Skip to content
Part 33 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Kinkiba

Har ya kunna mota da niyyar juyawa ya hango su, baisan hannun shi ya kai kan murfin motar har ya buɗe ba sai da ya ji iska ta dakar mishi fuska, gaba ɗaya zuciyarshi neman fitowa take daga ƙirjinshi ta ƙarasa wajen shi, jikinshi ko ina ɓari yake, so yake ya ƙarasa inda suke, musamman da ya ga wadda ta fito da su ɗin sun miƙe hanya.

“Yara na…”

Ya furta zancen da yake a zuciya, bai taɓa sanin kusanci irin wannan ba tunda yake a rayuwar shi, da duk wani abu da yake da shi yake son bin yaran ya riƙo su, ya gansu, tunda ya ɗora idanuwanshi akan su yake son ƙara ganin su don ya tabbatar suna nan, yaran shi ne, yanzun kam bashi da wani shakku, yadda yake jinsu a zuciyar shi kawai ya tabbatar mishi da jinin shi ne su ɗin. Bai koma motar ba sai da ya hango sun sha kwana tukunna, jikinshi ya gama mutuwa.

Yaran shi yake so, amma baisan abinda ya kamata ya yi ba, ya jima zaune a cikin motar kafin ya kunnata yana takawa, hankalin shi baya jikin shi, sama-sama yake jin shi, ba zai ce yana gane inda yake jan motar ba, tafiya kawai yake yi, yaran shi yake so babu ko shakku a cikin hakan, ya ƙi bari zuciyarshi ta faɗa mishi wani abu da ya wuce wannan, ba zai yi tunanin abinda sanin yana da yaran zai haifar ba, Majida, su Aslam, ba zai yi tunanin ta inda zai fara musu bayani kan asirin shi da yake shirin fitowa fili ba.

Wayarshi ya lalubo yana sauka daga kan titi tukunna, wayar Ashfaq ya kira har wajen sau takwas bai ɗauka ba.

“Don Allah ka ɗaga Ashfaq, bansan me ya kamata in fara yi ba…. Yarana ne wallahi, ka ɗaga don Allah.”

Yake faɗi yana sake kiran wayar Ashfaq ɗin, sai da ya kira wajen sau goma sha biyar, tukunna ya cilla wayar kan kujerar motar yana sake tayar da ita, zuciyarshi na wani irin dokawa da ta jima bata yi ba, lokaci zuwa lokaci yake goge hannunshi jikin wandonshi saboda zufar da yake ji sun mishi. Zazzaɓi sabo ya rufe shi lokacin da ya shiga cikin garin Zaria, ko wucewa zai yi tafiya ta kamashi, da ya gabato Zaria yake taka motar sosai ya ƙara gudu don ya wuce. A yanayin sababbin gine gine da yake cin karo da su ya fara ganin shekarun da ya ɗauka rabon shi da garin.

Lumshe idanuwanshi ya yi yana buɗe su, yana da halaye da yawa, amma ƙarfin halin fuskantar mutanen da yai ma laifi na mishi wahalar gaske, ko don suna da kusancin da shi ne bai sani ba, amma baya iyawa, hakan ya hanashi fuskantar Ashfaq, hakan ya hana shi fuskantar Wadata da ya shafi har su Yaks. Bai yi wahalar tsintar kanshi a ƙofar gidan Wadata ba, zuciyarshi yake ji har kan harshen shi lokacin da maigadi ya buɗe mishi gate, ya fi mintina uku kafin ya samu ya ja motar zuwa cikin gidan, banda fentin gidan babu abinda ya canza. Sai motoci uku da suke ajiye a wajen parking ɗinsu.

Kanshi ya haɗe da abin tuƙin motar, yadda numfashin shi yake fita na sa shi zaton ko yana fama da tsohuwar asthma da baisan da ita ba, jikin shi yake son motsawa don ya fita daga motar amma ya ƙi bashi haɗin kai, wani irin tsoro marar misaltuwa ne yake shigarshi, duk shekarun nan ya yi su ne da tunanin can ƙasan zuciyar Wadata ya yafe mishi, duk da yasan ya tsane shi, baya son ganin shi, amma yana jin sauƙi da tunanin cewa ya yafe mishi. Baisan yadda zai yi yanzun ba, tsanar da Wadata yai mishi da sanin bai yafe mishi ba za su fama mishi ciwuka da yawa.

