Skip to content
Part 34 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Kano

Bacci ya samu Ashfaq na yi, yasan da taimakon allura ko magunguna, tunda har ƙofar da ya turo da takun tafiyar shi bai tashe shi ba. Kujera ya ja yana ɗaukar lemon zaƙin da ke ajiye guda ɗaya tukunna ya zauna. Akwai nutsuwa a tare da Ashfaq ɗin da Tariq ya jima bai ganta ba. Kallon shi yake yi sosai, da tabbunan da ke jikin shi da baisan inda ya same su ba, akwai ɗinki a gefen fuskar shi, shi kaɗai ne zai iya tuna bayan rasuwar Amjad ne ya shigo da shi gida. Runtsa idanuwan shi ya yi yana jin wani irin ɗaci a zuciyarshi da sunan Amjad ɗin da ya kira, komai na ranar na dawo mishi kamar a lokacin ya faru. 

***** 

Ko bayan rasuwar Babansu da Mamansu, Tariq zai ce rayuwar bata yi musu ƙunci ba, bata yi musu duhu ba, duk da akwai canji mai girman gaske a cikin ta, canjin farko shi ne barinsu daga makarantar kuɗin da suke yi zuwa ta gwamnati, hakan ya faru ne da taimakon Amjad, don baban abokin shi ya ɗauke shi aiki a garejin gyaran motar shi. Nashi karatun a gefe ya ajiye don nauyin kula da su da mutuwar iyayensu ta ɗora mishi ba tare da shiri ko zaɓin hakan ba. 

Sai dai cikinsu babu wanda mutuwar mahaifiyar su ta gigita irin Ashfaq, ko bayan rasuwar mahaifinsu makaranta kawai take fitar da shi, yana manne da ita, lokacin da ta fara rashin lafiya kuwa daina zuwa ya yi, sai an yi da gaske yake miƙewa ya yi sallah, mutuwar ta shige shi ba kaɗan ba, dama ba mai yawan magana bane, sai ya sake yin wani irin sanyi na ban mamaki. Yanzun kam kullum yana tare da autarsu Arfa. Ko a waje yake zaune yana tare da ita, in ba makaranta za su je ko sun kaita gidan su Tasneem ba, itama yarinyar da kuka ake rabata da Ashfaq. 

Girki ma Ashfaq ɗin yake musu, don banda ruwan zafi babu abinda suka iya dafawa, Ashfaq kuwa yana taya mamansu girki lokuta da dama, in dai yana gida tana kitchen to suna tare. Yanzun ma da Tariq ya shigo gidan da sallama ya samu har ya gama dafa musu dafa-dukar shinkafa da kifi, ya zubo a ƙaramin plate, Arfa na zaune a jikinshi, shi kuma yana fifita abincin da alama ita zai ba. 

“Yaya me ka dafa?”

Tariq ya tambaya kamar bai ga abinda ke cikin plate ɗin ba, ɗagowa yayii ya kalle shi a kasalance.

“Shinkafa, dafa-duka Tariq.”

Yanayin yadda ya amsa a gajiye yasa Tariq ɗin yin ‘yar dariya. Yana wucewa kitchen ya zubo abincin ya fito tsakar gida, waje ya samu ya zauna, ƙafafuwan shi da sukai baɗe-baɗe da ƙasa Ashfaq ya bi da kallo. 

“Daga ina kake?”

Ya bukatae a taƙaice. 

“Maƙabarta…”

Tariq ya amsa yana saka abincin a bakinshi tare da taunawa. 

“Wa ya rasu?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Tariq ya yi. 

“Nima ban sani ba fa, na ga za’a tafi ne Na bi.” 

“Tariq…”

Ashfaq ya kira cike da damuwa, girgiza mishi kai Tariq yake da alamun yai shiru, kar ya fadie ko me yake shirin faɗa, don ba zai ji shi ba ma. 

“Ka barni Yaya…ina bukatare gani, ko da ban yarda da mutuwa ba yanzun tabbacinta ya zauna min daram, ina son sanin tana faruwa a kowanne gida kamar yacda ta faru da mu…kukan da suke yana sanyaya min zuciya, ba mu kaɗai ba ne ba.” 

