata yana sauke numfashi.

“zan faɗa miki. Ki min haƙurin zuwa safiya. Yanzu ina buƙatar jinku ne a kusa da ni kawai.”

Kai ta jinjina mishi.

“Allah ya kaimu goben lafiya.”

Ya amsa da,

“Amin. I love you.”

Murmushi ta yi mishi, yadda ba ya gajiya da faɗa mata yana sonta na mata daɗi kafin ta yi musu addu’a gaba ɗaya.

Hannunta riƙe cikin nashi, yaransu a tsakiyarsu bacci ya ɗauke su cike da ƙaunar juna.

*****

Tunda ta dawo aiki gaba ɗaya ba ta jin dadi. Nana ita ce marar lafiya ta farko da ta bari ta shiga zuciyarta har haka.

Har ranta fata take a samu match Allah ya taimaka a ceci rayuwar yarinyar. Ba ta samu Jabir a gida ba sai yaran kawai sun dawo daga makaranta.

Yasir da Umar sunata assignment ɗinsu. Ikram na kwance cikin kujera tana danne-danne da tablet ɗinta. Umar kaɗai ya yi mata oyoyo.

Ta riƙe shi a jikinta. Ta yi kewar yaran nata sosai. Yasir ma sannu da zuwa ya yi mata ta amsa tana zama. Sai lokacin Ikram ta ɗago.

“Sannu da zuwa.”

Kallonta tai. Fuskar nan a murtuke. Miskilanci da rikici tsaf na Jabir babu wanda Ikram ta bari.

“Yawwa ya jikinki?”

“Am okay. “

Ta amsa a taƙaice ta na miƙewa. Falon ta bar musu. Jana ta girgiza kai kawai. Yau ko Jabir ɗin ma ya zo da rikicin shi ba ta da ƙarfin jurewa.

Nan ta bar su Yasir ɗin ta wuce ɗakinsu. Wanka ta dan yi, don gaba ɗaya a gajiye take, ta yo alwalar magriba.

Tana nan zaune inda ta yi Sallah Jabir ya shigo da sallama. Ta amsa tana mishi sannu da zuwa. Gefen gado ya zauna yana kallonta.

Baisan ta inda zai fara ba. Har zuciyarshi abinda ya ke ji akan Jana bai canza ba. In ma ba zai yi ƙarya ba sonta ƙaruwa ya ke a zuciyarshi.

Kama yadda son Aina ya ke daban. Kowanne wajen shi daban. Dafe kanshi ya yi cikin hannayenshi. Kallonshi Jana ta yi.

Miƙewa ta yi ta cire hijabinta ta ƙarasa gefenshi ta zauna. Kafaɗarshi ta dafa. Hakan ya sa shi ɗagowa ya sauke idanuwanshi kan fuskarta.

“Mene ne? Gajiya?”

Ta jero mishi tambayoyin lokaci daya. Kai ya girgiza mata.

Hannuwa ta sa ta tallabi fuskarshi ta yi kissing kumatunshi gefe da gefe.

“To mene ne? Ba na son ganinka cikin damuwa ka sani ko?”

Hannuwanta ya kama ya sauke daga fuskarshi. Ba shi ya ke buƙatar lallashi ba ita ce. Yadda ya ke kallonta ya sa ta sanin akwai matsala.

A sanyaye ta ce,

“Honey J ko dai kan aikina ne?”

Hannunta ya riƙo.

“Idan nace eh zai canza ra’ayinki?”

Ya tambaya. Kai ta girgiza mishi don ba za ta yi ƙarya ba. Babu abinda zai canza ra’ayinta kan aikinta. Ta na son mijinta sosai. Kamar yadda ya ke ɓangare na rayuwarta hakama aikinta.

A nutse ya ce,

“Good. Kamar yadda na daina ma kaina karyan cewar rashin samun kulawarki ne yasani jin abinda na ke ji…”

Zuciyarta ta ji tana bugawa a tsorace. Hannunta ya riƙo a hankali ya ɗora kan ƙirjinshi dai dai inda zuciyarshi ta ke sannan cikin idanuwa ya kalleta ya ce,

“Kar ki ɗauka abinda zan faɗa yanzun ya canza wajen zamanki anan. Kar ki ɗauka sonki zai taɓa girgiza a zuciyata. Kar abinda zan faɗa ya yi sanadin taɓa zaman lafiyar mu.”