Jikinshi bai sake mutuwa kan cewar alaƙar da ke tsakanin su da Wadata ta samu tabo na har abada ba, sai da ya fito bayan ɗaurin auren shi bai ga Wadata ba, duk da bai gayyace shi ba yasan Ammi ta tura musu, tunda Hajiyar shi ta zo, kuma suna zumunci da Ammi har kwanan gobe, Barrah ya tambaya ko tana magana da Wadata, ta kalle shi kawai ta wuce, daya takura mata da tambaya cewa tai ya kira Wadata, in yana so yasan ko suna magana sai ya faɗa mishi da kanshi kar ya dame ta.

Sanin halinta yasa bai ƙara tambaya ba ya haƙura, yanzun ma baisan wanda zai tunkara ba, baisan inda zai ga Ashfaq ba, don babu tabbas zai same shi a gidan shi, amma Wadata yasan inda yake, zuwan ne kawai bai taɓa gwadawa ba sai yau. Sosai yake kokawa da numfashin shi, babu shiri ya buɗe murfin motar yana fitowa don iskar ciki ta mishi kaɗan, maida numfashi yake ƙoƙarin yi, kamar daga sama ya ji an ce,

“A-Tafida?”

Numfashin nashi ya ji ya tsaya cak na ‘yan daƙiƙu kafin ya samu ya shaƙi iska tare da juyawa, Wadata ne, jikinshi sanye da shadda ruwan toka mai cizawa, har da hula a kanshi, yadda ya ƙara jiki da wani irin kyau zai nuna maka rayuwar na mishi kirki, ko kaɗan shekaru basu nuna sun ja ba a fuskarshi, sai da Altaaf yai ƙasa da idanuwanshi ya ga yaron da hannunshi ke riƙe cikin na Wadata ɗin, sai dai ya fi Wadata haske, amma akwai kamannin matar Wadata sosai a fuskar yaron.

Wani irin luf zuciyar Altaaf ta yi a ƙirjinshi, yana jin nisan da Wadatan yai mishi duk da yana tsaye a gaban shi, bashi da wani abu a rayuwarshi muhimmi kamar yaron da yake riƙe da shi, hakan kuma ya tsaya mishi a ƙirji da yanayi mai wahalar misaltuwa.

“Ina kwana.”

Yaron ya faɗi yana kallon Altaaf da yake tsaye, a hankali ya tako yana ƙarasowa, tsugunnawa ya yi yadda tsayinshi zai zo ɗaya da na yaron, kafin a hankali ya sa hannuwanshi duka biyun yana tallabar fuskar yaron, soyayyarshi da yara baisan lokacin da ta fara ba, amma ta wannan yaron daban take saboda ya fito daga jikin Wadata. Muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Hey…”

Kallon shi yaron yake yi, kafin cike da shakku ya ɗora hannunshi kan na Altaaf da ke fuskarshi, yanayin da yasa Altaaf jin zuciyarshi ta karye, comfort yake nema ko yaya ne, yaron kuma ya bashi ba tare da yasan ya yi hakan ba.

“Ya sunan ka?”

Ya buƙata.

“Altaaf…”

Yaron ya faɗa, yana saka Altaaf ɗin ɗaga kai da sauri ya kalli Wadata da ke tsaye.

“Yaya Imran…”

Ya kira da wani yanayi mai wahalar misaltuwa, yana son ya tabbatar mishi da cewa da gaske sunan shi ya saka ma yaron, amman baiko motsa ba.

“Daddy na san shi ko?”

Yaron ya tambaya bayan ya zame fuskar shi daga hannuwan Altaaf ɗin.
“Jeka wajen Maminka, zan zo yanzun.”

Kai yaron ya ɗaga yana wucewa, da ƙyar Altaaf ya iya ɗagowa. Kallon shi Wadata yake yi, akwai hankali a tare da wannan Altaaf ɗin, duk da yana karantar tashin hankali kwance a idanuwan shi. Shekara kusan nawa, sai yanzun ne Altaaf zai tako ľafarshi gidan shi, cikin masu ƙarfin hali Altaaf na da babban matsayi sosai.

“Yaya Imran…”

Ya sake kira cikin yanayin da yasa wata dariya da bata da alaƙa da nishaɗi ta kuɓce ma Wadata.
“Me kake yi Altaaf?”

