Skip to content
Part 30 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

Bari na saka miki ZOBEN ALƘAWARI

Ya furta, yana riƙo hannayenta.
Lumshe idanuwanta ta yi tana jin yadda gefen zuciyarta ke wani irin zafi-zafi daga tsakiya na mata wani irin daɗi-dadi, daga ƙarshe na mata wani irin zuma-zuma. Tunda take, bata taɓa jin irin wannan abin ba. Hannunsa na da wani irin maganaɗisun da ke fuzgar zuciyarta ya cilla ta wani yanayi da har ba ta so jikinsu na gogayya da na juna.

Tana wannan halin take jin yanayinta na canjawa, tana jin damuwarta na dawowa, a haka kafin ta farga ya zare zoben Haisam daga hannunta, har sai da ya yi wani haske, a hakan ya fara ƙoƙarin tura nasa, ta yi wata irin miƙewa a bayan a tunkuɗe hannayensa, a hakan ta fashe da wani rikitaccen kuka.

“Menene haka? Ka ba ni abuna. Ko yatsa daya Allah ya mallaka mini Iyakar wuƙancin da za ka mini Ke nan. Duk ya tsunnan ba su ishe ka ba sai ka cire mini nawa?”

“Ba na sonsa to, wallahi zan sa guduma na fasa shi. A kan wannan banzan abin kike kuka?”

“Ka fasa wallahi zan rabu da kai, wallahi zan iya barin rayuwarka gaba daya sanadiyyar wannan Zoben.”

Ƙanƙance idanuwansa ya yi jijiyoyin kansa na miƙewa. Tabbas zarginsa ya gama tabbata, Haisam mutum ne ɗan uwanta take raina masa hankali da wai Aljani.
Dan haka ya karasa gabanta a bayan ya danƙo kafadunta ya jijjiga.

“Na yarda duk wata karuwa ta iya makirci, ki na cin dunduniyata da wani kike ce mini Aljanine? Ta ya ya za ki damu da abin da Aljani wanda ya fi kowa iya karya a duniya ya baki? Ki faɗa mini sau nawa kika yi alaka da shi da har ba za ki iya barinsa ba? Uban me ya baki da Ni ba zan iya ba ki ba?”

Da dukkan ƙarfinta ta kwace jikinta tana rufe bakinta jin wani rikitaccen kuka ya taho mata, mijinta fa? Mijinta ke cewa ta yi alaƙa da wani a bayan ya yi baikonta? Ke nan har gobe a mazinaciya yake kallonta. Dan haka ta kasa furta komai ta juya da gudu tana ficewa daga gidan, ba tare da ta dauki wayarta ba da jakarta da ke ta ringing a can gefe.

Dafe kansa kawai ya yi yana jin tamkar zai rabe tsabar bala’in kishin da ke cinsa, zoben ya kalla ya jefarshi yana sa ƙafa ya take shi, ganin zai ji masa ciwo ya sashi yin ball da zoben ya wuce can kasan wata kujera. Wayarsa da ke ta ringing ya jawo daga Aljihunsa, ba tare da ya duba Hammad ke kira ba ya daga wayar yana buga ta da bango tamkar ita ta kar zomon. Kafin ya zauna ta Reza ma ta dau kara, ya toshe kunnensa da ƙarfi jin kamar zai zare. Da sauri ya ƙara sa ga wayar ita ma ya haɗa ta da bangon ta watse a dandanyar gurin.

A haka ya karasa dakinsa yana bugo ƙofar.

12:30AM

Idanunsa a lumshe ya tasa TV gaba. Lokaci zuwa lokaci yana jin kirjinsa yana masa nauyi. Gaba ɗaya ya kasa barci. Damuwar da ke ransa tana ƙara ninkuwa, kamar a yanzu abin ke faruwa, musamman a yanayin da ta tafi  tana kuka, yana jin zafin maganganun da ya faɗa mata na kwankwatsarsa, sai dai, akan me ba za a cire zoben ba? Tabbas ya yarda labarin da take ba shi  na Aljanin ƙarya ce. Mikewa tsaye ya yi, yana fitar da wani irin huci.

