Skip to content
Part 3 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

“Sajen Garba!

“Yes Sir!” Kakkauran baƙin mutumin ya amsa yana sara masa.

“Shigo mini da waɗanda ka ce an kawo daren jiya sun shiga gidan Alhaji Saleh Tumbi.”

“Sir, karuwan gidan Kankana ne, shi ya sa nake ta cewa a rufe gidan tun kafin su kai ga mamaye ƙasarmu da fitina. Yanzu ga Alhajin nan a asibiti sun karya masa hannu. Ka ba ni dama kawai in tashi da babbar tantiriyar ta su Ashana….”

“Watch ur tongue, idiot! Ba surutun banza na tambayeka kayi min, ka shigomin da ita babbar.

“Okay Sir!” Ya faɗa cikin mazari yana mai juyawa da sassarfa.

Laɓɓansa na ƙasa ya tura duka cikin bakinsa yana nazarin abin da ya kamata ya yi, bai san me zai ma ta ta gane baya son ganinta cikin irin waɗannan lefukan ba, yana ma ta so ba na wasa ba wanda ko uwargidansa ba ta samu kwatar sa ba. Zai kashe koma nawa ne domin ta bar sata duk da baitaɓa samun abin da yake so kanta ba, a cewarta bakinsa ya cika girman da ba za ta iya jure ko da kallonsa ba, haka tsagun da suka cika fuskarsa a matsayinsa na ƙabilar ogbomoso sun taka muhimmiyar rawa wurin da sa ƙyankyaminsa a dukkan ruhin Ashana. To, ƙa ƙa zai yi? Ba lefinsa ba ne shi kam, na uwarsa ne da ta auri mummunan ubansa har ta bari aka haifeshi yana mai ƙin barin ko da farcensa ne.

A haka ta shigo ta same shi ya yi nisa cikin tunanin, gyaran murya ta ɗanyi ya ɗago yana dubanta, sai kuma ya dubi ɓarin da Sajen Ƙoza ke ƙame, da kallo guda ya juya yana mai rufo musu ƙofar.

Kujerar da ke gabansa ya nuna ma ta da ta zauna, ba ta zauna ɗin ba sai a wacce ke girke gefen hannunsa na hagu.

Bai damu ba ya ɗaga gorar ruwansa yana mai zubawa cikin tambulan ɗin da ke gabansa, a hankali ya miƙa ma ta ta karɓa tana mai yatsine fuska.

Shiru suka yi, sai can ya ɗago yana mai ɗora ma ta mitsi-mitsin idanuwansa masu kama da kwan Tsaka.

“Why?”

Ya furta yana mai danne abin da ke taso masa tundaga yatsan ƙafarsa yana faffarka duk wata jijiya ta jinin jikinsa.

“Ka sani ina da abin da ya shallake tunanin mai tunani, ba mu shiga dan ƙudinsa ba sai dan rashin kunyar da ya yi gareni…”

Ta dakata tana fesar da numfashi me zafi, yana gane yadda take kokawa da dukkan ɓacin ranta.”

“Soupy ya ɗaga ma hannu saboda ta masa ƙaramin abin da ni zai faɗawa na ɗauki mataki amma ya yi biris, ya nuna shi namiji ne mai ji da mazantaka. Ba zan taɓa ɗauka ba Officer! Ba zan taɓa ɗaukar abin da zai rage darajar gidan da duk wacce ka gani ciki akwai kalar rayuwar da ta kawota cikinsa. Da mutuncinsu da yancinsu na ‘ya’ya mata suke neman abin da za su rufama kansu asiri da dukkan gangar jikinsu. Ya za ai ka ɗaga ma wacce ka gama sakin goho da ihu hannu? Saboda ba ‘ya’ya ba ne? Ko kuwa dan ba a gansu cikin suturarsu ba? To Ni ce Suturar kowacce karuwar da ta zo neman abin da za ta ci da matantakarta! Shin kana tunanin zai taɓa dubanta idan da sunkwiyawa ta yi ƙasan fason ƙafarsa tana roƙonsa ya ba ta abin da za ta ci? Ko kuwa zai taimaka ma ta a yayin da take halin larura? Saboda haka ba zan yarda ba, KARUWAI WAI MA ‘YA’YANE a gareni.”

