Skip to content

Akan So | Babi Na Sha Hudu

0
(0)

Karanta Babi Na Sha Uku.

Agogon shi yake ɗaurawa. A cikin kanshi babu komai sai son barin ƙasar gaba ɗaya. So yake ya bar komai inda ya kamata ya zauna tun daga farko. Amma abinda yake so a zuciyarshi da kanshi ya sha banban. A ‘yan kwanakin nan mafarkan da yake sun yawaita. Har idanuwanshi sun faɗa saboda ba shi da wata wadatacciyar nutsuwa. Komai baya masa daɗi. Ba ya son zama shi kaɗai. Don ma Lukman na hutu sai abin ya yi masa sauƙi.

Gudun Haneef yake don ba ya son gaya mishi asalin abinda ke damun shi. Ta ina ma zai fara ce masa shi Fu’ad yau tunanin mace ya saka shi a gaba. Tunanin macen ma kucaka ‘yar ƙauye. Abin da ɗan nauyin faɗa. Tunda shi bai san me ya sa ma yake jin abinda yake ji ɗin ba. Ji ya yi an turo ƙofar tare da sallama. Ya lumshe idanuwanshi ya buɗe su. Haneef ne ya nemi waje a gefen gadon shi ya zauna. Kallon shi yake yi sosai da ya soma damun shi saboda ya san zai karanci damuwa a fuskarshi. Yace,

“Na san ba fushi kake min ba. Avoiding ɗina kake yi na kuma rasa dalili. Me ke damunka?”

Takalmin shi ya wuce ya ɗauka. Ya dawo ya zauna ya na saka socks. Ciki ciki yace,

“Ba abinda ke damuna. Ka bar ni in shirya a nutse.”

Idanuwa kawai Haneef ya zuba mishi. Yana ta kallon shi har ya ƙarasa shiryawa. Wata ‘yar jaka ya ɗauka. Hannun shi ya sa cikin gashin shi tare da faɗin,

“Fuck this…”

“Language Fu’ad…language please.”

Haneef ya faɗa yana murmushi.

Kai kawai Fu’ad ya jinjina ya kalle shi yace,

“Kawai wani abune yake damuna. Bana jin zan iya magana akai yanzun. Just drop it.”

Gira Haneef ya ɗaga masa. Yana kallon yadda yake kokawa da kalmar da zai faɗa. Da ƙyar ya iya cewa,

“Please. Just drop it.”

Miƙewa Haneef ya yi yana ‘yar dariya tare da faɗin,

“Since you asked so nicely. Mu je sai mu biya mu ɗauki Lukman mu raka ka.”

Bai ce komai ba ya buɗe ƙofar ya fita. Cije leɓe ya yi ya rufe idanuwanshi ya buɗe su da yake fassara ba ya son abinda ke shirin faruwa. Gaba ɗayansu suna falo tsaitsaye Abba ne kawai ba ya nan. A taɓare yace,

“Momma mana. Me yaran nan suke yi?”

Dariya suka yi gaba ɗaya. Sun san ba ya son bankwana. In da za a bar shi zai sulale kowa bai sani ba.

Fa’iza ta ce,

“Dame ka ga ya maka kama?”

Hassan ya amsa da,

“Bro ɗin mu za mu raka Airport.”

Momma ya kalla idanuwanshi cike da roƙonta ta ce musu su yi zamansu.

Dariya kawai ta yi ta ce,

“Allah ya tsare ya ba da sa’a a duk inda kake addini da tarbiyarka su zo farko Fu’ad. Karka zub da su domin ruɗin duniya…”

Fu’ad ya katse ta da faɗin,

“Banda abokan banza. Banda ɗauko al’adar da ba tamu ba…banda banda banda…momma na haddace duka.”

Haneef ya tallabe mishi kai. Ya dafe yana faɗin,

“Ouchh that hurt.”

