Skip to content
Part 17 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Mutane da yawa da kanyi magana kan aure, suna mantawa su yi magana kan nutsuwar da ke tare da shi, da yadda kake jin kamar wani ɓangare ne da baka san baya tare da kai ba ka samu. Yanayin da yake jinshi a satika biyun nan ba zai misaltu ba, kusan komai tare suke yi da Samira, ko fita zai yi sai ya ce ta raka shi. Saidai me, abinda baisan yana da shi bane ya bayyana, wani irin zafin kishi daya saka shi fara addu’ar neman sauƙin shi. 

Ranar da ta kasance safiyar Monday ce, zai koma Kano saboda akwai wani meeting da yake buƙatar bayyanarshi a satin, ranar ne kuma Samira zata koma aiki ita ma. Sai dai me tunda ya tashi yake jin zuciyarshi a jagule, har ɓangaren motsa jiki da ke cikin gidan ya shiga da sassafe ya ɗan motsa jikinshi, bai damu sai ya yi ƙwanji ko wani abuba, yana dai kula da lafiyarshi ne. 

Tunanin zuwa aikin Samira ya ƙi barin kanshi, har sai da ta kula da suna karyawa ta tambayeshi ko lafiya, ɗan ɗaga mata kafaɗa ya yi kawai yana rasa ko me zai ce. 

“Tun jiya shirun ka ya yi yawa…bansan sau nawa zan tambaya kafin ka faɗa min ba, ka daina cewa bakomai saboda nasan akwai wani abu, ina ji a jikina akwai wani abu…” 

Ta ƙarashe da damuwa a muryarta, shirun dai ya sake yi, zai so kanshi da yawa in ya ce ta ajiye aikinta baya so, dama ba da aikin ya aureta bane da sauƙi. Ya rasa meya shiga kanshi haka. Ko Nuri tana aiki da, yasan lokacin da take aiki, fara siyasar Daddy ne ta ajiye, kuma shima tana kasuwanci, tana taya Daddy abubuwa da yawa na ci gaban siyasar shi. Kuma ya sha tunanin tashi matar ta yi don ta dogara da kanta. 

Baisan lokacin da hakan ya canja ba. Yanzun kam baya son Samira kusa da kowanne namiji, yana jin idanuwanta na yawo kan fuskarshi, kamar suna son shiga jikinshi ne zuwa zuciyarshi don su tayata gano abinda yake damun shi. Har ta gaji ta sauke numfashi tana miƙewa, ɗakinsu ta nufa don ta yi shirin fita aiki, don ta ga har tara saura, sati biyu suka bata dama. 

Tana aiki a ma’aikatar da ke kula da siye da siyar da gidaje ne da ke nan garin Abuja, tunda fannin da ta karanta kenan daman. Suna kuma matukar ji da ita don bata da shiririta, itama kuma tana son aikinta sosai. Kaya take ɗaukowa ta ji shigowarshi yana rungometa ta baya, yadda ya kwanta jikinta na sakata riƙe hannunshi kar su faɗi. 

“Kishi ne yake damuna Samee, bana son kowane namiji a kusa da ke.” 

Ware idanuwanta ta yi, da murmushi akan fuskarta ta ce, 

“Baka yarda da ni bane?”

‘Yar dariya ya yi don yasan babu kowa a zuciyarta banda shi, baya jin akwai namiji banda mahaifinta da’ yan uwanta da suka taɓa zama a zuciyarta banda shi. Kuma daga shi ta rufe, hakan kawai na sakashi nishaɗi in ya tuna. 

“Ni kaɗai ne a zuciyarki na sani…”

A wasance ta ce, 

“A taka zuciyar fa? Ni kaɗai ce?”

Dariya ya yi. 

“Ban yarda da wasu a kusa da ke bane kawai. Za su yi ta kallon ki, banaso su kalle ki.” 

Ya ce maimakon amsar tambayar da ta yi mishi, bata damu da rashin amsarta ba, tasan yana sonta ko da yana tunanin baya yi, kishin da yake nunawa akanta ma kawai tabbacin hakan ne. Sake matse ta yayi gam. 

“Kamar karki je aikin nan.”

Ya faɗi maganar, yana jin yadda ta fito daga zuciyarshi, tana son Rafiq fiye da yadda zata iya faɗa, amma ita macece da ‘yancinta yake da muhimmanci a wajenta. Akwai layi a sadaukarwar da zata iya yi wa namiji, ba zata iya barin aikinta ba sai da wani dalili mai ƙarfi. Da kishin shi ta yi rayuwa, da shi take tare har yanzun, sanin a kowane lokaci yana iya haɗuwa da wadda zaiso makamancin son da take mishi kaɗai na sa zuciyarta matsewa. 