Tariq ya ƙarasa yana cika bakinshi da abincin don kar ya sake wata maganar, yana jin idanuwan Ashfaq na yawo akan shi, tun da ya ga Tariq bai yi kuka da rasuwar Mama ba yasan akwai matsala, ko yaya ne ya kamata ya rage raɗaɗin da ya san yana ji a cikin zuciyarshi, wata na uku kenan, amma kullum da dare sai ya yi kuka yake iya bacci, har yanzun in ya tashi da safe ya fito tsakar gida na ‘yan daƙiƙu zuciyarshi na tsammanin zata ga Mama tana hidimarta, sai ya tuna da hannunshi ya kama ta aka gitta a kabari, sai zuciyarshi tai wani irin ƙunci marar misaltuwa. 

Amman Tariq ko sau ɗaya bai yi kuka ba, yana shiga asibitin ya ga suna haɗa kaya ya tambaya mai ya faru, aka ce ta rasu. 

‘Ita ma?’ 

Ita ce tambayar da yai musu, bai jira amsar su ba ya fara taya su haɗa kayyakin, har aka haɗa ta, da shi aka yi komai, haka maƙabarta, amma Ashfaq bai ga ya yi kuka ba, da ya tambaye shi ko yana lafiya, cewa ya yi lafiyar shi ƙalau, mutuwa ce, su ma duk jiranta suke, kuma ba wai bata faru da su ba ne ba tunda Baba baya nan, sai ya ƙyale shi, amma har ƙasan zuciyarshi akwai damuwa da yake ji dangane da yanayin Tariq ɗin. Kuma bashi kaɗai ya kula Tariq ya samu matsala ba, har Yasir ma, don shi ya fara mishi magana kan baya jin Tariq na da lafiya. 

Kullum in ya dawo makaranta sai ya kai yamma bai shigo gidan ba, yana yawo unguwanni yana tambaya ko an yi rasuwa a je kai gawa da shi, haka zai dawo ƙafafunshi baɗe-baɗe da jar ƙasa. Yana hira kamar yadda yake yi da, yana damun su duka da tsokanar shi ko da ba za su kula shi ba, yana dariya fiye da su yanzun, idan ka ganshi ba za ka taɓa cewa wani abu na damun rayuwar shi ba, ko wani abu ya canza a tare da ita, haka yana maganar su Mama kamar rashin su baya mishi ciwo, amma su da suka sanshi sukan gane hakan, don in yai dariya Ashfaq najiny ta har cikin zuciyarshi, yana jin yadda kwata-kwata babu nishaɗi a tare da sautin dariyar. 

Baisan ya aka yi yake gane hakan ba, ko idanuwan Tariq ka kalla, akwai ƙunci shimfiɗe a cikin su, yana jin shi helpless, saboda baisan yadda zai taimaka ma Tariq ɗin ba in har baya nuna yana buƙatar hakan daga gare su. 

“Gishiri yai yawa a abincin nan, ba kamar na Mama ba.” 

Ya faɗi yana ƙarasa cinye wanda ya rage a farantin tare da ɗaukar ruwan da Ashfaq ya ɗibo ma Arfa ya fara sha. 

“Yaa Tariq nawa ne fa”

Arfa ta faɗi cike da rikici. 

“Ƙyale shi ya shanye ya ɗibo miki wani…”

In ji Ashfaq ɗin yana gyara mata zama a jikin shi, Tariq bai ma shanye ruwan ba, ya ajiye mata sauran. 

‘Ban shanye ba ma…”

“Nawa ya fi wannan yawa, ka ƙaro min.”

Daƙuna mata fuska Tariq ya yi, yana ganin tana shirin kuka, hararar shi Ashfaq ya yi, hakan na sa shi yin dariya. Yasir ne ya shigo gidan kamar wanda wani abu ya koro don ko sallama bai yi musu ba. Tsugunnawa ya yi yana kokawa da shige da ficen numfashin shi, kafin ya miƙe yana dafe kanshi da duka hannuwan shi biyu, har lokacin ya kasa dai-daita numfashin shi, yanayin shi na sa Ashfaq sauke Arfa daga jikinshi, ƙafafuwanshi na ƙarasawa inda Yasir yake tare da riƙo hannun shi. 