Wadata ya tambaya, da ya ce kar ya neme shi sai ya yi hankali baya nufin maganganun shi, ɓacin rai ne, ya kuma yi zaton Altaaf ɗin ya san hakan, ya yi zaton zai tako ƙafafuwanshi gidan ya bashi haƙuri, Altaaf ɗin da ya sani ba zai tafi ba tare da wani faɗa ba, in ya kama zai kwana a gidan ya ce ba zai tafi ba sai ya haƙura, zai mishi haukan da ya saba ko da yaushe, ba wai ya bar rayuwarshi kamar baida wani muhimmanci ba. Da ya ga an ɗauki watanni bayan gama makarantar Altaaf ɗin, kasa jurewa ya yi ya ɗauki waya ya kira amma sai ya ji a kashe, ya kira babu adadi bayan hakan baya samu, sai ya ƙyale shi kawai tunda ya ji yana lafiya daga wajen Barrah.

Ya sha rasa wayarshi, amma baya kwana bai dawo da layinshi ba, ko da Altaaf zai canza zuciyarshi ya kira wata rana, baya so ya kira ya ƙi samu, amma bai kira ba, sosai ya girgiza da jin maganar auren Altaaf a wajen Hajiya, amma bai faɗa mishi ba, ya so ya ƙi zuwa ɗaurin auren ya kasa, ya je har cikin masallacin, ya fita dai kafin ya ganshi, tun su Yaks na tambaya har sun haƙura, ba zai iya faɗa musu dalili ba saboda a bakin Altaaf ɗin ya kamata su ji. Matarshi ma har fushi tai sosai akan Altaaf, ta ce shi ya kamata ya je tunda shi ne babba, ita ma ta gaji ta haƙura.

Yarinyar shi ta farko macece, sunan Hajiyar shi ya mayar da suke kiranta da Ihsan, sai yaron shi na biyun, babu wanda yai mamaki lokacin da ya mayar mishi da sunan Altaaf, don kowa yasan ƙaunar da ke tsakanin shi da Altaaf ɗin mai girma ce, sai dai abinda basu sani ba, shi da kanshi baisan zai sama yaron shi sunan ba, kewar Altaaf ɗin ce kawai tai mishi yawa, sai da yasa kuma duk idan wani ya kira sai ya ji har cikin ranshi. Sai ya fara kiran shi da Babba, kasancewar yayi wata irin ƙiba da yana karami, yanzun kowa Babba yake ce mishi in ba a makaranta ba.

Ganin Altaaf yayi shiru yasa Wadata juyawa, da sauri Altaaf ɗin ya riƙo hannun Wadata, yana juyowa kuwa ya ɗauke shi da mari, duk shekarun nan sai yanzun ne zai tako mishi gida, me ya zo yi? Ko wajen Altaaf bai taɓa ba duk da marin ya shige shi nesa ba kusa ba, zafin hannun Wadata na nan.

“Allah kar ya sa yaron nan yai maka laifin da za ka dake shi…”

Altaaf ɗin ya faɗi don yana jin har lokacin kunnen shi na wata irin ƙara, marin na shiga har cikin haƙoran shi, har ranshi tausayin yaron ne ya kama shi, yanayin yadda yai maganar na sa dariya kubce ma Wadata, sosai dariyar ke fitowa daga zuciyar shi, kafin ya girgiza kai kawai, yana jin yadda kusancin shi da Altaaf bai yi komai ba duk shekarun nan.

“Ka tafi kawai, ka makara, ba tun yanzun ya kamata ka zo ba.”
Kai Altaaf yake girgiza ma Wadata tunda ya fara magana .
“Don Allah karka koreni, ka yafe min, ka ga har marina ka yi…”

Kallon shi Wadata yake yi kawai babu alamar haƙurin a tattare da shi. Cikin karyewar murya Altaaf ya ce,

“Wallahi banda inda zan je… Kaine kawai sai Ashfaq, ya ƙi ɗaga wayata…”
Numfashi Wadata ya sauke.

“Kana da matsalar gyara tsakaninka da mutanen da suke sonka da halayenka…karka ce min ka rasa Majida…”

Ware idanuwa Altaaf yayii cike da mamaki.
“Ka santa?”

