Skip to content
Part 7 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

“Kunne za ki fasa min?”

Muryarshi ta gane, gashi ɗayan hannunshi da take ji kamar wuta na mata yawo a jiki, hannunshi dake bakinta ta gartsa wa cizo tana hankaɗe shi, numfashi take zuciyarta kamar zata fito saboda dukan da take. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Ta faɗi tana kallon Haidar da ya zuba mata idanuwanshi cike da ɓacin rai. Nata idanuwan cike da hawaye, muryarta na rawa take faɗin, 

“Na shiga uku, don Allah ka rufa min asiri, karkai mun sanadin aikina. Wallahi shi kaɗai ne hanyar abincin mu. Don Allah ka ƙyale ni…”

Takowa Haidar yake tana matsawa har ya haɗe sauran wajen da ke tsakaninsu, ta maƙale jikinta da kantar kitchen ɗin kamar zata koma ciki, duk addu’ar da ta zo bakinta take karantowa. Tana roƙon Allah da ya yi mata katanga da Haidar don tana son aikinta.

Hannunshi ta ji a fuskarta yana wasa da yatsanshi akai. 

“Za ki bar gidan nan in kika yi numfashi da iskar abinda ya faru a kitchen ɗin nan kusa da Mummy balle ki yi kuskuren faɗa mata…”

“Wallahi bazan faɗa mata ba, don Allah ka ƙyale ni…”

Ta faɗi tana runtsa idanuwanta gam, hawaye masu ɗumi na zubo mata. Runtsa idanuwan da ta yi ne ya bashi damar ranƙwafawa yana sumbatarta. Ture shi ta yi tana girgiza kai, fita ya yi yana dariya ƙasan maƙoshi, zamewa ta yi ta zauna ƙasa ko’ina na jikinta na ɓari. Tunanin kar ya dawo yasa ta saurin tashi ta ƙarasa wanke tukunyar da take yi tana kuka tana goge wajen. 

Abincin ta ɗauka da kuɗin ta zuba duka a wata babbar leda tana ficewa. Tana tafiya tana goge hawaye. A bakin gate ta ga Baba Ayuba kamar yadda har Haj. A’i take kiran maigadin gidan. Ganin tana kuka yasa shi faɗin, 

“SubhanAllah Tasneem lafiya? Me akai miki?”

Kai kawai ta iya girgiza mishi ta buɗe ƙofar ta fice don bata san abinda zata faɗa mishi ba. Ko hanya bata gani sosai saboda kukan da take yi. 

“Allah ka isar min, Allah kai min katanga da Haidar.”

Take ta faɗi har ta kai ƙofar gida. Bata da wata hanyar da za su ci abinci, da ba zata koma gidan Haj. A’i ba, kuma bata jin ko da akwai wani gidan, za su yi mata irin karamcin da take mata. Ko yau ba zata manta da ita ba, tunda ta ji zuciyarta na dokawa ko ɗakin Haidar ta shiga ta san babu alkhairi a tare da shi. 

Ta jima a ƙofar gida, sai da ta tabbatar ta nutsu tukunna ta shiga, don bata son su Azrah su gane halin da take ciki. Amma sai da Hamna ta kula. 

“Kuka kika yi”

Ta faɗi da tabbaci a muryarta. Kai Tasneem ta ɗaga mata a hankali. 

“Na yi kewar Abba ne.”

“Kullum sai in ga kamar zan ga shigowarshi, sai Ummi ta dawo ta tuna min ya mutu bai bar mana komai ba tukunna…”

Hamna ta faɗi da wani yanayi mai nauyi a muryarta. Muryar Tasneem ɗin na rawa ta ce, 

“Karki bar maganganun Ummi a zuciyarki, tana faɗa ne saboda hidima ta yi mata yawa. Kuma babu mai taimaka mata shi yasa…”

Shiru Hamna ta yi, don bata son gardama kan abinda ba zata iya canzawa ba, baida amfani a wajenta. Ummi na goranta musu ne ba don hidima ta yi mata yawa ba, in akwai wanda hidima ta yi ma yawa Tasneem ce, ita take kula da su har Ummi ɗin, har kuɗi tana ba Ummi, Hamna na kula. 

Dubu biyu ta ba Ummi cikin kuɗin , aikam ta sha albarka kamar me, suna kwance a ɗaki da daddare Hamna tace mata, 

“Yaya Tariq shiru, tun ran arbai’in ɗin Abba.”

Gyara kwanciya Tasneem ta yi, magana ne bata yi, amma shirun Tariq na ci mata rai sosai. 

“Ya daɗe fiye da ko yaushe wannan karon.”

Hamna ta sake faɗi. 

“Yana lafiya. In sha Allah yana lafiya.”

Tasneem ta faɗi tana son gamsar da kanta Tariq ɗin yana lafiya, fiye da yadda take son gamsar da Hamna. 

“Allah yasa. Shirun ya yi yawa, sosai.”

“Satin nan za ku koma makaranta. Har da Sabeena in sha Allah.”

Ta faɗi tana canza maganar, tana da abubuwa da yawa a zuciyarta yau, ba sai ta ƙara da damuwar Tariq ba. Ya saba kula da kanshi, wannan karon ma ta san zai kula da kanshi kamar ko da yaushe. In abubuwa suka yi mishi sauƙi zai waiwaye su, yasan inda suke, zai zo da kanshi. 

“Ba’a ɗinka mata uniform ba.”

Azrah ta faɗi. 

“In na dawo daga aiki gobe in sha Allah, zan tambayi Haj. Sai in dawo da wuri inta barni…”

“Allah ya kaimu.”

“Amin Hamna. Kuma zan siyo muku takalman makaranta da litattafai.”

