Skip to content
Part 46 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Da ƙyar ya lalubo wayar shi da ke ringing daga aljihu, ko idanuwan shi bai buɗe ba saboda bacci yake mai ƙarfin gaske, a haka ya danna ya kara a kunnen shi yana yin shiru, kafin daga dayan ɓangaren ya ji an ce, 

“Hello Yayaa…”

Sake runtsa idanuwan shi Altaaf ya yi. 

“Aslam bacci nake yi.”

“Ka fito mu kama hanya, sai ka yi baccin a mota.” 

Tun kafin Aslam ɗin ya gama maganar Altaaf yake girgiza mishi kai, sosai bacci yake ji, baya son ko idanuwan shi ya buɗe ballantana ya sauko daga kan kujerar har ya fita waje. Shi kaɗai ne a gidan, don sun yi sallama da su Wadata da matar shi, za su fita unguwa, shi kaɗai suka bari a gidan ya kwanta yana bacci. 

“Aslam don Allah mana. Banda lafiya fa.”

Altaaf ya ƙarashe maganar yana ƙara sauke murya. 

“Na sani, ka fito mu tafi, Allah idan na juya sai dai ka hau motar haya.” 

Aslam bai jira amsar Altaaf ɗin ba ya kashe wayar daga ɓangaren shi. Dole Altaaf ya sauke wayar daga kunnen shi, yana buɗe idanuwan shi a hankali, da ƙyar ya ja jikin shi ya miƙe, wayar ya ɗauka yana miƙewa tare da ƙarasawa inda takalman shi suke ya zira a ƙafafuwan shi yana kama hanyar fita daga gidan, ƙofar ya ja tukunna ya taka har bakin gate don bai ga alamar motar Aslam a cikin harabar gidan ba. Ko maigadin Wadata da ke mishi Allah ya tsare bai amsa ba saboda baccin da yake ji. 

Yana fita waje ya ga motar Aslam ɗin a ajiye, ba tun yanzun ya tsani 406 ɗin nan ta Aslam ba, duk ta guggurje, shi da kanshi ya so ya sake mishi mota amma ya ce baya so, wannan ɗin dai ta ishe shi, Ammi ma tun tana magana har ta gaji ta ƙyale shi. Ranshi a jagule ya ƙarasa yana kama murfin motar ya buɗe ya shiga tukunna ya ja ya rufe.

“Duk motocin da ke gidan sai a wannan gwangwanin za ka zo ɗaukata?” 

Kallon shi Aslam yayi kawai yana mayar da hankalin shi kan tuƙin da yake yi. Ba zai ce baya jin haushin Altaaf ɗin ba tun jiya da sukai magana da Barrah. Ranshi in yayi dubu ya ɓaci, haka ya dinga juye-juye duk daren jiya da tunanin Nuwaira a ranshi. Shi kam Altaaf yanayin yadda Aslam ɗin yake fisgar motar yake kallo, in suna tafiya har sai ya zage shi kafin ya ɗan ƙara gudun motar, amma yau tunda ya ɗauki hanya gudu yake da su na tashin hankali, ga yadda yake riƙe da steering wheel ɗin kamar zai karya shi. 

“Aslam…”

Altaaf ya kira muryarshi can ƙasa, yana neman baccin da yake ji yana rasawa, a fitowar sirrikan da ya ɓoye, babu wanda yake ji sai Aslam, babu tangarɗar alaƙar da yake tsoron ta samu matsala sai tashi da Aslam, ba zai iya ɗauka ba, sam ba zai iya ɗaukar wani abu ya samu alaƙar da ke tsakanin shi da Aslam ɗin ba. Ba ƙaunar shi kawai yake yi ba, akwai girman shi da yake gani na ban mamaki, akan Aslam ya fara sanin jin kunyar munanan abubuwan da yake aikatawa, girman da Aslam yake bashi na daban ne, ko kaɗan baya son rasa hakan. 

“Aslam…”

Ya sake kira a karo na biyu, amma Aslam bai ko nuna alamar ya ji me ya faɗa ba ballantana ya nuna alamar amsawa. 