Ya tambaya, ɗan dafe goshi Wadata ya yi yana juyawa kawai, ba don bai yafe ma Altaaf ba tuntuni, wannan laifin ya jima da wuce wa, sai dai ba zai dawo rayuwar shi lokaci ɗaya haka ba, ba zai faru ba. Ganin da gaske tafiya Wadata yake yasa Altaaf ɗin takawa yana bin bayanshi.

“An kwana biyu ba’a taba lafiyar jikin ka ba ko?”

Wadata ya tambaya batare daya juyo ba.

“Tun dukan da kai min, sai kuma an mareni shekaranjiya, sai yanzun ka ƙara min wani.”

Numfashi Wadata ya ja yana fitar da shi da sauti, kanshi har ya fara alamun ciwo.

“Ka daina bina Altaaf, ka tafi kawai, ba ka buƙatata a rayuwar ka, shekararka nawa bana ciki?”
“A’a wallahi, kaine ka tsane ni shi yasa, bansan yadda zan yi in zo ba, amma yanzun da na zo ko dukan ka ba zai sa in tafi ba…”

Tsaye Wadata ya yi yana juyowa, tare da sauke idanuwan shi akan Altaaf ɗin da yai taku wajen huɗu yana matsawa daga kusa da Wadatan, hannuwanshi duka biyun ya ɗago.

“Okay, amma dai karka da ke ni ɗin….na wuce duka Allah kuwa… Don Allah ka barni ka ji.”
Yarintar Altaaf ba za ta taɓa barin shi ba, saboda yana yinta ne ba tare da ya sani ba sam, ba tare da Wadata ya ce komai ba ya fara shirin juyawa.

“Ina da yara, su biyu… ‘Yan biyu ne, mace da namiji.”

Altaaf ya faɗi da sauri, hakan yasa Wadata tsayawa cak, yana kokawa da murmushi da yake son ƙwace mishi, kafin mamaki ya gauraye fuskar shi, Barrah ta ce mishi matar Altaaf bata haihu ba, kuma ko wata ba su yi da yin magana ba, da tana da ciki ma da ta faɗa mishi. Mamakin Altaaf ya gani, wani abu yake ji ya mishi tsaye a maƙoshi, ga shi bakin shi ko yawu babu balle yai ƙoƙarin haɗiye shi.

“Nuwaira…ƙauyen Kinkiba… Yaran… Yaran…”

Altaaf yake faɗi yana kokawa da kalamanshi, ya rasa yadda zai faɗe su don sun mishi nauyi a gaban Wadata.

“Jiya na san da su…ban san me ya kamata in yi ba… Wallahi ban sani ba.”

Wani irin shiru ya biyo bayan maganar Altaaf ɗin, numfashi Wadata yake yi a hankali yana rasa abinda yake ji. Sai yanzun ya tabbatar da ƙaddara ce da rabon yaran ya kaisu Kinkiba, alƙalamin ƙaddara ya riga ya rubuta rabo a tsakanin shi da Nuwaira shi yasa lissafi ya ƙwace mishi akanta, yana kallon yadda tashin hankali yake shimfiɗe a fuskar Altaaf ɗin, sai dai ko yana da niyyar taimaka mishi ba yanzun ba, sai rayuwa ta nuna mishi ɗayan ɓangarenta sosai tukunna.

Bai ce komai ba ya juya.

“Yaya Imran… Don Allah karka barni… Ka ce wani abu… Ya zanyi? Majee zata barni, bata san A-Tafida ba, Altaaf kawai ta sani wallahi… Ka ji don Allah, asirina zai tonu, ba zan iya kallon idanuwan Aslam ba…”

Ba tare da Wadata ya juyo ba ya ce,

“Asirin ka ya rufu na tsawon lokaci, ba komai yake binnuwa ba…”

Ya ci gaba da tafiya abinshi yana jin Altaaf ɗin ya daina binshi, ba ƙaramin kokawa yake da kanshi ba don kar ya juya, in da gaske Altaaf yake yana buƙatar taimakon shi zai dawo, amma yanzun zai barshi yai tunanin in yana da sauran muhimmanci a rayuwar shi ko bashi da shi.