“Yasir…”

Ashfaq ya kira a tausashe, yana ganin yadda jikin Yasir ɗin ke ɓari 

“Yasir ka nutsu don Allah, ka zo gida, ka zo gida, ko menene ba zai biyo ka nan ba….” 

Dariya Yasir ya yi da sautinta ya samu wani waje ya zauna a zuciyar Ashfaq ɗin, don baya jin zai taɓa manta yanayin sautin, yana cike da fassara kala-kala, rashin yarda da furucin shi akan ko menene Yasir ɗin ya gani ba zai biyo shi ba, tsoro na cewar hakan na faruwa, ko meye ma jiran shigowar shi kawai Yasir ɗin yake yi. Tariq kuwa bai motsa daga inda yake ba, yana kallon su ne kawai. Hannun Ashfaq da ke jikinshi Yasir yake turewa, amma ya ƙi sakin shi. 

“Ka nutsu mana Yasir…”

Ashfaq ya sake faɗa, kafin ya ji takun tafiyar mutane suna ƙoƙarin ƙarasowa cikin gidan, lokaci ɗaya zazzaɓi mai zafin gaske ya lulluɓe shi, ga zuciyarshi da tai wata irin dokawa da ƙarfin gaske, kafin ya ji jikinshi gaba ɗaya ya yi sanyi. 

“Ku matsa daga hanya…”

Wani cikin samarin unguwarsu da Ashfaq ɗin ya gane ya faɗi, amma daga shi har Yasir babu wanda ya motsa, sai dai ture su suka yi suna shiga cikin gidan sosai, Ashfaq baisan ya saki Yasir ba, kallon su yake wani abu na kwancewa a zuciyarshi, ƙwaƙwalwarshi na kasa fahimtar abinda suke yi saboda ya fi ƙarfinta. Binsu da kallo Tariq yake tunda suka shigo, amma idanuwanshi na kafe ne kan Amjad da yanayin yadda suka riƙo shi kamar ya musu nauyin da yake tsoron ya fahimci dalili. Ƙirjinshi naɗe yake da irin rawananin nan da samari kan yi gayu da shi ta hanyar ratayawa akan wuyarsu. 

Sai dai Tariq ba zai ce ga kalar rawanin ba, jinin da ke jiki ya canza asalin kalar shi, kallon Amjad ɗin yake yi har suka shimfiɗar da shi a ƙasa, idanuwan shi a lumshe suke, baisan ya miƙe ba balle ya taka ya ƙarasa inda Amjad ɗin yake kwance, saida ya tsugunna gabanshi tukunna, hannun shi Tariq ya ɗago yana kaiwa daidai hancin Amjad ɗin, baisan lokacin da shiga da fitar numfashi yake ɗauka ba, amma baya jin ya kai tsayin da hannunshi ya ɗauka a saitin hancin Amjad ba tare da ya ji ya yi hakan ba. Bai damu da jinin da ke jikin rawanin ba ya ɗora hannun shi kan zuciyar Amjad ɗin. 

Wata irin lema mai sanyi ya fara ji a jikin hannun nashi, kafin ya danna, sai ya ji kamar ɗumi da alamar jinin na sake fitowa, nan ɗin ma wani irin shiru ya ji daga ƙirjin Amjad ɗin inda zuciyar shi take har cikin ƙwaƙwalwarshi, miƙewa tsaye ya yi, hannun shi da yake jin lema a jiki ya goge a wandon shi, sosai yake goge jinin a jikin kayan shi, murmushi ya yi yana kallon su Ashfaq da Yasir da suke tsaye fuskokinsu ɗauke da tashin hankalin da yasan ba zai canza abinda ya faru ba, har lokacin yana murmushi ya ce, 

“Ya rasu shi ma…”

Yana kallo Ashfaq na girgiza mishi kai, kafin Yasir da ke bayan Ashfaq ɗin ya ja wani irin numfashi yana sulalewa ƙasa, Tariq na kallon mutane sun yi kan Yasir da gudu, hankalin shi ya mayar kan Ashfaq. 

“Ka taɓa shi ka ji ko shima ya rasun ne.”

Ƙafafuwan Ashfaq na rawa ya ƙarasa inda Amja yake ya tsugunna, sai dai hannuwanshi duka ɓari suke, ya kasa ɗago su ya taɓa Amjad ɗin. 