Kai Hamna ta ɗaga. Kafin can ta ce 

“Ya Tasneem?”

“Umm.”

Tasneem ta amsa mata. 

“Rayuwar mu zata yi wahala sosai da bakya nan. Kin sani ko?”

Murmushi Tasneem ta yi tana juyawa ta fuskanci Hamna don ita da Sabeena ne suka sakata tsakiya. 

“Nima tawa rayuwar ba zata yi daɗi ba inda ba kwa ciki Hamna.”

“Saida safe. Mun gode da komai. Allah ya biya ki.”

“Amin. Allah ya tashe mu lafiya.”

Shiru ta yi tana jin Hamna ta yi addu’a ta juya kwanciyarta. Su dukkansu sun yi bacci banda ita. Ko ya ta runtsa idanuwanta sai ta ga kamar Haidar zai shigo ne, zuciyarta dokawa take, sam ta kasa samun wani baccin kirki.

Ganin sai juye-juye take yasa ta tashi ta fita ta yo alwala. Tunani ba zai amfaneta da komai ba, Allah ne kawai zai iya share mata kukanta. Don haka Sallah ta fara tana wani irin kuka, bata son maraici ya kaita inda ya kai su Tariq. 

Bata so Haidar ya shiga tsakaninta da hanya ɗaya da take samu ta kula da ƙannenta. Don haka kwana ta yi tana haɗa shi da Allah da ya yi mata maganinshi. Ya kawo mata mafita, nan kan dardumar bacci ya dauketa.

***** 

Da faɗuwar gaba take zuwa gidan Haj. A’i har ta gama aikinta, hankalinta baya kwanciya sai ta ganta a gida tukunna. In akwai abinda yake bata ƙarfin gwiwar zuwa aikinta a kullum bai wuce ganin su Azrah sun koma makaranta ba. Musamman saka Sabeena, da murmushi a fuskarta take tafiya wajen aiki kullum da safe idan ta barsu suna shiryawa.

Wajen sati biyu bata sake haɗuwa da Haidar ba, sauran yaran Hajiya A’i nada kirki matuƙa kamar mahaifiyarsu. Haka za su ɗauki kuɗi su bata lokuta da dama. Kuma basu taɓa sa ta ji kamar tana ƙasa da su ba, in sun zo waje sun riga ganinta suna fara mata magana. Hamida har kaya ta bata sun fi kala goma, masu kyau da doguwar riga sabuwa. 

Yau ma kamar kullum ta zo yin aikinta, sallama kawai ta yi ba don ta sa ran wani zai amsa mata ba, ta san bacci suke yi. Don haka ta shiga shararta, sai da ta gama share falon tas, tukunna ta nufi ɗakin Haidar, ta san bacci yake, a hankali ta tura ƙofar sanin a buɗe take, shiga ta yi yana kwance a falo kan doguwar kujera inda yawanci duk nan take samunshi yana bacci, sau ɗaya ta taɓa ganinshi a kan gadonshi da safe. 

Share falon ta yi nan da nan, da yake bashi da wani datti, ta goge, ta shiga ɗakin baccin shi, kayan da ya cire ta fara tattarawa gefe, tukunna ta soma sharewa, zuciyarta ta ji tana shirin faɗowa daga ƙirjinta da ta ji an turo ƙofar, kafin ta ɗago kuma an maida an kulle. Jikinta na ɓari ta ɗago da kai tana kallonshi.

Daga shi sai singlet da ƙaramin wando a jikinshi, ya haɗe bayanshi da ƙofar yana kallonta kamar bashi da wani muhimmin abu da zai yi da ya wuce kallon nata. Sun ɗauki lokaci a haka, Tasneem na tsanar hawayen da yake taruwa cikin idanuwanta. Kayan wankin da ta ɗauke a ƙasa ta tattara tana riƙewa a ɗayan hannunta. 

“Zan wuce.”

Ta faɗi daga nan inda take tsaye, tana mamakin yadda muryarta ta fito da ƙwarin da bata ji a zuciyarta. Ganin ko motsi bai yi ba ballantana ya nuna ya ji maganar da ta yi ne yasa ta fara takawa a hankali har ta kusan gab da shi. 

“Zan wuce.”

Ta sake maimaitawa. Numfashi ya sauke yana mata wani irin kallo. 

“Ya kike so inyi? Tunda sassafe na shigo ɗakina kina ciki?”

Maƙoshinta da ta ji ya bushe yasa ta haɗiyar wani yawu kafin ta ce, 

“Shara na yi. Ka yi haƙuri.”

Raba jikinshi ya yi da ƙofar a kasalance yana matsawa gefe. Zuwa ta yi ta raɓa shi tana buɗewa ta wuce, da gudu ta ƙarasa ficewa daga falonshi, sai da ta ganta a wajen ɗakin tukunna ta tuna ta manta mopper, da gudu ta sake shiga ta ɗauka ta fito, bama ya cikin falon. 

Daga nan kitchen ta nufa, aikinta ya rage yawa tun zuwansu Hamida, su duka ukun basa son tana share musu ɗakuna. Da kansu suke yin abinsu. Garama Ahmad wani lokaci in zai fita zai ce mata ta fito da kayan wankin shi daga ɗaki. Shi ma sai ya haɗa da Allah kamar alfarma zata yi mishi ba aikinta ba. 

Bata san me za’a yi ba da safe, don haka tana gama gyara kitchen ɗin ta koma ɗaki ta kwanta itama. Bacci ne ya ɗauke ta mai ƙarfin gaske, don har sai da Haj. A’i ta zo ta tasheta tukunna.

“Ki soya dankali da ƙwai Tasneem, ki haɗa da plantain. Zan je gaisuwa ƙauye yau. Hamida zata faɗa miki ko me suke so da rana sai ki taya ta ku girka.”