Abuja

A harabar gidan suka samu Aroob a zaune, ko motar bata gama parking ba ta miƙe tana zuwa ta tsaya, wannan karon bata ko kalli su Rafiq ba, hannu take miƙa wa Zafira tun kafin ta fito daga motar, ko bacci bata yi ba daren jiya, kwana ta yi salloli da karatun Qur’ani, dama gidan Rafiq ta kwana, da sassafe ta dawo gida abinta, damuwa ce fal ranta da halin da ‘yar uwarta take ciki, hawaye sun gama cika mata idanuwa, basu samu zubowa ba sai da Zafira ta fito daga motar ta ƙare wa fuskarta kallo, ta ga shatin mari shimfiɗe akai, da ƙananun ciwuka.

“Oh my goodness… Zaf… Zaf.”

Aroob take faɗi tana riƙo fuskar Zafira da take mata murmushin ƙarfin hali duk da hawayen da ke cike da nata idanuwan itama, rungumeta Aroob ta yi kamar za ta mayar da ita cikin jikinta.

“Babu abinda zai sake samunki in sha Allah… Yaya ba zai bari ba… Yaya ba zai bari ya sake taɓa ki ba.”

Aroob ɗin take faɗi da wani yanayi a muryarta da yasa Rafiq yin murmushin takaici, yadda suka yarda da shi har haka na bashi mamaki, suna da yaƙinin zai iya karesu daga duk wani abu marar kyau da Allah ya bashi iko, gashi yanzun sai da Zafira ta kira shi tukunna ya san da matsala a gidanta. Shi ya fara wucewa gaba tukunna suka bi bayanshi har cikin babban falon gidan da ya taka ƙafarshi ciki tare da yin sallama. Nuri da ke zaune ta taso tana riƙo hannun Zafira da ke cikin na Aroob, tsaye Zafira ta yi, bata saba raba damuwarta da Nuri ba, Rafiq ne a wannan ɓangaren na rayuwarta, don haka bata san ya zata fara ba.

Bata san tana buƙatar Nuri ba sai da ta ji ta rungume ta, wani irin kuka ta saki mai cin rai da ya sa Nuri kallon Rafiq, a hankali ya ce,

“Zan je gida, zan dawo Nuri.”

Kai kawai ta ɗaga mishi, Fawzan ya kalla.

“Ka huta, ka sha magungunanka. Aroob bacci ne a idanuwanki, ku kwanta don Allah ku barta a wajen Nuri, nima zanje gida in huta ne.”

Kai suka jinjina mishi su biyun. Harya juya Aroob ta ce,

“Yaya…”

Juyowa yayi yana kallon ta.

“Thank you…”

Ta ce, ɗan murmushi kawai yayie yana ficewa daga falon. Kanshi ya mishi nauyi sosai. Wajen motarshi ya nufa don Isah ne ya ɗauko su daga airport dama, yana buɗe bayan motar ya shiga, Isah ya ja su yana fita daga cikin gidan, sai da suka hau hanya sosai tukunna ya ce,

“Yallaɓai ba za’a tsaya wani waje ba? Mu wuce gida kawai?”

Kai Rafiq ya dafe yana faɗin,

“Mu biya in yi take away.”

Suna buƙatar ‘yar aiki, tunda Tasneem ba cikakkiyar lafiya gare ta ba, zai ma Nuri maganar, ya gaji da siyan abinci kullum. Ganin isa yai parking ne yasa Rafiq ɗin sa hannu a aljihu ya zaro katin shi yana miƙa wa Isah.

“Abinda duk kaga ya maka ka siyo guda biyu, sai ka siyan ma kanka da matarka kuma.”

Rafiq ya faɗi, bajin cin abincin yake ba, saboda Tasneem ne kawai zai siya, baya son fita daga motar kuma a yanayin da yake jin shi. Isah bai wani jima ba ya dawo da ledoji a hannun shi yana miƙa ma Rafiq ɗin wasu da kuma katin shi, tare da yi mishi godiyar da ya amsa da kai yana mayar da idanuwanshi ya lumshe. Bai sake buɗe su ba sai da ya ji tsayuwar motar ya tabbatar yana cikin gidanshi tukunna, Isah ya buɗe mishi ƙofa ya fito yana wucewa cikin gida. Da sallama ya shiga, zuciyarshi na wani irin dokawa saboda bai zaci zai ga Tasneem a falon zaune ba.

