Skip to content
Part 18 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

“Ya isa haka mana Safiyya. Sai kin ja ma kanki wani ciwon. Tunda kika ga har dare ya yi haka da wahala Ado ya zo ya faɗa wa su Baba.”

Jummai tace tana ɗan bubbuga bayan Safiyya da ke kwance jikinta tana wani irin kuka tun barin su wajen.

Lami taɓe baki ta yi.

“Ni ina ma mamakin ki ne wallahi. Duk abinda ya yi muku amma ki ce kin damu da shi?”

Idanuwanta ta daago cike da hawaye ta ce ma Lami,

“Tun da ance miki zuciyata ta san wannan ko?  Na gaya miki ne don na yi alƙawari ba wai don ki auna min abinda yake faruwa da ni ba. Na fi ki sanin rashin dacewarshi.”

“Ki rabu da Lami kema Safiyya. Allah dai ya kawo ƙarshen abin. Bari mu tashi mu tafi gida. Sai kuma gobe in Allah ya kai mu.”

Fadin Jummai tana janye Safiyya daga jikinta. Har suka sa kai suka fita daga ɗakin ta kasa ko magana.

Kukanta ta ci gaba da yi ko za ta ji sauƙi. Duk yadda Fu’ad ya rama dukan da su Ado suka yi masa bai mata ba. Su biyu suka tarar mishi. Ko ya ta rufe idanuwanta sai ta ga hoton abin. Girman jiki da shekaru ta tabbata su Ado sun fi Fu’ad.

Wata tsanarshi ta ƙara cika mata zuciya. Wani irin abu take ji a zuciyarta. Fata take Fu’ad ɗin ya kirata ta ji lafiyarshi.

Abinda zai biyo baya ba shi ke damunta ba. Lafiyar Fu’ad a yanzu ta fi mata komai.

*****

“Haneef ka ci wani abu mana.”

Girgiza kai ya yi. Ranshi yana ɓaci. Amma bai taɓa kai matakin na yau ba. Don har wani duhu-duhu yake gani cikin idanuwanshi.

Wani abu yake so ya kaima duka ko ma menene ya ɗan rage abinda ke tafasa a zuciyarshi.

Daga shi sai Lukman zaune a ɗakin da aka kwantar da Fu’ad . Bayan tabbatarwa da su Haneef cewar zai tashi.

Ya dai samu concussion saboda buguwar da ya yi akai. Amma komai lafiya ƙalau. Yana buƙatar hutu ne.

“Allah Lukman ko su waye sai sun gane kurensu….”

Wani numfashi Lukman ya sauke.

 “Fu’ad ɗin dai ya tashi mu ji ya akai.”

A ƙufule Haneef yace,

“I don’t care ko shi ne bashi da gaskiya. Abu ɗaya na sani. They are going to pay for this.”

Shiru Lukman ya yi. Don ko shi tun tasowarsu a yarinta bai taɓa ganin ran Haneef ya ɓaci haka ba.

Asali ma shi ne yake ƙoƙarin basu haƙuri in wani abin ya taso.

Nan suka kwana tare da Haneef. Tunda safe Lukman ya tafi saboda yana da lectures.

Har wanka a nan Haneef ya yi. Da su Fa’iza za su zo suka taho masa da kaya. Har suka gama zamansu suka tafi Fu’ad bai farka ba.

Haneef na zaune yana karatu da wayarshi ya ji kamar an motsa. Wayar ya ajiye ya matsa sosai kusa da Fu’ad.

Motsawa ya sake yi. Ya dafe kanshi yana faɗin,

 “Owwhh…”

“Fu’ad…?”

Idanuwanshi ya buɗe a hankali. Ya samu ‘yan mintina yana tunani kafin komai da ya faru ya dawo mishi. Abu ɗaya ne ke masa yawo cikin kai. Miƙewa ya yi da saurin shi. Haneef ya kama shi dam yana faɗin,

“Ka bi a hankali. Ba ka ganin ruwa ne a jikin ka?”

Muryarshi a dakushe yace,

“Tun yaushe nake nan?”

Da mamaki a fuskar Haneef ya amsa shi da,

“Tun jiya.”

