Skip to content
Part 2 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

“Kai fa ka ce za ka barni, ko bikin Yaya Rafiq banje ba… Haba don Allah.”

Zafira ta ƙarasa maganar tana jin hawayen baƙin ciki na cika mata idanuwa. Musamman yadda Omeed ɗin ke ɗaura agogo a hannun shi kamar bai tarwatsa mata farin cikin da ta yi wata ɗaya da kwanaki tana tarawa ba.

“Yanzun kuma na fasa, ko ban isa ba?”

Ya buƙata ba tare da ya juyo ba, asali ma hular shi ya ɗauka yana karyawa. Sannan ya zo ta gaban Zafira da ke zaune a bakin tanƙamemen gadon ɗakin ya ɗauki daya daga cikin turarukan da ya fiddo ya ajiye akai. Hawayen da take tarbewa ne suka zubo.

“Amman in kai haka ba ka yi min adalci ba wallahi… Kai ka ce za ka bar ni, kai ka faɗa.”

Sai a lokacin ya juya ya kalleta, hawayenta na ɓata mishi rai, don in akwai abinda ya tsana bai wuce hawayen rashin dalili ba, in yana son ganin su zai ba ta dalili mai ƙarfi da za ta zauna tana mishi kuka ba ƙaramin abu irin wannan ba.

“Ke adalci za ki min? Duka jiya na dawo, ba kya jin wani iri ki tafi har kwana huɗu ki barni ni kaɗai? Sayrah fa?”

Hannu Zafira ta sa ta goge hawayen fuskarta, wasu na sake zubowa.

“Kai ka ce ba zan tafi da ita ba, ka ce wajen Mami za ka kaita, sati biyu za ka yi Omeed, don Allah karka hanani, kai ne dalilin ƙin zuwana bikin Yaya, don Allah, ko kwana biyu ne…”

Girgiza kai Omeed yayi alamar a’a duk da yanajin rashin kyautawar hakan, ya san ta fi shi gaskiya, sai dai son kanshi ba zai bari ta tafi ba. Ya rasa me ya sa ita ba za ta fahimci ba ya son ko na kwana ɗaya ta yi nisa da shi ba, balle har kwana huɗu, ko yana wajen aiki ne kuwa, zuciyarshi na nutsuwa sanin tana gidan shi. Ganin ya ci gaba da shiryawarshi bai ce mata komai ba yasa ta ƙara Magana,

“Don Allah ko kwana biyu ne, ka ga har faɗa musu na yi na ce zan je cikin satin nan…”

Zafira ta faɗi zuciyarta na mata ƙuna da kewar gida da ta ‘yan uwanta, ta kusan wata takwas ba ta ga Nuri ba, gara ma Fawzan ya zo ya kawo Aroob ta yi mata sati, shi ma an fi wata huɗu. Shirun dai Omeed ya sake yi.

“Duk sanda kaso kake zuwa ka ga naka ‘yan uwan… Ban san me yasa kake hanani zuwa ganin nawa ba.”

Ta faɗa muryarta na rawa saboda ɓacin rai.

“Bana son jan magana, kin kuma sani. Ba zaki ba”

Girgiza kai Zafira take yi, ta gaji, sosai take jin gajiya da Omeed ɗin har a ƙasusuwanta.

“Ba wannan karon ba Omeed…ba wannan karon ba, na gaji Wallahi…”

Hularshi a hannu yake shirin hanyar fita daga ɗakin, ta miƙe ta sha gaban shi, hawaye na zubo mata.

“Don girman Allah ka barni, kwana ɗaya kawai, da zan iya wuni ɗaya ma zan yi, roƙonka nake Omeed…”

Sauke numfashi yayi, hawayen ta na ci mishi rai, haka nacin da take ya soma juya mishi kai. Raɓata ya zo yi ta sake tare hanyar, bai san lokacin da ya ɗauke ta da mari ba, duk da ba baƙon abu bane, marin ya mata bazata, har lokacin kunnenta na ɓarin haggu dum take jin shi.

“Babu inda za ki.”

Omeed ya maimaita, bai san sau nawa take so ya faɗa ba kafin ta gane. Ba marin ke ƙara gudun hawayenta ba, ba ta san me ya sa fuskarta ta kasa sabawa da zafin ba, amma zuciyarta da alama ta fara sabo da hakan.

“Me yasa? Me yasa baka son barina zumunci da ‘yan uwana?”

Ta tambaya muryarta can ƙasa, tana son sanin dalili, yau tana so ya faɗa mata ko da zai sumar da ita ne, in ta farfaɗo sai ya faɗa mata dalilin shi, ganin ‘yan uwanta ko ba komai zai sa ta shaƙar iska daban da ta gidanshi, zai ba ta ƙarfin gwiwar sake ci gaba da jure zama da shi, ya kasa gane tana buƙatar ganin su saboda dalilai da yawa. Kanshi ya ji ya fara juya mishi, in ranshi ya yi dubu ya ɓaci, rabon da Zafira ta yi mishi gardama irin ta yau tun farkon auren su, hannu yasa ya hankaɗe ta gefe yana nufar ƙofa, yana da abu mai muhimmanci da yake buƙatar yi, in ya tsaya za ta kara ɓata mishi rai ne.

Amma me? Bai kai ƙofa ba ta biyo shi da gudu, ta riƙe hannun ƙofar, kuka take sosai wannan karon.

“Ko me za ka yi min ka yi, don Allah ka barni ni dai, ina buƙatar zuwa… Ina buƙatar shaƙar iska daban da ta gidan ka, ina son wani ya faɗa min ina da hankali da nake zaune da kai… Omeed ina son ganin mahaifiyata… A karo na farko a shekaru ukku ina son ganinta in faɗa mata damuwa ta…. Ina son in kalli fuskarta in ji ko zama da kai ne abinda ya kamata…”

Tunda ta fara magana zuciyarshi ta yi tsaye waje ɗaya. Jin dalilin da yasa take son zuwa gida na ƙara gudun ɓacin ranshi, yana saka tsoro a wani ɓangare na zuciyarshi.

“Rabuwa kike shirin yi dani? Gida kike son zuwa don ki rabu da ni?”

Yake tambaya yayin da ya yi cilli da hular da ke hannun shi tare da ɗauke Zafira da wani irin mari da sai da ta faɗi ƙasa. Kuka ta saki mai cin rai tana kallon shi da wani yanayi da yake son ya ɓatar daga idanuwanta da duka. Ko za ta dawo hayyacinta, hannu ya sa ya riƙo kafaɗarta ya ɗago ta.

“Ba ki isa ba wallahi… Babu inda za ki…”

Omeed ya yi maganar yana sake ɗauke ta da wani mari, kafin ya tureta ta faɗi ƙasa, tana ji yatsun hannunta da ta faɗi akansu suka yi ƙara, zafin hakan na kaiwa har ƙwaƙwalwarta, ɗayan hannunta tasa ta kama wanda take zaton yatsun shi sun karye saboda azabar da take ji yana mata. Cikin wani irin kuka take bin Omeed da yake neme-neme cikin wardrobe ɗin dake jikin bangon ɗakin da kallo.

“Meye dalilin zama da kai? Ka faɗa min dalili ɗaya da zai sa in ci gaba da zama da kai!”

Juyowa ya yi yana sauke mata idanuwan da ke cike da masifa a tsawace ya amsata:

“Saboda ina son ki! Saboda kin koya min son ki!” Ya ƙarasa hannunshi na kaiwa kan belt ɗin da yake nema ya fito da shi yana takowa inda Zafira take zaune, hakan ya sa ta jan jiki tana matsawa cikin hanzari.

“Kar ka dake ni… Wallahi kar ka taɓa ni…. Wayyoo Allah na shiga uku…. Omeed don Allah ka…”

Belt ɗin da ya zabga mata ya sa sauran kalaman komawa. Zafin ya sa ta mantawa da na yatsunta ta saka hannayenta duka tare da murza duk wani waje da belt ɗin ya samu.

“Babu inda za ki… Ba za ki barni ba.”

Yake faɗi yana sake zabga mata belt ɗin, ko ta ina yake dukanta.

“Za ka kashe ni ne zan zauna dakai?!”

