Skip to content
Part 51 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Ya kasa zaune ya kasa tsaye tunda safe, babu yadda Majida bata yi ba ya ci wani abu amman ya ƙi. 

“Inata kiran Aslam bai ɗaga ba, wayar Ammi kuma bata shiga.” 

Ya faɗi yana shagwaɓe mata fuska. 

“In hwa yana tuƙi ne? Ka zauna ka ci wani abu ka ƙi zama. Mi kake so in yi yanzun?” 

Cewar Majida tana kafe shi da idanuwa da yasa shi samun waje ya zauna. Ya rasa inda zai saka ranshi ne ya ji sanyi. Tsoro yake ji kar su Ammi su kasa karɓo mishi yaran shi, baisan ya zai yi ba idan har ba’a bashi yaran ba. 

“Ka ci wani abu don Allah, ka ji.”

Majida ta faɗi tana dafa kafaɗarshi cike da kulawa, duk ya fita hayyacin shi tun da ya tashi da safe, da ƙyar take samu ta tashe shi yai sallar Asuba, yana turo laɓɓaa yana komai, amma yau tun kafin Asuba idon shi biyu don ita ma a zaune ta ganshi lokacin da ta tashin, tunda ya fita masallaci kuma ya dawo ya langaɓe a jikinta, kitchen ma haka ya dinga binta tana fere dankali yana kwanciya a bayanta, sai da ta gaji da shi ta kore shi saboda aikin baya mata sauri. Gashi itama ba wai tana jin daɗin jikinta bane ba. 

“In zuba maka dankalin?”

Kai ya girgiza mata, ba yunwa yake ji ba, baya son saka ma cikin shi komai in ba gani yayi su Aslam sun dawo ba. 

“Ko mu je can gidan mu jira su?”

Kallon shi kawai Majida ta yi tana sauke numfashi, don batasan me zata ce mishi ba kuma. Magana zai sake yi wayar shi ta fara ringing, da sauri ya ɗauka yana dubawa ya ga Wadata ne, tun kafin ya ɗaga ya shagwaɓe fuska, har mamakin Altaaf take wasu lokutan, babba da shi amma ko kaɗan baya hana shi sangarta inya tashi. Kamar abin na zuwar mishi ne ba tare da ya san yana yi ba. Shagwaɓar ta zamar mishi wani ɓangare na rayuwar shi. 

“Yaya Imran…”

Ya faɗi bayan ya kara wayar a kunnen shi, bata ji me Wadatan ya ce ba, Altaaf dai ta ga ya girgiza kan shi. 

“Har yanzun fa. Ina ta jira ni…”

Sake girgiza kai yayi. 

“Majee bata zuba min ba…”

Ware idanuwa Majida ta yi tana ture mishi kafaɗa tare da buɗe bakinta cikin mamaki, wayar ya kara mata a kunne yana dariya. Sallama ta yi ma Wadata da ya amsa yana ɗorawa da, 

“Nasan ƙarya yake Majida…”

Dariya ta yi a kunyace tana faɗin, 

“Ya iyali? A gaishe su gaba ɗaya, mungode ƙwarai.” 

“Alhamdulillah, duk za su ji in sha Allah. Kiyi ta haƙuri kin ji? Na san zama da Altaaf ba zai zama abu mai sauƙi ba. Amma in kika fahimce shi ƙasan duk yarintar shi zuciyarshi me kyau ce. Kiyi haƙuri don Allah karki riƙe shi da abinda yayi na baya, kiyi haƙuri da ƙaddarar shi, karki barshi.” 

Kai kawai Majida take ɗagawa, muryarta can ƙasa ta ce, 

“In shaa Allah…”

Tana miƙawa Altaaf wayar, da gaske Wadata yake, a ƙasan duk wata halayya na Altaaf yana da zuciya me kyau, kuma zata iya bada shaida akan canzawar shi, don da bata ji bayan shi ba, ko a mafarki ba zata taɓa alaƙanta mijin da ta faɗa soyayyar shi da rayuwar da A-Tafida yayi ba, mutane ne su mabanbanta, tun jiya ta haƙure ma zuciyarta, idan laifukan shi za su yafu a wajen Ubangiji wacece ita da zata riƙe shi? Rayuwar duk ba mai yawa bace ba in ka duba. Kallon shi ta yi yana daƙuna ma Wadata fuska kafin ya sauke wayar yana kallon ta. 

“Me ya ce miki? Ya ce min yaro ko?”

Murmushi ta yi a sanyaye, ko ba yaron ba ne shi yanayin da yai magana cikin shi a yanzun cike yake da yarinta. Hannu ya miƙa yana ja mata hanci tare da faɗin, 

“Na gode…”

Laɓɓan shi ta karanta, saboda sauti bai fito ba, a hankali yai maganar, yana tattaro duk wani yanayi da zai iya zuwa cikin idanuwan shi don ta ga yadda ba zai gaji da mata godiyar zaɓin da tai na ci gaba da zama da shi ba. Kai ta ɗaga mishi kawai tana miƙewa, kitchen ɗin ta je ta zubo mishi dankalin da ta soya a plate ta fito, ta san ba shayi yake sha ba, don haka bata haɗo ba, kan kujera ta dawo ta zauna ta ɗora plate ɗin akai. 

“Ka ci abinci don Allah.”

Shagwaɓe mata fuska yayi, hannu ta sa ta ɗibo dankalin tana haɗawa da sauce ɗin da ta yi ta miƙa mishi saitin bakin shi. 

“Bismillah…”

Ya faɗi yana buɗe bakin shi, kamar yaro haka ta saka shi a gaba tana bashi abincin sai da ya ture hannunta yana girgiza mata kai tukunna ta tashi ta mayar da plate ɗin kitchen ta wanke hannunta, ruwa ta ɗibo mishi a kofi tana dawowa ta miƙa mishi. 

“Ki bani mana.”

Ya ce yana tura mata fuskar shi da bata gajiya da yi mata kyau. 

