Skip to content
Part 29 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Inda suka sauka shi da Wadata gaban gidan daya sauke matarshi ne kaɗan. Sai da Altaaf ɗin ya watsa ruwa saboda zafin da yake ji tukunna suka fito wajen zaman makokin. Bawai yana son duk wani abu daya danganci mutuwa bane ba, da ba don Wadata bane babu abinda zai kawo shi. Gashi yarinyar nan ta manne mishi a zuciyarshi kamar ya ganta ne kawai don hakan ya faru. Don da kuyar ya iya mintina sha biyar a zaune kafin ya miƙe yana ce ma Wadata,

“Ina zuwa.”

Kai kawai Wadata ya ɗaga mishi don yasan hali. Babu nisa tsakaninsu da inda yaga mai awarar, don yana shan kwana ya soma takawa ya hangota. Yana jin yadda bugun zuciyarshi yake ƙaruwa kamar tana son ƙwacewa ta riga shi isa wajen yarinyar. Sauri ya ƙara yana son ya ga fuskarta a kurkusa sosai. Da mutane a wajen su kusan huɗu ‘yan siyan awara. 

Hankalinta na kan awararta, kallonta Altaaf yake yi komai na ƙara kwance mishi, ta fi kyau a kurkusa haka, har yadda take juya awarar ya zauna mishi. Tsugunnawa ya yi yana kafa mata mayatattun idanuwanshi. Tunda yake a duniya bai taɓa jin son taɓa wata mace kamar yarinyar nan ta gabanshi ba, hannuwanshi yake ji suna ƙaiƙayi da son yin hakan. 

“Ta nawa za’a baka?”

Ta faɗi, muryarta na dira kunnuwanshi tana sa tsikar jikinshi gaba ɗaya miƙewa, runtsa idanuwa ya yi gam yana buɗe su cikin nata da girmansu yake bashi mamaki, inda an ce mishi a ƙauye akwai me kyawunta ba zai taɓa yarda ba. 

“Nuwaira na riga shi fa, tun ɗazun na zo.”

Wani yaro ya faɗi, kallon yaron ta yi tana mishi murmushi. 

“Yi haƙuri ka ga shi babba ne.”

Ta faɗi tana mayar da hankalinta kan Altaaf da kallon shi kawai yasa ta tsarguwa, yanayin shi kawai ya nuna mata baƙo ne a ƙauyen nasu, bata san me yasa ba, amma zuciyarta bata aminta da shi ba, kalarshi batai ruwan mutanen kirki ba, ba shigarshi bace don ba ranar bane farkon da ta ga mai kalarta ya shigo ƙauyen, shi ɗin ne da kanshi, gara ta sallameshi ya bar wajen. 

“Kaji? Ta nawa zan baka?”

Ta sake maimaitawa tukunna Altaaf ɗin yasan da shi take yi saboda nutsuwarshi na tare da yadda take juya laɓñanta lokacin da take magana. Muryarshi a dakushe ya ce, 

“Nawa ne gaba ɗaya?”

Ware mishi manyan idanuwanta ta yi cike da mamaki da alamun rashin fahimta. 

“Duka awarar nawa ne? Duka nake so.”

Altaaf ya sake faɗi, robar da ke gabanta ta buɗe don ganin ɗanyar awarar da ta rage mata, kafin ta kalli Altaaf ɗin. 

“Ki sallame su tukunna, sai ki soya min duka.”

“Zata kai ta wajen ɗari uku fa.”

Nuwaira ta ce muryarta da alamun mamaki. Kai kawai Altaaf ya iya jinjina mata, saboda jikinshi gaba ɗaya ya mutu, yana sanar da shi akwai matsala in bai samu yarinyar nan ba. Idanuwanshi a kafe suke kanta har ta gama sallamar yaran ta fara soya mishi tashi tana kwashewa, duk wanda ya zo sai tace mishi ta ƙare, har sai da tagama, leda baƙa ta samu ta ƙirga mishi awarar tana zuba mishi albasa da su tattasai da yake a yayyanke sai yaji a wata ledar daban. 

