Skip to content
Part 4 of 5 in the Series Ba Kauyanci Ba Ne by Ummu Adam

Gidan Su Khadija

Wayewar garin alhamis kenan bayan an tashi daga makaranta Zubaida ta wuce gidansu khadija, a can ta yi wanka ta shirya tsaf ta can-cancaɗa kwalliya kamar ba gobe; shigowar Khadija ɗakin ke da  wuya taga ƙawarta kamar amarya cikin zolaya tace “gaskiya rigar nan ta yi miki kyau kin san an ce kayan aro yafi yiwa mutum kyau.”

Zubaida tace “lalle Khadija wato abunnaki harda wulakanci, toh ki fada kowa yaji ni abun kunya gaba na bashi ba baya ba.”

Khadija tace “aiko dai wannan kalmar ba ta dace da mace ba, karki manta watarana ke uwace. Tashi mu tafi na san yanzu haka Ahmad ya isa wajen yana jiranki.

“Gaskiya kam, to muje” Zubaida ta faɗa.

Gurin Su Ahmad

Bayan sun isa gurin da suka yi alkawarin haɗuwa da ahmad sai Khadija tace “kinga ɗan halak yana cikin mota yana jiranmu”

Suna isa wajen motan Ahmad ya fito yace sai yanzu? Ai harna fara shirin tafiya dan na jima ina zaune ina jiranku sai kace bani da abun yi.

Zubaida tayi murmushi tace “toh yanzu dai kayi hakuri, kasan mata da kwalliya tun ɗazu nake gaban madubi dan kar na bayyana a gabanka bancika goma ba”.

Sarauniyar kyau gaskiya nayi sa’a, ai wannan kwalliya ko ba kice na yi hakuri ba dole zanyi” Ahmad ya faɗa yana murmushi.

Khadija ta ɗan gyaɗa kai ta yi gyaran murya tace “tunda naga kamar banda wani amfani hasalima ba’asan ina gurinba to zai fi min alkairi na yi tafiyata.”

Cikin hanzari Ahnad yace “wai dan Allah kiyi hakuri tuba nake ayi min afuwa, barka da yamma ya ya hanya kuma ya hakuri damu?”

Khady tace “lafiya lau, hakuri kuma anata yi kamar yadda aka saba.”

Khadija na zo miki da tsaraba fa ina fatan ba za ki bani kunya ba?”

Tayi mamaki tace “ni kuma?, wani irin tsaraba kenan? Allah yasa abun arziki ne dan na sanka da tsokana.”

Ahmad yace “wanna karon ba zolaya bane, amma dai bari ki ganewa idanun ki” Take ya buɗe kofar mota sai ta ga wani sarurayi kamar balarabe daganin alama dan gidan manya ne.

Zubaida na ganinshi ya fito daga mota hankalinta ya tash. Ahmad yace “khadija wannan shine tsarabarki, abokina ne ya dawo daga Sudan; ya kawomun ziyara jiya sai mu kai hiranku da shi harma ya ga hotonki a waya ta. Shi ne yace yana san ki kuka in kin amince zai aure ki.

Ni kuma kinsan bana ƙasa a guiwa wajen haɗa masoya saboda haka nace ya shirya yazo ku gaisa ki ji komai daga bakins. Dan haka ga abokina sunansa Zannurain kai kuma ga Khadija sai ku ɗan ja gefe kayimata bayanin saƙon zuciyar ka.”

Zannurain suka ɗan ja gefe da khadija suna gaisawa. To amma Zubaida sam abun bai mata daɗi ba dan haka cikin fushi Zubaida ta kalli Ahmad tace masa “kai kuma Ahmad ya haka? Kawai sai ka haɗa mutane soyayya ba ko neman shawara ta baka yi ba?”

Ahmad yace “kinga ni fa ba haɗa su na yi ba, shi ne ya ganta yace yana so ni kuma na masa jagora dan haka banga abun laifi a nanba, kuma ma ke me ye matsalarki bayan naga ita Khadijan bata damu ba kiga yanda take murmushi kin san aboki na zai samu shiga.”

Zubaida muryatta ƙasa tace “hm! gaskiya da sake.”

Ahmad yace “me ki ka ce? Zubaida tace “ba komai, kawai maganar zucine ya fito fili”
“Amma ya naga duk yanayin ki ya canza ko dai akwai wani abune?”

Zubaida tace “ba komai kawai banajin dadin jikina ne, i think gara mu koma gida yamma tayi sosai.”

Ahmad ya yi mamakin yanda Zubaida ta sauya lokaci guda, abun ya sosa masa rai amma sai ya yi ta maza “yace baku jima da zuwa ba fa; kibari suɗan gaisa mana su fahimci juna sai ku tafi.” Zubaida tace “ai sun gaisa kawai zamu mutaf.”