Zai iya rayuwa tare da nata kishin shima. 

“Idan na ce bana so ka je Kano zaka fasa?”

Ɗan daƙuna fuska ya yi yana girgiza mata kai, ture shi ta yi tana ɗaukar kayanta zata fice daga ɗakin canza kayan zuwa na baccin su ya riƙota. 

“Raafik mana, kana so in yi latti ko?”

Ta faɗi tana sake ture shi ta fita da sauri, binta yayi yana jin yadda zai yi kewarta in yaje Kano, sun yi wata irin shaƙuwa mai ƙarfi a kwanakin nan da har mamaki take bashi, ita kanta Samira bata ɗauka zata iya sonshi fiye da wanda take yi ba sai yanzun, don har zuciyarta kashedi take mata cewar babu sauran waje, ko ina ya cika da soyayyar Rafik ɗin. 

Kan gado ta ajiye kayanta tana ƙarasawa gaban mudubi ta zauna, tsaye yayi a bayanta tana kallonshi ta cikin mudubin, kwalliyar fuskarta take ɗan gyaggyarawa, tana kallonshi ya ɗauki tissue yana nannadawa a hannunshi, bata gama mamakin me zaiyi da itaba taga ya janyo kujerar da take kai yana juyo da ita kamar bata da nauyin komai, kanta ya dafa ya fara goge kwalliyar da take fuskarta, hannunshi ta rike da sauri. 

“Raafik…”

Ta kira cikin mamaki, kai ya girgiza mata

“Ba zaki office da kwalliya a fuskarki ba.”

Numfashi ta sauke tana sakar mishi hannu, sai da ya gama gogewa yadda yake so tukunna ya tura kujerar yana gyara mata zama. 

“There, all done.”

Ya faɗi yana juyawa kafin ta amsa, kayan da suke ajiye kan gadon, wani material na riga da skirt ya ɗauka yana komawa ɗakin sake kayan, ya daɗe yana neme-neme, gaba ɗaya ya hargitsa kayan, don duk wanda ya ɗauko saiya warware ya ga menene, ya yanayin shape ɗin su yake, kafin ya ɗauko wata doguwar riga da hannu da wuya kawai aka fitar, babu wani shape, da ɗankwalinta. Mayafi ya duba kalar babba yana ajiyewa, sannan ya ɗauko wata lifaya daban ita ma yana fitowa ya ajiye mata kan gadon. 

“Wannan ko wannan… Ki ɗauka ɗaya.”

Kai Samira kawai take iya girgizawa mamakin rikicin Rafiq ɗin na hanata magana. Bata ce komai ba ta zo ta ɗauki lifayar ta wuce shi, don ta ga alama in ta biye mishi latti zata yi, zuwa ta yi tana sakkowa ta fito, sai dai me gani ya yi ta yi kyau, sai yanzun ne yake ganin kyanta da su Faruk kan faɗa mishi tana dashi. 

“Wallahi kina da kyau har yanzun…”

Ya faɗa kamar yana tsammanin da rashin kwalliyar da saka kayan da basu bayyana surarta ba zasu ɓoye kyan nata. Dariya ma ya bata, takowa ta yi inda yake tsaye tana sumbatar shi. 

“Allah ya tsare hanya ya dawo min da kai gida lafiya. Zan yi kewarka sosai…” 

Numfashi ya sauke, yana kallonta ta ɗauki jakarta tana saka takalma da alamun ta gama shiryawa fita kawai zata yi. Saida ya ƙarasa yana rungumeta sosai a jikinshi tukunna ya saketa da fadin, 

“Amin thumma amin. Ki kular min da kanki sosai, sai mun yi waya ko?” 

Kai ta ɗan ɗaga mishi tana ficewa, don bata so ta ga tafiyarshi ma. Ko kaɗan bata son ya yi mata nisa, bata san ya zata fara bacci baya kusa ba yau, tana tsoron kamar da ya tafi zai tabbata aurensu mafarki ne ba gaskiya ba. Yana kallonta ko juyowa bata yi ba ta fice daga ɗakin. Bayajin ta fita daga gidan gaba ɗaya amma har ya ji ya mishi girma, abubuwan da yake buƙata ya ɗauka shima yana tattarawa ya fita shima tunda sai ya biya ta gida yama Nuri sallama tukunna ya wuce dole. 

***** 

Yana shiga gida ya wuce ɓangaren Nuri suka gaisa tana dorawa da, 

“Ya Samira?”

“Ta koma aiki.”

Ya amsa da wani yanayi a muryarshi da yasa Nuri kallon shi cike da alamun tambaya, matsawa yayi sosai kusa da Nuri ɗin yana faɗin, 

“Bansan me ke damuna ba Nuri, don Allah ki min addu’a kar in zamana cikin mazan nan masu mahaukacin kishi…” 

Murmushi Nuri ta yi, kwanciyar hankalin da take gani a fuskarshi da kasancewar Samira matarshi na mata daɗi. 