“In sha Allah. Allah ya jiƙan musulmi ya kyautata namu ƙarshen.”

Ta fadi a sanyaye. Hajiya A’i ta amsa da amin tana ficewa daga kitchen ɗin. Da yake Tasneem bata da nawar aiki suyar dankali ce kawai ta ɗaukar mata lokaci. Haka ta gama aikinta tsaf sannan ma Hamida ta sauko. Da yake ta kai musu nasu dining area, kofin shayinta ta ɗauka da nata plate ɗin ta yi ɗaki. 

*****

Dambun shinkafa suka yi da rana ita da Hamida, ko tace rabin aikin ma Hamida ta yi don har da su hanta aka saka a ciki, bata taɓa ganin dambu irin haka ba. Sannan miyar yankakkun kayan miya Hamida ta yi, ta haɗa zoɓo don Tasneem na kula da Hamida bata cika shan lemukan gwangwani ko na kwalaye ba. zoɓo take dafawa ta haɗa abinta. 

Sosai dambun yai wa Tasneem daɗi. Harta ƙosa ta je gida don ta kai wa su Hamna suma su ci. Wanke-wanke take tana shan Zoɓonta da Hamida ta cika mata wani babban kofi da shi, har ma ya huce, don ta cika cikinta da dambun shinkafar. Fitsarin da ya kamata yasa ta tsame hannunta daga ruwan wanke-wanken zuwa ɗaki. 

Gidan ya yi shiru, ta san daga ita sai Hamida, su Ahmad sun yi ficewarsu. Hamida kuma na ɗakinta. Sa’adda ta dawo kitchen ɗin tana ɗaukar kofin zoɓon gabanta ya yi wani mummunan faɗuwa. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…” 

Ta faɗi da sauri tana dafa kantar kitchen ɗin ko zuciyarta zata rage dukan da take yi a ƙirjinta da sauri-sauri. Zoɓon ta ɗaga tana shanyewa duka ta ajiye kofin, jin zuciyarta bata daina dokawa ba yasa ta ci gaba da wanke-wanken da take yi. Sai dai kafin ta ƙarasa jikinta ya mata nauyi. Da ƙyar take motsa duk wata gaɓa ta jikinta. 

Hakan ba ƙaramin tsoro ya bata ba, ba kuma ta jin alamar rashin lafiya, kawai jikinta ne ya yi mugun nauyi, idanuwanta da kyar take ɗaga su. Ko goge wajen bata yi ba. Tana dafa bango ta kai ɗaki da ƙyar, tana shiga kafin ta ƙarasa wajen gado ƙafafuwanta sun mata sanyi, babu shiri ta zauna a ƙasa, tana jin ɗakin na mata wani iri. 

Nan kan kafet ta kwanta ta rufe idanuwanta, kafin ta ji kamar hakan jikinta yakeso dama. Can wata duniya daban ta ji kamar an shigo ɗakin, a duniyar kuma ta ji kamar an ɗagata cak daga ƙasa zuwa kan gado. Sai dai bata gama fahimtar mafarki take ko me ba, wani irin duhu ya mamaye mata duniyar gaba ɗaya. 

*****

Saloon Hamida zata je, don haka ta fito, tana son ce wa Tasneem ta tafi gida kawai. Tasan su Ahmad abincin ranar ne zai zame musu na dare. In ma ba za su ci ba sun fita su dukansu su ci wani abun a waje. Amma kitso take son zuwa ita kam. 

Bata yi tunanin ƙwanƙwasawa ba, sallama kawai ta yi tana turawa. Wayar da take hannunta da mukullin mota suka suɓuce suna faɗuwa.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Hamida ta faɗi hankalinta a tashe, idanuwanta kamar zasu fito ƙasa, ga wani irin juyawa da cikinta yake saboda tashin hankalin ganin Haidar na ɗaura belt a ƙugunshi, ga Tasneem kwance cikin mummunan yanayi, da alama bata ma san duniyar da take ba. 

“Yaya… Inalillahi wa inna ilaihi raji’un, Yaya me kayi? Me kai mata? Na shiga uku Yaya… Ka kasheta ko?”

Hamida take faɗi tana ƙarasawa kan gadon gefen Tasneem wani irin kuka na ƙwace mata, hannu takai ta fara gyara mata zaninta tukunna ta soma jijjigata cikin tashin hankali.  

“Tasneem…Tasneem!”

Take faɗi amma ko ɗan yatsa Tasneem bata motsa ba ballantana ta san inda kanta yake. Juyowa Hamida ta yi da idanuwanta da har sun yi ja saboda kuka da tashin hankali tana kallon Haidar dake tsaye bai motsa daga inda yake ba. Sosai take kallonshi tana neman kusancin da take dashi na ‘yan uwantaka amma ta rasa a wannan lokacin. 

Miƙewa ta yi tana ƙarasawa inda yake, mari ta ɗauke shi da shi tana cakumar wuyan rigarshi. Jijjigashi take. 

“Kace min baka yi mata komai ba Yaya. Kace min baka ɓata mata rayuwa ba. Yaya kace baka cuceta ka cucemu gaba ɗaya ba… Wallahi na tsaneka…”

Hannuwan Hamida ya kama yana ɓanɓarewa daga jikinshi. Babu alamar da na sani ko nadamar abinda ya aikata ya ce x

“Kina cika min kunne da ihu, babu abinda zata tuna inta tashi…”

Cike da rashin yarda Hamida ke kallonshi, ta kasa yarda da abinda kunnenta yake jiye mata, hannu ta ɗaga bata ma san abinda zata yi mishi ba, ya riƙe yana ɗauketa da marin da saida ta ga haske na gilma mata, da baya riƙe da ita sai ta faɗi, bata gama wartsakewa ba ya sake ɗauketa da wani marin, wannan karon tana jin iska ta daina zuwa mata a ɓangaren fuskarta. Runtsa idanuwanta take tana buɗesu da sauri da sauri don ta ɗauka ɗayan idon ma ya faɗi saboda azabar da take ji. 