A tsorace ta ce,

“Honey J…”

Da sauri ya katse ta da faɗin,

“Ki bar ni in ƙarasa please. Ina sonki. Ina sonki sosai babu abinda zai canza haka. Kin min halaccin da babu macen da za ta taɓa yi min shi Jana. Ba zan manta ba kuma. Banda iko da zuciyata da ban bari tai miki abinda ta yi miki ba. Ina son wata Jana…!”

Wani shiru ta ji cikin kanta kamar wani ya doka mata guduma a ciki. Lokaci ɗaya ta ji wani irin kishi da ba ta taɓa tunanin ta na dashi ba.

Da sauri ta soma jero duk wata addu’a da ta zo mata. Sama-sama ta ji Jabir ya sake riƙe hannunta gam cikin nashi ya ce,

“Ban faɗa mata ba. Na ce zan fara faɗa miki tukunna…”

Yadda ya yi maganar cikin rashin makama ya sa ta sake jin wani abu a zuciyarta. Sai ka ce fara faɗa mata yana son wata bayan ita zai rage mata kishin shi.

Hawayen da ke son zubo mata ta ke ƙoƙarin tarbewa. A hankali ta kalle shi. Sai da ta haɗiye miyau ya fi sau biyar kafin ta iya cewa,

“Wace ce? A ina take? Yaushe ka fara sonta?”

Kallon fuskarta ya ke. Ya kasa karantar komai akai. Ya kasa ganin ko ranta ya ɓaci ko bai ɓaci ba.

“Aina’u Mardiyya sunanta. Wajen aikin mu ɗaya. Bansan ko tun yaushe ba ne Jana. Farko na ɗauka ko don ba kya ba ni kulawa sosai ne ya sa ni son wata. Shi ya sa na so ki bar aiki ko zan daina ji ban…”

Riƙo hannunshi ta yi ta sumbata a hankali da ya sa shi yin shiru. Muryarta na rawa ta ce mishi,

“Ya isa Honey J. Zuciyarka ba don ni kaɗai aka yi ta ba. Ba ka da laifi a cikin son wata. Ka faɗa mata. Allah ya tabbatar mana da alkhairi. Zan roƙe ka yanzun ko da ba zan iya ba nan gaba.

Ba zan iya hanaka aure ba. Ba zan iya hanaka abinda Allah ya halatta ba. Ina roƙonka karka wulaƙanta ni don ka yi wata…”

Buɗe baki ya yi zai yi magana. Ta sa hannunta kan laɓɓanshi tana girgiza mishi kai kafin ta ci gaba da cewa,

“Karka mun alƙawari. Ba na son alƙawari ko ɗaya. Saboda ba na son ka ɗora zuciyata kan abinda za ka zo ka kasa in ji kamar ka ci amana ta. Allah ya ba ka ikon yin adalci. I need to be alone please…”

Hannuwanta ya riƙe ya matse gam yana jinjina ma ƙoƙarinta. Wata kima da girmanta na sake cika mishi zuciya.

Daga abokai ya sha jin labarin tashin hankali da hauka da matansu ke yi in suka zo da maganar kishiya. Yadda Jana ta yi mishi ba ƙaramin daraja ya ƙara mata ba.

Duk da barinta ita kaɗai a yanzun shi ne ƙarshen abinda ya ke son yi bai hana shi miƙewa ba. Wani light kiss ya manna mata a laɓɓanta da ta kasa mayar mishi da martani.

Fita ya yi daga ɗakin. Tana jin ya ja mata ƙofar ta ja jikinta kan gadon ta dunƙule ta saki wani irin kuka marar sauti.

Wani raɗaɗi ta ke ji cikin zuciyarta da wanda ya taɓa shiga cikin irin halin da ta shiga ne kawai zai fahimta.

Wanda ya san ya raba soyayyar miji ta ke. Ya tunanin zama da wata ya ke. Ya raba farin cikin Jabir ya ke. Kuka ta ke sosai.

Ji take kamar ta yi ta kurma ihu. A iya zamansu da Jabir ba ta taɓa hango raba soyayyarshi ba. Ko da wasa ba ta taɓa hango kalar wannan ranar ba.