Dariya suka yi gaba ɗaya. Dole ya yarda su Fa’iza suka bi su. Lukman suka kira ya fito suka ɗauke shi shi ma. Har Airport suka raka shi. Su Hussaina na jero mishi tsarabun da suke so ya siyo musu.

Ya amsa musu da sai ya kira mama ya ji suna ƙoƙari a islamiyya da boko sannan.

****

Bayan Watanni Biyu

Europe

Babu abinda ke taimaka masa sai bacci. Da hannu biyu yake tallabar mafarkanta yanzun. Da kanshi yake fatan dare yayi ya kwanta bacci. In da babu su bai san yadda zai yi ba. Komai ya jagule mishi a watannin nan. Komai yake yi kamar wanda aka yi wa caji akai masa loading ɗin abinda ya kamata ya yi.

Abinci ma timing ya yi yasa a wayarshi. Da ya ga reminder zai tura ma cikinshi komai ya samu ba don bakin shi na gane daɗin abin ba. Shi ba abokai yake yi ba. Sai dai team mates kawai. Maganar da ta wuce wadda ta danganci abinda yake tarasu ba ta haɗa su. Sai ya wuni baice ma kowa komai ba. Fuskar nan a daƙune. Ba mai shiga harkarshi kamar yadda ba ya shiga ta kowa.

Da niyyar sai ya yi wata shida zai je gida kwana biyu ya zo. Amma sam ya ga ya kasa.

A daddafe ya yi wata biyun nan. Ticket ɗinshi da ke kan gado ajiye yake kallo. Yana son da duk wani sauran ƙarfi da yake da shi ya yi faɗa da son zuwa gida da yake yi.

Da duk numfashin da yake shaƙa yana jin yadda komai ke ruguje masa. Yana so ya ganta. In bai ganta ba zai iya ƙarasa gigicewa. Yana da wasa cikin sati uku masu zuwa da zai iya zama silar ci gaban shi. Ba zai iya yinshi cikin kwanciyar hankali da nutsuwar da yake so ba in har bai je ya ganta ba. Tunda ya tashi damuwa labarinta kawai yake ji. Sai yanzun ne ta iso inda yake.

Tunda ya tashi ƙunci nisantarshi yake yi amma yanzu ya samu wajen zama tare da shi.

Tun girmanshi ya ke ɗauka an damƙa mishi ikon tsara rayuwarshi yadda yake so.

Yadda ya zanata shi ne zai kai shekara ashirin da takwas. Zai samu yarinya mai zurfin karatu wadda za ta dace da tsarin rayuwarshi ya so. Zai yi auren shi babu wata damuwa. Za su yi rayuwarsu daga shi sai matarshi.

Zai yi rayuwarshi da abu biyu ne.  Zuciyarshi za ta ƙaunaci abu biyu ne kawai. Daga ball sai matarshi.

Ba shi da wajen ajiye wata damuwa. Bai san ya akai ƙaddara ta yi masa wannan kamun ba.

Bai fahimci asalin abinda yake ji ba sai jiya da yamma da ya zauna yana kallon wani fim “Heartbeat” tukunna.

Abinda ke faruwa da shi, shi ne yake faruwa da guy ɗin ciki. Sun kira abinda yake ji da So.

Sai dai bai taɓa ɗauka cewar Akan So  zai ji ya rasa farin cikin shi ba. Akan so zai kasa walwala. Akan so zai ji ya kasa sakewa ya yi ball da ya taso da ita a zuciya tun yarinta.

Wani numfashi ya ja ya sauke tare da miƙewa. Ya gama tsaida magana. Gobe zai bi jirgin ƙarfe 8.

Don haka ya fita ya ga ko zai samu abinda zai siya wa su Fa’iza.

*****

“Don Allah ku sama min lafiya Lami.  Mutum ba shi da ikon ya yi shiru sai kun dame shi da baƙar tambaya.”

