Skip to content
Part 33 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Kuka take sosai. Can ƙasan ranta wani abu na faɗa mata babban kuskure ta yi na kiran Farhan. Idan kuma haukan Nawaf ya haɗa da shi fa?

Ba za ta taɓa yafe wa kanta ba in wani abu ya same shi ta sanadinta. Daga wani ɓangaren kuma yana gaya mata ko me Nawaf ya yi mata bai kamata ace ta bar shi ba.

Yana tare da ita lokacin da ta ke da buƙatar taimako itama. Kafin ta ƙarasa tunanin wayarta ta katse ta.

Tana dubawa ta ga lambar Farhan, ne gabanta ya faɗi. Salati ta shiga jerowa tare da miƙewa da ƙyar.

Wata azaba ta ratsata har tsakiyar kanta saboda zafin da ta ji a hannunta. Tallabe shi ta yi sabbin hawaye na zubo mata.

Da ƙyar ta iya ɗaukar mayafinta ta ɗan yafa shi. Ta riƙe wayarta tare da hannunta da ta ke jinshi ba dai dai ba. Ta yi waje.

Kallo maigadi ya bi ta da shi. Tana fita ƙofar gida ta ga motar Farhan yana ciki a zaune. Ƙarasawa ta yi ya miƙo hannu ya buɗe mata murfin.

Tana shiga Farhan ya kalli fuskarta ya ce,

“Ya Ilahi. Nuri…”

Ya ma rasa me zai ce. Kowaye Nuri ta aura zai iya cewa rashin tausayinsu in bai zo ɗaya da babanshi ba kaɗan ya hana.

In ba rashin imani da dabbanci ba. Bai ga abinda zai sa ka ware ƙarfi kana ma mace wannan dukan ba. Duk ya fasa mata fuska.

Yadda ta runtse idanuwa ta sake dafa hannu ya sa shi saurin kai idanshi wajen. A tsorace ya ce,

“Nuri saki hannun nan mu gani.”

Ba ta yi musu ba ta saki hannu. Wani zogi da raɗaɗi yasa idanuwanta suka kawo hawaye. Girgiza kai Farhan ya yi.

Ji yake kamar a ba shi bindiga a ajiye mishi Nawaf ya yi ta harbi sai ya ga babu sauran rai a jikinshi. Ya karyata. Hanunta a karye yake.

Wani ɗaci yake ji a ranshi. Zuciyarshi na hango mishi mamanshi a kwance jini na binta. Yana hango abubuwa da dama na rayuwar shi.

Tayar da motar ya yi suka nufi Asibitin Aminu Kano. Bai tsaya ɓata lokaci ba ya nemi wani abokinshi da ke aiki a wajen. Don yasan yanayin Nuri ba za su kula su ba babu ‘Yansanda ba.

Shi ya tsaya musu aka karɓi Nuri Farhan ya samu waje ya zauna da wani irin nauyi a zuciyarshi. Abu ɗaya ne ya ke gani.

Ko garin Kano za ta haɗe sai ya raba Nuri da wannan azzalumin. Ko da zai mutu yana ƙoƙari kuwa. Daga kan mamanshi ya yi rantsuwa sai inda ƙarfin shi ya ƙare akan masu irin wannan halin.

*

Bai san inda yake ba. Tunda ya ɗauki mota kawai tuƙi yake. Har ya samu waje ya yi parking. Kanshi ya haɗe da sitiyarin motar.

Zuciyarshi ƙuna take kamar ana zuba mata garwashi. Da ace yana da taɓin hankali sai a yi wa haukan da ya sauke kan Nuri uzuri.

Runtse idanuwanshi ya yi yana hango yadda ya taka mata fuska. Wani irin ihu ya saki da ya fito daga maƙoshin shi.

Kanshi ya ɗaga ya doka kan sitiyarin motar. Yana maraba da zogin da ya ziyarce shi. Kuka ya ke saboda komai ya masa zafi.

Gaba ɗaya duniyar ta haɗe mishi. Halin da ya bar Nuri ya ke tunawa. Tayar da motar ya yi ya ja ta da ƙarfin gaske yana hawan titi.

Gida ya wuce kanshi tsaye. Yana parking ko kashe motar bai tsaya yi ba ya wuce cikin gida da gudu.

Jini ne a falon kan tiles ɗin. Bango ya dafa yana jin yadda ƙafafuwanshi ke son kasa ɗaukar shi. Bai san ya mata wannan dukan ba.

Bai san inda hankalinshi yake ba.