Ta san shi na mace ne har huɗu. Sai dai hakan bai rage mata jin abinda ta ke ji ba. Don ɗazun ji ta ke kamar ta shae shi da ya ke gaya mata yana son wata.

Ganin da ta yi sheɗan na shirin saka mata hannu a zuciya ya sa ta miƙewa da ƙyar ta shiga banɗaki ta yo alwala. Sallar isha’i ta idar.

Wani sabon kukan ta tisa. A hankali ta kai hannu ta ɗauko Ƙur’ani ɗin da ke ajiye kan drawer ɗin gado ta buɗe.

Tana karantawa tana kuka har wata nutsuwa ta fara saukar mata. A hankali ta ke jin zafin da zuciyarta ke yi na hucewa. Sosai tai addu’o’i sannan ta ja jiki ta koma kan gadon ta kwanta.

Ko yaran kasa fita ta yi ta yi musu sai da safe kamar yadda ta saba in dai tana gida. Tana nan kwance sai juye-juye ta ke ta ji Jabir ya shigo.

Kwan ɗakin ya kashe. Ta na jinshi ya hawo kan gadon. Riƙota ya yi ta baya, cikin kunnenta ya shiga raɗa mata kalaman da sirrinsu ne.

A hankali ta ke jin wani sonshi na ƙara shigarta. Cikin sanyin murya ta ce,

“Ya kamata Ikram ta sani.”

Sai da ya sumbaci gefen fuskarta sannan ya ce,

“Zan faɗa mata da kaina. Ba yanzun ba. Sai Aina ta karɓe ni…”

Da sauri ta juyo ta cije mishi laɓɓa. Janye fuskarshi ya yi ya sa hannu yana shafa wajen. Muryarta a dakushe ta ce,

“Karka sake kiramin sunanta cikin ɗakin baccinmu. Balle kuma kan gadona alhali jikinka na haɗe da nawa Honey J. Sunana ne kawai ya kamaci laɓɓanka.”

Dariya ya yi sosai yana haɗe goshin shi da nata. Ta Yi ƙoƙarin tureshi ya riƙeta gam.

“Gabana har ya faɗi. Na ɗauka kin daina sona shi ya hana miki kishina.”

Mintsinar mishi hannu ta yi. Ya birkitata ya riƙeta sosai. A hankali ya shiga nuna mata yadda kowacece ta shigo rayuwarshi soyayyarta ba ta da fargaba. Da salonshi ya shiga tabbatar mata da har abada akwai inda ta kai a zuciyarshi da ya girmi hangen Aina…!

*****

Tun a cikin taxi abinda ke manne a ƙirjinshi madadin zuciya ya ke wani numfasawa har suka ƙarasa.

Bakin gidan mai taxi ɗin ya sauke shi. Ya ɗauko kuɗin shi ya ba shi don sai da ya biya wafa da shi ya yi canjin kuɗin da ke jikinshi.

Hotel ma credit card ya biyasu da shi. Lumshe idanuwanshi ya yi ya na jan wata iska da ta shiga har cikin ƙirjinshi.

“Sofi…”

Ya furta a hankali. Karo na farko a shekaru sha ɗaya da bakinshi ya buɗe da sunanta. Sai dai in ya gifta mishi a tunanin shi. Wani irin zafi ya ji a ƙirjinshi. Ya kai hannu wajen ya buɗe idanuwanshi yana wani yamutsa fuska. Da wani irin nauyin ƙafa ya taka ya ƙarasa ƙofar gidan.

Kallon gidan ya ke. Yana tuna ranar farko da ya fara zuwa gidan shi da Haneef. Sake yamutsa fuska ya yi.

Haneef ɗin da ya watsar da shi. Haneef da ya yanke alaƙa da shi kamar yadda Abba ya yi kawai saboda ya nemi tsara rayuwarshi babu shawararsu.

Ji ya yi ranshi ya wani ɓaci. Bai san wane hauka ya sa ya biyewa Lukman ba ya zo Nigeria. Yanzu kuma ya taho nan.

Hannu ya ɗaga zai kwankwasa ƙofar gate ɗin.

“Na tsane ka..!”

Ya ji muryar Sofi cikin kanshi. Ƙwanƙwasa ƙofar ya yi yana sake jin maganarta raɗam cikin kanshi kamar ta na gabanshi.

