Skip to content
Part 8 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Bata koma asibitin ba sai bayan sallar isha’i. Don ko tsoron daren ma bata ji ba sam. Hannunta damƙe da ledar da kuɗin da ta siyarwa Alh. Madu jikinta ya bata. Dubu ɗari ya bata cif tare da alƙawurran ko me take so ta zo wajenshi zai bata da sauran surutai da bata bari sun zauna mata ba. 

Tana shiga asibitin ta ƙarasa inda su Ummi suke ta taso da faɗin, 

“Kin samo kudin Tasneem?”

Ledar ta fiddo daga Hijabinta ta miƙa wa Ummi tana samun waje gefen Hamna dake rungume da Sabeena da ta yi bacci ta zauna. Ummi kuma na barin wajen. 

“Ina kika samo kuɗi?”

Hamna ta tambaya. Ba tare da Tasneem ta kalleta ba ta ce, 

“Ba satowa na yi ba.”

Yadda ta ji Hamna ta gyara zama kusa da ita yasa ta jin wani iri da yanayin data yi mata magana. Ba tare da Hamna ya kamata ta raba laifinta ba, don bata yi komai ba. 

“Ki yi haƙuri.”

Hamna ta faɗi muryarta a sanyaye da alamar kuka. Sauke numfashi Tasneem ta yi. 

“Alh. Madu ya bani.”

Kai kawai Hamna ta ɗaga ba tare da ta ce komai ba. Sai kanta data jingina a kafaɗar Tasneem ɗin da take ji kamar ta tureta don bata son dauɗar da take jikinta ta shafi Hamna ko kaɗan. Duk da ta yi wanka ya fi a ƙirga a gida kafin ta taho ta yi salloli, a sujjadarta ne kawai hawaye suka zubo mata. Daga shi ko ɗigo har yanzun. 

Anan suka kwana. Ga sauro ga rashin abinda za su ko shimfiɗa. Don ita Tasneem ko runtsawa bata yi ba. Idanuwanta ma da ta lumshe dole ta buɗe su. Saboda babu abinda take gani banda Alh. Madu da ƙazantar da suka aikata. 

*****

Sai ƙarfe goma na safe tukunna aka fito da Azrah zuwa wani ɗaki aka kuma basu damar cewar za su iya zuwa su ganta. Haka suka shiga suka zauna. Su shida ne a ɗakin, Ummi ta fita bakin asibitin ta siyo musu fanke da lemuka, amma ko ɗanɗane Tasneem ba ta ci ba. Haka ta ajiyeshi a gefe ta zuba wa Azrah idanuwa. 

So take ko motsi ta ga ta yi. Amma shiru har Azahar. Ummi da Hamna suka koma gida don su dafo wani abin, kuma Hamna ta taya Ummi su kawo musu kayan da za su ɗan buƙata. Suka bar mata Sabeena. Sai bayan sun tafi ne tukunna Tasneem ta riƙo hannun Azrah don ɗayan jini ake ƙara mata. Dumtsewa ta yi cikin nata tana jin yadda hannun ya yi sanyi ƙarara. 

Ɗago hannun ta yi tana kwantar da fuskarta a jiki. 

“Azrah ki taimaka min ki tashi…bansan ya zanyi in baki tashi ba. Ganin idanuwanki a buɗe zai bani ƙwarin gwiwar ɗaukar nauyin abinda na aikata don lafiyarki…don Allah ki tashi haka… Ki tashi in ji muryarki ko zan ji sauƙi…”

Ta ƙarasa hawaye sirara na zubar mata. Motsi ta ji hannun Azrah yayi cikin nata, da sauri ta buɗe idanuwanta tana kallon fuskar Azrah ɗin da ta buɗe nata idanuwan da ƙyar kamar hakan kawai na mata wahala. 

“Ruwa…”

Ta faɗi can ƙasa, ba don hankalin Tasneem gaba ɗaya na kanta ba da ba zata ji abinda ta ce ba. Ruwan da ke ajiye gefe Tasneem ta ɗauka da sauri tana ɗago kan Azrah ɗin a hankali don naɗe yake da bandeji bata kuma san inda yake da ciwo a jiki ba ta bata ruwan. Kurɓa biyu ta yi ta kauda kai. Ajiyewa Tasneem ta yi.

“Azrah…”

Ta faɗi hawaye na sake zubo mata, wannan karon wani nauyi ne ta ji ya ɗaga daga ƙirjinta da zubar hawayen. Nauyin da ya danneta na rashin tabbas akan tashin Azrah. 

“Na ɗaga miki hankali ko? Ina kika samo kuɗin magani na? Tun yaushe nake nan?”

Azrah ta faɗi tana runtse idanuwanta da alama ƙarfin hali kawai take. Tasneem girgiza mata kai take saboda kukan da take ya hanata magana. Hannun Azrah kawai ta riƙe tana ci gaba da kuka sosai. Shiru kawai Azrah ta yi tana dumtse hannun Tasneem ɗin cikin nata. 

*****

Satin su biyu a asibitin da Azrah, Ummi take kwana a wajenta wani lokaci da Sabeena. Da yamma ita da Hamna suke komawa gida. Kafin a nemi wani abu Tasneem ta ba Ummi kuɗin, sai dai tana kula da bata su a gaban su Azrah. Musamman Hamna da ko sun dawo gida ta fita in ta dawo haka zata tsareta da idanuwa cike da tuhuma kamar ta san abinda ta aikata. 