Safiyya ta ƙarasa maganar tana zabga wani tsaki. Su Lami kam kallon juna suke yi. Saboda sun rasa kan safiyya a watannin nan. Ta canza gaba ɗaya. Abu kaɗan za kai mata sai ta hau ka da faɗa.

Sam ba halinta bane. Safiyya na da fara’a da haƙuri. Su za su iya cewa abinda duk ya ɓata mata rai ba kaɗan bane. Amma yanzun kullum cikin ƙunci take. Babu fara’ar nan. Ga wata rama da ta yi. Takan ga kuskure a duk wata magana da za su yi mata.

Wani hawaye suka zubo wa Safiyya ta sa hannu ta goge su. Cikin tashin hankali Lami tace,

“Subahanallah. Safiyya ki yi haƙuri wallahi ba nufinmu mu ɓata miki rai har haka ba. Muna tambaya ne kawai don mun damu.”

Jummai ta dafata tace,

“Abinda Lami ta faɗa gaskiya ne. Ba mu saba ganinki haka ba shi ya sa muke tambaya.”

Wasu hawayen ta ji sun sake zubo mata. Ita kanta halayyarta ta dameta. Sai dai ba ta da yadda za ta yi.

Cikin sanyin murya ta ce,

“Karku damu. Ba ku kuka ɓata min rai ba. Abinda ke damuna ba shi da alaƙa da tambayar ku.”

Fuskokinsu suka nuna alamar jin daɗin ba su suka ɓata mata rai ba.

Suna gudun tambayarta ko mene ne. A haka malamin Hadisin su ya shigo. Ana ta karatu safiyya hankalinta na wani waje daban. In za ka yankata ba ta san me suke faɗa ba. Wannan abinda da ya same ta ya isheta. Ba ta da damar wani ƙwaƙƙwaran motsi sai ta ji shi manne da ita. Wani irin mannewa ya yi mata da za ta iya rantsewa tana jin danƙonsa har a fatar jikinta.

Da dare mafarkinshi. Da rana tunanin maganganun shi. A zuciya fatan sake ganin shi tunda tana son fitar da shi ya ƙi ciruwa.

A kwanakin nan abin ya ƙara taɓarɓare mata. Ado ne a tsaye a gabanta. Amman fuskar Fu’ad take gani cikin tashi. Magana zai mata muryarshi take ji. Tun Inna na tambayarta me ke damunta.

Har ta gaji ta haƙura. Wani lokacin in tana kwance shiru takan ji Inna ta shigo ta taɓa jikinta ta ji ko ba ta da lafiya ne.

Ta kasa dainawa. Tana son ta tsaida komai ko don mahaifiyarta da ta damu da ganinta haka.

Ba ta san ta yaya za kai faɗa da abinda ya fi ƙarfinka ba. Abinda ko ɗan yatsa ba za ka iya ɗaga masa ba ballantana kai tunanin yaƙi da shi.

Ta bar wama Allah komai. Shi ya ɗora mata koma menene kuma shi yake da ikon yaye mata shi.

*****

Hassan na zaune shi da Hussaina suna kallon wrestling a New World cinema sunata gaddamar da suka saba.

Hassan yace,

“Yarinya ki yi haƙuri kawai. Ba fa yadda John Cena zai yi da ‘yan shield.”

Hararar shi ta yi tace,

“Ai don suna da yawa ne shi ya sa. Inba tsoro ba ayi da ɗai ɗaya mana.”

Amsa zai ba ta suka ji sallama. Da gudu suka tashi suka ruƙunƙume Fu’ad saboda ba su zaci zuwan shi ba. Da gudu Hussaina ta ruga ta na kiran Momma da ta zo ga bro ya dawo. Hassan kuwa yana tsaye yana kallon shi sosai. Saboda tunda ya tashi bai taɓa ganin fuskar Fu’ad da gashi ba.

Banda kanshi ba ya tara gashi ko ina. Amma yau fuskar shi cike take da gashi. Da alama rabon da ya yi aski tun sanda zai tafi.