Dafe kai ya yi. Ba shi da lokaci mai yawa. Gobe ne ɗaurin auren Safiyya. Ganin da gaske saukowa yake son yi daga kan gadon ya sa Haneef faɗin,

“Ka nutsu mana. Ina za ka je ne haka?”

Ya dafe kanshi da ke juyawa. Yace,

“I need to go Haneef. Ba za ka gane bane. I have to…”

Tunanin Haneef ko buguwar da Fu’ad ya yi a kai ne take son bashi matsala. Miƙewa ya yi yana faɗin,

“Ko ma ina ne za ka je. Ka jira ni anan. I will be right back.”

Kafin ya amsa mishi ya fice daga ɗakin da sauri ya bar Fu’ad a zaune. Ƙarin ruwan da ke jikinshi ya cire. Kalle-kalle yake yi cikin ɗakin. Ya ko hango mukullin motar Haneef.

Ɗauka ya yi. Yanajin kanshi na wani sarawa kamar zai ɓalle ya faɗi. Takalmanshi da ke ajiye a gefe ya ɗauka.

Da ƙyar ya saka su. Ya lallaɓa ya fice daga ɗakin ya nufi hanyar da za ta fitar da shi daga asibitin.

Haneef kam fita ya yi don ya kira Likita ya faɗa mishi Fu’ad ya farka. Ya ci karo da wani abokin shi da tun da suka gama Secondary School rabon da su haɗu. Aka tsaya ana gaisawa. Yake tambayarshi ko wa ya kawo.

“Brother ɗina ne. Na ma fito ne in kira Likita. Kai fa?”

Abokin ya amsa shi da,

“Matar brother ɗina aka yi wa aiki. Ka faɗa min lambar ɗakin da kuke. In na fito sai in shigo in duba shi.”

Faɗa mishi Haneef ya yi. Suka yi musayar lambobi sannan ya wuce ya yi magana da wani likita. *

Ɗakin ya gani wayam. Ya girgiza kai. Zaton shi Fu’ad na banɗaki. Don haka ya cire ruwan.

Zama ya yi a kan kujera yana jiran ya fito. Har likitan da ya kira ya shigo amma Fu’ad shiru.

Da kanshi ya tashi ya je ya ƙwanƙwasa ƙofar banɗakin tare da kiran sunanshi. Nan ma shiru kake ji.

Turawa ya yi.

“Ya Allahu…”

Ya faɗi da ya ga Fu’ad ɗin ba ya ciki. Dawowa ya yi ɗakin ya sake dubawa ko dai idanuwanshi sun samu damuwa ne.

Mukullin motar da ya ajiye kan drawer ya kai idonshi kai ya ga ba ya wajen. Ai ko takan likitan da ke tsaye Haneef bai bi ba ya buɗe ɗakin ya fita da gudu.

Inda ya yi parking mota ya ƙarasa bai ga motar ba. Tsaye ya yi kawai don ya rasa me ma ya kamata ya yi.

*****

Inna ce zaune kusa da Safiyya da tun jiya wani irin zazzaɓi mai zafi ya saukar mata.

Ga ciwon kai. Abin ma ƙaruwa ya yi da ta ji Fu’ad bai kirata ba ballantana saƙon shi.

Dafa ta Inna ta yi.

“Safiyya ko dai mu je asibiti?”

Girgiza kai ta yi. Idanuwanta na cika da hawaye. Yanzun ta ƙara tabbatarwa ba za ta iya zama da Ado ba. Ji take in ta aure shi mutuwa za ta yi ko da kuwa ba za ta samu Fu’ad ba. Muryarta na rawa da sauri don karta kasa ta ce,

“Inna don Allah a fasa auren nan… “

A razane Inna ta dafe ƙirji.

“SubhanAllah! Safiyya?  Me ya shigeki haka?  Kin san me kike faɗa kuwa?”

Hawayen da suke idanuwanta suka gangaro. Kai ta ɗaga wa Inna alamar tana sane sannan ta ce,  

“Inna don Allah…”

Rufe mata baki Inna ta yi. Don jikinta har kyarma yake yi kar wani ma ya ji me Safiyya ke faɗi.