Tun abin yana damunta har ya daina. Ko me zatayi akan kula da su zata yi. Kuma zata tabbatar rayuwarsu bata faɗa inda tata ta yi ba. A asibitin ne ta samu ƙawa, Kausar da ta ke jinyar mahaifiyarta a ɗakin da aka ajiye su Tasneem ɗin. Sosai shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, don ko bayan an sallami su Tasneem ɗin tana zuwa duba mamansu Kausar. 

Haka ma bayan an sallame su basu yanke zumuncinsu ba. Takan zo har gidansu Tasneem, ita ma tana zuwa gidansu da ke Gwammaja. Inda duk Tasneem take son zuwa Ummi bata hanata, bama tambayarta take ba, ba kuma koda yaushe take ce mata ta fita ba. Su Azrah kawai take faɗa wa ta fita da kuma lokacin da zata dawo.

*****

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiyar musu, a hankali wata irin wayewa take shigar Tasneem, haka ta ce wa su Hamna ta sake samun aiki a wani kamfanin buga leda saboda tambayoyinsu sun fara isarta. Unguwa duka babu wanda bai san tana tare da Alh. Madu ba yanzun. Don ana ganinsu suna yawo a gari yana kuma zuwa gurinta. 

Haka yanzun da wahalar gaske ka ga mai mai babur yazo wajen Tasneem. Alhazawane ‘yan kasuwa manya. In babu kwalliya a fuskarta ba lallai ka sake mata kallo na biyu ba. Don tana da duhu kamar Abba, duk da ba za ka kirata fara ko chocolate ba, su Hamna ne suka yi fari da kyawun Ummi. Hancinta ba tsayi gare shi ba, haka bawata doguwa bace ba kuma siririya ce sosai. Haƙoranta na gaba manya ne sosai, duk da ba fitowa waje suka yi ba, irin haƙoran da mutane ke ma laƙabi da na zomo. Su dukkansu banda Sabeena haka haƙoransu na gaba suke, don Ummi suka biyo.

Wasu lokuta takan rasa abinda maza suke bi a tare da ita. Ƙalilan matasan da ke cikin samarinta kan jata wajajen shaƙatawa, anan ta yi ƙawaye da suka ƙara buɗe mata idanuwa suka kuma ƙara wayar da ita yadda zata karɓi kuɗin samari ba tare da wani babban abu ya shiga tsakanin su ba. Ta rasa lokacin ranar da ta wayi gari ta daina jin laifin da take aikatawa. 

Amma ya ɓace mata. Yanzun ta saba da riƙe kuɗi sosai. Ta kuma saba da jin daɗi. Ga wani irin shiri da suke da Ummi don duk faɗan nan ta daina. Haka kusan ko da yaushe tana gida. Shi yasa tun maƙota na kawo mata magana akan Tasneem har suka bari, don ta ɓata da kowa akan Tasneem a cewarta baƙin ciki ne kawai don an ga ‘yarta na da farin jini. Komai kuma ya canza musu, tana aikinta tana samun kuɗi shi yasa. 

Yanzun gashi har Azrah da Hamna na ajinsu shida a makaranta. Girmansu na bata mamaki. Musamman Hamna da kyawunta yake ƙara fitowa. Haka samari ke musu zarya, amma Tasneem ta hana su tsayawa da kowa, Ummi kuma ta goyi bayanta tunda ita take da gidan yanzun. Abinda duk take so shi ake yi. 

Yau ma kamar ko da yaushe saurayinta ne Baffa ya zo wajenta shi da abokinshi TJ da kuma budurwar TJ ɗin Aliya. 

“Gaskiya Tasneem za ki yi missing in baki je wajen nan ba. Kuma wallahi Jennifer ba zata ji daɗi ba…”

Aliya ta faɗi, Jennifer ƙawarsu ce ita ma, yaren Igala ce girman Kano, ta ji Hausa kamar me. Ita ce take shagalin ranar zagayowar haihuwarta, kuma ba za’a fara shagalin ba sai ƙarfe goman dare, a cewarsu kwana za’a yi. Ba zuwa bane bata son yi, ba zata kwana a wani waje ba. 

Abinda bata taɓa yi ba kenan, duk yawon da ta fita ƙarfe bakwai hankalinta in ya yi dubu a tashe ta dawo gida, don in ta yi dare bata san me zata ce musu Hamna ba. Ko ƙarya ta yi Azrah ta yarda a idanuwan Hamna take ganin ta san ƙarya take yi. Bata damu da maganganun mutane akanta ba, bata damu da mutuncinta a idanuwansu ba. Don bata jin sauran mutunci a tare da ita. Amma ta damu da yadda su Hamna za su kalleta. 

“Ai ba ƙaramin kwafsa min za ki yi ba wallahi.”

Baffa ya faɗi yana kallonta da idanuwan shi da su kaɗai ne abinda ke mata kyau a tare da shi. Ƙasa ta yi da muryarta

“Ka san bazan iya zuwa ba. Da da yamma ne.”

“Kabarta sai mu yi maka sabuwar budurwa kawai.”

