Skip to content
Part 7 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

Tsalle ta kama yi saman katifar tana watsa hannu, sai kuma ta sauko da gudu zuwa falon, ta yi kan matar da ke saman wheelchair ta manna mata kiss, ta ƙarasa ga Soupy da ke ƙoƙarin kunna TV, ta mata kyakkyawar runguma ta baya sai da suka kai ƙasa.

“Kin gani ko Soupy? Na faɗa miki ai Hamoudi ba zai taɓa bari na ba, alƙawari ne ya mini, kalli fa ki ga abin da ya rubuto mini.”

Ta faɗa tana nuna mata saƙon.

“Ni ce komai na shi, ya gaza barci domina…”

“Idan ma Sihiri ne Fakriyya ta masa, ƙarfin soyayyar da ke tsakaninmu ya karya shi…”

“Taho ki zaɓa mini me zan sa idan zanje wanda zai kankaro mini dukkan kyawuna.”

“Ko shopping za mu je, mu zaɓo wasu kayan?”

Ta furta kalmomin a jejjere, fuskarta ɗauke da wani farin ciki marar misaltuwa.

Soupy kallonta take yi tana ta ya ta dariyar, duk da a zahiri kawai yaƙe take yi.

Abin na su kuma ya shallake nazarinta, ta ma rasa ganewa gaba ɗaya, me kuma ya saura gurin mutumin da ya auri ‘yar uwarki, idan ba Reza da ba ta ganin gabanta ba. Ajiyar zuciya ta sauke, tana fatar koma menene ya zo da sauƙi.

Tun kafin lokacin da ya yanke ya cika, ita ta wanzu agurin, kwalliya ce ta yi, kyau ne akan kyau, turarukan da ta bulbulawa jikinta kaɗai, ya isa ya ta da hankalin duk wani balagaggen namiji.

A haka ta tsaya gun, tana mai kutsawa cikin park ɗin, idanuwanta na sauka saman ciyayin da suka fara furta sirrikan zuciyoyinsu ita da Hamoudi, anan ya fara furta mata kalmar so, anan itama ta fara amsa masa tayinsa.

Lumshe idanuwanta ta yi, abin na sake zauna mata can ƙarƙashin ruhinta, abubuwan da suka wanzu a lokacin ke dawowa tar-tar cikin idanuwanta, tamkar wadda aka kafawa Majigi, haka take kallonsu.

Tun bayan dawowarsu daga gidan Alhajin, zuciyarta ta kasa nutsuwa, ga haushin abin da Fakriyya ta yi na haiƙewa Dattijon, alhalin ta sani duk iya shegensu na karuwanci, ba a tilastawa wani ya yi harka da kai, sai idan shi ke so.

Ga kuma tunanin saurayin da ta gani a gidan, wannan shi ya fi ta da mata hankali akan abin da Fakriyya ta yi.

Ya ga fuskarta, ta sani sarai nemo su ba zai ba da wahala ba, sai dai abin ya fara bata mamaki da taga har an shafe sati ko labarin fashin da suka yi gidan Attajiran ba ta ji a labarai ba.

Tambayar zuciyarta take, akan dalilin da yasa suka ɓoye, ta sani sarai, saurayin da ta gani a gidan, ɗan Alhajin ne, to mai zai sa ya ɓoye ya ga fuskarta? Ko kuma dai bai ganta ba ne? ita ce kawai take tunanin hakan?
So take ta san inda za ta ganshi ba, tana kuma tsoron abin da zai biyo bayan.

Sai dai abin da take ji game da shi, ya girmi dukkan tsoronta, duk da bata hango yiwuwar lamarinsu, amma dole za ta neme shi, ko da kuwa daga ranar da ta ganshin, ba za ta ƙara wata kyakkyawar rayuwa ba sai a Prison, to kuwa sai ta neme shin.

Da wannan tunanin take takawa cikin Super market din, a daidai gurin turarukan ta tsaya tana zaɓa, har hannunta ya kai kan wanda take so Turab-azzahbi, ta kai hannu, shi ma ya kai hannu, a haka hannuwansu suka sarƙe da na juna kan turaren, ta ɗago tana kallonsa jin wani sanyi dake jikin hannunsa, shi ma ɗin ita ya kalla, idanuwansu na haɗewa cikin na juna, da wani irin yanayi da ke sanyaya jikinsu.