“Ba laifi bane don ka yi kishin matarka Rafiq.” 

Kai ya girgiza wa Nuri. 

“Yayi yawa, bana son kowanne namiji a kusa da ita, ko ya kalleta, ko ya yi magana da ita, Nuri ina nan zaune wallahi zuciyata na tunanin dawa-dawa ta yi magana da shi a office yanzun nan…na ce ta bar aikinta, ta ɗauka wasa ne, daga zuciyata maganar ta fito.” 

Kallonshi Nuri take yi tana ganin gaskiyar da ke tattare da kalamanshi. Da gaske ne kamar yadda ya faɗa kishin ya yi yawa, ba don babu maza masu irin kishin shi ba, sai don da yawa auren maza irin shi din nada matsala. 

“Ki min addu’a Nuri.”

Kai ta ɗan ɗaga mishi. 

“In sha Allah.”

Numfashi ya sauke yana jin indai da Nuri a kusa da shi kowacce matsala ta rayuwarshi zata zo mishi da sauƙi. 

“Me kuka ci?”

“Baka karya bane?”

Nuri ta tambaya da sauri. Girgiza mata kai ya yi. 

“Na ci abinci, kawai na yi kewar abincin ki ne shi yasa.” 

‘Yar dariya Nuri ta yi, ko da dare jiya ita ya kira a saka abinci da su aka aika musu. Bai ƙi kullum su zo gidan su ci ba, itama ba zata damu ba, amma hakan ba zai zama adalci wa Samira ba, duk yadda kuwa zata yi musu kara ba zata nuna ba. 

“Ko in bari ki dafa min, in tafi da shi wanda zan ci a mota anjima?” 

Yadda ya shagwaɓe fuska na sata kasa ce mishi a’a. 

“Amma next time ka faɗa wa Samira ta dafa maka.” 

Kai ya ɗaga mata yana sake shagwaɓe fuska, ya rasa dokar da ta ce don mutum ya yi aure dole sai abincin matarshi ne zai ci. Shi da son samun shi ne ba zai bar gida ba, zai yi zamanshi tunda akwai part ɗin da za su iya zama ba shi da Samira bama har da yara in suna da, amma Nuri ba zata bari ba. Miƙewa ya yi yana bin bayan Nuri, ita ƙasa ta sauka, shi kuma ya yi ɓangaren Aroob, Fawzan dai baya nan ya sani. 

Bakin kofa ya tsaya yana ƙwanƙwasawa, ya ɗan jima bata amsa ba, wayarta ya kira ya ji tana ringing daga cikin ɗakin, hakan ya tabbatar mishi da bata ciki, don bata da nauyin bacci, sauka ƙasa ya yi tana falon kuwa a zaune da mug a hannunta, da murmushi a fuskarta lokacin da ta ganshi ta ce, 

“Yaya… Ina kwana. Yaushe ka zo? Bansani ba.”

Ƙarasawa ya yi yana karɓar mug ɗin da ke hannunta, bata yi gardama ba ta sakar mishi, green tea ne a ciki take sha, kurɓa ya yi niyyar yi ya bata ya ji ya mishi daɗi, don haka ya samu waje ya zauna yana faɗin, 

“Ban wani daɗe ba, kin tashi lafiya?”

“Alhamdulillah. Anty Samee fa? Me yasa baku zo tare ba?” 

Murmushi yayi da Antyn da ta ɗora wa Samee, ko ya ce har Fawzan, tun daga ɗaurin aurensu basu sake kiran sunanta kai tsaye ba, yanajin daɗin girmanshi da suke gani har haka. 

“Ta je wajen aiki shi yasa, nima Kano zan tafi daga nan In sha Allah…” 

“Kano? Wai… Allah ya tsare hanya. Amma nan zata zo ko? Ita kaɗai a wannan gidan, ni bazan iya ba ai.” 

Dariya Rafiq ɗin ya yi, wayarshi ya danna yana rubuta wa Samira saƙo, 

‘Hey. Kin je office lafiya? Za ki ya kwana ke kaɗai kuwa? Ko in turo miki Aroob?” 

Ya aika mata, don baya son yanke mata hukunci ko ba zata so ba. ‘Yar aikin su bata kwana, ya ce yai wa Nuri magana ta ƙi, daga gidansu take zuwa ta yi mata share-share ta tafi kullum. Daga ita sai mai gadi a gidan, ita take shiga kitchen abinta in suna son cin wani abin. Dawo mishi da amsa ta yi, 

‘Alhamdulillah, har na fara kewarka. In Aroob ɗin ta zo zan ji daɗi sosai, zan biyo in ɗauke ta daga wajen aiki, na manta ban faɗa maka ba ina son zuwa saloon’ 

Tea ɗin shi ya kurɓa kafin ya rubuta. 