Miƙa mishi ta yi yasa hannu ya karɓa yana tabbatar da yatsunsu ya taɓa juna, yana ganin yadda ta janye nata hannun da sauri, a wajenta haɗuwar hannayen nasu tsautsayine kawai da zai iya faruwa. Amma shi yana sane don shi ya miƙa nashi sosai yadda zai taɓa ta ɗin. 

“Ta ɗari biyu da saba’in ce, ka bada ɗari biyu da hamsin kawai…” 

Ta faɗi cikin sanyin murya. Miƙewa Altaaf yayi yana zaro ɗari biyar a aljihun shi sannan ya koma ya tsugunna, miƙa mata ya yi. 

“Kudin awarar kawai kika faɗa min, na mai awarar fa?” 

Yana ganin yadda komai ya tsaya mata cik, kafin ta ci gaba da ƙirgo mishi canjinshi cikin sauri tana miƙo mishi. Murmushi ya yi saboda tsoron da ke bayyane kan fuskarta kawai ƙara mishi yanayin da yake ciki ya yi. Baida lokacin ɓatawa akanta, baida ma wannan kwanakin, kuma duk kyawunta bai canza cewar ‘yar kauye bace ba. Canjin ya karɓa wannan karon yana haɗawa da yatsunta ya murza. Fisge hannunta Nuwaira ta yi tana miƙewa babu shiri. Tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da namijin da ba muharraminta ba ya taɓa ta. 

Jikinta ko ina ɓari yake yi, wani irin tsoro gaba ɗaya ya cika zuciyarta, kar wani ya wuce ya gansu, musamman da Altaaf ɗin ya miƙe shima. 

“Ko nawa ne ki faɗa min zan biya…ba wani daɗewa zan a ƙauyen nan ba, ki faɗa min kuɗin da zai siyeki.” 

Shi kanshi mamakin kalamanshi yake yi, yasan shi da mata na da alaƙa mai girman gaske, amma kalamai kai tsaye haka ba kalarshi bane ba, ya fi alaƙanta faruwar hakan yau da sanin cewa ba shi da wani lokacin ɓatawa, gara ya fito mata a fili. 

“Ina neman tsarin Allah daga gareka.”

Nuwaira ta faɗi muryarta na rawa, tana ɗaukar kujerarta ta wuce da sauri. Takunta Altaaf ya bi da kallo da kuma gidan ƙasar da ta shiga. Wata ƙofar langa-langa ce da bugu ɗaya zai mata ta karye, bai ma ga amfanin ƙofar ba tunda katangar kanta bawani tsayin kirki ne da ita ba, kamu ɗaya zai yi ya haura. Ya kai mintina biyar ko zata fito, amma shiru, don haka ya ja ƙafafuwanshi yana wucewa. 

Gidan da suka sauka ya wuce kanshi tsaye, baisan ya daɗe ba sai da Wadata ya ce, 

“Ina kaje haka Altaaf?”

Ledar hannunshi ya ajiye tukunna ya zauna. Ya kasa samun muryar magana balle ya ba Wadata amsa. Ƙamshin awarar yasa Wadata janyo ledar ya buɗe don ya ga ko menene a ciki. 

“Awara? Ina ka samo awara?”

“Siya nayi”

Altaaf ɗin ya amsa muryarshi da wani yanayi. Cike da mamaki Wadata yake kallonshi, ko a makaranta ba kowanne waje Altaaf yake cin abinci ba, saboda yana da ƙyanƙyami, ballantana kuma awarar kan layi, layin ma a ƙauye. 

“Me za kai da ita?”

Wadata ya tambaya don yana da tabbacin ba ci Altaaf ɗin zai yi ba. 

“Ci zanyi.”

Girgiza kai Wadata ya yi. 

“Ƙarya kake.”

Ba zai iya dogon surutu ba a yanayin da yake jinshi. Don haka ya matsa yana buɗe ledar awarar sosai ya ɗauki guda ɗaya ya saka a bakinshi yana taunawa. Aslam ya koya mishi ci, yana son awara sosai, kusan koda yaushe yana siyowa, amma Altaaf zai rantse bai taɓa cin wadda tai mishi daɗin wannan ba. 

“Mai awarar, tamin Yaya. Yarinyar tamun…”

Altaaf yake faɗi yana sake ɗaukar awarar ya jefa a bakinshi. Kallonshi Wadata yake yi, ya daɗe da sanin Altaaf ba wadataccen hankali gareshi ba, sai dai bai taɓa ganin irin haukan da yake gani ba yau a tare da shi. 