Shi ya fara janye hannunsa, yana furta,

“Sorry! Ban san naki ba.”

A firgice ta lalle shi, gani take ya gane ta, sai dai ganin yarda ya nuna, kamar bai taɓa saninta ba, ya sata ƙaƙalo murmushin dole tana faɗin.

“Karka damu, wuce da shi kawai.”

“Ke kuma fa, na ga shi kaɗai ya rage.”

Girgiza kai ta yi, har yanzu da murmushin a fuskarta, sai kuma ta juya a hankali tana canja taku, tana jin yadda idanuwansa ke sauka a bayanta, da ta ɗame cikin wata ‘yar yaloluwar rigar da bata rufe gwiwowinta ba.

Ranar haka ta wuni cikin farin ciki tana bawa su Soupy labari, saboda kawai ta ganshi, sai ta ji ta tsani kowane namiji ma sai shi kawai, daga ran nan ta bar fita da kowane kare, tunaninsa kawai ya ishe ta biya mata bukakatunta.

Abin ya fara ɗaure mata kai, ganin duk inda za ta sai ta haɗu da shi, har fita take domin kawai ta san za ta ganshi.

A yau ma da take takawa zuwa cikin kasuwar, tana hangoshi yadda yake binta yana ɓoyewa dan kar ta kula da shi,

murmushi take yi a ƙasan ranta, tana mamakin abin da ya sa ba zai magantu ba, yake ta abubuwa kamar wanda bai taɓa furtawa mace kalmar so ba.

Ta gefen idonta taga yadda ya miƙe, ya dawo ta gabanta, ci gaba ta yi da tafiyarta kamar ba ta ganshi ba, a haka ya zo ya ɗan bangaje ta, kayan hannunta suka watse a ƙasa.

A tare suka sunkuwa, har suna gwara kansu.

“Auch!” Ta furta tana shafa gurin. Kafin kuma ta ɗora,

“Ban san yadda zan yarda ba bibiyata kake yi ba.”

“Ban san yadda zan fahimtarki akasi ne haduwarmu ba.”

“Ko?” Ta furta da murmushi saman laɓɓanta.

“Gaskiyar ke nan.”

Ya furta yana miƙa mata kayan, karɓa ta yi, ta juya, shi ma ya miƙe yana ɓacewa a cikin kasuwar.
Wasan nasa ke burgeta, dan haka ta ci gaba da fita akai-akai dan kawai ta san za ta ganshi.

Yau cikin nishaɗi take jinta, dan haka ta shirya zuwa Cindrella Park, wanka ta ɗauka sosai, ta hade cikin yar rigarta da bata wuce gwaiwarta ba, ta canja barimomin dake fuskarta,, ta saka wasu na zinari, ta saukar da gashinta da ta ƙara da na doki, ya sauka har tsakiyar bayanta.

A haka ta fice, tana baza ƙamshinta a duk inda ta gifta.

Mintuna arba’in ta kwashe ba shi ba dalilinsa, sai dube-dube take ko ya ɓoye a wani gurin yana hangenta, sosai kwakwalwarta ke ɗaukar Caji, ranta na wani irin ɓaci, ba ta san ta damu da shi har haka ba sai yau, a hankali take jin idanuwanta na cikowa da ruwan hawaye,

“I’m here, mene na Kukan?”

Ta ji sautinsa a saitin kunnenta, da sauri ta fara mai da hawayen, ta juyo gareshi tana ɗame fuskarta.
“Wai kai me ya sa kake bi na duk inda na shiga, ko na ci bashinka ne?”

Waige-waige ta ga ya kama yi, sai kuma ya juyo kanta yana ɗora yatsansa a kirjinsa.

“Da Ni kike?”

“A’a da inuwarka”

Ta furta cike da kuluwa tana murguɗa baki.

“Oh na tuna,”

Ya furta yana komawa jikin bangon da rabinsa ke kallon rana. A take inuwarsa ta wanzu gurin.

“Yawwa to ga inuwar tawa, faɗa mata dukkan abin da take miki, ki gaya mata ta daina binki.”
Ya faɗa kamar yaro, yana lankwashe kansa.