“Don Allah Aslam…”

Gefen titi Aslam ya samu yanayin parking ɗin motar, tukunna ya gyara zaman shi ya kalli Altaaf ɗin. 

“Ina jinka…”

Ya faɗi idanuwan shi cikin na Altaaf da ya rasa inda zaisa kan shi ya samu sauƙi, ji yake iskar da ke cikin motar ta musu kaɗan su biyun. Numfashi ya mayar. 

“Ka tsaneni na sani, banda kuma wani bayanin da zai ma abinda na aikata adalci, amma bayana ne wannan, abu ne da bazan iya komawa in sake ba Aslam, wallahi zan bayar da komai dana mallaka idan zan samu damar gyara kuskure ɗaya daga cikin tarin wanda na yi, amma rayuwa bata aiki a haka… Dama ɗaya kake samu lokaci zuwa lokaci, duk idan ta wuce bata dawowa… Ka yi komai, ka min ihu, ka yi faɗa da ni duk zan ɗauka, amma bazan iya ɗaukar tsanarka ba, shi ne abinda bazan iya ba…” 

Wannan karon Aslam ne ya sauke numfashin da baisan yana riƙe da shi ba, ƙirjin shi zafi yake tun jiya. 

“Me kake tunani Yaya? Me yasa zaka so kanka da yawa haka? Ba ka tunanin Barrah? Ba ka tunanin ayi mata abinda ka yi?” 

Wani abu Altaaf ya ji ya taso mishi daga ɗan yatsan ƙafarshi zuwa tsakiyar kanshi yana saka shi ganin wani haske ya gilma ta cikin idanuwan shi. 

“Zan yi kisa Aslam, zan kashe ko waye ya taɓa min Barrah, wallahi zan kashe ko waye…” 

Altaaf ya furta yana jin kalaman har cikin ƙasusuwan shi, tunanin wani zai taɓa mishi Barrah yadda ya taɓa Nuwaira na sa zuciyarshi rarrabuwa wajaje da dama. Yana da tabbacin mutuwa zai yi. Dariya Aslam yayi da bata da alaƙa da nishaɗi. 

“Yayaa…. Yayaaa”

Ya kira yana rasa da me zai fassara ma Altaaf ɗin ya gane, kafin Altaaf ya ji kamar an doka mishi guduma a tsakiyar kai. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Ya faɗi wani abu na kullewa a cikin shi, ba’a taɓa Barrah ba, tunanin hakan kawai na sa numfashin da yake yi shirin ɗaukewa, baisan me su Nuwaira suka ji ba, baisan me ita kanta tajie ba, jikin shi yake ji yana ɓari har cikin tsokar shi. 

“Abinda nake cewa kenan Yaya… Ɓarnar da kai mai girma ce…” 

Aslam ɗin ya faɗi a sanyaye, yanayin Altaaf ɗin na taɓa shi. 

“Ya zanyi? Ta ina zan fara gyara wannan ɓarnar? Aslam ka taimaka min don Allah, bansan ya zan yi ba, wallahi bansani ba.” 

Kai Aslam ɗin yake jinjina mishi, tun jiya yake tunanin yadda wanna ɓarnar zata gyaru, hanya ɗaya yake da ita. 

“Yaya karka rabata da yaran da ta saba da su, rashin adalcin zai mata yawa. Ka aure ta.” 

Runtsa idanuwan shi Altaaf yayi yana buɗe su, yayi hakan yafi a ƙirga, kalaman uku na amsawa a ko ina na jikin shi ‘Ka aure ta’. Dube-dube yake cikin motar, daga gaba har ya juya baya yana hango robar ruwa, jikin shi na ɓari ya ƙarasa ya ɗauka, bai damu da zafin da ruwan ya ɗauka ba, buɗewa yayi yana ɗaga robar ya sha, amma baiji ya dawo dai-dai ba, iska bata kai mishi inda ya kamata, da sauri ya buɗe murfin motar yana ɗaga robar ya sheƙa ruwan daga kanshi zuwa fuskar shi yana wankawa, bakin shi ya buɗe yana jan iska ta ciki saboda tashin hankali. 