“Na tambayeta nawa ne kuɗinta, nawa ne zai siye ta. Ta nemi tsarin Allah daga gareni, ban ma gane kan addu’ar ba.” 

Girgiza kai Wadata ya yi. 

“Ka ce min baka faɗa mata maganganun nan ba.”

Kafaɗu Altaaf ɗin ya ɗaga 

“Innalillahi Altaaf… Me yake damunka?”

Kallon Wadatan yayi kamar zai fashe da kuka don shima baisan abinda yake damunshi ba, tunda ya sauke idanuwanshi akan yarinyar baisan abinda yake damunshi ba. 

“Ban sani ba wallahi. Kawai ita ɗin nake buƙata.” 

“Snap out of it. Ba zai faru ba, ka bar maganar nan, kana jina?” 

Wadata ya ƙarasa cike da kashedi, kai Altaaf ɗin ya jinjina mishi. Numfashi ya sauke, yanayin Altaaf kan mata ya fara bashi tsoro, dole yayi wani abu akai kafin a samu matsala. In ba jaraba irin ta Altaaf ba, Wadata bai ga me zai yi da ‘yar ƙauye ba, mai saida awara bayan tarin matan da suke binshi da shi wanda yake bi. 

“Ka ci awarar to.”

Altaaf ya buƙata. Kai Wadata ya girgiza mishi yana zame jiki ya kwanta ya ci gaba da latsa wayarshi. Kafin maganar Altaaf ɗin ta faɗo mishi. Wata irin dariya ta kuɓce mishi da ta sa Altaaf ɗin kallonshi. 

“Neman tsarin Allah ta yi daga gareka saboda ta ga shaiɗan Altaaf.” 

Wadata ya ƙarasa yana ci gaba da dariya. Dariyar shi ma Altaaf yake yi, yana jin yadda yarinyar tai mishi tsaye a maƙoshi da wani irin yanayi. Awarar ya ci gaba da ci suna hira sama-sama shi da Wadata. 

***** 

Hasken wutar lantarkin da aka kawo Wadata ya ji cikin fuskarshi. Bai buɗe idanuwa ba, saboda yasan Altaaf baya son haske in yana bacci shi ma m. Zai tashi ya kashe ƙwan fitilar. Jin shiru-shiru Altaaf bai kashe ba yasa Wadata sauke numfashi. 

“Yaron nan…”

Ya faɗi can ƙasan maƙoshi yana buɗe idanuwanshi da ƙyar, yana jin yadda hasken da ya shiga idanuwanshi yake barazanar korar mishi bacci. Inda Altaaf yake kwance ya kalla bai ganshi ba. Wayarshi ya laluba a gefe yana duba lokaci, ƙarfe biyu na dare har da wani abu. Ɗauka ya yi Altaaf ɗin ya tafi banɗaki ne, don haka ya miƙe kawai da nufin kashe wutar ɗakin, wata leda da farin abu da yake a ƙasa ya ja hankalinshi. Babu shiri gaba ɗaya baccin da ke jikinshi ya sake shi. Ƙarasawa ya yi inda Altaaf ɗin ya bari ya tsugunna yana ɗaukar ledar, ba sai an faɗa mishi ba yasan cocaine ne. Altaaf bai daina ba duk yadda yake ganin illar hodar iblis ɗin. 

Ran Wadata in yai dubu ya ɓaci, ledar ya mayar ya ajiye, yana zuwa ya kashe wutar ɗakin ya koma ya kwanta abin shi. Yayi niyyar ya koma bacci ne ya ƙyale Altaaf ɗin, zuwa yanzun ya yi girman da ya kamata yasan abinda yake da kyau da wanda bashi da kyau. Ba saiya gaya mishi ba, tunda gashi ya nuna mishi bai isa da shi ba. Sai dai me, duk yadda ya so ya koma bacci ya kasa, Altaaf ɗin yake so ya ji ya shigo ɗakin tunda yasan ba cikakken hankali ne tare da shi ba. Ƙaramin tsaki Wadata ya ja yana tashi zaune, wayarshi yai amfani da ita ya haska yana fitowa tsakar gida, takalmanshi da ya bari ya a bakin ƙofar ya haska bai gani ba, saina Altaaf ɗin. 