Tana jin sallamar shi ta miƙe tsaye, fuskarta da murmushi, abinda ya kwana biyu bai gani ba, zai iya cewa tun daren auren su rabon da ya ga murmushi haka a fuskarta, atamfa ce a jikinta da ɗinkin ya zauna mata sosai, duk da babu kwalliya a fuskarta ta mishi kyau na ban mamaki, ta ƙara haske kamar ba ita ba, na minti ɗaya ya manta da matsalar da ke tsakanin su, yana jin yadda zuciyarshi ke buɗe mata, kafin ya ji kamar an soka mishi wani abu a ƙirji mai zafin gaske, maza nawa suka taɓa mishi fuskarta ɗin nan, kishin da ya taso mishi na barazanar saka numfashin shi ya tsaya.

Cikin idanuwan shi ta fara ganin alamar zai mata murmushi, kamar da gaske murmushi zai mata kafin ta ga wani abu da ta kasa fassarawa na maye gurbin murmushin, ta ɗan ga giccin Rafiq ɗinta kafin ya sake ɓace mata. Ba zata yi ƙarya ba, cikin jikinta ya bata wani irin ƙarfin gwiwa, kuma magungunan da aka bata a asibiti ta ji daɗin su, tun safe rabonta da yin wannan tarin, ƙirjinta ya mata sauƙin nauyin da yake yi.

“Sugar… Sannu da zuwa.”

Ta faɗi cikin sanyin murya, kai kawai yadani ɗaga mata daga farko, kamar bazai magana ba, tana kuma tsananin son jin muryarshi, ko yaya ne, kafin ya ce,

“Ya jikin ki? Da sauƙi ko?”

“Alhamdulillah.”

Ta amsa mishi da murmushi a fuskarta har lokacin, bata son ƙarasawa inda yake da ta karɓi ledojin hannun shi, ganin babu sauran abinda zata yi yasa ta koma ta zauna, sai da ya cire takalmanshi tukunna ya tako inda take yana ajiye leda ɗaya.

“Jiya ma girki muka yi da Aroob, tunda na ji ƙarfi yanzun ka daina siyowa.”

Kai yake girgiza mata tun kafin ta ƙarasa, bata da lafiya, likita ya ce ta samu hutu sosai, ba zai bari ta fara shiga kitchen ba, idan wani abu ya sameta ba zai yafe wa kanshi ba.

“Zan yi ma Nuri magana a turo mana me aiki.”

Wani murmushin Tasneem ta yi, yadda ya ce a turo musu, ya haɗa ita da shi a kalma ɗaya ya mata daɗi, zata yi iya ƙoƙarinta ko soyayyar da yake mata bata dawo ba ya yafe mata, don haka bata yi mishi musu ba.

“To shikenan.”

Ta amsa a taƙaice, bai ce komai ba ya wuce zuwa ɓangaren shi, ya ɗan jima a tsaye bayan ya tura ƙofar, kafin ya ajiye ledar hannunshi a nan ƙasa ya wuce yana zama gefen gado, fuskarshi yasa cikin hannuwa yana sauke numfashi, ko kaɗan baya jin daɗin rayuwar, komai yai mishi wani irin ɗif, kamar an saka shi a ɗakin da babu ko window ballantana ƙofa, babu wajen da iska zata shigo sai wadda ya samu a ɗakin da ta fara mishi kaɗan, yana buƙatar ya shaƙi wata iska daban ko zai samu sauƙi.
Tsoron kanshi yake yanzun, don yasan kamar bam haka yake, lokaci kawai yake jira ya tarwatse, baisan a yanayin da hakan zai faru ba, amma zai faru, har cikin ƙasusuwan jikinshi yake jin hakan zai faru ba da jimawa ba. Kwanciya ya yi ya rufe idanuwanshi ko zai samu bacci, amma zuciyarshi ta ƙi yin shiru da tunane-tunane da baisan tushen su ba. Ya jima sosai kafin bacci mai ƙarfi ya ɗauke shi.

*****

“Samee ki barni in huta dln Allah…”

Ya faɗi yana ture Samira da ke kwance a jikinshi gefe ɗaya yana juyawa, dariya ta yi tana sake matsawa ta kwanta saman jikin shi, ture ta ya sake yi wannan karon yana jin kamar lema a jikin shi da tasa shi taɓa wurin ya dawo da shi izuwa dubanshi. Ja da ya gani kamar alamun jini ya saka shi miƙewa babu shiri. Gaba ɗaya gadon da yake kai jini ne ko ina, Samira yake nema bai ganta ba, cikin wani irin tashin hankali ya duro daga kan gadon, sai dai me yanzun jinin yake gani a hannuwan shi duka biyun da yake gogewa a jikin kayan shi da sauri da sauri.

