Skip to content
Part 33 of 33 in the Series Asabe Reza by Fulani Bingel

HAMOUD

12:00PM

Ta masa kofar gidan. A hankali yake takawa yana jin nauyin abinda ya ma Amaryarsa na kara danne shi.

Surutu ya ke ji sama-sama dan haka ya karasa da sauri ya kwankwasa ƙofar.

Hammad ya bude. Aiko kawai ya cafke hannunsa ya na jansa. Bai dire shi ko’ina ba sai gaban Haroun. A kunnensa ya rada masa.

“Kai ka yi ladab, surukinka ne, Baban Juliet.

Fuskarsa ta fadada da murmushi yana kallonsa. A sannu ya fara kai gaisuwa. Haroun na amsawa cike da farin ciki, sosai ya yaba da zabin yar tasa.

Ya mike zuwa gaban Mama Ashana ita ma, an mata kwalliya sosai, Soupy Harda shafa mata barbada kumatu, kamar ba marar lafiya ba. Ita ma gaisuwa ya mata da tambayar ta jikin. Ka na ya mike yana watsa idanuwansa falon ganin babu Reza.

“Ka karasa, tana ciki.”

Muryar Soupy ta ratsa shi da yaji kamar ya mata likin Dollar

Ɗaga kafar ya yi da kyar yana jin kamar duka idanuwansu na kansa, a haka ya karasa ya tura kofar dakin yana mai fadawa ciki.

Tana zaune gefen mirror tana shafa jambaki. Sarai ta ji zuwansa, kawai share shi ta yi.

Karasawa ya yi. Kafin ta yi aune gaba daya da gata sama yana goge jambakin da kuncinsa.

Ba ki ta bude cike da masifa za ta yi magana. Caraf! Ya cafke bakin. Tun tana son kwacewa har ta haƙura tana jin jikinta na mutuwa.

A hankali ya cika ta, sanin inda yake.

Numfashi ta ja mai karfi tana harararsa.

“Allah ba zan hakura ba, Ni kake zargi…”

Labbansa da ta ji saman nata ne ya sata hadiye kalamanta. A hankali ya dago, Yana janta cikin jikinsa baki daya. A cikin kunnuwanta take jin zancensa.

“Dan Allah karki ce komai, ki yi shiru kinji, na daina.”

“Hm! Ta furta a hankali.

“Please karki ce komai.”

“To,”

Ta furta tana kara narkewa jikinsa.
*

Mun gama magana da Isma’il kawai ita Quraisha ta tare gidanta yau ko gobe, bansan wata hidima da Allah. Idan za su yi walima can ta yi da mijinta. Tunda an daura auren bansan kuma zaman me take muku nan ba. Ke ma kinga aure za ki yi Safiyya. Ni kuma zan dau Quraisha Babba mu tafi Jeddah ko za a da ce a can. Ya ce akwai asibitin da suke da sani kan ciwonta sosai can ɗin.

Haroun ya furta yana kallon Soupy.

A daidai nan kuma Alhajin Hammad ya shigo.

Sun gaisa sosai, kafin ya fadawa Soupy ya daga auren aurensu zuwa sati guda. Saboda Hammad ya masa magana jiya shi ma a ba shi Humaisa.

Hammad din da ke gefe yana jin haka ya miƙe da sauri yana sosa keya, ya fice yana satar kallon Mama Ashana.

Dariya suka yi gaba ɗaya, kafin kuma su ci gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da suka fice ba ki ɗaya.

Soupy da ke jira dama su tafi, da sauri ta mike ta bude dakin Linda.

Ta Na nan rashin samun wadataccen abinci ya sa har ta bushe, ta fara fita hayyacinta.

Fito da ita ta yi.

Ita dinma ba ta tanka ba. Dan tun safe suka fada mata sharrin da suka ma Fakriyya, ta kuma gama yanke shawarar abinda za ta yi.

Ba da ko ta dube su ba, ta fi ce a hankali. Mama Ashana na binta da kallo, tana iya tuna wasu alkhairanta. Tabbas komai kin da mutum zai maka, ba a manta alherinsa ko da guda daya ne, idan har akwai zuciyar kirkin!
*******
7Days ago.

High Court.

An saurari kararraki da dama, kafin a zo ta kan iyalan pastor.

Shi kan shi alkalin a bayan sauraran karar ya fara tunanin ta zare, saboda dukkan magana sai dai ta furta.

