Skip to content
Part 15 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Yana zuwa gida ya ɗauko ɗaya wayarshi da ya kashe yana kunnawa, sabuwar ya kashe ya ajiye sai kuma ranar da amfaninta ya tashi. Yana buɗewa saƙonnin Samira ne suka fara shigowa sun fi talatin, sannan wasu saƙonnin daban, bai buɗe ko ɗaya ba. Lambar Daddy ya kira, bugun farko ya ɗaga da faɗin, 

“Ka gama fushin kenan…”

Dariya Rafiq ya yi, yana ganin yarinta cikin abinda ya yi, akan Daddy zuciyarshi ta riga ta gama bushewa kuma, sai yanzun da ya kira shi yaga da wahala in akwai wani abu da zai ƙara yi wanda zai bashi mamaki. 

“Daddy…”

Ya faɗi cikin sigar gaisuwa. Yana ɗorawa da, 

“Ya aiki?”

“Alhamdulillah. Ina son ka je Kaduna, za ku gana da El-Labeeb Ibrahim Maska…” 

Dan daƙuna fuska Rafiq ya yi 

“Waye shi?”

“Dan wasan Hausa ne da Kaduna suke ji da shi, muna buƙatar shi kafin abokan hamayya su riga mu.” 

Girgiza kai Rafiq ya yi. 

“Shi ya kamata ya same mu ai Daddy, su ne fa suke neman kuɗin, mu kuma za mu je har inda yake?” 

‘Yar dariya Daddy ya yi da ke fassara har lokacin da sauran Rafiq a fahimtar yadda siyasa take. 

“Nayi bincike akan shi Rafiq, ka je ɗin kamar yadda na ce…” 

Jinjina kai Rafiq ya yi cikin amincewa da abin da Daddy ya faɗa, don gardama da shi bata da riba, ko me zai faɗa sai ya gama kuma ya je Kadunan. 

“Daddy daman ina son in maka magana ne kan Samee…” 

Cewar Rafiq ɗin yana canza akalar hirar gaba ɗaya. 

“Ina ji.”

Shiru Rafiq ya yi a karo na farko yana jin nauyin magana tsakanin shi da Daddy. Bai san ta inda zai fara ce mishi yana son a je mishi neman auren Samira ba, a wani ɓangaren yana ƙara jinjina wa ƙarfin halinta, ta waya kenan ma ya kasa faɗa wa Daddy wannan maganar, ya yarda girman soyayya daban ne, zata iya baka ƙarfin gwiwar da baka taɓa tunani ba. 

“Rafiq?”

Daddy ya faɗi daga dayan ɓangaren yana tunanin ko network ne ya samu matsala. 

“Zan maka text kawai…”

“Mene ne akan Samira da ba zaka iya faɗa min ba?” 

Shafa sumar kanshi yayi kamar Daddy na ganin shi. 

“Daddy mana, zan maka text yanzun fa.”

Ɗan jim Daddy ya yi kamun ya ce 

“Okay.”

“Allah ya taimaka ya tsare.”

Sai da Daddy ya amsa da Amin tukunna ya kashe wayar yana danna inda zai bashi damar yin saƙo, ya rubuta ya fi kala goma sai ya goge, har yaba kanshi dariya, don ko a text maganar tana mishi nauyi sosai. Kamun da ƙyar ya iya tura, 

‘Dama zan ce a nema min auren Samee ne.’

Yana kallon saƙon ya tafi, yana jin kamar ya bishi ya kamoshi, wata irin kunya ya ji ta kamashi, yana ganin kiran Daddy ya shigo ya miƙe tsaye, ya ajiye wayar akan kujera yana rasa inda ya kamata ya shiga. Banda 

“Innalillahi…Ya Rabb…”

Babu abinda yake iya furtawa, kunya yake ji da bai taɓa sanin irin ta ba a rayuwarshi. Yana kallo har wayar ta yanke, ya ma kasa zama, daga inda yake tsaye yake kallo, sabon kira ya sake shigowa, hannuwanshi yasa yana goge fuskarshi da yake jin kamar zufa ta taru, baya shiri da sanyi, a gida ko office baya son AC kwata-kwata baya kunnawa, fanka yake bari a ƙaramin lamba. 

Wayar ya ɗauka yana zama, da ƙyar ya iya ɗagawa ya kai ta kunnen shi. 

“Da gaske ne abinda ka turo min?”

Daddy ya faɗa muryarshi cike da annashuwa. 

“Na wa Nurin ka maganar nan, ta ce ba soyayya kuke da Samira ba.” 

Da sauri Rafiq ya ce 

“Eh ba soyayya muke ba…”

Kalaman na mishi wani iri bayan ya furta su, don bai san sa’adda suka fito ba. Dariya Daddy ya yi. 

“Kar mu je kenan.”

Girgiza kan shi ya yi. 

“A’a kuje…”

Ya furta muryarshi can ƙasa, yana jin fuskarshi ta ɗauki ɗumi saboda kunya. 