Zafira take tambaya tana ihun da ko a jikin Omeed ɗin, don ba shi yake buƙatar ji ba. Ci gaba ya yi da dukanta.

“Ba za ki barni ba… Kina ji na?

Mutuwa ce kawai za ta rabani dake…”

Azabar da take ji take son ta tsaya ko na minti ɗaya ne, sam Omeed ya ƙi bari ko numfasawa ta yi, gaba ɗaya ya gigita mata rayuwarta, jikinta babu inda bai ɗauki ɗumi ba, hawayenta kansu sun tsaya don azaba.

“Ba inda zani….wayyoo Nuri… Yayana… Omeed don Allah ka yi haƙuri… Wallahi ba inda zani… Ba inda zani don Allah ka bari… Bazan sake ba.”

Girgiza mata kai Omeed yake yana ci gaba, ba ta ji ba, yana son ta kwana biyu ko juyin bacci za ta yi tana jin tunin cewa ba za ta barshi ba, duk ihu da magiyar da take mishi bai sa ya daina dukanta ba, ya san iya ƙarfin da belt din yake sauka jikinta da shi, ba zai fasa ba, zai bar tambari na kwanaki dai. Sai da zuciyarshi ta faɗa mishi ya isa haka tukunna ya ajiye belt ɗin.

Zama yayi akan kafet ɗin gab da ita ya kamota zuwa jikin shi, a rikicen da take da azabar da take ji yasa ta faɗawa jikin shi  wani rin kuka ya ƙwace mata, za ta karɓi lallashi ko da nashi ne tunda ba ta da inda za ta je ta samu. Sai yanzu ta san yaudararta zuciyarta take da ta faɗa mata ta fara sabawa da irin azabar nan.

Ɗan satikan da ya yi ba ya nan, bai taɓa lafiyarta bane ya sa ta sakin jiki. Lokaci ɗaya dana sanin jan maganar da ta yi da shi yake lulluɓeta. Tana jin hannunshi kan bayanta yana rage mata raɗaɗin da take ji. Iska yake hura mata a gefen fuska.

“Laifin ki ne…kin sani? Kin san ke kika sa ni dukan ki ko?”

Kai take ɗaga mishi hawayenta na jiƙa  mishi gaban riga, sake riƙe ta ya yi gam yana lumshe idanuwanshi.

“Ina sonki… Me yasa kike tunanin barina? Me yasa kike tunanin zama dani kuskure ne?”

Ba ta son yin kowace magana, ba ta tunanin ƙwaƙwalwarta za ta iya wani tunani a yanayin da take ji.

“Kina sona kema… Ki faɗa min kina sona in ji.”

Omeed ya buƙata yana gyara zamanshi da sumbatar gefen fuskarta. Sai ajiyar zuciya take saukewa.

“Ina sonka…”

Ta tsinci kanta da faɗa, zuciyarta na wata irin dokawa, kamar tana son amincewa da abinda ta faɗa ɗin. Yadda yake sa ta tana faɗin tana sonshi har zuciyarta ta fara yarda da hakan. Ba za ta iya wani dogon tunani ba, don haka ta zagaya hannuwanta jikin bayanshi tana runtse idanuwanta hawaye na ci gaba da zubar mata.

Duk yadda yake son fita zama yayi, ba ya son ya bar mata dukanshi kawai a jikinta, hakan zai ba ta damar yin tunanin wani abu daban, ba ya so kuma. Don haka ya zauna ya riƙeta a jikinshi, ya san ba ta da wani ƙarfin kirki ba za ta jima ba za ta yi bacci, inya mayar da ita kan gado sa ya yi sauri ya fita ya dawo.

*****

Kano

A gajiye Altaaf ya kalli Majida da hannunta ɗaya yake riƙe da kwandon da yake cike taf da kayayyaki, ɗayan hannunta kuma riƙe da takardar da ta yi list ɗin kayayyakin da suke da buqata.

“Majee…”

Ya ja sunanta, kamar yadda yake kiranta, ɗago idanuwanta ta yi ta sauke su kan fuskarshi, tsaf ta karanci me yake son faɗa tun kafin ya furta.

“Sai da na ce hwa kai zamanka  gida, sayayyata da yawa… Ka ce sai ka biyo ni.”

Daƙuna mata fuska yayi.

“Tun ɗazun fa… Me za ki ƙara zubawa anan? Ba zai ɗauka ba ma.”

Kwandon Majida ta tura gaba tana faɗin:

“Ni kau ka takura mani gaskiya, ka tai mota ka zauna in ida.”

Girgiza kai Altaaf yayi yana ciza leɓenshi na ƙasa yadda yakan yi in yana jin rikici da kuma dariyar hausar Majida da duk da sabon da ya yi da ita ba ta gajiya da sa shi nishaɗi.

“Ya isa haka…kin dawo ke kaɗai ki ƙarasa.”

Buɗe baki ta yi da shirin mishi musu, ya ɗaga mata hannu.

“Gida zamu tafi Majee.”

Turo baki ta yi kawai, don ta san ɓata lokaci ne musu da Altaaf, abinda yake so ɗin dole shi za a yi. Tana kallon shi ya kama kwandon tare da juyawa ya nufi counter ɗin da ke cikin Mall ɗin. Bin shi ta yi a baya suka tsaya tare ana fitar da kayyakin tare da lissafa kuɗaɗen.

Da gudu wasu yara biyu mace da namiji, dukkan su babu wanda ya kai shekaru biyar suka shigo wajen, kafin matar da da alamu mahaifiyarsu ce ta biyo bayansu ta riƙo su duka biyun.

“Wallahi za mu koma in surutu za ku sakani…”

Ta faɗa tana maida numfashi da ke nuna da gudu ta biyo bayansu. Macen ce ta kalle ta kamar za ta yi kuka.

“Mummy ni Ice cream.”

“Noo! cookies mummy.”

Ƙaramin ya faɗa, ɗauke idanuwanta Majida ta yi daga kansu tare da mayarwa kan Altaaf da gaba ɗaya hankalinshi ya koma kansu, fuskarshi ɗauke da wani irin yanayi da ya sa ta kai hannu ta riƙo nashi tana matsawa cike da son nuna mishi tana tare dashi a kowanne yanayi.

Numfashi me nauyi Altaaf ya sauke yana riƙe da hannun Majida da yake cikin nashi sosai, dukkan zuciyar shi na tare da yaran da yake jin kamar ta bashi guda ɗaya. Credit card ɗin shi ya zaro ya miƙa wa Majida, har lokacin yana ci gaba da bin yaran da ido har sai da suka ɓace mishi. Ta mishi magana kusan sau huɗu da su tafi don har yaran wajen sun kwashi kayyakinsu, amma bai ji ta ba, sai da ta ja hannun shi tukunna ya juya ya kalle ta.

“Mu tai…”

Ta maimaita muryarta na rawa, bai ce komai ba har suka fita daga wajen. Mota ya buɗe ya shiga, ita ta yi tsaye aka gama saka musu kayan a mota, ta ɗauko jakarta da ke ajiye a ciki ta basu dubu ɗaya tukunna ta shiga ta zauna ta rufe murfin motar.

“Mi kake so in yi in ka ci gaba da haka?”

Ta buƙata idanuwanta kafe a fuskarshi, bai juyo ya kalleta ba, sai da ya tayar da motar tukunna yace,

“In na ci gaba da me?”

Ya amsa tambayarta da wata tambayar, duk da ya gane abinda take nufi, bai san yadda zai hana zuciyarshi ba, yana son yara tun tasowarshi, kuma yana da burin haihuwar nashi, amma yanzu yadda yake jin ƙaunarsu abin ya wuce duk wasu kalamai.