TJ ya faɗi yana kashe mata ido ɗaya. Hararar shi ta yi bawai don ta damu da budurwar daya ce zai ma Baffa ba. Tasan ba ita kaɗai bace budurwarshi kamar yadda ya san ba shi kaɗai bane saurayinta. Zuciyarta su Azrah ne kawai a ciki, bata da wajen wata damuwa bayan tasu. 

“Ni kam zan shiga gida. Kar in tsayar da ku. Aliya ki ba Jennifer haƙuri don Allah.”

Tasneem ta faɗi, hannunta Baffa ya riƙo yana marairace fuska. Murmushi Tasneem ta yi mishi daya tsaya iya fuskarta. 

“Da gaske tafiya za ki yi ki barni? Haba Pretty karki min haka mana…”

Hannunshi da ke riƙe da nata ta dumtse tana murza yatsun shi. 

“Ka yi haƙuri ba…”

“Tasneem?”

Ta ji kamar daga sama. Juyawa ta yi , hasken motar da TJ yake ciki ya tayar yana haska mata shi gaba ɗaya, kafin zuciyarta ta yi wani tsalle tana dawowa kan harshenta. Inda idanuwanshi yake ta fara kallo tana sakin hannun Baffa da sauri kamar wuta, tukunna ta mayar da hankalinta kan Tariq da idanuwanshi suke kafe a kanta yanzun. 

“Baffa ka je za mu yi magana…”

“Pretty…”

Ya fara ta katse shi ba tare da ta kalle shi ba. 

“Ka je za mu yi magana.”

Ta sake maimaitawa tana takawa ta ƙarasa inda Tariq yake tsaye yana kallonta har lokacin. Zuciyarta na ci gaba da dokawa take kallonshi. Shekaru wajen uku kenan rabon da ta sashi a idanuwanta. Ya canza sosai, kallon yadda ya yi tsayi da girma take yi, don da wahala kanta yakai ko kusa da kafaɗarshi. Ga suma cike da kanshi, sai dai akwai wani abu tattare da idanuwanshi da bata so.

“Tasneem…”

Tariq ya kira da mamaki, kamar yana son tabbatar ma kanshi ita ɗin ce ba wai ƙarya idanuwanshi suke mishi ba. 

“Ya Tariq…”

Tasneem ta faɗi tana kallon shi itama cike da mamaki. Tun tunaninshi na damunta har ta samu waje gefen zuciyarta ta danna shi ta adana. Hannunshi ya ɗaga kamar zai taɓa fuskarta. 

“Tasneem…”

Ya sake faɗi yana kasa samun wasu kalamai banda sunanta, yana son yace mata ta canza daga kwalliyar dake fuskarta zuwa komai nata, amma ya kasa samun kalamai, sun maƙale mishi. 

“Ka canja sosai…”

Murmushi ya yi mai sauti yana sauke hannunshi. 

“Kin canja kema…”

Ɗan ɗaga kafaɗunta ta yi, tana jin zuciyarta ta matse gefe ɗaya da jin zafin rashin shi na shekarun nan, tana jin yanayin mantawa da ya yi da ita na danneta. Hakan da ya kula da shi a fuskarta yasa shi faɗin, 

“Ban manta da ke ba, wallahi ban manta da ku ba…”

Cikin idanuwa take kallon shi.

“Shekaru nawa? Ina ka je? Babu kalar tunanin da ban yi ba Ya Tariq…”

Tasneem ta ƙarasa muryarta na rawa, tana jin kamar kuka ne ke shirin zuwa mata, abinda ta jima bata ji alamu ba, saboda ganin shi na son farkar mata da wani ɓangare daya daɗe da yin bacci a tare da ita. Haɗiye yawu ya yi don maoshin shi ya bushe da yanayin da bashi da alaƙa da ƙishin ruwa.

“Akwai dalili…”

Ya faɗi yana yin shiru, itama shirun ta yi tana saurarenshi ya ci gaba. Ko me zai faɗa ta san ba zai sake komai ba, lokaci ya riga ya ƙure mata, ya zo a makare, daya zo lokacin da take neman wani ko yaya ne ya faɗa mata akwai wata hanya banda wadda ta bi, ya haska mata duhun da ke mamaye da ita ko yaya ne, ƙila da bai zauna tare da ita har haka ba. 

Jin bashi da niyyar ƙara cewa komai ya sa muryar Tasneem ɗin can ƙasa ta ce, 

“Ka makara…”

Idanuwanshi ya ware a kanta yana son gane me take faɗa, jinjina mishi kai ta yi. 

“Ka makara Ya Tariq… Abubuwa da yawa sun faru. Ka makara….”

Ƙarar da ta ji ya katse mata kalamanta, yana saka Tariq ɗauke idanuwanshi daga cikin nata, hannu yasa a bayan aljihunshi ya ciro wata ƙaramar waya yana dubawa, runtsa idanuwanshi ya yi yana buɗe su akanta da faɗin,

“Zan dawo Tasneem, zan dawo…”

Murmushi ta yi da ke nuna alamar bata yarda da kalamanshi ba. 

“Yaya Ashfaq ne, na san yana tunanin ina naje ne saboda bai san na fito ba. Amman zan dawo…”

“Me yasa?”