Sama-sama yake jin Aslam da ya fita daga motar yana zagayowa ɓangaren shi. Yasan magana yake, amma can sama yake jin shi. 

“Yayaaa… Ka yi numfashi.”

Aslam ɗin yake faɗi, kai kawai Altaaf yake ɗaga mishi, abinda yake ƙoƙarin yi kenan tun ɗazun, amma abin ya gagara, iskar ta mishi kaɗan sosai, ya kai minti biyar a hakan kafin ya fara jin kanshi da ya ɗauki ɗumi yana washewa a hankali. Ƙafafuwan shi ya ja ya mayar cikin motar, ya ja murfin ya rufe, tukunna ya jingina kanshi da gaban motar yana mayar da numfashi a hankali, yana jin Aslam ya buɗe ya shigo, wasu mintina biyar ɗin ya sake bashi kafin ya ce, 

“Don na ce ka aure ta ne ka samu panic attack Yaya?” 

Cikin wani sabon tashin hankalin Altaaf ya ɗago, baisan ta inda zai fara yi ma Aslam bayani ya fahimta ba, ta yaya zai auri Nuwaira? Ta yaya zai fara zaman aure da ita? Yana da tabbacin fuskar shi ce ƙarshen abinda take son gani duk safiya. Idan shi ne a matsayinta baya jin zai iya zama da shi. Tunanin hakan kawai na sa amai taso mishi. Kai yake girgiza ma Aslam. 

“Majida fa?”

Ya buƙata yana rasa wani dalilin da zai yi amfani dashi daya fita. 

“Zata fahimta… Zata fahimci abinda ya kamata ka yi kenan.” 

Kai Altaaf ya sake girgizawa.

“Bazan iya ba, wallahi bazan iya aurenta ba, banda ƙarfin zuciyar da zan mata adalci.” 

Kallon da Aslam yake mishi na saka shi ɗorawa da, 

“Ko babu Majida bazan iya aurenta ba. Ni matsoraci ne, bazan iya jure zama da ita a ƙarƙashin rufi ɗaya ba. Zan kuma maka ƙarya idan na ce maka zan bar mata yaran nan…” 

Numfashi Aslam ya ja yana fitarwa. 

“Yayaa…”

“Don Allah Aslam, indai abinda za ka ce in aure ta ne ko in bar mata yaran ba zai yi aiki ba. Zuciyata zata fara tsayawa kafin in daina ƙoƙarin karbɓr yarana.” 

Mukullin mota Aslam ya murza tare da faɗin, 

“Kai ne babban marar adalcin da na taɓa cin karo da shi Yaya. In ba za ka aure ta ba ni zan aure ta, ta cancanci farin ciki ko ya yake a rayuwar ta.”

Aslam ya ƙarashe yana kunna radio ɗin motar tare da ƙure maganar, tukunna ya ja motar. Altaaf kam sautin maganganun Aslam ɗin sun fi mishi ƙara akan hayaniyar radio ɗin da ya kunna. Gyara zama yayi a cikin kujerar yana rufe idanuwan shi. Addu’a yake don yasan Allah ne kawai zai taimaka mishi wannan karon, komai ya riga da ya jagule. 

***** 

Hannu Altaaf yasa yana kashe Radio ɗin da Aslam ya kunna suna shiga garin Kano kafin ya ce, 

“Ka sauke ni a gida na…”

Don ya gaji, sosai gajiya yake ji, ga kewar Majida da ta danne shi. Har kofar gida kuwa Aslam ya kaishi yana jan motar ya tsaya ba tare da ya kashe ba, kan shi hayaƙi yake yi yau, Altaaf ɗin ya kula, duk da bai taɓa mishi rashin kunya ba, yana jin a jikin shi kuskure kaɗan zai sa ya fara yau. Ba da shi za’a yi wannan zubar da girman ba, don haka ya buɗe motar yana fita ba tare da ya ce komai ba. Tura ƙofar shiga yayi, yana ɗaga ma maigadi da ya gaishe da shi hannu kawai ya taka zuwa cikin gidan sosai. Tsaye yayi a bakin ƙofar yana jan wani numfashi ya fitar da shi kafin ya buɗe ƙofar, idan wuƙa Majida zata saka ta yanka shi yau kam babu abinda zai fitar da shi daga gidan nan baisan ya matsayin zaman su yake ba. 