“In kana kallon kowanne yaro da zamu haɗu da shi kamar za ka ɗauke shi, in kana kallon shi kamar ka cire rai ga samun naka…”

Majida ta ƙarasa maganar muryarta na rawa, tun zuwansu asibiti na farko da aka tabbatar musu su duka biyun lafiyarsu ƙalau, hankalinta ya kwanta ta wannan fannin, ta san duk yadda suke son haihuwa in lokacinta bai zo ba babu yadda za su yi. Duk da Altaaf ya ƙi haƙura, watannin nan yana karya mata zuciya, kullum cikin yawon sake asibiti suke yi. Abin ƙara haukata yake da duk rana. Jan motar ya yi yana juyawa da su, suka hau titi. Wani abu ne tokare da maƙoshin shi da ya hana shi magana. Ko da babu abin ma ba shi da kalaman da zai yi amfani da su, bai da ƙwarin gwiwar kallon Majida ya faɗa mata rashin dalilin rashin haihuwarsu, bai da ƙarfin zuciyar da zai furta ma kanshi dalilin a fili ko da shi kaɗai ne, ballantana kuma tare da Majida.

Ganin yadda yake fizgar motar ya sa Majida jan numfashi da faɗin,

“Yi parking…”

Babu musu ya samu waje gefen hanyar ya yi parking ɗin motar, bai ce mata komai ba ya fito suka yi masayar waje, don ya san sam bai da nutsuwar yin tuƙi. Lumshe idanuwanshi ya yi yana buɗe su a hankali.

*****

“A-Tafida banga period ɗina ba fa, na faɗa maka tun satin da ya wuce.”

Sigarin da ke hannunshi ya kunna, yana mata wani irin ja, haɗi da fitar da hayaƙin cikin ƙwarewa.

“Me ya sa kike abu kamar wannan ne karo na farko Anisa?”

Altaaf ya faɗi ba tare da ya juya ya kalleta ba, sigarin shi ya sake ja fuskarshi cike da alamun jin daɗin ta da yake yi.

“Kuɗin da suke hannu na ba za su isa ba.”

“Zan miki transfer anjima… Kar ki sake damuna da maganar nan.

*****

Girgiza kanshi Altaaf ya yi, da ƙyar ya yakice inda tunanin shi yake son su kai wa ziyara. Hannunshi ya kai ya kunna Radio, ya ci sa’a a tashar cool FM yake, sun saka waƙar Justin Bieber mai suna Love yourself, sosai ya ƙure volume ɗin kamar zai fasa musu dodon kunne.

Majida kamar ta san ba ya son ƙwaƙwalwar shi ta samu nutsuwar da zata tuna mishi abubuwan da zai yi komai don ya goge, ba ta hi ƙoƙarin rage mishi volume ɗin ba; har suka ƙarasa gidansu da yake a Hotoro.

*****

Yana dawowa Sallah a falo ya zauna ya ɗauki remote, ya kasa tsayawa a tasha ɗaya. Gaba ɗaya ba ya jin daɗin komai, ganin yaran ya taɓa mishi zuciya ta inda bai kamata ba. Bai ji fitowar Majida ba sai hannuwanta ya ji cikin gashin kanshi tana yamutsawa ta bayan kujerar da yake zaune.

Kama hannuwanta ya yi ya janyota, ta zagayo, murmushi da bai yi niyya ba ya ƙwace mishi, kumatunshi ta ja, ya ture hannunta yana murza wajen.

Zama tayi tana mishi dariya.

“Ko kai ha. Ka yi kyau da murmushin nan a huskarka.”

Murmushin ya sake mata, yana jin sonta a wurare fiye da zuciyarshi. Yasan shi ya kamata ya ke kwantar mata da hankali akan maganar haihuwar nan, amma ita take kwantar mishi, ta fishi buri saboda ba ta san abin da ya sani ba.

“Wani abu nake son ci.”

“Kamar me?”

Ɗan ɗaga kafaɗa ya yi.

“Ba yunwa nake ji ba…bakina ne ya yi switch off.”

Dariya Majida take yi sosai.

“Kwaɗayinka ya hi ƙarhi na… Sai ka ce mai ƙaramin ciki.”

Ɗaga mata gira ya yi duka biyun kafin ya matsar da kanshi saitin kunnenta yana faɗa mata maganar da sirri ce kawai a tsakanin su, dariya Majida take yi cike da kunya, kafin ta ture shi tare da miƙewa ta nufi kitchen. Ita ɗin ba mai yawan ciye-ciye bace ba. Indai cikinta ya ƙoshi. Altaaf ya sa dole ba ta rabuwa da wani dambun nama ko wasu snacks a fridge da za ta iya mishi warming. Ko kaɗan in ba azumi yake ba ba ya barin bakinshi ya huta. Kayan zaƙ har faɗa suke yi wani lokacin, don in ciwon ciki ya tasar mishi ita yake bari da tashin hankali fiye da ciwon da ke damun shi. Sanda ta dawo waya Altaaf yake yi, dan haka ta ajiye mishi plate ɗin dambun naman a gabanshi ta samu waje ta zauna da faɗin,

“Mi za mu ci ne da dare? Tun ɗazun nike tunani na rasa.”

Ɗan daga mata kafaɗa ya yi tare da ɗibar dambun naman ya sa a bakin shi.

“Ko in mamu dambun shinkahwa?”

Dariya Altaaf yake yi sosai, tun daga zuciyarshi yake jin dariyar,

“Majee ce shinkafa.”

Ya buƙata yana ci gaba da dariya, ita ma murmushi take yi, ta ɗauki pillow ɗin kujera da ke gefenta ta jefa mishi, ya tarbe da hannun shi yana ci gaba da mata dariya.

“Ki ce ko dambun shinkafa zan mana… Ba mamu da shinkahwa ba.”

Ita ma dariyar take yi, ba ta ga ranar da Altaaf zai daina tsokanarta kan hausarta ba.

“Ka ƙyaleni, ban iya wa da kai da marecen nan.”

Girgiza kai Altaaf yayi yana dariya. ‘Marecen’ da tace na tuna mishi farko-farkon auren su.

*****

Kallon Majida yake yi da ta fito daga gidan, da wani hijabi zundumeme kamar za ta tashi sama, don in da a ƙasa za su tafi, tsaf za ta share titin layin da hijab ɗin. Sauke numfashi ya yi cike da takaici, bai san ranar da za ta waye ba. Yanayin yadda take tafiya tana lauyewa kamar za ta faɗi ne da ta ƙaraso ya sa shi faɗin:

“Meye kike tafiya kamar za ki karye?”

Turo baki ta yi, gaba ɗaya yanayin fuskarta ya canza kamar za ta yi kuka ta ce mishi:

“Ba ni son takalma masu tsini, yaman tsayi, ji nike kamar zan hwaɗi.”

Murmushi ya ɗan yi kawai, yana kallonta, rana ce ta lumshe, hakan ya sa ta ɗaga kanta sama tana wani matse idanuwa.

“Hadari ke da kwai ma, ina ga ruwan marece za ai.”

Daƙuna fuska Altaaf ya yi yana kallonta sosai.

“Ruwan me?”

Ya tambaya.

“Ruwan marece.”

Ta amsa tana kallon yadda yake daƙuna fuska yana maimaita kalmar.

“Marece, wanne ne kuma ruwan marece?”

Hararar shi Majida ta yi, in akwai abinda ta tsana bai wuce tambaya ba, musamman ma ta rainin hankali.

“Meye marece?”

Ya sake tambaya.

“Ƙwaɗɗo”

Ta amsa shi ta jan murfin motar ta shige abinta.

“Marece, kwaɗɗo, ruwan marece? Ruwan kwaɗɗo?”

Yake maimaitawa don babu abin da ya gane, fuskarshi a daƙune da rashin fahimta ya zagaya ya shiga gidan motar shi ma ya rufe, mukullin ya sa jiki tare da murzawa, hankalin shi kan abin da yake yi ya ce,

“Ke meye kwaɗɗo ɗin wai?”

Hararar shi Majida ta yi ta gefen ido, tana sauke numfashi mai nauyi ta bakinta, ya cika tambaya har ta tsiya, ta ke faɗi a zuciyarta, bai ma san baƙar magana ta faɗa mishi ba. Shiru ta yi.

“Na tsani ina magana a yi banza a ƙyale ni.”

Ya faɗa ranshi a ɓace, bai san me ke damun Majida ba, kamar yadda bai san ya aka yi zuciyarshi ke da sanyi akan ta ba, wacece mace, da shi Altaaf Tafeeda zai mata magana ta yi shiru ta ƙyale shi, matan da suka fi ta aji, kyau da komai har so suke ya kula su.