Takalmanshi ‘yan zire ne, na Altaaf ɗin kuma ƙafa ciki ne. Haka ya taka ƙafarshi duk yadda ya tsani jin ya taka ƙasa, akwai sauran ɗakuna a gidan, kuma duk mutane ne a ciki suna bacci, don nan gidan aka barma maza baƙi na nesa da suka zo ta’aziyya ba zai yiwu su koma gidajensu washegari ba. Har bakin ƙofar banɗakin Wadata ya ƙarasa, sai dai me, ƙofar a buɗe take da wutar banɗakin a kunne, babu kowa a ciki. Numfashi ya sauke. 

“Damn it Altaaf…”

Wadata ya faɗi cike da damuwa, dawowa ya yi ƙofar ɗakin da ke kusa da nasu ya zira ma kafafunshi wasu silipas da ya gani yana nufar hanyar ƙofar gida. Sai da gabanshi ya faɗi da ya ga gidan a buɗe. Ina Altaaf ya je cikin daren nan, garin da bai sani ba. Shi yasa tunda yake kayan maye basu taba burgeshi ba, shi yasa sigari ce kaɗai abinda ya sha da suna makaranta, itama inya san su Jamal sun mata haɗin wani abu baya taɓawa. Bai ga ranar abinda duk zai raba ka da hankalinka ba. Bai ma yi tunanin kiran wayar Altaaf ba, don yasan ko yana cikin hankalinshi fita da waya ne ƙarshen abinda yake yi. 

Tsaye ya yi a ƙofar gidan yana rasa ta inda zai fara neman Altaaf ɗin. Garin ya yi wani irin shiru mai ban tsoro. Ko giccin kaza bai gani ba ballantana mutum, a ranshi yake saƙa mantawa da girman Altaaf ɗin ya zane shi in ya dawo, wannan ai rashin hankali ne. A gefe ɗaya kuma addu’a yake Allah ya ba wa Altaaf ɗin hankalin dawowa daga koma ina ne ya je ɗin. Ga tsoro kuma da yake cike da ranshi kar Altaaf ya kasa gane gidan, duk da mawuyacin abune ka je da shi waje sau ɗaya ya kasa ganewa. Amma sanin ba cikin hankalinshi yake ba yasa Wadata tsoron faruwar hakan. 

“Wallahi Altaaf sai na ci ubanka.”

Cewar Wadata yana sake duba wayarshi, uku saura mintina takwas. Hankalinshi gaba ɗaya ya tashi. Akan Altaaf ya san asalin ciwon kai, ko furfura ya fara yana da tabbacin damuwar Altaaf ce ta ja mishi tsufa da wuri. Yana shirin komawa cikin gidan ya taso wani ya rakashi neman Altaaf ɗin ya hango kamar mutum na tahowa, daga takunshi ya gane Altaaf ne, wani numfashi ya sauke da bai san yana riƙe da shi ba. Ƙarasowa Altaaf ɗin ya yi. 

“Wanne irin iskanci ne wannan? Me yake damunka Altaaf? Kasan ko ƙarfe nawa yanzun? Ina kaje?” 

Wadata yake tambaya ranshi a bace. Kallonshi Altaaf yake yi da wani irin nisantaccen yanayi a fuskarshi. Sosai yake kallon Wadatan kamar yana neman wani abu da ya ɓace mishi akan fuskar Wadatan. Sai lokacin Wadata ya samu ya ƙare mishi kallo, kayan jikinshi sun yi futu-futu kamar wanda yai birgima cikin ƙasa. 

“Altaaf…”

Wadata ya kira cike da alamun tambaya. Har lokacin Altaaf ɗin bai ce mishi komai ba, bai ma nuna alamun ya ji yana magana ba. Don haka Wadata ya kama kafaɗarshi yana girgizawa 

“Altaaf…”

Ya sake kira wannan karin a ɗan tsorace, ya sha ganin Altaaf ɗin cikin yanayi kala-kala, amma banda irin na yau, tunda yake bai taɓa ganinshi a hargitse haka ba, fuskarshi ta yi kamar babu jini a jiki, ga wani yanayi cikin idanuwanshi da Wadatan baya son gani saboda ya mishi tsaye a zuciya da wani irin tsoro na ban mamaki. Ganin ko alamun Altaaf ɗin ya ji shi bai nuna ba ballantana ya amsa yasa shi kama hannunshi ya janyo shi cikin soron gidan. A hankali ya mayar da ƙofar ya rufe yana saka sakatar sama da ta ƙasa. 