“Assalamu alaikum…”

Ya faɗi muryar shi can ƙasan maƙoshi yana ɗorawa da, 

“Majee…”

Yanayin sautin da sunan ya fito da shi bai yi zaton zata ji shi ba, don haka bai sa ran fitowar ta ba, sauran ƙarfin da ya rage mishi yake tattarowa yana so ya sake kiran ta, kafin ya ganta ta fito, zuciyar shi tai wata irin dokawa, doguwar riga ce a jikinta ta atamfa, ta mishi kyau da yake ji har zuciyarshi na matsewa, duk da babu kwalliya a fuskarta, idanuwanta sun mishi zuru-zuru, ta rame da wani yanayi da yai mishi tsaye a maƙoshi yana saka shi sake kiran sunan ta. 

“Majee…”

Numfashi Majida ta sauke da batasan tana riƙe da shi ba, tana ɗaki tana neman inda ta jefa wayarta, don tun ranar da ta haɗa mishi kayan shi ta saka ta a silent yadda ko ya kira ba zata ji ba ballantana ta yi tunanin ɗagawa, ta san zuciyarta a kanshi bata da wani ƙarfi, son da take mishi bana wasa ba ne ba, kwana ɗaya tsakani zuciyarta ta fara bata dalilin da ya kamata ta duba ta yafe mishi. Yau kam tunda ta tashi take kewarshi har ƙasan zuciyarta, tasan ya kirata har ya gaji, gaba ɗaya batasan inda ta ajiye wayar ba. Tana kuma jin nauyin ta je gidansu, har addu’a ta yi da tai sallah, Allah ya sa ya zo, yanzun ma wayar take nema ta ji kamar sallamar shi, kafin daga baya ta ji ya kira sunan ta, don ƙofar a buɗe take da bata jiyo shi ba. 

Ƙwaƙwalwar ta na faɗa mata kawai kewar shi ce ta sa kunnuwanta suka fara mata jiye-jiye, amma sam zuciyarta ta ƙi aminta sai da ta tako ta fito, shi ɗin ne kuwa, yana tsaye ya zuba mata idanuwan shi da suke rikita mata lissafi, sai ta ga yayi mata duhu, ga rama da damuwa kwance a kyakkyawar fuskar shi, ba zata manta ba, tun ranar data fara ganin shi kyawun shi ya zauna mata. Bayan zuciyarta ta fara doka mishi duk idan yai wanka zai fita zuciyarta na rawa, kar wata ta sauke idanuwanta akan mijinta. So take ta taka ƙafafuwanta zuwa inda yake, ta riƙo hannuwan shi cikin nata, ta fara tabbatar da shi ɗin ne, kafin ta kwanta a jikin shi ta bari ƙamshin shi ya cika mata hanci, ɗumin shi yai filling mata wajajen da kewar shi ta bari. 

“Altaaf…”

Ta kira tana addu’ar ya ji yadda take kewar shi, kamar hakan yake jira ya ƙarasa takawa yana haɗe tazarar da ke tsakanin su, hannuwan shi yasa ya tallabi fuskarta, da sauri ta ɗora nata hannuwan kan nashi tana lumshe idanuwanta tare da sauke wani irin numfashi mai nauyin gaske, iska ya hura mata cikin fuska, hakan na sa ta buɗe idanuwanta babu shiri, kai Altaaf ya girgiza mata, baya son ko motsin kirki yayi ballantana kuma ya motsa laɓɓanshi yai magana, yana son jin fuskarta cikin hannuwan shi na wani lokaci, kasalar da yake ji ta sa shi haɗa goshin shi da nata, har lokacin fuskarta na cikin hannuwan shi, nata hannuwan na saman nashi. 