‘Ina nan, zan kula da ku Ashfaq, bansan ta yaya ba, amma zan samo hanya, don Allah ka daina kuka kamar kun rasa komai gaba ɗaya, ina nan…’ 

Maganar Amjad ɗin bayan rasuwar Baba ta faɗo ma Ashfaq 

‘Don Allah kuban wata damar, na kasa akan Mama, amma bazan kasa akan ku ba, zan yi duk wani abu da Allah Ya bar ikonshi a hannuna, karku karaya, Ina nan tare da ku , ina nan.’ 

Wasu maganganun bayan rasuwar Mama da Amjad yai mishi, hannuwan shi duka biyun yasa yana girgiza Amjad a hankali .

“Ka tashi, ba haka muka yi da kai ba…wallahi ba ka ce min za ka barmu ba, ka ce kana nan… Ya kake so in yi da su Tariq? Ta ina zan fara? Ka tashi saboda ban shirya ba… Amjad kar kai min wannan wasan don Allah…” 

Ashfaq yake faɗi muryarshi ɗauke da wani yanayi, kanshi yake ji ya yi nauyi kamar an ɗora dutse, da rasuwar Mama wani irin duhu ya samu zama tare da shi, sai ya yi da gaske yake ganin haske cikin kanshi, wani karon sai yana sallah hakan yake faruwa, amma a hankali duk rana kulawar Amjad na shigar mishi da wani haske, yanzun ya fara jin ƙofofin hasken na dishewa a hankali, shi yasa yake ci gaba da girgiza Amjad ɗin, bashi kaɗai yake buƙatar ya tashi ba, har su Arfa. 

Mutuwa ba za tai musu haka ba, ba za su rasa makusanta uku a kasa da wata shida ba, hakan ba zai faru da su ba 

“Amjad don Allah….don Allah ka tashi? Meye wannan a ƙirjinka? Har jini kuka samo don kai wasa da hankalina? Ka yi haƙuri haka, indai kan rashin haƙuri da mutuwar Mama ne wallahi na haƙura, ka tashi, kana nan ai, komai zai yi sauƙi tun da kana nan, amma ka tashi.” 

Dariya Tariq yayi saboda ita ta fara zuwar mishi, hakan na sa Ashfaq ya ɗago ya kalle shi, shi ma murmushi yayi, tunda Tariq yayi dariya wasa Amjad yake musu. Girgiza kai Tariq yayi yana komawa kan kujerar shi ya zauna, su ma jira suke, haka mutuwa zata gano su ɗaya bayan ɗaya sai kowa ya ƙare tukunna, jiran Ashfaq yake ya gama surutan shi da ba za su canza komai ba su haɗa Amjad ɗin su kai shi, su dawo su jira kuma su ga waye zai riga wani a cikin su. 

Abban su Tasneem ne ya shigo gidan da saurin shi yana faɗin, 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Yana ƙara maimaitawa, Amjad ɗin ya hango a kwance, sai kuma mutane sun lulluɓe Yasir, wajen Yasir ya fara nufa yana kurɗawa cikin mutane ya tsugunna ya riƙo shi a jikinshi yana karɓar butar ruwan da ke hannun wani saurayi ya zuba a hannun shi yana shafama Yasir, amma ko motsi bai yi ba, ɗaya daga cikin Samarin ya kalla yana tambayar, 

“Me ya samu Amjad ɗin?”

Don shi yana wajen ginin da suke yi nan bayan unguwar aka zo aka kira shi, bai tsaya jin me ya faru ba ya kamo hanya, ko takalmanshi bai kula ƙafa ɗaya ya saka ba saboda tashin hankali, babu kalar addu’ar da bai yi ba a hanya, da yaran yake kwana da su yake tashi, baya jin za su iya ɗaukar wani rashin da wuri haka, sai dai lamurra na Ubangiji sun fi ƙarfin bawa ya fahimta, rubutun alƙalamin kaddararsu kenan. 

“Wallahi aiki yake yi ya shiga ƙarƙashin mota, baisan an riga an fara kwance wani ƙarfe ba, shi ya faɗo mishi a ƙirji, sa’adda aka je asibiti ma har ya rasu don sun ce ciwon da ke ƙirjinshi mai zurfi ne ya huda zuciyar shi, jinin ba a waje kawai yake zuba ba har daga ciki….” 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Abba ya faɗi yana runtsa idanuwanshi ya buɗe su kan Yasir, ruwan ya sake shafa mishi yana sauke ajiyar zuciya ganin ya buɗe idanuwa yana wani irin jan numfashi. 