“Sangarta tai ma yawa…”

Ruwan ta bashi ya sha yana faɗin, 

“Naji na yi sangarta ɗin… Idan da a waje na yi duka za ai min ai, tunda ke na yi wa babu yadda za ki yi da ni.” 

Murmushi kawai ta yi tana ajiye kofin a gefe ta zauna kan kujerar, kwanciya ta yi tana tayar da kanta da cinyar Altaaf ɗin da ya fara ture ta. 

“Jikina na min ciwo Allah.”

Tashi zaune ta yi kafin tai magana shi ya kwanta yana ɗora mata kanshi a cinya. 

“Ɗaga ni nima jikina ciwo yake man.”

Majida ta faɗi, sake gyara kwanciyar shi ya yi. 

“Ni da gaske nake yi, kuma ma banda lafiya, don Allah ki barni in kwanta…” 

Ƙyale shin ta yi tana ɗora hannunta tare da shafa sumar kan shi. Idanuwan shi ya lumshe yana sauke numfashi. 

“Majee idan basu karɓo yaran ba fa?”

“Sai ka yi haƙuri duk sati muna zuwa duba su…” 

Ƙara gyara kwanciyar shi yayi a jikinta yana riƙo hannunta da ke wasa da sumar shi. 

“In suka bani su zai fi min daɗi, zamu kula da su sosai Allah.” 

Ya faɗi a sanyaye. 

“Na sani, amma don Allah karkai rigima da su ko basu bado yaran ba, ka yi haƙuri ka ji?” 

Kai Altaaf ya ɗaga mata, a yanayin da yake ciki yanzun bashi da ƙarfin yin faɗa da su kan yaran, ba zai yi baƙin jini fiye da wanda zai yi nan gaba a idanuwan yaran ba. Laifin shi a wajen su da yawa ne. Bazai ƙara wani akai ba, hannun shi Majida ta dumtse haka kawai tausayin shi ta ji ya cika mata zuciya. Lokuta da dama mutane kan abu ba tare da hango yadda zai taɓa rayuwar su a gaba ba. Sallamar su Ammi suka ji, Majida ta yi saurin ture Altaaf daga jikin ta da ya tashi zaune yana daƙuna mata fuska. Sallamar ta amsa tukunna suka shigo cikin gidan. 

Kan yaran idanuwan Altaaf suka fara sauka, ya ji zuciyar shi tai wata irin dokawa kamar zata fito daga ƙirjin shi. Kallon shi Ammi take da yanayin da yake kan fuskar shi. 

“Ammi sannu da zuwa… Ki shigo.”

Cewar Majida, kai Ammi ta girgiza mata.

“Sannun ku da gida Majida, ni kam zamu wuce ne. Su Aslam na jirana a waje, yaran kawai muka zo saukewa…” 

Kai Majida ta iya jinjina ma Ammi, itama hankalinta ya koma kan yaran da suke ta kalle-kalle, kamannin su da Altaaf na bata mamaki. Allah kenan mai yadda ya so, ƙaddara abu ce mai cike da al’ajabi, babu yadda za ai ka wuce rubutun da Alƙalamin Ƙaddara ya yi maka ko wanene kai, lokuta da dama ka kan sauya shi ta hanyar addu’a, wasu ƙaddarorin sukan zo maka da sauƙi, wasu kuma sukan sameka don gwada imaninka. Ta yarda auren Altaaf na cikin kalar waɗannan ƙaddarorin da ta karɓa da hannuwanta a buɗe. 

“Kiyi haƙuri Majida, shi ne abinda zan iya ce miki kawai wallahi.” 

Ammi ta faɗi tana gode ma Allah da ya sa bashi ya gifta tsakaninta da mahaifin Majida har hakan ya zama sanadin aurenta da Altaaf, ita ɗin alkhairi ce a rayuwar shi. Tun jiya da sukai waya Altaaf ya faɗa mata yadda sukai da Majida ɗin take jinjina mata. Tasan ko a mugun wasa ba zata iya abinda Majida ɗin take yi yanzun ba. Ba zata iya riƙe yaran da mijinta ya kawo daga waje ba, ko na matar daya aura ya same su ta hanya me kyau ma bata tunanin kishinta zai bari ta riƙe su. 

“Zan wuce, kun kira ni in kuna buƙatar wani abu.” 

Ammi ta faɗi, Majida ta miƙe tana taka mata, Altaaf kuwa bai ma san ta fita ɗin ba, gaba ɗaya hankalin shi na kan yaran daya tashi daga inda yake yana ƙarasawa ya tsugunna a gaban su. 

“Zamu gida.”

Macen ta faɗi, kai Altaaf ya ɗaga mata yana jin wani abu ya tsaya mishi a wuya. 

“Zan kaiku, ya sunanki?”

“Hassana.”

Kai ya jinjina yana riƙo hanunta da bata yi musun kamawa ba, Hussain ɗin ma ganin hakan yasa shi saka hannun shi cikin ɗayan na Altaaf ɗin da ya miƙo mishi. Wani yanayi Altaaf yake ji da babu kalaman da za su fassara shi, bai taɓa sanin kusanci irin wannan ba, bai taɓa jin ƙaunar da ke mishi yawo a jinin jikin shi irin hakan ba, zai iya komai saboda Ammi, zai iya komai saboda su Barrah, zai iya komai saboda Majida. Duk yasan wannan, amma yaran nan yana jin ba komai kawai zai iya yi akan su ba, zai iya basu duk wasu gaɓɓai da sassa na jikin shi in suna buƙata, wannan kuwa abu ne mai girma a wajen shi, don yana son kan shi da yawa. 

Ɗaga kai yayi yana kallon Majida kamar yana son nuna mata su duk da tana ganin su, so yake ya ce mata ga yaran shi, so yake ya faɗa mata jinin shi na yawo a jikin su, ji yake kamar ya ɗauke su ya nuna ma duk wani wanda zai saurare shi cewar yaran shi ne. Amma kalma ko ɗaya ta kasa fitowa daga bakin shi. 