“Na ji daɗi wallahi Rafiq, ina alfahari da zaɓinka.” 

Jinjina kai kawai ya yi yana sauke wayar daga kunnen shi, wani irin abu mai wahalar fassaruwa na zama daram a zuciyarshi, kalmar yabo ko ya ta fito akan shi daga wajen Daddy yana jinta kusa da zuciyar shi, kawai nishaɗi yake ji da ya jima bai ji kalar shi ba. Kwanciya ya yi kan kujerar yana lumshe idanuwan shi, yanayin yake so ya haddace ya adana shi don kowanne lokaci zai iya buƙatar shi. Ɗakin ya ji ana dokawa bana hankali ba, kamar da hannuwa bibbiyu ake dukan ƙofar. Miƙewa zaune ya yi yana murza gefen kanshi da yake jin kamar zai yi ciwo, yasan su Fawzan ne, saboda auren abu ne da Daddy yake so har ya kirasu ya faɗa musu. Yaso ya faɗa musu da kanshi ne ya bari sai zuwa anjima in ya samu hutu tukunna. Shi kanshi maganar bata gama nutsa mishi ba har lokacin. 

“Yayaaaaaa, mun san kana ciki fa.”

Ya ji muryar Aroob, Fawzan na ɗorawa da, 

“Tarbiyar mu ce kawai abinda yake tsakanin mu da ɗakin nan ba wannan ƙofar ba tunda a buɗe take, wallahi ka ce mu shigo.” 

Girgiza kai yake yi, yana jin kamar ya yi shiru ya ƙyale su, sai dai hutun da yake son samu ɗin ne ba za su bari ba, duk da ba mukulli a jikin ɗakin ba za su taba shigowa baice su shigo ba. 

“Zamu buɗe ƙofar mu tsaya a inda muke…”

Aroob tace tana ƙarasa maganar da alamun dariya. 

“Sai mun shigo ne babu izini za mu karya wata doka. Yaya kana jinmu fa.” 

Murmushin da ke fuskarshi bai hana shi yin shiru ya ƙyale su ba, bai da wani zaɓi a takurar da yasan za su yi mishi, amma yana da zaɓin lokacin da zai barsu su shigo ɗin, ba zai kashe su ba in suka ƙara jira har ya gama shan ƙamshin shi. Wayar shi ce ta hau ruri, yana dubawa ya ga Naadir ne. Ɗagawa ya yi,

“Naadir…”

“Ka barsu su shigo Yayaa, sun ce akwai hot gist.” 

Runtsa idanuwa Rafiq ya yi yana buɗe su da jin a duniya ƙannenshi sun fi na ko’ina ban mamaki. Hararar ƙofar ya yi tare da faɗin, 

“Ku shi…”

Basu ma bari ya ƙarasa ba suka bankaɗo ƙofar suna shigowa, da gudu Aroob ta ƙarasa tana ruƙunƙume shi, hannuwanta da ta zagaya ta maƙale mishi wuya yake ƙoƙarin ɓanɓarewa, don ya ji numfashin shi baya fita sosai, muryarshi can ƙasa saboda shaƙarar da ya sha ya ce,

“Aroob za ki kasheni…”

Da sauri ta sake shi tana fadin

“Yi haƙuri, wallahi kawai daɗi nake ji ne shi yasa…” 

Ta ƙarasa tana ƙwace wayar da ke maƙale da kunnen shi har lokacin, bai ce mata komai ba, don hakan ya bashi damar murza wuyanshi da yake zaton jini ya taru saboda matsar da ya sha, hararar Fawzan da ke zaune yana dariya yayi. Aroob kuwa wayar tasa a kunnenta tana faɗin 

“Hello Naadir.”

“Aroob Love…”

Naadir ya faɗi daga ɗayan ɓangaren, a speaker ta sa wayar tukunna ta ce mishi, 

“Yaya aure zai yi…Samee zai aura.”

“You better not be kidding me Aroob (Karki fara ce min da wasa kike yi Aroob)” 

Dariya ta yi tana faɗin, 

“Wallahi da gaske nake, Daddy ne ya faɗa mana ma gobe zai dawo a je fixing rana.” 

“Oh my God! Holy freaking feels Yayaa…”

Naadir yake faɗa daga ɗayan ɓangaren, muryarshi cike da mamaki da jin daɗi yana ɗorawa da, 

“Hug him for me (ki rungume mun shi)…”

Wayar na hannunta ta juya, Rafiq da ake komai kan kunnen shi har ya miƙe tsaye yana ɗaga hannuwanshi duka biyun cikin alamun yin tsakani da Aroob ɗin 

“Kika matso sai na kwaɗa miki mari…”

Dariya Aroob take yi. 

“Come on Yaya…”

Cewar Naadir. 

Daga inda Rafiq yake ya ziro hannu yana fisge wayarshi daga cikin hannunta. 

“Naadir…”

Ya faɗi cike da kashedi. Dariya Naadir ɗin yake yi shi ma. 

“Yaya it’s just a hug…”

“Kana so ta kashe ni ne ba.”