Ahmad yace “shikkenan, ke ki shiga mota na sai ita Khadija su tafi a motarsa sai su ci gaba da firarsu a hanya.” Zubaida tace “a’a kubarshi kawai zamu shiga napep mu koma gida.” Cikin nuna soyayya Ahmad yace “to, ai yanda ki kace haka za’ayi.”

Zubaida taɗan ɗaga murya tace” Khady zo mu tafi, kaina yafara ciwo.” Ahmad ya buɗe kofar mota ya ɗauko wata jaka ya miƙowa Zubaida yace mata “ga tsarabarki nan dana miki alkawari.”
Babu murna ko farin ciki a fuskar Zubaida haka tasa hanu takarɓa kamar ba ta so ko godiya batai masa ba.”

“Naji duk abunda kace amma ina buƙatan lokaci zanyi shawara, ka bani kwana uku za ka jini in sha Allah; amma kafinnan gaskiya sunnanka yamin tsawo dayawa zan so in kira ka da Nuur.”

Zannurain ya ji daɗin yanda Khadija ta ƙarbe shi hanu biyu dan koba komai masu iya magana suka ce “shimfaɗar fuska ta fi ta taburma.”

“kina da daman kira na da duk sunan da ki ke so Khadiha.” Zannurain yaɗan sa hanu a aljihunsa ya zaro “ƴan canji ya mikowa khadija yace “ga wannan ku biya kudin mota ammafa kiyi hakuri ba yawa.”

Khadija tace “daka barshi kawai munada shi.”

Zubaida ta yi wuf takarɓa tace “ai ba’a maida hannun kyauta baya mun gode sosai.”

Khadija ta san halin Zubaida sarai shiyasa abun da ta yi bai bata mamakiba, amma ahmad sam bai ji daɗin abunda ta yi ba.

“Allah ya kaiku lafiya, sai munyi waya” Nuur ya faɗa.

Zubaida ta amsa da sauri tace to ba damuwa.

Dawowar Khadija da Zubaida Gida

A hanyarsu ta zuwa gida suka samu saɓani saboda karɓan kuɗin Nuur da Zubaida ta yi ba tare da yardan Khadija ba.

Suna shigowa gida sai maman Khadija ta fahimci akwai matsala, sai tace “ya kun fita cikin farin ciki kuma kun dawo rai a ɓace kamar an muku mutuwa?”

Zubaida tace “mama wai dan an bamu kyautar kudi na karba shine take fushi dani wai na fiye san abun duniya kuma naga babu kyau maida hannun kyauta baya shi yasa na karɓa.”

Maman khadija ta kalli “ƴarta tace “lalle ma Khadija wato duk huɗubar da na ke yi miki baya shiga kanki ko? a zamanin nan da muke ciki har za’a yi miki kyautar kuɗi ki ce bakya so, wai ke wace irin ‘yar ƙauye ce?”

Mama na san dama laifi na za ki gani ba na Zubaida ba, ta yaya daga haɗuwan farko da saurayi zai bani dubu ɗari kuma in karba? Mama kin manta cin kuɗin saurayi bashi ne watara za’a biya?”

Maman Khadija ta kau da kai kamar bata ji abunda ‘ƴarta take faɗamata ba, ta kalli Zubaida tace “dauko mata bulala ta zane ni kawai dan naga alamun na ɓata mata rai”

Khadija tace “haba mama, mai ya sa zaki ce haka? kada Allah ya nuna mun ranar da zan ɗaga murya ta a kan taki ballantana hannu na. Kawai dai ina ƙoƙarin fahimtar da ku ne duk budurwar da ta ɗauki dawainiyarta ta ɗaurawa saurayinta tamkar mijinta wata rana shima zai nai mi hakkinsa a wajenta kamar matarsa. Kullum ana faɗamana a islamiyya mu guji abun hanun maza dan mafi yawa ba alkhairi bane.”

Maman khadija ta dubi zubaida tace “Allah ya miki albarka da ki ka karɓo kudin, miko mun su in ba ki rabonki.”

Zubaida, da jin haka ta haɗa rai dan ta san ba abun arziki zata samu ba, watakila bazai wuce dubu ashirin ba. tana miƙa kudin sai ta ci gaba da bayani kamar haka…

“Mama saurayinda yace yana santa daganin shi ɗan manya ne, sai ma kinga irin shigar da ya ke yi dan na saba ganin hotunasa a wayar Ahmad kuma Mama in dai Khadija za ta aure shi to fa kin huta dan watakilama ba’a Nigeria zasu zaunaba dan daga sudan yazo.”

