Skip to content

Akan So | Babi Na Takwas

0
(0)

<< Previous

Lukman ne ya zo gyara kwanciya ya ga mutum a zaune. Idanuwan shi ya ware sosai. Ya lalubo wayarshi ya haska.

“Fu’ad?”

Ya kira muryarshi cike da bacci. Ɗagowa Fu’ad ya yi ya kalle shi da idanuwanshi cike da bacci.

“Ka kwanta mana.”

Ya yatsine fuska.

“Ba zan iya bacci anan ba Lukman. Ga zafi ga sauro. Wajen kuma ya matse da yawa. Just go back to sleep i will manage.”

Girgiza kai ya yi alamar eh. Haneef da ke bacci gefensu ya motsa saboda yanajin maganganu sama sama.

“lafiya?”

Ya tambaya yana kare idanuwanshi daga hasken fitilar wayar lukman.

“Fu’ad ne wai ba zai iya bacci ba.”

Cewar Lukman. Wani guntun tsaki Haneef ya ja. Matsalolin Fu’ad yawa ne dasu. Pillow kawai ya ja ya sauka daga katifar zuwa ƙasa. Lukman ma pillow ya ɗauka ya sauka ƙasa kan leda.

“Ku dawo bacci ne ba zan iya ba. Ga zafi ga sauro. “

Fu’ad ya faɗi cikin jin haushi.

“Ka kwanta malam.”

Inji Haneef. Girgiza kai ya yi. Yasan taurin kan Fu’ad kamar yunwar cikinshi.

“Lukman tashi mu koma. Dan ubanka karka kwanta.”

Baccinsu suka koma suka ƙyale shi. Shi kam da ya fara baccin ma farkawa yake. Ga kanshi na wani irin ciwo. Akan kunnenshi aka kira sallar Asuba. Ya tashi su Haneef. Abu ɗaya ne matsala. Banɗakin dazaie shiga. Haneef suka bari a ɗakin suka fita zuwa motar Fu’ad ɗin cewa shi zai ɗauko ruwan da zai yi alwala.

Suna hanyane yace:

“Damn. Wallahi na bar brush ɗina. Ban ɗauko komai ba.”

“Kar ka damu. Sanin halinka ya sa na ɗauko extra.”

Numfashi Fu’ad ya sauke. Suka je suka ɗauko. Suka koma. A bakin shagon suka yi brush ɗinsu.

“Haneef fitsari fa nake ji.”

“Zo ga bakina. Ka yi a ciki.”

Lukman ya bushe da dariya. Wani mugun kallo Fu’ad ya watsa mishi kafin yace:

“wallahi da gaske. Lokacin sallah na wucewa.”

Cikin shagon Haneef ya koma ya kira Khalid mai shagon. Ya tambaye shi ko da akwai banɗaki kusa sannan ya fito.

“Sai ka taso.”

Ba musu ya tashi ga mamakinshi cikin shagon suka koma. Haneef ya buɗe wata ƙofa da duk zaton su wadda za ta kaika cikin gida ce.

Banɗaki ne ɗan matsakaici. Shafe da siminti. A bushe yake tsaf. Bokitin ƙarfe a gefe sai kwandon soso. Sai masai irin namu na gargajiya da murfi a rufe.

Wani baya Fu’ad ya yi yana bata fuska kamar zai yi amai.

“Kar ka ce min anan zan yi fitsari.”

Takaici ya hana Haneef magana. Fita ya yi ya bar masa shagon. Ya fito ya samu Lukman yace:

“Seriously kana ƙoƙari. Ya kake ba ka fasa bakin Fu’ad ne?”

Dariya Lukman ya yi ya girgiza kai. Suna nan Fu’ad sai ga shi ya fito fuskar shi a yamutse.

“Allah ya kiyaye in ban kwashi infection ba. Ina komawa gida zance asibiti a mun check ups.”

Fu’ad ya faɗa yayin da ya samu wani dutse ya zauna zai yi alwala.

“Asibitin murtala ka kwasa ba infection ba.”

Haneef yace yana masa kallon ka-ƙure-rainin-hankali.