Dole ya koma ya zauna, saboda wani irin jiri da ke barazanar zubar da shi. Idanun ya mayar ya rufe ruf! Kamar mai barci.

“Quraisha ta raina mini wayo. Ta ya ya ma za ta zauna ta mayar da saurayin da take so aljani? Aljanin ma wai a cikin gidanmu ta yi ido huɗu da shi. Sai yanzu na gano dalilin da yasa ta mayar da HAISAM aljani.”

Ya furta tamkar yana fadawa wani.

Wani irin kishi ne ya ƙara turnuƙe shi, wanda har ya haddasa masa wani irin ciwon kai na gefe daya. Hannunsa ɗaya yasa ya  dafe kan, yana sake runtse ido. Duk tunanin da yake yi idanunsa a rufe suke.

“Zan yi maganinki! Ya zama dole ki zauna da ni babu Zoben, ko kuma  ki zaba! ko zobe ko kuma ni Hamoud.”

Ya ƙara faɗi a sarari tamkar zararre.

Wata iska ke saɗaɗowa  mai tsananin sanyi tana shigarsa, a hankali ta fara kaɗa labulan falon. Iskan ta ci gaba da wanzuwa, karfinta na daɗuwa tana ɗaga  abubuwa marassa nauyi.

Sannu a hankali iskar ta fara wuce dukkan tunanin Hamoud, domin da ƙyar ya buɗe idanunsa yana mamakin yadda ake iska a irin lokacin da ba na damuna ba,  abin ƙarin mamaki da al’ajabi iskar ta fara wuce yadda yake zato.

Idanunsa ya kafe akan katon plasma tv din da ke manne a falon, yana kallon, yadda iskan ke kokarin ɗauke Tvn.

Ko motsi bai yi ba, illa kafe Tvn da idanu da ya yi babu ko kiftawa.

Haisam da ke tsaye cikin iskar, ya kafe Hamoud da kallo, yana ƙara al’ajabin rashin tsoron sa. Duk da hakan ya ki amincewa zuciyarsa da ke sanar da shi Hamoud ba shi da tsoro, don haka ya sa yatsan sa ya kashe wutan falon. Tsaf! Hamoud ya ji alamun kashe wutan, amma abin ƙarin mamaki ko a jikinsa.

Haka Haisam ya dinga yin abubuwan mamaki, amma Hamoud bai motsa ba. Duk da yaso ya yi addu’a sai kuma bakinsa ya kasa ambaton komai. Cikin ƙarin jin zafi da wani kishin, ya miƙe tsaye, ya sa hannu ya mayar da komai a yadda yake, ya kuma kunna wutar ɗakin.

A take Haka iskar ta tsaya cak!

Haisam ya bayyana cikin kyakkyawar shigarsa. Sosai Hamoud ya razana, dan har sai da ya yi baya yana cin karo da Centre table ya fadi. Ganin wani yake yi da irin halittarsa, don haka ya miƙe da ƙyar yana kallon jikinsa, sai kuma ya kalli jikin Haisam. Hatta wani ɗan tabon baki da ke kusa da gashin kansa, Haisam yana da irinsa.

Hamoud ya shiga asalin abin da ake kira ruɗu. Daman irin hakan yana faruwa? Ko dai daman ‘yan biyu ne su? Kai ko ‘yan biyu suna da bambanci a wasu wuraren. Amma Hamoud ko rantsuwa ya yi ba zai yi kaffara ba, komai nasu iri daya ne. Sauransa ya yi magana ya ji irin tasa muryar.

“HAMOUD ko?” Zazzakar muryar Haisam ta furta. A cikin muryar kaɗai zaka iya tantance a halin kishi Haisam yake. Shi kuwa Hamoud daskarewa ya yi, yana ƙara al’ajabi. Muryar Haisam ta ƙara sa masa ruɗani a cikin tunaninsa.