“Abba wai Yaya Amjad ya rasu? Haka Tariq ya ce ya rasu…” 

Yasir ya faɗi yana jin wani waje na buɗewa a zuciyarshi, tunda ya gansu a wata ƙaramar mota ya hango sun buɗe, ya ga fuskar Amjad ɗin ya shige gida da saurin shi, yana addu’ar bai ga dai-dai ba, yana addu’ar ba Amjad ya hango ba, saboda yadda gaban shi ya faɗi ya tabbatar mishi akwai matsala. 

“Ku yi haƙuri Yasir…”

Shi Abba ya iya faɗi, ture shi Yasir yayi yana sauka daga jikin shi, ya kasa ma miƙewa gaba ɗaya, ba zai ce ga yadda ya ƙarasa kan gawar Amjad ba, fuskar shi yake taɓawa, sanyin ta da ya ji na tabbatar mishi babu rai a tare da shi, wani gunjin kuka ya ji ya taso mishi daga zuciyarshi zuwa maƙoshin shi. 

“Don Allah… Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…Yaya…” 

Yasir yake faɗi muryarshi na sarƙewa saboda kukan da yake, ganin Ashfaq na kallon shi yasa shi faɗin, 

“Ya rasu… Ya rasu wallahi… Ya rasu…”

Numfashi Ashfaq yake kokawa da shi, amma yana mishi wahalar fitarwa saboda ba su yi haka da Amjad ba, da bakin shi ya tabbatar mishi yana nan babu inda za shi, baisan me yasa zai mishi haka ba yanzun, kuka yake ji yana fitowa daga wani ɓangare na zuciyarshi da wani irin ciwo na gaske. Tariq na kallon su, Arfa ma yasan kukan da suke ne ya sa ta komawa kan bayan Ashfaq ta kwanta tana kuka. Kallon su kawai yake bai ga amfanin kukan da suke yi ba tunda ba zai canza komai ba. 

***** 

A hankali ya buɗe idanuwan shi, kanshi na wani irin nauyi, miƙewa yayi, syrup yake buƙata, dama komai ya fara ne bayan rasuwar Amjad ɗin, yana son rufe tunanin nan daga cikin kanshi, ba zai bari ya takura shi ba, akwai sauran awanni kafin ranar ta ƙare, ba zai yi su da tunanin abinda ba zai iya canzawa ba. Miƙewa ya yi yana ajiye lemon zaƙin inda ya ɗauke shi ya taka ya fice daga ɗakin. 

Abuja

A hanya ta kira mai musu gyaran mota ta ce ya zo gida ya ɗauki motar, yanzun hankalinta gaba ɗaya yayi gida, babu abinda zai hana Hamma Saifu ya kashe ta in ya ga ɓarnar da akai mishi a mota, saboda baisan ma ta ɗauka ba. Ta kuma san halin shi kamar yunwar cikin ta, zuciyarta ke dukan uku-uku lokacin da tayi parking cikin harabar gidan, da sauri ta fito daga motar tana rufewa, takawa ta yi zuwa cikin gidan. Nenne maman su Saifuddeen ta samu a falon a zaune tana kallon wani film ɗin Hausa da bata san ko wanne ba ne, ta dai gane Adam A. zango a ciki. 

“Usai e fuffto ki Nenne (Sannu da hutawa Nenne)” 

“Huda a wurtina name? (Huda, kin fita ne daman?)” 

Kai Huda ta ɗaga ma Nenne. 

“Miwaɗi hunde be jangirde…to mo yin be wuru do? (Nayi abu a makaranta ne….duk ina ‘yan gidan?) 

Murmushi Nenne ta yi. 

“Ba gani kin ganni ba.”

Nenne ta faɗi da harshen Hausa, duk da hausar tata ba fita take ba, kasancewar ta fulanin asali na garin Gombe, idan akwai abinda Huda take godewa bai wuce yaren babanta da take ji ba sosai, mahaifiyarta fulanin yola ce, amman ko zo in kasheka bata ji, Nenne tai tsaye wajen ganin suma suna jin fulatanci kamar sauran yaranta. Sun fi yin yaren a gida fiye da yadda suke Hausa, hakan yasa har mahaifiyar su Huda ɗin da suke kira da Yafindo tana ji yanzun, amma ba komai take iya mayarwa ba in hirar ta yi tsayi. 

