Skip to content
Part 31 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

HAROUN

“Ba ki mutu ba? Quraisha!! Kai! Sa’idu!!! Buɗ.. Buɗen motar.”

Abin da yake iya ambata ke nan a bayan ya saka dukkan ƙarfinsa ya ɗaga ta zuwa cikin jikin jikinsa.

A kusa da shi ya zaunarta yana gyara mata kwanciyar samansa. A take kuma Direban shi ma ya shiga yaja motar da gudun bala’i.

Ba sai an umarce shi da inda za shi ba a yadda yaga Maigidansa yana hawaye. Ba ma wannan ba, sama da shekaru goma da ya shafe da ubangidan nasa tun suna sokoto bai taba ganinsa da wata ɗiya mace idan ba yau ba. Ya sani kowacece wannan. To ba ƙaramin abu take zame musu ba.

Asibitin da ya san ya zame musu tamkar da kwabonsu aka gina shi ya kai su. Ba bata lokaci ma’aikatan jinyar suka yi abinda ya dace. Sai dai daƙiƙai biyar da likitan ya kwashe bai isa ga muradinsa ba ya sashi banka masa ƙofar a lokacin da yake kan duba wata patient ɗin.

“Wannan da kake ɓata lokaci numfashi take yi. Ni wacce na kawo bansan inda nata numfashin ya tafi ba. Wallahi ka ji na rantse wani abu ya sameta a wannan five minute din da ka share, zan maka koma menene ganin na mayarka yadda taken…”

Aminin nasa yake kallo yana lissafa girman tashin hankalin da yake hangowa cikin idanuwansa.

“Ka wuce mana…”

Ya katse masa tunani da tsawa.

Da ido ya bishi, ganin kamar baya hayyacinsa ya sa daga masa hannu alamun waca ce.

“Ita ce.”

Ba sai ya ji ita ce wa? Daga ita ce din ya gama gane wacece din. Tirkashi! Tabbas yana da tabbacin Haroun yanka shi ma zai iya yi idan har kan wannan halittar ce. Dan haka ya juya da sassafar yana aje takunsa kan na ma’aikaciyar jinyar da ta yi gaba da tarin kayayyakin aikinsu.

Sai da yaga shigarsa dakin da aka kwantar da ita, tukunna ya karbi ruwan da Sa’idu ya shafe sama da mintuna goma yana miko masa. Kallonsa ya tsaya yi. Kana ya ce, “Jeka unguwar da muka same tan ko za a ga wani nata, karmu sa su a tashin hankali.”

Daga haka ya daga gorar ruwan ya fara tuttulawa cikinsa. Sha ya yi sosai har sai da yaji babu dadi. Tukunna ya aje kansa kasa, abubuwa da yawa ke iya dawowa cikin kwakwalwarsa. Abubuwa da yawa kuwa sun riga sun shuɗe tamkar wanda ke barci suka faru da shi. Abu daya ke masa gizo cikin tarin abubuwan da ya gaza fahimtar farkonsa. Shi ne; tsayuwar mace mai ciki a gabansu, riƙe masa kafafuwa da wata mace me ciki ke yi cikin halin roko. Yana tuna yadda yake saka kafa yana hamɓare ta. Matarsa ke nan. Matarsa dai da yake da tabbacin kafin auransu yana mata so ba na wasa. Wanda a bayan ya rasa ta, son ya zama abin da ke ƙoƙarin fidda shi daga tunaninsa. Ta yiwu dan bai san inda zai ganta ba ne. Ta yiwu kuma dan an tabbatar masa da ta dade da mutuwa ita da abinda ta haifa. To idan da gasken ta mutu? Wacece wannan?.

Kansa ke sarawa. A hakan ya ke tuna shekaru ashirin ɗin da suka gaba ta.
*

Idan da ba a ba shi labari ba, zai iya rantsewa da mahaliccinsa a cikin jirgin saman Ethopian Airlines aka sabunta halittarsa. Sai dai kyakkyawan farin Dattijon da ya buɗi ido ya gani gefensa, shi ya canja masa dukkan tunaninsa.