“Ba na son ganinka wallahi. Ba na son sake ganinka.”

Lumshe idanuwanshi ya yi. Ƙirjinshi zafi ya ke masa sosai sosai. Wani numfashi ya ke fitarwa da sauri da sauri ko zai ji sauƙin abinda ya ke ji.

Buɗe ƙofar da maigadin ya yi ne ya ɗan taimaka mishi. Ware idanuwanshi ya yi kan fuskar maigadin. Kallon Fu’ad ya ke. Ganin kamannin da suka yi sosai da Nana ya sa shi buɗe mishi ƙofar tare da faɗin,

“Alhaji sannu da zuwa.”

Ko kallonshi Fu’ad bai yi ba ya shiga cikin gida. Wani abu ya ji ya ƙulle a ƙasan cikin shi. Ya yi kuskure babba. Son famo ciwukanshi ne su dawo ɗanyu suna zubda jini ya sa shi biyewa Lukman. Sai dai ya riga ya zo. Babu komawa baya kuma.

Da ƙyar ƙafafuwanshi suke motsi suna taka mishi. Komai na rayuwarshi a gidan ke ta masa yawo cikin kai.

Da ƙyar ya ƙarasa ƙofar gidan. Tsayawa ya yi ya rufe idanuwanshi yana kokawa da abinda ya yi saura a zuciyarshi.

Ƙwanƙwasawa ya yi. Yana jin koma meye a ƙirjinshi na dokawa da ƙarfin gaske.

*****

Da ƙyar ta iya miƙewa daga kan kujerar ta nufi ƙofa. Tun tafiyar Haneef ta sha kukanta ta more. Sai ta ke jin jikinta duk babu ƙarfi.

Ba ta tambayi ko waye ba. Kawai buɗe ƙofar ta yi. Cik zuciyarta ta tsaya. Idanuwanta suka kafe a kanshi. Ya ƙara girma. Jikinshi sanye da normal jeans blue. Sai tshirt ja da ta kama shi. Banda girma sosai da ya ƙara.

Sai sajen da ke kwance a fuskarshi da gashinshi da ya rage wa yawa. Tsaye zuciyarta ta yi. Tana shirin manta yadda ake shaƙar numfashi.

Idanuwanshi yawo suke a fuskarta. Bai ga ta canza da komai ba. A hankali ya ke jin abinda ke ƙirjinshi na buɗewa.

Ya yi tunanin ba shi da sauran zuciya ashe a ɓoye ta ke cikin abinda ya ke tunanin ya maye gurbinta a ƙirjinshi.

A hankali ta ke buɗewa. Sofinshi ce. Ta ƙara kyau fiye da yadda ya bar ta. Muryarshi ɗauke da wani irin yanayi ya ce,

“Sofi…”

Sai lokacin ta ji zuciyarta ta numfasa cike da wani abu da ya girmi tsanarshi. Kallonshi ta ke tana kokawa da iskar da ta ke son shaƙa saboda yadda ta ɗauki mintina wajen biyu ba ta shaƙeta ba.

Ƙofar da ta ke riƙe da ita ta ja ta na son kulleta ya sa hannu ya riƙe ƙofar yana kallonta.

“Ƙofar gidan nawa za ki kulle a fuskata, Sofi?”

Wani abu ta ji ya tokare mata wuya. Ji ta yi kamar ta kwaɗa mishi mari. Nana ce kawai dalilin da ya sa ba za ta kira maigadi ya ɗauke shi ya fitar mata da shi ba.

“Daga ranar da ka sa ƙafarka ka bar gidan nan ka yi losing right ɗinka na kiranshi naka.”

Wani murmushin takaici Fu’ad ya yi. Ashe shi ya yi shekara goma sha ɗaya yana kokawa da murmushi duk sanda tunaninta ya faɗo mishi.

Tana nan ta ƙara kyau abinta. Ba ya ranta. Tsanarshin da ta faɗi da gaske ne ta na jinta. Cike da takaici ya ce,

“Ko sofi?”

Ba ta son sunan nan yanzun. Ba ta son yadda sunan ya ke kaiwa zuciyarta yana wani matse mata ita.

“Karka sake kirana da wannan sunan. Sunana Safiyya.”