Rafiq ya ce yana sake murza wuyanshi inda yake jin hannuwan Aroob ɗin har lokacin, da turanci Naadir ya soma magana, Rafiq ya katse shi da, 

“Hausa Naadir, Hausa…”

Don bayason hausar ta ɓace mishi, duk da bashi bane yaren su, Kanuri ne, cikin su shi kaɗai ne yake iya yin yaren sosai, duk suna ji, amma saboda ba yi suke ba ba komai suke iya mayarwa ba, Naadir kam wanda yake fahimta kaɗanne, shi yasa Rafiq baya so Hausar ma ya saki. 

“Sorry, Yayaa… Yayaa.”

“Ina nan fa, ina kuma jinka…”

Ya faɗi don yadda Naadir ɗin ke kiranshi cikin son ya bashi hankalin shi gaba ɗaya ne. 

“Wata biyu za’a saka, ni zan kira Daddy wata biyu za’a saka saboda lokacin ne zan zo.” 

Ware idanuwa Rafiq ya yi yana girgiza wa Naadir kan da ba gani yake ba, wata biyu ya yi kaɗan, baisan me yasa ba, amma tunanin aure cikin wata biyu na saka wata irin zufa tsattsafo mishi. 

“Nope and Nope, wata biyu yayi kaɗan…”

Kamar Naadir zai yi kuka ya ce, 

“Ina rasa abubuwa da yawa na rayuwar ku, karka bari in rasa wannan Yaya… Don Allah…” 

Su Aroob yake kallo da roƙon su, girgiza mishi kai sukai su duka biyun, ba zai samu goyon bayansu kan maganar ba, don suna son Naadir ya samu bikin, ƙyale su ya yi yana faɗin, 

“Koma yaushe ne ai Weekend ne za’a saka, zaka iya zuwa friday ka koma ranar Sunday…” 

“Akwai training ranakun Yaya…”

Naadir yace muryarshi can ƙasa 

“Bazai canza komai ba dan baka je na kwanakin ba.” 

Cewar Rafiq.

“Zai hanani damar buga wasa tsakanin mu da Red Woods, wasan zai iya canza min komai, yin bikin ka nan da wata biyu bazai canza komai ba. Yaya don Allah ka ji…” 

Numfashi ya sauke. 

“Yaya don Allah fa…”

Aroob ta faɗi tana taya Naadir roƙon Rafiq ɗin da ke tsaye babu abinda zuciyarshi take yi banda dokawa kamar zata fito, aure ba abu bane ƙarami ya sani, tunanin ɗaukar nauyin amanar yarinyar mutane nan da wata biyu kawai na tsorata shi. Naadir ne ya katse su da faɗin, 

“I have to do something yanzun nan… Zan sake kiran ku, Yayaa don Allah fa ka yi considering. Aroob, Yaya Fawzan, love you guys.” 

Naadir ya ƙarasa yana kashe wayar daga ɓangaren shi, hakan yasa Rafiq komawa inda ya tashi ya zauna. Aroob ma ta yi, su duka suna zuba mishi idanuwa, kallon su yake yi, kamar yadda Naadir ya faɗa ne , ba zai canja komai ba don ya yi aure nan da wata biyu ko ƙasa da haka, ko fiye da hakan ma, nauyin auren ba zai canja ba. Wayar shi yake daddanawa, yana jin idanuwan shi akan su har lokacin. Text ya tura wa Daddy,

‘In ba damuwa a saka wata biyu Daddy, saboda Naadir ya samu ya zo.’ 

Saƙon na shiga, yana samun amsa, 

‘Karka dame ni Rafiq’

Dariya Rafiq yayi yana kallon su tare da ɗan ɗaga musu kai, su duka suka taso lokaci ɗaya suna ruƙunƙume shi. 

“Mun gode…”

Suke faɗi lokaci ɗaya, hannu yasa yana tutturesu. 

“Karku daƙuna min kaya don Allah…”

Sakin shi suka yi, Aroob zata yi magana suka ji an ƙwanƙwasa ƙofar. Fawzan ne ya ce a shigo, Nuri ce kuwa, da murmushin farin ciki a fuskarta, idanuwanta akan Rafiq, wani irin farin ciki take ji, kallon shi take, yau girmane yake shirin samun shi, ɗanta ne zai yi aure. 

“Rafiq…”

Ta kira muryarta cike da yanayoyi kala-kala. 

“Nuri…”

Ya amsa, farin cikin da ke fuskarta da muryarta na saka zuciyarshi yin wani tsalle-tsallen murna, tare da farin cikinta tsoron shi gaba ɗaya yana dishewa. 

“Yanzun Daddynka yake faɗa min. “

“Daddyn mu dai Nuri.”

Cewar Fawzan, ba tare da Rafiq ya kalle shi ba ya ce, 

“Don Allah kai mana shiru.”