Wannan karon harshi Fu’ad ɗin sai da ya dara. Tare suka je suka yi asuba suka dawo. Fu’ad na son ya ɗan yi gudu ko ya yake. Nan fa shi dole sai ya cire dogon wandon shi ya bar gajere da singlet. Ba yadda Haneef bai yi ba tunda bai zo da kayan gudu ba. Ko ya je da na jikinshi ko ya haƙura ya ƙi.

“Idan baka kwashi infection a banɗakin nan ba. Za ka maƙalo a jikinka ai.”

Lukman ya faɗa. Ai ba shiri ya ɗauki kayanshi ya maida yace ma Lukman su je. Tare suka fita gudun. Sun sami wajen awa ɗaya. Dan gari ya fara wayewa. Miƙe hanya kawai suka yi. Dan ma Lukman na ɗan taɓa kwallo lokaci-lokaci. Duk da haka yana ce ma Fu’ad ya ɗan rage gudu.

Fu’ad ya ji takalminshi ya ɗan kwance. Don haka ya tsaya ya gyara. Lukman yake wa dariya da ya yi wa nisa.Tsayawa ya yi yana jiran shi. Kamardaga sama ya ji saukar wani ruwa mai danƙo-danƙo tun daga wuyanshi har bayan shi. Wani numfashi ya ja na mamaki. Lokaci ɗaya wani ɓacin rai ya maye gurbin mamakin.

“What the hell!!!……”

A fusace ya juya ya sauke idonshi kan yarinyar da ke tsaye a ƙofar gida da wata tukunya da bayanta ya gaji da yin baƙi.

Yanayin fuskarshi kawai ta kalla tace:

“Na shiga uku ni safiyya. Wallahi ban ganka ba.”

Ta faɗi tana zaro idanuwanta.

Bai san me ya kamata ya fara yi ba. Gaba ɗaya gefenshi a jiƙe yake. Ruwan koma menene har cikin sumarshi da yake bala’in ji da ita ya shiga. Har gefen fuskarshi. Da tashin hankali Lukman ya ƙaraso yana riƙe baki.

“Fu’ad……”

Ya kira da alamomi da dama. Ban haƙuri. Tsoro da jimamin abinda zai auku tun kafin faruwarshi.

Takawa Fu’ad ya soma yi zuwa inda yarinyar take. Numfashi yake ja yana fitarwa. Yana ƙoƙarin kwantar da zuciyar shi. Idanuwanshi har sun ƙara hasken nan da sukan yi idan ranshi ya kai ƙarshe wajen ɓaci. Lukman ya riƙo masa hannu yana faɗin.

“Please Fu’ad……”

Ƙwace hannun shi ya yi. Ganin da ta yi ya tunkaro ta har yana gab da ita ya sa ta tura masa tukunyar.

Da sauri ya riƙe tukunyar da ta rigada ta gama lalata masa gaban riga. Cikin gida ta kwasa da gudu.

*****

“Innaaaaaa!”

Take kira da tashin hankali. Sanin cewar Safiyya ba mai kwaramniya bace ba. Ya sa Inna fitowa da sauri don ta ga ko lafiya. Bayanta Safiyya ta laɓe tana sharar hawaye.

“Ke wai lafiyarki. Me ya koro ki?”

Inna ke tambaya tana ƙoƙarin janyo Safiyya daga bayanta.

*****

Ganin Fu’ad riƙe da tukunya a hannu yana danna kai gidan mutane yasa Lukman riƙo shi.

“Fu’ad gidan matan aure ne fa. Don Allah ka yi haƙuri ka zo mu tafi.”

Juyowa ya yi da tukunyar a hannu.

“Wallahi ko ka sakeni ko in kafta maka tukunyar nan. Like hell in yi haƙuri.”

Ganin ran Fu’ad ya gama bi ya sa Lukman sakin shi. Ya san ba’a tantamar maganar shi. Tsaf zai kafta masa wannan baƙar tukunyar.

*****

Inna na ta ƙoƙarin ɓanɓaro Safiyya daga bayanta amma ina. A banza, sake maƙalewa take tana share hawaye. Tafiya Inna ta ji da ta sa ta kallon shigowar Fu’ad riƙe da tukunya da hannuwa duka biyu. Ga rigarshi da take fara ƙal ta gama tashi daga aiki. Jikin shi daga gefe rabi a jiƙe.

Dafe ƙirji Inna ta yi.

