Skip to content
Part 17 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Tun daga soron gidansu take jin hayaniyar mutane. Da mamaki ta yi sallama. Har ƙasa ta tsugunna ta gaishe da su, suka amsa.

Miƙewa ta yi ta ƙasan ido take kallon akwatinan da ta san na lefenta ne. Wani abu ne tsaye a wuyanta da ta kasa haɗiyewa.

Ɗaki ta wuce. Ko hijab ba ta cire ba. Ba ta taɓa sanin rashin son da take wa Ado ya kai haka a zuciyarta ba.

Ta ɗauka za ta iya haƙura ta yi biyayya wa iyayenta ta zauna da ado. Amma yau tunanin hakan kawai ya sa numfashinta na wani ɗaukewa.

Wayar da ke maƙale a ƙugunta ta ciro. Ta sa hannu ta shafi screen ɗin wayar. Wasu daga cikin maganganun Fu’ad na dawo mata.

Yakan kirata sau biyu ne kawai a rana. Da dare sai kuma da sassafe. Daga sun gaisa ba ta iya cewa komai, saidai ta yi shiru tana jin yadda yake gaya mata zai dawo. Kuma zai samar musu hanyar yin rayuwa waje ɗaya.

Saƙonni kam sai ya turo sunfi goma sha a rana. Haka za ta buɗe ta yi ta kallonsu. Fin rabinsu ba ganewa take ba saboda da Turanci yake turowa.

Kalmomin da take tsinta na turanci ba za su shige goma ba. Inya haɗa da hausane kawai za ta karanta.

Ba dai ta reply saboda ba ta iya ba. Inhar ta ce ga dalilin da ya sa take ɗaga wayar Fu’ad to ta yi ƙarya.

Abu ɗaya ne take da tabbaci akai. In har ya kira sai ta ɗaga. Ko tana cikin su Inna ne za ta shiga banɗaki ta amsa wayar.

Wasu hawaye ne ke bin fuskarta tana goge su. Ita kam ba ta son Ado ko kaɗan.

*****

Tana nan zaune shiru ta ji alamun mutane na tafiya. Kafin wani lokaci gidan yayi shiru. Tana jiyo muryar Usman da Inna suna magana kan lefen cewar ba ƙaramin ƙoƙari ado ya yi ba.

Akwatina ne huɗu. Duk da atamfofin ƙanana ne sosai. Bakowa ke wannan sa’ar ba a ƙauyen.

Ita kam ba ta wani damu da kaya ba. Addu’a take Allah ya bata ƙarfin zuciyar daurewa a yi auren nan ko don iyayenta.

*****

Kamar kullum a kwanakin nan bakwai Sallama ta yi ma su Inna ta shige ɗakinta ta kwanta.

Kiran Fu’ad take jira. Yau shiru bai kirata ba. Ba za ta ce ga adadin lokacin da ta ɗauka tana jira ba. 

Sai ta ji wani irin yanayi mai wahalar fassarawa. Wani ɗaci mai bambanci dana ɗazun.

Juye-juye kawai take baccin ya ƙi ba ta haɗin kai. Ta jima sosai a haka kafin wani wahalallen bacci ya ɗauketa mai cike da mafarkai.

*****

Tun kafin Asuba ta yi wata irin farkawa da ba ta san ta mecece ba. Wayar ta zaro ta duba.

Ta zuba mata idanuwa kamar Fu’ad zai fito ta ciki. Kwanciya ta yi tare dayin shiru. Kan kunnenta akai kiran sallar Asuba.

Alwala ta yo ta yi sallah. Tana idarwa ta kwashe shimfiɗarta ta gyara ɗakin.

Aikace-aikacen da ya kamata ta yi na safe ta gama tsaf. Sannan ta koma ɗaki ta zauna tana jiran kiran Fu’ad dabai shigo ba.

Yinin ranar ji take kamar ba ta da lafiya. Kamar akwai wani ɓangare nata da bai cika ba. Sai ta samu kanta da yi wa Fu’ad addua a duk inda yake ya kasance cikin lafiya.

Ga kwanakin bikinta sun mata tsaye cikin kanta. Duka duka yau saura sati biyu cif.