Don ko gashin kanshi haka yake. Ya ƙara yawa sosai ga babu ko gyaran fuska. Sai ya ga duk ya canza masa.

Da sauri Momma ta fito. Cikin farin ciki tace,

“Fu’ad zuwa babu sanarwa haka.”

Da murmushi yace,

“Nima fa bansan zanzo ba.  Wai na samu kwana huɗu ne shi ne nace barin zo inyi su a gida.”

Kallon shi take itama. Da damuwa a fuskarta tace,

“Aikam gara da ka zo. Duk ka canza. Fu’ad ji fuskarka. Wai me ke damun ka ne haka?”

Ya ji daɗin Fa’iza  da ta fito tana faɗin:

“Wooo bro. Kaine haka kwatsam?”

“Nagaji fa. Bari in ɗan watsa ruwa.”

Ya faɗa. Hassan ya karɓi akwatin shi ya hau masa da shi sama. Ba ɓata lokaci shi ma ya bi bayanshi.

Sai da ya kira Lukman a waya bai ɗaga ba.  Ya yi tunanin ko yana da lectures ɗin Asabar ne. Text ya yi mishi sannan ya shiga wanka.

Yana fitowa ko mai bai shafa ba. Ya sa wani 3 quarter loose da hoodie. Kwanciya ya yi akan gadon yana jin wata nutsuwa da bai san ta inda take fitowa ba.

Kiran Lukman ya shigo ya ɗaga wayar yana faɗin:

“Don Allah ka zo mu yi magana.”

Lukman ya amsa shi da,

“Ka zo school ka ɗauke ni. Motata na wajen gyara.”

Bai yi musu ba ya katse wayar yasauka falo. Momma ce tace masa,

“Ka zo ka ci abinci.”

Yana tafiya yace,

“Sai anjima tukunna. Bari in zo Momma. Ba daɗewa zan yi ba.”

“Allah ya tsare.”

Ya amsa da amin yana ficewa.

*****

“Me ke damunka?”

Shine kalmar farko da Lukman ya furta masa yana kallon shi.

“Safiyya.”

Ya amsa mishi yana jingina da mota. Shiru Lukman ya yi yana daƙuna fuska. Da alama yana tunanin ya taɓa jin sunan nan. Amma ya kasa tuna ko a ina ne.

Don haka yace,

“Wace ce Safiyya?”

Wani kallo Fu’ad ke masa da ke tambayar yana nufin bai gane ta ba. Hakan ya fahimta ya sa shi cewa,

“Ni ya zan yi in gane ta?”

Ba yadda zai yi ne shi ya sa zai faɗa wa Lukman. Amma har ya fara hango kalar iskancin da zai yi masa. Muryarshi can ƙasan maƙoshi yace,

“Safiyya ta Bichi…”

Ƙwalo idanuwa Lukman ya yi kamar wanda aka gaya wa an sace motar da ya kai gyara.

“Safiyya da ka kulle wa iyaye?”

Kai Fu’ad ya ɗaga masa. Shiru Lukman ya yi kafin yace,

“Allahu Akbar. Allahu Akbar. Umn Allahu Akbar.”

Da mamaki Fu’ad yace,

“Kabbarar me kake yi kuma?”

Jinjina kai Lukman ya yi yace,

“Ina miƙa yabona ga Ubangijin da ke da iko da dukannin halitta. Ubangijin da ya dasa maka zuciyarka yake kuma iko da ita.”

“Hmm…. “

Kawai Fu’ad ya faɗi yana kauda kai gefe. Don ya san gaskiya ne kalaman da Lukman ya yi.

A ‘yan kwanakin nan ya gane shi ba komai bane.

“Ni ban san ya zan yi ba.”

Kallon shi Lukman yake yi. Don har lokacin mamaki yake. Rayuwa kenan. Ba wai don ya fi ƙarfin Safiyya ba. Shi ba mai cika baki bane ba. Amman Fu’ad da safiyya. Wani haɗi ne da ƙwaƙwalwarshi ba za ta ko iya ɗauka ba.

