Skip to content
Part 23 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

Har agogon gefen gadon nasu ya buga ƙarfe 2:00 daidai na dare ta gaza runtsawa. Kawai juyi take yi tana ƙissima abin da za ta yi Alhaji ya karɓe kamfaninsa da ya bawa Hammad.

Juyawa ta yi tana kallonsa yadda ya baje sosai hanci a sama yana barcinsa.

Miƙewa ta yi cikin sanɗa, ta buɗe ƙofar a hankali ta fice daga ɗakin ta nufi nata. Ɗaukar abin da take tunanin ta yi.

Fitowa ta yi ta nufi Makzan ɗin Alhaji. A hankali ta buɗe da ɓoyayyen key ɗinta da take kwana da shi a rigar nono.

Ciki ta shiga ta ƙarasa jikin girkakken sunduƙin da in za a haɗa ƙarata goma ba za su iya cira shi sama ba.
Ƙirjinta na dukan sittin-sittin tana tunanin ko an canja lambobin sirrin haka ta fara zuba wanda ke kanta.

Ga mamakinta kuwa sun buɗe, idanuwanta suka sauka ɓarin da tarin gwala-gwalan suke, ciki harda nata.
Mamaki take yadda suka ƙara wannan yawan, tabbas shekaran jiya da ta buɗe iya nata ne kawai, amma da ta tuna Alhajin na taɓa harkar gwal, sai ta kauda tunanin ta maye shi da tattausan murmushin tsuntsu daga sama gahehhe.

Hannu tasa ta kwaso su tas! Ta aje can gefe daga ƙasa, ta rufe sunduƙin.

Hular Hammad da ta ɗauko daga ɗakinta ta jefar a dandaryar ƙasan.

Sunkuyawa ta yi za ta kwashe tarin gwala-gwalan, wani hannu zubin gajeru ya riga ta dafe su.

Wani irin baya ta yi, tana mannewa da bangon ɗakin, idanuwanta waje da wani irin firgitaccen tsoro.

Ɗagowa ya yi, hannuwansa cikin Aljihun jallabiyarsa, yana zuba mata kallo cike da ɓacin rai.

“Annamimiya, ashe ke ce ɓeranyar?”
Ya furta yana ƙara takunsa zuwa gabanta.

Tsayinta da ya ƙere nasa yake takaici da babu abin da zai sa shi zuba mata mari. Shi sai yanzu ma yake nadamar auren ta tun farko da wannan shegen tsayin. Yana tuna sa’adda suke matasa ko fa kiss zai mata daga tsaye, sai dai tasa masa kujera ya taka ya yi.

“Mtsswwwww…!”
Ya ja tsaki mai ƙarfi.

“Wallahi kinci darajar ɗiyar dake tsakaninmu, da yau sai dai ki ƙarasa kwana cikin gidanku, cikin wannan daren zan kaɗa keyarki. Ni fa Salamatu? Ni mijinki da muka cinye kusan rayuwar tare kike ma sata?”
“Ka…ka yi haƙuri Alhaji, sharrin shaiɗan ne”
Ta furta, idon nan bushe, babu ko ɗigon hawaye.

“Shaiɗan? Ai ke ce shaiɗan ɗin da baƙin ciki da hassada ya miki katutu cikin rai. Me Hammad ya miki a rayuwa da za ki saka masa da kalar wannan abin? Yaron da kika raina da hannunki, yake miki biyayyar da ko na cikin ki bai miki kalarta. Yanzu da ban biyo ki ba, na hana ido na barci dan san sanin wanene ɓarawon, da idan kika kwashe abin nan, gobe sai dai na kama shi ba bisa haƙƙinsa ba. Haƙƙin yaron nan kaɗai ba zai barki ki runtsa ba, za kuma ki ga kalar hukuncin da zan ɗauka, sai kinyi kuka da idanuwanki kina roƙona kan hakan, sakarya kawai…”

“Ki kuma dawo da duk abin da kika ɗauka.”
Ya furta yana mai juyawa a fusace zai fice, har ya kai ƙofa ya juyo yana kallonta. Tana nan yadda take ko kwakkwaran motsi ta gaza yi.

“Faɗa mini, ina kika samu zoben yatsansa shekaranjiyar?”

