Skip to content
Part 24 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Babu abinda ya fi tsana irin ya dawo gida ya samu Ammi bata nan, bayajin daɗi sam, nan falo kan kujera ya ajiye jakarshi ya wuce ɗaki ya watsa ruwa ya saka wando da ya ɗan wuce gwiwarshi kaɗan, sai farar riga marar nauyi ya fito yana wucewa kitchen ya duba, shinkafa da miya ce Ammi ta yi, ya samu plate yana zubawa, sai da ya buɗe fridge da baya rabuwa da lemuka masu sanyi ya ɗauki coke tukunna ya koma falon yana zama kan kafet. Aslam ne ya shigo da sallamarshi, Altaaf din ya amsa bakinshi a cike da abinci. 

“Sannu da gida.”

Ya ce wa Altaaf ɗin yana wucewa ba tare daya jira amsarshi ba, bai fi mintina sha biyar ba ya fito jikinshi sanye da uniform ɗin Islamiya yana wucewa kitchen shi ma ya zubo abinci ya fito, binshi da kallo Altaaf ya yi. 

“Kai baka gajiya da zuwa makaranta ne?”

Murmushi Aslam yayi yana janye jakar Altaaf ɗin gefe ya zauna kan kujera tare da ɗora plate ɗin abincin a saman kujerar. 

“Ana gajiya da zuwa makaranta ne Yaya?”

Daƙuna fuska Altaaf yayi. 

“Sau nawa zance ka kirani Altaaf ɗina sak? Dole sai ka ƙaƙaba min girma?” 

Dariya Aslam yayi wannan karon yana cakuɗa abincin shi. 

“Girma ko baka so ya kamaka ai Yayaa.”

Ya ƙarasa maganar yana jan kalmar Yayan akan harshen shi. Girgiza kai Altaaf yayi, Aslam yasa yanzun har su Barrah Yaya suke ce mishi, suna sa yana jin kamar girma ya kamashi, haka kawai da yarintarka aita ɗora maka girma. Abincin shi Aslam yake ci hankali kwance, ya ga kamar report card an nannaɗe shi an tura a aljihun gefen jaka, hannu yakai yana zarowa, Altaaf ɗin nabin shi da kallo a kasalance, an jima da bayar da report card ɗin, shi dai sai yau aka samu ganinshi aka bashi. 

Buɗewa Aslam ya yi, shafin farko jarabawar zangon farkoce, inda a C.A test ɗin da Altaaf yayi babu inda ya samu maki fiye da biyar, wasu ma bai je ba, haka jarabawar babu inda yake da sama da maki sha shida. Da sauri Aslam ya duba position ɗin, ya ga cikin su hamsin da huɗu, Altaaf ne yazo na 53. Ma’ana mutum ɗaya ya kayar, da sauri ya buɗe shafin zango na biyu, wannan karon na 52 yayi. Cikin tashin hankali Aslam ya ce, 

“Yayaaa”

Cike da halin ko in kula Altaaf yake kallon shi. 

“Yaya wannan ai abin kunya ne wallahi. Na biyun ƙarshe fa.” 

Harara Altaaf ya watsa mishi.

“Uban me zan ci da ƙoƙarin to?”

“Ban gane me za ka ci da ƙoƙarin ba?”

Hamma Altaaf yayi, don bacci ma yake ji. 

“Marasa galihu ne suke buƙatar karatu, kaima wahalar da ƙwaƙwalwarka kake yi, bayan kasan Ammi na da kuɗi.” 

Cike da mamaki Aslam yake kallon shi, don bai taɓa jin tunani kalar na Altaaf ɗin ba tunda yake, ya ma rasa abinda zai ce mishi, don shi kam karatu na da muhimmanci sosai a wajenshi, yana son zama Engineer babba, bai taɓa wuce na ukku a ajinsu ba, boko kenan, Islamiya kuwa shi yake zuwa na ɗaya, don ba ƙaramin abin kunya bane a wajen Aslam a ce ya gaza ta fannin addininshi. 

“Lallai Yaya sannu.”

Aslam ya faɗi, miƙewa Altaaf ya yi yana fisge report card ɗin shi daga hannun Aslam, ya ɗauki jakarshi tukunna ya ce, 

“Ciwo nake da za kai min sannu don ubanka?”

Dariya Aslam yayi. 

“Allah ya baka haƙuri. Kazo na biyun ƙarshe bai maka zafi ba sai sannu?” 