Yadda kalamanta ke sauka cikin kwakwalwarsa suna zarcewa cikin zuciyarsa da ke wata irin sanyaya ke ba shi mamaki. Tabbas ya gane dukkan zafin da take ciki, sai dai shin ta san haɗarin da ta jefa kansu ciki na taɓa Alhaji Saleh?

Numfashi ya furzar mai zafi yana ƙin kallon fuskarta.

“Kin san wa kika taɓo kuwa?”

“Na sani, sai dai ba mu muka ce ya zo ba har a kai ga hakan.”

Shiru ya yi yana mamakin taurin kanta.

“Yanzu ina abin da kuka ɗauka suke? Ku dawo da kome hakan ne zai ba ni damar sassauta lamarin.”

Murmushin da ba shi da alaƙa da yanayin da take ciki ne ya kufce a gefen kuncinta. Ta tsaida dubanta a cikin idanuwansa masu cike da fitina tana ƙara jin yadda ƙyanƙyaminsa ke damalmala ruhinta.

Ka da ka yi tunanin wannan zai zama damuwa a gareni, za a dawo da su, fatana dai ka yi abin da za ka samu wani matsuganni ko ya ya ne a zuciyata. Ka yarda da Ni, zan iya baka wasu awannin daga lokutana ko da hakan na nufin mutuwata ne yayin harkar!”

Ta faɗa da dukkan zuciyarta tana masa wani kallo mai wahalar fassara.

Ya ji baƙar maganar da ta gasa masa a ƙarshen zancenta. Sai dai shekara biyar ɗin da ya kwashe yana bibiyarta ba zai barta ta kufce a awa biyar ba.

Da abin da ya ɗauka murmushi ne yake dubanta, kwaɗayinsa na ƙara fitowa zahiri saman mummunan fuskarsa.

“Ku tafi na ba da belinku, ki ba Ni awanni(48) zan shafe zancen tamkar shafewar Allura cikin kogi… Ki riƙe alƙawari dai!”

Bai san ta zo kusa da shi ba sai da ya ji saukar tattausan leɓunanta saman goshinsa ta masa sumba, bai san a wacce duniyar yake ba tsakanin sama da ƙasa, ya ga dai lokacin da ta juya cike da yauƙi tana mai buga masa ƙofar saman fuskarsa.

“Kamar na daɗe da mutuwa?”

Ya faɗa yana kaima kuncinsa mintsili, a hankali kuma ya shafo goshinsa daidai gurin, hannun ya tura duka bakinsa yana tsotso.

A dukkan bugu na zuciyarta shi ne ke mata gizo a saman fatar idanuwanta. A dukkan kuma ɗaga kofin ruwan da za ta yi dan ta sha shi ne ke bayyana saman ruwan har sai tana rufe idanuwanta da murmushi. Ba ta san haka garɗin so yake ba sai yanzu da ta tsunduma cikinsa.

Tafiya take a daidai lokacin da agogon hannunta ya nuna ƙarfe 7:30 na dare ne ta wanzu a nesa kaɗan da shagon, lafewa take yi cikin duhun maghribar tana ƙara kafe idanuwanta kan ƙofar.

Zuciyarta ke azalzalarta da ta je ta buga ko zai buɗe ta faɗa masa abin da ke rayuwarta game da shi, wani abu ke danneta kan ta bi a hankali zai fito, ba ta san yarda yiwuwar alaƙar Karuwa da Limami zai faru a hankalinta ba.

Cikin halin shauƙin da take ta ji ƙarar ƙofar na buɗewa, sannu a hankali ya bayyana da kayansa irin na jiya, tsaye ya yi ƙofar shagon yana duban sararin samaniya kamar wanda aka ce ya fito dan ya san a kwai mai son ganinsa.

Nutsuwarta ke neman gagararta saitawa, abubuwan da ke dukan zuciyarta game da shi ke neman fasa kirjinta su sata zuwa gabansa ta durƙusa ta roƙeshi dan ya aureta.”

A hankali take jin wani garɗi-garɗi na cika bakinta suna zarcewa maƙogwaronta suna samun matsuganni can cikin tumbinta, hannu ta kai fuskarta cike da ɗumbin mamakin abin da ya sata hawaye, ita Ashana da rabonta da kwalla tun ranar da take naƙudar ɗan da ta bari…

‘Kukan na menene?’