Ta tambaya. 

“Me yasa me?”

Ya amsa cike da rashin fahimtar tambayarta. 

“Me yasa ka fito baka faɗa mishi ba?”

“Saboda in ya sani ba zai barni ba.”

Ya ƙarasa muryarshi can ƙasa. Shiru ta yi na wani lokaci, wayar Tariq ɗin ta sake ɗaukar ruri. 

“Ka ɗaga mana…”

Girgiza kai ya yi yana faɗin, 

“Zan dawo…”

Kai ta ɗaga mishi. Bai sake cewa komai ba ya juya da sauri, tsaye ta yi sai da ta ga yasha kwana tukunna ta sauke wani numfashi da batasan tana riƙe da shi ba, ta juya tana shiga cikin gida. Mayafinta kawai ta ajiye, Hamna ta ce, 

“Kin dawo da wuri.”

Ba zata iya da Hamna ba da daren nan, bata ma jin ƙarfin jan magana. Ganin Tariq na son hargitsa mata lissafi. 

“Ya Tariq ya zo. Amma ya koma ya ce zai sake dawowa.”

Shiru Hamna ta yi na tsawon lokaci, har sai da Tasneem ɗin ta yi tunanin ko bata jita ba, buɗe baki ta yi zata sake maimaitawa Hamna ta rigata da faɗin 

“Ya yake?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Tasneem ta yi. 

“Ya canja…”

“Canji mai kyau ko marar kyau?”

Hamna ta tambaya, ɗan shiru Tasneem ta yi, banda yanayin da ta gani a idanuwanshi, zata iya cewa canjin shi me kyau ne, kayan jikinshi tsaf suke, haka shima tas da shi harma da waya a hannunshi, duk da yadda take tsada a wannan lokacin.

“Me kyau.”

Jinjina kai kawai Hamna ta yi tana sauke numfashin da ita kaɗai ta san tana riƙe da shi. Komawa ta yi kan katifa ta kwanta tana juya bayanta, wata irin kewar Tariq ɗin na mata sallama. Sanin mintina kaɗan da suka wuce yana ƙofar gidansu yasa zuciyarta matsewa. 

Ta daina maganarshi ne saboda shirun ya yi yawa, saboda bata son zuciyarta ta fara tunanin wani abu ya same shi. A duk fitar da zata yi haka take kallon fuskokin samari ko zata ga tashi a ciki. Wasu siraran hawaye suka zubo mata masu ɗumi. 

‘Karka daɗe wannan lokacin Ya Tariq, don Allah karka daɗe.’

Take maimaitawa cikin zuciyarta kamar hakan zai sa saƙon ya isa gare shi. Hannu ta sa tana goge hawayenta tare da ƙara gyara kwanciyarta tunda ta yi isha’i bata jin zata sake tashi. Komai ya tsaya mata waje ɗaya, babu wani abu a cikin kanta banda fuskar Tariq da tunanin yadda Tasneem ta ce ya koma, hoton da zuciyarta ta hasko mata na sata yin murmushi. A haka bacci ya ɗauke ta cike da mafarkin shi. 

*****

Sai da ta yi sallar Asr tukunna ta shirya, yau banda hoda bata shafa wa fuskarta komai ba, atamfa ta saka ɗinkin doguwar riga sai ta ɗauki hijabin Hamna ta saka, har ƙasa yake ja mata don Hamna ta fita tsayi, Ummi na zaune tana tsintar wake da alama abincin dare zata ɗora. 

Tasneem ta bita da kallo cikin jinjina yadda rayuwa ta canza musu, Ummi ce da zaman gida da girki, ita kuma da fita, girgiza kai ta yi sannan ta ce, 

“Ummi zan je gidan su Kausar.”

“Ki gaishe da su. A dawo lafiya.”

“Allah yasa.”

Tasneem ta amsa tana ficewa. A ranta tana ƙudirtar zata yi wa Alh. Madu magana ya siya mata waya ko wani daga cikin samarinta don ta gaji da zama shiru haka. Da tana da waya da yanzun ɗaya daga cikinsu zata kira ya zo ya kaita ba sai ta shiga motar haya ba. Da tunanin a ranta ta taka zuwa titi. 

Takalma ne dogaye a ƙafarta, kuawayen da take haɗuwa da su suka koya mata saka dogoyen takalmi, aikuwa bata kula da wani dutse ba ta taka, gurɗewa ƙafarta ta yi, saura kaɗan ta faɗi, sai dai ba faɗuwar bace tasa zuciyarta dokawa, muryar da ta ji an ce, 

“SubhanAllah…”

Don ko kaɗan tunanin kiran Allah bai zo mata ba. A hankali ta ɗago kai tana sauke idanuwanta cikin nashi, ruwan ƙasa mai haske, kalar da bata taɓa gani a idanuwan duk mutanen da ta sani ba. Da shadda ruwan ƙasa mai duhu sanye a jikinshi. Shi ma kallonta yake, kafin a hankali ya ce, 

“Ba ki ji ciwo bako?”