“Nuri!”

Ya kira da wata irin murya. Da bin bango idanuwanshi kafe kan jinin dake kwance ƙasa kamar wanda zai taso ya kama shi yake tafiya.

Kafin ya juya ya shiga ɗakin su. Ba ta ciki. Da ƙarfi ya shiga Kjwala mata kira. Babu inda bai duba ba na gidan amma ba ta nan.

Da gudu ya fito ya tambayi maigadi ko ya ga Nuri yace mishi ta fice. Dafe kai ya yi da hannayenshi biyu. Shikenan ya rasata.

Motarshi ya shiga. Ya ja ta. Yadda ya figi motar har maigadi sai da ya tsorata. Yana hanya ya lalubo wayarshi ya kira yayanshi.

Bugu ɗaya ya ɗaga. Yana wani irin kokawa da numfashin shi ya ke faɗin,

“Yaya Nuri. Nuriyya ta tafi…”

Magana yayan nashi ya ke amma ba ya jin komai cikin kunnuwanshi da kanshi sai kalma ɗaya. Sakin wayar yayi yana jin wani luuu.

Kafin ya saki motar gaba ɗaya ya dafe kanshi da ke wani juya mishi. Hakan ya sa motar ta ƙwace daga hannun shi, ji ka ke wani ƙuuuuuuuu….

Sama Nawaf ya ji motar ta yi. Yana jinta ta dawo ƙasa da shi tana jujjuyawa kafin ya daina jin sautin komai cikin kunnuwanshi.

Wani abu ya ji yana bin fuskarshi kafin wani irin duhu mai tsanani ya lulluɓe komai na duniyarshi!

*****

Suna parking ɗin motar Hassan na fitowa daga gidan ɗauke da Junior saman wuyanshi suna hira. Kallon shi Fu’ad ya ke yi.

Lokaci ɗaya ya hango Hassan ɗin da ya bari. Ya kalli wannan saurayin da ke tahowa. Ba zai iya fassara abinda ya ke ji a zuciyarshi ba saboda bai san komenene ba.

Idanuwa ya dago ya fara sauke su kan Lukman da ya ce mishi,

“Hassan ana ganinka dama.”

Sam bai kula da Fu’ad ba. ‘Yar dariya ya yi ya amsa da,

“Ina wuni. Wallahi aiki babu lokaci sosai. Yanzu ma na je gidan yaya Haneef na ce bari na biyo…”

Kasa ƙarasa maganar ya yi ganin Fu’ad. A hankali duk fara’ar da ke fuskarshi ta soma dakushewa har ya zamana babu ita ko kaɗan.

Junior ya sakko daga kan wuyanshi zuwa ƙasa. Da gudu ya ruga wajen Lukman ya riƙe hannunshi.

A daƙile Hassan ya ɗauke idanuwanshi daga kan Fu’ad ya mayar kan Lukman.

“Zan wuce. Sai anjima…”

“Hassan…”

Fu’ad ya kira. Banza ya yi ya ƙyale shi. Yana Kjarasawa inda mashin ɗinshi ya ke ajiye ya hau. Kallon Lukman Fu’ad ya yi. Ya ɗan ware mishi idanuwa da ke fassara babu ruwana. Da hanzari Fu’ad ya ƙarasa inda Hassan ya ke yana ƙoƙarin tayar da mashin ɗinshi. Hannu ya sa kan mariƙin mashin ɗin ya riƙe gam.

Gefe Hassan ya kalla don ba ya son sake ganin fuskar Fu’ad ɗin ma kwata-kwata. Zagayawa Fu’ad ya yi, muryarshi ya sauke ya ce,

“Hassan.”

Ba tare da nuna alamar sanayya ba ya ce,

“Sannun ka fa.”

Ya ji yanayin muryarshi sarai. Ya share da faɗin,

“Hassan please mana. Ka daina mun magana kamar yau ka fara ganina.”

Sai lokacin ya ware idanuwanshi kan fuskar Fu’ad ɗin. Ranshi a ɓace ya ce,

“Na sanka ne?”

Ɗan runtse idanuwa Fu’ad ya yi ya buɗe su.

“Harshenka ba zai canza matsayina a wajenka ba.”

Kallon mamaki Hassan ke mishi kafin ya ce,

“Wanne matsayi kenan?”

Ya wani ƙanƙance idanuwa. Fu’ad ya amsa shi da,

“Yayanka.”

Wata irin dariya Hassan ya yi. Kafin lokaci ɗaya ya haɗe rai. Ya nuna mishi Lukman da ke tsaye riƙe da Junior.

