Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Amnah by Zainab Muhammad

“Amnah kar kimin haka dan Allah ki taimakamin ina cikin wani hali.”

Wani shu’umin murmushi Amnah ta yi mai rikita zuciyar wan da akai wa kafin Ta ce, “Alhaji kenan ka manta wace Amnah kenan? To idan ka manta bari na tuna maka ‘Amnah ce baki mai maice sai dai sabo’, Ka fahimta?”

Ta ƙarasa faɗa tana ɗaga masa gira.

Cikin hawaye Alhaji Yace,

“Amnah na san da wannan amma ni yan zu ina cikin wani hali ki taimakamin.”

Ya faɗa yana haɗe hannayansa duka biyun alamar roƙo.

Sunkuyawa Amnah ta yi ta ɗauki jakarta kafin ta ɗau key ɗin motarta tai hanyar barin ɗakin, har takai bakin ƙofa sai kuma ta tsaya, kafin ta ce,

“Kafin na isa gida naji alert awayata, idan ba haka ba kuwa…”

Tai kwafa kafin ta fice daga ɗakin.

Shikwa Alhaji zagi ya shiga surfawa Amnah yana cewa ƴar bariki ba abar riƙo ba, kafin bacci wahalalle ya kwasheshi.

A firgice ya farka sakamakon tunawa da ya yi da abinda Amnah ta faɗa masa kafin ta fita, wayarsa ya ɗauka ya tura mata kuɗi naira dubu ɗari 200 biyu. Kafin ya tashi ya kimtsa ya fice daga gidan.

*****

A ɓangaran Amnah kuwa koda ta fita daga gidan Alhaji ba gida tai ba, wayarta ta ɗauka ta danna wasu numbobi tai waya kafin ta shiga motarta ta bata huta.

Star hotel ta nufa kai tsaye, koda isarta nan ma’aikatan wajan suka shiga gaisheta domin sun saba da ita tana yawan ziyartar hotal ɗin.

Kai tsaye ɗaki mai number 10 ta nufa knocking tayi, batai minti ɗaya cikakke ba, sai ga wani haɗaɗɗan matashi kyakykyawa fari tas kamar balarabe ya fito. Buɗe mata ya yi ta shiga kafin ya maida ƙofar ya rufe.

Bakin gado ta samu ta zauna tare da aje jakarta a kusa da ita, dama ba wani mayafi a jikinta. Kusa da ita ya zauna kafin, ya ce, “Babyna kinyi kyau fa.”

Yatsina fuska Amnah tayi kafin ta ce,

“Nifa yunwa nake ji Taufiq.”

Da sauri ya mike yana cewa, “Ok bari nasa a kawo miki.”

Wayar tarho ɗin dake ɗakin ya ɗanna lambobi, bayan an ɗaga yai musu bayanin abinda za a kawo.

Bayan ƴan mintina ka ɗan sai ga shi ma’aikacin wajan ya kawo.

A baki Taufiq ya dinga bawa Amnah abincin har ta ƙoshi.

Bayan ta gama cin abincinne ta ɗauki wayarta nan taga kuɗin da Alhaji ya turo mata, murmushi ta yi taci gaba da latsa wayar.

“Babyna me zan samu ne?”

Taufiq ya faɗa yana mai kallon Amnah.

Ba tare data ɗago ba ta ce, “Taufiq kasan dai halina ko? Kuma kasan bana mai mai ce, Amma saboda kai son ka nake shi yasa nake sakar maka jikina sosai.”

Taufiq ya ce, “Na sani Amnah shi yasa nima son ki kullum yake daɗa ruruwa a zuciyata.”

Amnah ta ce, “Ka yi haƙuri Taufiq yau dai bazan iya ba.”

Taufiq ya ce, “Shikenan Allah yaja da ranki gimbiyata.”

*****

“Alhaji dan Allah ka dubi halin da yaron nan yake ciki.”

Hajiya Maryam take faɗawa mijinta fuskarta cike da damuwa.

Tsaki Alhaji ya yi kafin ya ce,

“Kin ga Hajiya babu bakin ki cikin wannan maganar, idan ba haka ba kuwa ranki zai mummunar ɓaci.”

Mikewa Hajiya Maryam ta yi ya yin da idanunta ke zubar da hawaye, ta ce,

“Shikenan Alhaji na bar zancen, amma wallahi ni a matsayina na mahaifiyarsa babu sa huna a ciki.”