“Na gansu, na gansu…”

Majida ta ce mishi idanuwanta cike taf da hawaye, tausayin mahaifiyar yaran da halin da take ciki na lulluɓeta, sai kuma Altaaf, kallon shi take tana mishi tunanin ranar da zai amsa dukkan tambayoyin da yaran zasu jera mishi, ranar da zaisan matsayin shi a wajen su, ranar da zata basu zaɓin yafe mishi ko akasin hakan, har cikin ƙasusuwanta take jiye mishi tsoron ranar, take kuma fatan ita da shi zasu samu damar cika zuciyoyin yaran da soyayyar Altaaf ɗin, tana kuma addu’ar ta yi girman da zasu yafe mishi laifin da yai musu. Ta gefensu ta bi tana wucewa kitchen ta zubo musu dankalin ta dawo da shi falo, ta koma ta ɗauko musu lemukan roba guda biyu ta dawo, miƙa musu ta yi suka karɓi lemukan suna kallon ta. 

Tasan suna cike da baƙunta, ta yi mamaki da basu fara kukan son komawa gida bama, da alama yaran ba masu rikici bane ba. 

“Ku zauna ku ci abinci.”

Altaaf ya faɗi yana kama hannuwan su, ba su yi mishi musu ba suka zauna ɗin kuwa. Da kanshi ya so basu dankalin amma sun ƙi ci. Ɗan taɓa shi Majida ta yi ya juya ya kalleta, kai ta girgiza mishi tana nuna mishi ya ƙyale su, ba don ya so ba ya bar su, hannu Hassana ta sa a plate ɗin tana ɗaukar dankali ɗaya ta sa a bakinta, kafin shi ma Hussain ɗin ya ɗauka ya fara ci, daga Majida har Altaaf sun koma sakarkaru, kallon yaron suke kamar basu taɓa ganin yara ba a rayuwar su. Sosai suka ci dankalin basu ma iya cinyewa duka ba, Majida ta ce mishi su je su siyo musu kayan sakawa, don Ammi ma ta manta da wasu kaya da aka haɗo su da su bata basu ba. 

Kwasar yaran suka yi suna fita tare, kamar mahaukata haka suka koma a cikin Baby Dream, kaya kawai suke ɗiba ba tare da tunanin kuɗin ba, ɓangaren kayan wasa kuwa yaran suka bari, tun in suka ɗauki abu sai su juya su kalli su Altaaf da suke basu ƙarfin gwiwar ɗaukar duk wani abu da suke so har suka fara ɗan sakin jikin su, bayan mota suka cika taf da kaya, kuɗin dake account ɗin Altaaf din daya ɗauko ATM basu ishe shi ba, saboda ya zuba kuɗin shi a wasu dogayen riguna da za’a kawo musu kasuwa daga Dubai. Majida ta ƙarasa biyan sauran kuɗin. 

Bayan motar Altaaf saida suka cika shi taf da kaya suka dawo gida, suna shirya ɗakin da suka tanada don yaran su kawai, su Hussain kam sun samu kayan wasa, abinka da yaro ko takan su Altaaf ɗin ma basu yi ba balle su tuna suna son komawa gida. Yinin ranar babu wani abin kirki da suka yi a cikin gidan daga shi har Majida, duk wani abu da yaran za su yi nishaɗi yake saka su marar misaltuwa, tabbas akwai Rahma a samun yara, akwai nutsuwar da ke tattare da zama a cikin yaran da ko ba daga cikinka suka fito ba, akwai yanayin yadda suke tasu rayuwar ba tare da tunanin komai ba, yadda zuciyar su take a tsarkake babu dauɗar komai zai taɓa taka zuciyar ta fanni mai wahalar fassarawa. 

Bayan Sati Biyu

Tsaye yake a ƙofar gidan yana jiran Nuwaira da ya aika a kira mishi ta fito. Zuciyar shi yake jin ta ƙagauta da ta fito ya ganta. Zai yi ƙarya idan yacee daga farko ba tausayinta bane zai sa ya aure ta, saboda bai ma san ya kalarta yake ba ballantana ya ce ko wani kyanta ko fuskarta yake so. Har ranshi yasan ko ya take zai aure ta, don zai yi hakan ne tsakanin shi da Allah. Ranar da ta leƙo ya fara ganinta ya girgiza, ya daɗe yana jinjina ma Iko na Allah da yake halittar kyawawa a ko ina cikin duniya, Nuwaira na da kyau da ya bashi mamaki. 

Duk da yanayin rayuwar ƙauye, babu wanda zai kalleta bai ga kyawunta ba, musamman idanuwanta da suke mishi kamar ƙanƙarar ruwa ta ɗauko narkewa. Ranar da yazo sukai magana bata ce mishi komai ba, kawai ta ce zata yi magana da iyayenta ne tukunna, amma yanayin amsarta ta ɗaga burin shi, bai kuma ga ƙiyayya a cikin idanuwanta ba. Motsin da ya ji ne yasa shi ɗago kai da sauri, sai dai ba Nuwaira ba ce, matashin saurayi ne da zai yi sa’an Altaaf ya fito a madadinta, hannu Aslam ya miƙa mishi yana mishi sallama. 

Duk wani abu da Tawfiq ya fito da shi ya ji ya yi sanyi da ganin Aslam ɗin, Nuwaira ta faɗa mishi abinda yake faruwa, ya ga rauninta sosai, ya kuma fahimci tana son amincewa buƙatar Aslam ɗin saboda ta samu kusanci da yaranta da take ganin kamar an raba ta da su kenan. Amma ba zai bari ta sake cutuwa ba in har zai iya hana hakan, yaran kam ba ita kaɗai take kewar su ba, a satikan nan biyu ya sha sai bayan ya siya musu abu ne zai tuna ba sa gidan. Ya fito ne ya gaya ma Aslam ya ƙyale Nuwaira ba za su bashi ita ba, amma sai yai mishi wani irin kwarjini. Ganin yayi shiru ya sa Aslam yin murmushi yana faɗin, 

“Na san kana cike da shakku akaina, kana da dukkan haƙƙin yin haka. Wallahi Allah ne shaidata ban zo da niyyar cutar da ita ba. Tausayin ta da son ta samu daidaito ko yaya ne a rayuwarta ya sani fara son aurenta tun kafin in ganta. So bai cika shiga ƙanƙanin lokaci ba, bansan ko shi nake ji bayan na ga Nuwaira ba. 