“Kin mantani ko? Don ina zama waje ɗaya da ku yasa kike neman rainani. Ni sa’anki ne da zaki ɗaga min hannu Hamida?”

Kai take girgiza mishi jikinta ko ina na kyarma, dama can suna tsoron Haidar, ballantana yanzun da ta ga asalin rashin imanin shi. Bawai labari aka bata ba. Abinda take gani cikin idanuwanshi ya gama tsoratata. 

“In Hajiya ta ji maganar nan saina danne kanki da pillow kina bacci, kin jini ko?”

Ya faɗi yana girgizata. In hankalinta ya yi dubu ya gama tashi, tsoronshi take ji har cikin ƙasusuwan jikinta. Ta tabbata zai iya ɗin, kasheta zai yi in ta faɗa, kai kawai take iya ɗaga mishi. Sai da ya ƙara mata wani marin tukunna ya saketa yana ficewa yabarta nan durƙushe. Kuka take kamar ranta zai fita, ko’ina na jikinta kyarma yake. 

So take idan mugun mafarki ne take yi haka ta farka, ko zata samu ta yi sadaka Allah ya nisanta mata sharrin da ke ciki. Amma ta ƙi farkawa. Ta kuma kasa fita daga ɗakin. Tsoron fita daga ɗakin take ji ko Haidar na waje yana jiranta. Har ruwa ta shiga banɗaki ta ɗibo ta shafa wa Tasneem amma bata tashi ba. 

Sai da ta kula tana numfashi a hankali tukunna ta tabbatar Haidar bai aikata kisan kai ba. Nan ta zauna da Tasneem ɗin, ko Sallar Asr ta kasa tashi ta yi tana jin aka kira, amma ta kasa tashi. Tasneem bata motsa ba sai wajen ƙarfe shida saura. Kanta take jin ya mata wani dum. 

Kafin ta motsa jikinta ta ji wani irin canji har cikin zuciyarta. Wayam take jin cikin kanta, bata iya tuna komai banda barin kitchen zuwa ɗaki, amma ba sai wani ya faɗa mata wani abu ya faru da ita ba. Sosai ta buɗe idanuwanta jin kamar ana kuka. Juyawa ta yi tana kallon Hamida, ganinta a gefenta yasa ta tashi da zaune da sauri, kanta take kallo da yanayin jikinta. 

Wani bangare ne na zuciyarta ta ji yana bushewa a hankali. Ganin kukan Hamida daya tsananta yasa Tasneem faɗin, 

“Wani abu ya same ni ko Hamida?”

Hamida bata iya cewa komai ba, sai kukanta da ya tsananta. 

“Haidar ya yi min wani abu ko?”

Tasneem ta sake fadi muryarta babu alamar komai. Hamida na ɗaga mata kai ta ji ɓangaren ya ƙarasa bushewa a zuciyarta. Hawaye ko alamunshi bata ji ba. Kawai duniyar ce ta yi mata wayam. Bata sake jin rayuwa ta zo mata ƙarshe ba sai da ta sakko daga kan gadon ta miƙe tsaye tukunna. Zaninta ta kwance daga baya tana gyara ɗaurinshi. Amma ji take kamar bata ɗaura ba ma. 

“Tasneem…”

Hamida ta kira cikin kuka. Bata ko juyo ba ballantana, hanyar ƙofa ta nufa ta buɗe tana ficewa. Bata san ƙafafuwanta na ɗaukarta zuwa ɓangaren Haidar ba sai da ta ganta cikin ɗakin shi. Yana zaune a falo yana kallo. Ganinta tsaye yasa shi maida hankalinshi kanta. Cikin idanuwa take kallonshi, tana barin zuciyarta ɗaukar hotunanshi da wani irin ƙuna. 

“Ka raba ni da duk wani mutunci da mace take tinƙaho da shi. Nasan kuma bani bace ta farko, ba kuma lallai in zama ta ƙarshe ba. Amma Allah ba zai barka ba Haidar.”

Tana ƙarasawa ta juya tana ja mishi ƙofar. A tsakiyar falon ta ci karo da Haj. A’i. Da mamaki Hajiya take kallonta. 

“Tasneem yau kin yi yamma…”

Kallonta Tasneem ta yi, yanayin da ke fuskarta yasa Haj. A’i faɗin 

“Tasneem? Lafiya?”

“Zan fita daga gidan nan saboda banda ƙarfin faɗa da ku, ko ina da shi babu wani ɗan Adam da zai iya hukuntaku yadda nake so. Allah ne kawai zai hukunta ku, zan bar komai a hannunshi…”

“Tasneem me…”

Haj. A’i ta fara Tasneem na katseta ta hanyar ɗaga mata hannu. 

“Ki daina min magana kamar ba ki san laifukan da Haidar yake aikatawa kina kauda kaiba. Kirkin ki ba zai wanke yadda kike kauda kai daga ɓarnar da yake yi ba. Karki ban haƙuri, karkiyi ƙoƙarin bina ko nemo ni.”

Tasneem ta ƙarasa tana raɓa Haj. A’i da ta kasa cewa komai ta fice daga ɗakin. Harta fita daga gidan komai wayam take jin shi a rayuwarta. Duk da akwai kuɗi a jikinta da ƙafafuwanta ta kai gida ba tare da ta ji gajiyar komai ba. Azrah ta amsa mata sallamar da ta yi. 