‘Saloon? Me za ki yi a saloon?’

‘Zan wanke gashi.’

‘Yar dariya ya yi a fili data sa Aroob kallon shi, harararta ya yi yana faɗin, 

“Bana son sa ido Aroob.”

“Me nace? Banyi magana ba fa.”

Shareta ya yi yana ci gaba da rubuta saƙon shi. 

‘Me zaki wanke a saloon? Gashin nan da bai kai rabin nawa ba, come on Samee ko ni a gida nake wankewa.’ 

‘Karka sake min magana.’

Dariya ya sake yi.

‘Sorry sweetheart. Zan bada kuɗin wankin gashin.’ 

Shiru bata dawo mishi da amsa ba, hakan yasa shi sake tura, 

‘Na fa baki haƙuri.’

‘In aka kore ni daga aiki kai ne, muna meeting.’ 

Da sauri ya aika mata.

‘Da sun taimaka min.’

Ta ɗan sake jimawa kafin ta turo mishi reply, 

‘Da gaske sun fara kula hankalina baya kansu. Allah ya tsare hanya, wannan shi ne maganata ta ƙarshe.’ 

Murmushi yake yi.

‘Ko na ce ina kewarki? Like sosai sosai.’

‘Yaa Rabb Raafik da gaske muna meeting.’

Murmushi yake sosai har haƙoranshi suka fito. Text ɗin ƙarshe ya tura mata da sirri ne a tsakanin su. Nan da nan ta dawo mishi da amsa,

‘Na kashe wayar.’

Aikam da gaske take ta kashe wayar, don daya sake tura mata saƙon bai nuna alamar an karanta ba. Dariya ya yi yana saka wayar a aljihu. 

“So, so, soyayyaaaa…”

Aroob ta fara wata waƙa da ta sa kiris sha yi ya biyo wa Rafiq ta hanci, tari yake yi yana maida numfashi, tare da matse hancin shi da yake jin alamun ruwan shayi a ciki, kafin ya kalli Aroob da ta kwashe da dariya.

“Tashi… Bar wajen nan Aroob”

Dariya take yi sosai.

“Ni me nayi? Shi kenan bazan yi waƙa ba.”

Ganin Rafiq ɗin ya miƙe ne yasa ta tashi babu shiri, dai-dai fitowar Nuri daga kitchen, kallon su ta yi. 

“Rafiq ba zaka zo har gidansu kana daga mata hankali ba.” 

Buɗe baki ya yi yana dafe ƙirjinshi.

“Nuri…”

Ya kira yana wani ƙyafta idanuwa.

“Ni ba don gida bane kenan…”

Girgiza mishi kai Nuri ta yi. 

“Mun yaye ka, ka zo ka kwashe sauran kayanka ma.” 

Komawa Rafiq ya yi ya zauna yana ƙarasa shanye shayin shi. 

“Yaya in kira Anty Samee ta zo ni da Yaya Fawzan mu tayata kwashe kayan?” 

Harararta yake yi. 

“Aroob ba za ki ƙyale ni ba ko?”

Kitchen Nuri ta koma don ta duba girkin ta, Aroob ɗin tana bin bayanta. Komai ta kammala ta haɗa mishi tana sakawa a ƙaramin kwando ta fito mishi da shi. Sai da suka zauna su ukun suna ƙara yin hira, yake fadama Aroob ɗin zata taya Samira kwana har ya dawo, bai bar gidan ba sai wajen sha biyu saura tukunna, tunda ko ya isa Kano babu inda zai je sai washe gari. 

*****

Watansu biyu cif da aure Samira ta fara wani irin laulayi da ke matuƙar wahalar da ita, gashi saboda ƙaratowar zaɓen Daddy, Rafiq bashi da wani wadataccen lokacin da zai kula da ita sosai. Dole Aroob ta koma gidan da zama, aiki ma sai hutun ta ɗauka da babu yadda zata yi, surutu kuwa ta sha shi wajen yayyenta mata, don suna ganin duka yaushe akai auren da har zata fara laulayin ciki. Ko ɗan honeymoon ɗin da ake zuwa basu je ba. 

Bata ce musu komai ba, don maganar wani honeymoon ita ce ta ƙi, sai da Rafiq yai mata magana in tana so su je, wacce kasa ce zai kaita da babanta bai riga yakai ta ba, duk inda take sha’awar zuwa ɗin ta je har ta gaji. Sun bar shi sai lokacin azumi su je Umrah ita da shi, ba sai sun san wannan ba. Yi musu bayani ɓata lokaci ne, rayuwar turawa suke yi abinsu, wadda Samira bata da ra’ayi.