Ba zan yi maka ƙarya ba kuma, amma nasan zuciyata na doka mata da koma menene, don Allah karku hanani aurenta in har na cika sharuɗɗan mijin da kuke niyyar bata…” 

Aslam ɗin ya ƙarasa da wani irin sanyi da yasa Tawfiq cewa. 

“Bana so wani abu ya sake samun ta ne, tasha wahala a rayuwarta wallahi, ina tsoron wani abu ya sake samun ta.” 

Kai Aslam ya jinjina mishi yana fahimtar tsoron shi. 

“Karka yarda da ni to.”

Da mamaki Tawfiq yake kallon Aslam ɗin yana son gane me yake nufi, kai Aslam ya jinjina mishi. 

“Karka yarda da ni, ka yi mata addu’ar alkhairi, nima zan yi mata hakan, idan ni alkhairi ne a rayuwarta Allah ya tabbatar mata da ni, idan har bazan zame mata alkhairi ba Allah ya bata wanda zai riƙe muku ita fiye da yadda nake ganin zan riƙe ta. 

Kar mu yi gaggawa, mu bi abin a hankali, karka yarda da ni. Ka yarda da Allah da Ya fi mu sanin abinda ya dace da mu gaba ɗaya…” 

Numfashi Tawfiq ya sauke jikin shi ya gama yin sanyi. 

“Allah yai mana jagora.”

Ya faɗi da wani irin rauni. Hannu Aslam ya sake bashi suka gaisa tukunna ya koma cikin gida. Bai jima ba Nuwaira ta fito ta sha hijab har ƙasa, a kunyace ta yi mishi sallama da ya amsa, muryarta na dira kunnuwan shi da wani yanayi da yasa shi sauke idanuwan shi daga kallon da yake mata. Gaisawa kawai suka yi ya wuce mota ya ɗauko ledojin da yai mata siyayya. Da ƙyar ya samu ta amsa bayan ya mata nasihar ƙin amsar kyauta. Har ranshi siyayya ya so yi mata mai yawa, amma bayaso suga kamar yana ƙoƙarin rufe musu ido ne da abin duniya, yana fatan gaba dai ya samu damar yi mata abu ba tare da tunanin za aima niyyar shi fassara ta daban ba. 

Sallama suka yi ya koma ya shiga mota yana juyawa. Ko kaɗan bai hangoma kanshi aure a wannan lokacin ba, sai dai bai hango ma rayuwar su gaba ɗaya abubuwa da yawa ba, ciki harda ƙaddarar Altaaf da ta jeho Nuwaira rayuwar shi. Abin bai bashi mamaki ba, ba don zurfin ilimin addinin da yake da shi ba, sai don sanin da yai na cewar tsarin mu muke kawai, ikon komai na hannun Allah ne, ba ma taɓa wuce rubutun da Alƙalamin Ƙaddara yai mana. Addu’a yake ta neman alkhairi a cikin auren shi da Nuwaira dan da gaske ta samu waje a zuciyar shi tayi zaune.

Bayan Wata Uku

Abuja

“Aroob ki tashi don Allah…”

Zafira da take naɗa mayafi a saman kanta ta faɗi tana sa Aroob ɗin da take kwance cikin kujera yatsina fuska. 

“Da kun je kawai Zaf, bana jin fitar Allah.”

Idanuwanta Zafira ta mayar kan Fawzan da ya ɗan ɗaga mata kafaɗu, su dukka biyun saboda Aroob ɗin suka tsiri tafiyar. Idan ta ce ba zata je ba shikam ba shi da ƙarfin yi mata dole. Gidan ne gaba ɗaya ba daɗin shi suke ji ba, idan za’a tsira shi da tambayar yadda akai kwanakin suka wuce mishi a watanni ukun nan zai ce bai sani ba. In ya tashi daga bacci ko karyawa baya yi yake fita wajen aiki. Wata rana acan yake kwana ko da kuwa ba shi da aikin dare, zai karɓarma wani. Idan na dare yake da shi zai karɓarma wanda yake dana safe don kar ya wuni a gidan. 

Lokutta da dama zai tashi aiki ƙarfe shida na yamma yai zaman shi a office har sha ɗaya, ba aikin da yake yi, wayar shi yakan saka a gaba yana kallo ko Rafiq zai ji a jikin shi cewar ya kai dare a waje haka ya kira shi. Amma shiru. Da ya ce musu yana buƙatar barin kasar don ya huta basu taɓa tunanin har da su zai bari gaba ɗaya ba. Fawzan bai taɓa tunanin zai iya ɗaukar kwanaki uku bai ji lafiyar su ba, amma shiru har watanni sun ja haka. Nuri kanta sai ka tausaya mata, kullum ta fito sai ta kalle su da wani yanayi a fuskarta, tana jiran su ce mata Rafiq ɗin ya neme su, amma basu da wani labari suma. 

“Aroob…”

Zafira ta sake kira, tashi zaune Aroob ta yi tana kallon su. 

“Fitar nan ba zai canza komai ba, za mu dawo cikin gidan, za mu dawo kuma baya nan…” 

Ta ƙarasa maganar idanuwanta na cika da hawaye. 

“Zai dawo…”

Zafira ta faɗi tana ƙoƙarin danne hawayen da ke son tarar mata itama. 

“Hmm

Fawzan ya ce kawai yana sa Zafira sake faɗin, 

“Zai dawo…”

“Idan kuma bai dawo ba fa?”