Aroob kam ta san Rafiq ya gama samun lokacin su tunda Nuri ta shigo, don haka ta tashi daga kusa da Rafiq din tana komawa kujera mai mazaunin mutum ɗaya. Inda ta tashi Nuri ta ƙaraso ta zauna tana kallon Rafiq ɗin, girmanshi da komai na bata mamaki, yadda lokaci yake tafiya na saka tsikar jikinta tashi. 

“Da gaske aure za ka yi?”

Kai yake ɗaga mata, yana kasa magana saboda wani irin yanayi da ya tsaya mishi a wuya. 

“Oh Allah Rafiq… Aure za ka yi”

Ta sake maimaitawa, auren shi na sa zuciyarta matsewa fiye dana Zafira, bata san ko don ta jima da sanin su ba ne ko lokaci ne da su a tare da ita, auren su kuma ya fi nashi kusa, har Aroob ma na iya aure ta barshi tunda namiji ne. Murmushi kawai take yi , Rafiq kam fuskarshi zuwa lokacin ta fara ɗaukar ɗumi da yadda kunyar Nuri da ƙaunarta suka haɗe mishi. 

“Innalillahi… Kunya yake ji wallahi.”

Cewar Aroob da ke kallon fuskar Rafiq ɗin da ta yi ja tana kwashewa da dariya, Fawzan ma taya ta yake yi, don ko mace ba zata nuna wa Rafiq ɗin kunya ba, sosai kunyarshi ta fi murmushin shi zama kusa. 

“Yaya Nurin kake jin kunya?”

Cewar Fawzan, pillow ɗin kujera Nuri ta ɗauka tana jifan Fawzan, ta sake ɗaukar wani ta jefa wa Aroob. 

“Ku fita ku ƙyale min yaro… Kunya ai abune mai kyau…” 

Shi kam maganganun su babu abinda suka ƙara mishi sai kunyar Nurin, dariya suka tsaya suna yi. Sai da suka ga Nuri ta miƙe tsaye tukunna da gudu suka fice daga ɗakin. Kallon su kawai Rafiq yake yi yana jin yadda zuciyarshi take ƙara kumbura da ƙaunarsu. Duniyarshi bata da girma, amma cike take da ƙauna mai girman gaske.

***** 

Bai taɓa sanin lokaci yana gudu ba sai yanzun da aka saka mishi rana, bai kuma taɓa sanin haka aure yake da hidima ba sai yanzun, wai don ma su Muneeb ke ta hidimomin duk da ya kamata. Gashi kuma zaɓen su Daddy saura watanni huɗu, hakan ya ƙara sa komai jagule mishi waje ɗaya. Samira kanta sai da ta ce mishi dama haka auren yake da hidima da yawa. 

Jikin shi kamar wanda mota ta taka haka yake ji lokacin da ya shigo gida, satin su ɗaya suna yawo cikin garuruwan arewacin Nigeria, can ma ya baro Daddy saboda in bai dawo gida ba komai zai iya faruwa, ya gaji da hayaniyar, ya gaji da kalar rayuwar gaba ɗaya. Tun a hanya yake wa kanshi alƙawurra cewar ko kusa da siyasa ba zai taɓa zuwa ba. 

Yana ganin ƙoƙarin Daddy ba kaɗan ba, kanshi tsaf zai tarwatse da hayaniyar da ke cikin siyasa in ya ce yinta zai yi. Rayuwar hayaniya ba tashi bace ba, da ɗaukar nauyin mutane, tunani ma ba zai barshi samun wadataccen bacci ba. Addu’a yake kar wanda ya samu a falo, don ko sallama bai iya yi ba, ɗakin shi ya wuce kai tsaye yana murza handle ɗin, don yakan yi watanni bai sa mukulli ya kulle ba. Wani irin numfashi ya sauke da shirun da ya ziyarce shi, bai kula kofar a buɗe ya barta ba ma, hannunshi ya kai yana kunna ƙwan ɗakin saboda yammaci da ya yi liƙis. 

Takalman ƙafarshi ya zame yana ƙarasa shiga cikin ɗakin sosai, ƙafafuwan shi na haɗuwa da kafet din ya ji ba zai iya ƙarasawa ciki ba sosai, zama ya yi yana jan jikinshi kusa da kujera. Kanshi ya ɗora a sama a zaunen, wani iri yake jinshi. Ba zai tuna ranar ƙarshe da yai wani ciwo banda na kai ba, wannan ma ya riga da ya saba. Don ko hayaniya tai mishi yawa ko damuwa sai ciwon kai. 

Yau banda ciwon kan bai gane ma jikinshi ba, sanyi ma yake ji sosai, idanuwan shi ya rufe, yana jin kamar hucin zafi har cikin su duk da sanyin da yake ji. A cikin zuciyarshi ya gwada tashi tsaye ya ƙarasa kan gadon don ya lulluɓa, hakan kawai na sa shi jin amai zai yi kowanne lokaci. Ya fi kwana huɗubai ganema jikin shi ba, abincima in ya sa a baki da ruwa yake bi yana haɗiyewa, jiya ma da ya ci amai ya yi ta kwarawa. 