“Hamma mi ɗon tefa Nenne (Su Hamma nake nufi Nenne)” 

Cewar Huda tana ƙarasawa cikin falon sosai, mayafinta ta cire ta ajiye kan kujera. 

“Ni ba mutanen gida bace ko?”

Dariya Huda ta yi ta wuce tana ɗaukar robar ruwan da ke gaban Nenne. 

“Kin gama da shi?”

Ta buƙata, kai Nenne ta ɗaga mata, kwancewa ta yi tana sha daga bakin robar, saboda ba wani mai yawa bane ya rage. Da robar a hannunta ta wuce ɓangaren su don ta duba Yafindo, sai lokacin Rafiq ya faɗo mata a rai, ranar farko da ta ganshi a KFC ba ƙaramar bugawa zuciyarta ta yi ba, banda ‘yan uwanta bata taɓa jin kusanci da wani irin yadda ta ji kusanci da shi ba, ta jima da ta dawo gida tana tunaninshi da inda ta taɓa ganin shi, ta kasa tunawa, amma tana da tabbacin ko ma a ina ne ta taɓa ganin shi. Haka kuma sa’ adda ta sake ganin shi na biyu, ta ji ta sanshi, shima kuma yasan ta tunda har ya tambaye ta ko ya santa a wani wajen. 

Ta kwana biyu da shi a rai, ta gaji da tunani ta haƙura, sai yau da ta sake ɗora idanuwanta akan shi, ta tambayi sunan shi ne ko in ta sani zai sa ta tuna inda ta sanshi, amma babu abinda sunan ya jefata ciki sai wani ruɗanin, don ta sha jin Mustafa Shettima, haka kuma take tunanin ta sha jin Rafiq Mustafa Shettima, kamar ‘yan siyasa ne ko ‘yan kasuwa, ta kasa tunawa, amma sanannu ne a garin Abuja, ta yi zurfi cikin tunani ta ci karo da Yafindo da ta fito daga ɗaki. 

“Ina hankalin ki yake?”

Yafindo ta tambaya tana riƙe Huda da ke shirin faɗuwa, kallon ta Huda take kamar ranar ta fara ganinta, har hakan na sa Yafindo faɗin, 

“Lafiya dai ko?”

Sai yanzun Huda ta ga dalilin da yasa take tunanin tasan Rafiq, kama yake mata da Yafindo, kama sosai da ko su da Yafindo ta haifa ba su yi kama da ita haka ba, sannan muryarshi iri ɗaya da ta Hamma Zaid, har buɗewarta, ko yadda ya lumshe idanuwanshi da ya kalli ƙanwarshi haka Yafindo takan yi duk idan ranta yana shirin ɓaci. 

“Innalillahi wallahi kamarku ɗaya Yafindo…”

Huda ta faɗi tana yin dariyar jin daɗin ta warware ruɗaninta akan Rafiq. Cikin rashin fahimta Yafindo ta turata. 

“Shirmen naki ne ko? Waye kuma kamar mu ɗaya.” 

Riƙo mata hannu Huda ta yi.

“Wallahi wani ne Yafindo, ina kwanaki da mukaje KFC?” 

“Ranar da kika uzzuramin muka tsaya KFC kike nufi?” 

Yafindo tai maganar tana hararar Huda da ke dariya. 

“Ranar na fara ganin shi to, kina fita na juyo na ganshi…” 

Wata irin dokawa zuciyar Yafindo ta yi, don bata manta da ranar ba saboda dalilai da yawa, da duk kalmar da zata fito daga bakin Huda da yadda bugun zuciyar Yafindo yake ƙaruwa. 

“Sai na sake ganin shi kuma, ina ta tunanin inda nasan shi wallahi, sai yau da ƙanwar shi ta buga min mota… Kamar ku ɗaya Yafindo, sai kin ganshi tukunna, har yanayin yanda kike yi da fuska… Muryarshi sak ta Hamma Zaid….Ya ban katinshi ma in kira in an duba motar in faɗa mai kuɗin gyaran…” 

Muryar Yafindo can ƙasan maƙoshi ta ce, 

“Huda ki barni nikam…”

Ta ƙarasa maganar tana juyawa zata koma ɗakinta, Huda na maƙale da ita har lokacin, don haka tare suke nufar ɗakin. 