Don tun jiya da dare take jin Baba na cewa ba zata sake fita ko’ina ba. Ko da Islamiyya ce ma.

*****

Matakin rashin kwanciyar hankalinshi ya ƙara hawa tsakanin jiya zuwa yau da safe.

Ya rasa inda ya yadda wayarshi. Tsakanin wajen training da restaurant ɗin da ya tsaya ya ci abinci zuwa gida.

Wata wayar ya fita ya siya. Ya bada tsohuwar lambar shi aka rufe akai masa wata.

Ko gida bai bari ya ƙarasa ba ya saka lambar Safiyya ya yi dialing. A kashe wayar take.

Yasan ko ƙarfe nawa ne lokacin a Nigeria. Sai dai bai san dalilin da ya sa wayarta take a kashe ba.

Kanshi ya ji ya soma ciwo na babu dalili. Babban takaicin shi ɗaya ne. Hotunan safiyya da yake da su suna cikin waccan wayar da ya yarda.

Gashi ya yi rashin dubarar saka su a system. Gida ya koma ya rage kayan jikinshi ya kwanta muryarta na masa yawo cikin kai tana rage mishi damuwar da yake ciki.

*****

Usman take jira yazo ya karɓo mata batirinta da ta aika shi ya kai caji.

Ɗaya daga cikin dalilan da yasa take ƙaunar yaron. Gashi da ƙarancin shekaru amma yana da sirri sosai.

Farkon da ta bashi yakai mata batir ɗin ya tambayeta na wanene. Ta ce masa nata ne.

Abu ɗaya da ya buƙata shi ne Inna ta san tana da waya. Ta girgiza masa kai. Bai sake cewa komai ba ya karɓa ya kai mata.

Daga lokacin zai kaimata ya amso mata. Inhar ya sameta da Inna baya ba ta sai su kaɗai.

Haka yauma yana shigowa ta ba shi ashirin yaje ya karɓo mata. Don kuɗaɗen makarantarta tara su take yi. Ita ba mai yawan ciye ciye bace ba.

Batir ɗin ta saka a wayar. Wani sanyi ta ji da ta ga saƙonnin shi sunata shigowa.  Ta san yana lafiya.

Lokacin da ya saba kiranta ya kirata yauma. Gaisawa suka yi ta yi shiru. Tanajin yace,

“Sofi kin ga ban kira ba ko?  Na yarda wayata ne shi yasa.”

A sanyaye ta amsa da,

“Allah ya mayar da alkhairi.”

“Amin. Bari barki ki yi bacci ko?  Bana so kiyi ciwon kai.”

Wani murmushi ya ƙwace mata. Lokaci ɗaya ya dauke da ta tuna wannan wayar da suke ba ta da wani amfani.

Asalima ƙarin matsaloli ne a wajenta. Ya kamata ace tayi duk wani abu da zai nisantata da Fu’ad don yana da alaƙa da yawan tsanar Ado da ta yi a zuciyarta.

“Don Allah karka sake kirana. Ina maka fatan alkhairi a rayuwarka.”

Da alamun tashin hankali taji yace,

“Sofi tsaya…me kike nufi?  Saboda me ba zan kiraki ba?  Baki san muryarki kaɗai ce abinda ke riƙe min sauran hankalina ba.

Please karki mun haka…”

Katse shi tai da faɗin,

“An kawo lefe na yau. Sauran sati biyu ɗaurin aurena. Meye amfanin kiran nan da kake min?

Ka daina don Allah. Wallahi kana sake rikita min tunani ne.”

Shiru ya ɗan yi kafin yace,

“Ba zaki auri kowa ba sofi. Zan dawo kafin lokacin. Ni da ke are meant to be. Babu abinda zai shiga tsakani kina jina ko?

Kar bakinki ya sake furta min cewar na daina kiranki. Sai da safe.”

Kafin ta ce wani abu ya kashe wayar. Ba ta yi ƙoƙarin goge hawayen da suke zubo mata ba.

Don sun daɗe da ƙwacewa daga idonta. Zuba suke duk sanda suka so fitowa.

Duk idan yace ita da shi ɗin nan sai ta ji wani abu ya yawata mata a zuciya. Ta san babu wani abu wai shi ita da shi.