Murnar da Rafiq yayi da jin ciki ne da ita kaɗai inta tuna takan ji sauƙin laulayin da take yi. Ita kanta ba zata misalta yadda take ji a zuciyarta ba, daga ita har shi hannuwansu kan cikin suke kwana, ta cika babban burinta na farko, tare da Rafiq in yara goma ne tana so, tana son duk wani abu da zai ƙara mata kusanci da zuciyarshi, tana kuma ganin yadda maganar cikin kawai yasa hakan ya faru. 

Yauma kamar kullum a ‘yan kwanakin nan, bai shigo gidan ba sai wajen ƙarfe tara, don har sun yi bankwana da Aroob ma, ta kwanta saboda zazzaɓin da ya rufe ta, sai dai baccin yaƙi samuwa, hankalinta bai nutsu ba sai da ta ji shigowarshi. Tana jin yadda yake lalabawa yana tunanin tayie bacci, don ta kashe wutar ɗakin, da fitilar ƙaramar wayarshi yake amfani, ya shiga banɗaki yai wanka yana fitowa ya je ya saka kayan da zai kwanta. 

Duk tana jinshi, har ya hawo kan gadon yana matsowa dab da ita, hannunshi ya zagaya yana ɗorawa kan nata ya haɗa su waje ɗaya tukunna ya ɗora su akan cikinta, yana sumbatar bayan kanta. 

“Sannu da zuwa…”

Ta faɗi dai-dai kunnen shi. 

“Ba bacci kike yi ba ko?”

Murmushi ta yi duk da ba ganinta yake yi ba. 

“Bazan iya bacci ba in ba gani nai ka shigo gida ba.” 

Wannan karon gefen fuskarta ya sumbata.

“Ya kuka wuni? Ya jikin ki?”

“Alhamdulillah, mun wuni lafiya, jikina da sauƙi. Ya ka wuni kai? Ya gajiyar ka?” 

Numfashi ya sauke kafin ya ce, 

“Akwai gajiya sosai, jikina ciwo yake min. Kinga ban samu na kira ku bako? Ina cikin hayaniya tunda muka fita.” 

Hannunshi ta dumtse tana son faɗa mishi ta fahimta. Matsawa ya yi jikinta sosai yana ɗan ɗora fuskarshi kusa da tata, ɗumin jikinta ya wuce misali. 

“Zazzaɓin ne ko? Yarinyar nan na wahalar min da ke.” 

Juyowa ta yi tana fuskantarshi, kusan numfashi daya suke shaƙa. Tunda aka faɗi maganar cikin yake kiran shi da mace, ba kuma ta taɓa mishi gardama ba, mace ko namiji zata yi murna da duk abinda ta samu. Don haka ta ce mishi, 

“Ka ci abinci?”

Kai ya girgiza mata, da yammaci sosai ya samu ya ɗan ci cake da lemo, bacci kawai yake ji, hakan yasa shi ɗorawa da, 

“Bana jin yunwa amma, bacci kawai nake ji.”

“Ba zaka kwanta cikinka bakomai ba.”

“Samee don Allah ki yi haƙuri, Allah na gaji sosai. Ke kin ci abincin?” 

Tashi ta yi zaune tana faɗin, 

“Kasan Tea kawai nake iya sha, ko me zan ci amai nake yi. Kai dai ne za ka ci abinci yanzun.” 

Riƙo hannunta ya yi. 

“Ki bari da safe. Kin ga ba ma ki da lafiya.”

Zame hannunta ta yi, ba zata iya bari ulcer ta kamashi ba, ita zai bari da tashin hankali. Ƙwan ɗakin ta kunna, hasken na sa shi runtsa idanuwan shi, ji yake kamar yasa kuka saboda gajiya. Babu yadda ya iya da rikicin Samira, hannu ta miƙa mishi, dole ya saka nashi ciki yana miƙewa, kitchen suka nufa, ganin wainar shinkafa ya saka shi yin murmushi don yasan aikin Aroob ne, bata gajiya da waina. Da ƙyar Samira ta samu ya ci guda uku, yana yi yana lumshe mata idanuwa a dole bacci yake ji. 

Hannu ma ita ta wanke mishi, suka koma ɗaki, da gaske yake yi ya gaji, yana kwanciya ya yi bacci, ita ta rufe shi ma tunda ba sanyi yake so ba, tana kwanciya a bayanshi tare da riƙe shi kamar wani zai ƙwace mata, a haka har bacci ya ɗauke ta itama. 