Tana gama faɗar haka ta fice daga ɗakin, tana goge hawayen fuskarta.

Ɗakinta ta shiga tana mai cigaba da kukanta.

“Mommy lafiya? Me ya faru? Wani abun akai maki?”

Mommy ta ji muryar Yusra tana tambayarta.

Sai da Mommy ta goge fuskarta sannan ta ɗago ta kalli Yusra da cewa,

“Yusra barin gidannan zan yi ba zan iya ci gaba da zama da mahaifinku ba”

Dafe ƙirji Yusra tayi kafin ta ce, “Na shiga uku ni Yusra, Mommy me nake jin kina faɗa?”

Mommy ta miƙe ta fara haɗa kayanta a akwati tana mai cewa,

“Yusra mahaifinku ba abin zama bane domin baya saurarata akan abin da nake buƙata, Yusra idan na buƙaci Daddynku ya yi min abu idan har akan kune baya yimin.”

“To Mommy dan Allah kiyi haƙuri wallahi zai dena.”

Yusra ta faɗa tana kuka.

Mommy ta dafa kafaɗar Yusra kafin ta ce,

“Yusra mahaifinku sai dai yasa nai ta asarar ƴaƴana a gabanki ya kori ƴar uwarki ya kori yayanku yanzu kuma gashi yana so Heesham shima ya bar gidan.

Yusra ya mahaifinku yake so na yi? Nifa mutum ce kuma zuciyata tana da rauni amma ina da haƙuri ba wai yabon kai ba, amma mahaifinku yasa na gaza da wannan haƙurin.”

Rungume Mommy Yusra ta yi tana kuka kafin ta ce, “Wallahi Mommy kika tafi nima ba zan zauna ba sai na bi sahun ƴar uwata, domin saina barwa Daddy gidan nan.”

Rarrashinta Mommy ta shiga yi tana cewa,

“Yusra dan na bar gidannan bayana nufin lalacewar rayuwarku ba, a’a niba a haƙƙu bane dana rayu cikinsa ba domin ni ba gidan mahaifina bane, ku kuwa gidan mahaifinku ne.”

Yusra ta ce, “To Mommy mu kuma rayuwarmu fa idan ta tarwatse wa mu kaiwa? Ke ce fa mahaifiyarmu wadda ta san wahalarmu.”

“Kinci uwarki Yusra ki ke tsai da ita ta tafi mana idan bata fasa tafiya ba ita ba sunanta Maryam ba.”

“Alhaji Sadeq nice ka ke faɗawa haka akan ina faɗa maka gaskiya?”

Hajiya Maryam ta faɗi haka tana nuna kan ta.

Alhaji Sadeq ya ce, “An faɗa maki ɗin ki bar gidan idan ba gidan ku bane.”

“Haba Daddy mene kake aikatawa hakane? Daddy kafa sani ita ce ta haifemu dan haka ba za muji daɗin ganin ana ci mata mutunci a gabanmu ba koda kwa a ce mahaifin…”

Kafin Yusra ta gama rufe bakinta Daddy ya wanke ta da wani gigitaccen mari, kafin ya ce,

“Zagina za ki yi ko Yusra? Kin ɗauko halin mahifiyarki na mugwayen halaye da baƙar zuciya ko?”

Girgiza kai Yusra ta yi kafin ta ce,

“Allah karya nuna min ranar da zan zageka Daddy, bama kai ba koda wan da bai kaika bane, kuma Daddy wallahi Mommy bata taɓa koya mana wani hali mara kyau ba saboda samun mace kamar Mommy sai an tona.”

Mommy ce taja akwatinta tayi han yar barin ɗakin, da gudu Yusra ta bita ta rungume tana mai magiyar dan Allah karta tafi.

Da kyar Mommy ta kwace Yusra daga jikinta ta fice daga ɗakin, faɗuwa Yusra tayi a wajan tana rafsa uban kuka.

Kai tsaye Mommy inda Motar ta take ta nufa, buɗewa tayi ta shiga tare da kunnawa tabar gidan, zuciyarta na tafarfasa.

*****

“Ke kuma dan uwarki sai ki bita idan bazaki zauna ba.”

Daddy ne ya faɗawa Yusra data faɗi tana gursheƙen kuka haka bayan fitar Mommy, kafin ya fice daga ɗakin shi ma.