Kai ta ɗaga mishi tana sauke idanuwanta daga cikin nashi, saboda yadda ta ji jikinta ya ɗauki ɗumi, kwarjinin shi ya cika mata zuciya, abinda bata taɓa ji game da wani ɗa namiji ba. Muryarta da wani irin sanyi ta ce, 

“Nagode…”

Tana duba ƙafarta da gyara takalminta ta soma tafiya, duk da ƙafafuwanta sun mata nauyi na rashin dalili. Ji ta yi kamar ana binta a baya hakan yasa ta juya, fuskarshi ya daƙuna mata. 

“Baki faɗa min sunanki ba.”

Ya faɗa muryarshi da yanayin mamaki, kamar yana mamakin dalilin da zai sa ya so jin sunanta, ba kuma a muryarshi kawai ta ji ba har a fuskarshi da take a daƙune har lokacin. Kawai sai ta ji ranta ya ɓaci. 

“In kana mamaki ne, to dalilin me yasa ka tambaya?”

Sake daƙuna fuska ya yi. 

“Excuse me…”

Ya ce yana kallonta. 

“Sunana nake nufi… Me yasa ka tambaya?”

“Saboda ina son sani.”

Ya amsa yana tsura mata idanuwan da ‘yan mintina kaɗan da fara ganinsu sun samu waje a tare da ita sun yi zaune. 

“Tasneem…”

Ta tsinci kanta da faɗi, abinda ta sake jimawa bata yi ba, tun tana sabon shigar samari kafin ta waye.

“A nan unguwar kike?”

Ya sake buƙata. Ɗaga mishi kai ta yi. 

“Ki min magana da bakin ki.”

Kallon fuskarshi ta yi wannan karon, yana da kyau dai-dai nashi, amma akwai samarin da ta yi da suka fi shi kyau, duk da akwai kwarjinin da take gani a fuskarshi da bata taɓa gani a ta samarinta ba, hakan baya nufin zai dinga buƙatar abu a wajenta kamar ya santa. Buɗe baki ta yi don ta ce mishi zai iya ɗaukar fuskarshi da idanuwanshi masu kyau ya maida su inda suka fito amma sai ta samu kanta da cewa, 

“Eh, nan unguwar nake. In ka miƙe layin nan kwanar farko.”

Kafin ta gama mamakin abinda ta yi ya ɗan ɗaga nashi kan, tare da juyawa ba tare da ya ce mata komai ba. Har ta shiga mota tana ma kanta faɗa a zuciyarta. Dole ya tafi ya barta a tsaye ba tare da ya ce komai ba, daga tambayar ko nan unguwar take ta saki baki har da faɗa mishi inda gidansu yake. 

Gidan su Kausar ɗin ma da taje bata wani daɗe ba, don gaba ɗaya hankalinta baya jikinta, fuskarshi ta mata tsaye a zuciya ta rasa yadda zata yi. Har Kausar ta kula akwai abinda yake damunta. Da zata rakota ta hau motar dawowa gida sai da ta tambaya ta ce mata babu komai. 

Haka ta dawo gida da sanyin jiki. Haka kuma ta yi kwanaki har biyar da tunanin shi, ta san zata bari na wani lokaci, don mamakin shi ne kawai da abinda ya yi mata da babu namijin daya taɓa mata shi, in mayyar zuciyarta ta gaji zata daina damunta da tunaninshi da idanuwanshi. 

A ranar bayan Magriba suna zaune a ɗaki, Sabeena na kwance a jikinta yaro ya yi sallama ana kiranta.

“Sabeena ɗaga ni in ga waye…”

Ta faɗi ranta a ɓace tana ɗaukar hijabin da ta yi sallah da shi, don a kwana biyun nan babu inda ta je, bama ta son ganin kowa, bata kuma son faɗa wa kanta dalilin hakan. Fuskarta babu walwala ta fita, unguwar fayau da yake akwai hasken lantarki. Zuciyarta ta yi wani irin dokawa a ƙirjinta ganin shi jingine jikin motarshi da farin kaya a jikinshi, har hularshi fara ce, hannuwanshi naɗ a ƙirjinshi. 

Takawa ta yi tana zuwa inda yake, zuciyarta na ci gaba da dokawa musamman da taga fuskarshi kurkusa, rannan bata kula da ƙasumbar da ke kwance a fuskarshi ba saboda idanuwanshi sun ɗauke mata hankali, bata kula da abubuwa da yawa a tattare da shi ba. Har lokacin bai kalleta ba, idanuwanshi na kafe a wani waje daban da inda take. 

Zuciyarta na ƙara gudun dokawar da take ta jingina bayanta da motar da yake jingine a jiki shima, ba don ta gama kallon shi ba, sai don tana ganinshi kamar wani ƙaton kogi da ta fara saka ƙafafuwanta a ciki, tana jin in ta ci gaba da tafiya nutsewa za ta yi a cikin shi ba tare da ta san abinda zata samu ba ko ya zata yi ta fito ba. 

“Me nake yi anan?”

Ya faɗi da alama a zuciyarshi ya yi niyyar maganar bai kuma san ta fito fili ba. Runtsa idanuwanta Tasneem ta yi don jin maganar ta taɓa wani waje a ƙirjinta da ya yi mata ciwo. Tsintar kanta ta yi da yi mishi sallama. Sai lokacin ya juyo kanshi yana kafa mata idanuwa ba tare da ya amsa ba. Tana jin yadda idanuwanshi ke yawo kan fuskarta kamar mai neman wani abu, kafin ya amsa sallamar a hankali. 