Maman Khadija ta buɗe baki ta yi shewa cikin farin ciki harda guɗa sannan ta kalli Zubaida tace mata “ai aure kamar an yi shi an gama, dan anjima zan tafi da kuɗin nan gidan dan iyaa ya kama mana shi a hannun mu dan kada ya kuɓuce mana”

“Cikin tashin hankali da nuna damuwa Khadija tace “haba mama bakyau zuwa gurin boka fa, dan Allah kar ki je; na miki alkawarin zan bashi daman samun soyayya ta kuma zan kira shi a waya in sha Allahu.”

Maman khadija tace “rufemun baki, wayace miki boka ne? tai mako yake badawa kawai, dan haka sai na je baki isa ki hana ni ba.”

Zubaida tace “gaskiya kam Mama, dan in ya kuɓuce ba ƙaramun asara zamu yi ba.”

Mugun kallo Khadija ta yi wa Zubaida sannan tace “Zubaida ta shi ki fi ta, ki koma gidanku dan Allah nasan inna tana jiran ki.”

Maman khadija tace “rabu da ita Zubaida je ki gidan zan ne me ki, ki mun ƙarin bayani gobe, ke kuma Khadija zan yi maganin ki muddin ki ka ƙi amincewa da sairayin nan; dan baki isa ki rusa mun mafarki na a kanki ba. In da a garin nan na haife ki zance an canza mun ke watakila Zubaida ce ‘yata ba ke ba dan halinmu yafi zuwa ɗaya.”

Muryarta a sanyaye Khadija “tace mama bana jin daɗin abunda ki ke faɗa! amma dai ki yi hakuri kin san ɓanasan ɓacin ranki ko kaɗan.”

Khadija, kinfi kowa sanin halin da muke ciki babanku ya rasu tun kuna yara dangin shi sun ƙi ɗaukanku kuma basa kula da ku, haka na yi rainonku ni kaɗai.
Dangin babanku basa son aurena da shi wai ni musulunta nayi, haka na rayu dasu cikin bakin ciki, mugunta da kuma hassada; ba abunda banganiba na wulaƙanci.
Na aurar da yayunki biyu da taimakon ƙanin mahaifinku wanda Allah ya masa rasuwa mako uku da suka wuce. Mazajen yayyenki ba suda komai sai talauci da tsiya, na yi ta ƙoƙarin fahimtar da su amma suka zabi soyayya akan mahaifiyarsu.
Dan haka ke bazan taɓa bari ki watsamun ƙasa a ido na ba, dan haka dole ne ki auri mai kuɗi damin da ke zan yi alfahari kuma na futo duniya ta sanni.”

Khadija tace “mama duk wani wahala da ki ka sha a baya jarrabawa ce, Allah ne yake gwada imaninki. Ki yi haƙuri kuma ki yi ƙoƙarin cin jarrabawar in sha Allahu sa ki samu lada kuma za ki huta a gidan aljannah domin a gurin Allah kaɗai hutu yake ba’a dukiyaba.”

“Hm! Khadija ke yarinya ce bakisan rayuwa ba, dan haka wannan wa’azinnaki bai samu shiga zuciyata ba kamar dai kullum.” Mama ta faɗa.

Khadija tace “shikkenan, amma Mama ina neman alfarma awajenki”

Maman khadija tace “ina jinki, wani alfarma kenan?”

Khadija taɗanyi ajiyan zuci sannan tace “ina so na rabuda Zubaida dan bata dace da ni ba, bana san ƙawance da ita.”

Maman khadija tace “wannan kuma tsakanin ku, ai kwalliya ta biya kudin sabulu daman na hadaku ne dan naga ta fiki wayewa zata taimakamun wajen samo miki miji nagari mai arziki.”

Jin haka daga bakin Mamanta ya ba ta mamaki matuƙa, sai tace “dama dan haka ki ka haɗamu ƙawance da ita? haba mama wai mai ya sa baki damu da halinda na ke cikiba?
Na yi ta hakuri da Zubaida dan bana son halayenta kuma duk sanda na fadamiki bakya damuwa, Mama ni ce ‘yarki ba Zubaida ba fa.

Maman khadija tace “na sani ai tunda ni na haifeki.”

Khadija tace “shikkenan, yanzu dai ba za kije gurin dan iyan ba ko?”

Maman khadija tace “ba zan je ba, tunda kince za ki bashi dama, amma fa in har naga kin saɓa alƙawari to ni ma zan saɓa nawa alƙawarin.”

Khadija tayi murna sannan tace “in sha Allahu bazan saɓa alƙawarina ba. na gode mama.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba Kauyanci Ba Ne 3Ba Kauyanci Ba Ne 5 >>

1 thought on “Ba Kauyanci Ba Ne 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×