Duka Altaaf ɗin ya ɗirka wa Aslam a baya.

“Don kana ganin haƙorana shi yasa za ka rainani ko?” 

Wajen Aslam yake murzawa, duk da Altaaf ya bashi shekara kusan biyu, girmansu daya, dan da alamu zaifi Altaaf din girman jiki nan gaba, yana bashi girman shi sosai, duk rainin nan da ke tsakanin saƙo da saƙo babu shi a tsakanin su, barshi da tsokana dai. Altaaf ɗin kanshi yasan Aslam na bashi girma, ya fita daban a cikin su huɗun, Barrah ma bata da kunya ko kaɗan, ko laifi tai mishi yana dukanta tana watsa mishi zagi, bakinta ba zai taɓa shiru ba. Wucewa yayi ɗaki abinshi, ko kaɗan maganganun Aslam basu sa ya ji wani iri kan rashin ƙoƙarin shi ba. 

Kamar ko yaushe, marasa galihu sune suke mayar da hankali kan karatu, don basu da wata mafita da ta wuce hakan. Kwanciya yayi kan gado yana jin wata irin gajiya a duk jikin shi. Bai san ƙofar ɗakin shi a buɗe take ba sai da ya ji muryar Barrah kamar daga sama tana faɗin, 

“Yayaaa…. Yayaaa.”

Buɗe idanuwa da suka rine saboda baccin da ya fara ɗaukar shi yayi yana sauke shi akanta, tana tsaye saman kanshi, jikinta sanye da uniform, tana rataye da jakar data saƙala hannayenta duka biyun a jikin hannuwan jakar tana kallon shi fuskarta a shagwaɓe. 

“Yayaa ina Ammi?”

Wani irin tsaki ya ja, kanshi na taruwa da alamun ciwon kai. 

“Ka ji ina Ammi?”

Ta sake tambaya tana shirin yin kuka. 

“Barrah…”

Ya kira can ƙasan maƙoshi

“Na’am…”

“Ki fitar min daga ɗaki.”

Ya ƙarasa maganar yana jin in har ta bari ya tashi komai zai iya faruwa. 

“Ni yunwa nake ji kuma banga Ammi ba.”

Barrah ta faɗi hankalinta a kwance, kamar bata jin yadda ranshi yake a ɓace ba. 

“Uban me zan miki to?”

“Kar dai ka ce za ka za gi Baba wallahi.”

Tashi zaune Altaaf ya yi yana kallon Barrah, rashin kunyarta har mamaki take bashi lokuta irin haka, ‘yar ƙaramar yarinya da ita shekaru basu wuce biyu ba sai rashin kunyar tsiya, cikin idanuwa take kallon shi. 

“Fitar mun daga ɗaki.”

Maƙale kafaɗa ta yi alamar a’a. Idanuwanshi ya runtsa yana buɗe su, ciwon kan da ya fara ji yana ƙaruwa. In ma dukanta ya yi zama za ta yi ta dinga rusa kukan da sai dai ya fita ya bar mata gidan. 

“Ya kike so in yi da ke?”

“Ka zo ka zuba min abinci.”

“Ina Aslam?”

Ya tambaya, don yasan duk da ya saka Uniform ɗin Islamiya sai an yi sallar la’asar tukunna yake tafiya. Ba zai wuce kallo yake a falo ba. 

“Yana bacci a falo.”

Barrah ta amsa da alamun ta gaji da magana. Cike da mamaki yake kallonta. 

“Ba za ki iya tashin Aslam ɗin ya zuba miki abinci ba?” 

“Kanshi zai yi ciwo.”

Dariyar takaici mai sauti Altaaf ya yi. 

“Don ubanki ni ba kya tunanin kaina zai yi ciwon? Za ki zo ki tashe ni?” 

Buga ƙafafuwanta ta fara yi. 

“Ni ka tashi ka zuba min.”

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”

Altaaf ya faɗi yana runtsa idanuwanshi tare da buɗe su, yana da tabbacin Ammi ta haifi Barrah ne kawai don ta takura wa rayuwarshi. Miƙewa yayi ta kama hannunshi ta riƙe dam, kallonta yayi ta turo laɓɓanta tana zubar da ruwan ƙwalla. Numfashi ya sauke yana wucewa tana riƙe da hannunshi kamar zai gudu har suka je kitchen. Abincin ya zuba mata yana ɗaukar cokali ya saka mata a plate ɗin. 