“Ya Tasneem hankalinmu ya tashi. Baki dawo da wuri ba yau…”

Fuskarta Hamna take kallo, yanayin ta kawai ya nuna ma Hamna akwai wani abu daya faru da ya girmi tunaninsu duka. 

“Me ya faru?”

Hamna ta tambayeta muryarta can ƙasan maƙoshi. Kallon su Tasneem ta yi su dukkansu, tana jin yadda babu abinda ya rage mata a rayuwarta face su, Haidar ya kunna wa darajarta wuta ba tare da ta san meya faru ba, sai tokar ta farka ta gani. 

“Na bar aiki na.”

Shiru suka ɗan yi na wani lokaci kafin Hamna ta ce, 

“Allah ya musanya miki da alkhairi”

“Wani abin ne ya faru?”

Azrah ta tambaya ita kuma tanajin babu daɗi ko don yanayin Tasneem ɗin da take gani. 

“Ko ba abinda ya faru tunda ta ce ta bari akwai dalili.”

Hamna ta faɗi a daƙile, jinjina kai Azrah ta yi. 

“Hakane. Allah ya musanya mata da alkhairi.”

“Amin.”

Hamna ta faɗi, sai dai Tasneem bata ce musu komai ba. Wajen ruwa ta nufa ta ɗauki babban bokiti ta shiga banɗaki. Wanka ta fara yi don ta tsarkake dauɗar da take ji manne da jikinta duk da bata san lokacin da ta manne mata ba. Tukunna ta sa sabulu ta sake wanke jikinta, bata wani dirje ba, don hannuwan Haidar ba a wajen fatarta suke ba, sam bata jin su, cikin tsokarta take jinsu, ba kuma zata iya ɓare fatar saman ta wanke ba. 

Don haka ta barshi kawai. Wankan da za’a yi wa gawarta ne kawai zai wanke mata abinda take ji. Da ta fito alwala ta sake yi, suma su Hamna haka sannan ta shiga ɗaki. Sallar Asr ta fara yi tukunna ta mayar da Maghrib. Da kanta ta ɗauki kuɗi ta fita ta siyo musu biredi da shayi ta dawo. Tana sha ne kawai don ta san ko kowa yasha in har ita bata sha ba Hamna ba zata saka a cikinta ba. 

A ɗaki suka yi sallar isha’i suka kwanta don ko hira basa yi. Suna jin sallamar Ummi ta dawo gidan. Sai da zuciyar Tasneem ta sake dagulewa da jin muryar Ummi. 

“Tasneem!”

Ta kira jin basu fito ba. Tashi Tasneem ta yi tana fita tsakar gidan. Ummi na washe baki take faɗin, 

“Yau me aka samo mana gidan Hajiya?”

“Ba abinda na samo.”

Tasneem ta faɗi muryarta a dake. Sai yanzun take auna abubuwan da rashin aikinta zai janyo. Tun ɗazun wayam take ji a duka duniyar, dole ta yi tunanin wani abu kafin Ummi ta hargitsa rayuwar su Azrah, don ita bata jin akwai wani abu da zai sake hargitsata banda wanda ya faru da ita yau. 

“To. Garin yaya kuma? Kin san yunwar da nake ji kuwa?”

Kallonta Tasneem ta yi. 

“Nabar aikin ne duka Ummi.”

Cike da mamaki Ummi take kallonta.

“Wanne irin kin bar aiki? Akan wanne dalili? Korarki suka yi? Me kikai musu Tasneem? Duk abinda matar nan take miki sai da kika nuna mata baƙin hali irin na ubanki.”

Wani abune ya taso tun daga ɗan yatsan Tasneem na ƙafa zuwa ko’ina na jikinta kafin ya samu wajen zama a zuciyarta. 

“Abba ya samu shaida mai kyau a wajen mutanen da basu da kusanci da shi, ban san me yasa ke kaɗai kike ganin baƙin halinshi ba Ummi, ban san me yasa ba. Ya bar miki duniyarma bai huta ba…babu abinda na yi musu, aikin ne kawai na bari, dama nice na ce zan yi daga farko yanzun kuma na ajiye. Shi ne abinda ya faru…”

Tasneem ta tsinci kanta da faɗi, mamaki Ummi take don ko da wasa Tasneem bata taɓa mayar mata da magana ba irin yau. Kuma ranta ya ɓaci sosai. 

“Rashin kunya za ki yi min Tasneem? Wallahi ajiye aikinki ku zai shafa. Don banda yacda zan yi in ciyar da ku, sai ki san yadda za ku yi don bawai…”

Tasneem bata bari Ummi ta ƙarasa maganar ba ta juya ta shige ɗaki tana rufo ƙofar duk da ba kullewa suke yi ba. Ta yi hakanne ko zai rufe mata jin Ummi, ƙrjinta take jin kamar an kunna wuta a ciki. Jingina jikinta ta yi da ƙofar tana zamewa ƙasa. 

“Me yasa Ummi ba zata daina mana haka bane? Dama ai ba ita take ciyar da mu ba. Me yasa zata dinga miki faɗa bayan baki mata komai ba?”

Hamna take maganar muryarta na rawa da alama kuka take.

“Hamna…”

Tasneem ta faɗi, don ko alamar hawaye bata ji ba. Ƙirjinta ne kawai yake ciwo, sai kuma duniyar da take jin ta haɗe mata waje ɗaya babu inda zata shaƙi numfashi na daban. 

“Dama ita ta rasu ba Abba ba.”

“Hamna mana!”

Tasneem ta faɗi ƙirjinta na ƙara zafi da maganganun Hamna ɗin. Cikin kuka Azrah ta ce, 

“Ba ita kaɗai take wannan tunanin ba. Nima ina yi wallahi. Na san ba kyau amma ina yi lokuta da dama.”

“Oh Allah na.”