Kukan jariri ne ya ji ya gauraye ɗakin, duddubawa yake ya ga ko daga ina yake fitowa, kafin ya duba ƙasa kusa da ƙafafuwanshi yana fara ganin towel ɗin yara fari ƙal da ya gama ɓaci da jini, kai yake girgizawa cikin sabon tashin hankali yana neman Samira a ko ina na ɗakin, bai kuma daina jin kukan jaririn ba…

*****

“Innalillahi wa inae ilaihir raji’un…”

Rafiq ya furta da ƙarfi yana buɗe idanuwan shi, ya haɗa wata irin zufa, duk da AC ɗin da ke aiki cikin ɗakin, miƙewa ya yi zaune yana maida numfashi tare da duba hannayenshi da kan gadon ko zai ga jini, amma bai gani ba, wanne irin mafarki ne wannan? Yake tambayar kanshi, sunan yarinyar cikin mafarkin yake son tunawa amma wani irin ciwon kai ya ji yana mishi sallama babu shiri ya runtsa idanuwan shi gam, yana ganin wani irin haske ya gilma mishi ta cikin idanuwanshi daya ƙara mishi ciwon kan da baisan yana kiran sunan Allah cike da neman taimako ba.

Da duka hannuwan shi biyu ya dafe kan, sai da ya koma ya kwanta, baisan yadda hauka yake ba, amma yana jin shi yake shirin samun shi don ciwon kan da yake ji ya wuce misali, da ƙyar yake iya mayar da numfashi. Ya samu ya fara mishi sauƙi, wayarshi ta ɗauki rurin da kamar cikin ƙwaƙwalwar shi take yinshi, cikin sauri ya sa hannu cikin aljihu yana ciro ta, kashewa zai yi amma hasken ta na shigar mishi ido, dishi-dishi ya ga sunan Aroob, hakan yasa ya ɗauka babu shiri, yana karawa a kunnenshi.

“Yaya Fawzan na maka text tun ɗazun ina ta kiran wayarka ban samu ba, wata na buga ma mota, ka duba ka ga inda nake, ka yi sauri ka zo, karka faɗa ma Yaya Rafiq zai kashe ni wallahi.”

Aroob ta ƙarasa kamar zata yi kuka, ciwon kan da yake ji bai hana shi miƙewa zaune ba, yana kuma tunanin yadda akai daga Fawzan har Nuri suka bar Aroob ta fita da mota.

“Ni kika kira ba Fawzan ba. Kina dai-dai ina?”

Rafiq ya faɗi muryarshi can ƙasan maƙoshi.

“Yaya…”

Aroob ta kira a tsorace

“Kina ina Aroob?”

Faɗa mishi ta yi, wajen babu nisa da gidan shi, kashe wayar ya yi, ya kira Isah, da ƙyar ya iya miƙewa kanshi kamar zai rabe gida biyu ya fito daga ɗakin. Tasneem tana nan zaune tana kallon wata tashar Hausa da baisan waccece ba, kawai ya ji maganarsu da Hausa ne. Ita kuma jin takun tafiyarshi ne yasa ta juyawa, kallo ɗaya taima yanayin shi bata san lokacin da ta miƙe tana ƙarasawa inda yake tsaye tare da kamo hannun shi ba.

“Sugar… Me ya same ka?”

Ta tambaya cike da damuwa da kulawa, hannunshi yake ƙoƙarin ƙwacewa, baya son tana taɓa shi da nata jikin da wasu suka gama taɓawa, baya so ko kaɗan, ƙazantar hakan yake ji. Amma ta ƙi sakin shi, asalima ɗayan hannunta ta kai fuskarshi tana taɓa kuncin shi da wuyanshi.

“Zazzaɓi ne a jikinka… Sannu… Zo ka zauna in ɗauko maka panadol.”

Tasneem take faɗi, hannunshi ya ƙwace, yana saka ɗayan yana ture hannuwanta, har ranta hakan yai mata ciwo sosai, amma ta danne, ƙyamarta yake, tana ganin hakan ta hanyar yanayin da ke fuskarshi.

“Ki barni Tasneem.”