Wani yanayi ta ji ya lulluɓeta da ta kasa gasgatawa, don ta san sun yi hannun riga da kunya da jimawa, babu dalilin da zai sa ta ziyarce ta a wannan lokacin.

“Dare yayi ki koma gida…”

Ya furta muryarshi a daƙile kamar ta mishi dole. Bata ce komai ba ta raba bayanta daga jikin motar da take zaton tashi ce, ba don bata da abinda zata ce ba, sai don wani abu ya mata tsaye a maƙoshi. Tunawa ta yi ko sunanshi bata sani ba, in har a gani na biyu yana saka zuciyarta gudu haka, yana saka jikinta ɗaukar ɗumi ya kamata ta samar wa fuskarshi suna a zuciyarta. 

“Ya sunanka?”

Ta buƙata ba tare da ta juyo ba. 

“Rafiq Mustafa Shettima.”

Ya faɗi, ci gaba ta yi da tafiya, tana jin muryarshi na binta, tana kuma jin yanayin da ya faɗa mata sunan da shi, kamar a cikin sunan akwai saƙon da yake son faɗa mata, kamar a cikin sunan akwai dalilin tambayar da ya yi wa kanshi ta ‘me yake a wajen ta’, a cikin yanayin akwai abubuwa da yawa da ta kasa fahimta saboda komai tare da Rafiq Mustafa Shettima na mata ihun banbancin da ke tsakanin su. 

*****

Tari ya sarƙeta da ta soma ba ƙaƙƙautawa tana jin ciwon shi daga zuciyarta da yadda ta buɗe tsofaffin tabo suna zubda jini. Rafiq ko motsi bai yi ba har ta samu tarin da take ya tsagaita mata. Kallon shi ta yi 

“Kasan abin da ya faru daga nan…. Daga haɗuwar mu da kai zuwa yanzun…”

Ta ƙarasa da wani irin wahaltaccen yanayi. Idanuwanta take so su sauka cikin na Rafiq ko zata fahimci kaɗan daga cikin abinda labarinta yasa shi ji, amma ya ƙi yarda su haɗa idanuwa. A hankali ya miƙe tsaye yana juyawa da niyyar barin wurin. 

“Sugar… Tsaya… Karka tafi… Ka ce wani abu don Allah ka ce wani abu…karka tafi…”

Tasneem ke roƙon shi hankalinta a bala’in tashe, ƙoƙarin miƙewa take amma ta kasa, saboda bata jin ƙarfi ko kaɗan, tana kallon Rafiq ko alamar ya ji me take cewa bai nuna ba ya bar falon yana nufar ɓangarenshi. Ƙarar doko ƙofar shi na haɗawa da wani ɓangare a zuciyarta.

Kano

Sakin Tariq ya yi yana miƙewa da shirin fita daga ɗakin. 

“Ina za ka je?”

Ashfaq ya buƙata muryarshi can ƙasa, idanuwanshi ɗauke da wani nisantaccen yanayi. 

“Zan kira likita ne…”

Dariya Ashfaq ya yi sautinta na mishi wani iri a jikinshi. Da ɗayan hannunshi ya nuna Tariq da ko ina na jikinshi ke ɓari, idanuwanshi sun yi wani fari, ya kalle shi tukunna ya maida kallonshi kan Yasir da faɗin, 

“Ba likita yake buƙata ba…babu abinda likita zai mishi a wannan yanayin Yasir.”

Ashfaq ya ƙarasa muryarshi na sauka ƙasa sosai. Girgiza kai Yasir ya yi. 

“Kasan haɗarin, Faq kasan zai iya komawa gidan jiya…”

Cikin fuska Ashfaq ya kalli Yasir ɗin da ke girgiza kai cike da alamar rashin yarda. 

“Meye bambancin? Bazan iya mayar da shi wajen nan ba…. Wallahi bazan iya ba”

Ƙofar Yasir ya daka da hannunshi kamar zai karyata, kafin ya tura hannu cikin sumar kanshi yana sake hargitsa ta. 

“Ka bashi kawai… Nasan akwai a jikin ka…”

“Faq…”

Hannu ya daga mishi. 

“Na san baka daina ba…Kamar yadda nasan shima bai daina ba. Ka bashi kawai.”

Ba tare da musu ba Yasir yasa hannunshi a bayan aljihunshi ya zaro takardar da ke ɗauke da cocaine, nufo inda Tariq yake kwance ya yi. A gefenshi ya yi layi biyu da cocaine din dogaye, a ƙasa kan tile yana sa hannu daya ya mirgino da Tariq ta wajen.

Tariq kam da yake jin kanshi na shirin tarwatse wa saboda surutan da ke ciki, Yasir na mirgino ta gefen idonshi ya fara ganin layin cocaine din, ba sai an faɗa mishi ko menene ba, cikin bacci yana da tabbacin zai jita in tana kusa da shi. Hannunshi da ke kyarma ya ɗago yana gyarata tare da kai hancinshi wajen, ja ɗaya ya yi ya zuƙe layin. Runtsa idanuwanshi yayi gam yana jin shigarta har cikin ƙwaƙwalwar shi. 