*****

Yau sauran kwana uku kacal a ɗaura mata aure da Ado. Sai dai babu komai a zuciyarta da ya wuce ƙin auren da kuma Fu’ad.

Tun jiya yake kiranta ba ta ɗagawa. Saboda ba ta son yadda kalamanshi suke mata tasiri. Ya turo saƙonni sun fi talatin tsakanin jiya da yau. Duk da in ya kira sai ta yi da gaske take ƙin ɗagawa. Gaba ɗaya ta wani yi zuru-zuru. Tun Inna na tambaya har ta gaji ta ƙyale ta.

Hidima kawai suke abinsu. Don ranar ma mutanene cike da gidansu ana ta hidima za a je a yi jere.

Su Lami da Jummai suka kwance mata kai. Ta wanke tas. Jummai ta yi mata kitso.

Kawai binsu take. Duk yadda suka ce mata. Saboda ba ta da ƙarfin ko yawan magana ma. Su kansu basu dame ta da yawan tambaya ba.

Tana jin wayarta na zuu ta sake gyara kwanciya tana wani haɗe jikinta. Zuciyarta na bugawa da ƙarfin gaske.

Yadda jikinta ke mata har tsoro abin yake ba ta. Nan da kwana uku ko ba ta so dole ta cillar da wayar nan.

Ta saba da rashin shi tun yanzun. Tana ta ƙoƙarin ƙaryata cewar ta ƙwallafa ranta akan shi.

JI ta wayar ta yi shiru na ɗan wani lokaci kafin ta ji ta sake ɗaukar vibrating. Sai dai wannan karon na alamar text ya shigo ne.

Wayar ta ciro ta buɗe. Gajeren saƙo ne kamar haka,

‘Ki na so inyi menene? Na miki wani abu ne?’

Lumshe idanuwanta ta yi. Hawayen da ke son zubowa take ƙoƙarin umarta da su koma. Wani saƙon ya sake shigowa.

‘Yanzun zan taho gida. Ki yi bacci mai daɗi.’

Wayar ta mayar tana sauke wani numfashi. Bacci ne ya ɗauke ta cike da mafarkai masu hargitsi. *

Rashin nasarar wasansu ba shi bai dame shi kamar ƙin ɗaga wayarshi da Sofi ta yi ba.

Har wani ɗaci-ɗaci yake ji. Babu abinda ya tsaya siya. Haka ya ɗauki jakar system ɗin shi sai waya da abinda yake buƙata ya yi Airport.

Nigeria

Ba su ji wani mamakin ganin Fu’ad ba don suna saka ranshi cikin satin dama.

Daga Fa’iza sai Momma a gidan. Don haka suna gama gaisawa ya hau sama. Ɗakin shi a gyare tsaf. Wanka ya yi ya shirya kanshi cikin jeans baƙi da riga simple ja. Gashi ya taje ya fesa turaruka ya sa takalma suma jajaye ya fito.

Lukman ya kira a waya ba ta shiga ba. Gidansu ya wuce kanshi tsaye. Hajiyar su Lukman take faɗa mishi yana makaranta.

Ba ya jin zai iya jiran Lukman ɗin don har wani ihu-ihu zuciyarshi take masa.

Daga shi har ita haƙurinsu bashi da yawa akan Safiyya. Balle bai ji muryarta ba. Don haka gida ya koma. Mukullin mota ya karɓa wajen Momma ya ce mata zai fita amma ba wai jimawa zai yi ba don yamma ta fara yi.

Addu’a kawai ta yi masa ya fice. *

Tuƙi yake yi. Yana jin zuciyarshi na bugawa har cikin tafin hannunshi saboda wani maiko da suke yi da zufa.

AC ɗin motar ya duba ya ga ko bai kunna ba. A kunne take, zufar da yake yi ta daban ce.

Komai da yake ji ƙaruwa ya yi da ya ganshi zai sha kwanar da za ta kaishi gidansu Safiyya.

Inda ya saba tsayawa ya tsaya. Ba don komai ba sai don baya son ja wa Safiyya matsala. Ba ya son ganinta cikin damuwa da babu mai hanashi parking a ƙofar gidansu.

Wayarshi ya ɗauko ya yi dialing lambarta.

Zaune suke a ɗaki. Su Jummai na ta faman hira. Wayarta ta ji tana vibrating.