“Dake fa nake.”

Dira ƙafafuwanta tayi cikin motar ta wani bula ƙaton hijab ɗinta kamar mai shirin hawa bori, muryarta cike da shirin yin kuka tace:

“Nikau bani son tambayar tsiya… Wai ba ka ƙyaleni?”

Motar ya kashe, bakin shi a sake yake kallonta, sun gama kwana waje daya shi ya sa ta raina shi haka.

“Ke?”

Ya faɗi, har lokacin mamaki ya ƙi barin fuskarshi, kallon shi ta yi tana jin ba ta kyauta ba, amma ya isheta ne da tambaya.

“Da gaske kake wai ba ka san miye marece ba?”

Ta buƙata.

“In na sani me yasa zan tambaye ki.”

“Yamma hwa”

Ta amsa, yanayin da ta yi maganar ne ya sa bai gane ba har lokacin. In akwai abinda ya tsana bai wuce ya kasa fahimtar wani abu ba, ko a makaranta Allah ya mishi nacin tambaya. In bai gane komai ba sam hankalin shi ba ya kwanciya, Majida ta fara sashi ciwon kai.

“Yamma fa ki ka ce, Yamma ta gabas ko wacce?”

Dafe kanta ta yi cikin hannuwanta, gab take da kurma ihu, muryarta can ƙasa tace:

“Evening…evening nike nihi.”

Ware idanuwa ya yi cikin mamaki, murmushi ya ƙwace mishi, musamman yafda ya ga ya ƙure haƙurinta. Bai san me ya sa hakan ya sa shi nishaɗi ba.

“Kwaɗɗo fa?”

Ta kai minti ɗaya shiru, har lokacin ba ta ɗago da kanta ba kafin tace:

“Frog”

Dariya ta ƙwace ma Altaaf da ya sa Majida ɗagowa tana kallon shi don ba ta san me ya bashi dariya ba.

“Kwaɗo ne kwaɗɗo? Kwaɗɗo fa…”

Ya ƙarasa yana dariya, takaici ya sa ba ta ce mishi komai ba.

*****

Ringing ɗin wayarshi ne ya katse mishi tunanin da yake yi, ɗaukar wayar ya yi, har lokacin da murmushi a fuskarshi kafin ya kara a kunnen shi haɗi dayin sallama.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…

Yaushe?”

Altaaf ya buƙata, zuciyarta ta ji ta doka, don tasan kowane labari ne ake bashi ta ɗayan ɓangaren ba mai daɗi bane ba.

“Allahu Akbar… Oh Allah. Allah ya jiƙanta. Yanzu nan gidan zan zo mu tafi gaba ɗaya ko ya za a yi?”

Shiru ya sake yi, Majida kuwa ta ƙagu ya sauke ya faɗa mata ko waye ya rasu.

“To shikenan. Yanzun za mu taho muma In sha Allah. Allah ya jiƙanta ya ƙara haƙuri. Altaaf ya ƙarasa yana sauke wayar daga kunnen shi, kallon Majida ya yi.

“Gwaggo Rakiya ce ta rasu.”

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Allah sarki… Baiwar Allah…oh an sha jinya.”

Majida ta faɗa, don sau biyu suna zuwa Kaduna duba ƙanwar Maman Altaaf ɗin, ta sha jinya sosai baiwar Allah.

“Allah yasae mutuwar ta zame mata hutu a gare ta.”

Majida ta faɗa. Altaaf ya amsa da amin sannan ya ce,

“Su Ammi har sun tafi, ki haɗa mana kayanmu, mu bi bayan su.”

Miƙewa Majida ta yi ta nufi ɗaki din ta hadae musu kayansu. Tana jinjina yadda duniyar babu wani tabbas a cikinta.

Abuja

“Rafiq da ka tashi ka tafi gida. Ka ga har takwas da rabi… Kama kira matarka kuwa?”

Nuri ta ƙarasa maganar da tambaya. Girgiza mata kai Rafiq ya yi, in akwai abinda ya tsana a rayuwarshi bai wuce ƙarya ba.

“Ka kyauta kenan? Sarai ka san hankalinta zai tashi tun da ka wuce lokacin komawarka gida…”

Katse Nuri yayi da faɗin:

“Hankalina ne ba a kwance ba Nuri…bari in kirata yanzun.”

“Ka tashi ka tafi dai… Tun da duk muna nan.”

Girgiza mata kai ya yi. Babu inda zai je in bai ga Fawzan ya farka ba. Yana son tabbatar da cewa zai samu lafiya da kanshi, bai yarda da maganar likitocin ba, tunda ba su suka ɗauko Fawzan ba ya numfashi ba.

“Ki yi haƙuri in kirata ɗin …hankalina ba zai kwanta ba in ba gani na yi ya tashi ba.”

Cikin taushin murya Nuri ta ce,

“Rafiq… Ba yau ya fara ba. Ka sani, lokacin sanyi yana shiga yanayi da ya wuce wannan ma. Sau nawa muna fidda rai akan Fawzan? Sai kuma ka ga ya tashi. Zamanka ba zai canza komai ba… Addu’arka ya fi buƙata, kuma ko daga ina ne za ta same shi.”

Ɗan dafe kai Rafiq ya yi, ba ya jin ƙarfi ko kaɗan a jikinshi. Abubuwa sun taru sun mishi yawa, duk yadda yake son zama sai Fawzan ya tashi bai kai yadda ba ya son jan magana da Nuri ba. In gidan ya koma ma hankalin shi ba kwanciya zai yi ba, zaman asibitin ya ɗan cire mishi zuciyarshi daga matsalar can gidan. Isah ya kira ya faɗa mishi ya zo ya ɗauke shi. Bai sake cewa komai ba har sai da Isah ya kira shi cewa yana wajen asibitin tukunna ya miƙe da faɗin:

“Allah ya kara sauƙi… Inya tashi ki kirani.”

Kai Nuri ta ɗaga mishi.

“In shaa Allah…ka kwantar da hankalin ka don Allah…”

“Hmm…”

Rafiq ya iya cewa yana jan wani numfashi.

“Na gaji da kin faɗa min n dalilin da ya sa bana iya tuƙi da kowa yake yi Nuri…naso in ji daga bakin ku… Koma menene zai min sauƙi in ku ne kuka faɗa min. Na gaji da jira…na gaji da jira Nuri.”

Ya ƙarasa muryar shi can ƙasan maƙoshi kafin ya ranƙwafa ya sumbaci Nuri a kuncinta, sannan ya kalli Aroob.

“Komai zai yi dai-dai…”

Idanuwanta cike taf da hawaye ta ɗaga mishi kai. Suna kallon shi harya karya kwana, hawayen da Aroob take tarbewa suka zubo.

“Nuri ta ina zamu fara faɗa mishi? Me za mu ce mishi?”

Ita kanta Nurin idanuwanta cike suke da hawaye lokacin da take amsa Aroob.

“Ban sani ba. Wallahi ban san me za mu ce mishi ba.”

“Kin san Yaya Rafiq… Zai gano da kanshi…in ba mu faɗa mishi da kanmu ba wani zai gaya mishi a waje.”

Jinjina kai Nuri ta yi cike da yarda da maganar Aroob ɗin. Don kullum zuciyarta dokawa take da sanin cewa a kowane lokaci wani zai iya suɓutar baki ya faɗi abin da zai sake birkita musu komai. Duk da iya inda Rafiq yakan shiga, mutanen da yake mu’amala dasu daga wajen aiki har zuwa abokanshi ta san suna kaffa-kaffa akan maganar kamar yadda sukeyi.

“Mu kanmu ba mu gama dawowa dai-dai ba… Ban san me zai faru ba.”

Hannu Aroob ta sa tana goge hawayen da suka sake zubo mata. Kafin ta ce,

“Allah ya kawo mana ɗauki…”

Ajiyar zuciya Nuri tayi ta amsa da amin. Ta jingina kanta da bangon wajen tare da rufe idanuwanta.