Hannun Altaaf ɗin ya kama yana janshi, binshi Altaaf yake kamar ƙaramin yaro, har suka ƙarasa ɗaki, wutar ɗakin Wadata ya kunna yana kashe ta wayarshi ya ajiye wayar a gefe. Tukunna ya kalli Altaaf dake tsaye kamar robot ya kafa. 

“Altaaf menene?”

Sai lokacin Altaaf ya nuna alamun ya ji Wadatan, kai yake girgizawa kamar wanda yake ganin wani abu da Wadatan baya gani. Yana ji Wadata ya kamashi ya zaunar da shi, ji yake kamar an watsa mishi ruwan ƙanƙara, ƙafafuwanshi ya ja yana haɗe su da jikinshi tukunna ya ɗora kanshi a jiki. 

‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Nuwaira!’

Muryar matar ta dawo mishi, hannuwanshi duka yasa yana toshe kunnuwanshi da su. Yasan lokacin daya kasa bacci saboda koya ya runtse idanuwanshi hotunan yarinyar yake gani cikin yanayi mai wahalar faɗi. Yasan sa’adda ya kunna sigari ya sha ta fi kara goma, sai da ya ƙarar da gaba ɗaya wadda ya zo da ita, amma bai samu sauƙin abinda yake ji ba, hakan yasa shi ɗauko cocaine ɗinshi tunda ba shi da maganin tarin dazai sha ya yi bacci. Zai tuna lokacin da ya shaƙa har sai da ya daina gane abinda yake faruwa. Bai san lokacin da ƙafafuwanshi suka fitar da shi daga ɗakin ba ballantana kuma gidan gaba ɗaya. 

Girgiza shi Wadata yake yi. 

“Wai Altaaf lafiyarka? Ka min magana. Menene?” 

Wadata yake tambaya cike da damuwa. Amma ba ta shi Altaaf yake yi ba, runtsa idanuwanshi yayi gam, hotunan abinda ya faru ne yake gifta mishi, yana jin kamar wani ne ya yi amfani da gangar jikinshi yasa shi yake kallon me yayi da ita yanzun. Ba zai ce ga yadda akai ya je ƙofar gidansu Nuwaira ba, ya kasa tuna wannan ɓangaren. Ya ganshi a cikin gidan ne kamar mafarki, bai kuma san daga ina take ba, yadai ganta ne a tsaye ta ajiye wani abu da ba zai ce gashi ba, ya tuna tsoron da ke cike da idanuwanta da ta ganshi. 

Ɗago kanshi ya yi yana buɗe idanuwa babu shiri. 

“Altaaf!”

Wadata ya kira. Riƙo hannuwan Wadata Altaaf ya yi hankalinshi a tashe yana faɗin, 

“Ka ce min ban fita ba Yaya Imran. Ka ce min ina nan don Allah…” 

“Ka min magana. Menene?”

Kai Altaaf yake girgizawa. Wadata ba zai gane ba, tunda yake a rayuwarshi yaune ya fara sanin me ake kira da tashin hankali, yaune yasan me ake kira da tsoro, yau kuma ya fara fahimtar dana sani, ko kusa bai taɓa cin karo da yanayin ba a rayuwarshi. 

“Kace min ban fita ba kawai.”

Shi ne abinda Altaaf ya fi buƙatar ji fiye da komai, yadda Wadata ya fisge hannunshi yasa wani hoton gilmawa a kwakwalwar Altaaf ɗin, sai dai hannuwan bana Wadata bane ba. Kai ya sake girgiza ma Wadata yana ƙoƙarin miƙewa tsaye, amma Wadata ya fisgoshi ya zaunar da shi. 

“Altaaf… Ka nutsu. Menene?”

Kan dai ya sake girgiza ma Wadata, baya son yana tambayar shi ko menene, saboda baya son haɗa hotunan da ke gilma mishi ballantana ya bashi amsa cikakkiya, ya fi buƙatar ya tabbatar mishi da cewar bai je ko ina ba. 