“Baka bani lemo ba.”

Barrah ta ce ganin yana shirin fita daga kitchen ɗin, baya son surutu, don haka ya buɗe fridge ya ɗauko mata fanta na gwangwani. 

“Bana son shi, mai apple nake so.”

Kanshi ciwo yake yi kamar zai faɗo, Barrah ta zo mishi har wuyanshi. Mayarwa ya yi yana duba cikin fridge ɗin, bai ga wani lemo mai apple ba. Muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Barrah babu wani lemo mai apple a nan.”

“Bani wancan ɗin to.”

Ɗauka ya yi ya miƙa mata yana rufe fridge ɗin, har ya kai ƙofa ya juyo ya kalleta. 

“Idan na ganki a ɗakina saina karya miki ƙafa.” 

Yana jin dariyarta lokacin da ya fice, gaba ɗaya ta mayar da shi abokin wasanta, da ya koma ɗaki yasan ba zai iya komawa bacci babu taimakon wani abu ba, don haka ya ɗauki maganin tari kwalba ɗaya ya shanye ya koma ya kwanta, a hankali maganin ya soma aiki, bacci mai ƙarfin gaske ya yi gaba da shi. 

***** 

Bai tashi ba sai wajen isha’i, jikinshi yayi wani irin nauyi kamar ba nashi ba, da kuyar ya ja ƙafafuwa zuwa banɗaki ya watsa ruwa ya yi alwala ya fito. Salloli ya jero daga Azahar zuwa Isha’i yana yinsu a lokacin, tukunna ya sake kayan jikin shi zuwa ƙananun kaya masu tsadar gaske, baƙaƙen takalmanshi ya ƙarasa daurewa yana ɗaukar baƙar hula hana sallah ya saka a kanshi. Don in dai fita zai yi irin haka sai ya saka ya riga ya saba. 

Agogo ya ɗaura a hannunshi shi ma baƙi, tukunna ya feshe jikinshi da turaruka, wayarshi da ke kan gado ya ɗauka yana kashewa ya mayar ya ajiye. Yasan yau zuwan club ɗin zai banbanta dana ko yaushe tunda za su yi murnar zagayowar ranar haihuwar Ruma ne. Ba zai yiwu kuma ace bai sha wani abu ba, shi yasa ma ya ajiye wayarshi a gida. Falo ya fita yana samun Ammi da Baba a zaune suna kallo suna hira. Tana jin takun tafiyarshi ta mayar da idanuwanta kanshi 

“Altaaf samarin Ammin shi, haka maƙiyanka za su ganka su barka.” 

Ammi tai mishi kirarin da takan yi duk idan ta ga yayi shigar da ta fito da kyawunta, har ƙasan zuciyarta take alfahari da shi. 

“Allah ya kare min kai daga bakin mutane.”

Da murmushin jin daɗi a fuskar Altaaf amsa da, 

“Amin Ammita. Shi yasa nake ƙara son ki.”

‘Yar dariya ta yi, kallon su Baba yake yi, dama ba sosai yaran suka damu da shi ba, gaisuwa kawai ke haɗa su, matsalolinsu duka wajen Ammin su suke zuwa, gara ma Aslam shi ne yake zama su yi hira, don ranakun da babu Islamiya har kasuwar kantin kwari yake shiga shagon Baba ɗin ya taya shi ayyuka, har sai lokacin rufe shago yayi su dawo gida tare. Amma Altaaf ba ko yaushe ma gaisuwar ke haɗa su ba. 

“Ammi zanje wajen taron birthday ɗin Ruma ne…” 

Baba da ke zaune ya karɓe zancen da faɗin, 

“Da daren nan? Ku dawo ƙarfe nawa?”

Ɓata rai Altaaf ya yi yana kallon Ammi. 

“Kai kam ka cika takura wa yara wallahi. Ruman ne baka sani ba? Abokin sune fa.” 

Cewar Ammi.

“Allah ya kyauta.”

Baba ya faɗi yana ɗauke idanuwanshi daga kansu. 

“Idan dare yayi zamu kwana a gidansu Ruma ɗin… Na bar wayata a ɗaki.” 

Jinjina kai Ammi ta yi. 

“Allah ya tsare hanya, kuɗin hannunka za su isheka dai ko?” 