Aroob ta faɗa yayin da ta sa ɗan yatsanta ta sharce hawayen da ke gefen idonta. 

“Laifin Daddy ne, bansan me yasa ya bar shi ya tafi ba. Kuma ba ku goyi bayana ba da ina roƙon shi kar ya tafi.” 

Waje Zafira ta samu ta zauna, a yanayin yadda Rafiq yake a ranar bata jin tana da zuciyar hana shi yin duk abinda yake so, ya ce yana buƙatar shaƙar wata iskar ta daban, ya gane yana da mata da yarinya da ta rasu wanda ko tuna su ya kasa yi, hargitsin bai gama sakin shi ba ya ji mutanen da ya ɗauka iyaye ba su suka haife shi ba, bai tsaya a nan ba sai da sanin hanyar da aka same shi ɗin ba mai kyau bace ba, idan yana bukatar shaƙar iska daban da wannan me yasa zata ce kar yayi hakan. Ba zata iya son kanta da yawa ba. 

“Ban ɗauka zai daɗe har haka ba Aroob, wallahi ban yi tunanin zai kai yanzun ba…” 

Fawzan ya ce yana jin wani irin ɗaci tun daga zuciyar shi da yadda Rafiq ɗin bai kyauta musu ba, kafin ya ci gaba da faɗin, 

“Ko text ya yi ya ce yana lafiya hankalin mu zai kwanta… Me yasa Yaya zai mana haka?” 

Ita kanta Aroob ɗin tunanin ko yana lafiya ya fi komai tsaya mata. A firgice take farkawa cikin dare da tunanin shi manne a ranta. Naadir ma tun shekaranjiya daya kirata yana tambayar ta ko Rafiq ɗin ya neme su, ihun da tai mishi har yau bai sake kiranta ba, ko a makaranta yanzun ba mai mata magana, haushin kowa da komai take ji, ciki har da su Nuri da suka bar Rafiq ya tafi, su Zafira ma tana ɗan musu magana ne saboda takan ji sauƙi-sauƙi in sukai maganar Rafiq ɗin. 

“Ko za mu bishi ne to?”

Zafira ta ce da wani yanayi a muryarta, tana sa Fawzan yin wata dariya da bata da alaƙa da nishaɗi. 

“Ina?”

Ya tambaya, ɗan ɗaga kafaɗa ta yi, rashin hankalin da ke cikin zancenta yana danneta. 

“Inda nasan ta inda zan fara da yanzun muna nan tare da shi Zaf, da yanzun na bishi ko bai yi niyya ba mun dawo.” 

“Ko mu zauna can ɗin inda yake gaba ɗaya ba.”

Aroob tai maganar, Zafira na jinjina mata kai .

“Yeah idan ba ya son dawowa sai mu zauna can ɗin.” 

Shiru sukai na wani lokaci, kafin Aroob ta ce, 

“Ya za mu yi idan bai dawo ba? Yaya Fawzan ya za mu yi?” 

Bai kai da bata amsa ba, saboda takun saukowa daga bene da suka ji kamar ba da lafiya ba, a hargitse Nuri ta sauko daga saman tana dube-dube. 

“Nuri?”

Fawzan ya kira cike da alamar tambaya. Kallon shi ta yi, zata rantse ta ji kamar Rafiq na cikin gidan, a kwance take a ɗaki, bacci ne ma ya soma ɗaukarta tajie kamar yana cikin gidan shi yasa ta taso don ta duba, a watanni ukun nan duk da ta yi wata irin kewar shi, ko na minti ɗaya bata taɓa tunanin ba zai dawo ba, yaron ta ba zai barta ba, ƙaunar da take mishi kawai ta isa ya dawo. 

“Na ji kamar Rafiq ne…”

Kai Fawzan ya girgiza mata alamar ba shi ɗin bane ba, amma har a ƙasusuwan jikinta take jin Rafiq na cikin gidan. Ko takalma babu a ƙafarta, doguwar riga ce ta abaya a jikinta sai hula a saman kanta, duka ɗinkin Aroob ne. Takawa ta yi tana ƙarasawa wajen ƙofa ta leƙa kanta, amma bata gan shi ba. Numfashi ta sauke, jikinta a sanyaye ta dawo cikin ɗakin tana juyawa ta nufi hanyar da zata hau ta koma sama, ta taka step ɗin farko na benen zuciyarta tai wata irin dokawa da ta sa ta juyowa tana zuba ma ƙofar ido. 

“Nuri ba shi bane ba…”

Fawzan ya faɗi, kamar daga sama ya ji an ce, 

“Waye ya ce ba ni bane?”

Rafiq yai maganar yana tsayar da hankalin shi da idanuwan shi gaba ɗaya kan Nuri da murmushin da take mishi. Wata irin kewar ta na cika zuciyar shi. 

“Nuri…”

Ya faɗi can ƙasan maƙoshi, itama kallon ɗan nata take da ya canza mata gaba ɗaya, so take ta ga meye a fuskar shi da ya canza mata da yawa haka, kafin ta tsayar da idanuwan ta kan sumar daya tara a kan nashi, sumar dake nuna alamar ya haɗa jini da larabawa duk da ba’a kwance take luf-luf ba. Sai kuma ƙananan kayan da suke jikin shi da takan yi shekara bata ga ya saka ba ko da a cikin gida ne. 

“Yayaaa…”

Kusan su duka ukkun suka faɗa a tare, amma ko alamar ya ji su bai nuna ba, gaba ɗaya hankalin shi na kan Nuri, jakar da take rataye a kafaɗar shi ya sauke yana takawa ya ƙarasa inda take a tsaye. 