“Na fita?”

Altaaf ɗin ya tambaya da wani irin yanayi a muryarshi da yasa Wadata ɗaga mishi kai. A lokaci ɗaya kuma Wadata ɗin na tunanin ko aljanu Altaaf ya haɗu da su a hanya suka firgitashi haka. Miƙewa Altaaf ɗin ya yi, wannan karon Wadata bai hanashi ba 

“Ina za ka je?”

“Wanka zan yi. Ina buƙatar in yi wanka.”

Kai Wadata ya ɗaga mishi yana miƙewa shi ma, sai rijiya a gidan, bokiti Wadata ya ɗauko a banɗaki, da kanshi ya janyo ma Altaaf ɗin ruwa yana cika mishi bokitin, ko yana cikin hayaccinshi ne ma ba iya janyo ruwa zai ba ballantana kuma yanzun da yake a firgice. Banɗaki ya kai mishi ruwan ya tsaya daga bakin ƙofar don bai yarda da yanayin Altaaf ɗin ba. Ƙofar banɗakin Altaaf ya tura yana jingina bayanshi da ita tare da zamewa ya zauna a ƙasa ba tare da ya damu ba. Numfashi yake mayarwa da sauri-sauri saboda tashin hankali. 

Runtsa idanuwanshi ya yi yana ganinta a tsaye har lokacin kafin ta yi yunkurin gudu, yana kuma ganin yadda ya riƙota jikinshi, yadda ko ina na jikinta ke ɓari amma ihunta bai fita ba, da dukkan ƙarfinta take son ƙwatar kanta, Har ya kaita ƙasa bata daina kiciniyar ƙwacewa ba, yana ganin hawayen da ke zubar mata amma ta kasa ihu. Ƙwanƙwasa banɗaki da akaine yasa shi buɗe idanuwanshi. 

“Altaaf?”

“Gani nan.”

Ya amsa Wadata cikin rawar murya yana miƙewa tsaye da ƙyar, ruwan ya samu ya watsa ko zai ɗan ji dai-dai ya fito. Yana jin idanuwan Wadata na bin shi da kallo kafin ya ji takun tafiyarshi alamun yana binshi a baya har suka koma ɗaki. Waje Altaaf ya samu ya zauna zazzaɓi mai zafin gaske yana rufe shi. 

“Ba zaka faɗa min abinda ya faru ba?”

Ɗago da kanshi ya yi yana sauke idanuwanshi cikin na Wadata, wani sabon tashin hankali na ziyartarshi 

‘Wanne irin kaskanci da rashin sanin darajar mace ne zai sa ka yi mata fyaɗe?”

Maganganun Wadata suka dawo mishi wani lokaci can baya da suna hira da su Jamal kan wani da aka ce ya ma wata yarinya fyaɗe a makarantarsu. 

‘Ni da za’a dinga kashe masu laifin fyaɗe abin zai min daɗi ne fa.’ 

Wani abu daya tokare wa Altaaf a wuya yake ƙoƙarin haɗiyewa ya ƙasa. 

“Me ya faru?”

“Karka tambayeni, don Allah karka tambayeni abinda ya faru.” 

Altaaf ya faɗi yana jin wani irin sanyi na ratsa shi har sai da tsikar jikinshi ta miƙe, kafin sanyin ya gauraye ko ina na jikinshi. Baisan ya fara kyarmar sanyi ba saida ya ga Wadata ya miƙo mishi riga saboda ta jikinshi mai gajeren hannu ce. Karɓa ya yi yana sakawa amma kamar babu kaya a jikinshi haka yake ji, hannu Wadata yasa yana taɓa wuyan Altaaf ɗin. 

“Me yasa bazan tambayeka abinda ya faru ba? Ka ji zazzaɓin da ke jikinka Altaaf? Innalillahi, ni kam gari ya waye mu tafi gida.” 