“Uhm Alhaji dam…dama dai…!”

“Ke nake sauraro!”

Ya furta a tsawace.

“Na ce dama wani yaro nasa ya zuba masa abin da zai gusar da hankalinsa yadda zai gagara tuna komai. Shi ne to aka ciro min zoben.”

Wani kallo ya mata yana mamakin kalar muguntar ta.

“Lambar sirrin fa?”

“Uhmm a wayarka na gani lokacin da kake turawa Hammad.”

“Key ɗin da kike buɗe ɗakin da shi?”

“Ka yi haƙuri dan Allah, a cikin kayanka na ɗauka na gwada da sabulu aka yanko miki irin shi.”

“Da kyau.”

Ya furta yana barin ɗakin.

Wani yawu ta haɗiye mai kauri tana sauke idanuwanta kan gwala-gwalan, sunkuwa ta yi ta kwashe ta maida su ma’ajiyarsu.

A haka ta fice, gabanta na faɗuwa, tsoron ta ɗaya kar hukuncin Alhaji ya wuce tunaninta.
*******

HAMOUD.

7:30am

Ta masa cikin asibitin.

Matar kawu da ya hango ya sashi nufarta da sauri har yana tuntuɓe.

“Ina Mamy?”

“Tana ciki”

Ta furta tana nuna masa ɗakin.

Shiga ya yi kai tsaye ya zarce gadon da take.

“Mamy…”

Ya furta da sanyin jiki, yana jin wani abu na tokare masa maƙoshi.

Ita ma muryarsa da ta ji ya sata buɗe idanuwanta, duk da zuciyarta na kwaɓarta da gizo ne yake mata, amma a hakan ta daure ta juyo saitin da taji sautin. Idanuwansu suka sarƙe guri guda, da sauri ta fara ƙoƙarin miƙewa da duk wani ƙarfi da ya sauran mata.

Riƙe ta ya yi yana girgiza kai.

“Ki yi haƙuri, ki yafe mini abin jiya…”

Juya kanta ta yi tuna kalamansa, abu ne mai girma da ba zai taɓa barin zuciyarta ba. Ɗanta da ta haifa a cikinta, ke mata Allah ya isan nononta da ta sha.

Da ƙyar ta buɗe baki tana tattara kalmo min da za ta furta.

“Siyan ka na yi Hamoud, ka tafi kawai, ina da haƙurin da zan iya dangana da rashinka In aje ma zuciyata ka mutu. Na ƙare rayuwata da sa’ada ba tare da na ƙara zubda kwallar tuna ka…”

Hannuwansa da yasa duka biyun ya toshe bakinta ya sata yin shiru tana jin yadda wani abu tamkar ƙaya ke sukan ta a ƙirji.

“Ki yafe mini dan Allah Mamy, ban san sharri ba ne.”

Ya furta da ruwan hawayen da bai san sa’adda suka fara sauka ba.

Kallon da ta masa ya sa shi haɗiye su da sauri.

A hankali ya kwashe dukkan abin da ya faru ya gaya mata. Abu ɗaya ya ɓoye, wato giwar da ya sha. Ba zai iya faɗi ba. Shi ya sa ma ya tsaya a gidansa ya dinga wankan da bai barshi ba sai da ya tabbatar duk wata alamarta ta tafi.

Ɗauke kanta ta yi daga kanshi ta juya tana kallon ɓarin da Fainusa take.

“A yi ma likitan magana Hajiya. Su ba ni sallama haka nan.”

Da haka ta koma kwanciyarta, tana juyawa Hamoud baya ba tare da ta ce da shi ƙanzil ba, tana sauke ajiyar zuciya jin wani sanyi dake ratsa ta.

Shirunta, hmm, shi kaɗai ya san ma’anar hakan a duk lokacin da ta yi shiru kan wani lamari.

Dan haka ya matsa da sauri yana leƙa fuskarta.

“Mamy baki ce komai ba?”

“Na ji ai Hamoudi, bari muje gida.”

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yana mai da kallonsa ɓarin da Ammatinsa Fainusa take.

Ita ma ido ta ɗaga masa alamar bata gane komai ba.
*

3:30pm

A babban Falon ƙasan suka taru gaba ɗaya.