“Nuri…”

Ya sake kira, amma ta kasa amsa mishi, banda hawayenta da suka samu damar zubowa ko motsi ta kasa yi. Rafiq ɗin baisan lokacin da ya kai hannun shi yana tallabar fuskarta ba, kai yake girgiza mata, shi ba ƙaramin yaro ba ne, amma yadda yake jin kewarta na son saka hawaye zubar mishi, baisan abinda yake tsakanin shi da kuka ba yanzun, ko kaɗan baya mishi wahalar yi. Hannunta Nuri ta kai saman na Rafiq ɗin tana riƙewa tare da sauke wani irin numfashi mai nauyi. Tana jin yadda ya fita tare da wani dunƙulallen abu da yai mata tsaye a wuya. 

“Karka sake tafiya ko ina. Kana jina?”

Kai yake ɗaga mata, shi ma baya jin zai iya sake nisa da su haka. Amma yana buƙatar hutun ne daga komai da kowa shi yasa ya tafi, kuma hutun ya mishi daɗi, ya samu nutsuwar da yake jin ya rasa, ya kuma karɓi ƙaddarar shi da hannuwa biyu, yanzun baya jin zata canza wani abu tattare da shi, ba shi da iyayen da suka wuce Nuri da Daddy, bashi da ‘yan uwan da suka wuce su Fawzan. Duk wani abu da zai biyo wannan ba zai taɓa canza hakan ba. Sun tabbatar mishi, yana jin komai zai yi sauƙi. 

“Good…”

Nuri ta ce tana zame fuskarta daga cikin hannuwan Rafiq ɗin. Gajiyar duk da ta tara a watanni take ji tana danneta, kuma ta ga fuskokin su Fawzan, suna buƙatar yayan su fiye da yadda take buƙatar ɗan ta, don haka ta juya tana hayewa benen. Sai lokacin Rafiq ya juya shima, kan Fawzan ya fara sauke idanuwan shi yana mishi murmushi. 

“Yaya…”

Fawzan ya faɗi muryar shi na rawa da alamun yanayin da yake ji. Hannu Rafiq ya miƙa mishi, da sauri ya tako, maimakon ya riƙe hannun Rafiq ɗin rungume shi yayi, sosai ya matse shi kamar zai karya shi. 

“Fawzan… Karka karya ni.”

Bai saurare shi ba, saboda ba zai gane abinda yake ji ba, kalar tsoron da ya ji na tunanin Rafiq ɗin ba zai dawo ba. Ya kai mintina biyu kafin ya saki Rafiq ɗin yana kallon shi. 

“Ko text ka yi ka ce mana kana lafiya hankalin mu zai kwanta Yaya…” 

Yanajin rashin kyauta musun da ya yi har ƙasan ranshi  

“Fawzan…”

Ya fara magana, Fawzan ɗin ya katse shi ta hanyar ɗaga mishi hannuwan shi duka biyun yana takawa baya, da baya yake tafiya kafin ya juya yana ficewa daga gidan gaba ɗaya. 

“Fawzan!”

Rafiq ya kira, amma ko juyowa bai yi ba, hakan yasa Rafiq sauke numfashi yana juyawa ya kalli Aroob da ta sa hannunta tana goge hawayen da suka zubo mata. 

“Kana lafiya Yaya?”

Ta buƙata. Kai Rafiq ya ɗaga mata, kewarta na saukar mishi, gani yayi ta rame sosai, idanuwanta sun yi zuru-zuru. Kai ta jinjina tana miƙewa, hannuwan shi Rafiq ya miƙa mata, don yasan ta, yasan zata riƙe shi fiye da yadda Fawzan ya riƙe shi. Amma ga mamakin shi ta gefen shi Aroob ta wuce tana hayewa sama abinta. 

“Aroob.”

Ya faɗi, mamaki bayyane a fuskar shi, ita ma bata juyowa ba. 

“Me kake tunani Yaya?”

Zafira ta faɗi muryarta a sanyaye. 

“Zaf banda ke, don Allah karku min haka mana.”

Yai maganar muryar shi can ƙasan maƙoshi. 

“Kana buƙatar lokaci na fahimta Yaya, baka so mu san inda kake, wannan ma na fahimta saboda ka san mu, idan muka san inda kake sai mun biyoka ko baka buƙatar mu. Amma idan ka turo mana saƙon kana lafiya ya ishe mu. 

Aroob ta ɗauka ka bar mu, a wata na biyu koni na fara tsoron ko maganar ta da gaske ne, baka taɓa son kanka da yawa irin wannan karan ba, kana tunanin mu kafin ka yi komai, wannan karan har Nuri ba kai tunanin ta ba Yaya. 

Naadir kullum sai ya kira ko ka dawo, ba ina son sa ka ji baka kyauta ba ne , baka kyauta mana ba, in ka ce mana kana lafiya, text guda ɗaya kawai…guda ɗaya Yaya…” 

Ta ƙarasa ƙirjinta na mata nauyi don haka ta miƙe kawai. Ko motsi Rafiq bai yi ba balle ya iya ce mata wani abu, ta gaban shi ta wuce itama. Ya kai mintina biyar tsaye a wajen, ko kusa bai yi tunanin me shirun shi zai musu ba, saboda kanshi kawai yake tunani da yadda yake buƙatar yin nesa da komai da yake barazana da zaman lafiyar hankalin shi, baiyi tunanin za su ɗaga hankalin su da tunanin ko wani abu ya same shi ba. Sam wannan tunanin bai zo mishi ba sai yanzun. 

“Yaa Allah…”

Ya furta yana tunanin halin damuwar da ya saka Nuri da bata iya wuni bata ji lafiyar shi ba. Ko yana Kano ne, idan yai dogon meeting bai kirata ba sai ya sha faɗan ta, haka su Fawzan ɗin, ko bai kira ba yakan tura ma ɗaya daga cikin su saƙo ya sanar musu halin da yake ciki. Wannan karan su kansu bai yi tunanin ya tasu lafiyar take ba ballantana yai tunanin sanar musu da tashi, gara ma Aroob akan Fawzan wajen kula, ba fita yake da inhaler ɗin shi ba. Allah kaɗai yasan lokutan da ya fita babu ita, zuciyar shi ya ji ta tsinke, nan falon ya bar jakar shi shima yana wucewa ɗakin shi. Sai dai a kulle yake, ba shi da ƙarfin zuwa ɓangaren Nuri ya karɓo mukullin shi. 