“Zafin zazzaɓi ne kawai Safiyya. Ki yi shiru kar ma wani ya ji ki. Bari in ga ko Usman ya kawo maganin.”

Miƙewa Inna ta yi ta fice daga ɗakin ta bar Safiya ita kaɗai.

Hijabin da ke jikinta ta ja ta rufe kanta tana ci gaba da wani kuka marar sauti da yake fitowa daga zuciyarta.

Ba magani take buƙata ba. A warware maganar aurenta da Ado shi ne kwanciyar hankalinta.

Ga Fu’ad shiru har yau ɗin nan babu kiranshi babu saƙon shi. Addu’o’in duk da suka zo mata ta shiga jerowa tana fatan Allah da ya ɗora mata wannan abin ya kawo mata mafita.

*****

Wani irin gudu yake da motar.   Ko da ya ganshi kan titin gidan su Safiyya bai tsaya ba. Inda ya saba tsayawa ya ja motar ya tsaya.

Aljihunshi ya laluba. Ya sauke wata ajiyar zuciya tare da gode wa Allah jin wayarshi na ciki.

Kunnata ya yi ya ga ta sake mutuwa alamar babu caji a jiki. Cikin motar ya sa caji ya yi zaune ya jingina kanshi da sitiyari.

Wani irin bugawa zuciyarshi take yi kamar za ta fito daga ƙirjinshi. Hanya ɗaya ce ta rage masa akan safiyya.

Hanyar da yake tsoron Safiyya ba za ta taɓa amincewa ta bi tare da shi ba. In kuwa har ba ta bi ba bai san me zai iya faruwa da shi ba.

Wayar ya duba ya ga ta ɗan hau. Hannunshi har rawa yake yi ya dubo lambarta ya danna kira.

Bai taɓa jin tashin hankali irin na yau ba tunda ya zo duniya. Cikin shi ya wani ƙulle.

Wayarta ta ji tana vibrating. Da sauri ta miƙe daga kwanciyar da take ta ɗauko ta.

Dannawa ta yi ta kara a kunne tana jin wanni sanyi na ratsa ta. Har zazzaɓin da take ji ya soma sauƙi.

“Kana lafiya?  Ba abinda ya same ka ko?”

Safiyya ta tambaya muryarta na rawa saboda wasu sabbin hawaye da ta ji sun zubo mata.

Shi ma tashi muryar na rawa yace,

 “Ina inda kika sameni jiya. Ki fito please. Ki fito tukunna insan ko zan samu lafiya ko ba zan samu ba.”

Kafin ta ce wani abu ya kashe wayar. Zuciyarta kawai ta biye wa ta miƙe. Fitowa ta yi daga ɗakin. Mutanene cike da gidansu ana ta hidima.

Buta ta ɗauka da ke can gefe kamar za ta shiga banɗaki. Ta tsaya jim ta ga ko wani na kula da ita.

Hidimarsu suke ta sha. A hankali gabanta na wani irin faɗuwa ta wuce da sauri ta nufi soro.

Jin ƙafafuwanta take yi kamar na roba tsabar tashin hankali da zullumin kar wani ya ganta da take ciki.

Hijabinta ta jawo ta sama ta sake rufe fuskarta don kar wani ya gane ta.

Unguwar shiru kamar babu mutane. Mamakin ƙafafuwanta take yi. Har sarƙewa suke su kaɗai kamar wanda babu ƙashi a ciki.

Motar da ta gani duk da ba ta taɓa ganin kalarta ba ya sa ta san Fu’ad ne a ciki. Ta ƙarasa tana dube-dube ko wani na ganinta.

Yana zaune sai zufa yake kamar babu AC a motar. Wani irin yanayi yake ciki mai wuyar fassarawa.

Idanuwanshi na kan hanya yana kallon ta inda za ta ɓullo ya hangota. Wani ɗan ƙaramin relief ya ji.

Buɗe murfin motar ya yi yace mata,

“Shigo Sofi…”

Idanuwan nan nata da ke hargitsa masa tunani cike da tsoro ta sauke masa tare da girgiza kai.

“Don Allah ki shigo mu yi magana. Ko kina so wani ya ganki?”