Take tambayar kanta tana ƙara kallon in da yake.

A jikinsa ya ji ba shi kaɗai ba ne a ilahirin gurin, dan haka ya sauke kansa a hankali yana mai ƙurawa inda zuciyarsa ke hasaso masa da ido.

Ganin babu kowa ya sashi gyaɗa kai yana nufar ɓangaren massallacin da yake limanci yake.

Hannu ta miƙa daga inda take ɓoye kamar za ta ce ya tsaya ta. A hankali kuma ta juya fuskarta ɗauke da murmushi zuwa inda ta fito.

Satuttuka ta kwashe ba ta fasa zuwa ƙofar shagonsa ba dan kawai ta hangeshi daga nesa, ita kaɗai ta san maganin da hakan ke mata a dukkan ruhinta. Akwai wani abu da ke ba ta mamaki na yadda duk lokacin da ta je shi ma zai fito ƙofar shagon ya ɓata lokuta a duban sararin samaniya. Tana ji a ƙasan ruhinta kamar akwai wata zaunannar damuwa da ke damun masoyin nata.

Yau ita kaɗaice a ɗakin da ke ta kori duk wasu abokan harkarta da ta san za su shiga tsakaninta da tunanin mutumin da ta kira da Ruhinta. Wani abu ke azalzalarta da taje kawai domin ta ganshi a wannan farar Asubahin, miƙewa ta yi da sauri ta hau mai da riga da wandon felan da ake ya yi a wancan lokacin, da gaggawa take ƙoƙarin ficewa daga gidan.

“Maa?”

Sautin muryar Soupy ya ratsa kunnuwanta.

Juyowa ta yi tana duban abin da take nuna ma ta na lokaci, ƙa’idar gidance ba a fita ƙarfe 4:30 na dare.
Gyaɗa mata kai kawai ta yi tana ƙarasa ficewa da sassarfa.

Da ido take bin bayanta, tana sane da halin da uwarɗakin nata ke ciki duk da bata furta ba, tabbas alamunta sun gama nuna tana cikin wata irin soyayya me wahalar samuwa, ko wanene? Oho.

Yatsine fuska ta yi tuna abin da bai shafeta ba ne.

Da dosuwarta ta hangi wucewarsa cikin layin da mutane ba su cika bi ba. Ƙirjinta ke bugawa na rashin sanin abin da zai kai shi gurin. A sannu take bibiyarsa tana kula da motsinta har suka iso gurin me yawaitar bishiyoyi, busasshen ganyen da ta taka ne ya ankararshi ba shi kaɗai ba ne.

Ganin ya dakata ya sata saurin lafewa a jikin bishiyar da ke gefenta, juyowa ya yi yana ƙarewar hanyar kallo, ganin wata mage ta fita aguje ya sa shi tunanin motsinta yake ji.

Sai da ta tabbata ya nausa ta fito, mamaki na sake kasheta kan abin da ke sashi ƙara nausawa cikin daji da ba ta taɓa zaton wanzuwarsa a gun ba. Da ƙamshin turarensa da ya cinye dukkan lissafinta ta gano in da yake.

Zaune yake ƙasan ‘yar kututturar bishiyar da ta saura ita kaɗai a fadin gurin. Fuskarsa ɗauke da wani irin yanayi yana duban huddajjen sau cikin dake ƙafarsa, Naira Hamsin ɗin da ta rage masa a duka duniyarsa yake jujjuya, tunaninsa ya cure kan abin da zai yi da ita, sabulun wanki zai siya ko kuwa abinci zai ci?

A hankali ya ji saukan numfashinta tana mai zama kusa da shi, kyakkyawan gashinta da iska ke kaɗawa ya lulluɓe rabin fuskarta, a shekaru da wahala ya ba ta uku.

“Auzubillahi Minashshaiɗanir Rajim!” Ya ambata yana mai komawa gefe, ya santa farin sani, yana yawan ganin hotunanta a jikin Taxi ko Bus, Quraisha Ashana tantiriyar karuwar da ta gagari gwamnati ce zaune kusa da shi.

“Karka gujeni dan Allah! Ba shaiɗan ba ce Ni. Tana jin yadda hawaye ke sauka akan silin kumatunta suna wucewa can cikin bakinta.