Mommy tayi tafiya mai nisa wadda itama bata taɓa tunanin zata yi taba, a garin Abuja ta sauka a babban gidansu.

Tun da tai parking yaran gidan suka zo suka mamayeta suna ta murnar ganinta, wata ƴar kyakykyawar yarinya ce ta tawo da gudu wadda ba zata wuce 5 years ba ta rungume Mommy tana mata oyoyo cikin ba gwariyar muryarta. Ɗaukar yarinyar Mommy ta yi tana cewa, “Oyoyo my babyna na yi kewarki da yawa.”

Kafin su rankaya su yi cikin babban gate ɗin gidan.

Kai tsaye ɗakin Hajiya Yana suka nufa (ita ce tushan gidan da mijinta Alhaji Habeeb)

Koda Hajiya Yana dattijuwar tsohuwa mai cike da kwarjini da kamala tai arba da fuskar ɗiyar ta take ta fahimci bata cikin daɗi.

Bayan Mommy sun gaisa da Hajiya ne sai duk yaran suka mike suka fita (tarbiyar gidan kenan), ya rage daga Hajiya sai Mommy.

Bayan Mommy ta ci abinci ta ɗan nutsune, sai Hajiya ta dubi Mommy kafin ta ce, “Maryama”

Mommy ta ɗago ta kalli Hajiya tare da amsawa.

“Maryama meke damunki?”

Hajiya ta tambayi Mommy.

Ƙasa da kai Mommy tayi ya yin da hawaye ke ɗiga daga fuskarta.

Hajiya ta sake Cewa”Maryama a lamunki ya nuna kina cikin babbar damuwa amma me yasa kika zaɓi ki ɓoyeta fiye da ki faɗeta?”

Ɗago da kai Mommy tayi idanunta cike da hawaye ta fara cewa,

“Hajiya ai kun dai san tatsuniyar gizo bata huce ta ƙoƙi, Hajiya a koda yau she Alhaji Sadiq yana mun abubuwa da yawa ina sharewa amma na yau da ya yi min ba zan iya ba.”

Sai kuma ta saka kuka. Rarrashinta Hajiya ta yi kafin ta ci gaba da ce wa, “Hajiya Alhaji Sadeq yana so ya sake korar Heesham daga gida saboda wani ban zan dalilinsa, kuma Hajiya idan na zuba masa ido haka zaita yiwa ƴaƴana.

Idan baki manta ba Hajiya hakafa yai sanadiyar barin Abdurrahman daga gidan akan wani banzan dalilinsa, sannan yai sanadiyyar barin mai sunanki daga gidan nan ma saboda wani dalili nasa, yanzu kuma yana so ya kori Heesham shima saboda wani banzan dalilin nasa, to ya yake so nayi da raina? Ga Yusra nan na barta itama ban san halin da zata shiga ba ta sanadiyar barinta da nayi ita ɗaya a gidan matsayinta na mace.”

Kuka sosai Mommy ta fashe dashi, wannan karan Hajiya bata yi gigin hana Mommy yin kukan ba saboda ta san abin da yake faruwa da ita dole tai kuka.

Sai da Mommy ta yi mai isarta sannan Hajiya ta samu damar rarrashinta, kafin ta ce ta tafi ɗakin da take sauka idan tazo ta huta kafin ƴan uwanta duk su dawo.

Haka Mommy ta shiga ɗakin zuciyarta cike da kewar ƴaƴanta, gashi bata san halin da ɗiyarta take ciki ba ga babban ɗanta shima, ga Heesham da Yusra haka ta baro su cikin wani yanayi, ganin damuwar da tunanin ba shi bane yasa Mommy ta miƙe ta shiga toilet ta ɗauro alwala tazo ta shimfiɗa dadduma ta fara jero salloli zuwa ga mahaliccinta domin ya kawo mata ɗauki.

Heesham da shigowarsa gidan kenan ya nufi ɗakin Mommyn sa domin sanin ya ake ciki ta shawo kan Daddyn ya janye ƙudurinsa a kan abin da yake shirin yi ko a’a?.

Amma cikin rashin sa’a yana shiga ya sami Yusra kwance tana sheshsheƙa numfashinta yana sama yana ƙoƙarin barin jikinta. Da sauri ya ƙarasa kan ta yana jijjigata yana kiran sunanta,

“Yusra!  Yusra!!  Yusra!!!”

Ba amsa sai kawai jijjuya idanu da take yi.