Da alama maganarshi ta yi tasiri don shiga motar ta yi da saurinta. Hannu ya kai ta rakuɓe jikinta.

Gyarawa ya yi ya rufe motar. Yana kallon yadda ta matse jikin kujera kamar za ta shige ciki don kar hannunshi ya taɓa jikinta.

Gyara zama ya yi.

“Ni bansan ta inda zan fara ba.”

Ya faɗa yana murza zoben da ke yatsanshi kamar zai bashi idea ne.

Safiyya kam gabanta ke wani irin faɗuwa. Ɗan sauran hankalinta na son ta yi amfani dashi wajen tunani amma zuciyarta ta fi ƙarfin shi yau.

Ita ke da mulkin a hannu. Ganin Fu’ad. fuskar shi da take a kumbure. Sanin sanadinta ne hakan ya faru da shi.

Jin muryarshi. Komai saiya ƙarasa ƙwacewa daga hannunta. Yau zuciyarta ce da mulkin. Sai dai tana tsoron hukuncin da za ta iya yanke mata.

A tsorace da abinda zai iya biyowa Fu’ad yace,

“Na so ace iyayenki sun ba ni aurenki lokacin da aka zo nemar min sofi…

Bamu da lokaci. Gobe war haka na rasa ki…”

Muryarshi ta wani maƙale saboda abinda yake ji a zuciyar shi.

Lumshe idanuwanta ta yi. Tunanin maganarshi na mata yawo. Gobe warhaka ta zama mallakin Ado.

Girgiza kai take yi. Ba za ta taɓa iya zama da Ado ba. Wautar amincewa aurensa take gani ƙarara.

Wani kuka ya ƙwace mata. Ganin hakan ya sake ɗaga wa Fu’ad hankali.

Jin kukan yake yana wani ci masa rai.

“Sofi… Please. Hanya ɗaya muke da ita. Ki zo mu gudu! Ki bi ni mu je a ɗaura mana aure a wani waje…”

Da sauri take masa wani kallo dake faɗin tabbas bashi da hankali.

Hakan ya karanta yasa shi ƙarawa da,

“Karki mun haka Sofi… Wallahi zan iya mutuwa. Zuciyata za ta iya tsayawa in kika auri wani…”

Kuka take yi sosai. Zuciyarta na son amincewa abinda Fu’ad ɗin ya zo da shi. Bayan haka ma ai aure ya ce za su yi ba wani abin ba.

Cikin kuka tace,

“Inna fa?  Ga Baba ma. In ce musu me?  Akan Sonka na bar su?”

Abinda ko da wasa wani yace zai yi a shekarunshi abin ba ƙaramar dariya zai bashi ba wato kuka.

Hawaye ne yake jinsu cike da idanuwanshi yau. Shi Fu’ad zai yi kuka wa wata mace.

Cikin rawar murya yace,

 “Ki kalleni mana ni.  Akan so yau ni Fu’ad zan iya yin komai Sofi. Akan sonki komai ya warwaremun. Inna da Baba za su gane. Ba wai mun tafi kenan ba. Zamu dawo mu yi musu bayani.”

Ganin yadda kalamanshi ke shirin yi mata tasiri ya sa ta buɗe motar ta fita. Da sauri ya buɗe ya rufa mata baya.

Tsugunnawa ya yi ƙasa. Gwiwa biyu yana faɗin,

“Sofi…. Karki min haka. Don Allah karki auri wani.”

Kallonshi take yi. Bata damu da duk wanda ma zai wuce ba. Hawaye ta gani yana zubo masa.

Yana kallonta da idanuwansa da take karantar roƙon da zuciyarshi take mata ta cikinsu.

Zuciyarta a dake ta ce,

“Ka jira ni. Ka jira ni anan. In har da gaske kana sona za ka jira ni.

Zan yi wani abu guda ɗaya. In har bai yi daidai ba zan dawo…”

Kafin ya ce komai ta juya ta koma. Idanuwa ya bita da su yana kallonta.

Miƙewa ya yi ya koma kusa da motarshi yana jin kamar a tashi rayuwar komai ya ƙare.

Zamewa ya yi jikin motar ya zauna a ƙasa cikin dattin da ke wajen. Ko damuwa bai yi ba.

