Skip to content
Part 8 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Anushka Shetty

In ka ji taken manya ai daban dana yara

In ka ji sautin manya ai daban dana yara

In ka ga tafiyar manya ka san ta zarce ta yara

In ka ga fitowar manya ta zarce a kai bara. 

Ga zakkar matan kudu Anushka ta

Kin yi gaba kin zarce su a fadata

Ga ta gaban-goshin Prabhas Anushka ta

Ko ba a so da kin zo dole a sassauta.

Devasena ba kya tsoron a fafata 

Ga kirarin mace ɗaya kama da dubu Anushka ta 

Kai kauce ga jarumata ku bubbuɗa 

Babban daushe wane goro wajen gatsa. 

Babbar bishiya kin zarce a daddatsa 

Ɗanyen gwal ta yaya zai tsatsa? 

Karsana ba ki ramewa ko kullum za a yo tatsa 

Bayan bushiya ko mahaukaci bai takawa. 

Gaba dai gaba dai Anushka ‘yar lele 

Kyakkyawa ce an sani ko bata sa lalle ba 

Ko babu ado mata dole su yo shayi 

Masu kyan ma a gabanki zama suke kamar ‘yan tayi. 

Ga nasarori gareta fa ta tattara 

Dama an ce da safe ake kamun fara 

Na yi jinjina ga Sarauniya 

Ni ne Jamilu katibin Gimbiya 

Na yi rattabe kuma zan ƙara ga Sarauniya 

Fatan watarana za ki zo Nijeriya 

Kuma in kin zo za ki ganni ya Sarauniya 

Ko ba komai in na ganki zan samu nutsuwar zuciya. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 7Ba’indiya 9 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 8”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.