Kai ya ɗan ɗaga mata yana gyara zaman wandonshi kan ƙugunshi yasa kai ya fice daga gidan. Mashin ya tare da zai kai shi Elangantee Night Club. Yana ƙarasawa ya shiga ya miƙa wa masu gadin wajen ɗan katin da zai bashi damar shiga. Dubawa suka yi tukunna suka buɗe mishi ƙofa, yanayin wajen ya kalla yana jan wani irin numfashi kafin ya saki murmushin nishaɗi, ta baya yaji an rungumeshi, hannuwanta da ke kan ƙugunshi ya ɗora nashi akai yana jin yanayin hannuwan. 

“Jennifer…”

Ya faɗi, dariyarta ya ji cikin kunnenshi, ma’aikaciya ce a club ɗin, a ƙalla zata bashi wajen shekaru takwas, tun ranar da suka fara zuwa club ɗin ta ƙyalla idanuwanta akan A-Tafida ta ji yaron ya mata, ita ce mace ta farko da wani abu ya fara haɗa shi da ita, da taimakonta ya lalace sosai ta wannan fannin. Ko kaɗan bata son ta ga yara ƙanana a kusa da shi in ya zo club ɗin. Sai dai A-Tafida duk da ƙarancin shekarun shi yana nuna alamun namiji ne da ba zai juyu cikin sauƙi ba. 

Yau kuma ba shi da ra’ayinta, don haka ya kamo hannunta ya dawo da ita gabanshi. 

“Wani lokacin Jennifer”

“Altaaf…”

Yatsanshi yakai kan laɓɓanta tare da girgiza mata kai, yana sauke su ya wuce abinshi ya barta a tsaye. Can cikin club ɗin ya ƙarasa yana hango su Ruma suna rawa, yanayin kiɗan ya fara bi yana takawa a hankali, idan ka ga yana rawa zaka rantse da Allah ya yi shekaru yana koya ne, hannu Kaigama ya ɗago mishi saboda hayaniya ta yi yawa ko magana ya yi ba za’a jiyoshi ba. Sosai Altaaf yake kutsawa har sai da ya ƙarasa inda Ruma yake zagaye da ‘yan mata. 

“Happy Birthday!”

Ya faɗi da ƙarfi, dariya Ruma ya yi yana jinjina mishi kai, taɓa mishi ƙafar da aka yi yasa shi juyawa, glass cup Naz ya bashi da yake da tabbacin giya ce a ciki, in ba a yanayi irin haka ba, shaye-shayen shi baya taɓa wuce syrup, sai kuma taba da ta zame mishi jiki fiye da komai. Karɓa ya yi yana ɗagawa ya shanye ya runtsa idanuwanshi saboda zafinta daya ji kamar maƙoshin shi ya kama da wuta. 

Ba zai ce ga adadin abinda ya sha ba, ko me ya ƙarasa faruwa a daren, kawai ya buɗe idanuwanshi ne, kanshi kamar zai rabe gida biyu saboda ciwon da yake yi, yanayin ɗakin ya kalla yasan na Jennifer ne, bazai kuma tuna sa’adda ya biyota suka zo ba, a hankali ya sauko daga kan katifar, rigarshi ya fara hangowa ya ɗauka ya saka, tukunna dogon wandon shi, a hannu ya ɗauki takalmanshi yana jin kamar ana yaƙin duniya na uku a cikin kanshi. 

A hankali ya buɗe ƙofar yana ficewa, ɗakin da Jennifer take haya cikin sabon gari ne, irin gidan yawan nan, yana da tabbaci ɗakuna sun fi ashirin a cikin gida. A bakin ƙofa ya saka takalmanshi, yana dafe da kanshi yake tafiya har ya fice daga gidan. Sai da ya ɗan samu waje ya huta tukunna ya ci gaba da tafiya, mashin ɗin da ya fara cin karo dashi ya tare yana faɗa mishi Bachirawa zai kai shi. Iskar ma jinta yake kamar tana ƙara mishi ciwon kai. Da ƙyar yake ɗaga idanuwanshi yana nuna wa mai mashinu ɗin hanyar da zai bi har ya ƙaraso da shi ƙofar gidan su Ashfaq. 

Sai dai me aljihunshi duka biyun ya laluba bai ji kuɗi ko alamarsu ba, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce wa mai mashin ɗin, 

“Bari in karɓo maka kuɗin.”