Kanshi ya haɗa da gwiwarshi wasu hawaye da bai san ta inda suke fitowa ba suna zubar mishi.

Tari ya ji ya soma zuciyarshi na wani irin zafi. Kamar iskar da ke cikinta na fita.

Da wani irin ƙarfin gwiwar da ba ta san daga inda ya zo ba. Ta shiga gida. Inna ta hango. Ta ƙarasa wajenta. Hannunta ta kamo ta ja ta zuwa ɗaki.

Ita kanta Innar mamaki ya hanata magana. Haka ta bi Safiyya baki a sake.

Sakin hannun Inna ta yi ta tsugunna ƙasa ta riƙe kafafuwanta. Idanuwanta sun wani bushe.

“Inna don Allah kar a aura min Ado. Wallahi ba na son shi. Wallahi zan iya mutuwa idan na auri Ado.”

Salati Inna ta saka. Tana ƙara wani kan wani. Ko dai asiri a kai ma Safiyya ne haka. Wannan wanne irin abu ne.

“Oh ni. Safiyya wai me ya shiga kanki haka?  Gobe fa ɗaurin aurenku. Sannan za ki ce ba kya son shi?

Girgiza kai Safiyya take yi. Inna ta gane mana. Ta fahimci amsarta ita zata yanke mata hukuncin da take son ɗauka.

Da faɗuwar gaba da Inna ke ta fama da shi tun jiya ta ce,

“Kin ga ki yi shiru. Wallahi in har Baban ku ya ji maganar nan ranki da nawa in ya yi dubu sai ya ɓaci.

Kin fi kowa sanin ba ya magana biyu. Ko da gawarki za a kai gidan Ado sai kin aure shi.

Kar kuma na sake jin wannan sakarcin don kar ma wani ya ji baki ya kama ki.”

Kan Safiyya a ƙasa ta ce,

“Ki gafarceni Inna. Ki ce wa Baba ma ya gafarce ni.”

Kamata Inna ta yi tana janyewa daga jikin ƙafarta. A tausashe ta ce,

“Bakomai Safiyya. Ki yi ta addu’a kin ji ko?  Kin ga mutane na jirana. Na san su Lami za su zo babu jimawa.”

Ba ta ce komai ba har Inna ta fito. Kamar wadda take cikin ɗimuwa haka take jinta. Miƙewa ta yi.

Har ta fice babu wanda ya kula da ita. Wani abu can cikin ranta da ba ta san ko menene ba yana ta mata wasu maganganu da ba ta ganewa. Ba kuma ta fasa tafiya tana nufar inda motar Fu’ad take ba.

Bai san iya lokacin da ya ɗauka nan a zaune ba. Kawai dai ya san komai ya ƙare masa.

Da tafiyar Safiyya ta tafi da duk wani farin ciki nashi. Ya rasa me ke ja masa tarin nan da ke sarƙe shi. Numfashinshi ne yake fita da ƙyar da ƙyar. Kamar daga sama ya ji ta ce,

“Mu je…”

Sam bai ji zuwanta ba sai muryarta. Ɗago kanshi ya yi. Yana ci gaba da tarin dake tsayar masa da iska. Da ƙyar ya iya cewa,

“Sofi ke ce ko dai ni ne nake hallucinating?”

Tsaye ta yi ba ta ce masa komai ba. Ita kanta ji take kamar ba ita ba. Kamar wani abu ne ya yi taking control ɗin jikinta yake aiwatar da komai.

Miƙewa ya yi. Ya buɗe mata mota yana kallo ta shiga. Tsaye ya yi na ‘yan mintina yana kallonta.

Gani yake kamar za ta ɓace. Kamar komai dake faruwa mafarkine kawai da zai iya farkawa ko da yaushe.

Tuƙi yake yana yi yana kallon Safiyya ko za ta ɓace. Tana nan zaune. Banda fitar numfashinta da yake ji, za ka iya rantsewa ba ta motsi.

Safiyya kam har lokacin wani shiru take ji cikin kanta. Wani abu ke shirin faruwa da ita. Tana ji a jikinta.