Da dariya ta kwashe, dariya irin wacce ta daɗe ba ta yi ba, sai ya yi tsai yana kallonta, zuciyarsa na ƙara girmama girman kudurir Allah.

A hankali ya taka yana ƙarasawa gareta, hannunta ya riƙo yana haɗe su cikin nasa.

Shiru ta yi, yanayin na ratsa ta da wani irin abu da bata taɓa ji jikin kowanne namiji ba, da mamaki ta ɗago tana kallonsa, jin wani sanyi dake jikin hannuwansa.

“Karki damu, haka jikina yake.”

Ya furta yana luma idanuwansa cikin nata.

“Ya Rabb, You have a golden eyes like her!”

Yatsine fuska ta yi tana kallonsa da tarin tambaya.

“Wa?”

“Hajjatee.”

Ya furta a hankali, tana kula da yadda zafin sunan da ya kira ya sashi runtse ido.

Sai ta ji ranta ya ɓaci, ke nan ma da budurwarsa take masa yanayi, shi ya sa yake ta bibiyarta.
Hannunta ta fara ƙoƙarin zarewa, tana son tafiya.

“A’a Please, ba zan taɓa bari ki kubce min ba.”

“Me za ka yi da macen da ta shiga gidan mahaifinka, ta keta masa mutunci kan abin da yake haƙƙinsa ne? Me ya sa ba za ka kaini Prison ba a rufe?”

Ta furta, muryarta ɗauke da zafin kiran sunan wata da ya yi, gwara ta gaya masa, ya ɗau matakin da zai ɗauka.

“Na yafe mata, zan kuma rayu da ita, mahaifina ma zai yafe mata, saboda ba lefinta ba ne, haka ta ta rayuwar ta zo mata. Abin da kuka ɗaukan shi ne rabanku.”

Runtse idanuwanta ta yi, a karo na farko ta ji bata yarda da shi ba.

“Kasan kuwa abin da ‘yar uwata ta ma mahaifinka? Shi kake cewa za ku yafen?”

Buɗe idanuwansa ya ƙara yi sosai yana dubanta.

“Akwai wani abu da kuka yi ne bayan satar?”

‘Bai sani ba.’

Ta furta a ƙasa ranta, sai kuma ta ji kunya me nauyi ta lulluɓe ta, ta ya ya za ta faɗawa mutumin da take ƙauna a duka duniyarta, ‘yar uwarta ta haiƙewa Ubansa? Nooo! Ba ta yi wannan lalacewar ba.

“Ki faɗa mini me kuka aikata bayan satar?”

Ya faɗa wannan karon a kausashe.

“Umm… Ba komai fa! Kawai dai ina mamakin yadda za ku yafe ne.”

“Ba ma daga cin mutanen da ba su san ƙaddara ba, abin da kuka ɗauka, bai kai rabin abin da ya mallaka ba, me ya sa ba za mu yafe ba, karki damu ya wuce fa.”

Murmushi ta yi, da ya tsinka zuciyarsa, ya kai hannunsa saman barimar fuskarta yana shafawa.

“Zan cire, ba ka so ko?”

Girgiza kai ya yi da sauri.

“A’a karki cire, ina son su sosai, Sak! Irin na Hajjatee.”

Tsaki ta ja me ƙarfi, ta fincike hannuwanta daga nasa, ta miƙe da sauri tana faɗin.

“Sai ka je ga Hajjateen, karka ƙara wanzuwa gabana kuma.”

Ba ta san sa’adda ya motsa ba, kawai ganinsa ta yi a gabanta, gwiwarsa a dandaryar kasar, yana miƙa mata hannunsa.

Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata, kin kuwa san menene dalili? Saboda a kodayaushe ke ce abu mafi kusanci da zuciyar tawa, su kuma idanuwan kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya ɗaya. Ki aure Ni domin Allah.

Ji ta yi kanta ya yi wani irin girma, wai ita Reza da ta gama sanin duk wani kalar karuwanci ake nema da aure?Bata taɓa hango wannan ranar ba. Kunya ta ji na lullubeta ganin yadda yake duƙe gabanta, ga mutane duk hankalinsu ya kawo gurin.