Parking mai mashin ɗin ya gyara yana cakumar rigar Altaaf.

“Ina kake tunanin za ka je?”

Hannunshi Altaaf ya ture. 

“Dalla Malam cire ƙazamin hannunka daga jikina. Kuɗinka zan karɓo maka ko baka jini ba ne?” 

Sake riƙe shi mai mashin ɗin ya yi don ya riga yasan yara irin su Altaaf, hanyar da zai gudu kawai yake nema, kallon mai mashin ɗin Altaaf ya yi, yana jin dariyar takaici na kubce mishi. 

“Ka sake min riga.”

Ya faɗi cike da kashedi. 

“Ka bani kuɗina kawai sai ka tafi.”

Cewar mai mashin yana ƙara riƙe Altaaf dam, hannu Altaaf ya ɗaga zai zabga mishi mari ya ji an ce 

“Altaaf?”

Juyawa Altaaf yayi yana ganin Amjad, yayan su Ashfaq na kuarasowa inda suke tsaye shi da mai mashin ɗin. 

“Lafiya? Me yake faruwa? Malam sake mishi riga.” 

Amjad ya faɗi yana kallon yadda mai mashin ɗin ke cakume da rigar Altaaf ɗin 

“Idan na sake shi kai zaka biyani kuɗina?”

“Nawa ne kuɗin naka? Ka sake shi in baka.”

Sakin rigar Altaaf ɗin ya yi kuwa yana faɗin, 

“Ɗari biyu ne.”

Lalubawa Amjad yayi ya zaro ‘yan naira hamsin guda uku sai ashirin biyu da naira goma ya haɗa ya ba mai mashin ɗin , hankalin shi ya mayar kan Altaaf da yanayin shi. 

“Daga ina kake da sanyin safiyar nan?”

Dan sosa kai Altaaf yayi. 

“Daga gida.”

“Ƙarya kakeyi Altaaf.”

Shiru Altaaf ɗin yayi yana sadda kanshi ƙasa, yana jin idanuwan Amjad ɗin na yawo a kanshi kafin ya numfasa yana faɗin, 

“Don Allah Altaaf ka dinga kula.”

Shirun dai Altaaf ya sake yi sai da ya ji takun tafiyar Amjad tukunna yakai hannu yana dafe kanshi da ke ciwo har lokacin, ɗaya daga cikin dalilan da baya shan giya kenan, saboda duk wani abu da ke da wahala a cikin shi baya kusanta, baya son rashin jin daɗi ko kaɗan. Cikin gidan ya shiga, yana cin karo da Hamna jikinta sanye da uniform ɗin islamiya. Kallonta yayi kamar bata sha saka shi kuka ba, ƙarfin yarinyar sai ka ce na doki, gashi sam da yana gidan jininsu bai haɗu ba, da ciwo da yaƙushi sai ta kaishi ƙasa. 

Harara ta zabga mishi 

“Baka taɓa ganina bane?”

Kai ya girgiza mata, yana runtsa idanuwa, don ganinta yasa ya manta da ciwon da kanshi yake yi. 

“In ba zaka wuce ba ka matsamin malam.”

Ta sake faɗi, gefe ya rakuɓe duk da haka sai da ta bangaje shi da kafaɗa tukunna ta wuce, jiki babu ƙarfi ya ƙarasa gidansu Ashfaq yana addu’a kar ya haɗu da Mama a tsakar gidan, kamar ɓarawo haka yake lallaɓawa har ya ƙarasa ɗakin Ashfaq ɗin yana ɗaga labulen ya shiga. Ashfaq da ke kwance kan bayanshi, hannunshi ɗaya na sama kanshi kamar mai son kare haske, hannun ya sauke ya juyo yana kallon Altaaf da ke cire takalman shi. 

Gefe ya ajiye su yana shirin zama kan katifar Ashfaq ɗin ya dakatar dashi da faɗin, 

“Karka zauna min kan katifa da najasa a jikin ka. Ka je ka yi wanka don Allah…” 

Ashfaq ya ƙarasa maganar yana mayar da idanuwanshi ya rufe, fita Altaaf yayi yana zira silifas ɗin Ashfaq da ke bakin kofa ya nufi banɗaki ya ɗauko bokiti ya zo ya ɗibi ruwa, Mama ce baya son haɗuwa da ita bai nutsu ba, yasan don ranar ta kasance ƙarshen mako, wato Asabar, tana ɗaki tana hutawa tunda su duka babu mai zuwa makaranta. Wanka ya yi, alwalar ma a cikin banɗakin ya yi ta, tukunna ya fito da dogon wandonshi a rataye jikin kafaɗarshi tunda akwai gajere ya wuce ɗakin Ashfaq ɗin. 