“Hahaha! Na yi losing. Allah kuwa.”

Har ya gaji zai ba da umarnin a kaita asibiti a fara duba kwakwalwarta, tukunna a dawo a ci gaba da shari’ar.

Sai kuma ita kadai aka ga ta yi shiru. A bayan jikinta ya yi wata irin girgiza tamkar wacce Aljanu suka shafa. Sai kuma ta fashe da kuka tana magana.

“Yallabai Ni na sace shi. Za mu yi amfani da shi a kungiyarmu. Na dade kuma ina sararar Hodar Ibliss”

Linda da ke gefe tana sauraren shari’ar ihu ta buga wani ihu tana mikewa.

“Karya take mai Shari’a.”

Wani irin murmushi FAKRIYYA ta mata, a bayan Lindar ta karasa jikinta.

Da sautin namiji take jin tana magana.

“Karki damu, ba ita ke magana ba, Ni Haisam ke magana, kema ki furta naki lefukun kafin na koma jikinki ki fadi yarda kika yanke harcen uwarki, kika saka a bakin gawa, saboda ta daina miki rokon Allah ki bar bariki.”

A razane da wani irin firgita Linda ta yo
baya tana nuna ta, ita kadai take ganin me take ganin. In da Fakriyya ke tsaye, taga babu Fakriyyar sai Hamoud, Hamoud dai tsohon sirikinta take gani sanye cikin wata irin alkyabba tana ta walwali.

Wani kallo ya mata, ta zura da gudu tana bangaje yan sanda da  wani irin ƙarfi  da ya zo mata, ba ta dire ko’ina ba, sai jikin kantar Alƙali.

“Kai,aa,Ina, Sam! Wallahi fa gardi ne, yallabai ba ita ba ce, kalli ka ga namiji ne. Ta fada tana juyawa, sai dai wayam babu kowa gurin, sai Fakriyya, tana ta sharar hawaye.

A hankali itama ta fashe da kuka, jin Yan sanda sun rike ta.

“To to to bari kuji, Ni ce na kashe Saleh Tumbi, Ni ce na ba shi guba.”

Gabadaya kotun ta dauki hayaniya suna dubanta.

“Af wallahi ko, ina da shaidu ma.”

Ta fada, akwai alamun rashin hayyaci jikinta.

Alƙali ya yi rubuce-rubucensa, ya ɗago ya yankewa Fakriyya shekaru 20 gidan kaso.

Yana furtawa, ta kwashe da dariya.

“Hahaha! Na yi losing. Allah kuwa.”

Ita kuma Linda ana jiran Shaidunta, an dai tsare ta.
******

Bayan Wata Biyu

AT

TEEMAH ICE CREAM AND SNACKS

RO/JU

“Wai dan Allah da gaske kike Soupy ciki gare ta? Hamoud ya furta yana kunshe dariya.

“Wai me ruwanka?Kai fa dadina da kai baka samun labari ka yi shiru.”

“A’a fa ba ruwana, kawai so nake na ga inda cikin zai zauna mata.”

Sosai ta saka dariya tana dubansa.

“To da a ina ciki ke zama idan ba a ciki ba, Abban Twins?”

“A’a, wasu fa a hanci yake zama, wasu kumatu, irin kawarki kuma Teemah Zaria a Laɓɓa yake zama, ki ga baki ya yi tudu kamar an tauna ganda

“Oh kai? Ashe kalle mini kawaye kake, yanzu yaushe Teemah ta yi  aure da har kasan inda cikinta zai zauna?”

“No kawai Ina kwantantawa ne, yanzu ina kawarki Farha? Da na ce miki idan ta yi ciki a goshi zai fara bayyana, sanda tana da cikin ba ki ga goshinta ya kara fadi ba?”

“Hamoud karka kashe Ni. Zan kai ka dai ka gano Soupy cikin satinnan, amma idan ka sake ka yi dariya, ba na kara zuwa da kai har abada.

“Ina sonki Quraisha!”

Ya furta, yana rafka tagumi da hannu biyu.

“Me zance Ni to?”
Ta furta tana langaɓe kai.

“Karki ce komai, kawai ki yi shiru, ina son shirun!

Ƙarshe.

Alhamdulillah

Asma’u 
Ummita
Husnah
Fulani
Bingel
Lamtana.
08025272635
A yafi juna dai!

Mu Hadu A Fitilar Sharri

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Asabe Reza 32

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×