Kallonta ya ke da mamaki. Sofi ta koyi rashin kunya. Sosai shi ta ke kallo cikin ido tana faɗa wa magana babu tausasawa.

Ware idanuwanshi ya yi a kan fuskarta.

“Kin canza sosai.”

Kallonshi kawai ta yi. Tana ganin yadda ya ke ɗin nan da halinshi da ta kasa kallo acan baya.

Ji ta ke dama bai zo ba. Saboda ba ta son yadda Nana ta saka shi a ranta. Ta san kuma ba sonta zai yi ba. Babu son kowa a zuciyarshi sai na kan shi. Ba su da waje a zuciyarshi. Daga ita har ‘yarta.

Buɗe baki ta yi za ta yi mishi magana ta hango Ansar ya taho. Ba ta san lokacin da murmushi ya ƙwace mata ba.

Wani ɗan guntun murmushi Fu’ad ya ji ya bayyana a fuskarshi. Yaushe rabon da ya ji shi haka har ranshi.

Ta wani ƙara kyau. Yana son murmushin nan a fuskarta. Ganin hankalinta na wani waje ya sa Fu’ad juyawa.

Wani abu ya ji ya tokare mishi wuya. Waye wannan da ta ke ma murmushi haka. Kallon-kallo suke yi da Ansar ɗin.

Hannu Ansar ya miƙa wa Fu’ad, da ƙyar ya karɓa suka yi musabaha. Kanshi tsaye Ansar ya wuce zuwa cikin falon.

Safiyya tace mishi,

“Yanzu na ke shirin kiranka. Na ji ka shiru.”

Da biyu ta ke maganar. So ta ke Fu’ad ya gane ba shi da wani muhimmanci a rayuwarta yanzun. Kuma ya ji hakan.

In a shekarun nan yana tunanin ya yi da na sanin tafiya. Abinda ya ke ji yanzun ya ninka na da. Wani ne zaune a falonsu shi da Sofi.

Da ido Ansar ke kallon safiyya yana tambayarta. Duk da kamannin da ya gani kawai ya tabbatar masa da wannan ne Fu’ad ɗin.

Yanayin shi kawai ya san zai aikata abinda Safiyya ta ba shi labari. Saboda akwai wani attitude tattare da Fu’ad da ko wanda bai sanshi ba zai karanta a kallo ɗaya.

Sake kallon safiyya ya yi. Duk yana jin wani irin awkwardness ya baibaye ɗakin. Ita tana tsaye. Shi a zaune a falo, Fu’ad ɗin kuma yana bakin ƙofar a tsaye ya kafe su da idanuwa.

Kai ta ɗan girgiza mishi alamar yanzu Fu’ad ɗin ya zo. Ansar ya buɗe baki zai yi magana maigadi ya rugo da gudu.

“Hajiya ga wasu mutane nan su da yawa bakin ƙofa. Wai sai sun shigo suna son ganin Nana.”

Haɗa ido Safiyya da Ansar suka yi. Kafin Ansar ya miƙe ya bi maigadin zuwa ƙofa. Ƙarasawa ta yi ta ɗauki mayafinta da ke kan kujera. Ta zo ta raɓa Fu’ad da ke tsaye tsaye kaman an dasa shi ta wuce ta bi su Ansar.

‘Yan Jarida ne cike da ƙofar gidansu. Ta lumshe idanuwanta tana tunanin yadda akai suka gano gidansu.

Ansar ta kalla da idanuwanta da suke roƙon shi da ya san yadda zai yi da ‘yan jaridar nan. Ba ta son su ganta a yanzu.

Duk da ta ma Nana alƙawari. Ba haka ta shirya Fu’ad ya ji labarin Nana ba. Ta zo ma babu matsala ba ta tunanin zai karɓe ta ba.

Ballantana yanzu kuma. Kamar ya ji zancen shi ta ke a zuciyarta ya ƙaraso inda ta ke. Sai jin muryarshi ta yi yace mata,

“Me yake faruwa? Me waɗnnan suke yi anan?”