A zabure ya sunkuceta yai hanyar barin ɗakin, kai tsaye in da motarsa take ya nufa ya saka ta a baya shi kuma ya shiga ɓangaran driver yaja sai asibiti.

Koda ya isa da sauri yaje ya kira nurse suka zo suka ɗauketa sai ɗakin jinya domin bata taimakon gaggawa.

Sun jima a kan ta kafin su samu bugun zuciyarta ya daidaita allura sukai mata ta bacci, sannan suka chan ja mata ɗakin zuwa ɗakin hutu.

Bayan an gama ko mai ne likitan ya ɓukaci ganin Heesham, koda Heesham ya shiga office ɗin Doctor ɗin waje Doctor ɗin ya nuna masa ya zau na.

Sai da Doctor Mansur ya gama ƴan rubuce – rubucen sa sannan ya ɗago tare da yin ajiyar zuciya kafin ya ce,

“Heesham gaskiya anci sa’a sosai domin da ba’ai saurin ka wota asibiti da wuri ba da sai an rasa ta, amma dake kwananta yana gaba sai gashi Allah ya bada nasara ba wani a bune ya sameta sosai ba.”

Sai ya yi shiru, kafin yaci gaba da cewa, “Kuma ciwon zuciya ya ɗan ta ɓata sakama kon wani tashin hankali na farat ɗaya daya sameta,”

“Innalillahi wa inna ilaihirraju’un! Doctor yarinya ƙarama ka mar Yusra ne ciwon zuciya ya fara kamawa?”

Heesham ya faɗa cikin tashin hankali.

Doctor Mansur ya ce, “Ba abin tambaya ko mamaki bane, Allah yana iya ɗorawa bawa duk irin ciwon daya ke so koda dalili ko babu, jaririn da bai ma san mene ba zai iya ka muwa da ciwon zuciya a ranar da yazo duniya.

Ballanta na ita Yusra da dalili na faruwar cutar a jikinta, dan Allah Heesham kuyi ƙoƙari ku cire mata wannan damuwar koda bata fita duka ba.”

Da kyar Heesham ya iya saita nutsuwarsa, sannan Yace”Insha Allah Doctor za’a kiyaye”

Hannu Doctor Mansur ya bashi su kai musabiha sannan ya miƙe ya fice.

Koda ya fita daga office ɗin Doctor Mansur, kai tsaye restaurant ya nufa domin samo masu abin da zasu ci dan yasan itama ba wani abu taci ba.

Bayan ya dawo ne sai tunanin Mommyn su ya faɗo masa. To ina ta tafi? Mene yai sanadiyyar shigar Yusra wannan halin? Duk waɗannan amsoshin sai Yusra ta farka, Amma bari ya taɓo number Mommyn yaji.

Koda ya kira a kashe, abin da bai sani ba shi ne tun da Mommy ta fito daga gidan ta kashe wayarta har kama sannan bata kunna ba.

Koda Yusra ta farka bayan tayi wanka ya bata abinci da magani tasha, sai ya shiga jero mata tambayoyi. Shiru Yusra tayi idanunta na kawo hawaye. Da sigar masifa Heesham zai magana sai kuma ya tuna ashe fa bata da lafiya kuma Doctor ya gargaɗe su, dan haka ya sassauta murya. Ya ce, “Yusra tambayarki nake baki ce min ko mai ba alhalin bani da mai am samin sai ke.”

Fashewa da kuka Yusra ta yi kafin ta ce, “Ya Heesham Daddy ya ƙori Mommy.”

Iya abin da ta iya faɗa masa kenan. Duk dauriyya irinta Heesham sai da yai hawaye kafin ya ce,

“Wai ya Daddy yake so da mune? Ko dai ba shi ya haife mu bane? Amma idan shi ya haifemu ai ba zai din ga tarwatsa farin cikinmu da mu kan mu ba? Kuma mene Mommy ta masa da zai saka mata da wannan muguwar sakayyar? Yusra tashi mu tafi Abuja.”

A firgice Yusra ta kalleshi. Ya ɗaga mata kai.

“Eh ki tashi mu tafi domin na san Mommy ba zata taɓa huce can ba.”

Girgiza kai Yusra tayi

“Ya Heesham ka san fa halin su Uncle Bashir idan har Daddy ya ce Mommy ta tafi gida mu ka bita koro mu suke.”