Tamkar wanda ya farka daga barci haka yake mutsu-mutsu  yana ƙoƙarin kwance kansa.

“Me nake anan? Ina ne nan? Ina Quraisha? Yau fa ta tare. Me ya sa zan fito?

Tambayoyin da ya jero kenan ga mutumin da ke gefensa yana ta doka masa murmushi.

A zahiri za ka za ci murmushi ne na rainin hankali ko kuma irin na wanda ya ci nasarar sace wani mutum.

A baɗini kuwa murmushi ne da ke nuna girman farin cikin da yake ciki.

Yana ƙara jinjina girman kudurir Ubangiji. Tabbas addu’a ba ta bar komai ba. Idan yau ka yi ba ka ga biyan bukata ba, gobe idan ka yi sai ka ga biyan buƙatar har ya zarce zatonka. Wani imani ya kara nutso a cikin zuciyarsa, har bai san sa’adda ya matsa sosai jikinsa yana shafa kansa ba.

“Bari mu sauka, za ka ji komai. Amma lalle ne matarka da kake ambato. Yau shekaru uku ke nan mu kanmu ba mu san inda za mu nemo ma ita ba. Kana cikin halin rashin lafiya ne. Ni kuma ka ɗauke Ni a matsayin mahaifinka.”

Shiru Haroun ya yi yana sauke wani irin numfashi. Haka kawai yaji kalmomin Dattijon sun saka masa nutsuwa. A hankali ya sauke idanuwansa saman fatar jikinsa. Ya ga yadda ta yi kyawu tamkar yana rayuwa cikin wata ni’ima. Tufafin jikinsa kansu ba zai iya tuna ko haƙoransa zai siyar ba, za su iya kawo masa irinsu.

Sun sauka kasar ta Masar a cikin dare. Shi dai kawai bi yake duk inda aka nufa da shi. Ba wai fahimtar komai yake yi ba. Yana dai bin umarni ne kamar yadda aka umarce shi
da ya bin. Sun isa masauki cikin hali na gajiya. Dan haka inda aka nuna masa da na san nan ya shige shi ma. Ya kwanta da tarin tunanukan me ke faruwa?

Da Safiyar Allah Dattijon da ya kira kansa da Mahaifinsa ya kira shi.

A bayan shiru na tsawon lokaci ya fara masa bayani.

Ban san menene farko ba. Sai dai abin da na sani a garin Sokoto na ganka. A cikin wani dare da yan fashi suka tare mana hanya. Ku kuma kun taho kan bayan a kori kura. Mai Akuri kurar ya juya, kai kuma ka sauko domin kawai ka taimake mu. A sanadin haka suka harbe ka a kafa. Yanzu da za ka duba za ka ga tabon harbin. A bayan ka watsa su kuma, na tambaye ka inda za ka je ka ce ba ka sani ba. Na tambayi Sunanka ka ce Haroun Ali. Kana da mata, Da na tambaye ka ka san ina ne nan inda kake ka ce a’a, garinku ma ka ce baka sani ba. To ka ji dalilin da yasa na gane tabbas ba ka cikin nutsuwarka. Dan haka na wuce da kai gidana. A bayan na sada ka da Asibiti, suka yi bincikensu kan kwakwalwarka, ya nuna lafiya kalau kake. Wannan dalili ne ya sa mai dakina ba da shawarar a gwada gurin Malamai. Anan muka da ce da wani Babban Malami. Shi ya tabbatar mana da Sihiri ne jikinka mai karfin gaske. Wanda dole sai an bi a hankali. To, tun daga lokacin ake maganin. Ba ka tuna garinku ba sai da ka yi shekaru biyu tare da mu. Anan muka saka ka gaba ka kaimu har gidanka da ke lagos. Sai dai kaki shiga ciki. Tunda muka tunkari gidan ka dakata. A ka yi juyin duniyar nan kaki shiga. Anan Na sa yaro na ya fasa kofar muka shiga ciki. Babu wani abu da ke nuna ana rayuwa gidan. Sai ma tulin kaya da aka jibge gefe kamar dai mai gidan ne ya yi haka. Ba mu dau komai ba sai wasu file na takaddunka da yaro na ya gano. Daga haka muka baro garin. Har kuma wasu lokutan suka shuɗe ba ka kara cewa mu koma ba. Ka ci gaba da rayuwa da mu. Har zuwa wancan watan da malamin ya tabbatar mini ya gano makarin sihirin da ke jikinka. Shi ne a dauke ka daga kasar ta Nijeriya gaba daya. To ka ji dalilin da yasa na ta so da kaina domin na kawo ka nan Masar ko karatu ne ka yi zai maka amfani gaba. Amma idan ba ka so za ka iya yanke duk hukuncin da kake so.