Numfashin shi ya ji yana fita wani iri, duhu-duhu ke fizgarshi bana alamun bacci ba, na wani yanayi da bai taɓa sani ba. So yake ya fito da wayarshi dake aljihunshi ya kira Nuri amma ya kasa motsawa. Shiru ya yi kawai yana barin ikon komai a hannun Allah. 

*****

Fawzan ne ya shigo gidan, shi ma ya kwaso tashi gajiyar ta daban, saboda yau asibitin a cike yake. Mutane basu da lafiya, ƙarfe biyu ya kamata ace ya tashi. Amma zuciyarshi sam ta kasa bari ya taho gida, tunda akwai mutane da dama da ke buƙatar agajin gaggawa, dole ya tsaya ya taimaka. Ɗakin shi ya zo shiga ya hango hasken ɗakin Rafiq har waje kasancewar ƙofar da take a buɗe. 

Jiya sun yi waya bai ce mishi zai dawo ba kuma, ɗan daƙuna fuska ya yi cike da mamaki, kafin ya ɗan ɗaga kafaɗunshi, in dai Rafiq ne ƙila kewar Nuri ce zata dame shi ya ce sai ya zo gida. Mukullin shi ya lalubo ya buɗe ɗakin shi ya shiga, agogon shi ya fara kwancewa ya ajiye tare da mukullin, kafin farar rigar da ke saman kayanshi, tare da ID card ɗin da ke wuyanshi. 

Banɗaki ya wuce ya watsa ruwa, tukunna ya fito ya samu riga da wando ya saka wa jikinshi. Fitowa ya yi da nufin sauka ƙasa ya samo abinda zai ci ya sake ganin ƙofar Rafiq a buɗe take har lokacin, sai abin ya yi mishi wani iri, don in ba sauri Rafiq yake ba, zai shiga ya ɗauki wani abu ya sake fita baya barin ɗaki a buɗe haka. 

Kasa wucewa ya yi, sai ya samu kanshi da ƙarasawa ƙofar ɗakin Rafiq ɗin, daga nan inda yake tsaye ya hangoshi zaune ya ɗora kanshi cikin kujera, zuciyarshi ya ji ta yi tsalle har cikin maƙoshin shi, ko takalma bai cire ba ballantana ya yi tunanin sallama ya shiga cikin ɗakin yana tsugunna wa gaban Rafiq ɗin tare da sa hannu ya kamo damtsen hannunshi. 

Wani irin zafi ya ji duk da hannun rigar Rafiq ɗin dogo ne, ba sai an faɗa mishi ba yasan zazzaɓi ne mai zafin da zai iya zama haɗari a tare da shi in bai samu taimakon gaggawa ba. A rikice ya ɗago da Rafiq ɗin da ko idanuwanshi baya iya buɗewa yana faɗin, 

“Yaya…Yaya…”

Amma da alama bai ma san duniyar da yake ba. Ƙarfin zuciyar Fawzan a asibiti yasa ko masu haɗari aka kawo ake kiranshi, don babban likitan da suke ƙara koyan ƙwarewa a ƙarƙashin shi yana son Fawzan, yakan ce ma sauran dole sai sun raba zuciyar su da aikin su, ya zamana babu wani yanayi banda son ceton ran marar lafiyarsu, wani ruɗewa da tausayi ba shi marar lafiya yake buƙata ba. Fawzan na amfani da duk wannan, amma yanzun kam ya neme shi ya rasa, banda tsoro da tashin hankali babu komai a tare da shi, gaba ɗaya ya rikice, gyara Rafiq ɗin ya yi yana kwantar da shi sosai kan kafet ɗin, hakan bai sa komai ba sai rawar sanyi da ya fara, ko’ina na jikin shi na kyarma cikin yanayin da ya goge wa Fawzan duk wani karatu da ya taɓa yi a fannin lafiya. Ɗago Rafiq yake yi yana rasa abinda ya kamata ya yi mishi, banda, 

“Yaya…Yaya mana…”

Babu abinda yake kira, ganin da duk yadda ya tsaya kamar jikin Rafiq ɗin ƙara rikicewa yake yi yasa dabarar ya kira Nuri a waya faɗo mishi, sai dai wayarshi na ɗaki, ba zai kuma iya matsawa nan da can ba ya bar Rafiq a halin da yake ciki. Aljihun Rafiq ɗin ya laluba yana samo ƙaramar wayarshi, lambar Nurin ma ita ce kiran ƙarshe da ya yi don haka ya sake dialing. 

Bugun farko ta ɗaga. 

“Rafiq…”

“Nuri bashi da lafiya, bansan me ya same shi ba, na kasa tashin shi wallahi, ki zo yanzun…” 

Fawzan ya ƙarasa yana mayar da numfashi saboda tashin hankali. Yana jin muryar Nuri tana faɗin, 

“Ina tahowa yanzun nan, karka kashe wayar Fawzan, ka kuma kwantar da hankalin ka, rashin lafiya ne, kowa ma yanayi, kaima kanayi, karka ɗaga hankalin ka, ka dinga numfashi kana jina?” 