Heesham ya ce, “Yes na san wannan amma sai mun je koda zasu koremu, kuma ni Yusra bana jin haushin su domin mahaifinmu ne yaja mana.”

Haka suka tattara ko mai nasu bayan Doctor ya basu sallama suka shiga mota suka ɗauki hanyar Abuja.

Basu suka isa ba sai 10:15pm na dare a sannan ma koda suka buga gate ɗin gidan da kyar mai gadi ya buɗe musu gate suka shiga bayan yaga kosu wane.

Bayan Heesham ya yi paking motarsa ne suka fito suka rankaya zuwa ɓangaran Hajiya Yana (wato kakar su data haifi Mommy).

Nan ma da suka yi knock an ɗan jima kafin a buɗe masu.

A ɓangaran Mommy kuwa tana ɗaki kawai taji jikinta ya bata a cikin ƴaƴanta akwai wanda ya bi yota. Ai kuwa ilee suka ji bugun kofa, da sauri ta miƙe ta fito domin ganin wane.

Ko da tai arba da fuskokin ƴaƴan nata sai ka wai taji wani farin ciki ya ziyarceta, suka ƙaraso in da take suka rungumeta.

Ana cikin haka suka jiyo muryar Uncle Yaseer yana cewa suna ina suzo su koma inda suka fito (dama Uncle Yaseer yafi sauran ƴan uwan Mommy nasu faɗa, kuma shi Mommy take bi) ai ba su san san da suka ƙara ruƙunƙume Mommy ba suna kuka itama Mommy ta ruƙunkume su tana kukan.

Da ya so ya ji tausayinsu gaba ɗaya har Mommy, amma sai ya sake dakawa su Heesham tsawa,

“Ko ba daku nake ba?”

Da sauri suka saki jikin Mommy suka ƙarasa inda yake suka tsugguna kafin Yusra ta fara cewa,

“Dan girman Allah Uncle ka bari Allah ya kaimu gobe zamu tafi domin kaga yan zu dare ya yi sosai kuma idan mun tafi ba mu san halin da zamu shiga ba mummunan abu zai iya samunmu.”

Duk wajan sai da Yusra ta basu tausayi saboda yadda tai magana a san yi cikin sigar kwantar da kai.

“Shikenan zan bar kune saboda sarajar ƴaƴa amma da sai na kore ku, ku tashi kuje Allah ya kaimu.”

Uncle ya faɗa kafin ya juya ya fice daga ɓangaran Hajiya Yana.

Komawa su kai wajan Mommy su kafin su ran kaya har Mommy su nufi ɗakin da aka bawa Mommy.

Bayan tafiyar sune kowa ya watse daga ɓangaran Hajiya Yana.

*****

Wayar dake ajiye akan center table ɗin dake wajan gado, a yayin da ita kuma gwanar da a kewa wayar sun lula wata duniyar ita da abin son nata Taufiq ta hanyar romantic ka wai, ɗan ture shi tayi tasa hannu ta ɗau ki wayar ta kara a kunne.

“Amnah Baby mai zamani ran ki ya daɗe.”

Abin da aka faɗa kenan bayan ta kara wayar a kunnanta.

Ɗan ya tsina fuska tayi, kafin ta ce, “Ya akai ne Alhaji Hamisu?”

Murmushi Alhaji Hamisu ya yi, kafin ya ce,”Ranbki ya daɗe ai ba a ne manki sai da dalili, idan kika ji kira to alkairine.”

“Bana son jan nagana ka sani, dan haka faɗi me kake buƙata.”

Amnah ta faɗa cikin takaici.

Alhaji Hamisu ya ce, “Ina buƙatarki ne ya za ai?”

Amnah ta ce, “Alhaji ka manta taken nawa ne bafa na mai mai ce dan haka na sake tuna maka.”

Raunana murya Alhaji Hamisu ya yi kafin ya ce, “Ranki ya daɗe ki taimaka dan Allah.”

Amnah ta ce, “Abu ɗaya zan maka shine zan sama maka wan da zata iya da kai, amma ka san saura dai?”

Alhaji Hamisu ya ce, “Shi yasa nake ƙara sonki Babyna, za ki ji alert yanzu. Amma na so a ce ke ɗin ce da kan ki.”

Bayan sun aje waya ne Amnah ta ji message ya shigo wayarta, ko da ta duba sai taga Alhaji Hamisu ne ya turo mata kuɗi har naira dubu ɗari 500.