Allah ya sani ba za ta iya jure ƙin da zai gwada ma ta ba, ba za ta iya zama yana ƙyama tar ta haka ba. Tana jin yadda zuciyarta ke wani irin kumbura. Ba ta taɓa tsanar sana’arta ba sai yau da ake neman tsari da zama kusa da ita, ita kaɗai tasan yarda kalmomin suka danne duk wani kwarin gwiwar da take da shi.
Siririn gyalenta ta sa tana goge hancinta da ke yoyo.

“Ƙaddara ce ke sawa ka haɗu da wanda zaka rayu kana fatar kasancewa dashi har ƙarshen rayuwarka. Haka ba ka da cikakken sanin dawa zaka kasance, shi ɗin ko wani? kuma baka da masaniyan lokacin da hakan zai faru. Amma na tabbata Ƙadr ɗinka na nan tana jiranka kazo. Dan haka ka yadda Ni ce, ka kuma bawa soyayyata damar da zata samu hanyan shiga zuciyarka, kai kaɗai tawa zuciyar ta sani, ta kuma ba ta wannan damar.”

A cikin sautin muryarta yake jin tsoron tabbatuwar tunaninsa. Tabbas wannan kyakkyawar matashiyar a buge take, idan kuwa ba haka ba to anyi harka ba a biya ta ba, ko kuma an samu wani kwarton da ya mata mugun dukan da ya datse lissafin hankalin da ke kwakwalwarta ta zo tana masa zancen banza irin na mutanen banza.

“Na roƙe ka, ka aure Ni domin Allah!”

Ya ji kalmomin sun shiga kunnuwansa da wata irin kuwwa suna zarcewa can cikin ruhinsa. Bai san sa’adda ya juyo gaba ɗaya yana kafeta da manyan idanuwansa ba.

Sadda kai ta yi, wani abu ta ji na ƙara sanyayya gudun jininta, rana ta farko da ta kasa haɗa ido da wani ɗa namiji.

“Da han…hankalina.”

Ta ƙara faɗa bakinta na karkarwa.

Har yanzu kallonta yake kamar mai naziri, sai dai a zahiri idanuwanne kawai a kanta, shi kansa da za a tambayeshi bai san kalar tunanin da yake ba.

Akwai wani rauni a idanuwanta da ke danne duk wani abu da ke ta so masa game da ita.

Zuciyarsa ke azalzalarsa da ya yi ya sallami wannann mahaukaciyar tun kafin masu zuwa cikin gari su fara wucewa ta jejin girmansa ya yi wanwar a ƙasa.

“Tun yaushe kika Sanni?”

Ya faɗa ba tare da sanin sa’adda kalmomin suka samar da kansu ba, tabbas ba wannan ne abin da yake son faɗi ba.

“Wata biyu yanzu, menene sunanka?”

A dukkan buɗe bakin da za ta yi da irin mamakin da take sake wanzar masa.

‘Ba ta ma san sunansa ba take cewa tana sonsa?’

Wani tsaki ya ja a ƙasan zuciyarsa.

“Haroun Ali!…”

Da gefen ido take kallonsa.

Ba auren karuwa ba ne matsalar, tarbiyyar da za ta ba ‘ya’yan da ta samu da kai, me sunanta?”
Ya faɗa yana mai ƙin dubanta.

Tana jin yadda kalmomin ke ratsa dukkan ɓargonta, tana jin yadda zuciyarta ke wani irin dahuwa, ba ta taɓa tunanin tana da irin wannan haƙurin ba, a hankali take ƙoƙarin mai da kwallar da ke taho ma ta.

“Zan yi kome domin na ɓatar da wannan sunan daga rayuwata, zan bar koma menene dominka Haroun!”

“Domina? Ba domin Allah da ya halicceki ba wanda kike karya dukkan dokokinsa saboda tsabar shaiɗanci, wane irin tuba ne wannan?”

Shiru suka yi na tsawon mintina, daga inda yake zaune yana iya jin bugun zuciyarta.

“Ki ba Ni lokaci zanyi tunani, zanyi istikhara kan lamarin.”

Ba ta ce kome ba ta miƙe, harta fara tafiya sai kuma ta juyo tana dubansa cike da karaya.

“Nan da yaushe zan dawo dan jin muhallin da nake?” “Nan da shekara Biyar!”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 2Asabe Reza 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×