Kai kawai yake ɗaga mata, tabbacinta na sa numfashin shi fara dai-daita. Jin da ya yi muryarta na fitowa fiye da ta cikin wayar ya sashi sauketa daga kunnenshi yana juyawa, tana tsaye, idanuwanta kafe kan Rafiq ɗin ta kasa ƙarasowa, tashin hankali kwance a fuskarta. Sai lokacin ta sauke wayar daga kunnenta, katse kiran Fawzan ɗin ta yi, tana lalubo lambar Dr. Abdulƙadir tana kira, don shi yake zuwa gida ya duba su, sai in buƙatar zuwa asibitin ta kama, shi ma yawanci Fawzan ne. 

Faɗa mishi ta yi Rafiq ne babu lafiya, bata ma jira ta ji me zai ce ba ta kashe wayarta. Ƙafafunta sun mata nauyi da ƙyar take iya ɗaga su tana ƙarasawa cikin ɗakin, bata taɓa ganin Rafiq a yanayi irin na yau ba, tun yana yaro bata taɓa ganin shi haka ba, hankalinta ya gama tashi gaba ɗaya. Tsugunnawa ta yi tan kamoshi daga jikin Fawzan ta ɗora kanshi a saman cinyarta. 

Rafiq da bai san duniyar da yake ba, a zuciyarshi ya fara jin kusancin Nuri, kafin a hankali ya ji numfashin shi na kaiwa inda ya kamata, hannunta ya ji kan fuskarshi, kafin sama-sama ya ji muryarta tana faɗin, 

“Rafiq… Oh Allah, me ya sameka haka?”

Yanayin da ke muryarta ne baya so, don kamar kuka take yi, da ƙyar ya iya ɗago da hannunshi yana ɗorawa saman nata, don shima bai san meya same shi ba, kawai bai gane ma jikinshi ba ne, kanshi kamar ana wasan kalangu a ciki. 

“Yawwa… Rafiq… Kana jina?”

Nuri ke tambaya yanayin muryarta na canzawa, ba zai iya magana ba, don haka ya ɗan samu ya matse hannunta da ta saka cikin nashi. Fawzan ya ji yana faɗin, 

“Nuri wayarki na ringing…”

Ɗagawa ta yi ta ga Dr. Abdulƙadir. Bata ma ɗaga ba don ta san yana ƙasa. Fawzan ta sa ya je ya shigo da shi. Yake ce ma Fawzan, 

“Ashe ma kana gida.”

Kai kawai Fawzan ya ɗaga mishi, bai ce komai ba har suka shigo ɗakin, ‘yar jakar taimakon gaggawarshi ya ajiye a ƙasa yana zama tare da soma duba Rafiq ɗin, Fawzan tsaye ya yi yana kallon shi don har lokacin babu abinda ya dawo mishi. Allurai ya yi wa Rafiq ɗin sannan ya ce wa Fawzan su kamashi zuwa kan gadon, hakan kuwa akai. Lokacin ne ya ɗibi jinin shi da zai tafi da shi a yi test. 

Ruwa ya ɗaura mishi yana samun waje jikin bangon inda za ka iya sargafe kaya ya maƙala ruwan a jiki. Wani guda ɗaya ya ajiye, ya zaro takarda ya yi rubutu akai yana miƙa wa Fawzan ɗin, dubawa ya yi lokacin komai ya dawo mishi, yasan abinda ya kamata yayi wa Rafiq ɗin, Dr. Abdulƙadir ya kalla cike da alamar tambaya, ɗan murmushi yai mishi da faɗin, 

“Karka damu, ba ko yaushe zuciyarka ke jurewa ba in family ne, ya faru da ni akan daughter ɗina…” 

Ɗan jinjina mishi kai Fawzan ya yi, sai da ya yi ma Nuri sallama tukunna. Bin bayanshi Fawzan ya yi don ya siyo sauran alluran, ruwa da za’a ƙara sakama Rafiq ɗin sai kuma magungunan da za su ɗan taimaka mishi kafin a yi gwajin jinin a ga asalin me yake damun shi. Ƙwanƙwasa wa Aroob ɗaki ya yi bayan ya ɗauko mukullin motarshi da kuɗi. Sai da ta ce ya shiga tukunna ya buɗe daga inda yake ya ce, 

“Ke Yaya ne bashi da lafiya…”

Dirowa ta yi daga kan gado ta fito da sauri. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Yaushe? Yana ina? Me ya same shi?” 

Aroob ke tambaya muryarta na rawa, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin dokawa. 

“Bansan ko tun yaushe ba, zazzaɓi ne mai zafi dai, zai iya yiwuwa Typhoid ko malaria dai, yana ɗaki tare da Nuri. Ki zo mu je tare…” 

Kai Aroob take girgiza mishi tana wucewa zata yi hanyar ɓangaren su Rafiq ɗin. 