Shi ne abinda Tasneem ta iya faɗa kawai tana miƙa musu hannuwanta. Tasowa suka yi daga inda suke kowannen su na kama hannuwanta ɗai-ɗai suka riƙe suna wani irin kuka. Kwantar da su ta yi a jikinta. Yadda rayuwarta ta yi wayam ba zata bari tasu ta yi haka ba, zata karesu daga komai na rayuwa dai-dai iyawarta. Ko me zai taɓa su zata shiga tsakani ko da Ummi ce da kanta kuwa. 

Anan jikinta suka yi bacci, ko runtsawa Tasneem bata samu yi ba, saboda zafin da ƙirjinta yake yi. Kan kunnenta aka kira Sallah tukunna ta tashi su Azrah. Da ƙyar ta iya yin alwala don ko tafiya da ƙyar take yinta. Ciwuka take ji a ko’ina na jikinta. Azkar ɗin safe ma bata yi ba, ta koma kan katifa ta kwanta ko zata samu bacci ya ɗauke ta, ƙila kanta da yake sarawa ya yi mata sauƙi.

Bayan Wata Shida  

Kallon kanta take a ƙaramin mudubin da ke riƙe a hannunta. Zuciyarta ta kasa gane taswirar da ke cikin mudubin, daga kan janbakin da ke laɓɓanta, zuwa komai na fuskarta ya canza. Daga ranar da Haidar ya cinna wa darajarta wuta ta san wani abu ya canza tattare da ita. 

Halin da suka shiga na baƙar yunwa watanni kaɗan bayan wannan ya sake busar mata da wani ɓangare na zuciyarta. Bata sake jin duniyar ta mata wayam ba sai da Ummi ta fara zaman gida, tana aiken su Azrah, samari na soma musu zarya a ƙofar gida. Ta san abinda ya faru da ita zai faru da su Azrah Ummi ba zata taɓa damuwa ba in dai za su kawo mata abin duniya. 

Bata jin akwai wani abu daya rage mata banda kula da su Azrah, banda tabbatar da abinda ya faru da ita bai faru dasu ba, ganin sun samu duk wani abu da Abba yake da buri su samu a rayuwar su. Da taimakon Ummi da ta bata zaɓin ko ita ta dinga tsayawa da duk wasu samari da za su aiko kiranta ko kuma ta bar su Azrah, ciki kuwa harda Alh. Madu yasa ta fahimtar abubuwa da dama. 

Sosai take kallon kanta a mudubin tana jin dauɗar da duk yadda ta sama jikinta ruwa baya taɓa barinta yanzun. Tana kuma jin da duk rana dauɗar na ƙara mata nauyi, zuciyarta na ƙara bushewa da duk fita siyayyar da za su yi da Alh. Madu yadda hannuwanshi ke yawo a jikinta. Bata ƙoƙarin hanashi, zama take kamar gunki, sai abin ya isheta ne zata ce mishi zata shiga gida. 

Bakinshi a washe zai bata kuɗi masu yawa, Abbanta ne kawai yake sakawa bata wa maza kuɗin goro, ta san a cikin tarin dubban lalatattu ba’a rasa ko mutum ɗaya mai nagarta. Sai dai duk wanda zai zo wajenta da burin hannunshi ya kai jikinta ne. Dauɗarsu da yadda ta bar su suna shafa mata ya canzata ta fanni da dama. 

Ajiye mudubin ta yi, Alh. Madu take jira yauma don ya ce zaizo su fita siyayya. Bakin Ummi a washe yake yanzun kullum, ko faɗa ba koyaushe take yi ba, in ka ji ta ita da Hamna ne, don basa zama inuwa ɗaya.

“Fita za ki yi?”

Hamna ta faɗi da wani yanayi a muryarta da yasa zuciyar Tasneem ɗaukar zafi. In ba su ba, babu abinda yake taɓa mata zuciya yanzun. Su kaɗai take kallo ta tabbatar tana jin wani yanayi yanzun. Mudubin ta ajiye tana juyawa, kallonta Hamna take kamar bata ganeta ba. Kamar tana nemar yayarta wadda a da take da tabbacin tana wani waje a cikin Tasneem ɗin amma batasan yadda zata yi ta fito da ita ba. 

“Siyayya kawai za mu yi Hamna. Ba daɗewa zan yi ba.”

Girgiza kai Hamna ta yi. 

“Bana so, kin canza, kuma bana so.”

Hannu Tasneem tasa a ƙirjinta inda yake mata zafi tana ɗan dannawa ko zata ji sauƙi. 

“Hakan ne kaɗai zai rufe bakin Ummi, kuma kin ga muna samu mu ci abinci, kuma kuna zuwa makaranta.”

“Alh. Madu ne kawai da, yanzun wasu ne daban, ba shi kaɗai bane kina fita tare da wasu daban. Ki auri ɗaya a ciki mana…”

Hamna ta ƙarasa kamar zata yi kuka. Murmushin takaici Tasneem ta yi, cikinsu babu wanda ya taɓa mata maganar aure ko da wasa. Ba aurenta suke son yi ba ta sani, ba shi bane a gabansu kamar yadda ita ma yanzun ba shi bane damuwarta. 

“In lokaci ya yi Hamna…ki yarda da ni, zan iya kula da kaina da ku duka.”

Hawayen da Hamna take riƙewa ne ya siraro kan kuncinta. Hannu ta sa ta goge shi, muryarta can ƙasa ta ce, 

“Karkiyi abinda Abba ba zai so ba, karki ɓoye bayan kula damu…”

Tana ƙarasa maganar ta fice daga ɗakin ta koma tsakar gida inda su Azrah suke zaune ita da Sabeena. Tana barin Tasneem da nauyin maganganun da ta yaɓa mata. Suna samun waje suka yi mata zaune a gefen dauɗar da take tare da ita. Sai dai tana jin lokaci ya ƙure mata yanzun. Ana kiran Maghrib ta tashi ta yi Sallah don ta ðauro alwala da ta yi wanka dama.