“Ka ga wancan shi ne yayana. Yaya Haneef. Babban yaya. Banda su banda wani yaya. Oh na manta da wanda ya yarda mu kamar ba mu taɓa haɗa alaƙa da shi ba. Now if you will excuse me ina da abin da zanyi…”

Ƙoƙarin jan mashin ɗin ya ke Fu’ad ya riƙe gam.

“Saboda me ya sa ba ka kirani ba? Ko da yake ba wannan ba. Kawai zan ji ya ka ke ne.”

Cikin idanuwa ya kalli Fu’ad. Da gaske ya ke tambayar da ya yi. Ya ga alama inya tsaya biyewa Fu’ad ranshi ƙara ɓaci zai yi.

Shekaru goma sha ɗaya sai yanzu ne zai dawo ya ce zai zama yayanshi. Gaba ɗaya cikin ‘yan gidansu burin Hassan bai wuce in ya girma ya zama irin Fu’ad ba.

Shi ne role model ɗinshi. Daga ranar da ya sa ƙafa ya wargaza duk wata alaƙa da ke tsakaninsu ya haɗa da burin hassan ɗin ciki. Mashin ɗin ya tayar ya ja shi baya. Ba tare da ya sake kallon Fu’ad ɗin ba ya ja.

Har ya kusa gate ya tsaya. Juyowa ya yi ya ga Fu’ad ɗin tsaye yana kallonshi. Da alamar roƙo a fuskar shi Hassan ɗin ya ce,

“Do me a favour. Karka je inda Hussaina take. Ba ta buƙatarka. Mu duka ba ma buƙatarka.

Ba na son ka sake hurting ɗinta. Akwai wanda suka damu da ita da yawa.”

Bai jira amsar shi ba ya ja mashin  ɗin ya fice. Hannuwan shi ya sa ya rufe fuskarshi yana sauke numfashi. Yana tsanar yadda zuciyarshi ke faɗa mishi bai duba halin da kowa zai shiga ba ya yi abinda ya yi.

Lukman ya ji ya dafa shi. Hakan ya sa ya buɗe fuskarshi ya sauke idanuwanshi da har sunyi ja saboda ɓacin rai.

“Ba na son maganar please…”

Ɗan ɗaga mishi kafaɗa kawai Lukman ya yi. Ya daina saka matasalar Fu’ad a rai.

“Ga junior…”

Kallon yaron Fu’ad ya yi ya shafa kanshi tare da yi mishi murmushin da bai san ta inda ya fito ba ma a yanayin da ya ke ji.

Lukman yace ma junior.

“Ga uncle Fu’ad…”

Dariya Junior ya yi ya ce ma Fu’ad,

“Nima ɗayan sunana Fu’ad ne.”

Da sauri Fu’ad ya ɗago ya ware ma Lukman idanuwa. Murmushi ya yi ya ɗan ɗaga mishi kai. Alamar yes sunan Junior kenan.

Wani irin abu ya ji a zuciyarshi. Bayan duk abinda ya faru. Da wani irin yanayi a muryar Fu’ad ɗin ya ce,

“Ion’ deserve duk wannan.”

Ɗan yatsa Lukman ya kai kan laɓɓanshi yana nuna ma Fu’ad ɗin ya yi shiru kawai tare da faɗin,

“Zumuncinmu na yi wa.”

Kasa magana ya yi. Kawai ya ja Junior jikinshi  ya riƙe tsam yana rasa abinda zai ce ko abinda ya kamata ya yi.

“Mu je ciki ku gaisa da Zainab.”

Kai Fu’ad ya girgiza mishi. Ba zai iya ganinta ba yanzun. Ba zai iya tuna abinda ya kamata ace ya yi ma Lukman bai mishi ba.

“Zan tafi Lukman. Za mu gaisa wani lokaci. Ka kula da su duka.”

Kai Lukman ya ɗaga mishi. Gaba ɗaya yanayin Fu’ad ɗin ya ba shi tausayi.

“Mu je in sauke ka to.”

Lukman ya faɗi yana ƙoƙarin zaro mukullanshi daga aljihu Fu’ad ya ce,

“Karka damu. Zan taka har sai na ɗan ji dai dai.”

Magana Lukman zai yi ya katse shi da,

“Please.”

Sauke numfashi Lukman ya yi. Ya ma rasa me zai ce. Fu’ad ɗin ya shafa kan Junior tare da faɗin,

“Boy me kake so?”