A je wayar tayi ta miƙe tana shirya kan ta.

Mikewa shima Taufiq ya yi ya na cewa, “My Amnah yanzu kin kyauta ki din ga magana da wani a kan jikin da yake mallakina a gabana?”

Dariya Amnah ta ɗan yi irin tasu ta ƴan duniya, ta ce, “To in ban da abin ka Taufiq nifa wannan ne burina kuma ka san ko wane bawa yana da buri kuma da shi ake haifarsa da shi kuma zai bar duniya, kuma ka san ba wai kan bana da arziƙin da zan iya ma kai na wahalhaluna bane, iyayena masu kuɗine amma dalili ɗaya yasa na zama karuwa kuma nake burin na buga tambarin da duk wata karuwa bata taɓa yin sa ba.”

Taufiq ya ce, “Amma My Amnah kin san fa wannan abin da muke yi baya da amfanin komai a tare da mu.”

“Wannan daka ga ina yi nasan ba dai dai ɗin bane kuma nayi karatuna na addini domin sai da nai saukar alqur’ani duk da kuɗin iyayena bai hanani samun karatun addini ba, amma dalili ɗaya yasa na zaɓawa rayuwata wannan harkar.”

Amnah ta faɗa tare da ɗaukar jakarta da wayarta tai hanyar barin ɗakin.

Komawa Taufiq ya yi jabar kan gadon, tare da dafe kan sa.

Ya sani Amnah kyakykyawar yarinya ce haɗaɗɗiyar mace wadda bama namiji kaɗaiba hatta ƴar uwarta mace sai ta yaba idan tai arba da ita.

Ta haɗu ta ko ina kamar ita ce tayi kanta, kyau diri da duk wata halitta mai jan hankali ubangiji ya bata masu ɗau kar hankali.

A jiyar zuciya ya sau ke kafin ya miƙe ya shi ga toilet domin yin wanka saboda ya na da meeting a wajan aikin sa.

Ita kwa Amnah kai tsaye data fita da ga hotel ɗin gidan ta ta nufa, gidane mai kyau ɗan karami dai – dai zaman mace ɗaya ba yara.

Gidan ya tsaru abun ka da yar gayu kuma mai dan shin hannu (kuɗi). Ko da ta shi ga gidan toilet ta shiga, wanka ta sake yi kafinta dawo parlo ta ta ɗauki juice a firij ta koma kan kujera ta zauna, bayan ta kurɓi lemon ne ta ɗauki wayarta ta danna wasu numbobi kafin ta tafi kira.

Ring 1-2 aka ɗaga.

“Allah yaja da ranki Gimbiya Sayyada Amnah”

Aka faɗa haka bayan an ɗaga wayar.

“Ki zo gida ki same ni yanzu.”

Amnah ta faɗi haka kafin ta kashe wayar taci gaba da shan juice ɗinta.

Bayan kamar 15 minute sai gashi a na knocking ɗin ƙofar parlon, sai da aka yi yafi sau 3 sannan ta miƙe ta nufi kofar tana buɗewa ta juya ta koma parlon.

Sai da tai mata gaisuwa irinta su ta ƴan bariku sannan ta ce, “Baby gani na amsa kiranki.”

Ajiye cup ɗin juice ɗin Amnah tayi kafin ta dube ta ta ce, “Sadee yau da misalin ƙarfe 10:00pm kije gidan Alhaji Hamisu.”

Sadee ta ce, “To baby idan na dawo na biyo ne?”

“No ko mai ya baki naki ne ni ban son komai.”

Amnah ta faɗa tare da miƙewa tai hanyar barin ɗakin, sai kuma ta juyo ta kalli Sadeey kafin ta ce, “Idan kin fita kija mun kofar yadda zata rufe.”

Da to Sadee ta amsa sannan ta miƙe tayi hanyar fita, data fita taja ƙofar kamar yadda Amnah ta umarceta.

Kwanciya tayi akan makeken gadonta, bacci take son yi amma sai ga wani bakon yana yi na tunani ya ziyarceta.

Allah sarki duniya wai ni Amnah na koma haka, nutsatstsiya kamila dani amma yanzu rayuwa ta chanja min? Tabbas ƙaddara bata wuce ɗan adam.

Ganin tana ƙoƙarin tuno abin da ya daɗe sannan kuma abin da ke mata suya a rai idan ta tuna, yasa ta miƙe taje ta ɗauro alwala ta fara jero salloli.