“Na shiga uku ni Lami. Safiyya ba dai ruwan Ɗanwaken bane kika yi masa wanka dashi?”

Tukunyar Fu’ad ya ajiye a ƙasa, yana ƙare wa gidan kallo. Gidan ƙasa ne na asali ma kuwa. Ko shafe babu a ƙasan gidan. Ƙyaurayen langa-langa. Duk da tsaf yake babu datti, kwai komatsai cikin gidan.

“Don Allah ɗana ka yi haƙuri.”

Inna ta faɗi a raunane. Don kallo ɗaya za ka yi wa Fu’ad ka gane hutu da kuɗin da ke tattare da shi. Ga wata isa da gadara dake fita daga jikinshi kamar hayaƙi.

Ɗaga wa Inna hannu ya yi.

“Kar ki sake haɗa sunanki da nawa a waje ɗaya. And ba ke ki kai min laifi ba. ‘Yarki ce da take laɓe a bayanki. Haƙurin daga bakinta nake son ya fito.”

Kallon shi Inna take baki a sake. A ranta tace Safiyya ta janyo musu bala’i, wannan tsageran kuma ko daga ina ya fito oho. Da alama dai baƙo ne a garin, don ko kala kalar shi ba ta taɓa gani ba. Safiyya ta fizgo.

“Ba shi haƙuri….”

Hawayenta Safiyya ta share. Ta sauke idanuwanta cikin na Fu’ad. Ta kasa magana saboda tunda take sau ɗaya ta taɓa ganin mai irin idanuwanshi. Shi ma aikenta siyan ruwan sanyi aka yi da azumi gidan Malam Mudi ta samu suna kallo. Aka nuno wani bature har tana mamakin kalar idanuwan.

Kallon da take masa yasa shi ya ji wani iri. Lokaci ɗaya ya ji abin da bai taɓa ji ba a zuciyarshi.

Wani squeezing ya ji ta yi har numfashin shi na son tsayawa. Idanuwanshi ya lumshe don wani abu da ke fizgarshi cikin nata.

Dai dai shigowar Lukman da ya ga shirun ya yi yawa kar ace wani ɗanyen aikin Fu’ad ya yi. Domin ya san kaɗan da aikin shi.

Inna Lukman yace ma:

“Ina kwana.”

A mutunce ta amsa ta ɗora da:

“Yaro don Allah ku yi haƙuri. Wallahi Safiyya ba mai kwaramniya ba ce, na tabbatar da kuskure ne.”

Hannun Fu’ad da yake tsaye kamar an dasa shi Lukman ya kama. Tun da har Allah ya tsare bai yi wani rashin mutuncin ba.

Fu’ad kam duk wani rashin mutuncin d ya yi niyya yana jin shi yana narkewa. Sai dai koma mene ne ba a yi masa laifi a tafi a banza. Fisge hannunshi ya yi yace:

“Sai ta bani haƙuri. Wallahi sai ta ban haƙuri.”

Da sauri Safiyya ta sauke idanuwanta daga cikin nashi sakamakon jin maganar da ya yi. Wani yanayi take ji. Kamar zazzaɓi ya kamata. Muryarta a sarƙe ta tsugunna gaban Fu’ad tace:

“Ka…ka kayi haƙuri don Allah.”

Sanda ya shigo gidan ya yi niyya ta ja ma kowa. Duk sai an kulle ‘yan gidan. Sai ya yi rashin mutuncin da ba su taɓa tunani ba.

A karo na farko a rayuwarshi da ya ji ya kasa abin da ya yi niyya, ya kuma rasa dalili. Hannu ya sa ya ɗan daki goshin shi. Yana son koma mene ne ya same shi ya warke. Dan ji ya yi tsugunnawar da safiyya ta yi mishi baya so.

Har Lukman ya zaro wayar shi daga aljihu zai kira Haneef. Fu’ad ya kalle shi yace:

“Mu je Please.”

Ba musu Lukman ya ɗauki hanyar waje. Domin ji yake idan ya tsaya Fu’ad zai iya sake shawara. Suna fita ya miƙe hanyar da suka biyo da gudu ba tare da ya waigo ya ga ko Lukman na biye da shi ba.

Wata hamdala Lukman yake jerowa don har ya gama hango su ana rikici a Police Station. Shi kanshi mamakin abinda ya faru yake.