Ta lumshe idanuwanta kawai. Tana jin yadda wayar ke wani zuu. Addu’ar duk da ta zo bakinta take yi. Can wayar ta yi shiru kafin ta ƙara ɗaukar vibrating. Danne zuciyarta dake mata ihun ta ɗauki wayar take ta yi.

Sake ɗaukar vibrating ta yi a karo na babu adadi. Can ta yi shiru sai ta ji alamar saƙo ya shiga.

Hannu ta sa ta lalubo wayar ta gyara zama yadda ita kaɗai za ta iya ganin wayar.

Saƙon da ya turo ta buɗe.

‘Ina wajen gidanku. Ki zo.’

Kafin saƙonshi ya ƙarasa isa inda ya kamata a cikin kanta wani ya sake shigowa.

‘Wallahi zan ƙaraso idan ba ki fito ba. Believe me ba za ki so hakan ba.’

Wani zufa ta ji ya lulluɓeta. Jikinta ya ɗauki ɓari. Ta san ba ƙarya yake ba. Ƙarasowa zai yi gidansu.

Ita yanzun ba ta san yadda za ta yi ba. Wayar ta ci gaba da zuu alamar kiranshi ya shigo. Tasan wannan karon ba ta da zaɓi.

Ɗaga wayar ta yi ta kara a kunne tare da mishi sallama da ya dawo da hankalin su Jummai kanta suna mata kallon mamaki.

“Me na yi miki?”

Lumshe idanuwanta ta yi tana jin yadda zuciyarta ke wani numfashi da ta kwana biyu ba ta yi ba.

Har wata iska ta daban ta ji tana shaka.

“Sofi….ina tsaye tun ɗazun.”

Maganarshi ta dawo da ita hankalinta. Cikin sanyin murya tace,

“Ka yi haƙuri. Ba zan iya fitowa ba akwai mutane sosai. Karka sake dawowa. Na faɗa maka nan da kwana uku aurena kuma…”

Katse ta ya yi, ya yi muryarshi can ƙasa ɗauke da wani irin yanayi da ta ji ko’ina na jikinta yace,

“Ion’ give a damn da mutanen dake nan Sofi. Abu biyu na sani.

Ba a ɗaura miki aure ba. Sannan ina son ganinki.

Idan ba ki fito ba ni zanzo ƙofar gidanku ko na shigo har ciki… “

A tsorace Safiyya tace,

“Fu’ad…”

Karo na farko da ta ɗora sunanshi akan harshenta. A zuciyarta take faɗarshi ko da yaushe.

Wani abu ta ji na daban. Tana jin sauke numfashin da ya yi tare da faɗin,

“Sofi….. Ki fito please. Idan na ƙara mintina biyar banganki ba zan ƙaraso.”

Kashe wayar ta yi kafin ta amsa. Idanuwanta ta sauke kan su Jummai da fuskokinsu ke ɗauke da tambayoyi kala-kala.

“Don Allah ku taimaka min in fita daga gidan nan na ‘yan mintuna, ba na so kowa ya kula da na fita.”

Safiyya tace musu murya na rawa. Jummai ta kalleta sosai.

“Saboda me? Me za ki yi a waje? Dawa ki ke waya kuma?”

Miƙewa Safiyya ta yi tace,

“Don Alla ku taimaka min. Wallahi zan muku bayanin duk abinda yake faruwa.”

Sai lokacin lami tace.

“Ni na san da akwai wata a ƙasa. Me zai hana ki faɗa mana yanzun?”

Jummai ta gyada kai alamar yarda da abinda Lami tace. Kallonsu ta yi idanuwanta cike da hawaye.

“Banda lokaci sosai. Ku taimaka min don Allah Wallahi zan faɗa muku…”

Yadda ta ƙarasa maganar da wasu hawaye da suka zubo mata ya karya musu zuciya.

Miƙewa suka yi su duka suna tunani. Kafin Lami ta basu dabara.

Ya kasa tsayawa waje ɗaya. Sai kai kawo yake yi. Har zuciyarshi yake nufin maganganun da ya gaya wa Safiyya.

In har ba ta fito ba zuwa zai yi. Ko me zai faru ya faru bai dame shi ba. In har zai ga fuskarta it will be worth ko me zai fuskanta.