Bayan ta idar da sallar ta shiga jero addu’oi na neman yafiya a wajan ubangijinta.

Bayan ta gama ne ta miƙe ta nufi kitchen domin samawa kan ta abin da zata ci dan taji cikinta na baibureshin.

Indomie ta dafa da kwai taji kayan haɗi da attahuru sai ƙamshi take dama fagen girki Amnah ba baya ba ce, bayan ta gama ta kashe gas ta zuba a plate ta ɗau ki plate ɗin ta koma falo ta zauna ta fara ci.

Bayan ta gama ci ta buɗe firij ta ɗauko ruwa ta buɗe ta fara sha.

*****

Zama su kai bakin gado kafin Heesham ya dubi Mommy, Ya ce,”Wai Mommy mene ya haɗaki da Daddy har kika dawo gida?”

A jiyar zuciya Mommy ta sauke kafin, ta ce, “Heesham mahaifinku…”

Sai kuma tai shiru saboda bata so ta sawa yaran tsanar mahaifinsu a ran su.

“Mommy ya kuma kikai shiru?”

Heesham ya faɗi haka yana mai kallon Mommy.

Miƙewa Mommy ta yi cikin basar da zancen ta ce, “Bari na sama maku wani abun na san ba kuci abinci ba tun da kuka taho.”

Ta na faɗar haka ta shige kitchen dake da kitchen ɗinta da store da kayan abinci a ciki.

Heesham ya kalli Yusra, Yusra ta kalleshi.

“Wai Yusra me yasa Mommy bata son ta faɗa mana lefin Daddy? Amma shi koda yaushe cikin faɗar nata lefin yake kuma alhalin bata da wannan lefin da yake faɗa?”

A jiyar zuciya Yusra ta yi, “Hmm! Ya Heesham ke nan abin da ya fi sauƙi kawai mu dena tambayarta in ya so lokacin da ya kamata mu sani zamu sani ai.”

Heesham ya jinjina kai, “Hakane maganarki, shikenan.”

Haka Yusra ta mike ta nufi kitchen ɗin dan ta taimakawa Mommy, koda ta shiga sai Mommy ta ce ta bar shi taje ta huta domin ta san sun gaji. Cikin ƙanƙanin lokaci Mommy ta kammala dafa masu jallof na taliya sai kamshi take tashi, zubo musu tayi a plate ta kawo masu sannu su kai mata sannu su ka fara ci.

*****

“Hhhhhhhhh, wane ya isa yaja damu yaci ƙasa babu shi.”

Wasu narka – narkan mutanene maza dattawa masu kiba da salkar ciki, a wani ɗaki suke mai duhu ba abin da kake gani sai muryar su da ake ji.

Can wani shima naji ya ce, “Ai mai ja damu uwarsa ma bata haife shi ba, jayayya da mu nakasa ce,hhhhhhhh”

Wani ɗan ƙoƙo naga mutum na farko ya ɗauka wani jan a bune a ciki mai kama da jini ya ɗaga ya kwankwaɗa sannan ya miƙawa ɗayan shima ya sha.

Wata baƙar mata ce ta shigo cikin tashin hankali ta zube gaban su tana cewa, “Ran ka ya daɗe matsala fa babba ta kunno kai.”

A zabure na farkon ya kalleta,”Matsala? Matsala? Lantau matsala fa kike faɗi? to kiyi saurin maganceta idan ba haka ba zata dawo kanki wannan matsalar”

“Na shiga uku ran ka ya daɗe ni kuma ina zan sa kai na?”

Matar ta faɗa tana kuka saboda ita kaɗai ta san matsalar dake kunnowar amma ga shi an ce kan ta zata dawo.

Tsawa ya daka mata,”Ta shi ki fice ki aiwatar da abin da zai fidda ke!”

A tsorace ta tashi ta fice jikinta na rawa.

Juyawa ya yi ga ɗayan, ya ce, “Kai kuma kaje waɗan nan mutanan a zo da su yanzu.”

Mutumin ya ce, “Yan zu kuwa aiki zai tabbata.”

Yana faɗar haka shima ya fice daga ɗakin, ya rage saura shi kaɗai wasu surutai ya shiga furtawa waɗanda basa da daɗin ji bare saurare.

Comment and share please

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

2 thoughts on “Amnah 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×