Sai kuma ya tuna yadda Fu’ad yake riƙe da tukunya. Me zai yi in ba dariya ba. Hanya ya miƙa yana sassarfa yana shan dariya.

*****

Babu ko sallama Haneef ya ji an turo ƙofar shagon. Kallo ɗaya ya yi wa yanayin Fu’ad ya miƙe da hanzari yana faɗin:

“Ya Rabb. Fu’ad me ya same ka haka?”

Cikin wani sanyin murya ya tsinci kanshi da faɗin.

“Safiyya ce ta watsa min ruwan Ɗanwake.”

“Ruwan Ɗanwake? Safiyya?”

Haneef ya tambaya yana son ya gane ma’anar maganar Fu’ad. Sake kallonshi yake daga sama zuwa ƙasa.

“Gaban rigarka kuma fa?”

Ya tambaya yana kallonshi sosai.

“Tukunyar Ɗanwaken ce ta miƙo min.”

Abin ya yi yawa. Wata irin dariya Haneef ya kwashe da ita har da hawaye. Sai da ya samu waje kan katifa ya zauna ya dafe ciki yana dariya. Lukman ne ya shigo da sallama. Kallon Fu’ad da yake tsaye ya yi cuku-cuku yake yi. Ya maida kallonshi ga Haneef da ya kasa controlling dariyar da yake.

Gefe ya zauna ya tusa tashi. Da sun fara dainawa suka sake kallon Fu’ad sai su kwashe da wata dariyar.

Tsaye yake yana kallon su. Abin ma ya wuce na takaici. Murmushi kawai ya yi ya juya musu baya yana kwance takalmin shi.

Da ƙyar Haneef ya iya controlling kanshi yace:

“Wane Police Station ‘yan gidansu suke?”

Yana miƙewa don ya san dole ya je solving rigima.

Girgiza masa kai Lukman ya yi yace:

“Ba abinda ya faru fa…….”

A nutse ya gaya masa duk yadda suka yi. Da tsananin mamaki ya kalli Fu’ad da yake tsaye daga shi sai boxers ya sa rigar da ya cire yana goge gashin kanshi yace:

“Who are you and ina ka kai min ƙanina?”

Rigar dake hannunshi ya jefa wa Haneef da ya caɓe ta yana dariya.

“But guess what? I am proud of you. Like sosai little one. Yau kai ne da haƙuri?”

Murmushin da ba ko yaushe yake yi ba ya yi wa Haneef saboda wani rawa zuciyarshi take yi har yanzu.

“In kun gama dariyar wanka nake son yi. And Lukman ka ɗauko min kaya a mota.”

Lukman da yanayin maganar Fu’ad bai dame shi ba ya ɗaga kai kawai alamar ya ji. Don in da sabo ya saba da yadda yake magana cikin gadara.

“Yan gidan nan suna da karamci. Ga ruwa nan ansa an jawo mana. Kai amfani da bokiti ɗaya ka bar wa lukman ɗaya.”

Haneef ya yi masa bayani. Wani ƙwalalo idanuwa ya yi waje. Ya taka a hankali ya tura banɗakin ya ga ruwa a bokiti. Tunda yake a rayuwarshi banda ɗazun da asuba bai ma taɓa shiga irin wannan banɗakin ba. Bai ma san ya zai fara wanka da ruwa a bokiti ba.

Juyowa ya yi ya kalli Haneef.

“Da me zan yi wankan?”

Ɗaure fuska Haneef ya yi yace:

“Wannan ruwan na bokiti. Ka watsa kawai tunda ba mu ɗauko soson mu ba. Yau zanje gida ni ma in ɗauko kaya sai in taho da shi. “

Girgiza kai Fu’ad yake yi alamar ai shi fa bai yarda ba.

“Ni Momma nake son magana da.”

Ya faɗa yana kallon Haneef da Lukman a lokaci ɗaya kamar wani yaron da aka yi wa laifi yake neman mamanshi ya gaya mata.

Ganin sun yi banza sun ƙyale shi ya sa shi shiga banɗakin yana doko ‘yar ƙofar langa-langar kamar zai karya musu ita. Haɗa idanuwa suka yi shi da lukman suka sake bushewa da dariya.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×