***** 

Wannan karon nasara bata tare da su Daddy, domin kuwa sun sha kaye a zaben da aka yi. Hakan ba ƙaramin girgiza Daddy ya yi ba. Sai dai shi mutum ne da rashin nasara ke ƙara wa ƙarfin gwiwar dagewa don ganin ya samu nasarar. Rafiq na ji a jikinshi wata rana har ƙasar gaba ɗaya sai Daddy ya mulka, ba kujerar mataimaki ba, ta shugaban ma duka zai hau. Haka suka ci gaba da harkoki ana damawa da su ta fagen siyasa da kuma kasuwanci da yake da rassa da dama. 

Rafiq kuwa gama siyasar yasa shi samun wadataccen lokacinl tare da matar shi, duk sa bata samu sauƙin laulayin ta ba sai da cikin ta ya yi wata huɗu, ko lokacin Aroob bata bar gidan ba. Samira da Rafiq ɗin suka roƙi Nuri da abarta har ta haihu, don tana bala’in ɗebe mata kaɗaici, ba don Rafiq ya so ba ta koma aikinta, kuma don likita ya ce motsa jikin na da muhimmanci a wajenta. Duk da haka zuciyar Rafiq ɗin ta ƙi samun nutsuwa, sai ya yi mata kira nawa a rana, bata dai gajiyar da kanta da yarinyarshi ba ko? Me take yi? Ta ci abinci? Ya take jin jikinta? 

Haka ma Aroob, kulawa take samu da takan rasa kalarsu, kasancewar Aroob a gidan yasa Fawzan yana yawan zuwa shima, kulawa take samu sosai wajen su. Musamman yanzun da cikinta yake cikin wata na tara, gaba ɗaya komai baya mata daɗi, da ƙyar take zama, in zata tashi sai Aroob ko Rafiq in yana nan sun taimaka mata, wani irin girma cikin yayi kamar yara biyu ne a ciki ba ɗaya ba. Babu yadda Rafiq bai yi ba tunda aka yanke mata lokacin haihuwa, su tafi ƙasar waje yafi yarda da likitocin su ta ƙi. 

Asibitin da take ma ta yarda da ƙwarewarsu, kuma an tabbatar musu lafiyar ta ƙalau ita da babynta, bata ga menene abin ɗaga hankali ba, yadda aka faɗa yau sauran sati ɗaya ko fiye da haka ma, kafin haihuwarta. Zaune take hankalinta a kwance kan kafet tana shan lemon zaƙi, Aroob kuma na kan kujera a zaune suna kallon wani fim ɗin indiya suna hira. 

“Haba Anty na faɗa miki shi yake kashe matan nan.” 

Girgiza kai Samira ta yi. 

“Nifa na kasa yarda ne har yanzun…”

Cewar Samira, buɗe baki Aroob ta yi zata yi magana yadda ta ga Samira ta runtsa idanuwanta yasa ta tattara hankalinta kanta da faɗin, 

“Anty? Lafiya dai ko?”

Kai Samira ta fara ɗaga mata, kafin ta ji wani irin ciwo kamar ƙashin bayanta ya karye, azabar na sata faɗin, 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Ba shiri Aroob ta sakko daga kan kujerar tana dafa Samira 

“Anty… Anty… Ko dai naƙudar ce?”

Wani irin numfashi Samira take fitarwa, tunda take a duniya bata taɓa tunanin akwai azaba irin wannan ba, ta rasa asalin inda yake mata ciwo, amma tana da tabbacin babu sauran ƙashin da yake dai-dai a gadon bayanta, duka sun karye. Ganin zufar da take yi yasa Aroob ɗaukar waya tana kiran lambar Rafiq. Ɗagawa ya yi da faɗin, 

“Aroob? Yadai? Ina hanyar gida.”

“Yaya to ka yi sauri don Allah, ina jin Anty Samira fa naƙuda take yi.” 

Bata ji amsar da ya bata ba, ta sauke wayar saboda wani riƙo da Samirar ta yi wa hannun Aroob ɗin kamar zata tsaga mata ƙashi. Da ƙyar ta samu ta ƙwace hannunta tana miƙewa ta koma gefe tana mata sannu tana murza hannunta. Gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi. Samira kuwa jin kamar wani abu na fitowa daga jikinta yasa ta dafa ƙasa tana samu da ƙyar ta miƙe tana hawa kan kujera. Numfashinta har sama-sama take jin yana yi saboda azaba.

Don ma sunan Allah kawai take kira da duk wata addu’a da zata zo bakinta. Aroob na shirin sake kiran Rafiq ya shigo gidan a rikice, kan Samira yayi yana riƙo hannuwanta. 

“Innalillahi…. Aroob kira Nuri, sannu, sannu kin ji.” 

Rafiq yake faɗi, zuciyarshi banda dokawa babu abinda take yi, hanjinshi sai yamutsawa suke saboda tashin hankali, yana jin yadda jikinshi ke kyarma, so yake ya kama Samira ya miƙar da ita su tafi asibiti. Yana jin Aroob na faɗa wa Nuri. 