Wani abune mai girma da ta kasa tsayar da aukuwarsa. Gaba ɗaya kamar wadda ta rasa hankalinta take ji.

******

Momma ya faɗa wa duk abinda ya faru. Da yadda ya ɗauko tasi zuwa gida.

Salati kawai take yi.

“Anya ba asiri a kai wa Fu’ad ba?  Ko dai aljana ce ya haɗu da ita? Wannan wanne iri bala’i ne?”

Haneef da ke zaune ya karɓi ruwan da Fa’iza ta miƙo masa.

“Wallahi ni abin ma tsoro yake ba ni kuma. Ban ma san me zan yi ba?”

Fa’iza ce tace,

“Mu bi shi ko can ɗin ya nufa.”

Kai Haneef ya ɗaga mata yana fadin,

“Bari in ji ko Lukman ya dawo gida. Ba zai ji daɗi mu tafi babu shi ba.”

Momma da ke tsaye ta rasa abinda za ta yi tace,

“Bari ni ma in kira Abbanku in sanar da shi. Ya kamata a ɗauki mataki ba sai ya je ya kashe kanshi ba.”

Wucewa ta yi zuwa ɗakinta inda ta baro wayarta. Ta bar Haneef da Fa’iza anan don ‘yan biyu suna makaranta.

*****

Bai san inda zai yi da su ba. Bai san wa zai kira ya ɗaura musu aure ba.

Bai san me zai yi ba . Ba ya son ya kira Lukman ko Haneef. Ya san babu wanda zai goyi bayanshi.

Saboda babu wanda yake gane abinda yake ciki ko yake ji. Hamza ya kira suna shiga cikin Kano ya faɗa masa inda zai zo ya same su.

Cikin mota ya bar Safiyya. Ya fita suka yi magana da Hamza ya faɗa masa abinda yake so da kuma yadda yake a shirye da ya biya ko ma nawa ne.

Ya san malamin da da dubu goma zai ɗaura wa Fu’ad aure. Sai dai shi kanshi yana ganin rashin hankalin Fu’ad ɗin.

Duka-duka nawa yake da zai jajibo wa kanshi aure. Jin ya yi shiru ya sa Fu’ad faɗin,

“In ba ka sani ba ka faɗa min in nemi wani.”

“Sorry. Daɗina da kai gajen haƙuri.”

Bayanin komai Hamza ya yi mishi. Wajen Hamza ya ranci kuɗi don bai fito da atm ɗinshi ba suka tafi.

Har lokacin Safiyya kamar ba a hayyacinta take ba, ba ta san meke damunta ba.

*****

Momma, Haneef, Lukman, Fa’iza, ‘yan biyu da Abba su duka suna zaune a falo jugum.

Har Bichi su Haneef sun je ba su ga Fu’ad ba. An kira duk wasu abokai da ake tunanin ko yana tare da su amma shiru.

Sam ba su san inda ya yi ba. An kira wayarshi a kashe. Gaba ɗaya hankulansu a tashe yake.

Don Hussaina ma kuka take ta yi tunda suka dawo makaranta aka faɗa musu.

Abba na shirin tashi su kai report Police Station suka ji sallamar Fu’ad.

Miƙewa suka yi duikansu. Momma na Hamdala da Allah ya dawo mata da ɗanta lafiya.

“Ina ka je haka Fu’ad?”

Haneef ya tambaya. Kan Fu’ad ɗin a ƙasa har lokacin yana kuma tsaye bakin ƙofa ya kasa ƙarasawa.

“Ina ka je ka ɗaga wa mutane hankali?”

Abba ne da wannan tambayar. Jin muryar Abba ya sa Fu’ad ɗagowa, ya dai kasa haɗa ido da kowa.

Muryarshi a sanyaye yace,

“Aure na yi..!”

Safiyya kam tana cikin mota a zaune. Tunda aka ɗauro mata aure da Fu’ad take jin ba ta da lafiya.

Hannuwanta take kallo kamar za su ba ta amsar abinda take ji. Kai su ta yi zuwa fuskarta.

Tana son idan ma mafarkin da ta saba yi ne gara ta farka haka nan kafin komai ya dagule mata.

Ya ma za ai a ce tayi aure ba tare da sanin Baba ko Inna ba.