“Rafiq sunan shi.”

Tsaye Yafindo ta yi cak, tana kai hannu ta dafe zuciyarta da take ji kamar zata fito saboda tsallen da ta yi, kula da zufar da ta fara tsattsafo mata a goshi Huda ta yi, da sauri ta sa hannu tana taɓa kuncinta  

“Yafindo me yake faruwa ne? Me ya sameki?”

Girgiza mata kai Yafindo ta yi. 

“Zan biya kuɗin gyaran motar”

Ta faɗi tana ture hannun Huda da ke taɓa mata fuska. 

“Yafindo… Ɓarna fa sukai min.”

“Na ce zan biyaki ni kuma…”

Yafindo ta faɗi muryarta a dake. 

“Ai ya ce in kira shi.”

Kai Yafindo ta girgiza ma Huda

“Indai na isa da ke karki kira zan biya, ki cillar da lambar kuma.” 

Tana ƙarasawa ta shige ɗakinta tana barin Huda a tsaye a bakin ƙofa da tunanin me ya faru yanzun nan, bata taɓa ganin Yafindo cikin yanayi haka ba, bata kuma taɓa mata magana da kalar muryar da tai mata ba yanzun. Jujjuya zancen Rafiq da tai mata take yi, tana tunanin ko ta faɗi wani abu da bai kamata ta faɗa ba amma ta rasa, ƙofar ta buɗe tana bin Yafindo cikin ɗakin. 

Abuja

A ɗakin Nuri tai wani irin bacci da ta kwana biyu bata yi irin shi ba, tana buɗe idanuwanta Nuri ta gani a zaune tana riƙe da hannunta. 

“Zafira… Kin tashi…”

“Nuri…”

Zafira ta kira muryarta a dakushe saboda kukan da ta yi. 

“Kina buƙatar wani abu ne? Ruwa? Kina jin yunwa?” 

Gyara kwanciyarta Zafira ta yi tukunna ta girgiza ma Nuri kai, bata buƙatar komai ita kam yanzun da ya wuce kulawar su, da gina mata katanga tsakaninta da Omeed, ta manta rabon da ta samu kanta cikin nutsuwa irin wannan, sai yanzun ta san bacci ma tana yin shi ne da fargabar tana buɗe ido zata ga Omeed, za tai abinda zai jibgeta kamar an aiko shi, tunanin shi kawai na sata ƙara matsawa jikin Nuri a tsorace. Hakan Nuri ta kula da shi yasa ta sake dumtse hannun Zafirar cikin nata, tana jin ciwon yadda bata zame mata mahaifiyar da take buƙata ba lokacin da ya kamata. 

“Nuri…”

Zafira ta kira

“Ina nan Zafira… Ba inda za ni.”

“Don Allah karki bari Daddy ya ce in koma ko Omeed ya zo… Nuri dukana yake wallahi, don Allah ku yi haƙuri karku mayar dani, dukana zai yi saboda na kira Yaya Rafiq…” 

Zafira ta ƙarasa muryarta a karye, tana jin zuciyarta cike da tsoro, gam ta runtsa idanuwanta, Allah kaɗai yasan abinda Omeed zai mata in suka bari ta koma gidan shi, ya sha faɗa mata gawarta za’a ɗauka daga gidanshi, hakan ne kawai hanyar da zata iya rabuwa da shi, ta kuma yarda, sai yanzun da ta ganta a gidansu, tana kuma tsoron Daddy ya ce sai ta koma. 

“Kashe ni zai yi… Zai kashe ni idan kuka mayar dani.” 

Zafira ta faɗi hawaye masu ɗumi na zubo mata, riƙe ta kawai Nuri ta yi tana kasa magana saboda wani abu da yai mata tsaye a maƙoshi ya ƙi wucewa, in ranta yai dubu ya gama ɓaci, rabonta da ɓacin rai irin wanda take ciki yau an kai shekara talatin da wani abu, tun dangin Alhaji Mustafa na mata gori kan rashin haihuwa, sai yau da Omeed yake tunanin sun bashi Zafira ne don ya jibga kamar ganga. Ta san Daddy ba zai taɓa haƙura ba ballantana har ya ce Zafira ta koma gidan Omeed ɗin. 