Lumshe idanuwanta ta yi ta buɗe su tare da faɗin,

“Ba matsalarka ba ce. “

Kafin ya gama mamaki ta juya ta yi cikin gida. Binta ya yi da sauri yana faɗin,

“Sofi…”

Ko tsayawa ba ta yi ba balle ya yi tunanin za ta juyo. Yana ina shekaru sha ɗaya da suka wuce. Sai yanzu zai tambayeta me ke faruwa. Bai tsaya ya tambayi me zai faru da ita ba kafin ya tafi. Ya manta ta bar komai Akan so, ba na kowa ba nashi.

Badon Nana da za ta iya komai Akan sonta ba bai ishe ta ko kallo ba ballanta har musayar magana. Bai da wannan darajar a idanuwanta ko kaɗan. Ƙofa ta tura ta shiga. Tana ƙoƙarin tarbe hawayen da ke son zubo mata. Ta riga ta ma kanta alƙawari ta gama kuka akan Fu’ad ba tun yanzu ba.

Ta na shiga cikin gidan Nana na fitowa daga ɗakinta. Da alamun bacci a fuskarta ta na murza ido.

Ganinta kawai ya sa zuciyar Sofi wani yawatawa da ƙaunar ‘yar tata. Za ta iya komai saboda ita. Koda kuwa daina numfashi ne in dai za ta yi hakan da sanin cewar rayuwar Nana za ta ci gaba da wanzuwa.

A shirye ta ke, cikin abubuwan da za ta iya yi har da jure ganin Fu’ad da jin muryarshi duk da yadda suke yi mata kamar zuciyarta za ta tarwatse saboda ciwo.

Kama Nana ta yi tana ƙoƙarin janyeta ta mayar da ita ɗaki. Ba ta son ta ga Fu’ad sai ya fara sanin da zamanta tukunna.

“Sofi…”

Ta ji ya kira. Wani yar ta ji duk jikinta. Tsaye ta yi cak. Sannnan a hankali kamar mai ciwon wuya ta juya. Nana da ke jikinta ta fito ta tsaya ta na kallon Fu’ad. shi da ya ke tsaye idanuwanshi kafe kan Safiyya sam bai kula da Nana ba.

Safiyya ta mayar da dubanta kan Nana tana ganin yadda ta ware idanuwanta tana kallon Fu’ad. In da ya ga fuskarta ta bi da kallo ya sauke kanshi.

Ya ko yi nasarar sauke idanuwanshi cikin na Nana. Lokaci ɗaya ya ji komai ya tsaya mishi. Kallonta ya ke da wani irin yanayi.

Kallonta ya ke saboda yana tunanin bai taɓa ganin halittar da ta yi mishi kyau ba kamarta. Kallonta ya ke yana jin yadda komai na jikinshi ke narkewa da ƙaunarta.

Kallonta ya ke yana jinta kamar wani ɓangare na rayuwarshi. Kafin ya ji zuciyarshi ta yamutse. Idanuwanta.

Akwai wani abu tattare da idanuwanta da yake son gane ko meye. Kamar wanda aka daka da ƙarfe akai abin ya zo mishi. Irin idanuwansu ɗaya sak. Hancinsu da bakinsu iri ɗaya ne.

Ba sai ya tsaya wahala ba. Wannan yarinyar tamkar an ciro shi ne an ajiye a jikinta. Ji ya yi ko ina na jikinshi na kyarma.

Wani murmushin takaici Sofi ta yi tare da faɗin,

“Fu’ad ga Nana fa…”

Ya kasa janye idanuwanshi daga kan Nana duk da ya ji abinda Safiyya ta ce. Baya son ko na daƙiƙa ɗaya ya daina kallon fuskar yarinyar.

Nana Safiyya ta kalla ta ce,

“Ga M.”

A tsorace Nana ke kallonshi. Ta na ganin kamar da ta yi wani abu ba dai dai ba ɓacewa zai yi. Tunda ta yi wayau ta ke jin ƙaunarshi cike da zuciyarta. Tunda ta yi wayon sanin mene ne mahaifi ta ke jin son ganin shi ko da sau ɗaya ne a rayuwarta. Wani murmushi ya ƙwace mata duk da hawayen da suka zubo mata.

“Kai ne babana…”

Bangon da ke wajen Fu’ad ya dafa saboda yadda ya ji ƙafafunshi na rawa da maganar da ta fito daga bakin Nana.

“No way…!”

Ya furta yana girgiza kai.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×