Kanshi tsaye ya nufi jakar Ashfaq yana samun wani wando iya gwiwa ya ɗauka ya saka, tukunna ya samu riga ya sa, zuwa yayi ya ja darduma yana kabbara Sallah, kallon takaici Ashfaq yake binshi da shi har ya idar. 

“Inda mutuwa ta sameka a inda kake fa? Wanne uzuri za ka bayar na jinkirta sallah har zuwa yanzun?” 

“Ba zaka bada misali da wani abu ba sai da mutuwa? Kullum maganar mutuwa.” 

Altaaf yake faɗi yana daƙuna fuska cike da rashin jin daɗin maganar mutuwar da Ashfaq yai mishi. 

“Baka so ana tuna maka za ka mutu ko?”

Ashfaq ya tambaya, shiru Altaaf yayi, yana miƙa hannunshi ya janye pillow ɗin da Ashfaq yake kwance ya ajiye a ƙasa yana kwanciya kan kafet ɗin da ya idar da sallar. 

“Bacci nake ji don Allah ka ƙyale ni.”

Girgiza kai kawai Ashfaq yayi, bai cika son yawan magana ba, musamman da safiya haka. Fitowar Mama ya ji daga ɗaki, don haka ya miƙe shima yana ficewa don yasan abin kari za ta haɗa musu, don ya kama mata aikin. 

***** 

Zai ce abu ɗaya yasaka shi jin kamar da alamun zai ci jarabawarshi ta aji shida wato WAEC, saboda ana kawo musu duka amsoshin, abinda suke yi shi ne su kalla su rubuta kawai, amma duk da haka ji yake hannun shi ya gaji da rubutun tunda ba sabawa yayi ba. Yana dagewa ne ya yi kawai saboda yana son zuwa jami’a, yana son ganin yadda rayuwar jami’a take, ba don haka ba ba zai ma zauna awanni haka a aji yana rubuta wata jarabawa da yake tunanin bata da wani amfani a wajen shi ba. 

Yau yana gama jarabawar ya fito daga makaranta ya fara tunanin ko ya je gidansu Ashfaq ko ya wuce gida abinshi, yana tunanin kamar Ammi bata nan, don ya ji tana faɗin zata fita unguwa da safe, da wahala kuma idan ta dawo. Sai dai shi ma Ashfaq ɗin da wahala in yana gida, shi ya gama jarabawar shi ta aji shida tun waccan shekarar, bai kai da samun gurbin karatu bane ba har lokacin. Don haka ya wuce gida abinshi. 

Yana shiga ya samu Aslam a tsaye, Barrah da Anam na zaune kan kujera, yanayin shi kawai ya kalla yasan babu lafiya, don ko sallamar da ya yi bai amsa mishi ba, 

“Aslam?”

Altaaf ya kira da alamun tambaya a muryarshi, ɗago kai Aslam ɗin ya yi. 

“Yaya.”

Ya ce da alama sai lokacin ma ya kula da Altaaf ɗin yana wajen. 

“Lafiya? Me ya faru.”

“Ammi bata kira ka ba kenan?”

Girgiza kai Altaaf ya yi. 

“Rasuwa aka yi a gidan su Ashfaq.”

Barrah ta faɗi da sauri, wani irin tsalle Altaaf ya ji zuciyarshi ta yi kamar zata fito daga ƙirjinshi. Gwiwoyinshi na yin sanyi kamar ba zasu iya ɗaukar nauyin shi ba. 

“Rasuwa kuma? Wa ya rasu?”

Ya tambaya muryarshi na rawa. 

“Kawu Hisham.”

Aslam ya bashi amsa, hanjin cikin shi Altaaf ya ji sun tattare waje ɗaya, zazzaɓi na kawo mishi ziyara. 

“In jiraka ne ka sake uniform? Gidan zanje yanzun don in samu jana’iza.” 

A tsorace Altaaf yake kallon Aslam ɗin, tunanin zuwa gidan su Ashfaq ɗin na ƙara saukar mishi da sabon zazzaɓi, bai taɓa zuwa jana’iza ba, asalima ko makara ya gani sai zazzaɓi ya kama shi , balle a ce ya je maƙabarta rakiyar gawa, abu ne da bazai taɓa faruwa ba. 