Wadata ya faɗi, damuwar da ke muryarshi na ƙara jefa Altaaf cikin wani sabon tashin hankalin. Shima jiran wayewar garin yake, da yasan Wadata zai barshi cikin daren nan zai gudu daga garin, ba zai jira gari ya waye mishi ba, da duk lokacin da ke wucewa da yadda abinda ya faru ke zaunawa tare da shi. Ɗaya daga cikin sauran ruwan robobin da suka sha Wadata ya ɗauko ma Altaaf ɗin yana bashi. Sannan ya samu waje kusa da shi ya zauna. Zai barshi ya samu nutsuwa tukunna ya sake tambayarshi me ya faru. Altaaf kam ya haɗe jikinshi waje ɗaya yana jiran gari ya waye. Awanni kaɗan ya rage, amma yana da tabbacin a rayuwarshi gaba ɗaya babu daren da zai taɓa kai wannan tsayi. 

***** 

Nuwaira ita ce yarinya ta uku a wajen Malam Bashari da matarshi Zulai. Wanda ‘yan asalin ƙauyen kinkiba ne. Abdullahi ne yaronshi na farko yana da mata da yara huɗu, sai Tawfiq, Nuwaira, Mariya, Asma’u, Anas da autansu da ya ci sunan mahaifin Malam Bashari suna kiran shi da Bappa. Talakawa ne sosai, noma Malam Bashar yake yi, ga rauni na manyantaka ya fara kama shi yanzun. Tawfiq ne ƙarfin gidan, shi kuma aikin kanikanci yake yi a cikin garin Zaria. 

Sa’annan shi duk suna da yara biyu, babu kalar surutun da baya sha, amma aure ne ƙarshen abinda yake gabanshi, ya fi son ya ga an aurar da ƙannenshi matan tukunna, hankalinshi zai fi kwanciya shima saiya nutsu waje ɗaya. Duka gidansu babu mai kyawun Nuwaira, za’a iya sakata cikin jerin ‘yan matan da suke tashen kyau a ƙauyen kinkiba, duk da ba boko suke ba, sun samu wadataccen ilimin addini. Sai dai me, da yake aure nufin Allah ne, Mariya ta fara samun miji don ita aka fara aurarwa. Sun sha surutu sosai kan cewa ba a kawar da yaya ba an kawar da ƙanwa . 

Malam Bashari da Zulai haka suke toshe kunnuwansu. Ko da Nuwaira ta ce zata fara awara don su haɗu a rufa ma kai asiri Tawfiq bai so ba sam, amma tausayin yarinyar yasa shi amincewa don shi ya bata jarin ma. Yana sane da surutun da ake mata a gari don sa’anninta duka suna da yara, har da ma mai guda uku, ko ƙanwarta Mariya tana da yarinya ɗaya. Zuciyarshi na zafi duk idan ya ji ana magana kan aurenta, bai san matsalar mutane da rashin sanin cewar aure na da lokacin shi ba. 

Baisan lokacin da mutane za su fahimci, aure, haihuwa da kuma mutuwa duka lokaci suke da shi ba, lokacin da yake da banbanci a ƙaddarar kowanne bawa, sun kasa gane kamar yanda babu gasa a wajen mutuwa haka bai kamata ace akwaita a wajen aure ba. 

Lokacin kowa in ya zo zai yi. 

Amman mutane ba za su taɓa fahimtar hakan ba, yadda duk suke son ganin lokacin auren Nuwaira yana da tabbacin ta fi su son ganin hakan ya faru ko don ta huta da surutunsu. Hakan yasa shi ci gaba da sakata a addu’arshi a kullum don ta samu miji ita ma. Sai dai hakan bai faru ba har sai bayan an saka ranar Asma’u da take ƙanwa ta biyu a wajen Nuwaira. 

Mutane da yawa kan ce ma Inna ko an yi ma Nuwaira asiri ne tunda ba kyau bane bata da shi, wasu kan ce ko aljanu ne, sukam sun bar komai a hannun Allah ne, wata biyu ya rage bikin Asma’u tukunna Allah ya kawoma Nuwaira tsayayye ita ma, duk da yana da mata da yara biyar, sun yi murna kamar me, hakan kuma yasa aka ƙara wata biyu kan bikin Asma’u don a haɗa a yi a tare. Lokacin da su Altaaf suka zo ƙauyen kinkiba saura wata ɗaya bikin Nuwaira. 