Hanya yake kallo. Su uku ya hango. Tafiyarta kawai ya gane. Wani lallausan murmushi ya kuɓce masa.

Ajiyar zuciya ya sauke yana takawa ya suka haɗe akan hanya. Idanuwanshi kafe suke kan Safiyya. Sam ba ya ganin su Jummai da suka zuba masa idanuwa.

Kallonta yake yana cike guraben da suka yi kewarta a kwanakin nan. Kanta a ƙasa tace,

“Tunda ka gan ni ka tafi don Allah. Wannan ya zama karo na ƙarshe da za ka dawo.

Wallahi za ka iya sakani cikin matsala. Bana son fushin iyayena akanka.”

Kallonta yake yi sosai. Muryarshi da alamar lallashi yace,

“Hey…. Bana nufin na ja miki matsala Sofi. Ki fahimceni. Kawai dai ba zaki auri wani bane ba.

Nikuma inyi yaya kenan? In sa kaina ina? Kin san me nake ji kuwa?”

Jajayen idanuwanta ta ɗago ta sauke su cikin nashi. Ba ta da kalaman da za ta yi amfani da su.

Ƙila zai iya karantar halin da take ciki ta idanuwanta. Zai iya ganin yaƙin da take gabzawa da zuciyarta akanshi.

*****

Shi da abokinshi Hashimu ne suke tafiya cike da nishaɗi suke hirarsu, sai Hashimu yace,

“Ado wata nake hangowa kamar Safiyyarka tsaye da wani ko?”

Girgiza kai Ado yake da alamun rashin yarda yace,

“Haba dai. Safiyya fa kace.”

Da hannu Hashimu ya nuna masa su. Wani abu ya ji ya tsaya masa a wuya. Safiyya ce kuwa tsaye da wani saurayi.

Da sauri yake takawa ya ƙarasa wajensu Hashimu na bin bayanshi.

Tsaye suke suna kallon-kallo. Kamar daga sama su Jummai sukaga Ado da har wani huci yake yi.

“Safiyya me kike yi a waje? Waye wannan kuma?”

Wani abu ta ji ya ƙulle a cikinta. Shikenan, abinda take gudu ne ya faru. Dole su Inna su sani. Asirinta ya tonu.

Cike da matsanancin tsoro ta kalli Ado. A daburce ta soma cewa.

“Umm…Wallahi…Ado…”

Fu’ad da ke tsaye kallon Safiyya yake yadda ta rikice gaba ɗaya kafin ya maida kallonshi kan Ado.

“Waye kai kuma ɗin?”

Ya tambaya yana masa wani kallon wulaƙanci. Shi ma Adon kallon da yake mayar masa kenan.

 “Me ya sa kake tsaye da matata?”

Ya tambaya. Wata dariyar takaici Fu’ad ya yi. Me ma sofi za ta yi da wannan ɗan ƙauyen, ƙazami. Yake tambayar kanshi. A fili kuma yace.

“Ka kama hanya kawai. And kar bakinka ya sake kiranta da matarka.”

Ya ƙarasa yana nuna Safiyya da ke tsaye kamar an dasa ta. Su Jummai kansu baki buɗe suke kallon ikon Allah.

Cikin ɓacin rai Ado yace,

“Lallai ma. Ka ji mun wani ƙarfin hali. Kai a su wa to?  Malam tunda mutuncinka ka bar wajen nan wallahi. Bansan ya akai take tsaye da kai ba. Ba kuma zai sake faruwa ba don matata……. “

Bai ƙarasa ba ji kake wani tas!

Fu’ad ya kwaɗa masa mari. Ai kam Ado bai tsaya jira ba ya kaima Fu’ad ɗin naushi a fuska.

Ramawa ya yi. Hashimu ya yi ƙoƙarin shiga tsakaninsu amma sai Fu’ad ma ya sauke masa naushin da yake ƙoƙarin kai ma Ado. Ko da wasa ba za ka haɗa girman jiki da ƙarfin Fu’ad da na Ado shi kaɗai ba ma ballantana da Hashimu.

Kafin ka ce wani abu Hashimu ya yi sama da Fu’ad ya tiƙa da ƙasa.