“Wallahi abin nan ya min girma Fu’ad na rasa ta ina zan fara ko kuma me zan faɗa.”

“Ni kawai ina so inganta ne. Shi ne kawai abinda ya dawo dani. Ko ban mata magana ba Lukman.”

Sauke ajiyar zuciya Lukman ya yi yace,

“Mu je ka aske wannan fuskar. Ka ɗan nutsu tukunna mu yi magana.”

Girgiza kai Fu’ad ya yi.

“Ba aski nake buƙata ba. Nutsuwa ta za ta samu idan naganta ne kawai.”

Wani abu Lukman yake ji da ba zai fassaru ba. Gaba ɗaya lamarin duniya ya ƙara tsorata shi.

Kalli yadda lokaci ɗaya Fu’ad ya birkice. Wato mutum ya ji tsoron Allah a duk inda yake. Ka gode masa in yana tallaba maka.

Za ka gane kai ɗin ba komai bane lokacin da Allah ya saukar maka da ƙaddarar da za ta birkita maka lissafi cikin ƙanƙanin lokaci.

“In kana so ka gan ta. Saika aske wannan gashin Fu’ad.”

Ba ya son yawan surutu da jan magana din haka ya zagaya ya buɗe mota ya shiga ya bar wa Lukman wajen zaman driver.

Har suka je shagon mai aski ba su ce komai ba. Kowa da abinda yake saƙawa a zuciyarshi.

Aski akai mishi. Har ya ɗan nutsu. Sai dai askin sai ya fito da ramar da ya yi sosai. Dama shi ba wata ƙibar kirki ba. Farin ne kawai sai dogon hanci. Suna mota ne ya ga Lukman ya ɗauki hanyar gida.

“Ya haka kuma Lukman?”

Kallonshi ya ɗan yi ya maida hankalinshi kan tuƙin da yake yi.

“Ai dai ka bari in ci abinci. In watsa ruwa mu yi sallar azahar ko?”

Haɗe fuska Fu’ad ya yi.

“Ni da mun tafi yanzun.  Ni ba ma na jin yunwa.”

Shiru Lukman ya yi mishi. Ya bar shi ya ji da abinda ke damun shi ma. Ya ga alamun Fu’ad ɗin so yake ya rage damuwar dake ranshi ta hanyar jan shi da rikici.

Dole ya haƙura suka je gidansu Lukman. Ya yi wanka ya fito. Ba yadda bai yi da shi ba su ci abinci yace ba ya ci.

Jiran shi dai ya yi ya gama ci. Tare suka yi alwala suka fita masallaci. Suna dawowa sallar Azahar Lukman ya tuƙa su zuwa Bichi.

Da duk kusancin su da Bichi da yawaitar ƙarin bugun zuciyarshi. Lukman kanshi da yake gefe sai yanzun yake ganin tsantsar wautar da suka yi.

Yana ganin lokacin da Fu’ad zai san mene ne rayuwa ya yi. Lokacin da zai girbi abinda ya shuka.

Sai wani tausayin shi ya kama shi. Saboda ya san ko ba su raba wannan abin tare ba. Zai samu nashi kason.

Fu’ad kam ya rasa inda tunaninsa ya kamata ya tsaya. Ya rasa me ya kamata ya ji. Ya ɗauka farin cikin shi zai dawo daga lokacin da suka ɗauki hanya. Amma sai ya ji banbancin haka. Saima da ya gan su cikin garin Bichi. Ya ga motar ta yi kwana  zuwa layin su Safiyya.

Ya ga da gaske shi ne a cikin garin Bichi. Shi ne ya zo ya ga Safiyya.

Lokaci ɗaya wata fargaba da tsoro suka cika mishi zuciya…!

Babi Na Sha Biyar

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×