Ɗakin Fawzan ya wuce ya murza hannun ƙofar ya ji shi a buɗe, turawa yayi ya shiga ya mayar da ƙofar ya rufe, banɗaki ya wuce ya watsa ruwa ya fito, wani abu yake ji ya danne shi gaba daya. Gurin canza kayan Fawzan ɗin ya ƙarasa, bai yi mamakin ganin kayan shi a wajen ba. Shadda ya ɗauka ya saka yana sauke numfashi kamar su kansu manyan kayan yayi kewar saka su ba kaɗan ba. Ɗakin baccin Fawzan ɗin ya koma yana hawa kan gadon shi ya kwanta yana lumshe idanuwan shi, fushi suke mishi da baisan ta inda zai fara basu haƙuri ba. Da tunanin hakan fal a ranshi bacci mai nauyi ya ɗauke shi. 

Kano

Tsaye yake a ƙofar gidan ya kasa ɗaga ƙafar shi ballantana ya shiga. Runtsa idanuwan shi yayi, hotunan rayuwar da yayi cikin gidan na dawo mishi. Hotunan da zai iya komai don ganin sun goge ko zai samu sauƙi a rayuwar shi. 

“Yaya zaka iya…”

Tariq da yake tsaye a gefen shi ya faɗi yana saka shi buɗe idanuwan shi da suke a rufe. Jinjina kai kawai Ashfaq ɗin ya iya yi. Tun fitowar shi asibiti suka je wajen wani babban Malami da maganar yadda zai yi ya tsarkake dukiyar da yake da ita, ya fada mishi tunda babu na sata a ciki abin zai zo da sauƙi, zai ɗibi iya abinda zai ishe shi yin jari ne ya sadakar da sauran, wanda zai ɗiba ɗin ma don kar yanayin rayuwa yasa shi komawa gurɓatacciyar hanya ne. Da ƙarfin gwiwar su Yasir ɗin ya iya yin hakan, don a shekarun nan kuɗi na cikin abubuwan da suka shiga ranshi fiye da tunani. 

Saboda ya ga abinda kuɗi za su iya yi, ya ga yadda tare da kuɗi asirin su ya rufu, ya ga yadda kuɗi suka siyar musu mutuncin da kirkin Abban su ya kasa siyar musu. Mutane sun koya mishi son kuɗi na fitar hankali, yanzun ɗin ma baisan ta inda zai fara da sauran kuɗin da suka rage mishi ba. Su Tariq suka bada shawarar su koma gidansu da suka gada saboda inda suke ciki ɗin haya ne, a motar Ashfaq ɗin da bai siyar ba suka dinga zirga-zirgar kwashe kayayyakin su, can ɗin suka gyara tsaf kamar basu taɓa barin shi ba. Sai da suka gama komai su uku tukunna suka ce mishi ya zo. 

Gashi a ƙofar gidan, shiga yana neman ya gagare shi, rabon shi da takowa unguwar ma gaba ɗaya tun satin rasuwar Arfa. Wani irin yanayi yake ji da ba zai misaltu ba, da ƙyar ya sauke numfashi mai nauyin gaske ya ɗaga ƙafar shi ya ɗora cikin soron gidan. 

‘Ashfaq sai yanzun ka dawo? Ina ka tsaya yau?’ 

Muryar Ummin shi ta dawo mishi, ɗayan ƙafar ya sake ɗagawa ya shigar da ita. 

‘Kun yi sallah ne?’

Wannan karan muryar Abba ce kamar yana gaban shi. Takawa ya ci gaba da yi har yai kwanar da zata shigar da shi nasu ɓangaren. 

‘Wai kai dln ƙaniyarka ba’a saka kayan ka? Takalmin da na ɗauka na je masallaci shi ne zaka cinye ni haka? Anya Ashfaq in kai kuɗi za ka kula da mu?’ 

Maganganun Amjad ne suka dawo mishi. Idanuwan shi ya lumshe yana shiga cikin gidan, ganin babu abinda ya canza, duk da sabon fentin da su Tariq suka yi, hakan bai sa gidan ya canza mishi ba. 

“Dukkan sauƙi da Allah yake ma bayin shi ina roƙon yai muku. Dukkan haske da Allah yake ma bayin shi mafi soyuwa a gare shi ina roƙon ya kai ƙaburburan ku.” 

Ashfaq ya faɗi a hankali yana buɗe idanuwan shi da wani irin yanayi. Kuka ne a watannin nan yayi su kamar ba zai bari ba, yanzun kam baya jin yana da sauran hawaye. Yana son gyara rayuwar shi yadda zai kula da su ba tare da wata

fargaba. 

 Amma tun satin da ya wuce yake tunanin sana’ar da ya kamata yayi ya rasa. Ya iya kasuwanci fiye da tunani, amma na miyagun ƙwayoyi kawai. Yanzun duk wani abu da yai tunanin siyarwa ribar yake hangowa da tunanin abinda zatai mishi. 

Takawa yayi ya ƙarasa har ɗakin shi ya kama labulen yana ɗagawa, yadda sukai kokarine shirya mishi ɗakin na saka shi murmushi. 

“Sannun ku da aiki.”

Ya faɗi yana kallon su ukun da suke tsaye a bayan shi. In ya kira Yasir yanzun su duka biyun sukan amsa shi, shi yasa yake kiran ɗayan Yasir ɗin da Aboki. Yasir kuma Abokin Yaya yake ce mishi. Tariq dama tun kafin ya ji yadda Yasir ɗin da taimakon Allah ya kare rayuwar Ashfaq ɗin a lokuta da dama da suka shiga hatsari kala daban-daban Yaya yake kiran shi, yanzun kalmar tun daga zuciyar shi yake jin tana fitowa, ba su hada jini ba, amman zumuncin su abune da yake da yaƙinin har ƙarshen rayuwar su ne. 