“Yayaa.”

Aslam ya kira jin Altaaf ɗin ya yi shiru, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Ka je kawai.”

Wucewar kuwa Aslam yayi yana barin Altaaf da yake jin komai ya kwance mishi. Ɗaki ya wuce ya kwanta, sai dai me, da ya rufe idanuwanshi Kawu Hisham ɗin yake gani, mutumin kirki, don baya tunanin akwai mai kirkinshi duk a dangin Baba, lokacin ko dawowa yayi daga tafiya zai aiko musu da tsarabar su har cikin gida, haka in yana nan ranar juma’a yakan tattarasu duka ya saka su a gaba su tafi sallar juma’a tare. Sai da lokacin tunanin bai yi sallar Azahar ba ya faɗo mishi. 

Da sauri ya tashi yana zuwa ya yi alwala, rabon da yayi azahar ita kaɗai ba tare da ya haɗa da sallar la’asar ba har ya manta, in ba ranakun juma’a ba. Amma yau kam ya bala’in tsorata da jin mutuwar Kawu Hisham. Nan ya zauna kan dardumar yana rasa me ke mishi daɗi, yasan ya kamata ace ya je wa Ashfaq, ya kamata a ce yana tare da Ashfaq ɗin amma ba zai iya zuwa ba, tsoron shi yayi tasiri akan kusancin shi da Ashfaq ɗin. 

Komawa ya yi ya kwanta, yinin ranar babu abinda ya saka wa cikin shi har dare tukunna da ƙyar ya sha robar yogurt ɗaya ya kwanta, bai iya samun bacci ba sai da taimakon syrup ɗin shi tukunna. Washe gari ma jikinshi babu ƙarfi ko kaɗan ya tafi makaranta don yin jarabawar ranar, su Ruma kansu sai da suka kula babu walwala a tare da Altaaf ɗin, da suka tambaya ya ce musu baya jin daɗi ne kawai. A taƙaice a satin ya hau mashin yana sauka unguwarsu Ashfaq ɗin yai tsaye bakin titi yana kasa ƙarasawa ya fi a ƙirga. 

Yau ma sadakar bakwai, kuma yayi dai-dai da ranar da ba shi da jarabawa, don sauran kwara biyu ta rage mishi ya kammala. Ya jima tsaye a bakin titi yana kasa ƙarasawa gidan, ƙarshe ruwa ya siya a shagon dake kusa da titin yasha tukunna ya sake tare mashin ya koma gida. Banɗaki ya shiga ya ji kamar an shigo dakin shi, yasan ba zai wuce Barrah ba, sai dai me yana fitowa Ashfaq ya gani a tsaye ya jingina bayanshi da bangon ɗakin, sai da ya ji zuciyarshi tai wani irin dokawa. 

“Ashfaq…”

Ya kira cike da ban haƙuri da wasu yanayoyi a muryarshi, kallo ɗaya za kai wa Ashfaq ɗin ma kasan babu nutsuwa a tattare da shi, ga ramewa da ya yi kamar wanda ya tashi daga jinya. 

“Ina buƙatar shaƙar iska daban ne Altaaf…”

Kai Altaaf ɗin yake ɗaga mishi duk da yasan ba zai taɓa fahimtar halin da yake ciki ba. Yana kallon Ashfaq ɗin yana sauke numfashi kamar yayi gudu, kafin ya zame jikinshi a hankali yana zama ƙasa. 

“Karka zauna a ƙasa mana… Ka tashi akwai sanyi a wajen.” 

Altaaf yake faɗi yana ƙarasawa ya miƙa wa Ashfaq ɗin hannu don ya taimaka mishi ya miƙe, girgiza mishi kai Ashfaq ɗin yake yi, yana saka fuskarshi cikin hannuwanshi.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…

Yake furtawa yana maimaitawa, yanayin yanda muryarshi ke fita yasa Altaaf ɗin ware idanuwanshi cikin tashin hankali, kuka Ashfaq yake yi, abinda ko a yarintarsu bai taɓa gani ba, babu shiri ya tsugunna yana dafa kafaɗar Ashfaq ɗin. 