“Samee tashi mu tafi asibiti.”

Kai take ɗaga wa Rafiq ɗin, tana sake riƙe hannuwanshi da duk wani ƙarfi da take da shi, sauƙi kawai take nema ko ya yake, miƙewa take shirin yi, nishin da ta yi yasa ta jin da gaske wani abu taho mata yake. 

“Raafik… Ba zan iya ba… Fitowa zaiyi”

Cikin tashin hankali Rafiq ke kallonta

“Don Allah ki rufa min asiri ki tashi mu tafi asibiti, menene zai fito?” 

“Yaron mana!”

Ta faɗi a tsawace tana jin kamar ta rufe shi da duka saboda surutun da yake yi mata a saman kai, azaba ta isheta, in fitowa zaiyi ai gara ya fito ko zata huta. Kai kawai Rafiq yake girgiza mata yana ƙoƙarin miƙar da ita, fisgoshi ta yi tana riƙe hannunshi sosai. 

“Ka duba yaron ya taho…Raafik… Innalillahi wa inna ilaihi raji’un…” 

Samira ke faɗi cikin ƙarajin azabar da take ji, ƙafafuwan shi ya ji sun yi sanyi, bai taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba, wata irin kimar Nuri ke ƙara shigarshi, in haka ake haihuwa shi kam daga wannan sun haƙura, ba zai iya sake saka ‘yar mutane cikin wannan tashin hankalin ba. Aroob kuwa tana tsaye tana kallon su, a zuciyarta ta gama yanke hukuncin yadda zata bi su ai mata karo-karon yara, don wannan wahalar kam bada ita za’a yi ta ba. Tsugunnawa ya yi yana leƙawa ya ga ko da gaske take babyn ne ya taho, dagowa yayi babu shiri. 

Kan da ya gani, yanajin yadda gudun zuciyarshi ya ƙaru, kafin ya soma jinshi sama-sama kamar yana yawo akan iska, Aroob ya ji tana faɗin, 

“Yayaaaa…”

Da ƙarfi , kafin komai ya ɗauke mishi, wani irin duhu na mamaye duniyarshi gabaki daya.

***** 

Bai san iya lokacin daya ɗauka a haka ba, sama-sama yake jin maganganun su Nuri, muryar Fawzan na faɗin, 

“Wai shi Yayan ya akayi ya suma?”

“Wallahi bansani ba, ina shigowa nima a sume na same shi, sai Aroob na faman kuka, Allah ya taimaka ina gidan Haj. Ramatu ne fa, da ta ji naƙuda ce muka taho tare, ita ta yi wa Samira komai ma harta sauka lafiya, tukunna muka yo asibiti gaba ɗaya.”

Yake jin muryar Nuri na ma Fawzan bayani, duk da bai gane sauran ba, hankalinshi ya tsayane kan jin Samira ta sauka lafiya, hakan na nufin ta haihu. Yana da baby kenan, buɗe idanuwanshi ya yi daga yanayin ɗakin ya fahimci a asibiti yake, miƙewa zaune ya yi yana ƙarasa buɗe idanuwanshi gaba daya. 

“Nuri ina Samee?”

Murmushi Nuri tayi tana faɗin, 

“Tana hutawa ne, bacci take yi ta haihu lafiya.” 

Murmushi yake yi shima, idanuwanshi cike da farin ciki tare da kunya. So yake ya tambayeta babyn fa, amma ya tsinci kanshi da kasawa. 

“Mace ta haifa…”

Wani irin tsallen murna zuciyar Rafiq take yi, babu shiri ya sauko daga kan gadon yana jin sanyin tile ɗin na ratsa tafukan ƙafafuwan shi, don bashi da takalmi. Ganin ya kasa magana yasa Nuri faɗin, 

“Muje kagansu…”

Tare suka fita daga ɗakin su ukun suna nufar inda Samira take, bakin ƙofa Nuri da Fawzan suka yi zamansu nan kan kujerar da ke wajen, shi kuma ya shiga ciki, tun daga nesa ya hango Samira riƙe da babyn, yanayin su kawai na saka numfashin shi wani irin tsai-tsaiyawa saboda farin ciki. Aroob da ke tsaye kusa da Samira ta rugo da gudu tana ruƙunƙume shi.