Da sauri Junior ya ce,

“Machine irin na Uncle Hassan.”

‘Yar dariya Fu’ad ya yi.

“Umm sai ka girma kamar Uncle Hassan then. Amman yanzun zan siyo maka wanda bai kaishi ba.”

Cike da jin daɗi Junior ya ce,

“Yeee ina so. Dady Uncle zai siya min mashin.”

Murmushi Lukman ya yi. Ya rasa me zai ce har lokacin. Fu’ad ya kalle shi ya ce,

“Za mu yi waya…”

Ya wuce yana fita daga gidan.

 *****

Lafiya ƙalau suka ci abincin dare gaba ɗaya da yaran kamar babu wata matsala.

Jabir na nazarin yanayin Jana. Zai iya karantar damuwar da ta ke ta son ɓoyewa. Kishin da ta ke son dannewa nashi.

Yau tare da shi suka raka yaran suka kwanta banda Ikram. Don ji take ita ta girma. Suna kulloma yaran ɗaki ya riƙe hannun Jana.

Sumbatar hannun ya yi. Ta yi mishi wani murmushi a kasalance tana zame hannunta. Ɗakinsu ta wuce ya bi bayanta.

Tana zaune kan gado Jabir ya samu waje dab da ita ya zauna shi ma. Wani irin dokawa zuciyarshi take. Yadda komai ya ke tafiya da sauri na ba shi mamaki.

Kamar yadda karɓar shi da Aina ta yi. Duk da ba ta yi hakan ba saida ta fara tambayarshi ko matarshi ta sani. Ya amsa ta da cewar sai da ya fara faɗa mata.

Da saƙon Janar a wajenta. Sosai Aina ta ji daɗi domin ta faɗa mishi ba ta son namijin da ba shi da adalci ko kaɗan. Sauke numfashi ya yi.

“Jana…”

Ya ja sunanta. Idanuwanta ta sauke mishi. Sai ya sake jin kwarjininta ya cika shi. A sanyaye ya ce,

“Aina ta amince da ni. Ba na son aja lokaci tunda ni ba yaro bane da zan tsaya wannan abubuwan. In anjima wata uku.”

Wani irin numfashi Jana ta ja tanajin yadda zuciyarta ta ke tafasa. Wannan karon ta kasa jure hawayen da ta ke ji. Suka zubo mata a hankali.

Jikinshi Jabir ya ja ta. Tana wani irin kuka marar sauti. Sumbatar kanta ya yi da duk wani waje inda bakinshi zai iya kaiwa yana ɗan bubbugata sigar lallashi.

“Jana ba zan taɓa wulaƙantaki ba in shaa Allah. Wallahi ina sonki. Ina sonki sosai.

Ba don ba na sonki zan ƙara aure ba. Ban san dalili ba nima……”

Jin yadda duk ya rikice ya sa ta ɗagowa ta haɗa bakinta da nashi na ɗan wani lokaci. Sannan ta kalli fuskarshi. Hannunshi ta riƙo ta dumtse cikin nata.

“Na sani Honey J. Ina sonka nima. Ba zan iya hana zuciyata kishinka ba ne. Allah ya sanya alkhairi. Ina ma Aina godiya da karɓar mijina da ta yi. Allah ya ba ni ikon tayaka sonta. Allah ya tabbatar da alkhairi ya kaimu wata ukkun.”

Lumshe idanuwa ya yi. Yana wa Allah godiya da ya ba shi mata kalar Jana. Haƙiƙa ita ɗin alherice a rayuwarshi. Riƙe ta ya yi tsam a jikishi yana kwantar da su.

Yanajin yadda ta ke kuka a hankali har ranshi. Sun jima sosai a haka. Kafin ta zame daga jikinshi. Toilet ta shiga ta ɗauro alwala. Yana kwance yana kallonta ta shimfiɗa kafet ta fara nafila.

Tun yana kallonta har bacci ya ɗauke shi. Sosai Jana take roƙon Allah har da kukanta da ya bata ƙarfin zuciya ya ba ta juriya na danne kishin da ta ke ji.

Ta kuma yi wa Jabir ɗin ma addu’a ta fatan Allah ya tabbatar mishi da alkhairi. Kishin shi bai sata baƙin ciki da auren shi ba sam.

Akan kafet ɗin ta yi bacci. Da wata irin nutsuwa ta ban mamaki!

Haƙiƙa rashin taɓewa na tare da duk wanda ya riƙi addu’a da kai kukanshi wajen Allah.