“Ashfaq….ban san ciwon da kake ji ba…”

Altaaf yace muryarshi na karyewa, yanayin kukan Ashfaq ɗin kawai zai faɗa maka yanayin halin ƙuncin da yake ciki amma baisan yadda zai sauƙaƙa mishi ba. Muryar Ashfaq ɗin a shaƙe ya ce, 

“Minti biyar, minti biyar kawai nake buƙata.”

Miƙewa Altaaf ɗin ya yi yana zuwa kitchen ya haɗo shayi mai kauri ya dawo ɗakin yana zama kusa da Ashfaq ɗin. A hankali ya ajiye cup ɗin yana turawa ɓangaren Ashfaq ɗin. Ya jima yana kallon kofin kafin ya ɗauka ya soma kurɓa hankali. 

“Ban zo ba, kayi haƙuri, bansan a wanne yanayin zan ganka ba, tsoro nake ji wallahi shi yasa na kasa zuwa.” 

Kai kawai Ashfaq ɗin ya iya jinjina mishi yana ci gaba da kurɓar shayin. 

“In zubo maka abinci?”

Kai ya girgiza alamar a’a, tas ya shanye shayin yana dafa bango ya miƙe da ƙyar. 

“Ina son in ɗan watsa ruwa sai in tafi.”

Ashfaq ɗin ya faɗi, kai Altaaf ya ɗaga yana mishi nuni da hanyar banɗakin, kafin ya fito ya ɗauko mishi kayan da yake tunanin za su yi mishi. Sauran kuɗin da ke hannunshi gaba ɗaya ya kwashe yana sakawa a aljihun wandon ya fita daga ɗakin yana komawa falo, yana nan zaune Ashfaq ɗin ya fito sanye da kayan da ya fito mishi da su, sai yanzun ma yake ganin ramewar da ya yi sosai. 

“Har ka gama?”

Da Kai ya amsa mishi yana nufar hanyar ƙofa, da sauri Altaaf ya mike yana bin bayanshi. 

“Ka zauna… Zan zo da kaina a in ina buƙatar hakan.” 

Ashfaq ya faɗi.

“Ka tabbata?”

Altaaf ya ce yana tsare shi da idanuwa. 

“Yanzun ba ni na zo ba?”

“Hakane. Akwai kuɗin mashin a jikin kayan.”

Kai Ashfaq ya jinjina mishi yana ficewa, wani irin numfashi Altaaf ya ja, yana ƙara jin yadda ya tsani ko jin an furta mutuwa ma. Nan falon yayi zaman shi har Ammi ta fito tana samun shi. 

“Altaaf ba’a fita bane yau?”

Juyawa ya yi yana shagwaɓe mata fuska. 

“Ni bana jin daɗin jikina ne Ammi.”

“Subhanallahi…to ko mu je asibiti?”

Kai ya girgiza. 

“Stress ɗin jarabawa ne yake tambayar ka.”

Kafaɗa ya ɗan ɗaga mata alamar zai iya yiwuwa gajiyar ce ko wani abin daban kuma. 

“Sannu. Yaushe ne Jamb ɗin?”

Ammi ta tambaya cike da kulawa, shi tunda suka gama cike komai ance musu dai su saurara tukunna, da yake ɓangaren Art yake tunda bai da ƙoƙarin da zai yi joining science class, ba don art ɗin na marassa ƙoƙari bane, sai don suna tunanin zai fi mishi sauƙin fahimta. To can ɗin ma ba ya damu bane ba, zaɓin abinda zai karanta ma mai cike abin jamb ɗin ya bar wa, ya ce dai zaɓin makaranta na farko jami’ar Ahmadu bello da ke Zaria yake so. Ammi sai da taita tsegumi daya faɗa mata, taso shi da Bayero ne ko don kar yai mata nisa. 

“Ban sani ba dai tukunna.”

“Ok to Allah ya nuna mana lokacin…ka ci abinci?” 

Kai ya girgiza. 

“Bana jin yunwa.”

Hararar shi Ammi tayi,

“Bakaci komai ba kana fadamun bakajin yunwa. A haka kake son tafiya har Zaria karatu? Yazant yarda zaka kula da kanka” 

Yar dariya yayi,halin da Ashfaq ya ke ciki ya mishi tsaye a zuciyarshi da wani irin yanayi. A plate ɗaya Ammi ta zubo musu abincin suka ci ita dashi. Nan falo kuma sukai zamansu suna hira.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.3 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 23Alkalamin Kaddara 25 >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 24”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×