“Nikam fita zan yi.”

Ashfaq ya faɗi. 

“Ina za ka je?”

Tariq ya buƙata, su duka suna tsare shi da idanuwa suna jiran ya basu amsa. 

“Bana son haka, duk inda za ni dole sai kun sani?” 

Ashfaq ya ce yana ɗaure fuskar da bata hana Tariq faɗin 

“Wajen Nudra za ka je ko?” ba. 

Ƙanƙance mishi idanuwa Ashfaq ɗin yayi. Nudra ita ce yarinyar da ya haɗu da ita a asibitin mahaukata lokacin da ya kai Tariq. Baisan me yasa yarinyar ta tsaya mishi ba har yaima ‘yan uwan da suka kawo ta magana. A hankali kuma duk sa’adda zai je duba Tariq zai tsinci kanshi da zuwa wajen ta itama. Ya fara alaƙanta hakan da labarin ta da ya ji. Ita ƙaddararta hatsari suka samu na mota da duka ‘yan gidansu, ita kaɗai ta rayu, a gabanta suka ƙone ƙurmus, duk da taɓin hankalin da ta samu bai da alaƙa da mutuwar su da ta gani, sai buguwar da ta yi sosai akai. 

Lokaci zuwa lokaci abin yakan taso mata, duk da ana samun ci gaba, amma ciwo na hauka ba abu ba ne mai sauƙin sha’ani. Zuwa yanzun har gidan kawunta da yake riƙe da ita yanzun ya sani. Mutanen kirki ne matuƙa. Su Tariq tunda suka ji suka addabe shi da cewar son Nudra yake. Bai musa musu ba, amma bawai ya yarda ba ne ba. A ƙasan zuciyar shi yana jin in ya tsaya da ƙafafuwan shi zai iya auren ta, amma ba wai don ya yarda da abinda yake ji a kanta ɗin so bane yanzun. 

Yana son kula da ita, yana son kare ta daga duk wani abu da yake ƙarƙashin ikon shi har numfashin shi ya tsaya, in yai kwanaki bai ganta ba yana jin son ganin ta, ko da ba wata hirar kirki za su yi ba, idan ya ganta yakan ji nutsuwa ta daban. Kawai lokuta da dama yakan ji son ta a kusa da shi, amma ba wai soyayya suke ko wani abu ba. 

“Na san can za ka je Yaya, a dawo lafiya.”

Tariq ya sake cewa yana murmushi.

“Meye wannan murmushin na fuskar ka? Bansan sau nawa zance muku ba budurwa ta bace ba, Yaya ma take ce min fa, amma sai ku dinga wani murmushi kamar kunsan abinda ban sani ba.” 

Dariya Yasir ya yi. 

“Yanzun meye na faɗan? Babu wanda ya ce ba haka bane ai.” 

Sake ɗaure fuska Ashfaq yayi. 

“Ni dai bana son irin haka. Ku nemi abinda zaku ci.” 

Ya ƙarasa maganar yana tafiya

“Kai dai, mu Hamna ta sa abinci da mu”

Cewar Tariq ɗin, yana jin sunan Hamnan daya kira har cikin zuciyar shi. Shi ma ba zai ce ga inda rayuwa zata kaisi shi da ita ba, tunda yana da sauran shekara ɗaya a makaranta, ko zai nutsu waje ɗaya yasan da sauran lokaci, neman aiki a zamanin da ake ciki ma abu ne da yake zaune da kanshi. Ya dai san Hamna alkhairi ce a rayuwar shi, kamar yadda yasan babu macen da zata so shi yadda Hamna take son shi, tare da ita ba zai taɓa ɓoye yadda da taimakon asibiti yake fama da addiction ɗin ƙwayoyi ba, baza ta taɓa mishi gori akan hakan ba, tare da ita tun yanzun yana samun fahimta akan ƙaddarar da ta jefa shi inda yake a yanzun. 

Duk da yana jin Tasneem har yanzun, sai dai a hankali Hamna take turata can wani waje ƙasan zuciyar shi da soyayyar ta mai sanyi. Daga ita har shi ɗin ya kula ba gwanaye bane a furta abinda suke ji, amma a aikace suke nuna ma juna yadda suke da muhimmanci a rayuwar junan nasu. Tun da suka fara hidimar dawowar nan ko tana gida ko tana makaranta da su ake abinci a gidan. Yana mamakin canzawar Ummin su haka, amma yafi kowa farin ciki da canjin, don ya tabbatar ba su Tasneem kaɗai suka san halin da suke ciki shi da Hamna ba, har ita Ummi ɗin, a tsorace yake shiga gidan ko zata kira shi da kashedin ya bar mata yarinya ba zata ba ɗan shaye-shaye ba. Duk sa’adda zai gaishe ta a tsorace yake yin hakan, babu yabo ba fallasa a fuskarta takan amsa mishi, amma cikin idanuwanta yake ganin karɓuwa. 

Numfashi ya sauke, rayuwa bata kawo su inda suke yanzun cikin sauƙi ba, sai dai sauƙin ya samu a rayuwar su yanzun, sauƙin da baida tabbacin ɗorewar shi, don in akwai abinda rayuwa ta koya mishi yanzun bai wuce rashin tabbas ɗin da take da shi ba. Yasan babu wani sauran rubutu da Alƙalamin Ƙaddara zai musu da ba za su iya ɗauka ba, da taimakon Allah suka ɗauki na baya, yanzun ma da taimakon shi za su ɗauki na gaba. In dai suna tare da junan su duk yadda rayuwa zata ɗibo su ta kayar, za su taimaki junan su wajen sake miƙewa su jira faɗuwar gaba. Lumshe idanuwan shi yayi yana jero duk wata kalar godiya da tazo cikin kan shi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 50Alkalamin Kaddara 52 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×