*****

Da nauyin zuciya ya shiga gida, wani rauni-rauni yake ji, ba zai iya tuna lokaci na ƙarshe da ya zubda hawaye ba. Yanayin da yake ji a yanzun, in da hawayen za su zubo mishi ƙila da ya samu sauƙi. Ko ta ina rayuwar ta hargitse mishi, ya kamata ya tsayar da zuciyarshi kan Aslam ne, amman ya kasa.

Bayan damuwar Fawzan, akwai matsalarshi da Tasneem, bayan ita akwai son sanin ko me ya faru da shi da kowa ya ƙi faɗa mishi. Yana shiga ɗaki, wayarshi kan gado ya jefata, a nan tsakiyar ɗakin ya cire kayanshi ya nufi toilet. Ya jima a tsaye ya sakar ma kanshi ruwa mai ɗumin gaske, in za a tambaye shi ba zai ce ga kalar tunanin da yake yi ba.

Amma sam babu nutsuwa a tattare da shi, ya fi mintina sha biyar kafin ya fito ɗaure da Towel a Ƙugun shi, kayan da ya bari ya ɗauka, in komai na rayuwar shi daga ciki a hargitse yake, ba zai zamana har a wajen komai ya hargitse mishi ba. Ya ninke rigar kenan yana ɗaukar wandon kamar wanda aka buga wa guduma akai ya ɗago yana ware idanuwanshi, gam ya runtse su yana girgiza kai. Sosai yake duba ƙwaƙwalwar shi amma ya kasa tuna komai.

“Me yake faruwa da ni haka?”

Ya tambayi kan shi, zuciyar shi cike da tsoro, ko a cikin kanshi ba ya son maimaita abinda zuciyar shi take zargi, ya san in ya tsaya a ɗakin shi kaɗai abinda duk ba ya son ya yi tunani shi zai yi. A gaggauce ya saka boxers ɗin shi da singlet ya fita daga ɗakin.

Ba don ya san inda zai je ba, zuciyarshi ya ba wa ragamar gangar jikinshi, sai ganin kanshi yayi a ƙofar ɗakin Tasneem. Kafin ya sake tunani ya kai hannu ya murɗa handle ɗin tare da turawa. Kan gado ya hangota a kwance, don haka ya ƙarasa shiga gaba ɗaya ya tura ƙofar ya kulle ɗakin.

Har kan gadon ya ƙarasa, hasken da yake gauraye da ɗakin ya bashi damar ganin fuskarta, zuciyarshi ta matse waje ɗaya, don ko motsawa ba ta yiyba ballantana ta yi ƙoƙarin ɓoye mishi hawayen da ke bin fuskarta suna jiƙa pillow ɗin da kanta yake a sama.

“Neem…”

Ya kira muryarshi can ƙasa, idanuwanta kawai ta motsa tana sauke su akan shi.

“Ban san me yake damuna ba…”

Ya faɗa muryarshi cike da wani irin yanayi da ya sa Tasneem jin kamar ta kai hannu ta tallabi fuskarshi, sai dai ba ta son ya tashi ya fita, ƙarshen lokacin da ta ƙoƙarin taɓa shi, bar mata wajen ya yi. Don haka jikinta ta ja tana matsawa sosai tare da bubbuga mishi kan gadon cike da alamar cewa ya kwanta. Sosai yake kallon wajen kamar yana so ya gano ko akwai wani abin cutarwa. Kafin a hankali ya maida dubanshi kan Tasneem ɗin. Bai san me yake ji ba, bai san kalar tunanin da ya kamata ya yi ba. Ƙafafuwan shi ya ja ya maida su kan gadon ya kwanta. Jin shi gab da ita sosai ya sa Tasneem matsawa, ko kaɗan ba ta son ƙara mishi damuwa, ba ta son saka shi cikin yanayi fiye da wanda take gani akan fuskarshi. Ga mamakinta hannun shi ya miƙa mata, cike da shakku ta kama hannun tana shirin matsowa.

“No please…”

Rafiq ya faɗi da sauri yana dumtse hannunta dake cikin nashi. Runtse idanuwanshi ya yi yana son kauda hotunan Tasneem da wasu dake mishi yawo, ga wani irin azababben kishi da ya taso mishi yana barazanar sa numfashin shi ya tsaya.

“Sugar…”

Tasneem ta kira shi muryarta na rawa, har lokacin idanuwanshi a runtse suke gam. Sam ba ya son ya buɗe su ya kalle ta. Sosai ƙirjinta yake zafi, tana jin wani abu na tattarowa daga zuciyarta da ke ciwo zuwa maƙoshinta yana hana mata wucewar numfashi yadda ya kamata, hakan bai barta da wani zaɓi da ya wuce soma tari ba.

Sosai tarin yake sarƙe ta har dukkan jikinta na amsawa. Buɗe ido Rafiq ya yi yana kallon yadda a tare da tarin Tasneem na kokawa da dai-daituwar numfashin ta, hannunta ta zame daga cikin nashi tana ci gaba da tarin.

Sauka yayii daga kan gadon, da alama ba ta ma kula ba, cikin sauri ya fita zuwa kitchen, ya dawo da kofin ruwa, lokacin da ya shigo tarin ya soma tsagaita mata. Miƙa mata kofin ya yi, ta tashi zaune ta kawo hannu don ta karɓa. Sai dai ya ƙi sakin kofin, nazarin fuskarta yake yi tashi fuskar a daƙune. Yanayin da ke cikin idanuwanshi ya sa ta faɗin,

“Mene ne?”

Ɗayan hannun shi da ba ya riƙe da kofin ya miƙa zuwa laɓɓanta, yana son dangwalo abinda yake gani a gefen bakinta, yana son tabbatar wa zuciyarshi abinda yake gani. Dangwalowa ya yi ya kawo ɗan yatsan shi zuwa dubanshi, zuciyarshi na wani irin bugawa kamar zatae fito daga ƙirjin shi.

Jini ne, sake kallonta ya yi, kafin ya kalli hannun da ta miƙo ta karɓi ruwan, babu shiri ya ajiye kofin a ƙasa ya hau kan gadon sosai ya zauna.

“Sugar…”

Tasneem ta fara don ta fahimci abin da yasae yake mata kallon nan yanzun. Kai kawai ya girgiza mata alamar ba ya son jin koma menene za ta faɗa. Idanuwanta cike taf da sabbin hawaye ta yi shiru. Duka hannayenta ya kamo cikin nashi yana buɗe tafukansu. Tsilli-tsillin jini ne a jikin su don ta yi amfani da su ta rufe bakinta lokacin da take tari. Fuskarta ya sake kallo, akwai wani baƙi-baƙi a ƙasan idanuwanta da ke nuna alamar rashin wadataccen bacci, ga wata irin ramewa da ta yi, a cikin idanuwanta yake ganin alamar ba ta da lafiya.

Hannuwanta ya saki, ya maida nashi jikin fuskarta. Sosai yake feeling ɗin fuskar cikin hannuwanshi zuwa wuyanta.

Zuciyarshi na ƙara shiga wani irin yanayi da jin yadda jikinta yake ruf da wani irin zazzaɓi. Ya fara jin rashin kyautawarshi na rufe shi tun kafin zuciyar shi ta faɗa mishi.

“Tun yaushe ne ba ki da lafiya?

Tasneem tun yaushe? Me ya sa ba ki faɗa min ba?”

Ba ta san yanayin sanyin da ke muryarshi bane ko kuma son da zuciyarta take na son ya sake nuna mata kulawa komin ƙanƙantarta bane ya sa wani irin kuka ƙwace mata. Hannuwanshi da ke kan fuskarta ta riƙe dam da nata, tana ci gaba da wani kuka marar sauti da yake fitowa daga ko ina na jikinta.

“Tarin jini kike yi…kina ƙarƙashin kulawata ban sani ba… In wani abu ya sameki ta ina kike so in fara yafe wa kaina? Abinda kika yi min bai isheki ba Neem?”

Rafiq yake fadi yana jin ta ko’ina duniyar ta haɗe mishi waje ɗaya. Yan kasa sanin yanayin da yake ji, don ba shi da kalaman da za su dace da abin da yake ji. Tarin jini, ba ya son fara tunanin komai hakan yake nufi. Sakin fuskarta ya yi, ya sauka daga kan gadon tare da kama hannunta ya ɗago da ita.