Wata ƙara Safiyya ta saki. Shi aka doka da ƙasa amman ciwon har cikin zuciyarta ta ji shi.

Dafe fuska ta yi da hannuwa biyu. Ko ta ko ina Ado da hashimu suke turmusa Fu’ad kamar wanda akaima wahayi.

Ganin mutane sun fara taruwa ya sa Jummai da Lami jan Safiyya tana turjewa tana wani irin kuka.

Janta suke tana ƙoƙarin komawa kamar za ta shigar wa Fu’ad da yanzun ya daina ma rama dukan da suke masa.

Duk sun fasa masa baki da gefen fuska. Ga shi sun turbuɗa shi cikin ƙasa ya yi butu-butu.

Sannan mutane suka fara kula aka taru kansu. Da Kjyar aka janye Ado daga kan Fu’ad yana faɗin:

“Kai ɗin banza za ka zo har ƙauyenmu kai mana fitsara.

Wallahi ka sake dawowa sai dai waninka. Safiyya matata ce kana jina!!!”

Wasu ne suka kama Fu’ad suka ɗaga shi yana maida numfashi. Ciwon da yake ji daban ne da na jikin shi. Idanuwanshi da guda ɗaya har ya soma rufewa da alamar kumbura yake duddubawa bai ga Safiyya ba.

A firgice yake faɗin,

“Sofi…No…Sofi…”

Wani mutum ne ya kama shi saboda yadda ya ga kamar jini na ƙoƙarin ɗibarshi.

Duba shi ya ya ga ya fasa bayan kai. Jini kuma bai bar zuba ba har lokacin. A rikice yace:

“Subahanallah. Don Allah ku kamashi a je ko chemist ne jini yake zubarwa…”

Ture shi Fu’ad ya yi muryarshi har ta soma canzawa. Hannu ya sa ya dafe gefen kanshi yana faɗin,

“Sofi…Ta tafi…”

Wani ya dafa yana tafiya yana haɗe hanya. Mutane suka kamashi. Kanshi ya saki yana ture su. Ba ya son taimakon kowa. Momma yake so. Gida yake son zuwa. Wannan faɗan ba na shi bane shi kaɗai.

Dole mutane suka sake shi saboda yanda yake ture su yana faɗin:

“Fuck off!”

Wajen motarshi ya nufa. Kanshi ya sake dafewa yana jin wani luu. Da babu motar daya kai hannu jiki da ya faɗi. Wani datijjo mai ruwan kamala ya dubi mutanen dake tsaye yace,

“Malam garba ka taimaka wa yaron nan mana. Ko gidansu ya faɗa a tuƙa shi. Kana ganin yadda jini ke ɗiibarsa.”

Da yake malam garba direba ne. Yana jan motoci. Daga shi har datijjon mutanen arziƙi ne matuƙa da ake girmamawa da gani da mutunci a unguwar. Babu musu ya ƙarasa wajen Fu’ad.

“Kai kam samari ka bari a taimaka maka mana.”

Da ƙyar Fu’ad yace,

“Ni gida zanje. Kaina…”

“Sannu ka ji. Ka faɗa min inda kake sai inje in sauke ka. Ni direba ne.”

A yanda yake jinshi kaman ba a duniya yake ba. Yasan ba zai iya tuƙi ba. Haka ya gaya wa malam garba inda zai kai shi.

Shi ya karɓi mukullin motar. Ya buɗe ya kama Fu’ad ya saka shi a ciki. Sannan ya kalli dattijon da ya yi magana yace,

“Sai inga wani ya zo mu tafi tare. Don gudun matsala.”

Kallon-kallo suke an rasa wanda zai bishi don tunda sukagar motar Fu’ad ɗin kowa ya sha jinin jikinshi. Datijjon nan ya taka zuwa inda motar take yace:

“Muje…”

Sun nisa sosai. Sama-sama Fu’ad ke jin ringing ɗin wayarshi. Hannu ya sa a cikin aljihunshi ya zaro wayar da screen ɗinta ya farfashe.

Kanshi na wani irin juya mishi. Da Kjyar ma wayar ta dannu ya amsa ya kara a kunne.

“Ina ka shiga haka. Inata kira not reachable?”