Kawu Hussein ya buɗe taron da addu’a suka ƙara godewa Allah da yadda ya warware musu lamarin cikin sauƙin da ba su zata ba.

“Hamoudi…”

Kawu ya furta yana gyara zaman babbar rigarsa.

“Mun gama magana da mahaifiyarka, ta ce a sanar maka batun auren nan an goge shi. Idan kuma za ka yi to ba da yawunta ba. Ni ma kuma na yarda da hakan, dama ba dan ka yaudare ni da cewar yarinyar ɗiyar malamai ba ce ai da tun farko ban bari. Ka sani ba zan taɓa yarda ka auri karuwa ɗiyar karuwa jikar karuwa ba.”

Zancen wani irin bugu ya masa, har bai san sa’adda ya gigice ba, ya ɗago yana kallon saitin da Mamy take, ɗauke kallonta ta yi daga kansa kamar bata san Allah ya yi ruwansa wurin ba.

“Ba karuwa ba ce kawu, wallahi ta daɗe da tuba, mahaifiyarta ma tun kafin ta haifeta ta bar harkar. Haka mahaifinta ma malami ne.”

“Yana ina yanzu? Kai ba na son shirmen banza, karuwa ko ta tuba, sunanta tubabbiyar karuwa yake komawa. Wato karuwan nan dai na nan naniƙe da sunan.”

Kafin ya san abin yi ya ji sautin Mamy.

“Hamoud, ina ce dama auren nan za ka yi revenge ne…?”

Da sauri ya hau girgiza kai.

“To na ce abar shi ba na so, haka ita kanta Fakriyar babu wani hukunci da za a ɗauka kanta ba, a barta duniya kaɗai ta ishe ta. Idan har kuma na isa da kai, to karka ƙara kawo min batun matan nan. Abin da ya faru ma ya ishe mu. Kai ban yafe maka ba idan ka ƙara taka ko da unguwarsu ne. Ban yafe maka ba idan ka ƙara waya da wata Quraisha. Kayan da aka kai musu su riƙe can, mun bar musu!”

“Nooo Mamyyyyy!”

Ya furta da ƙaraji yana rarrafawa zuwa gefen Kawu. Kallonsa yake kan ya taimaka masa ya taushi Mamy.

“Babu abin da zan maka sakarai kawai, kai idan ba marar hankali ba, ina kai ina waɗanda suka zo har cikin gidanku sukai fashi? Me zai haɗa ka da su idan ba ɗauri ba? Kai ko uwarka ta yarda Ni ba zan yarda ba. Matsa daga gabana ko na hamɓare ka, sakarai kawai!”

Matsawar ya yi cikin rashin hayyaci, har bai san sa’adda ya isa gaban Kawu Hussein ba.

“Kawu ka taimaka mini kan su Mamy, wallahi ina sonta da gaske, ta fa daɗe da barin komai. Haka auren irin su kamar jihadi ne.”

Miƙewa Kawun ya yi yana kallon agogon hannunsa.

“Hamoud haƙuri za ka yi tunda iyayenka ba sa so to ko ka matsa kan lamarin ba albarka zai yi ba.

Yanzu dai ke Mamyn Hamoud ki masa alfarma guda ya kira yarinyar dan su san abin da ke faruwa.”

“Bari ba shi haƙuri, kar ma ya haƙura. Jihadin gidansu dan ƙundun uba mu zai gwadawa so? Dubi halin da yasa mahaifiyarsa kan wannan batun, shi ko ishara bai gani ba, ba zai gane yarinyar ba Alheri ba ce gare shi?”

Kawu ya furta shi ma yana miƙewa.

“Yawwa ina kabar min mota ta? Shashasha har ciwo ka jiya Direba na wai kai me baƙar zuciya.”

“Ka yi haƙuri Kawu Hussein, na riga na yi rantsuwa kan ba zai sake waya da ita ba.

Ina da Number yarinyar, Ni da kaina zan mata maganar.”

A haka suka watse, Mamy ma ta haye sama aka bar Hamoud nan gurin a durƙushe, yana jin kamar an tara duk wani bala’i na duniya an dora tsakiyar kansa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 22Asabe Reza 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×