Ganin irin kallon ƙasƙancin da Haisam yake masa, yasa shi dawowa hayyacinsa. Hamoud baya iya ɗaukar komai, balle kuma cin fuska. Hatta irin kallon da Haisam yake masa, irinsa Hamoud yake yi idan ya tsani mutum, ko kuma yana jin zafin ka. Don haka ne baya buƙatar ƙarin bayani, domin kallon da Haisam kaɗai yake masa ya ganar da shi abin da kallon ke nufi.

“Bawan Allah, baka iya sallama ba ne? Ko baka fahimci gidan musulmai kake ba?”

Haisam ya yi matukar tunzura da kalaman , har kana iya jiyo yadda kirjinsa ke bada sauti.

“Ka ci DARAJA ƊAYA tak! Da kayi da na sanin furta min kalamai masu kama da irin wanda ka yi yanzu.”

Da alama shi ma Hamoud ya kai iya ƙarshe, don haka ya miƙe sosai da niyyar gasa masa maganganu son ransa. Sai dai, kamar an sa cingam an liƙe bakinsa, haka yaji ya kada furta komai, dole kawai ya zuba masa idanu.

“Ba ka da ikon gaya min magana. Baka isa ba! Kuma ba a yi ka ba. Idan kana ji da zafin rai, sai in ce gidansa ka zo. Ya zama dole ka saurare ni, ya zama dole ka saurari duk wasu maganganuna marasa daɗi. Kai ya kamata ka saurare ni, don baka isa in saurare ka ba. Ka ci sa’ar gaya min magana, bana tunanin zaka sake aikata kuskuren nan.”

“A yadda kake zato ke nan! Ka yi kaɗan ka biyo ni gidanmu ka yi tunanin zaka iya gaya min magana in kyale ka. Kai waye? Me kake taƙama da shi? Kudi? Kyau? Mulki, ko kuwa ilmi? Ka adana su, a wuri guda, domin ni ma ina taƙama da su. Me kuma zaka nuna min? Zan saurareka ba don ka isa ba, sai don darajar fuskata da ke tare da kai.”

Hamoud ya tsinci bakinsa da buɗewa, ya kuma tsinci muryarsa da gaya wa mutumin da har yanzu yana mamakin kasancewarsa mai kama da shi magana.

Idanun Haisam sun ƙanƙance saboda ɓacin rai. Mamaki ya kasa barinsa ya sake furta komai. Lallai bai taba ganin wanda baya tsoron aljanu ba irin Hamoud. Ya yi mamakin yadda ya rufe masa baki, amma saboda masifa da baƙin kishi na cinsa sai da ya furta.

Murmushi ya yi, wanda iyakarsa fuska. Wuri ya nema ya zauna. Hamoud ya tsaya kawai yana kallonsa. Hatta murmushin su iri ɗaya, tafiyarsu iri daya, zaman da yake yi, irinsa Haisam ya yi.

Sannu a hankali ciwon kansa ya ci gaba da tsananta. Da idanu kawai ya raka Haisam.

“Sunana Haisam! Wanda kake tantama akan kasancewarsa aljani. Kai kuma ka kira ni, dalilin cire zobena da ka yi daga hannun Quraisha. Har abada ba zan daina faɗa maka ba, ka ci DARAJA ƊAYA tak! Da na ɓatar da kai.”

“Babu wanda ya isa ya ɓatar da wani sai Allah. Ba na tunanin kana da abun da zaka iya batar da ni a wannan ɗan tsugunnon naka.”

Hamoud ya furta cikin huci, da jin zafin sa. Sosai yake jin tsanar Haisam a ransa.

Murmushin ya sake jefa masa. Sannan ya miƙe ya nufi taga kamar mai son tuna wani abu.

“Na kasance a cikin gidan ku. Kuma a nan wurin na haɗu da Quraisha. Ina sonta, son da ba na jin bayan matata Hajjatee akwai na biyunta. Zan faɗa maka haka ko da za ka mutu…”

A hasale ya ɗago, yana watsa masa wani irin kallo, sai dai ya kasa ce masa komai, illa idanu da ya zuba masa.