Har lokacin ba ta daina kukan da take yi ba, shi ne ke cikin yanayi amma ita take kuka, ita take samun sauƙi ta hanyar rage wani abin da zubar hawayenta. In da yasan ta inda zai fara da yayi kukan shima ko zai samu sauƙi.

“Ina hijabin ki?”

Ya buƙata, ta kasa samun kalamai saboda kukan da take balle ta amsa shi. Numfashi mai nauyi ya sauke yana fuskantarta. Ya rasa ko me zai ce mata, kanshi yake ji kamar zai tarwatse saboda tunaninka da suka yi mishi yawa a ciki. Space ɗin da ke tsakanin su ya haɗe ya ɗora hannuwanshi akan kafaɗunta, ta ƙi ɗago fuskarta, kukanta kawai take yi, rigar dake tsakanin hannuwanshi da kafaɗunta bai hana shi jin zafin zazzaɓin da take yi ba. Haɓar shi ya ɗora a saman kanta yana runtse idanuwanshi gam. Muryar shi can ƙasan maƙoshi yace,

“Ya kike so in yi ? Na ɗauka aurenki zai dai-daita min rayuwa ta wani fannin… Na ɗauka ko ba komai zuciyata za ta samu farinciki…”

Maganganun shi da kusancin shi da ita na ƙara mata yanayin da take ciki.

“Zuciyata na ciwo… So… Sosai zuciyata na ciwo Sugar.”

Tasneem ta faɗa a lokacin da wani irin kuka ya sake ƙwace mata, sakin ta Rafiq ya yi, yana da tabbacin zuciyarshi ta fi nata ciwo. Sakin ta da ya yi ya bata damar kallon fuskarshi. Sai da ta goge fuskarta da hannu, duk da hakan bai tsayar da hawayen da take yi ba.

“Don Allah ka bar asibitin sai da safe in Allah ya kaimu, bacci kawai nake son yi.”

Sosai yake kallon ta, sauke numfashi ya yi a gajiye, har lokacin yanajin wasu bangwaye da idanuwa ba sa iya gani na haɗe shi waje ɗaya, numfashin da yake ja yana fitarwa kan shi a takure yake jin shi. Har ƙasan zuciyar shi yake fatan ba zai yi da-na-sanin biye wa Tasneem da barin zuwa asibitin har safe ba.

“Ka ji…”

Ta faɗa, kai ya ɗaga mata, ya samu waje a gefen gadon ya zauna, Ita ma ƙarasawa ta yi ta zauna a gefen shi, zuciyarta na matsewa waje ɗaya, kar ya matsa. Ga mamakinta, kwantar da kanshi yayi a jikin kafaɗarta, hakan ya sa ta juya da sauri tana kallon fuskar shi. Ji ya yi wuyar shi har ya soma riƙewa saboda ya mata tsayi, hakan ya sa shi ɗagowa, ƙafafuwanshi ya ja zuwa kan gadon, da su ya yi amfani ya janyo abin rufar da ke can ƙarshe, ya gyara sosai ya rufe rabin jikin shi, ba tare da ya kalli Tasneem da ke bin shi da ido ba ya zame jikin shi ya kwantar da kanshi a cinyarta yana rufe idanuwa.

“Kaina yamin nauyi, tunani yamin yawa Neem, na gaji sosai…”

Idanuwanta cike taf da hawaye ta ɗora hannunta akan fuskarshi. Muryarta na rawa take fadin,

“Ka huta, yau kawai ka cire tunanin komai ka huta”

Tana ji ya ja wani irin numfashi yana saukewa kafin ya saki jikin shi.

“Sugar…”

Ta kira, yana jinta, bai amsa ba saboda ko motsi ba ya so ya yi, nutsuwa yake so ko ya take, inda za ta taimaka mishi da ta yi shiru. Hawayenta ta yi saurin tarbewa don kar ya ɗigar mishi a fuska.

“Duk da ban cancan ci yafiyarka ba, ba zai hanani baka haƙuri ba. Ka yi haƙuri… Ka yi haƙuri don Allah…”

“Shhhhh….. Please.”

Rafiq ya katse ta, ba ya son ji, baya son jin komai, shirun kuwa ta yi, ba ta jin ƙarfin jikinta, kuma ba ta son motsawa don kar Rafiq da ya yi pillow da cinyarta ya sauka, hannu ta kai da ƙyar ta ɗauko pillow, ta kwanta akan bayanta tare da runtse idanuwanta.

Ba wai ba ta ɗauka soyayyar da ke tsakanin su ba za ta canza a daren su na farko a matsayin ma’aurata ba, sai dai ba ta ɗauka za ta yi kewar Rafiq har haka ba. Ciwon da take ji marar misaltuwa ne, ko yanzun da yake kwance a kusa da ita tana jin kewar shi. Sauke numfashi ta yi tana laluba inda duk ta adana soyayyar shi don ta san irin yau na jiranta.

*****

Jingine suke a jikin motarshi.

“Me yasa ba ka son muna zama a cikin motarka? Ƙafafuwanka ba sa gajiya da tsayuwa?”

Ta tambaya tana kallon shi. Murmushi ya yi mata.

“Na ce in buɗe miki ki zauna, ni in tsaya a waje kin ƙi… Kar ki ce min kin gaji da tsayuwa Neem.”

Shagwaɓe mishi fuska ta yi

“Kar ki fara…”

“To ka faɗa min ko me yasa?”

“Idon mutane, shi ya sa, ba don na damu da me za su faɗa ba, sai don na damu da abin da za su ce akan ki.”

Numfashi ta ja tana saukewa.

“Mutane na tarar ka da maganganu a kaina ko?”

Ta tambaya cikin sanyin murya.

“Na yarda da ke, ko me za su ce ba zai canza yadda nake ji a kanki ba, ke kaɗai za ki iya sa hakan ya faru, kar ki taɓa bani dalilin yin da-na-sanin yarda dake.”

Murmushi ta yi tana ƙoƙarin ɓoye yadda zuciyarta ke dokawa. Ta sa hannuwa ta goge fuskarta don ta ji ta soma zufa.

“Kunshi, kin yi ƙunshi Neem.”

Rafiq ya faɗa yana murmushin da ya kai har cikin idanuwan shi. Hannuwan ta sauke tana jujjuya mishi ja da baƙin zanen lallen da ya yi matuƙar yi wa hannuwanta kyau. Runtse idanuwan shi ya yi yana mayar da numfashi, kafin ya buɗe su a hankali.

“Ki mayar da hannuwanki inda bazan gansu ba.”

“Me yasa?”

Ta faɗa tana ƙara jujjuya mishi hannuwanta.

“Tasneem…”

Ya kira sunanta muryarshi can ƙasan maƙoshi.

“Ba kya sona ko?”

“Ina sonka mana.”

Harararta ya yi, hakan ya sa ta yin dariya.

“Kina so in aikata abinda bai kamata ba, ko in faɗi abinda bai kamata ki ji ba yanzun.”

Hannuwanta ta mayar cikin hijab ɗin da ke jikinta. Komai na Rafiq daban yake da na sauran mazan da ta taɓa cin karo da su a rayuwarta. Ita ya kamata ace tana jin kunyarshi, amma shi yake jin kunyarta. Ko tsaye suke, sai ya tabbatar akwai tazara a tsakanin su. Akan shi ta fara sanin menene so. Mecece ƙauna saboda Allah. Ta kula da yadda ya saka hannuwanshi cikin aljihun rigarshi, da yadda yake duk wani ƙoƙari na ƙin barin shaiɗan ya yi nasara wajen sa shi ya riƙe hannuwanta.

*****

Buɗe idanuwanta ta yi, muryarta a sanyaye, hawaye na bin gefen fuskarta take furta:

“Ka yafe min Sugar, Allah ya baka ƙarfin zuciyar yafe min, ba sai ka sake sona ba, ba sai ka sake yarda da ni ba, in ka yafe min zan yafe wa kaina laifin da na yi maka…”

Ta ƙarasa maganar ƙirjinta na ƙara zafi kamar an kunna mata wuta a cikin shi, hakan ya sa ta saurin runtse idanuwanta, tana ƙoƙarin fitar da numfashi a hankali, don hakan kamar ƙara mata ciwon da take ji yake yi.