Shiru ya yi yana jinjina girman lamari. Ya gano. Ya kuma tuno. Gata nan ma tana masa gizo da tsohon ciki. Ga wani Almajiri nan cikin idanuwansa a lokacin da ya bude kofa. Ya tuna wata fura da ya mata muguwar kurɓa. A tun ranar kuma bai zai ce ga komai da ya faru ba idan ba yau ba. Inaaa! Ba zai zauna ba. Quraisha ta fi komai da Komai gurinsa.

“Alhaji na gode da karamci. Amma ka maida ni. Matata da tsohon ciki na barta.”

Murmushi Alhajin ya yi yana ganin yadda wutar so ke rurarsa.

“To ba mu kwatancen inda za a samo ma matar taka, idan dai ita ce zansa a kawo ma ita, amma kam waccar ƙasae ba ka koma ta yanzu. Ba ka san wahalar da muka sha ba ne kan ciwonka. Ka zame mini tamkar dana, babu yadda za ai na barka ka tafi”

Shiru ya yi yana jin ba zai iya musa mishi ba. Dan haka ya zano mi shi kwatancen inda da za a ga Quraishar. Har kauyensu bai bari ba. Sosai Alhajin ya tada mutane a dubata. Sai dai har tsayin sati guda labarin daya ne babu labarin Quraisha. A ƙauyensu ma sun tabbatar suma ganinta suke son yi. Yo Shekara uku ne fa ba kwana uku ba. Shi kansa mamaki yake yadda ya ƙiƙe kan za a gano ta.

A bayan an hada da rokon ALLAH ya fara rage damuwar neman nata. Ya zauna a Masar kamar yadda Alhajin ya umarce sa. Ya mai da hankali kan karatunsa har ya isa ga matakin PHD. Anan ya kulla aminta da DR. Isma’il Kanawy. Wanda shi ma ke karatun likitanci a nan ƙasar.

A takaice bai dawo Nigeriya ba sai a shekara ta tara da tafiyarsa. Idan ka hada da ukun da ya yi a bayan ya bar Quraisha. Shekaru goma sha uku ke nan!

Satinsa guda da dawowa ya tafi Lagos, har kofar tangamemen gidan Barikin. Ya ja ya tsaya yana kallon kwawawan yaran da basu gaza shekaru 13 ba na wasa.

Dayar da hasken ta ya ciza ita ta fara tahowa gare shi. A murmushinta ya ke hasaso fuskar Quraisha ciki. A tsayuwarta kuwa yake ganin kamar ma shine. Tsaki yaja jin ya tafi wani shirmen  tunanin. Dan haka da irin murmushinta ya tsaya yana kallonta ganin tana masa gatsine.

“Aunty Linda ta hana masu kalar larabawa zuwa gidan nan. Dan haka ka tafi kafin tazo.”

Murmushin ya yi yana duban dan bakinta.

“Mai sunanki?”

Sai da ta sake masa gatsine kana ta amsa.

“Quraisha. Ka tafi gobe ma za mu koma Kano gaba ɗaya an tashi anan.”

“Karya take, Reza sunanta. Ni kuma Ree”

Dayar yar matashiyar yarinyar ta ƙaraso.