Da ƙyar ya iya ce ma Hanee;

“Ka zo dai dai Dawanau. Please ka taho…”

Cikin alamun razana Haneef yace,

 “Fu’ad, are you okay?”

Da ƙarfin hali ya amsa shi da.

“Ka zo mana. Ka taho…”

Yanajin Haneef na magana amma ba zai iya amsa shi ba

Kanshi ma wani ciwo yake da duk Kjarar da ta shiga kunnen shi.

Dattijon da ke baya tare dashi ya miƙa ma wayar da fuska yake rokonshi da ya taimaka ya karɓa.

Karba ya yi ya kara a kunne tare da sallama. A razane Haneef yace,

“Waye kai?  Me ya same shi ne wai? Kuna ina?”

A nutse ya fara ma Haneef bayani da cewa,

“Ka kwantar da hankalinka. Mu taimakon shi muka yi. Faɗa su ka yi ne ya ɗan samu raunuka. Kamar yadda yace ka zo zamu tsaya daidai Dawanau.”

Jin anyi shiru yasa shi miƙa wa Fu’ad wayar da yake jingine jikin kujera.

“Lafiya wai?”

Momma ke tambayar Haneef da duk ya rikice.

“Momma Fu’ad…zan miki bayani…”

Da gudu ya fita daga falon tana ƙwala masa kira. A harabar gidan ya ci karo da Lukman.

“Mu je please… “

Kawai yace suka buɗe mota. A hanya yake faɗa mishi iya abinda ya sani.

Daidai Dawanau suka hango Range Rover ɗin Fu’ad tsaye. Parking ya yi suka fita shi da Lukman.

Wani dattijo suka hango tsaye jikin motar. A ƙagauce yace,

“Yana ina…?”

Lukman kam baibi takansu ba. Motar ya buɗe. Hannunshi ya kai ya dafe kai. Kwata-kwata kamannin Fu’ad ɗin sun sauya.

Ga wani numfashi yana ja da ƙyar. Rasa ina zai kama a jikinshi ya yi. Don jinin da yake gani bai san daga inda yake fitowa ba.

Haneef ya zagayo ya ture Lukman.

 “Ya Rabb…”

Ya faɗa yana zira jikinshi cikin motar ya kamo hannuwan Fu’ad ya tallaboshi ya fito dashi.

“Fu’ad…”

Yake kira amma da alamu ma bai san abinda yake yi ba. Ɗaga shi ya yi cak a kafaɗa ya nufi mota da gudu. Lukman ne ya tsaya. Ya zaro kuɗi a aljihunshi ya kamo hannun dattijon nan ya damƙa mishi tare da faɗin,

“Mun gode sosai Baba.”

Zagayawa ya yi inda Malam Garba yake ya karɓi mukullin motar da ke hannunshi ya ja motar yana bin bayan Haneef.

Asibitin Aminu Kano suka nufa da shi. Suna ƙarasawa suka yi parking. Haneef ya buɗe bayan motar. Lukman ya ƙaraso suka tallabo Fu’ad.

“Fu’ad…”

Haneef ya sake kira yana taɓa kumatunshi. Da ƙyar ya buɗe idanuwanshi kafin ya sake lumshe su ya wani langaɓe a jikin Haneef ɗin. Ƙasa suka yi a tare saboda wani nauyi da bai yi tsammani da Fu’ad ɗin ya yi ba.

Lukman ya dafa a rikice yana faɗin,

“Call for help…”

Da sauri Lukman ya tashi ya  ƙarasa cikin asibitin da gudu.

Girgiza shi Haneef yake yi yana faɗin,

“Wake up Fu’ad…..su waye sukai maka haka?”

Wasu nurses ne suka fito da wheel chair. Kama Fu’ad suka yi suka saka shi ciki.

Da sauri suka gungura shi. Wata nurse ke cema Haneef.

“Ba zamu taba shi ba saida ‘Yansanda gaskiya…”

Kai kawai Haneef ke jijjiga mata. Lukman ne mai ƙarfin halin ɗauko waya ya kira su Momma yake faɗa musu. Su taho da’ Yansanda.

Wani numfashi Haneef ya ja tare da faɗin,

 “Am going to fucking end ko waye ya taɓa Fu’ad …!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 16Akan So 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×