*****

“Majee wai har yanzu?”

Altaaf ya Kjwalla mata kira, don ya rasa duminiyar da take yi wajen mintina ashirin, yamma na ƙara yi. Mutuwa ba ta sallama ga wanda za ta ɗauka, balle kuma makusantan shi, in ba haka ba, mai zai sa shi ɗaukar hanyar Kaduna da yammacin nan, jikin shi ma wani iri yake jin shi.

“Yi hakuri, kayan nike ida haɗawa.”

Murmushi ya yi yana girgiza kai, yadda Hausar Majida ba ta daina saka shi nishaɗi a ko a wane hali yake ciki na ba shi mamaki. Motsinta ya ji, ya juya yana kallonta da dogon hijab ɗin ta da har ƙasa take ja. ‘Yar ƙaramar jakar da ta haɗa musu kaya a ciki ta ajiye sai kuma wata ƙaramar jakar daban.

“Me za ki yi da jakunkuna har biyu?”

“Snacks ne na ɗiba maka, kar mu je ko ba ka cin abinda suka dahwa.”

Shiru ya yi yana kallon ta, akan ƙananan abubuwa irin wannan Majida kan nuna mishi yadda yau da gobe ta koya mata damuwa dashi.

“Miye kake kallona kamar ba ka sanni ba?”

Ta tambaya tana daƙuna mishi fuskarta da ta yi mishi kyau. Miƙewa ya yi, bai da kalaman da zai ɗora yanayin da yake ji a yanzun, don haka bai ma ko gwada ba, jakunkunan duka biyun ya ɗauka ya nufi hanyar waje.

Majida ba ta yi mamakin shirun shi ba, inda sabo ma yanzu kam ta saba, ba komai yake da amsa a wajen Altaaf ba, in shi ya tambaya fa dole a ba shi amsa, ko babu sai an nemo. Bayan shi ta bi da sauri ta riƙo hannun shi.

“Ba ka yin addu’a? Haka zaka hita…”

Tsayawa ya yi suka yi addu’a tukunna suka fita tare har wajen mota ya buɗe wa Majida ta shiga. Shi kam zagayawa ya yi ya buɗe ya jefa jakunkunan a bayan motar tukunna ya zauna.

“Jikina nake ji a sanyaye…”

Altaaf ya fada yana murza mukullin motar.

“Rasuwar nan ce, ka yi ta Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Kai ya ɗan dagae mata, yana fita da motar daga gidan ya hau titi Kjirjin shi ya yi wani irin bugawa kamar zuciyar shi za ta fito waje, da sauri-sauri yake maimaita Inalillahi wa ina ilaihi raji’un, bai faɗa wa Majida ba, amma akwai wani abu tattare da tafiyar da yake mishi wani iri. Ba ya jin akwai alheri a tattare da tafiyar, yana fatan sharrin zuciyar shi ne kawai. Shiru suke tafiyar har suka fita daga garin Kano suka soma shiga ƙauyukanta.

“Mi ke damun ka?”

Majida ta tambaya tana korar shirun da ya cika motar.

Muryarshi a sanyaye ya amsa,

“Babu komai. Me kika gani?”

“Yau baka yin gudu, wanda suke tahiya da machine har sun wuce mu.”

Tsoron taka motar yake ko bugawar da zuciyar shi take na da alaƙa da titin da suka hau.

“Kina kewar gudun da nake da mota ne?’

Dariya Majida tayi.

“Wacce kewa? Addu’a ta Allah ya amsa.”

“Oh! Wato Addu’a kika zauna kina min ko? Dame-dame kike roƙa? Faɗa min, hancina ya shige ciki kamar naki ko?”

Sosai Majida ke dariya.

“Ka ƙyale man hanci, a haka dai kake so, har sumba kake manna mai.”

Wannan karon shi ya yi dariyar.

“Allah ya shirya min ke.”

“Amin.”

Ta amsa tana mishi dariya. Ɗan gudun motar Altaaf ya ƙara, Majida kam bacci take yi, ya san hali, tafiya indai ta wuce ta awa ɗaya da Majida a mota sai ta yi bacci.

*****

Suna gab da shiga Zaria Magriba ta yi musu, lokacin Majida ta tashi, ya san za ta ce ya tsaya su yi Sallah, don haka ya faɗa mata ta bari su shiga Zaria. Ai kuwa haka aka yi, wani gidan mai ya samu da ke da Masallacin mata da na maza, suka yi Magrib, kafin nan suka sake ɗaukar hanya. Motar yake ji tana jerking don haka ya samu gefen hanya ya yi parking.

“Taɓɗi, Allah ya kiyaye kar motar nan ta yi mana tsiya kuwa…”

Altaaf ya faɗa yana fita, buɗe gaban ya yi, ya dudduba iya abinda zai iya ganewa tukunna ya dawo cikin motar. Sai dai me, babu yadda bai yi ba amma motar ta ƙi tashi.

“Mi ya same ta?”

Majida ta tambaya.

“Ban sani ba wallahi, shekaranjiya fa aka dudduba min komai.”

Altaaf ya fada ranshi a ɓace ya sake fita ya ƙara duddubawa ya dawo, wannan karon ta tashi, amma da ya fara takawa sai ta ci gaba da jerking, ga wani irin kuka da take yi.

“Bari in samu mu lallaɓa haka, ƙila ƙauyen da za mu samu a gaba ba za a rasa mai gyara ba…”

“Allah dai ya ida kaimu lahiya, ya sa karta sake macewa.”

“Amin dai…”

A hankali yake tafiyar har suka karasa ƙauyen. Hango wani mai rake da mutane zaune a wajen ya sa shi gangarawa da motar har wajen tukunna ya yi parking. Fitowa ya yi tare da yi musu sallama, bayan sun amsa ya ɗora da,

“Don Allah ko akwai mai gyara a ƙauyen nan, motata ke da ‘yar matsala…”

Ɗaya daga cikin su ne yace,

“Wai, mai gyaran mota?”

“Tawfiq mana.”

Ɗayan ya faɗa mishi ganin yana tunani.

“Tawfiq ɗan gidan Malam Bashari?”

“Eh shi.”

Jinjina kai ɗaya daga cikin su ya yi.

“Ai kam da wahalar gaske Tawfiq ya fito yanzun.”

Da sauri Altaaf ya ce,

“Don Allah ko za ku dubo min shi, ko nawane zan biya.”

“Aiba dubo shi ɗin bane wahala, sai dai ko muje tare, wataƙila in ya ganka yazo.”

Ɗan jim Altaaf ya yi kafin yace musu,

“Ina zuwa…”

Mota ya koma ya faɗa wa Majida, haɗi da ba ta mukullin motar.

“Ki kulle daga ciki, ki rufe glasses ɗin duka…”

Karɓa ta yi tana dariya.

“Sai kace yarinya?”

“Majee…”

Altaaf ta ya faɗi cike da kashedi. Rufe glasses ɗin ta yi da ƙofar daga ciki, tukunna ya juya ya koma, biyu daga cikin matasan ne suka tafi da shi zuwa gidan su Tawfiq ɗin da suke magana.

Kalle-kalle Altaaf yake yi, don akwai wuta a garin, ko ina tarau sai ɗai-ɗaikun gidaje da ba su da hasken Lanarki a ƙofar gidajen su. Daƙuna fuska ya yi, akwai wani abu tattare da ƙauyen da ya zauna mishi. Yana jin kamar ba yau bane karon shi na farko da zuwa ƙauyen.

“Ya sunan ƙauyen nan?”

Ɗaya daga cikin samarin ya amsa. Tari ya ƙwace wa Altaaf, don bugawar da zuciyar shi ta yi wannan karon har cikin maƙoshin shi ya ji tsallen, hakan ya sa maƙoshin ya bushe mishi kamar ya kwana bai sha ruwa ba.

‘Kuɗinka da matsayinka ba za su shiga tsakanina da illata ka fiye da yadda kai mana ba in har idona ya sake sauka akanka, ba ɗauri ba, ka saa ɓatar da ni, sai na illata ka in ka tako ƙafa hamsin tsakaninka da gidan mu.’