“Bacci yake ko kin je, an mishi allurai… Ki zo mu je don Allah…” 

Juyowa ta yi tana kallon Fawzan ɗin sosai, kamar tana son gane ko ƙarya yake mata, sai da ta yi kamar ba zata je ba tukunna ta ɗaga mishi kai, wando ne a jikinta na jeans sai rigarta da ta ɗan sakko, don Rafiq na faɗa sosai kan saka kayan mutunci, sannan kanta ɗaure da ɗankwali, Zafira zata iya fita da kalar shigar lafiya ƙalau, amma banda Aroob, ɗaki ta koma ta cire ɗankwalin kanta ta ɗauki dogon hijab har ƙasa, pink me wata irin kwalliya a jikin goshin da hannuwan. 

“Sai ka ce matar liman…”

Fawzan ya faɗi, bata jin biye mishi. Bata cikin yanayin, bata jin zai fahimci yadda take ji a cikin hijabinta da kuma manyan rigunanta duk in zata fita. Suna sata jin daraja da addini ya bata, tana jin ‘yancinta da musulunci ya ƙwatar mata, kuma ba zai tayata amsa tambayar fito da tsiraicinta ba, saboda haka ra’ayinshi kan shigarta bai dameta ba. 

***** 

Suna hanya aka kira Magrib, masallaci Fawzan ya samu ya tsayawa don ya yi sallah, Aroob ya bari a motar, ringing ta ji waya na yi, hakan yasa ta kai hannu ta ɗauka, ta ga wayar Rafiq ce ma. Samee ta gani a rubuce, tana zuwa ɗagawa kiran na yankewa, dialing ɗin lambar ta yi tana mayar da kiran, Samira ta ɗaga da faɗin, 

“Na ɗauka ma baka kusa…”

Hakan yasa Aroob faɗin, 

“Ba shi bane ba, ni ce…”

“Aroob?”

Samira ta ce muryarta cike da son jin tabbaci. 

“Eh, Yayan bashi da lafiya ne…”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Me ya same shi? Yana ina yanzun?” 

Samira take tambaya cike da tashin hankalin da ke saka Aroob ɗin ƙara jin wani iri. 

“Yana gida. Mun fito mun siyi magunguna ne ni da Yaa Fawzan… Mu biyo mu ɗauke ki ne?’ 

Da sauri ta ce, 

“Eh don Allah… Amma yanzun za ku zo ko?”

“Sallah Yaa Fawzan ya tsaya yi, da ya shigo zan faɗa mishi sai mu biyo.” 

Aroob ta faɗi, itama muryarta da damuwa a cikinta kamar ta Samira ɗin. Kafin ta bata amsa ma Fawzan ya buɗe motar ya shigo. 

“Gashi nan ma…”

Aroob ta ce tana miƙa mishi wayar, karɓa ya yi ya duba ya ga waye kafin ya kai kunnen shi. 

“Fawzan don Allah ku biyo ku ɗauke ni…”

Jinjina kai yake yi. 

“Ki shirya to, ba muyi nisa da wajen ku ba, yanzun zamu ƙaraso.” 

Sai da ta amsa da to, tukunna ya kashe yana miƙa wa Aroob wayar. Karɓa ta yi shi kuma ya kunna motar yana ja, miƙewa ya yi maimakon ya shiga U turn, suka nufi gidansu Samiran. A ƙofar gida suka sameta a tsaye tana kallon hanya. Su duka suna kallon yadda ta damu da Yayan nasu cikin yanayin rashin nutsuwar da ke tattare da ita. Baya ta buɗe ta shiga tana rufe ƙofar. 

“Na gode sosai…Na gode…”

Take faɗi har ranta tana jin daɗin yadda Aroob ɗin da kanta ta buƙaci su biyo su ɗauke ta. Su duka babu wanda ya ce mata komai, haka suka juya suke tafiyar shiru. Tana jin zuciyarta na ƙara gudu, kamar tana son tsere ma wanda Fawzan yake yi da motar don ta rigata zuwa ta ga yadda Rafiq ɗin yake. Gaba ɗaya ta rasa nutsuwa. Bata taɓa ganin gidan ya mata nisa ba sai yau, sa’adda suka ƙarasa har wani numfashi take saukewa. 

Su duka suka haura saman tare, suna nufar ɗakin Rafiq ɗin suna shiga tare da Sallama, Nuri ce zaune a gefenshi, shi kam bacci ma yake. Gaishe da ita Samira ta yi tana ɗorawa da, 

“Ya jikin nashi?”

“Alhamdulillah, yanzun Dr. Ya kira ma babu komai a jininshi, ya ce gajiya ce kawai da rashin hutu…” 

Numfashi da suke riƙe da shi suka sauke su duka ukkun, Aroob na ƙarasawa ta zagaya ɗayan gefen tana hawa kan gadon gaba ɗaya ta matsa can kusa da Rafiq ɗin ta zauna. 

“Baya son hutawa wallahi…”

Samira ta ce tana kallon shi, duk da baccin da yake tana ganin rama a idanuwanshi. 