*****

“Hello… Hello Nawaf wai ba ka jina ne?”

Ibrahim ke faɗi kafin ya kula kiran ya katse. Ajiyar zuciya ya sauke ya miƙe daga kwanciyar da ya ke. Jallabiyar jikinshi ya cire ya sake kaya yana ƙwalawa Jidderh da ke kitchen kira.

Da saurinta ta ƙaraso.

“Afuwan dear. Ban ji ka ba ne…”

Ganin yana sa kaya ya sa ta faɗin,

“Ina za ka?”

Sai da ya ɓalle maɓallan shaddar shi sannan ya amsa ta da,

“Nawaf ne wallahi. Ban san me ya yi ba. Ya ce Nuriyya ta bar gidan. Kin san shi dai zai iya yin wani haukan. Ya kira ba ya jina. Kuma sai kira nake ta ƙi shiga. Zan je in duba…”

Bai ƙarasa ba wayarshi da ke kan gadon ta hau ringing. Ya ɗauka yana faɗin,

“Ina ga ma shine…”

Dubawa ya yi ya ɗan daƙuna fuska ganin sabuwar lamba ce. Ajiyewa ya yi ya ƙarasa saka links ɗin rigarshi.

Jidderh ta ce,

“Bakwai picking ba…”

“Baƙuwar lamba ce.”

Ya faɗi a taƙaice lokacin da wayarshi ta sake ɗaukar ringing.

“Bansan sau nawa zance maka ka dinga ɗaga baƙuwar lamba ba. Emergency ake gudu wallahi.

Ko wata lalurar ta daban.”

Ɗan daƙuna fuska ya sake yi alamar ya takura. Kafin wayar ta yanke. Ɗauka ya yi yana kallonta da faɗin,

“Sai na dawo.”

Ta buɗe baki za ta yi magana ringing ɗin wayar ya sake katse ta. Ta kalli Ibrahim da ya ke fassara. Ka ga me na ke ce maka ko.

Wayar ya ɗaga ya kara a kunne tare da faɗin,

“Hello…”

Daga ɗayan ɓangaren aka ce,

“Please ko waye ya zo titin da ke zoo road ta wajen masallaci. An samu mummunan hatsari ne kuma wannan ce lambar na ƙarshe a wayar mai haɗarin.

Babu rai a jikinshi. Ka zo da hanzari.”

Subuce wa wayar ta yi daga hannun Ibrahim. Wani irin jiri ya ji na ɗibarsa. Bai san sanda ya yi ƙasa ba. Yana dafa gadon.

Da sauri Jidderh ta riƙo shi a rikice take faɗin,

“Mene ne? Don Allah kai mon magana…”

Yana wani irin jan numfashi ya amsa ta da,

“Jidderh Nawaf…Nawaf… “

Girgiza shi take tana faɗin,

“Menene?  Me Nawaf ɗin ya yi?”

Wata zufa ya ke ji tana fito mishi ta ko’ina na jikinshi.

“Nawaf…ya yi accident…”

Wani irin kuka Jidderh ta saki tana riƙe baki. Waje ta samu ta zauna ita ma ko’ina na jikinta na kyarma.

Miƙewa Ibrahim ya yi. Ya ɗauki wayarshi yana fita daga ɗakin da gudu. Babansu ya fara kira yana buɗe mota yana shiga!

*****

Tunda ta tashi daga bacci ta ganta wani shiru-shiru ba ta ce komai ba.

“Nana? Lafiya?”

Da ƙyar ta iya ce mata,

“Cikina ciwo Mummy… Ciwo sosai.”

A rikice Sofi ta miƙe. Ta kama Nana ta saɓe ta a kafaɗarta. Mayafinta ma a kafaɗa ta ɗora shi ta ɗauki mukullin motarta ta fita.

Sai da ta kwantar da Nana a bayan motar sannan ta zo ta buɗe gaban ta shiga. Maigadi ta faɗa ma kowa ya zo ya ce suna asibiti.

*****

A hanya ya yi sallah. Ya samu taxi zuwa gidan Safiyya da wani irin nauyi a zuciyarshi. Sam bai ji daɗin abinda Hassan ya yi mishi ba. Mai taxi ɗin na ajiye shi ya ba shi kuɗin shi ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa. Maigadi ya ce mishi suna asibiti.

Allah ya so mai taxi ɗin bai tafi ba. Don haka ya koma ya shiga yana faɗa mishi sunan asibitin.