“Na daɗe a gidanku. Sau tari kana ajiye kuɗi, sai in sauya masu wurin zama, kana ajiye abinci, kafin ka dawo zaka sami abincin ba inda ka ajiye ba. Da zarar ka shiga dogon tunani, nake ɓatar da tunaninka. Akwai lokacin da kake tafiya a hanyarka ta shiga Kaduna, barayi suka tare hanya. Haka kawai na ji sha’awar in bika ni ma in bai wa idanuna abinci, sai na tarar da ‘yan fashi, har sun tare ka, sai kuma ka ga sun gudu. Ni na kore su.

Ka tuna ranar da mahaifiyarka ta kirawo ka  ɗakinta, har kuka yi magana akan kawunka? To ba da mahaifiyarka kayi magana ba, da ni kayi magana. Na kasance a tare da kai, wanda ban san dalilin da nake bibiyar rayuwarka ba, kuma nake taimakonka. Duk da nafi tunanin saboda kamanninmu ne…”

Cikin mamaki Hamoud ya yi saurin tarar numfashinsa, “Allah ke taimakona ba wani gardin Aljani ba. Duk abin da ka ga bai faru da ni ba, Allah ne bai hukunta hakan ba. Da Allah ya rubuta ‘yan fashi ne ajali na, ba na tunanin ka isa ka hana su.”

Haisam ya haɗiye wani abu mai ɗaci, yana girgiza kansa.

“Haka ne. Allah ya kareka, ni kuma na zama sanadi. Wasu abubuwa sun faru bayan bana nan, ka sa hannu ka mari Quraisha ba tare da haƙƙinta ba, ka wulakanta ta, ka kirata mara hankali, ka ce mata daƙiƙiya. Ina son ka sani, Quraisha bata tabɓ sonka ba, bata taɓa saninka ba, don kai baka da ce da ita ba. Baka da tausayin da zaka iya fahimtar da mutum abin da bai fahimta ba. Ka sani fushi da cin fuska kwata-kwata bai kamace ka ba, ba su bane hanyar ganar da mutum kuskurensa.”

Hamoud ya haɗiyi wani irin miyau mai ɗaci.

“Ka tabbatar bata taɓa so na ba? Me ya sa baka aureta ba? Ai za ka iya aurenta ka hana kowa kusantar ta. Na aikatawa Quraisha hakan ba a cikin hayyacina ba. Don bana jin na taɓa cin mutuncin wata ‘ya mace, bare macen da take ikirarin tana sona. Yanzu kuma na fahimci dalilin da yasa ka zo ka same ni. In dai Quraisha ce ka tafi ka aureta na barta. Bana tunanin ina da karfin halin da zan iya haɗa son mace da wani, wanin ma Aljani.”

Maganganun Hamoud sun kai matuƙa a fusata Haisam, ta yadda ya dinga danne ɓacin ransa, domin ba zai so ya ɓata wa Reza rai ba. Yana nan a kan bakansa ba zai taba amincewa da hannunsa ya cutar da ita ba.

  Sannu a hankali ya warwarewa Hamoud dukkan rayuwarsa, da kuma dalilin da yasa ya bar Quraisha, da kuma rokon da ya dinga yi mata akan ta kula Hamoud a matsayin masoyi, duk da wulaƙanta ta da ya yi a idon duniya, har izuwa maganar da ya yi mata, na zai zo ya yi wa Hamoud bayani.

Gaba ɗaya jikin Hamoud ya yi sanyi, wani irin zufa ke keto masa ta ko’ina. Tausayin Haisam ya dirar masa a karo na farko.

Lallai samun irin Haisam a cikin Aljanu akwai matuƙar wahala. Wane Aljani ne zai so abu ya kuma sadaukarwa wani? Haisam ya sami dama da zai iya cutar da Reza musamman idan aka yi la’akari da rashin Sallar da bata yi, amma ya kasa aikata hakan. Haisam ya dauki ragamar gyara rayuwar Reza. Kuma shi ya taimaka masa wajen samun macen da yake jin ƙaunarta har cikin ransa. Shi ya tsamo Rezs daga rayuwar karuwanci.