Wani abu ta ji ya tokare mata zuciya. Tasneem yau ba Neem ɗin ma, sauke hannayenta ta yi, tana kallon shi har ya kai ƙofar tukunna ya ce mata,

“Zan dawo yanzun…”

Yana ficewa abinshi, wajen mota ya ƙarasa inda Isah yake tsaye yana jiranshi ya buɗe ya shiga yana faɗa mishi inda zai kaishi, har wajen Isah ya ƙarasa, suna hango su Aroob ɗin suma sunyie parking a gefen titi, fita daga motar Rafiq ya yi, ‘yan ƙanƙance idanuwanshi ya yi saboda hasken da yake ƙara mishi ciwon kai, a nutse yake takawa har inda suke tsaye, idanuwanshi kafe kan Aroob.

“Yaya…”

Yanayin kallon shi da ya canza yasa Aroob ɗin yin shiru, juyawa ya yi yana kallon ɗayar yarinyar don su yi magana, ganinta yasa shi ware idanuwanshi gaba ɗaya, zuciyarshi na wata irin dokawa da wani irin kusanci da ita marar misaltuwa. Itama da sanayya take kallonshi, wannan ne gani na uku da yai mata, baisan me yasa yake jin kamar ya santa duk tsawon rayuwarshi ba.

“Sannun ki…”

Ya ce mata.

“Sannu.”

Ta amsa, muryarta na dukan kunnuwanshi da wani irin yanayi, da duk kallon da zai mata da yadda yake jin wani irin abu na fisgarshi a tattare da ita.”Ki yi haƙuri don Allah, zan baki katina, in kun yi magana da mai gyaranki sai ki faɗa min ko nawa ne, ko kuma in kira mai gyarana sai ya duba.”

Rafiq ɗin yake faɗi yana laluba aljihunshi don yasan ba zai rasa katin shi na wajen aiki dazai iya bata ba, aikam ya samo yana miƙa mata, hannu tasa ta karɓa.

“Zan kiraka in mun yi magana da mai gyara na.”

Kai ya jinjina mata, akwai wani abu tattare da yanayin hausarta da yai mishi tsaye.

“Na gode…”

Ya faɗi yana ɗauke idanuwanshi daga kanta tare da mayar da su kan Aroob.

“Don Allah ya sunanka?”

Ta buƙata, tana sa Rafiq juyawa.

“Rafiq Mustafa Shettima.”

Ya faɗa mata yana kallon yadda yanayin fuskarta yake nuna alamun tana son tuna inda tasan shi ko ta taɓa jin sunan shi, kafin ta girgiza kanta cike da yanayin da ke fassara ‘Ina na san shi?’. Ɗan murmushi ta yi mishi tana juyawa tare da ci gaba da duba yadda Aroob ɗin tai mata ɓarna sosai, ya ga mutuncin ta da bata kira ‘yan sanda ko ta nemi tara ma Aroob ɗin mutane ba. Ganin babu maganar da za su ƙara yi ne yasa Rafiq juyawa da nufin komawa motarshi, da gudu Aroob ta bi bayanshi tana saƙala hannunta cikin nashi ta riƙo shi.

“Yaya… Wallahi abu kawai zan siya in koma fa.”

Hannunshi yake ƙoƙarin zamewa, ba zai iya da Aroob ba yanzun kam, kanshi na ciwo, ganin yarinyar nan kuma ya saukar mishi da wani yanayi da ba zai iya misaltawa ba. Tsayawa ya yi yana kallon Aroob da ke shirin yi mishi kuka.

“Amma na hana ki fita da mota ke kaɗai ko?”

Kai ta daga mishi, idanuwanta cike da hawaye
“Ki tafi gida, kiyi tuki kaman kina kaen keke, ko ya dai ki yi, amma don Allah karki  sake buga ma kowa mota, ba don banda kuɗin biyansu ba sai don lafiyarki, kaina na min ciwo bazan iya miki faɗa ba.”
Cike da damuwa ta ce,

“Sannu… Don Allah ka yi haƙuri… Ka ji?”

Kai Rafiq ya ɗaga mata yana jin kamar yayi shifting ƙwaƙwalwar shi da yadda hakan yasa ta amsawa. Hannun Aroob ya zame daga cikin nashi yana wucewa ya shiga motar shi, Isah ya ja shi zuwa gida.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 32  Alkalamin Kaddara 34  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×