Ya kai minti biyu a haka kafin ya buɗe idanuwanshi ya sake zuƙe ɗayan, sake runtse su ya yi yana mirgina kwanciyar da ya yi tare da dunƙule jikinshi waje ɗaya yana jin wata irin nutsuwa na saukar mishi, a hankali yake jin surutun da ke cikin kanshi na ragewa, jijiyoyin jikinshi da suke rirriƙe suna koma mishi dai-dai. 

Duk abinda yake Ashfaq bai ɗauke idanuwanshi daga kan Tariq ba, kallon shi yake da wani irin ciwo a zuciyarshi. 

“Ina so in bari… Da duk zuciyata ina so in daina amma na kasa. Ina ganin komai kamar yanzun ya faru… Tana dishe min wannan ɓangaren…”

Yasir yake faɗi a hankali. Yana so Ashfaq ɗin ya gane, yana so ko yaya ne ya fahimce shi, ya fahimci Tariq, don yanayin da ke idanuwanshi yasa zuciyar Yasir ɗin riƙewa ta ɓangarori da dama. Baya so ya ƙara mishi matsaloli fiye da wanda yake ciki, baya son ya ɗora mishi damuwar shi akan tarin wadda yake ɗauke da ita a kullum.

“Na ɗauka abinda ya samu Tariq ya isa yasa ka bari, na ɗauka ka gane da duk ja ɗaya da yadda kake nisanta da hankalinka da lafiyarka…cocaine da ƙwayoyi ne za su raba ku da hankalin ku, damuwar ku ce zata yi sanadin nawa.”

Ashfaq ya ƙarasa yana gyara zamanshi kan gadon tare da jingina bayanshi sosai. Yasir bai ce komai ba, ba don bashi da abin faɗa bane, sai don yanayin Ashfaq daya nuna ba zai saurara ba. Takawa ya yi ya ja kujera ya zauna suna zuba wa Tariq da yake shirin tashi zaune idanuwa. 

Ba zaman ya yi ba. Miƙewa ya yi gaba ɗaya, idanuwanshi sun sake launi, cocaine ɗin da ya ja na saka shi jin babu wani abu da zai iya taɓa nutsuwar da ke duniyarshi. Hannu yasa yana danne hancin shi da ya ja. Kafin ya sauke yana kallon Ashfaq. Cikin muryarshi da ta ƙara buɗewa ya ce, 

“Kasan me? Ban ma san rashin hankalin daya sani ɗauka zaka yarda na ga Ya Yasir ba… Ko me zan sha, ko me zan ƙi sha ba zai hanani gane shi ba… Na san bambancin abinda nake gani a cikin kaina dana zahiri…”

“Ka samu wajen zama Tariq.”

Ashfaq ya faɗi cike da kashedi. Hannuwanshi Tariq ya naɗe a ƙirjinshi.

“Saboda me? Da ka bishi ranar ƙila da ka ganshi…”

Runtsa idanuwanshi Ashfaq ya yi yana ƙirga ɗaya zuwa goma cikin kanshi. Tariq baisan abinda yake ba, cocaine ke hura mishi kai, ba zai bari maganganunshi su mishi tasiri ba. 

“Baka so ya dawo ko? Shi yasa yanzun ma baka yarda na ganshi ba. Kai ya kamata ka ɓace a madadin shi… Halin duk da yake ciki kai ya kamata ka shiga ba shi ba… Da shi ne ba zai bar abu ya sami Arfa…”

Baiga dirowa da ƙarasowar Ashfaq inda yake ba, sai da ya ji katsewar kalamanshi ta hanyar shaƙar da Ashfaq ɗin ya yi mishi. Kwata-kwata bai damu da ciwon da ke jikinshi ba, don bai kai wanda maganganun Tariq suka jefa a zuciyarshi ba. Yasir ne ya taso yana ƙoƙarin ƙwace Tariq ɗin daga hannun Ashfaq da ke girgiza Tariq da faɗin, 

“Nasan ba zaka taɓa yafe min kan abinda ya sami Arfa ba…ban roƙe ka ba saboda bazan iya yafe wa kaina ba…hakan bashi zai baka damar ɓoyewa bayan cocaine kana jefa min babban kuskuren rayuwata a fuska ba Tariq…karka gaya min abinda nake so ko bana so akan Yasir…. Karka fara…”

“Faq za ka ji mishi ciwo…”

Yasir ya faɗi yana ƙoƙarin ɓanɓare hannun Ashfaq daga wuyan Tariq da har ya soma tari. Tarin ne yasa Ashfaq sakin shi da sauri yana ƙoƙarin kamo shi. 

“Tariq…”

Tunkuɗe shi Tariq ya yi yana bin bango ya nufi hanyar ƙofa, bayanshi zai bi Yasir ya riƙeshi. 

“Ashfaq!”

Ya faɗi a tsawace. 

“Kar ya fita Yasir, baya cikin hankalin shi.”

Jan shi Yasir ya yi ya mayar da shi kan gadon ya zaunar. 

“Bayau ya fara fita shi kaɗai cikin yanayi irin wannan ba. Allah kaɗai yasan ranakun da ya hau titi da mashin cikin maye…karka damu da Tariq baka da lafiya…”

Dafe kanshi Ashfaq ya yi da hannuwanshi duka biyun yana neman hawaye ko zai samu sauƙi a zuciyarshi amma ya kasa samu. Ko bai faɗa ba yasan jini ke fitowa daga ciwon da ke jikinshi yana bullo bandejin da yake rufe da shi, amma bai damu ba. 