“Yaya ka samu yarinya…”

Take faɗi muryarta na karyewa, shi ma riƙe ta ya yi gam yana kasa magana saboda wani abu da ya yi tsaye a maƙoshin shi. Sakin shi tayi tana faɗin, 

“Tana da kyau sosai, ka je ka ganta…za mu yi maganar sumanka anjima…” 

Tana ƙarasa maganar ta sake shi tana raɓawa ta wuce, a hankali yake takawa yana nufar inda suke, sanyin tile ɗin yake ji sosai, amma a karo na farko bai damu da rashin takalmin shi ba, wani abu mai muhimmanci na faruwa da shi a cikin ɗakin da ya fi wannan muhimmanci, Samira ma da ƙyar ta iya raba idanuwanta daga kan yarinyar tana mayar dasu kan Rafiq da ta ga ya ƙi sauri ya ƙaraso. 

Hannu ta miƙa mishi, alamar ya ƙarasa, da sauri kuwa ya ƙarasa ɗin yana riƙe hannunta ta ja shi ya zauna kusa da ita. 

“Sannu da aiki, sannu…”

Ya samu kanshi da faɗa, kai take jinjina mishi idanuwanta cike taf da hawaye, babu wanda zai iya fahimtar yanayin da take ji sai mahaifiya, data san zafin naƙuda ta kuma san yadda riƙe yaronka na farko a duniya yake, farin cikin abu ne da ba zai taɓa misaltuwa ba. Miƙa wa Rafiq yarinyar ta yi, hannunshi na kyarma da hamdala a bakinshi ya karɓe ta. Yana sauke idanuwanshi a kanta, yana jin yadda daga kallo ɗaya ƙauna marar misaltuwa ta shiga tsakanin su. 

Ƙauna daban da wadda yake mata lokacin da take cikin Samira, yana tabbatar da duka duniyarshi ta tsayane akan yarinyar da take hannunshi, yana jin yada ƙaunarta ba zata rabu da kowacce mace ba, yana jin ɓangaren zuciyarshi da zai zama nata har abada. Ɗagota ya yi sosai yana soma karanta mata kiran Sallah a kunnenta, kafin ya mata huɗuba da Hafsatu, sunan Nurin shi. Ya kasa daina kallon ta, yana ƙara jin imani na shigar shi da ganin tsantsar ikon Allah akanta. 

Kallon Samira ya yi yana rasa kalar godiyar da zai mata, yana jin yadda babu wani abu da zai iya bata a duniya, don ta gama bashi dukkan wani farin ciki, ta gama yi mishi komai, ta bashi kyautar da har ya mutu ba zai taɓa biyanta ba, ko sonta ta yi yana jin yadda yai kaɗan akan kyautar da ta yi mishi. Yana kuma ƙara mamakin mazajen da ke wulaƙanta matansu. Ya ga yadda naƙuda take, ya ga tashin hankalin da baya jin zai iya ɗauka. 

Yaga girman abinda Samira ta yi mishi, yadda duka rayuwarta ta canza saboda shi, ɗaukar cikin nan wata tara kawai aka barka da shi ba ƙaramin aiki bane ba, ballantana naƙuda, da har ya mutu ba zai manta tashin hankalin da ya gani ba, tunawa kawai yanzun na saka cikinshi yamutsawa da sabon tashin hankali. Kallon Samira yake da wani yanayi cike da idanuwanshi.

“Banda kalamai Samee, banda su wallahi, me zance miki? Sannu? Na gode? Babu kalaman da za su yi ma kyautar nan adalci…babu su.” 

Ya ƙarasa yana sake kallon yarinyar da ke hannunshi kafin ya matsa sosai kusa da Samira ɗin, yana saka yarinyar a tsakanin su, yana son ta ƙara ganin ikon Allah, ta ga yadda yarinyar nan ta fito daga jikinta, ta ga dalilin da zai sa ba zai taɓa iya biyanta ba har abada. 

“Daga jikin ki ta fito…”

Ya faɗa muryarshi cike da abubuwa da dama, farin ciki, mamaki, ƙarin imani da wasu yanayoyi da basu da kalamai. 

“Daga jikin mu… Ni da kai.”

Ta gyara mishi, kai ya jinjina mata, yana riƙota da ɗayan hannunshi, sosai ta kwanta a jikinshi, idanuwan su duka kafe kan yarinyar da ke bacci hankalinta kwance a jikin Rafiq ɗin , kallon yarinyar yake, da duk bugun da zuciyarshi zata yi da yadda yake jin ƙaunar ta na ƙaruwa, kafin ya sauke numfashi mai nauyi yana furta, 

“Ina sonki Samira, ina sonki, na gode…”

Yanajin yadda ta sake riƙe shi gam, kamar zai gudu, yadda take fitar da numfashi ya tabbatar mishi da kuka take yk, sake gyara zama ya yi yadda zai riƙe ta shima, yana jin yadda yarinyar su ta ƙara girman alaƙar da ke tsakanin su, yadda zuciyarta ta sa nasu zuciyoyin suka ƙara haɗewa. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 16Alkalamin Kaddara 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×