*****

Kasancewar ta kira Dr. Jana ta riga da tabar asibitin ya sa ta wucewa emergency da Nana. Suna zaune suna ɗan jira aka shigo da wani ya yi haɗari da gudu.

Idanuwa Nana ta kafe a kanshi. Tana kallon fuskarshi. Duk da jinin dake jiki da yanayin yadda suka wucewa da shi bai hanata gane shi ba.

Ganin yadda jikinta ke kyarma ne ya sa safiyya kamata tana ƙoƙarin ɓoye ta a jikinta don ko ita nata jikin ɓari yake.

Tureta Nana ta yi tana binsu da kallo har suka ɓace wa ganinta. Sakkowa ta yi daga inda take zaune. Safiyya ta kamata.

Kuka take. Kuka take sosai tana faɗin,

“Mummy shi ne. Wallahi shi ne…”

Kamata Safiyya ta yi tana ƙoƙarin lallashinta amma a banza. Ta san za ta iya samun matsala. Firgici na komai ko excitement in ya yi yawa yana iya ba ta matsala.

Dai dai shigowar Fu’ad wajen. Yanata hange-hange ya hango su. Da gudu ya ƙarasa. Ganin kukan da Nana ke yi yasa shi jin wani abu ya soki zuciyarshi.

Da hawaye cike idanuwan Safiyya ta ce,

“I need to calm her…”

Tsugunnawa Fu’ad ya yi. Ya tallabi fuskar Nana cikin hannunshi yana ƙoƙarin haɗa idanuwanshi da nata.

“Shhhhhhhh. Nana kalle ni.”

Kuka take sosai. Har numfashinta na wani sama-sama. Sai a lokacin ta sauke idanuwanta cikin na Fu’ad muryarta na sarƙewa ta ce,

“Shi ya taimakeni na ganoka. Shi ya biya min kuɗi…… Shi ne ya biya aka sa wasiƙa ta… Mutuwa zai yi ko?”

A rikice Fu’ad ya kalli Sofi. Don zancen Nana babu wanda ya fahimta. Dafe kai Safiyya ta yi za ta yi magana Nana ta ci gaba da jan wani irin numfashi.

Za ka rantse asthma attack ne ya kamata. Jikinshi Fu’ad ya riƙota yana ƙwalawa duk wani wanda zai saurare shi kira.

Da gudu kuwa wasu Nurses sukayo kansu. Ƙoƙarin karɓar Nana suke a hannun Fu’ad ya ƙi ba su ita. Ji yake kamar zai miƙa musu zuciyarshi.

Saida Safiyya ta ce,

“Fu’ad ka basu ita. Taimaka mata za su yi…”

Sannan ya sakar musu Nana yana binsu da gudu. Dai dai ɗakin suka yi ƙoƙarin dakatar da shi.

“She is mi’ daughter. Babu hankali a jikin duk wani wanda yake tunanin zai hanani shiga…”

Ganin da gaske Fu’ad ɗin shirin bangaje Nurse ɗin yake. Likitan da ke ciki ya ce ta bar shi ya shigo. Tsaye ya iyana dafe da haɓa yana kallonsu.

Wata allura suka yi wa Nana. Har lokacin ba ta daina kokawa da numfashinta ba. Kafin ta yi wani laƙwas.

Wani tsalle zuciyar Fu’ad ta yi kamar za ta baro ƙirjinshi. Yau ne rana ta farko a rayuwarshi da ya san meye asalin tsoro.

Da gudu ya ƙarasa kan gadon da take ya na ture likitan da ke ƙoƙarin saka wa Nana ruwa.

Tsugunnawa ya yi. Ya sa hannu ya taɓa fuskarta. Muryarshi a dakushe ya ce,

“Me kukai mata?”

Dafa shi likitan ya yi.

“Relax. Allurar bacci muka yi mata. Tana buƙatar hutu sosai.”

Yana nan tsugunne suka gama mata duk wani taimako da take buƙata a lokacin. Likitan ya ce Fu’ad ya fito daga ɗakin don ta ɗan huta.

Ya ƙi. Sai Barinshi suka yi. Hannun Nana da ba shi da komai ya kama ya sumbata. Ya kamashi ya ɗora kan fuskarshi yana rufe idanuwanshi.

Tunanin abubuwan da ya rasa na rayuwarta ne ke wani irin ci mishi zuciya. Da zai iya da ya karɓar mata wannan ciwon.

Don a yanzun ji yake ta fi mishi muhimmanci akan komai na rayuwarshi!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Akan So 32Akan So 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×