***** 

Jikinta take ji a sanyaye tun safe, agogon hannunta da ba zata tuna sunan saurayin daya siya ba ta janyo ta duba lokaci, koyaushe su Azrah za su iya dawowa daga islamiyya yanzun. Wani irin zafi ake gashi babu wuta ko da fankar ɗakinsu ba wani yi take ba sosai saboda tsufa amma takan rage wani abun. 

Don haka Tasneem ta tashi tana fitowa tsakar gida ko zata ɗan ji sauƙi-sauƙi. Ko zama bata yi ba Hamna ta shigo da gudu tana mayar da numfashi kamar zata shiɗe da alama gudun da ta sha ne da kuma Sabeena da take goye da ita. Sauketa ta yi tana ƙoƙarin dai-daita numfashinta. 

“Lafiya?” 

Tasneem ta tambaya duk da kallo ɗaya taima Hamna ɗin ta san ba lafiyarta ba.

“A… Azrah…”

Hamna ta faɗi da ƙyar hawaye na zubar mata. Sai lokacin Tasneem take kallon Hijabin Hamna ɗin da jini yake a jiki da gefen wandon ta, haka ma jikin Sabeena, girgiza kai take a karona farko bayan watanni da dama da ta ji idanuwanta sun ciko da hawaye, ta ɗauka wannan ɓangaren nata ya riga da ya mutu. 

“Azrah…”

Hamna ta sake faɗa tana kasa dai-daita hankalinta waje ɗaya taima Tasneem ɗin bayani. Bata jira bayaninta ba, takalman da ta ji a ƙofar daki su ta zura wa ƙafafuwanta ɗayan ma ba nata bane na Ummi ne, kuma ba ƙafar ba, amma bata ji ba. Cikin wani irin tashin hankali ta ture Hamna tana fita da gudu ko Hijab babu.

“Yaya Tasneem!”

Hamna ta kira da karfi, amma ko waiwayowa Tasneem bata yi ba, kiran ne ya fito da Ummi daga ɗaki tana kallon Hamna data zame a ƙasa tana wani irin kuka. 

“Hamna? Lafiya? Me ya faru?”

Ɗago kai Hamna ta yi, da rarrafe ta samu ta fara tafiya kafin ta dafa ƙasa ta miƙe tana faɗaw jikin Ummi da ta riƙeta a tsorace, don ko rasuwar Abbansu bata ga rikicewar Hamna haka ba. 

“Innalillahi… Hamna me ya faru ne? Menene?”

Ummi take tambaya. Kuka Hamna take tana riƙeta don tunda take a rayuwarta bata taba sanin asalin tsoro irin na yau ba. Da ƙyar tana wani jan numfashi take faɗin, 

“Az…Azrah… Ummi Azrah.. Mota…”

A tsorace Ummi ta ware idanuwanta kan Hamna. 

“Me ya sami Azrah ɗin? Tana ina?”

“Mota ta bugeta… Ta mutu Ummi.. Jini…Jini ko’ina…”

Hamna ta ƙarasa da ƙyar, tureta Ummi ta yi tana rugawa ɗaki da sauri, hijab ta ɗauko ta fito, takalmanta ta zo sawa taga sai wari ɗaya. Haka ta haɗa nata da na Tasneem ta saka, ta kama hannun Hamna da na Sabeena suna ficewa. Gidan ma janshi ta yi, har can ƙofar gaba ɗaya bata kulle ba, janta kawai ta yi. Rabonta da karatun Qur’ani mai yawan wanda take yi yanzun a hanya harta manta. Don ko a sallolinta surori marasa yawa take yi. 

Ba kuma zata ce ga abinda take karantawa ba. Ba son su Azrah bane bata yi, bata san yadda zata nuna ba, ba kuma ta san son ya girma haka ba sai yanzun. Rasa Abbansu ba komai bane ba, dama soyayyarshi ba wai girma ta yi a zuciyarta ba. Amma tunanin rasa Azrah, tunanin rasata kawai yasa hawaye na dishe ganinta. Bata taɓa sanin Islamiyyarsu na da nisa ba sai yau. Don tafiya take amma ta ga sun kasa zuwa, ba don su Hamna da take riƙe da su gam ba da ta faɗi, don ko hanya bata gani sosai saboda kukan da take yi. 

*****

Ta san mutane na kallonta, amma bata damu ba, ƙafafuwanta kawai take so ya kaita titin da zai tsallaka da ita Islamiyyar su Azrah. Mutanen da ta gani a gefen titin yasa zuciyarta ƙara gudu wajen dokawar da take yi . Ture mutane kawai take tana son ƙarasawa.

“Baiwar Allah lafiya?”

Wani mutum ya tambaya. Ko kallonshi Tasneem bata yi ba, wanda yake gabanta kawai tasa hannu tana fisgo rigarshi ta ture shi gefe ɗaya. Ganin yadda take ture mutane yasa su tabbatar da tana da alaƙa da yarinyar da ke kwance, don haka suka matsa mata.

“Wai ya ma akai mai motar nan ya gudu? Wanne irin rashin imani ne wannan?”

Tasneem ta ji muryar wani mutum na faɗi, sai dai ba ita bace matsalarta. Idanuwanta na kafe kan Azrah da ko motsi bata yi, hijabinta ko ina jini ne. Ƙasa ta zauna ba tare da ta kula ba ma, ta kamo Azrah ta rungume a jikinta ta sa ɗayan hannunta tare da shafa fuskar Azrah ɗin. 