Wannan karon hanjin shi ne ya tattaru ya koma gefen cikin shi yana ƙullewa waje ɗaya. Ga zuciyarshi da ke ci gaba da bugawa. Girgiza kan shi yake yi, ba ya son tunawa, ba ya son gasgatawa. Babu yadda za a yi Alƙalamin Ƙaddara ya rubuta mishi dawowa ƙauyen nan ta wannan hanyar kuma a irin wannan lokacin.

‘Allah ya ɗauke maka farin ciki kamar yadda ka yi min, Allah ya tsayar maka da dukkan al’amuranka kamar yadda ka tsayar mana da namu, Allah ya tarwatsa maka rayuwarka ta fannin da baka taɓa zato ba, A-Tafida ko? In shaa Allah sunan ka kanshi sai ya zamar maka tashin hankali kamar yadda ya zamar min, ka ji ni? Wallahi ba za ka taɓa samun wadataccen farin ciki ba.’

Zufa ce ke tsatstsafo mishi ko ta ina, har cikin sumar kanshi, musamman tafukan hannuwanshi, shekaru bakwai da ɗoriya, amma jin maganganun su yake a cikin kanshi kamar yanzun suke furta su. Ya ɗauke shi fiye da shekara uku yana kokawa da ɓangarori da dama na zuciyarshi kafin ya dishe addu’ar can, kafin ya yakice yadda duk sanda ya tunata sai tsoro ya kama shi.

Don ba ya son yadda ta sa yake duba rayuwarshi, yake duba kamar ta canza Alƙalamin Ƙaddarar shi. Musamman in ya duba yadda ko kaɗan ba ya son wani ya kira shi da A-Tafida. Suna ne da ke tattare da abubuwan da ya yi rami ya binne, ramin da ko Majida ba ya so ta gifta ta wajen balle ta kula akwai shi har ma ta san me yake ciki. Ba ya son ya duba ya ga yadda addu’ar ta soma tasiri a kanshi, sai yanzun da yake cikin ƙauyen da ko a mafarki ba ya fatan ya sake takowa. Bai san ya tsaya da tafiyar da yake ba, sai da ya ji an dafa kafaɗar shi.

“Lafiya dai ko?”

Ɗaya daga cikin samarin ya tambaya ya na girgiza shi. Don ya yi mishi magana ya fi sau huɗu, amma zurfin da ya yi a tunani ya sa bai ji ba. Da sauri ya ɗaga mishi kai, ya samu muryarshi da faɗin,

“Ba na ɗan jin daɗi ne kawai, mun kusa?”

Jinjina kai suka yi su duka.

“Ayya, Allah ya ba ka lafiya, eh mun kusa, nan kwanar kawai za mu sha.”

Bin su kawai Altaaf yake yi, inda suka sa ƙafarsu nan yake mayarwa, amma ba wai don yana gane abinda yake faruwa a duniyar da take wajen shi ba. Ya tattara hankalin shi ne yana ƙoƙarin tsayar da shi kan samarin dake gabanshi. Ganin sun tsaya ya sa shi tsayawa shi ma, bangon gidan da suka tsaya ɗin ya jingina da shi, yana neman nutsuwa komi ƙanƙantarta.

‘Ka nutsu Altaaf, mai gyara kawai za ka tafi da shi , a duba muku motar ku wuce, babu abin da zai faru, babu abin da zai faru, yau za ta wuce, za ka koma kamar kullum, kamar komai da ƙauyen nan bai faru ba.’

Haka yake ta nanatawa a cikin kanshi, amma zuciyarshi ta ƙi amincewa, sallamar da samarin suka rafka ta sa shi kallon su. Sai da suka yi har sau biyu, tukunna Altaaf ya ji alamar motsi.

Da gudu wani yaro da ba zai shige shekara shida ba ya fito yana dariya, wata yarinya na rufa mishi baya. Bai san me ya sa idanuwanshi na sauka a kansu ya ji zuciyarshi ta yi tsalle tana son fitowa daga ƙirjin shi ta bisu ba. Fuskarsu yake ƙoƙarin gani.

“Hassan! Hussaina!”

Altaaf ya ji an faɗi a dai-dai bakin ƙofar, kafin wani saurayi ya fito da a tsayi da girman jiki ya fi Altaaf ɗin, ya bi bayan yaran dake wasan zagaye zagaye yana riƙo hannuwan su.

“Ba za ku sa min ciwon kai da daren nan ba, ku koma gida.”

“Kawu ni tare da kai zan koma…”

Macen da ya kira da Hussaina ta faɗi, muryarta na dira kunnuwan Altaaf da wani yanayi da ya sa zuciyarshi matsewa, idanuwanshi na fara sauka kan fuskar yaran da bakin shi ke motsi da alamar magana yake, amma sauti da duk wata ƙara ta daina isowa kunnuwan Altaaf. Ba ma sauti kaɗai ba, duka duniyar shi ta tattaru ta tsaya cak kan fuskar yaron, har cikin kunnuwanshi yake jin bugawar da zuciyarshi take yi, hannuwanshi duka biyun ya kai yana shafa fuskarshi, yana son tabbatar wa da kanshi cewar tana nan tare da shi.

Sosai yake shafa fuskar shi, sai da ya ji daga bakin shi, ido, hanci duka suna nan jiki tukunna ya sauke hannunshi yana sake ware idanuwanshi kan yaron, duk da fuskarshi ya ji ta a jikinshi, kuma ta yaron ta fi tashi ƙaranta bai hana shi jin kamar tashi aka cire aka liƙa a jikin ta yaron ba.

Ammi na son hoto, tun da can, din tarin Albums ɗin su kawai da hotuna tun suna yara da tasowarsu kawai za ka gani ka san haka. Ya san yadda yake yana shekarun yaron nan da ke tsaye, kuma kamar shi ne aka ciro aka ajiye. Da ƙyar ya iya ɗauke idanuwan shi daga kan yaron yana mayarwa na yarinyar.

Ɗankwalin da ke kanta ya kalla, cikin zuciyarshi ya hango yadda zai yi in an saka mishi kayan mata, kuma kama zai yi sak da yarinyar. Bai san ƙafafuwanshi sun ƙarasa da shi wajen ba, sai da yaji su cikin durƙushe cikin ƙasa.

Kusancin da ke tsakanin shi da Ammi mai girma ne, amma ba iri ɗaya bane sam da kusancin da yake ji tsakanin shi da yaran nan. Ko Majida kusancin ta daban yake da abinda yake ji yanzun. Yanayi ne da babu kalaman da za su yi mishi adalci.

Hannu ya kai zai taɓa su ko zai tabbatar da gaske yana ganin su, ya ji an hankaɗe shi har yana faɗuwa a zaune cikin jar ƙasar da ke wajen.

“Malam lafiya? Meye haka?”

Saurayin da Hassan ya kira da kawu ya faɗa a tsawace, haka ya dawo mishi da sauti cikin kunnuwan shi, su kuma yaran suka koma bayan ƙafafuwan shi suka ɓoye suna leƙen Altaaf ɗin.

“Tawfiq tare muke…”

Ɗaya daga cikin saurayin ya faɗa wanda hakan ya sa Tawfiq juyawa ya kalle su.

“Lafiya?”

Ya buƙata don har lokacin a harzuƙe yake, bai ma jira amsar su ba ya sake juyowa yana kallon Altaaf, wannan karon ya tsaya akan fuskar shi. Sosai yake kallon shi. Ƙasumbar da ke kwance a fuskarshi bai hana kamannin shi da Hassana da Hussaina ƙin fitowa ba.

Ware idanuwa Tawfiq ya yi ya saka hannuwa duka ya ja yaran ya sake mayar da su bayan shi cikin son kare su daga Altaaf. Miƙewa Altaaf ya yi yana kallon Tawfiq, ya buɗe bakin shi yana rufewa ya fi sau biyar. Marin da Tawfiq ya ɗauke shi da shi ne ya saka haske gilmawa ta cikin idanuwanshi kafin ya ji wani tsuu cikin kunnen shi na gefen dama…!

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 1Alkalamin Kaddara 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×