  Nadamar maganganun da ya gaya masa suka dirar masa. Musamman da ya fahimci Haisam yana da matukar haƙuri, kishi kawai ke damunsa, wanda ya zama dole ya yi kishi.

“Ba lallai ku sake ganina a rayuwarku ba, dalilin zuwana gareka a yau shi ne in roke ka, ka barta da zoben nan don Allah. Sai maganar da na faɗa mata zan sa ka so ta, kawai na faɗa ne ba tare da zan iya yin hakan ba. Amma da yake Allah ya rubuto dole sai ka so ta ɗin, sai gashi soyayyarta ta ratsa dukkanin ilahirin jikinka. Ita kanta tana ikirarin bata sonka, bata san soyayyarka ta yi mata mugun kamu ba, bata san ba zata taba iya rayuwa babu kai ba. Yau na zo maka da kokon bara na, ina fatan zaka yi min wannan taimakon?”

Jikin Hamoud ya ƙara sanyi,  yana ji ina ma yana da abin da ya fi wanda Haisam ya roka, ya tabbata zai iya yi masa mafiyinsa. Abubuwan sun faru kamar tatsuniya, ko kuma a cikin mafarki.  A haka ya tsinci kansa da miƙe wa, ya riƙo hannun Haisam. Wani irin sanyi ya ziyarce shi, har sai da ya ɗago yana dubansa. Rungume juna suka yi, na tsawon wasu lokuta, kafin Hamoud ya ɗago shi suna kallon juna.

“Idan akwai abin da kake bukata, wanda ya fi wannan ka tambaye ni zan baka. Ban taɓa gani ko jin labarin Aljani mai sauƙin hali irinka ba. Zan bar Quraisha da zobenka har ta mutu. Idan ta mutu, zan ɗauki zoben in ba jinin Quraisha, don ka ci gaba da ganinsa. Ka roƙe ni wani abun da ya fi wannan zan yi maka.”

Murmushi ya yi, yana mai jin daɗi a cikin ransa. A gefe guda kuma kishin Hamoud ya kasa barin sa. Ƙoƙarin boyewa ya yi, don yasan Hamoud yana fahimtar ko da tarinsa ne. Kasancewar jikin Hamoud yana jikinsa. Komai na su iri ɗaya.

“Na gode Hamoud. Babu abin da nake buƙata da ya wuce wannan ɗin. Sai kuma nasiha, ka rike Quraisha amana. Ka zama mai haƙuri. Na gode ni zan wuce. Sai watarana.”

Hamoud yana tsaye kamar wanda aka dasa yana kallonsa.

“Ina neman wata alfarma.” muryar Hamoud ta ratsa ko ina dake cikin falon. Cak! Haisam ya ja ya tsaya.

“Kada ka nisance mu. Kada ka tafi ka bar mu. Za mu so mu yi rayuwa da kai.”

Ya ji daɗin furucin Hamoud, sai dai kuma a wani ɓangaren, yana yi wa Hamoud kallon wanda ya sha wani abu. Idan ba haka ba, ta ya ya zai yi tunanin zai iya rayuwa yana kallon wani a kusa da Quraisha? Lallai yana son wataran zuciya ta sa shi  ya kashe shi ke nan. Yana wasa da irin son da yake yi wa Quraisha.
Girgiza kansa ya yi.
“Kayi hakuri. Zan je in fuskanci mulkin ƙasa ta. Mutane na suna buƙata ta a kusa. Ƙila watarana in kawo maku ziyara.”

Yana gama faɗin hakan ya ɓace cike da wani irin kishi. Hatta wurin da ya ɓace tururin hayaƙi yake yi.

Hamoud ya lumshe ido yana kara al’ajabin wannan lamari.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 29Asabe Reza 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×