“Hmm…”

Kawai Nuri ta iya faɗa don ta san gaskiya Samira ɗin ta faɗi, Fawzan ma zagayawa ya yi yana zama ta ɗayan gefen kusa da Aroob. Samira ce kawai a tsaye, ba don gidan baƙon ta ba ne ba, har kwana ta sha yi, tana zuwanshi ko Rafiq na nan ko baya nan, ɗakin shi tana shigowa, amma yanzun akwai nauyi a tsakaninta da Nuri da bata san lokacin da ya fara ba.

“Ki zo ki zauna mana…”

Cewar Nuri tana matsa mata, tunda gadon ƙato ne, a kunyace ta ƙarasa ta zauna. Su dukkansu suna zuba ma Rafiq din idanuwa da yake baccin shi hankali a kwance, ruwan da ya ƙare ne yasa Fawzan tasowa ya kashe, ya kwance ya ɗaura sabo, tukunna ya koma ya zauna. Miƙewa Nuri ta yi da faɗin, 

“Isha’i na gabatowa ko Magrib ban yi ba…”

Kai Aroob ta ɗan ɗaga mata, ita a dai-dai take shi yasa hankalinta yake kwance. Fita daga ɗakin Nuri ta yi tunda suna tare da shi zata samu nutsuwar yin Sallah, ana kiran isha’i Fawzan ya tashi ya tafi masallaci. Su dukkansu suna nan zaune har wajen tara na dare, kafin ƙarar shigowar text ya shigo wayar Samira. Dubawa ta yi Kabir ne don ta mishi text cewar ya zo ya ɗauketa tunda dare ya yi. 

Bason shiga mutane yake yi ba, yana son shigowa ya duba Rafiq ɗin amma dole sai dai ta fita su shigo tare. Nuri ta kalla. 

“Nuri, Kabir ne wai yana ƙasa, na ce ya zo ya mayar da ni gida ne yana son ya duba jikin Raafik…” 

“Da baki wahalar da shi ba Samira. Fawzan sai ya mayar da ke ai.” 

Dariyar ƙarfin hali ta yi kawai, Fawzan ɗin Nuri ta kalla tana sashi ya je ya taho da Kabir, gaisawa suka yi yana musu ya mai jiki tukunna shi da Samira suka yi musu sallama, duk da tana jin yadda ta bar zuciyarta tare da Rafiq ɗin, kunyar Nuri kawai ce ta sa ta tafiya gida, amma da babu inda zata je. Ta riga da ta san ba bacci zata iya yi ba, gobe kam tunda sassafe za su ganta. 

Cikin Fawzan ne ya yi wani irin kugi daya sa Aroob da Nuri kallon shi, 

“Yaushe rabon cikin ka da wani abu?”

Nuri ta buƙata. Ɗan yatsina fuska Fawzan ya yi yana faɗin, 

“Tun da safe, sauka ƙasa zan yi ɗazun in ci dana dawo, sai kuma na shigo ɗakin Yaya…” 

“Ka tashi ka je ka ci wani abu, Aroob kema haka…” 

Nuri ta yi maganar muryarta babu wajen gardama, don haka suka tashi su biyun. Tare suka shiga kitchen ɗin, Aroob ta yi wainar shinkafa tunda rana dama da ta ji tana marmari, abinda Fawzan ya zuba kenan shi don yana son waina. Aroob kuma ta ɗauki snacks tana haɗa tea, a kitchen ɗin suka zauna tunda akwai wajen cin abinci a ciki. Sai da ta kurɓi shayin ta tukunna ta ce, 

“Allah na ji tsoron daban taɓa ji ba yau.”

Abincin da ke bakin shi Fawzan ya haɗiye yana faɗin, 

“Don ma baki ganshi ba ɗazun, wallahi gaba ɗaya aikin likitancina ya ɓace ɓat…” 

Dariya Aroob take yi. 

“Ba za ki gane bane ba, abin bana dariya bane Aroob, da wani abu ya same shi bansan ya zan yi ba, like na kasa yin komai fa, rasa abinda zan mishi na yi…” 

Da murmushin ƙwarin gwiwa a fuskarta ta ce wa Fawzan ɗin, 

“Babu abinda ya same shi, ba laifinka bane ba, da Yayan nema sai ya fi ka ruɗewa, ba za ka so ka ga yasda ake faɗa da shi in muka kai ka asibiti ba…” 

Ware mata idanuwa Fawzan ya yi. 

“Wallahi fa, hmm, akwai sa’adda ya ɗauki kujera ƙiris ya kwaɗama wani Nurse daga yace me yasa ba’a kawo ka da wuri ba…wai ya tsaya surutu in ka mutu wallahi ba zai yarda ba…” 

Wannan karon Fawzan ɗin ne yake dariya, hirar Rafiq ɗin suka ci gaba dayi suna dariya, suna kuma jin yadda ƙaunar da yake musu ta ninka wadda su suke mishi, don a cikin ƙaunarshi ne suka koyi yadda zasuyi tasu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 14Alkalamin Kaddara 16 >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×