“Na yi kuskure na sani… Me yasa Tariq zai dinga jifana da shi?”

Ya tambaya ba tare da ya ɗago ba. Sauke numfashi Yasir ya yi. 

“Me yasa ba zaka daina dukan kanka akan abinda ba zaka iya canjawa ba? Ka daina saka maganganun Tariq a ranka… Bama cikin hayyacin shi yake ba. Zuwa dare ba zai tuna abinda ya faru ba.”

Shiru Ashfaq ɗin ya yi. Ina ma zai iya komawa baya, sai dai haka rayuwa take, duk lokacin daya wuce ka ba zai taɓa dawowa ba, lokaci abu ne mai muhimmanci, zaɓin da za ka yi a lokutan da ka gani na da haɗari, ko ka yi kuskure a cikin zaɓinka ba za ka iya komawa ka sake wani ba. 

“Ka gani ko? Jini ciwon ka yake yi…. Karka motsa. Ina zuwa…”

Yasir ya ƙarasa, yana jin fitarshi daga ɗakin, faɗawa Ashfaq ya yi kan gadon ta bayanshi yana maraba da ciwon da ya ratsa kwanyarshi saboda ya ɗauke mishi hankali da wanda yake a zuciyarshi, ya kuma san zai taya shi danne abinda ke zuciyar na wani lokaci. Ƙarar shigowar saƙo ya ji a wayarshi da tunda Yasir ɗin ya ajiye mishi ita gefen kanshi bai ko bi ta kanta ba. 

Ya ɗauka ma ya yarda a hargitsin daya faru, lalubawa ya yi ya ɗauko yana dubawa. Bai yi saving lamabar ba, amma yasan ko wanene. Lumshe idanuwanshi ya yi yana jin wani ciwon na daban. Yana kuma tuna yadda akai har ya samu lambar shi 

*****

Jijiyoyin gefen kanshi sun tashi saboda ɓacin rai, wayar ya sake kalll da saƙon da ya shigo, kafin ya kalli Yasir da yake tsaye babu alamar razana a tare da shi, asali ma a nutse yake kallon Ashfaq ɗin don ya ga ko me zai yi. 

“Me yasa zaka bashi lambata?”

“Saboda ɗan uwanka ne, saboda ya tambaya.”

Numfashi Ashfaq ya ja yana saukewa. 

“Da na ce bana son ganin shi hakan bai faɗa maka bazan so ya samu lambata ba!”

Hannu Yasir ya ɗaga mishi. 

“Kar kai min ihu akai Ashfaq, za ka iya blocking ɗinshi, banga kana niyyar hakan ba…”

Ba don Yasir yasan Ashfaq kamar yadda yasan kanshi ba da bai ga tahowarshi ba balle hannu daya kawo saitin fuskarshi, hakan ya bashi damar kaucewa yana kai wa Ashfaq ɗin duka a gefen fuskarshi, yadda hannunshi ya haɗu da fuskarshi yasan ko bai karya wani abu ba ya dake shi sosai. Hankaɗe shi ya yi baya. 

“Bansan abinda ya faru tsakanin ku ba…”

Sake tahowa Ashfaq ɗin ya yi, Yasir ya sake tare shi, yana saka mai gwiwar ƙafa a ciki, girman jikinsu da ƙarfinsu ba ɗaya bane, Ashfaq ɗin ya sani don ba yau bane karo na farko da faɗa yake haɗa su, amma yaga alama yau dukan yake buƙata shi yasa yake haye mishi. 

“Amma kana buƙatar ‘yan uwanka…”

Yasir ya faɗi yana riƙe da Ashfaq ɗin dam. 

“A shekarun da na sanka, babu wanda ya nace da son gyara ko me ya faru a tsakanin ku sai Altaaf. Ka faɗa min, ka faɗa wa kanka yadda ka tsane shi bai dame ni ba, amma duk zuwan da zai yi ka ƙi yarda ko ganinshi ka yi ina kula… Ina ganin yadda abin yake ci maka rai fiye da yadda nake gani a fuskarshi. Zaka iya gogewa ba matsalata bace, zan yi bacci mai daɗi sanin na maka zaɓin da baƙar zuciyarka ta hana ka yi…”

Yasir ya ƙarasa yana sake kai mishi wani dukan da sai da gwiwoyinshi suka kai ƙasa, sannan ya fice daga ɗakin ya barin shi a nan. 

*****

Yadda bai yi saving ɗin lambarba, bai kuma yi blocking ba, saƙon ya buɗe yana karantawa;

‘Ko ba za ka yafe min ba, kai min magana, ka zage ni, ka ce wani abu ko menene don Allah.’

Key ya saka wayar yana ajiyewa inda ya ɗauke ta, miƙewa ya yi zaune, yana jin ciwon shi ya sake buɗewa da wata irin azaba, hakan kuma yake nema don baya son ba ƙwaƙwalwar shi wani sarari da zata saka shi tunanin abinda baya son sake ziyarta. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 7Alkalamin Kaddara 9  >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 8 ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×