“Nayi kewar ki, sosai, don Allah karki raba ni da ke, ko ba za ki iya yafe min ba karki ra bani da ke Majee, zan jure komai indai kina tare da ni…” 

Ya tsinci kan shi da faɗi, muryar shi a dakushe da yanayin da yake ji, hannun shi ta sauke daga fuskarta, yana shirin mayarwa ya ji ta zagaya nata tana riƙo shi jikinta, wata irin ajiyar zuciya ya sauke, yana ƙara riƙe ta, jin ɗumin hawayenta kan kafaɗarshi.

“Bansan soyayyarka taman illa haka ba sai a kwanakin nan…” 

Cewar Majida, hawayenta na ci gaba da zuba. 

“Mi za mu yi yanzun? Yaran fa?”

Sake riƙeta yake yi kamar zai mayar da ita cikin shi, yanajin kamar in ya saketa zata kubce mishi ne. 

“Zan karɓo su, sai su zauna tare da Ammi.”

Ya fadi, yana rasa daga inda maganar ta fito, ba zai takurata ta riƙe mishi yara ba, duk da zai so hakan, amma da gidan Ammi ɗin, da nan gidan shi duk ɗaya ne. Ji yai tana ƙoƙarin zamewa daga riƙon da yai mata, da sauri ya sake riƙe ta, amma ture shi ta yi tana sa hannu ta share hawayen fuskarta, muryarta a kausashe ta ce, 

“Mi kake nihi da zasu zauna wurin Ammi?”

Da ban haƙuri a fuskar shi ya amsata da, 

“Bana so in takura ki, bana so in shiga rayuwarki fiye da yadda nayi, bazan yafewa kaina ba idan na takura ki Majida…” 

Wani murmushi ta yi da ba shi da alaƙa da nishaɗi. 

“Riƙe ma yaran ne takura? Bansan ko na yahe maka ba, zan ma ƙarya in na ce banjin zahi har ƙasan raina, amma su yaran miye laihinsu? In akwai wanda aka shiga rayuwa su ne wallahi, ci gaba da zama da kai zaɓina ne, amma su babu wanda ya basu zaɓin nan. Karka sake man zaton za ni takura don na riƙe su, sai dai in ba ka yarda za ni…” 

Hannu ya kai yana rufe mata baki tare da girgiza mata kai, sake riƙo ta yai jikin shi yana furta, 

“Na gode…”

Kafin ya saketa yana kama hannunta zuwa kan kujera, shi ya fara zama kafin ya nuna mata gefenshi, zama ta yi itama tana jingina da jikin shi, hannunta ya riƙe cikin nashi yana lumshe idanuwan shi, dai-daito yake ji ta wurare da dama, can ƙasan zuciyarshi hamdala yake ta saukewa tare da sake neman yafiyar Ubangiji, don yasan Rahmar Allah ce kawai take binshi ba don kyawun halayen shi ba, sai don ƙaunar da ke tsakanin Allah da bayin Shi. Majida ma sake gyara zama ta yi a jikin shi, tasan shi, in yana cikin yanayi haka, baya son magana, kawai so yake ya ji ta a jikin shi, itama yau ɗin bata jin zata iya magana. 

Ta faɗi duk abinda zata faɗa cikin Sujud ɗinta, banda mahaifiyarta batai ƙudirin sanar da kowa sirrinsu ba. Ta roƙi Allah akan tabbatar alkhairi a sauran rayuwar aurenta, bata da tabbaci akan asalin lokacin da zata daina jin zafin da take ji a zuciyarta kan rayuwar Altaaf ɗin ta baya, amma tana da tabbas akan amsuwar addu’arta don ta yi ta cike da yaƙini da yarda mai girma. Ba zata bari abinda ya riga ya wuce ya taɓa rayuwarta da yanzun take faruwa ba. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 45Alkalamin Kaddara 47 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×