Saboda lokacin yana shari’a, duk idan an samu matsala na fyaɗe da maza masu dukan matansu ko su hana su abinci ko ba ka da kuɗin biyan shi Daddy zai tsaya sai an ƙwatar maka haƙƙinka, ballantana kuma ‘yar shi, suna ganin Daddy na takura su ta sani, amma soyayyar su a wajen shi mai girma ce, yana nuna musu ne ta hanyar da ya iya kawai. Sosai Nuri take riƙe da Zafira, kukan da take na ci mata zuciya. Tana kuma jin yadda take jiran Omeed ya tako ƙafafuwanshi cikin gidan. 

Ƙwanƙwasa ƙofa ta ji. 

“Shigo…”

Ta faɗi a taƙaice, ta ma ɗauka Fawzan ne sai ta ga Aroob ce ta turo ƙofar tare da yin sallamar da Nuri ta amsa muryarta can ƙasa. 

“Zaf kinsan me?”

Aroob ta faɗi tana dariya tare da ƙarasawa gefen gadon ta zauna kamar bata ga tana goge hawaye sa’adda ta shigo ba, tana buƙatar lokaci kafin ta raba damuwarta da Aroob ɗin, ta fahimta, zata kuma bata lokacin duk da take buƙata har sai ta shirya. 

“Me ya faru?”

Zafira tai maganar tana zame jikinta daga na Nuri zuwa kan pillow din 

“Wallahi mota na fita da, na je na goge ma wata yarinya tata motar.” 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Aroob yaushe kika fita daga gidan da mota ban sani ba?” 

Nuri ta tambaya tana girgiza kai, dariya Aroob ta sake yi. 

“Nuri mana, ba abinda ya faru, ba gani na dawo ba?” 

Harararta Nuri ta yi, amma Aroob ce, dariya kawai ta yi tana maida hankalinta kan Zafira. 

“Ina ta kiran Yaya Fawzan bai shiga ba, na mishi text don ya zo wajen, sai na sake kira, yana shiga na ce yai sauri yazo bana son in kira Yaya Rafiq, zai kashe ni in yasan na fita da mota…” 

Jinjina mata kai Zafira ta yi. 

“Yaya zai kashe ki ko yanzun idan ya sani.”

Kai Aroob take ɗaga mata tana ci gaba da dariya. 

“Yaya Rafiq na kira…maimakon Yaya Fawzan…” 

Ware idanuwa Zafira ta yi kafin wata dariya da ta kwana biyu bata yi ba ta kubce mata, don zata so ganin fuskar Aroob ɗin lokacin da tasan Rafiq ta kira ba Fawzan ba. 

“Kayya, wallahi sai yanzun abin yake ban dariya, amma ɗazun hankalina ya tashi, da yazo bai min faɗa ba ma… Wai kanshi na ciwo in zo gida kawai.” 

Har Nuri murmushi take ganin yanda suke dariya, kafin Aroob ta ɗan daƙuna fuska. 

“Kin san me?”

Kai Zafira ta girgiza mata. 

“Wallahi yarinyar ko? Kama suke da Yaya Rafiq, ko mu ba mu yi kama da shi ba, dama kin san hasken shi dai na Nuri ne, to wannan wallahi kamar su har ta yi yawa, yadda kika san ƙanwar shi….” 

Aroob take faɗi tana kallon Nuri da faɗin, 

“Ina jin fa ita ma taga suna kama ne, sai kallon shi take yi.” 

“Dama an ce kowa akwai mai kama da shi a duniya… Nima na taɓa ganin wani mai kama da Abbana sosai, lokacin mun je Umra da Daddynku…” 

Nuri ta ce, kan gadon Aroob ta hau gaba ɗaya suna ci gaba da hirar su, duk so suke su ga Zafira ta ɗan warware ko yaya ne, bata kuma basu wahala ba, don dariya take daga zuciyarta, har cikin idanuwanta za ka iya ganin hakan. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 33Alkalamin Kaddara 35  >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 34 ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×