Ta ya ma za a ce ta auri Fu’ad ɗin da duk soyyar da ta yi da shi kaso 98% cikin 100% a mafarki ne.

Wata irin dariya ta kwashe da ita. Yau kuma inda haukan mafarkinta ya ɗauko ta ya kawota kenan.

Lallai son Fu’ad wata irin ƙaddara ce mai ban mamaki akanta.

“What!!!??? “

Lukman da Haneef da Fa’iza suka faɗa a lokaci ɗaya. Abba kam ya daƙuna fuska yana jin maganar Fu’ad kamar daga sama.

Momma ta ƙarasa kusa da shi ta kama kafaɗar shi ta girgiza tana so ya dawo cikin hankalin shi.

Hannunta ya ture a hankali yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya.

“Da gaske nake aure na yi. Aure aka ɗaura min. Sofi na aura.”

Fu’ad ya faɗi da wani yanayi a muryarshi.

Momma ta juya tana kallon su Abba don su kawo mata ɗauki. Tabbas Fu’ad ya samu matsala.

Kama hannunshi ta yi tana son ta ja shi ta zaunar amma kamar an dasa shi.

“Mu je ka zauna a kawo maka ruwa.”

Momma ta faɗa da sigar lallashi. Girgiza mata kai ya yi.

“Sofi na cikin mota. Me yasa kuke mun wannan kallon?  Da hankali na. Aure muka yi.”

Fu’ad ya faɗa yana duban fuskokinsu. Abba ya kasa cewa komai. Yanzu yake ganin abinda matarshi take faɗa masa.

Lukman ne ya nufi hanyar waje. Don ganin abinda Fu’ad ɗin yake faɗa ko gaskiyane.

Da gudu ya dawo ya kalle su yace,

“Da gaske yake tana mota.”

Haneef ne da Fa’iza suke rige-rigen fita waje don gano gaskiyar abinda Lukman yake faɗa.

Ko shi ma abinda yake damun Fu’ad ɗin ya haɗa har da shi. Ganin ta suka yi a zaune.

A tsorace Fa’iza ta koma bayan Haneef. Ko aljana ce. Ƙarasawa ya yi ya buɗe motar ya kalli Safiyya da take a firgice.

“Fito.”

Yace mata. Babu musu ta fito tana kallon shi da kuma gidan ma gaba ɗaya. Ƙafarta ta matsar tana binta da kallo kamar tana son tabbatar da ko ba ƙasa bace take takawa.

Ba ta san me ke damunta ba. Me ke faruwa da ita ne haka. Su kuma waɗannan su wanene.

Fa’iza ke ƙarewa Safiyya kallo. Allah kenan. Mai ƙaddara yadda ya so. Wannan ce ta rikita bros ɗinta haka kuwa?

Gaskiya in ba Aljana bace to Mayya ce. Don ita ba ta ga abinda ke jikin Safiyya da zai ja hankalin Fu’ad ɗin ba.

Komawa ta yi ta nufi cikin gida. Haneef da Safiyya da ke taka ƙasa kamar tana tsoron za ta tsage ta faɗa da ita na biye da ita a baya.

Ko sallama basu yi ba suka shiga ciki. Suna ƙarasawa cikin falon sosai. Kallon su take ɗaya bayan ɗaya. Sannan ta maida dubanta kan Fu’ad da ke gefenta.

Zuciyarta ta ji tana wani rawa. Wani abu ya ƙulle a cikinta. Kallonshi ta yi cikin tashin hankali tace,

“Mafarki nake ko da gaske ne?”

Shima kallonta yake yi yana jin wani iri.

“Da gaske ne Sofi. Aure muka yi.”

Innalillahi wa inna ilaihir raji’un take furtawa a cikin zuciyarta. Ba mafarkin komai take ba da gaske ya faru. Da gaske ne ta bar komai ta zo ta auri Fu’ad. Ta baro Inna da Baba.

Ta watsar da duk wata tarbiya da suka gina mata shekaru goma sha takwas.

Wani jiri ta ji ya kwasheta. Kafin wani ya lura da me ke faruwa ta kai ƙasa!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 17Akan So 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×