Ita ce kuma ta kauda masa tunaninsa na abin da da ya kusa mantar da shi me yake yi.

“Quraisha!” Ya furta a ƙasan zuciyarsa yana jin kamar ma ya dauke ɗiyar ya tafi da ita tunda sunan matarsa gare ta.

Kai ku yi cikin gidan ku haɗa abin da za ku iya haɗawa kunji ko.

Riƙaƙƙiyar Ƙaruwar ta ƙaraso, Linda ba,  tana furtawa a bayan ta watsa wa yaran harara. Da gudu suka juya cikin gidan dan cika umarninta.

Ita kuma ta tako gabansa tana hadiyar yawu tun daga nesa..

“Fatar Ni ka zo nema?”

Ta furta tana ƙoƙarin shigewa jikinsa.

Da sauri ya yi baya yana jan a’uzuiyya.

Kafin kuma ya yi mata murmushin da ya sata jin ko da bata shirya aure ba, da wannan zai ce yana sonta, nan da nan za ta amince.

“Am, Quraisha nake nema. Dan Allah idan tana ciki ke ce mata ta zo mijinta ya zo.”

Ba dan ta gama rika da sanin duniyanci ba. Da a take zai fahimci tsantsar firgicin da take ciki. Tabbas ta gano shi. Ta taɓa ganinsa sau daya daga nesa lokacin yana kamar a hure. Inaaa! Ai ko Bitil na raye ba zata bari Quraisha ta san wannan mutumin ya zo nemañta ba. Balle ma ta san abu daya da zata wa Bitil Sadaƙatul Jariya da shi a yanzu da take kwance cikin kabarinta, shi ne ta fatattaki wannan mutumin yadda ba zai kara takowa neman wata Ashana ba. Tana tuna shekarun baya da wasu ke zuwa neman Ashanar wai daga Masar. Bitil din ke korarsu ta ce musu ba a san inda take ba.

“Ya dai?”
Ya furta, yana jin yadda yanayinta ke tafiya da bugun zuciyarsa.

Da sauri ta waiga gefe tana sharce gumin da ya jika fuskarta. Ƙara takowa ta yi gabansa, a hankali kuma ta fashe da wani kuka tana face hanci.

“Dole na fita hayyaci na. Ka tuna mini mace mafi karamci da na taba rayuwa da ita a tsayin lokatunnan. Quraisha ta mutu, shekaru goma sha uku. Ta mutu tana kan gwiwarta ta nakuda. Ta mutu tana ambaton sunanka da ka tafi ka barta. Ta mutu ita da komai nata, har abinda ta haifar. Tare suka mutu…”

Waɗannan kalmomin, sune kalmomin da ya shafe shekaru sama da biyar yana mafarkinsu. Da taimakon Abokinsa Isma’il ya fara nutsuwa. Da taimakonsa kuma ya jawo shi zuwa Kano. Har ya samu sa’ar zama Lecturer a Jami’ar Bayero (BUK), bayan kasuwanci da yake taɓawa. Bai ƙara marmarin aure ba. Duk da ga matan nan kamar sa cinye shi. Shi kam abu daya ya sani, Domin shi kawai aka yi Quraisha. Tunda kuwa ba ta nan. To ba zai iya bawa wata kansa ba. Ya gwammace ya zauna a haka nan. Babu ma abin da ke sashi jin nutsuwa a yanzu idan ba gina masallatai ba.

Shi ya sa duk unguwar da yaji ta cika babu masallaci zai yi kokari ganin an sanar mata.

A haka a duk tsayin shekarun da yayi A Kano. Babu unguwar da yake jin nutsuwar yin masallacin cikinta kamar Quarters din A Watse. Ta yiwu dan an tabbatar masa cewa karuwai ne a unguwar. Ta yiwu kuma dan yana jin duk wata karuwa kamar danginsa.

Shi ya sa tunda aka fara ginin duk sati yana unguwar. Har a yau gashi ya hadu da Matarsa a kofar ginin masallacinsa. Wannan wace irin sitfah ce?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 30Asabe Reza 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×