***** 

Sallar dare ta riga da ta zame mata jiki tun lokacin da surutu ya yawaita akan maganar aurenta, lokacin ne kaɗai take da damar yin kuka ba tare da ta ƙara ɗaga wa Inna hankali ba. Takan samu nutsuwa duk idan ta juye dukkan damuwarta a Sujjada. Allah ne kawai zai mata maganin matsalarta, tana da yaƙinin Bai manta da ita ba, da rana ɗaya imaninta bai taɓa samun rauni kan cewar lokacinta na nan zuwa ba. Sai gashi ya zo ɗin kuwa. 

Ko da addu’arta ta samu karɓuwa bai sa ta yi sanyi ba, hakan ma ya ƙara mata kusanci da Ubangiji ne fiye da lokacin da take cikin damuwa. Yau ɗin haka kawai bacci ya ƙaurace mata, tun suna hira da Asma’u har tai bacci ta ƙyaleta. Yanzun ɗin ma fitowa ta yi don ta yi alwala, banɗaki ta shiga ta fito, buta ta ajiye don ta ɗibi ruwan da sukan janyo su zuba a bokatai saboda alwala. Ta ji gabanta ya yi wata irin faɗuwa, don ta tsargu ana kallonta, hakan ya sa ta ɗagowa ta juyo, wani irin tsalle zuciyarta ta yi kamar zata fito daga ƙirjinta ganin Altaaf a tsaye. 

Tana da tabbacin ta katanga ya shigo, tunda katangarsu ba wahalar haurawa take da shi ba, basu taɓa damuwa da hakan ba tunda basa samun yawan sace-sace a ƙauyen. Ƙauye ne da zaman lafiya ya yawaita ta wannan fannin, harshenta kamar an ɗaure shi, su Asma’u sun sha mata dariya, don in ta ga abin tsoro komai daskare mata yake yi, gudu ma bata iya yi in ba wani ya janyeta daga wajen ba. Amma a karo na farko yau batasan yadda akai ƙafafuwanta suka fara aiki ba sai da ta ji hannuwan Altaaf sun riƙota cikin yanayin da zai kasance da ita har ƙarshen rayuwarta. Da dukkan ƙarfinta take kiciniyar ƙwacewa amma ta kasa. Tureshi take yi tana son ƙwace jikinta amma riƙon da yai mata bana wasa ba ne. 

Hankalinta bai ƙara tashi ba saida ta ji hannunshi kan maɗaurin zaninta tukunna. Bata tunanin a duniya akwai abinda yakai sanin kana gab da rabuwa da mutuncinka ta hanyar da tafi kowacce ƙasƙanci tashin hankali, yanayin da take ji ba zai taɓa misaltuwa ba sai wanda ya taɓa shiga cikinshi ne kawai zai fahimta. Ji take kamar a mafarki ne wannan ƙaddarar take shirin samunta, musamman da ta ji ta a ƙasa, da dukkan karfinta take son tunkuɗe Altaaf daga jikinta, nashi ƙarfin na ban mamaki ne, jikinta ta ji ya mutu gaba ɗaya, kafin wasu hawaye da suke tahowa daga zuciyarta su fara zubar mata. 

Fuskar Altaaf ta kalla da tasan fitar raine kawai abinda zai iya rabata da hotonta a wannan yanayin kafin ta mayar da idanuwanta tana rufewa, tana jin numfashinta na barazanar ɗaukewa jin hannuwan Altaaf a wajejen da bai kamata ba, kafin wani irin firgici yasa iska daina kaiwa cikin kanta, wani irin duhu-duhu ya fara fisgarta. Yanayin da take ciki ba zai taɓa misaltuwa ba, babu kalaman da zasu misalta sanin ka rabu da mutuncinka ta hanyar da bata kamata ba, duniyar da ta tsinci kanta a ciki baƙuwa ce. 

Ba zata ce ga abinda yake faruwa ba sai dai muryoyin da take ji sama-sama kafin ta ji an lulluɓa mata zani, suturar da ta samu na sakata rufe idanuwanta don kamar hakan ne abinda take jira dama ta bar duhun yai nasarar mamayeta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 28Alkalamin Kaddara 30 >>

2 thoughts on “Alkalamin Kaddara 29 ”

  1. Ina karanta littafin nan amma na kasa comment. Ji na ke kaman da gaske
    Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Lallai

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×