A hankali ta miƙa masa hannun, ya rike cikin nasa da wani irin ƙarfi.
Tana jin yadda mutanen gurin suka ɗauki sowa, sai ta ji kunyar da ba ta taɓa sanin tana da irin ta ba ta mamaye dukkan jikinta.

Wannan shi ne mafarin soyayyarsu, bari mu dawo cikin tunaninta.

Murmushi ta yi tana sake jinjina girman ranar a rayuwarta.

A daidai lokacin ta hangi shigowarsa cikin park din, miƙewa ta yi, idanuwanta suka sauka kan hannunsu da ke sarƙe da na juna.

Shi da Fakriyya ya zo mata, lalle rashin mutuncin ya girmama.

Da sauri take takawa zuwa gare su, so take kawai ta ƙarasa ta ji ta cika hannunta da wuyan Fakriyya.
Da dukkan ƙarfinta ta shaƙeta, tana haɗa ta da bangon gurin ba tare da ta farga ba.

“Me na miki kike son kassara rayuwata, ki faɗa mini!!!”

Ta faɗa tana ƙara shaƙe wuyanta.

Wani wawan mari ta ji ya sauka a kuncinta, kanta farga ya ƙara sauke mata wani marin da ƙarfinsa ya sata kifewa a saman ciyayin, ta ɗago ido jajir tana dubansa, kafin kuma hawayen su fara sauka sif-sif saman kuncinta.

“Ham…Ham.. Hamoudi Ni kake mara saboda waccar?”

Ta furta, kalmomi na watsewa a bakinta ganin yadda ya rungume Fakriyya yana rarrashinta.

“Na rasa ke a cikin karnuka wane layi kike, na ce ban sanki ba, ban taɓa wata alaƙa da ke ba, me ya sa kike bibiyata kina son wargaza rayuwar aure na? Ke Tunkiyar ina ce da ba za ki gane na tsani ganinki ba. Ina gargadinki, ki fita rayuwata, wallahi kinji na rantse da girman mahallaci na, zan iya garƙame rayuwarki, ki ƙarasata a Prison, I’m warning you!”

Mamaki ya gama kasheta, wato saboda yana tare da Fakriyya shi ne yake son nuna ba shi ya mata saƙota zo ba ko kuwa wani sabon makircin ne irin na maza?

Miƙewa ta yi da wayar ta a hannu, har yanzu hannunta na saman kuncinta.

“Kai ka ce min na zo Hamoud, me ya sa ne kake son tsarwatsa kwakwalwata, ga saƙon ka duba.”

Ta faɗa tana jefa masa wayar, ya cafe Yana dubawa.

Murmushi ta ga ya yi a gefen kuncinsa yana duban Fakriyya.

“Amma wannan ƙawar taki sa’adda kuka yi karatu ZERO take samu a takardunta ko?”

Bai jira amsarta ba ya juyo kan REZA

“Lalle ke a cikin daƙiƙan ma degree gareki. Saƙon naki da aka turo tun 17 july 2014 kike cewa Ni na tura miki yau? A gidan ubanki na samu Number dinki halan, ba ki ga sunan wanda ya turo ba? Haisam ne ya turo ba Hamoud ba, Mahaukaciya.”

Ya faɗa yana jefa mata wayar, ya juya akan idonta ya sakalo kugun Fakriyya suna mikewa cikin park ɗin, tana ganin yadda Fakriyya ta juyo ta kashe mata ido ɗaya, da murmushi kwance saman fuskarta.

A gigice da ɗauko wayar da ke yashe a gurin, ta fara dubawa, tabbas hakane, Haisam ya turo, kuma tun 2014, wayar take sake kallo ko dai ba ta ta bace, ɓare wayar ta fara yi ta ciro layin tana dubawa ko dai ba na ta bane.

Tabbas shi ne, amma kuma ya kai saƙon Hamoudin da ya shigo cikin wayarta ya koma Haisam? Idan wuƙa za a sa mata a wuya, za ta rantse kan saƙon Hamoudi ta karanta ɗazu da safe, wanene ma Haisam ita a rayuwarta?”

‘Me ke faruwa da rayuwata?’

Ta furta tana riƙe kanta, tana durƙushewa a dandaryar wurin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 6Asabe Reza 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×