“Azrah… Azrah… Azrah…”

Tasneem take faɗi a tsorace, ko motsi bata yi ba, hawaye ke zuba daga idanuwan Tasneem kamar an mata gorinsu, bata yi ƙoƙarin gogewa ba, fuskar Azrah kawai take shafawa ko zata samu taga ta motsa. 

“Ba za ki barni ba kema… Kina jina ko? Tashi za ki yi Azrah… Wallahi ku kaɗai ne dalilin da nake ƙoƙarin rayuwa kullum… Karki barni a wannan lokacin… Azrah ki tashi.”

Tasneem ke faɗi tana wani irin kuka. Dai-dai lokacin da Ummi ta ƙaraso, dafa Tasneem ɗin ta yi da ta juyo. 

“Ummi ta ƙi tashi wallahi… Taƙi tashi…”

Tasneem take faɗi tana riƙo hannun Ummi dam, don yau buƙatar lallashi take da ta jima bata yi ba. Bata jin zuciyarta zata iya ɗaukar rashin Azrah. 

“A kaita asibiti mana.”

Wani mutum ya faɗi, hakan ya kawo tunanin su Ummi zuwa asibiti. Ummi da kanta ta sunkuya ta ɗauki Azrah tana saɓata a kafaɗarta. Adai-daita sahu aka taro musu suka shiga zuwa ƙaramin asibitin da ke nan unguwar, sai dai kallo ɗaya suka yi wa Azrah suka ce su tafi babban asibiti. 

Aikuwa adai-daitar suka sake shiga zuwa Aminu Kano, ba don wani mutum daya bisu ba, da basu san yadda za su yi ba. Don ana cewa haɗari ne suka ce ba za su karɓeta ba sai da ‘yan sanda. Shi ya barsu ya koma da mai adai-daita ya ɗauko Ɗansanda aka shigar da report. Hatta kuɗin shi ya biya tukunna ya yi musu fatan samun sauƙi ya tafi. 

Sai lokacin aka shiga da Azrah don a dubata. Kowa ya daina kuka banda Hamna. Har lokacin kuka take har zazzaɓi ya fara saukar mata. Kafin wani likita ya fito ya kira Ummi zuwa office ɗinshi. Su duka suka bita ya dakatar da su bakin ƙofa. 

“Ita kaɗai nake son gani. Ku jirata anan.”

“Ko me zaka faɗa mata in ya shafi Azrah ya shafemu duka. In ka ga ban shigo na ji me zaka ce ba bana numfashi ne malam.”

Hamna ta faɗi muryarta a dakushe. Tasneem ma da idanuwanta take faɗa mishi babu abinda zai hana su jin ko me zai faɗa. Numfashi ya sauke don bai ga ma amfanin shiga office ɗin ba. Kafin ya kalli Ummi da ta ɗan ɗaga mishi kai alamar zai iya faɗan koma menene. 

“Ciwukan da ke wajen jikinta basu da wani haɗari amma tana zubda jini ta ciki, da alama akwai ciwo a cikinta. Dole sai mun mata aiki, kafin mu taɓa ta muna buƙatar dubu tamanin…”

Ware idanuwa Ummi ta yi tana jin hanjinta ya ɗaure waje ɗaya. Don ko dubu biyar bata ajiye ba bata kuma san inda zata samo ba balle har dubu tamanin. Kallonshi Tasneem ta yi zuciyarta na yin shiru a ƙirjinta. 

“Zan kawo…ku dubata wallahi zan kawo.”

Daga shi har Ummi da mamaki suke kallon Tasneem ɗin. 

“Ki zauna da su Ummi, zan kawo kuɗin…”

Tasneem ta sake faɗi bata jira sun ce komai ba ta wuce da gudu tana fita daga asibitin. Mai mashin ta samu daga nan zuwa gida kai tsaye don bata son ɓata lokaci. Cikin gida ta shiga ta ɗauko mishi kuɗinshi ta saka wa jikinta Hijab. Sannan ta fito, tana tafiya tanajin duniyar sama-sama.

Gidan Alh. Madu ta tsinci kanta da yake nan cikin unguwarsu. Ta ko yi sa’a ya fito yana shirin shiga mota ganinta yasa shi washe baki. 

“Tasneem?”

Ya faɗi cike da shakku da mamakin ganinta. Muryarya can ƙasan maƙoshi ta ce, 

“Dubu tamanin nake so.”

Ware idanuwa Alh. Madu yayi da faɗin, 

“Toh! Dubu tamanin?!”

Kai ta ɗaga mishi a hankali. 

“Tasneem kuɗin da yawa”

“Na sani shi yasa na zo.”

Tace tana kallon shi. Wani murmushi ya yi mata daya sa ta jin abincin da ta ci na shirin fitowa daga cikinta. 

“Mu shiga daga ciki in duba in gani. Amma dubu tamanin…”

Ya faɗi yana ƙara jinjina maganar. Bin bayanshi Tasneem ta yi suna komawa cikin gidan. Tana jin ana kiran Sallar Maghrib, tana kuma jin idanuwan maigadinshi na binta da kallon ƙyamata. Bashi bane matsalarta a yanzun, yadda zuciyarta ta yi shiru a ƙirjinta ne damuwarta, ta san imaninta ne ta yi nisa da shi sosai, shaiɗan ne yake son mamaye hasken daya yi saura a rayuwarta, ba kuma ta da ƙarfin faɗa da shi. 

Haka ta ci gaba da bin shi har cikin gida, har cikin wani ɗaki, da duk takun da ta yi da yadda take jin duhun na sake mamaye ta, har sai da ta shiga ciki ya mayar da ƙofar ya rufe da sauran hasken da ya rage mata.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 6Alkalamin Kaddara 8  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.